You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farouq ya saki,daga inda yake yana kallonsu,duk kuma da
bayajin abinda suke fadi amma yadda yake kaffa kaffa da ita ya tabbatar masa dude
dinsa ya qarasa zarewa......hauka tuburan na soyayya yasan ya sameshi,baisan kuma
ya za'a qare da lamarin kula da gold da diamond ba,lokaci yayi na daukan sabbin
ma'aikata kenan amintattu na kusa kusa dasu.

Ta bangaren maamah kuwa ta shaqa iya shaqa,wannan karon kasa riqe
ashar dinta tayi sai data furtata,ta furzar da iska tana dan dukan gefanta. Ta
yadda duk macen data taba bariki.masifa ce,abune a jininsu da komai dadewa sai an
saida hali. A nata tunanin sabreen tana sane tayi hakan,tunda ta ganta,tayi ne
kawai don kada su hadu da fu'ad din kai tsaye,tayi ne kawai don ta nesantata
dashi,daga qarshe kuma tayi ne kawai don ta gwada mata tata iyakar.

"Zakiga taki iyakar a sanda kika qare a gidan tabbabbu mahaukata" Ta fadi a fusace
tana qoqarin danne abinda takeji. Tanajin kaman ta saka hannu aka ta fasa ihu,tana
jin kaman yanzu yanzu ta bude ido taga babu sabreen an shafe babinta daga tarihin
rayuwarsu.....akwai lokaci abinda zuciyarta keta nanata mata kenan. Ta yarda da
hakan,to amma shi lokacin yaushe xaixo?,amsar tambayar da bata santa ba kenan.

A nutse ya koma baya yana qare mata kallo bayan ta gama aman tana
wanke kyakkyawar fuskarta da take wani fresh da ita. Ta kammala ta gyara hijab
dinta sannan ta juyo,saidai ba zato ba tsammani ta sameshi tsaye yana qare mata
kallo kamar yau ya fara ganinta.

Qaramar harara ta watsa masa da fararen idanunta,sai ya daga
hannayensa sama alamun surrender sannan ya hade tafukan hannayensa alamun ban
haquri kafin ya sauke yace.

"Kinci wani abune da yake baki reaction?" Ya tambaya da yanayi na seriousness. Dan
shuru tayi tanason tunawa,saidai kuma iya saninta ba wani abu da taci din. Kai ta
girgixa masa tana tsane hannunta da towel din daya miqo mata. Taku biyu yayi ya
matso gabanta,ya cire hannunsa a hankali yana taba fuskarta kafin ya xare ya
xurashi ta qasan hijabinta yana tattaba dogon wuyanta. Abinda ya dauke mata
numfashinta kenan na wucin gadi,don bayan jin temperature na jikinta sai daya hada
da tsokanota har sai da taja baya tana ture hannuwansa. Jirin da taji yasa ta
tsaiwa tadan dafe kanta,kaman walqiya yakai gareta tana riqota jikinsa.

"Idan bazai yiwu ba mu wuce Seychelles......ki qara hutawa a can saimu
samesu......xatafi burgeki akan Maldives" Ya qarasa maganan cikin kulawa. Fararen
idanunta ta sake watsa masa. A abinda take gani cikin idanunsa ba hutawa zai barta
tayi ba,saidai ya qara mata lalura ne kawai. Batasan inane Seychelles ba.......iya
Maldives ma ya suka qare ya kaita qasan ruwa?,ita kuma Seychelles ai qila cikin
cikin kada(crocodile)xasuyi rayuwa. Ta fahimci a son ranshi kowa ya mutu a barsu su
rayu su kadai.

"Muna sake makara" Ta fadi a shagwabe kaman xata narke. Abunda yayi masifar qayatar
dashi,har sai da yaja baya yana gwada yadda tayin. Dariya taso qwace mata amma tayi
hanzarin kauda kanta,sai kawai ta dauki wayarta ta soma takawa zata tafi ta barshi.

"Ganganci ma kenan" Ya fada yana zaburowa ya daidaita tafiyarshi da tata.

Wannan karon farouq suka fara taraswa,suns hada ido da farouq din dai
ya wani basar,yana dauko wannan tsohon dabi'an nasa na miskilanci wa mutane ya
azawa fuskarsa.

"To waye ya damu dakai?" Farouq ya fada yana jifansa da harara,ya maida kallonsa ga
sabreen da kunya ta fara mata qawanya. Tanaso ta zame hannunta ne daga nashi amma
yaqi bata damar hakan

"Madam barka da zuwa......inajin xamu iya wucewa ayi miki screening,minti arbain ya
rage lokacin tashin yayi dama" Farouq ya fada a girmame.

"Izinin wa ka nema da xaka kama yiwa mutane magana da mata?,if kana da wani
important issue da kakeso lallai kayi magana da ita a kai ba gani ba?,dani zaka
fara magana na nema maka izini ai ko?" Fu'ad ya fada sounding seriously. Dariya ta
kama farouq sosai,yaja da baya ya kama kabbara kafin yace
"Dole ne kam,dole ne na nema izini ai.....don ko bugeni kayi na fadi ai ba'a
shari'a da wanda ba cikin hayyacinsa yake ba......madam kiyi haquri
kinji......wannan zama dashi sai me haquri".

" Na rantse harda Allah farouq kana qarawa kanka da kanka kwanakin bikinka ne"
Fu'ad ya fada da gaske gaske,abinda ya sanya farouq ya fara shiga taitayinsa kenan.
Yasan halinsa,idan har yace abu yasan ta yadda zai maida abunnan yadda yace din,shi
kuwa wannan ruwan madarar soyayyar da yaga ana aiwatarwa shi a haramta masa
wanzuwar tasa ai anyoshi......gwara yaje ya dandana shima kam.

"Nif bance komai ba.....daga welcoming naku?.....madam ki qarasa ciki"

"Ba ruwanka......banason kana min magana da mata fa,kana takurata,banaso kana sata
magana.....she's sick".

"Sick?" Farouq ya tambaya,daidai sannan taji xamanta tsakanin drama din farouq da
fu'ad ba nata bane,ta sabule hannunta ta qarfi ta soma yin gaba tana barinsu.

"Dude......ba sake lahani kayi mata ba ko?,wallahi wannan karon anni ba zata barka
ba". Harara ya wurga masa

"Wai sa'anka ne ni farouq?"

"Inafa.....mutumin da yaje inda ni banje ba?" Murmushi ya saki,yasan da gaske
farouq ya damu dashi da lamarinsu ne gaba daya,kowacce tambaya yana yinta ne don
tabbatar da lafiyar kowannensu.

"Juts a fever" Ya maida masa a taqaice idanunsa suna kan sabreen data iss gaban
maamah ta tsugunna tana gaidata.

"Allah yasa qwallonka ne ya fada a raga......zanso naga first born na gold runner"
Sosai maganar taja hankalin fu'ad,sai ya kasa cewa farouq komai yadai bishi da
kallo. Zuciyarsa bugawa takeyi so fast amma yanason dakatar da ita. Bayason maganan
farouq ta masa tasiri,ya tasirantu da cewa shine kuma bashidin bane.

Sautin dariyar maamah a sanda take tsugunne gabanta tana gaidata shi
yaja hankalinta,ta daga kanta a hankali ta kalleta. Qaqqarfan murmushi takeyi da
gaske wanda yafi kama da dariya

"Kin gama naki......ni kuma zanyi nawa" Abinda tace da ita kenan kawai tana maida
kanta ga wayarta.

"Tashi kije yarinya" Hakanan ta samu qwarin gwiwar aje mata murmushi itama sannan
ta yunqura ta miqe tana fadin

"Hasbunallahu wani'imal wakeel,ni'imal maula wa ni'imannasir". Da kallo maamah ta
bita sanda take takawa tana barin wajen. Ta aje mata shakka sosai cikin ranta,ta
sani itadin kuma shaida ce,ba kasafai murmushin yarinyar yake xama alkhairi ba,so
amma koma meye wannan karon ta shirya kawar da ita me gaba daya idan ta kama ayi
hakan.

Amna ce ta rugo da sassarfarta ta kawo mata runguma,abinda ya kusa
sabbaba faduwarsu gaba daya,Allah ya kawoshi ya sanya hannu ya tareta ta fada
hannunsa.

"Ki kula" Ya fada adan dake sannan ya maida dubansa ga amna.

"Be soft with her amna" Kai ta gyada a sanyaye kunya tana kamata. Kwanaki ne kadai
tayi bata ga adda sabreen din ba,amma sai taga ta canza mata gaba daya. Wani
ajiyayyen kyau na musamman,qamshinta da komai nata ya zama wani na daban


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 109



109



a nutse amna ta riqe mata yatsu,duk da yadda ta fahimci fu'ad din kaman
yafi so tabar masa kayansa,to amma itama sabreen ita ta naniqewa,saboda bataso yayi
wani abu daban da zai sanyata jin kunya gaban anni. Tayi imani kuma dukka hankali
da idanun maamah yana a kansu,nunawa ne kawai ba zatayi ba. Abu guda daya daya
tsaye mata a rai,ya gaza barin kwanyarta ta huta duk da yadda takejin jikinta shine
dariyar maamah din. Ta gama karantar kowanne taku da motsi na matar......ta kuma
sake sallamawa al'amarinta daga labarin fu'ad din. Ta tabbatar ba wata halitta da
bazata iya cutarwa ba tunda har ta iya cutar da mijinta da kuma d'anta. Directly or
indirectly tana farautar rayuwar 'ya'yanta ne ba tare da tasan hakan ba. A ranta
taji dole ta qara takatsantsan da ita fiye da baya,sai taji kaman a baya ma kulawa
da kiyayewa al'amuranta da takeyi kaman tayi sakaci,tabbas inda tasan wacece ita
har haka......inda tasan wacece ita irin sanin da tayi mata a yanzu lallai ba
shakka zata kiyaye komai nata fiye da yadda tayi a baya.

"Hannunki dumi adda.....kaman akwai zazzabi a jikinki" Amna ta fada cikin kulawa
dab da zasu qarasa kusa da anni. Kai ta girgizawa amna din tana sanya murmushi
saman fuskarta

"Ba wani me yawa bane......zai sauka in sha Allah,karki gayawa anni ki daga
hankalinta" Dan jim tayi kaman ba zata amsa ba,don bataga dalilin da mutum baida
lafiya ba kuma sannan yace kada a fadi.

Hannu anni ta miqa mata sanda take shirin durqusawa ta gaidata.

"Dawo nan ki zauna" Ta fada qasan ranta wasai da farinciki. Iya yadda taga fu'ad
din ya koma a 'yan kwanakin da baya kusa dasu kadai ya bata tabbacin lallai komai
yana tafiya daidai,ba fu'ad kawai ba.....hatta sabreen din ta canza mata gaba daya.
Fatarta wani glowing kawai takeyi,hakanan idanunta sun qara haske da kuma girma.

Tsananin kunyar anni takeji kaman zata nutse......ko kusa ko alama
yadda takejin nauyin anni yana kamata batajin koda kusa da haka akan maamah,bata ce
kuma ga dalili ba.

"Sai kuma ka buge da sacemin diya ko?" Anni ta fada tana duban fu'ad daya gaidata.
Karon farko shima kunyar anni ta kamashi,tattausan murmushin nan nasa da anni ta
jima bata gani ba ya subuce masa,yasa hannunsa ya shafi baqa sidik din sumarsa da
kudin da take lasa yayi jarin mutane da yawa.
Matsawa amna kadan tayi kusa da anni tana rada mata sabreen din
zazzabi takeyi. A nutse amna ta dubi fu'ad

"Me ya samu ameenatu?" Fararen idanunsa ya sauke kan fuskar sabreen din sannan ya
dubi anni.

"Dan zazzabi ne dazu da zamu fito ya sauko mata......nace ma muje ta karba magana
but ta dage wai zatayi managing" Kai anni tadan kada kadan.

"Manage da ciwo?......to Allah ya sawwaqe,idan muka sauka dubai bai tsaya ba sai
taga likita,ba kyau zama da ciwo ai"

"Ameen" Ya amsa yana satar kallon sabreen din. Jinsu kawai takeyi,amma wani sabon
amanne suketa kokawa dashi.

"Bani ruwa amna" Ta fada a hankali tana tunanin idan tasha ruwan zai fada mata.
Motsin bakinta kadai ya kalla ya fahimci me tace,ya matso a hankali bayan ya karbi
gorar ruwan hannun jordan dake nesa kadan dasu,ya bude mata ya tako inda take yana
tsugunnawa saman qafafunsa yakai robar bakinta.

Tsam maamah ta dauke idanunta tana kullesu gaba daya,qirjinta na sake
bugawa sosai tana jin kaman haki yanason kamata. Zazzabi?.....wanne irin zazzabi
bayan ba'a Nigeria ake ba ballantana ace malaria ce?,wannan tsugonnan bata
ruwan......ko ita da take uwarsa ba zata iya tuna ranar daya tsugunna haka gabanta
yana bata ruwa ba......lallai dole ta batar da yarinyar nan bat daga duniya.

Kai ta girgiza masa alamun xata iya sannan ta karba da kanta. Kurba
uku tayi taji kaman ya isheta,sai ta miqa masa robar.

"Is okay?" Ya fada yana motsa labbansa a nutse idanunshi a kanta kaman me tsoron
kada ta bace masa. Kai ta gyada a kunyace tana saka kanta cikin mayafinta,bataso
batason wannan kallon,halakata yakeyi gaba daya.

"Kai Muhammadu" Maamah data gaza jurewa ta qwala masa kira,tana jin ya kamata ko
yaya tayi wani abu da zata shiga lamarin ciwon don samun report da zai bata daman
aiwatar da duk abinda ya dace da gaggawa.

Tsam ya miqe yana amsa mata,sannan ya fara takawa gabanta sanda
farouq ya iso yana gaya musu lokacin tashinsu yayi.

"Sakamin takalma na......bazan iya durquso ba" Ta fadi tana qoqarin saisaita
fushinta. Baice komai ba ya tsugunna gabanta yana tura mata takalman,ta fara saka
qafafunta a ciki qirjinta a quntace.

"Ita matar taka me ya sameta da ni bani da mutuncin sanin komai saidai naji daga
bakin bare?". Daidai sanda ta gama zura takalman sai ya zare hannuwansa yana shirin
miqewa.

" Zazzabi ne kawai......shima din dazu ne yazo bawai a kwance take ba".

"Zazzabi?,tana iya cin abinci?" Kai ya gyada mata a nutse don baisan me zaice mata
ba,ita sabreen idan ya sakata sahun masu cin abinci ma ya zalunci sakamakon da zai
gayawa.me bincike.

"Akwai tashin zuciya?" Ta sake tambaya cikin bin qwaqwafi da son tabbatar da
zarginta. Kai ta girgiza mata alamun a'ah.

"Ciwon mara ko ciwon ciki fa?" Ta sake tambaya tana kafeshi da idanunta. Kansa ya
mayar gefe kafin ya dawo da dubansa kanta.

"Ban sani ba maamah.... Duka duka zazzabin na awa daya ne".

" Eh dama da irin sakacinnan naku sai ciki ya shiga ya fice abinsa ma baku sani
ba......banason ganganci da rayuwa shi yasa nake tambaya,dama wani aikin ai sai uwa
ita data damu da rayuwar 'ya'yanta damuwa ta haqiqa.......tana yin amai ne?"
Tambayarta ta qarshe da yaji yakai bango,hannuwansa suna zube a aljihun wandonsa
sai kawai ya zubewa maamah kallonsa. Karon farko kenan tun bayan shudewar shekaru
ashirin kusan da hudu rabon daya kalleta tsakiyar qwayar ido irin haka. Komai daya
danganceta yaji yana dawo masa.......gaba daya tambayoyin nan nata basu zama komai
ba face suna sake bude masa wani abu da yake zargi a kanta.

Duk yadda ake maganar kwarjininsa bata taba yarda da gaske yana da wani
irin kebantaccen kwarjini ba sai yau. Idanunsa sukayi mata wani irin nauyi,sai taji
tana daburcewa.

"To Allah ya kawo sauqi,sai a bincika ai aji meye,ko tsohuwar malaria ce" Ta fada
tana miqewa tsaye,wanda hakan bai sakashi dauke kallonsa ba a kanta,har sai da yaji
muryar farouq

"Dude....." Waiwayawa yayi yana dubansa,sai ya nuna masa agogon dake daure a
tsintsiyar hannunsa,wannan shine ya ceci maamah daga irin kallon nasa ya juya yana
nufar farouq din.

"Wai......ka jini da yaro?,haka yakewa mutane?......muje zuwa,na rantse har da
Allah muddin abinda nake zargi ya tabbata ga yarinyar nan bazan taba aminta na hada
jini da ita ba......muddin wani me rai ne a jikinta ni mariyatu bazan bari ya taka
duniya ba" Ta fadi tana cike da fatan ya zamana ma ba abinda take tunani bane.

Amna najin takunsa a bayansu ta zame hannunta daga na sabreen din
ta qara sauri zuwa gaba ta cimma anni abinta suka jera tare. Matsowa yayi yana
daidaita tafiyarta da tashi,ba zato y dauki hannunsa ya aza saman kafadarta yana
jawota zuwa jikinsa.

"Kinga yadda kike tafiya kuwa?,you need my support......dont reject it" Ya qarasa
fada yana furzar da iska.

"Inajin body temperature dinki kaman yana hawa......you need medical
care........banaso komai ya tabaki duniyata" Ya fadi yana waiwayawa ya dora mata
qwayoyin idanunsa. Nauyin nan dai taji,sai tadan basar tana dauke kanta gefe

"Zafin kaman na dazu ne,bai wani qaru ba" Ta fadi saboda batason yace zaa kaita
asibiti. Idan tayi ciwo a Maldives ba zata damu ba......amma ciwo tsakanin makka da
madina bata son hakan ta kasance,saboda qashene da take da burin xuwa a rayuwarta
kafin ta koma ga mahaliccinta.....qasa ce da ta tara tarin shigifar addu'o'i take
kuma kuma son tayi bajakolinsu a nan.....ba zataso wani abu ya kawo.mata tsaiko ba.
Tana da tarin buqatun da batasan adadinsu ba,batasan kuma kwanaki nawa zata shafe
kafin ta gama jerosu ba.

Ba idanun wanda sukayi masa nauyi,a haka suka jera suna taka steps na
jirgin har suka isa ciki. Suna shiga din matuqin jirgin yayi salute nashi sannna ya
bashi hannu sukayi musabaha ya buqaci magana dashi,wannan ya sanya ta zame jikinta
suka jera da amna suna wucewa ciki don samun seat din zama.

Tuni maamah ta yiwa kanta mazauni a executive suit,a nata zaton shine
guri na qarshe da yafi kowanne tsari,batasan sam da VIP suit ba,wanda wada dama
mazauni ne na fu'ad din shi kadai,saidai idan yaso wani ya shigo ya zauna.
A Aminitiy anni tayi zamanta,zaman jirgi ba baqonta bane,amna ma a nan
ta zauna sai sabreen ta zauna kusa da ita suna taba hira abinsu,saidai komai ya
tsaye mata a wuya,hatta ruwan da tasha.

Yana takowa ta tsakaninsu xai wuce VIP suit zazzafan aman ya taso
mata,ta saka hannu da nufin tareshi ta miqe da saurin don wucewa
lavatory.......saidai inaaa,wani karo da tayi da fu'ad din take aman ya qarasa
fitowa ta kuma soma kwararashi tun daga qirjinsa saman lafiyayyar suit dinsa har
saman qafafunsa. Ba wannan bane damuwarsa.......yadda take kakarin amai duk jikinta
yana kyarma shi yafi daga hankalinta,ya bita da sauri a rude yana fadin.

"Subhanallah......ya salam......sannu.....am sorry" Kaman zai sake mata kuka. Yadda
ya kanainaye abarsa su anni sai baya suka tsaya suns jera mata sannu tana ci gaba
da yunquri kaman zata fidda kayan cikinta.

Kafin ta gama kanta ya fara sarawa da wani irin ciwo,zazzabi jikinta
kuma ya sake ninkuwa akan nada.

Shi ya karbi ruwan daga hannun daya daga cikin crew din ya bata tasha
saboda yadda take haki,ya saka hannu ya dagata suka wuce lavatory.

Da idanu take binsa kawai sanda yake qoqarin gyara mata jikinta ba
tare da ya damu da qazantar data zuba masa a nasa jikin ba. Idanunta ta lumshe a
hankali a kansa sanyi yana ratsa gabbanta. Ta dauka zaiyi mata fada,ko zai nuna
fushi saman fuskarsa,ko yayita hargagi idan ta kama ya tureta ma,amma sai taga
sabanin hakan. Gaba daya ya bata attention dinsa,tanaji anni na cewa amna ta biyosu
ko xata tayashi da wani abun yace "no need.....zauna kawai".

Wani irin abu taji yana ratsata a kanshi,ta zuba masa ido sosai sanda
yake goge mata saman qafafunta da takalminta daya dan baci,saita miqa hannu ta zaro
napkins dake ajiye a lavatory din ta tsugunna a gabansa tana daidaita tsahonsu. A
nutse ya dago suka hada idanu,fararen zagayyun idanuwansa sun qara haske wanda suke
sauya launi nan da nan da wani abun ya taba zuciyarsa,sai ta langabe sannan a nutse
ya dora napkin din saman qirjinsa tana cewa.

"Am sorry" Ta furta a hankali. Labbanta yabi da kallo yana jin suna qara
burgeshi,murmushi ya subuce masa wanda ya sake qara fidda kyansa,hannuwansa duka ya
saka ya daga kafadunta suka miqe tsaye,idanunta yake kalla

"Sorry for what?" Shima ya tambayeta muryarsa can qasan maqoshi. Idonta ta janye
tana nuna qirjinsa da yatsarta,sai shima ya maida dubansa wajen. Murmushi ya kuma
saki,ya kamata yana jinginata da jikin mirror din gurin,sannan yaja da baya ya soma
balle button din suit din farkon,ya xareta ya ajiyeta a gefe,ya sake balle button
din ta biyun itama ya ajiyeta a gefe,sai ga shirt din cikin ta ukun ta fito fes ba
abinda ya tabata. Idonsa ya sake dagowa ya kalleta sannna ya daga mata kafadunsa
gami da watsa hannuwa alamun ba abinda ya sameshi. Murmushi ta saki itama abinda ya
kusa narkar dashi kenan,fararen jerarrun haqoranta sun fito reras tamkar adon
lu'ulu'u,har qasan ranta taji dadi da dayar rigar bata baci ba,ya sunkuya a nutse
ya zare takalman qafarsa sai socks kawai daya rage,sai ya miqa hannu ya kama
hannuwanta,a hankali yace

"Kinga abinda nake gudu ko?,zazzabin nan ya dawo sosai".

" Ba matsala......zai"

"Da matsala mana......bakisan yanzun nan sai na rasa nutsuwata ba saboda wannan
zazzabin?" Ya tambayeta da dukka idanuwansa a kanta suna kuma karanta gaskiyar
abinda yake fadi daga qasan zuciyarsa ne. Wani abu na daban takeji,wai yau ita ake
damuwa da ciwonta?,matar da saidai ta damu da ciwon wasu amma nata ciwon dai
damuwar qannenta ne kurum?.

A nutse ya riqe mata hannu suna takowa har xuwa bakin wani dan box,yasa
hannu ya danna ya budeshi,saiga loafers masu kyau ya ciro ya saka a qafarsa sannan
ya kalleta



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 110



110


"Zan iya daukarki mu qarasa?" Kai ta girgiza masa da sauri,sai ya dauke
kai bai sake cewa komai ba.

Qafafunta takejin kamar ba zasu iya daukarta ba sanda daya daga cikin
crew din ke gyaran wajen aman haka taja jiki tana komawa gurin ta. Xarginta yana
sake qarfi da kowanne motsi na yarinyar,amma jikinta da zuciyarta sunqi aminta da
cewa coki zai iya kasancewa a jikinta. Ita ta kawo yarinyar rayuwarsa kuma har
yanxu bata manta da fafatawar da akayi dashi kafin ya karbeta ba......to mene haka
yayi sautin sauya masa ra'ayi game da yarinyar idan ba sihiri bane?. Wannan abun
yafi qarfin bariki......ta samu kalar kulawa da damuwar da ko amernatun bata sameta
ba. Har yanzunda take zaune idanunta suna iya gane mata yadda hankalinsa yayi mugun
tashi da aman da takeyi din,baya jin kunyar kowa dake tsaye a wajen,kamarma ya
manta da wanxuwar kowa a wajen saishi da ita kawai....dole ta lalubo musabbabin
ciwon nan da dukka iyawarta,musaddiq ne kawai kuma zatabi ta kanshi ta samu
information din da takeso hankali kwance.

Tayita zuba idanu ta gansu ta inda su anni ko maamah suke amma sai tsintar
kanta tayi a VIP suit. Ta yita maimaita sunan bayan ganin wajen,wajen yaci sunansa
dari bisa dari,zama rantse da Allah ba cikin jirgi kake ba,don ko windows sai ka
danne wani abu sannan zai yaye maka su. Akwai mini bed da sofas masu tsananin kyau
da taushi a gurin,tamkar kana cikin wani qawataccen madaidaicin parlor maras
tarkace da hayaniya,harda office area da aka yiwa gurin daya ajiye tarkacen kayan
aikinsa kamansu system dinsa da wasu documents nashi.

Gadon yaso tayi kwanciyarta amma taqi,sai ya ajiyeta saman recliner,ya
jawo foot setter din dake qasanta ya dora mata qafanta akai sannan ya lullubeta da
wani sky blue din blanket sannan ya juya a hankali yana fita a wajen ta wata
qaramar qofa.

Numfashi taja sosai tana saukewa,tana yawo da qwayar idanunta cikin
wajen. Wani nutsatsen guri ne da yaci sunan VIP suit din,daga ita saishi a
wajen,guri ne da idan kana nan bazakasan meye yake faruwa cikin jirgin bama. Tabbas
duniya girma gareta kuma fadi gareta,sannan ta sake yarda ta sallama kuma rayuwa
mataki!mataki ce. Daga shigarta family din jadda taga abubuwa masu yawan gaske da
idan a baya akace mata akwaisu a duniya hankalinta bazai dauka ba,da gaske ne kudi
ba wasa bane.....arziqi kuma ba qarya bane......kudi nada wani irin power......suna
mallakawa mutum girma da fadin ikon da baisan iyakarsu ba. Wani lokacin idan ta
kalleshi sai ta dinga jin yafi qarfinta nesa ba kusa ba......ya kuma tserewa
ajinta.....wani lokacin saita dinga jin kokwanto da shakkar sake masa dukka gaba
daya.....kada a gaba ya samu dukkan komai ya kuma zame ya barta tunda tabbas ita ba
ajinsa bace,saidai kuma wucewar kowacce daqiqa da second yana sake bata dukkan wani
dalili na soyayyar gaskiya a aikace ba wai a baki ba. Maida idonta tayi ta rufe
tanajin yadda zazzabin ke ratsa qasusuwanta,gefe guda kuma tana jin irin tababar da
akeyi tsakanin bangarorin zuciyarta dukka akan MUHAMMAD FU'AD JADDA.

Motsinsa taji kafin taji sautin nutsatstsiyar muryar nan tasa da
sautari takan mata gizo.

"I'd appreciate it if everyone could stay where they are,am looking for some peace
and quite,i need some time to myself.......madam bata da lafiya" Yayi maganar cikin
dakiya da miskilancin nan nasa.

"Okay sir" Crew din data kawo masa abubuwan daya buqata ta fadi tana juyawa bayan
ta ajjiye masa. Idanunsa ya daga ya mayar kan farouq daya tsayar daga qofa ba tare
da ya barshi ya qaraso ba.

"Karkace komai.....wannan saqok ba da crew dinka kawai kake ba.....ni akewa jirwaye
da kaman wanka.....aini kaina yanzu nasan kafi qarfina.......system zaka bani zan
rage wani aiki kafin mu qarasa dubai......acan zamuyi layover". Hannu ya miqa cikin
shariya ya jawota ya miqa masa yana kafeshi da idanu,dole dariya ta qwacewa farouq
ya amsa yana komawa.

"Wallahi duk kaci bashi saina rama"

"Can maka" Ya fada yana takowa ciki,sai tayi saurin lumshe idanunta don kada ya
kamata tana qare masa kallo. Rigar ta zauna masa sosai ta fidda muscle dinsa dake
boye a rigar,hakanan ta sake haskashi qwarai,dram dinsa da farouq sai data sakata
murmusawa duk da yadda takejin zazzabin na rarakarta. Shikam yayi sa'a daya samu
amini kaman farouq a sanda yake cikin yanayi na tsanani......ita ta rasa kaman
farouq din,ta kuma rasa abbanta da ummienta,su huda kadai suka rage mata,take taji
wata kewarsu tana kamata.

Tayi nisa a tunaninta ta jishi cikin jikinta.

"Oya.....get up" Ya fada

Please Login or Register in order to submit comment