You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganganunta da lafuzzanta sunfi masa kama da na
mutanen da idonsu ya rufe......mutanen da buqatar gabansu kawai suka sanya a
gaba,mutanen da ba ruwansu da damuwar kowa sai tasu......mutanen da ba wani
burbushi na nadama a tare dasu ballantana dana sani.
"Kiya haquri" Ya jefeta da kalmar da yakejin iya ita kadai kawai zai iya furta mata
don bashi da wani sauran abun fada.

Sake zube masa idanunta tayi tana sake jaddada zallar miskilanci da
taurin fu'ad din. Ba wani alamun sarewa ko saukowa a tare dashi?,tamkar ma an sanya
fetur da ashana an qone dukkan wata qauna ta mahaifiya dake zuciyar kowanne d'a.
Anya ba zancan hajja harira bane akan hanya da take hasashen hadda farraqu hajiya
ameena ta sanya akayi musu?.

"Zanje abuja yau din.....nace bari na sanar miki,sai mun dawo" Ya furta bawai don
yana sanya ran zata masa addu'a ko wani abu daya dace ba,don yana kaiwa qarshe ya
miqe yana gyara hannun rigarsa.

Dan runtse idonta kadan tayi tana hasashen yau dinma kenan babu
nasara?. Da qyar ta iya controlling kanta da fadin

"Sai ka dawo" Duk kuwa da tarin tambayoyin da takeson masa akan me zaije yi
abuja?,yaushe zai dawo?.

Binsa tayi da kallo har ya fice daga falon,taja wani mataccen
numfashi idanunta na qanqancewa saboda bacin rai.....dole suje plan B bata kuma
fatan su isa plan C don zaifi kowanne mataki wahala a gareta dasu gaba daya

"Yaro baisan wuta ba sai ya taka.......yaro man kaza......idan kasan wata bakasan
wata ba" Dukka ta furta a sarari tana daukan wayarta gami da kiran hajja harira.

Cikin wani iri ya dawo cikin gidan. Saidai yayi qoqarin daidaita
yanayinsa lokacin daya isa parlor din anni.

Can babban dining area din dake parlor din ya samesu saman dining. Anni
abba da farouq suna breakfast,yaja kujera kusa da anni ya zauna yana gaida abba da
basu samu haduwa ba sai sannan.

"Abba.....nace ya kamata ace tare muka fara hawa jet dinnan". Dan murmushi ya saki
yana ciro tissue cikin tissue box.

"Nikam wannan jumaar a kibiya zanyita me babban suna......indai muna da rai ai za'a
yita hawa ko don zuwa ibada qasa me tsarki.......yanzu kam ku wuce sabgar
gabanku.....saidai kads ku manta da addu'a,Allah yasa a shiga a sa'a,ya kauda dukka
abunqi"

"Allah yasa a fara hawa cikin sa'a,ubangiji yasa rai aka yiwa" Anni itama ta furta
tana murmushi. Har qasan ranta tana jin dadi gami da jin alfaharin kasancewarta
uwar goyo a gareshi. Koda muhammad bai kasance me dukiya da arziqi kaman haka
ba.....shi din abun alfahari ne ga dukka uwa me hankali......yana da wasu
nagartattu kuma kebantattun halaye na daban da ba kowanne dan adam yake samun
baiwar mallakarsu ba.

Da dukka zuciya da idanu ta takawa hasken idaniyar tata har zuwa
sashen da kowannensu zai hau mota tana rakasu da addu'o'i na neman kariyar ubangiji
da kuma tsarinsa. Abban yau sunyi kibiya shi da musaddiq,wanda dama kusan kowanne
qarshen wata ko sati idan ya samu chance acan yake sallar juma'arshi,hakanan yakan
tafi musu da tarin alkhairai daga arziqin da Allah ya wadatashi dashi bayan wasu
daga cikin 'yan uwan da suke zaune a gidan. Wannan din wata dabi'a tasa ce dake
qara masa farinjini da soyayya wajen al'ummar garin,domin kuwa alkhairinsa ba wai
iya ga 'yan uwansa kadai ya tsaya ba......ya kewaye kowa da kowa.

A saman idanunta dukka motocinsu suka tashi,sai gidan ya rage daga
ma'aikata sai ita sai musaddiq.......sai mutanen dake can boys quarter da ba
kasafai suke iya jiyo motsin abinda ke faruwa cikin ainihin gidan ba ko kuma su aji
nasu.

Idanunsa lumshe cikin jirgin,sanda yake lulawa dasu sararin subhana
daga abujar birnin tarayya zuwa kanon dabo. Abujan da duka duka awa biyar sukayi
cikinta suka fito. Acan sukayi sallar jumaa cikin centra mosque abuja,daga nan suka
wuce unguwarsu fanna.

Rashin sabo da wannan sabgar ya sanya mintuna talatin kawai yayi gidan
ya cewa farouq zan dan kama masauki na wucin gadi da yafi kusa da airport.......zai
tura masa location din sai ya sameshi a can su wuce.

Shigarsa masaukin yayi arba da abinda ya sake tsuke tunaninsa ya kuma
sake dora masa mamaki me azabar nauyi......ya shiga daidai sanda mashkur ne
gangarowa daga sama riqe da wayarsa a mugun gigice yana cigiyar hotonta daya buda
cikin wayarsa. Hoton da yakebin duk wanda ya gani da tambayar

"Don Allah kaga wannan?,yanzun nan ta sauko daga dakina fa.......ta yasheni ta
kwashemin komai daga accounts dina guda biyun". Da irin wannan bayanan ya tareshi
sanda yake yunqurin kiran elevator ya haura dashi zuwa sama bayan yabar guards
dinsa guda cikin reception din.

Duba daya tak ya yiwa hoton ya dauke idanunsa a hankali ya maida
fuskar mashkur da tayi wani irin hautsinewa.....da alana ta zare masa kudi masu
yawan da tsaf zai iya taba rayuwarshi. Wacce irin hatsabibiyar yarinya ce
wannan?,fu'ad ya yiwa Kansa da kansa tambaya sanda elevator din ya qaraso ya bude
ya soma shiga. Har a sannan yana jin muryar mashkur dake bulayin neman wanda ya
ganta.

Lumshe idanunsa yayi yana jin wani mummunan bacin rai yana saukar masa.
Yana buqatar qarin information a kanta abinda ya raya kenan a ransa,ya fiddo
wayarsa yana neman Jordan,sukayi maganganun da zasuyi,dab da zai ajiye wayar kuma
kiran abdus_samad ya shigo masa.

Dukkan wasu bayanai ya karanto masa akan rufai ahmad mu'azzam.

"Caca" Shine alaqar data hadasu da mikail?,ta yaya zai zama mutumin banza yana
zaune kudinsa ya tafi ta qazantacciyar hanya irin caca?.

"Thanks for your effort" Ya amsa masa yana gintse kiran. Still yana shiga dakin
daya kama din kiran saddiq ya shigo masa

"Hamma......mikail keta neman haduwa dakai......" Idonsa yadan lumshe kadan kana ya
bude kaman yadda ya saba a duk sanda ranshi ya baci yake kuma qoqarin hadiyewa

"Ya samawa kansa mafita.....koda bai kawo kanshi ba tabbas zan sanya a kawomin
shi.......bani da time na ganinsa yanzu......sai zuwa Monday......ka tuntubi Easter
kan investigation da na saka suyi cikin company"

"Itama tayi dropping min massage.....tace in sha Allah zuwa Monday din komai zai
kammala"

"Alright" Ya amsa a taqaice kanshi yana sake shiga rudani.

Wannan din shine abinda ya zurfafa tunaninsa cikin jirgin,har sai da
farouq ya magantu

"Wani abu ya sake faruwa ne?" Idanunshin da suka sauya launi ya bude a hankali
sannan ya girgiza kai
"Nothing.....kawai dai kaman akwai abubuwan da nake ganin ba haka ya kamata su tafi
ba.....but everything will be fine". Kai farouq ya kada masa yana dubansa da kyau

"Whenever you need assistance........kada ka manta farouq na side dinka.....am
ready to be a good partner". Dan qaramin murmushi ya sakar masa yana gyada kai

"Na sani tuntuni".

Tun kafin sabreen tayi nisa da gida ta zura hijabinta zuwa gurin daya
gaya mata ta duba zaya ajjiye mata sabuwar waya torch. Yadda ya kwatanta matan haka
ta sameta a wajen,ta dauketa cike da murnar zataji muryar da tayi kewa qwarai ta
wuce zuwa gida.

Murmushi ya saki bayan informers dinsa dake wajen ba dare ba rana sun
shaida masa abinda ya faru

"Yadda zaki bare sabuwar wayar nan yarinya haka zan bareki nan da kwanaki uku kacal
masu zuwa" Yayi maganar cikin shauqi da wassafa ta yadda a ranar zaici karensa babu
babbaka,ya dauki tiyo dake maqale da bututun tukunyar shisha ya zuqi hayaqin har
cikinsa ya fesar,sannan ya kalli matashin dake gefansa.

"Aikinka na yau tunda ta dauki wayar zai fara da tura mata zazzafan saqo da zai
nuna asalin kewa da shiga rudani da rashin jin muryarta"

"An gama oga" Ya fada yana bude wayar ya fara abinda aka umarceshi,shine kuma
kwangilar daya dauko takanas zai yiwa naseer din.

Jikinta har rawa yake sanda ta kunna wayar saqon ya shigo. Tana gama
karantawa taji idanunta sun cika da qwalla,tausayinsa ya cikata.

"Allah sarki bassam.....bazan sake yarda adda sabreen tayi silar yin nesa dani ba"
Tayi maganar yana yunqurin kiransa saiga nasa kiran ya shigo.

A yadda ya marabceta a yau din sai da zuciyarta tayi narkewa da qwalla
ta fita.

"Tun daga ranar bani da lafiya huda.....fargabata na mutu ba tare dana cika muradan
zuciyarmu ba....baqincikina kuma sai na jima a kushewata qilan kafin labarin
mutuwata ya riskeki....."

"Allah ya kiyaye.....in sha Allah ba zaka mutu ba" Ta fada muryarta tana rawa tana
tuna yadda ta rasa abbanta da umminta,yanzu kuma sai ace shi?.

"Ganinki ne kawai zai sanya na warke huda.....ki taimkeni muddin kinaso na farfado
naci gaba da rayuwa kizo na ganki"

"Bansan gidanku ba.....bansan inda zan ganka ba"

"Indai zakizo din huda zan tura miki da adress....ki taimakeni kizo......amma karki
takura kanki daga nan har zuwa litinin,har sai kin gamsu da kanki na cancanci kizo
din na ganki.....".

Ko kusa ko alama bata ji saukar damuwa saman zuciyarta akan mashur
ba,wanda ta tabbatar ta masa gagarumar barnar da zaiyi wahala ya maida gurbinta.

Wani tabbataccen labari data samu a daren jiya akan mashkur shi daya
ya qara mata qwarin gwiwa da jin cewa ya cancanci ta rabashi da komai da yake sanya
shi jin xai iya shiga ko bata rayuwar dukka diya macen da yaso a sanda yaso.
Da confidence dinta take takowa zuwa cikin gidan nasu. Kamar ko
yaushe bata damu d kallon me kallo ba......bata damu da hasashen me hasashe
ba......hakanan bata damu da zunden me zunde ba,ta keta a hankali har ta isa qofar
dakin nasu da tayi tsammanin samunshi a bude saboda lokacin lokaci ne da tasan suna
makaranta a irinsa.

Da mamaki hadi da wata cakudaddiyar fargaba ta murxa qofar ta tura ta
bude tana shigewa,saita samu kanta da takawa a hankali har zuwa qarshen falon.

Ba kowa,kuma wajen yana tsaftace kaman kullum,don haka ta juya tana
sanya kanta cikin dakin tana mamakin waye yake magana haka kaman masu gulma?.

"Nayi maka alqawarin xuwa ka ganni muddin ba'a wata qasa kake ba.....zanzo har inda
kake don ka tabbatar da ingancin son da nake maka!". Qididdigaggun jimlolin da suka
zamewa sabreen tamkar saukar aradu a tsakiyar kanta.

Wuta ce gaba daya taji ta dauke mata sanda take iya hasken waya a
kunne huda.

"Anya huda ce?,meye hakan yake shirin faruwa?,d waye take magana haka?.

"Waya" Taji an rada mata cikin kunnuwanta,abinda ya sanyata xabura ta kuma sanya
hannu ta yaye blanket din da hudan ke ciki,take ta bayyana kwance maqale da waya
tana ta doka murmushin samun abinda zuciya takeso.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 87


Bayyanar haske cikin duhun blanket din ya sanya huda zabura,haduwar idanunta kuma
dana sabreen ya sakata miqewa cikin matuqar kaduwa da zabura har wayar na neman
subucewa,saidai kuma kafin yakai qasa sabreen din ta sanya hannu da zummar
tarota,abinda ya bawa huda qaimi itama takai nata hannun don bawa wayar kariya.

Sabreen din ta rigata samun nasara,batayi wata wata ba ta sanya wayar
a kunnenta,lokacin da Naseer keta faman maimaita kalmar

"Hello......hello baby?" Wani abu taji ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har
zuwa tafin qafafunta. Wannan muryar ba baquwa bace a wajenta da zata iya bacewa
daga kwanyarta.......ba muryar naseer ba......maza da dama da suka taba shiga
qaddarar rayuwarta,suka kuma ratsa ta DUNIYARTA bata wasa da komai daya shafesu
bare ta bari ya bace mata

"Nnn......" Tayi niyyar furtawa,sai kuwa ta dunqule maganar ta hadiye ta maidata
cikinta,ta sauke wayar tana katse kiran sannan ta maida dubanta ga huda dake tsaye
tana fuskantarta idanunta fes kan fuskar sabreen.

"Ki bani wayata adda" Ta tattaro dukka qwarin gwiwar daya rage mata ta furta tana
miqawa sabreen hannu. Saidai maimakon ta bata wayar yadda ta buqata sai ta maye
gurbin hakan da ajiye mata lafiyayyen mari saman fuskarta,sanda take yunqurin maido
hayyacinta cike da matsanancin mamaki ta sake sauke mata wani marin a daya kuncin
nata. Gigicewa tayi duka ta sanya hannayenta ta dafe kuncin nata gaba daya,wannan
baiwa sabreen din ba cikin matsanancin fushi ta turata ta koma saman gadon tayi
zaman dabaro sannan ta bita tayi tsaye a kanta tana damqe hannunta a cikin matuqar
dimuwa da gigita.

"Kinsan waye wannan?,kinsan waye kike tare dashi huda?....kinsan hadarin da kike
shirin jefa rayuwarki dama mu gaba daya?,kinsan waye Naseer?!" Taqarasa fada
idanunta a waje sosai suna nuna girma da yawan bala'in data tarko musu.

Gaba daya ido ta zubawa sabreen din tana mamakin maganganunta

"Wayeshi din?" Hudan ta fada zuciyarta a tsaurare.

"Ba sunanshi naseer ba,sunanshi bassam". Ta sake fada tana ji a ranta ya kamata
itama tayi tsaiwar daka har sabreen din ta fuskanci nata zabin.

"Basma......bassam.....innalillahi" Sabreen ta furta duka a tare tana komawa qasan
dakin gaban hudan ta zauna jabar.

"Tun yaushe kuke tare?,kun taba haduwa?,shine ya baki waya?,dame dame yake gaya
miki?,tun yaushe kike waya dashi?!" Tayi maganar wani irin zafi yana taso mata daga
qasan zuciyarta. Iya kallon da huda ke mata.....iya abinda take gani daga idanun
hudan kawai sun isa bata amsar zuciyarta ta fara soyewa.

"Dake nake magana huda!" Ta furta da wata gigitacciyar tsawa data ratsa hudan ainun
ta cakude da radadin marin da baibar fuskarta ba har yanzu.

"Ki barni yaa sabreen.....ki barmin zabina......bassam ya cancanta,shi nakeso kuma
yayimin alqawarin bani kulawa kaman yadda iyaye ke bawa 'ya'yansu......banyi wani
abu da ba daidai ba fa,kema kin tsara rayuwarki ne daidai yadda kikeso......kina
kuma abinda kk ga dama a sanda kikeso.....ni ko nadra ko haneefa akwai wanda ya
taba tsaidaki ko ya hanaki?,ni mene ma nayi?,abinda ban taba wuce layin bayan
gidanmu ba?,ban taba zuwa hotel ko joint joint ba.....ba'a taba ganina da wani d'a
namiji a cikin mota mun kebe b.......".

Sake saukar wani lafiyayyen marin da yafi na dazu shi ya daukewa huda
dukkan wata kalma da zata ci gaba da fita a bakinta. Marin da wannan karon ya jawo
digar jini daga hancin hudan,muryar sabreen din kuma dake shaking tace

"Huda?.....kinyi hauka ne?,eh idan ma haukar kikayi kisan wadanne kalamai zaki
gayamin.......nice sabreen da na baki tazarar shekara kusan biyar cikin
rayuwarki.....nice sabreen da na sadaukar da walwalata farincikina da martabata
saboda kuji dadi!....nice sabreen dana hana muku kuka......nice sabreen dana hana
muku jin yunwa da wulaqanta.....nice sabreen dana zame muku garkuwa......nice
sabreen dana maye muku gurbin uwa da uba wanda kece ta farko daya cancanci ta zama
shaida akan hakan......na zame miki garkuwa a sanda baki da wani abu na shaawa ko
burgewa a jikinki da d'a namiji zai gani ya burgeshi......na zame miki garkuwa a
sanda baki da wani abu da zaki amfana mini face zallar qauna da 'yan uwantaka fa
fisabilillahi......wanne sauran kulawa kike buqata da ban baki ba?,wacce sauran
qauna ce da tafi wannan girma da fadi?......soyayya huda?.....kin san wanne abune
da yafi tarwatsa rayuwar diya mace?,kinsan wanne abu ne yafi zama girman nadama
cikin rayuwar 'ya mace?,kinsan mene ne mabudin nadama......wahala da azabtuwa da
zuwa da qaddarar da bata sauyuwa cikin rayuwar mace?......ba komai bana face
SOYAYYA kuskure na gaba da rayuwar kaso casa'in dake afkawa shine
AURE......namiji!.....bashi da imani......bashi kuma da tausayi.....namiji BUTULU
ne dake iya bijirewa halasci komai girmansa.......namiji halittar data fi kowacce
halitta son kanta cikin duniya.....halittar da babu imani cikin ruhinta ta fannin
azabtar da ruhin diya mace.......samun salamar rayuwaki ki rayu ke daya.....baki
saka kanki cikin sabga ko sha'anin kowanne d'a namiji ba......wannan wani karatu ne
da rayuwa tayimin bayan gushewar abba da ummina.....mutum na farko da ya fara
qoqarin bata rayuwata shine ALHAJI LAWAN......" Da wani irin kallo huda ta dubi
sabreen,saidai ta kasa furta komai
"Eh....alhj lawan maqoci kuma aboki ga mahaifinmu,......tun daga wannan rana na
fara karatun waye namiji?,daki bayan daki kinsan komai kafin na fara sakaya wasu
al'amuran daga idanunki saboda samun damar saituwar tunaninku.....huda!......dago
kanki ki kalleni da kyau!" Ta furta da gasken gaske,abinda ya sabbabawa hudan duban
nata da idanunta da suka hada hawaye masu yawan gaske

"Ba suna kirana karuwa ba?,ba cewa suke ina yawon ta zubar ba?,ba cewa sukeyi nayi
cikin shege yafi sau a qirga ba?,ina bin maza?,ina sata?,ba haka suke bada shaida
ba?......to na barsu da Allah na kuma barsu da ranar da zasu tsaya gaban Allah su
baida shaida akan hakan......ni aminatu ahmad na rantse miki da girman Allah ban
taba bawa kowanne d'a namiji kaina ba.....ban taba sanin d'a namiji ba ban taba
kwanciya da kowa ba,idan kuma na taba....."

"Aah yaa sabreen" Huda da kuka ya kecewa ta fada da hanzari tana dora hannunta
saman bakinta yayin da dukka hannayenta ke rawa.

Wani qauna da tausayi na 'yan uwantaka ke tsirgawa kowannensu. Daga ita
har huda din hawaye ne da kuka ya ballewa kowannensu har zuwa wani lokaci

"Me yasa kika boyemin wani abu daya shafi rayuwarki huda.....bayan hudubata kullum
a kanku itace.....komai girman matsala ko qanqantarta.....kome girman abu da
qanqantarsa da kukaga alamun zai afka cikin rayuwarku.... Alkhairi ne a idanunku ko
sharri ban yarda a boyemin ba?.....kinsan wayeshi?". Kai kawai huda ke kadawa
ragowar hawayen idanunta suna sauka tana jin wani abu maras dadi cikin qirjinta

"Sunansa na asali shine naseer bawai bassam ba......yayi amfani da sunan bassam ne
saboda sunan dana bashi nawa shine basma a madadin sabreen......dila ne na qwayoyi
da cocaine da dukkan wani nau'in kayan maye,yana dillancinsu da safararsu zuwa
qasashe masu yawa ta wannan qazantacciyar hanyar ya tara duk wata dukiya da yake
qafafa da ita. Ya qware ainun wajen ta'ammali da mata duk kalar wadda ranshi yayi
mishi.....yarinya ko babba musulma ko Christian,koda kuwa ba harkarki bane idan
wani abu a kanki ya darsu zai sanya a dauko masa yarinya yayi mata fyade......a
irin haka muka hadu,kuma na zama sanadiyyar daya buga gagarumar asarar da har yau
ya kasa murmureta bayan kuma ba haka ya tsara ba......yayi zaton ya samu irin matan
barikin da zai kashema kudi ya gama da tenure dinsu ya sallamesu........tashi d'aya
na bace masa bat......yana da balain naci da bibiyar da nayi imani ita ta bashi
daman gano ni wace da inda nake......yayi nufin yin ramuwar gayya ne a kanki
huda....saidai kuma naci alwashin sai nayi silar qarar da ragowar rayuwarsa a gidan
maza tunda har bai daddara ba ya dawo cikin hurumina.......yaso kuma taba
killataccen gold din da hannu vai isa yakai gareshi ba".

Ta sani ta kuma dade da sani zantukan adda sabreen kamar rubutu ne
saman dutse.......bata qarya komai runtsi komai wahala,don haka maganganunta akan
waye bassam naseer sukayi matuqar tsoratata. Jikinta ya sake daukan rawa.....wannan
shine dalilin da ko yaushe yake qoqarin yadda zai shirya haduwarsu tana rushewa?.

"Ki rabu dashi don Allah adda.....kada ki sake jefa kanki cikin hadari.....". Bata
saurareta ba ta jefa mata wayartata zuciyarta na mata wani irin ciwo da kuma son
daukar fansa

"Bakin alqalami ya riga ya bushe......kirashi ki jaddada masa zaku hadu da yammacin
litinin,saidai kice kina tsoron kada a gane kin fita a gida.....kuna da event a
wani guri dab da wajen acan kikeso ku hadun" Tayi maganar tana qoqarin yago paper
cikin wani memo dake saman bedside din hudan tana rubuta mata sunan wajen.

*_LITININ DIN DA MUTANE DA YAWA SUKA CIWA BURINTA.....LITININ DIN DA ZATA ZANA
QADDARORI CIKIJ RAYUWAR WASU,WASU QADDARORIN KUMA DA SUKE ZAMA MABUDIN QOFOFI MASU
TARIN YAWA GA RAYUWAR WASU.....MABUDIN FARA GWAGWARMAYA DA TIRKA TIRKAR DA ZATA JA
MANA RAGAMA HAR ZUWA QARSHEN LITTAFIN NAN.....ZAMU GANI WAYE LITININ DIN ZATA
ZAMEWA FARAR RANA KO AKASIN HAKAN?_*

_KUCI GABA DA BIBIYAR 'YAN MUTAN HUGUMA_🥰🥰🥰



*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*_Matsalarki inda zaki samu ingantattun kayan kitchen na kece raini cikin farashin
rangwame da rahusa me kama da KYAUTA?_*

*CHINA*
*DUBAI*
*INDIA*

_Duk kasu a sanqame a waje daya,amintattun kaya nau'i daban daban masu daukar
hankali don qawata kitchen,siyan daya ko sari_

*_Ko damuwarki kayan kitchen DESIGNERS na alfarma da kece raini?_*

*_maza garzaya cikin gidan HUGUMA UTENSILS UNIVERSE,domin kuwa ta shirya tsaf dom
share muku hawayenku da galla gallan kayan kitchen cikin qanqanin farashi_*


Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/EzM8Qst8A2XAevw3akx5ub
__________________________

PAGE 88


Lokacin da motarsu ke shan kwanar layin nasu wayarsa ta dauki tsuwwa.
Kaman bazai dauka ba amma sai ya miqa hannunsa,saboda duk kiran daya shigo ta
wannan wayar yana da tabbacin yana da alaqa me qarfi dashi.

Sunan Musaddiq ne ke yawo saman screen din. Ya sake zama sosai yana
daga wayar sannan ya karata a kunnensa.

Kafin yace komai muryar Musaddiq din da sautin sallama ya ziyarci
kunnensa. Ya amsa masa a nutse.

"Hamma kun dawo ne?" Ya tambayi fu'ad din

"Muna dab da shiga gida.....wani abu ne?" Siririyar ajiyar zuciya ya sauke kafin
yace

"Hamma muna asibiti" Yanayinsa ne yadan canza kadan ya bude baki yana tamba cikin
fargaba

"Asibiti?,kai da wa?,waye ba lafiya?"

"Maamah ce hamma......muna dawowa nida abba saiga kira da asibiti.....wai an kai ta
ta fadi"

"Ta fadi?" Ya maimaita kalmar cikin mamaki
"Eh hamma" Shuru kaman bazaice komai ba,sai kuma ya sauke ajiyar zuciya

"Me ya sameta?,ko kuma me sukace yana damunta?". Kai Musaddiq ya girgiza yana sauke
idanunsa akan hajja harira,sai ya miqe kuma a hankali yana tura qofa ya fice daga
dakin.

"Wasu bayanai likitan ya fara,saidai yace yana da buqatar ganinmu ni dakai a tare
don yayi mana gamsashen bayani"

"Alright.....zan shigo" Ya amsawa Musaddiq yana sauke wayar a kunnensa.

Guri daya ya zubawa ido yana kallo qwaqwalwarsa na tafiya zuwa wani
nazari. Ya bude bakinsa a nutse da zummar bawa driver umarnin wucewa asibitin,sai
kuma ya lumshe idonsa yana tuna wani abu daya faru a shekarun baya wanda sai daya
sanya shi sauke wani numfashi me nauyi,kana a hankali ya hadiye kalmarsa yana maida
idanunsa ga gate din gidan da suke dosa.

"Waye a asibiti ba lafiya?" Farouq da yake amsa waya sanda fu'ad ke wayar ya
tambaya bayan ya kammala wayar yana duban fu'ad

"Maamah ce" Ya bawa farouq din amsa a gajarce ba tare daya kalli farouq ba.

"Maamah kuma?,amma inaga ya kamata ace mun juya akalar tafiyar tamu zuwa asibitin
ko?"

"Ba yanzu ba farouq.....na gaji,sai na huta tukunna......kaina kaman zai tsage da
abubuwan dake cushe akai".

"Duk da hakan bai zama hujja na kasa zuwa dubata ba.....ka huta din idan mun
dawo......janar....." Ya qwallawa driver nasu kira wanda ya rage gudun motar saboda
kawowarsu tafkeken gate din gidan alhaj hamza kibiya

"Sir" Ya amsa masa a a ladabce

"Juya motar nan mu koma titi" Ya bashi umarnin idanunsa saman wayarsa yana lalubar
number wayar Musaddiq don yaji a wanne asibiti suke?,don ya tabbatar yace fu'ad zai
tsaya tambaya zai bata lokacinsa ne kawai.

"SAMHG hospital kuke?" Ya tambaya Musaddiq ga zaton suna can din. Kebantaccen
asibiti ne da ake duba iyalin gaba daya bayan asibitinsu na cikin gida da fu'ad
keson maidashi babba ya fadadashi sosai cikin sabon ginin mansion house din da yake
musu yanzu haka

"Okay.....turon address din" Ya fadi yana kashe kiran.

A haka zakayi zaton kunnuwa da hankalinsa basa tare da farouq din,saidai
kuma har yayi wayar ya gama yana saurarensa. Ta yaya za'a kaita wani asibitin da ba
nan ne asalin inda kowa yake zuwa ba?. Tambayar da ya samu wani guri na musamman
cikin kwanyarsa ya adanata.

Kira farouq din ya sakeyi,a wannan karon anni ya kira. Dab da zata
tsinke ta daga da cikakkiyar sallama da muryar nan tata ma'abociyar kwarjini da
nutsuwa.

"Mun dawo anni.....amma mun wuce asibiti dubiya,kada ki jimu shuru"

"Waye ba lafiya?" Ta tambaya cikin kulawa

"Maamah ce" Ya amaa mata kai tsaye
"Subhanallahi......amma ba wanda ya sani cikin gidan nan......ince ko jikin nata da
sauqi?"

"Ban sani ba anni,sai munje yanzun zamu gani"

"To don Allah kuyi mata sannu,idan akwai wani abun kuyi gaggawar sanar mini"

"To anni" Ya amsata yana sauke wayar. Dubansa yakai ga fu'ad,har yanzu waje daya
yake kalla,yadda yayi dif

Please Login or Register in order to submit comment