You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sulalewa tayi ta zauna saman sofa din,koda farouq yace ta fara shiga
batajin zata iya hakan,gwara a cikinsu wasu su fara shiga din,yanayin fuskar
kowannensu shine zai bata qwarin gwiwar shiga ko akasin hakan.

Kaman anni zatayi magana sai kuma ta fasa,ita da abban sukayi gaba
farouq yana musu jagora suka buda qofar suka shige.

Zaman jiran fitowarsu annin ba wani abu bane me sauqi a wajenta,sai
ta jita tamkar tana zaman jiran isowar layin mutuwa kanta,kanta a qasa ta saka
hannuwanta dukka biyun ta dafe kanta tana jin yadda zuciyarta ke harbawa kaman zata
fado qasa. Wani motsi takeji mararta tanayi,baqon abune da bata taba jinsa ba sai a
ranar kamar ana d'allinta da yatsa.

"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ta
dinga maimaitawa labbanta kadai ke motsawa. Da yatsunta ta dinga irga kowanne
wucewae second,tanajin kaman suna wucewa da kowanne dama na rayuwarta,tana jin
kamar suna wucewa ne da farincikin rayuwarta gaba daya.

Sai da su abba suka kwashe mintuna kusan goma harda doriya kafin taji
fitowarsu. Duk yadda taso daga kai ta kalli reaction na fuskarsu ta gaza yin
hakan,ta kasa koda motsawa,tana jin tsoron abinda zata daga ta gani tattare dasu.
Saidai takum tafiyarsu su biyun bata tsinci komai a ciki ba,karsashi ko akasin
hakan,wanda hakan ya sake sanyata a taraddadi me yawa da kokwanto.

"Ni zan shiga" Ta fada da wani irin fusgar kalma cikin ba zata a sanda saddiq da
musaddiq ke takawa zuwa qofar dakin.

Miqewa tayi ta zauna sosai tana dubansu sanda suka dakata daga shigar
da juyyayyun idanunta,tana jin kamar kafin su shiga su fito zata iya rasa
numfashinta da rayuwarta gaba daya,koma meye gwara ta shiga ta gani ta kuma
fuskanceshi da.dukkan iyawarta,da wannan qudurin ta taho,ba kuma zata iya canzashi
ba.

Da baya suka dawo,ba wanda ya musanta mata ko yace wani abu,saita
miqe a hankali tana jin kamar qafafunta ba zasu dauketa ba ta doshi dakin.

Ta kusa sakkani talatin riqe da handle din ta kasa murzawa,har sai da
muryar farouq dake bayanta ta dawo da ita daidai

"Are you okay?" Ya tambayeta yana leqen fuskarta. Kai ta gyada masa.

"Ko na bude miki?" Ya sake tambaya cikin kulawa saita girgixa kanta ta kuma tattara
gaba daya qarfin daya rage mata ta murda qofar tana shiga.

Jijiyoyin jikinta ne taji tamkar suna tsinkewa,numfashinta kamar an
musanya mata da wani abun daban me tauri bawai lallausan iskar da kowanne me rai
yake shaqa ba. Ta dinga ganin idanunta kaman gizo suke mata,ba ainihin abinda zata
gani bane take gani......gani take zolayarta kawai idanun nata sukeyi saboda abinda
take kwana ta tashi da fatarsa kenan.....abinda take kwana ta tashi tana mafarki da
burin ya kasance kenan.

Yana zaune saman gadon da aka tallafo bayansa aka dago kan gadon
sosai yadda zaiji dadin zama. Jikinsa sanye da rigar asibitin ruwan sararin
samaniya me haske sosai. Lallausan blanket ne lullube da qafafunsa zuwa qugunsa.

Fararen idanunsa tarr bisa fuskarta,idanun da suka dan rusuna kamar
wanda bacci yake cike a idanun nasa. Kallon kallo ya wanzu a tsakaninsu,zukatan
kowannensu yana bugawa da sauri da wani irin doki da zumudin ganin daya bangaren
zuciyar tasa.

Wasu irin abubuwa ya dinga sakar mata suna ratsa sassan
jikinta......wani irin shauqi mahaukaciyar soyayya da zazzafar qauna ke kurdawa ta
kowanne lungu na zuciyarta. Kewarsa me matuqar qarfi ta taso ta lullube zuciyarta
ta sakata jin wani rauni na mamayarta,take idanunta suka cika da hawayen da bata da
ikon tsaidasu.

Hannunsa daya ya miqa mata yana ware mata su alamun marabtarta
yakeyi,cikin wani irin zaquwa da dokin isowarta gareshi,batayi wata wata ba ta soma
takawa da sassarfa zuwa inda yake tana jin kaman lokacin isarta inda yake ma ya
mata yawa.....inama zaiyiwu ta zama walqiya cikin qiftawar idanu ta samu isa
gareshi.

Jikinsa ta fada gaba daya kuka yana qwace mata,tsam ya riqeta cikin
jikin nasa yana mata kyakkyawan masauki zuciyarsa na tsananta bugu cike da wani
bahagon so,idanunsa suka dinga lumshewa da kansu,dumin jikinta yana ratsa qashinsa
bargo harda jinin dake harbawa kowanne sashe na jikinta. Hannunsa daya ya sanya ya
riqo fuskarta,idanunta yake son kallo,qwayoyin idanun nan nata da yayi matuqar kewa
yakeson gani.

Bata hanashi ba,ta daga oily eyes dinta masu sheqi da suka jiqe da
hawaye tana kallonsa. Nutsewa idanunsu sukayi cikin na juna,wani irin feeling ke
ratsa kowannensu wanda yafi qarfin baki ya bayyanashi. Wani deep connection ya
qullu a tsakaninsu,magana ce tsakanin zuciya da zuciya kawai wadda tafi qarfin baki
ya bayyanata. Idan ya motsa labbansa sai yaji sun masa nauyi.....sai yaji kaman
sunyi kadan su isar da saqon da zuciyarsa keson fadi

"Sabrrrr" Ya samu ya fusgi kalman da qyar zuciyarsa naci gaba da bugawa. Itama
kaman zai bace mata takeji daga qiftawa qwaya daya tak da zata yiwa idanunta,don
haka ta motsa labbanta ba tare da amsar NA'AM din da takeson furtawa ta fita a
bakinta ba.

"Love is in the eyes.....eyes don't lie.....sabrrrr.....kalli idona.....me kika
gani?" Ya motsa labbansa ya fada da wata irin narkakkiyar murya irin wadda soyayya
ta yiwa lahani.

Inda yasan yadda qwayoyin idanunsa suke narka mata bargo da bai buqaci
ta kallesu har haka ba....saidai kuma kallon nasu wani abune na musamman cikin ruhi
da zuciyarta. Ci gaba tayi da kallon idanun nasa.....taga abubuwa masu tarin
yawa.....taga abubuwa masu yawan da sai da taji kaman zata zauce,duka ita daya?,duk
ita daya muhammad fu'ad kewa wannan zazzafan son?.
Hannu ya kama ya riqe kumatunta yana aza shimfidadden murmushi kan
fuskarsa.

"You're a thousand miles away.......but no one else is closer to my heart than you
are" Ya qarasa fada yana kama fuskarta sosai gami da hade goshinsu guri daya.

Musayar numfashi suka fara yi a tsakaninsu,kowanne yana shaqar
numfashin da dan uwansa ya fesar,hakan na sake qara musu wani qaqqarfan alaqa
tsakaninsu data tsananta bugun zuciyarsu duka su biyun.

"Zan iya mutuwa.......Allah zan iya mutuwa idan ka sake matsawa daga gareni irin
wannan matsawar da kayi.......zaka iya rasani......ka rasa kuma babies dinmu gaba
daya" Ta qarashe maganar tana sakar masa kukan da ya koma zuwa na shagwaba kuma a
wannan lokacin.

"Nayi alqawari DUNIYATA.....nayi alqawari bazan qara ba,i promise" Fuskarta ta
qwace ta cusata cikin qirjinsa tana shaqar wannan tattausan qamshin nasa da tayi
matuqar kewa kamar zata zauce.

"I pray to god that you will stay permanently in my life".

"I pray too my world" Ya fada yana kissing tsakiyar kanta. Qanqameshi tayi da kyau
don sake bawa kanta tabbacin reality ne bawai mafarki ba. Kalmar "wash Allah na"
Daya fada ita ta sakata saurin sakinsa tana kallon fuskarta.

Idanunan dai nashi ya zuba mata murmushi na fita a fuskarsa,sai ta
tabe baki kaman zata saki kuka. Da sauri ya mata nuni da hannunsa,ta waiwaya a
hankali zuwa sashen da yake nuna mata din.

Miqewa tayi ta zauna da sauri saidai ya hanata hakan,ya jawota jikinsa
ya maidata sosai yadda zaici gaba da jin qamshinta da duminta.

"A nan suka harbeka?" Ta tambayeshi a sanyaye da wani irin emotion na bacin rai
saman fuskarta. Girarsa kawai ya dage mata yana dubanta har yanzu fuskarsa da
murmushi duk da yadda yadan fada kadan.

"Allah ya isar mana....Allah ya saka mana"

"Very soon duniyata......mu ajiye wannan maganar yanzun......i need you
duniyata.....kaman dazu naji kince babies instead of baby right?" Ya tambaya yana
tsareta da idanunsa. Tsam tayi tana dubansa,sai kuma ta saka tafukan hannayenta
duka biyun ta lullube fuskarta dasu.

"Yes......twins n....." Bata qarasa fada ba taji yana lalube rigarta,saidai jikin
ba qwari kwata kwata da alama don haka ya ajiye hannun nasa yana maida numfashi.
Koda ta kalleshi kwantaccen hawaye ta gani saman idanunsa,batasan me yasa akan duk
abinda ya shafeta ba shi rago ne na gasken gaske.

"Please sabrrrr......ki dagamin rigar na gani,haka Allah ke sona?" Yadda yayi
maganar da gaske abun ya taba ranshi,ba zata iya hanashi ba,don haka ba musu ta
miqe ta yaye abayan jikinta,tayi qasa da under wear dinta take farar fatar cikinta
ta fito. Jawo qugunta yayi sosai,a hankali ya aza labbansa saman mararta.

Har tsakiyar kwanyarta taji wani yaarrrrr,wani abu ya tsarga mata ya
saukar mata da wani irin yanayi a sassan jikinta. Lips dinsa nakan marartata ya
daga idanunsa ya kalli yanayin fuskarta,kunya ta sakata runtse idanunta sai ya aje
mata tattausan kiss sannan ya janye bakinsa ba tare daya saki rigar ba. Batasan me
ya karanta ba,amma ya kusa mintina biyu bakinsa yana motsi kafin ya matsa kusa ya
tofa mata abinda ya karanta din,ya sake kai hannunsa ya aza akai ya sake karanta
wasu addu'o'in sannan ya sake mata rigar.

Still hankalinta yana kan hannunsa,tayi taku biyu zuwa wajen ya sake
jawota jikinsa

"I really missed you......kiban koda 10minutes naji duminki......ban taba zaton zan
sake rayuwa ba......dazu na tashi daga suman da nayi duniyata" Yayi maganar yana
aza kansa saman kafadarta,yana jin ya samu wani peace daya dauke masa duk wani abu
da yakeji a jikinsa da zuciyarsa.

Idanunta sukayi rau rau da hawaye

"Ko waye wannan bazan taba yafe masa ba.....ko wayeshi" Ta fada muryarta tana rawa.
Ya buda baki zaiyi magana muryar farouq ta ratso dakin,yadan bude qofar kadan amma
fuskarsa da idanunsa sun basu baya.

"Su musaddiq kuwa zasu samu yin dubiyar nan?,ko kuma su koma kawai sa dawo?".
Sassanyan numfashi ya aje kafin ya motsa labbansa.

"Bansan me yasa baka da imani ba farouq....aidai ka tausayamin ko?.....na yafe
dubiyar,kaima ka bisu kuje ku huta......thanks so much dude". Baki kawai farouq ya
sake,ya dauka fu'ad din zai tuna dasu anni a wajen ya sakaya zancansa?.

" Dama shi dan adam butulu ne ai,na maka welcome to the world ai
ko?,alright.....but kasan hannunka yadda yake......yana buqatan a kula
dashi.....still itama me jinyar taka ba'a dade da sallamarta daga asibiti
ba.....banajin she can take good care of you".

"I can BB.....i can wallahi" Sabreen ta samu kanta da fadin haka ba tare da wani
kunya ko d'arr ba.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 127


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA
KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA
IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE
SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA
A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*


127



"Pay no attention to him,brush him off" Fu'ad ya fadi yana
lalubenta,abinda ya dameshi kawai shine yaga abinda ya sameta don yaji farouq yace
bata da cikakken lafiya.

Fes farouq yaji abinda dukkaninsu suka fada,ya jijjiga kai yana mamaki

"Fu'ad......farouq ne fa?,lafiyanka nake magana kana gwaleni?". Hannun sabreen ya
kama ba tare daya waiwaya sashen da farouq ke tsaye ba,a yanzun baya buqatar
kusanci da kowa idan ba ita ba.....idanma akace wani zaya zauna dashi a dakin ai
yana ganin an gama zaluntarsa. Yasan tsiyar farouq tsaf zaice shine zai zauna dashi
saboda mugunta,yadda ta gayawa farouq kai tsaye zata iya kulawa dashi ya matuqar
burgeshi,don haka ya qara encouraging nata.

"Take what he says with a grain of salt,dont let him get to you" Ya fadi yana sake
juya hannuwanta yana dubawa.

Salin alin farouq yaja qofan yana wucewa,saidai a ransa ya ayyana dashi
fu'ad din yaci tuwo,zaisan kuma miya yasha


"What's wrong with you my world?" Ya tambayeta yana tallafo fuskarta,yaga alamun
bata fahimta ba sai ya canza salon tambayar.
"Farouq.....yace baki da lafiya.....da gaske ne?" Murmushi ta sakar masa,ta miqa
hannunta a nutse tana kama habarsa me cike da kwantaccen gashi.

"Kana tunanin zan iya lafiyayyar rayuwa sanda ake shaidamin muffin dina yayi batan
dabo cikin DUNIYARSA?" Tambayar ta sanya murmushi kubce masa shima,ya girgiza kai
yana kallon zara zaran eyelashes dinta.

"Wannan ciwon nayi.....amma daga yau na warke in sha Allah". Knocking na qofar da
akayi shi ya katse musu wannan daddadan tattaunawar,ya kalleta yana dan hade rai da
alamun gajiya da rashin jin dadi a fuskarsa.

"Inda zai yiwu.....zan sanya a sauyamin dakin da babu wanda ya sanshi bare a
dameni" Idanu ta waro waje tana miqewa a nutse.

"Da BB yace na hure maka kunne....kuma daka cika me butulci".

"Kibar ganin farouq haka duniyata....zai iyayin abinda yafi nawa"

"Qarya kakemin......kunyarka tafi tawa yin qaranci" Muryar farouq din ta ratsa
dakin sanda sabreen ta bude musu,itadai sai tayi baya tana boye fuskarta. Da idanu
kawai ya bita yana sake ganin ta canza masa,ko takan tsiyar da farouq keyi masa da
raddin da yake maida masa baibi bama sam sam.

Likitansa ne ya shigo a bayan farouq din,sai fu'ad ya kimtsa yanayin
fuskarsa ta hanyar rage fara'arsa yana duban sabreen.

"Ki shiga toilet ki gyara lullubin kanki sosai.....banaso ko gashi daya ya fito" Ya
qarasa fada yana maida dubansa ga likitan wanda dauke idanunsa kenan daga kan
sabreen din.

Fuska a hade fu'ad din ya kalli farouq sanda likitan ke buda qirjinsa
yana auna gudun zuciyarsa.

"Ka gaya masa,He should look down when she's around,matar aure ce".

"Tashin hankali" Farouq ya fadi,yasan ba qaramin daru za'a sha ba.....kowa ma sai
ya shiga uku muddin duniyarsa tazo......wannan ya sanya yaso ya boye har sai ya
fara samun lafiya da kuma sauran dalilai na tsaro da sukeso su gama binciken duk
wanda keda hannu a cikin attack din ba tare da kowa ya ankare ba. Yasan da biyu ya
fadi ragowan maganan da turancin englishi,dole yasan likitan zai fahimci wani abu.

Sanda ta dawo daga toilet din gyaran mayafin kujera farouq yaja mata
yace

"Zauna a nan" Ya fada yana ajiyeta kusa dashi. Likitan yaci gaba da duk wani dube
dubensa,ya kammala yayi rubuce rubuce ya ajiye file din ya fita farouq ya bishi.

Idanunta still akan hannun,har yanxu tana jin ciwon kaman cikin
jikinta,yanzu kenan ida harbin ya subuce ya sameshi a inda ba'aso yanzun da wani
zancan daban kenan akeyi?.

"Subhanallah" Ta samu kanta da furtawa tana dauke idanunta sai caraf suka fada
cikin nasa. Abinda bata sani ba kallonta yakeyi da duk wani motsi nata. Ya miqa
mata hannu yana daga kwance rigingine. Kafadarta ta noqe tana dubansa a shagwabe.

"Kasan wadanne irin wahalallun kwanaki na dinga yi cikin duniya kuwa?" Idanunta
suna tara hawaye har batason tuna wannan kwanakin.

"Inda nine inajin da tuni fargaba ya kasheni.......kinsan adadin son da nake miki
kuwa?" Kallonsa take har bata qiftawa,tanason gwada ma'aunin sonsa a zuciyarta da
yadda yake iqirarin nashi yafi nata.

"Kina tantama ko?" Ya tambayeta da murmushi,kafin wani ya sake cewa komai a cikinsu
an sake shigowa.

Anni ce da musaddiq saddiq abba da farouq gaba daya,kunya ta
lullubeta,tayi qasa da kanta tana niyyar tashi a wajen anni tace

"Yi zamanki" Suka koma saman ragowar sofas din dake dakin suka zauna. Duk
budurinnan gogan idanunsa yana kanta bai iya dauke idanunsa ba sam sam.

Sabuwar gaisuwa da jaje suka sake yiwa juna,dakin yayi shuru sanda
farouq yake bada labarin yadda abun ya kasance.

"Kaman gawa mukazo dashi abba......dazu da safe ya farka......amma ko jiya da
daddare bayan an gama wasu test likitan ya sake jaddada mana abinda suka shaqa
masan guba ce me qarfi....kuma idan ya wuce yau bai farka ba ICU zasu
maidashi.....cikin hukuncin Allah sai gashi ya farka da yake yaji a jikinsa
duniyarsa tana hanyar zuwa gareshi". Kunya sosai ta sake kama sabreen,tayi qas da
kanta tana jan mayafinta. Abba da annin duka dariya kawai sukayi,saddiq ya bude
abincin da sukayi takeaway da complete set da plate da spoons ya soma zubawa kowa
ma'u tana tayashi.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 128


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA
KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA
IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE
SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA
A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*

___________________________


128



ma'u tana tayashi. Parlor abba ya fita don amsa waya,sai sukaci gaba da
tattaunawa a tsakaninsu.

Zukata sunyi sanyi sun kuma samu nutsuwa daidai gwargwado,sauran abinda
ke cikinsu bashi da yawa,godiya kawai sukema Allah daya tsallakar dasu daga
fuskantar wannan bala'in.

Idanunsa yake saukewa a kansu,kowa cikin walwala yake da farincikin
samun kubutarsa.....kowa kuma a cikinsu soyayya da qauna ce irin ta fil'azal
tsakaninsu,amma abu guda dake taba zuciyarsa shine sam ba MAAMAH ba dalilinta.
Maman daya kamata itace a gaba kafin kowa?,maman daya dace a bisa mizani na hankali
dacewa da kamata ace itace damuwarta ta dara ta kowa.....ta d'ara ta babarsa
anni.....ta d'ara ta 'yan uwansa,ta kuma d'ara ta matarsa......saidai sabanin hakan
maamah din itace halittar da tafi kowacce halitta rashin damuwa da yanayin nasa,sai
ya maida idonsa ya rufe yana jin wannan zafin har tsakiyar zuciyarsa.

Saddiq ya gama da kowa farouq ya dubi musaddi

"Zubawa dude ka bashi ko kadanne ko zai karba". Harara fu'ad ya zubawa farouq,yaso
ace su anni basu wajen da ya bashi amsa daidai dashi. Idanunsa ya juya a hankali
inda sabreen ke zaune tana juya zoben dake yatsanta,don ita ba kowanne abinci take
iya ci ba.

"Ke ba zakici abincin ba?" Ya fadi da wata murya can qasa yana mata kallon qurilla.
Sau daya ta dago kai ta kalleshi ta mayar qasa tana ci gaba da juya zoben hannun
nata.

"Na qoshi". Motsawa yayi kadan yana son gyara zamanshi.
"Zubo kizo nan" Ya sake fada ba tare daya dubi inda anni take ba.

"Yauwa....gwara ka tilastata taci,ko ba yawa aizai zauna,ta yaya kina da lalura
amma cin abinci ya zama yaqi ameenatu?". Idanunsa ya sake maidawa kanta,sunan
ameenatu yana masa dadi sosai,idan ya kalli fuskarta yakuma ambaci sunan sai yaji
tayi bala'in dacewa da sunan,musamman idan ya tuna tarihin asalin me sunan.

A kunyace ta miqe,ta zuba komai dan kadan kadan sannan ta dawo.

"Zauna a nan" Ya nuna mata gefansa. Dan satar kallon anni tayi kafin ta zauna din
tana bada tazara kadan tsakaninsu sannan ta ajiye plate din a tsakiyarsu.

Spoon ta zura masa a ciki ta kalleshi,sai ya langabe kai yana bata
fuska.

"Bazan iya ci ba.....aikinsan bani da lafiya ko?" Sai kuma yayi qasa qasa da
muryarsa yana satar kallon farouq.

"Idan kuma so kike farouq yayi mana dariya ya yadda da gaske ba zaki iya bani
kulawa ba to".

"Anni muffin.....anni a gurin"

"Kada ki damu,ita hirartama take dasu saddiq,ita kanta zatafison taga kina kula
dani......oya bani abinci" Ya fada yana lumshe idanu saboda yadda yakejin wani
yanayi yana ratsashi.

A d'arare ta debo abincin ta taho dashi bakinsa,sai ya kauda kai
yana kallonta.

"Eat first" Ya fadi yana tsareta da ido. Fuska ta bata,batasan ta shagwabe masa ba
tace

"Hamma.....bazan iya ci ba".

"Zaki iya.....zakici in sha Allah,kada kiji tsoro" Ya bata tabbaci yana kallonta.
Da kadan da kadan ta dinga miqa cokalin bakinta har ta juye abincin,ta soma taunawa
tana rolling idanunta cikin tsoron kada amai ya biyo baya,sai taji zuciyarta ko
cikinta basu wani hautsine ko juya ba yadda suka saba ta hadiyeshi tsaf.

"Good girl.....am next" Ya fada yana gyaran zamanshi. Debowa tayi ta miqa masa,ya
bude baki ya amshe kaman qaramin yaro.

"Hmmmm........dadin abincin daya fito daga hannunki daban yake......ban taba jin
abincin da yayi dadin wannan ba......Allah ya qarawa hannuwanki da rayuwarki
albarka". Ya fada yana lumshe ido a kanta.

"Ameen" Ta amsa tana sadda kai tana satar kallon dakin. Wayam ta gani,ba wanda ta
samu a dakin duka sun fice ba tare da tasan sanda suka fice ba,saita dawo da
dubanta kan fuskarsa idanunta a warwaje. Dariya me qaramin sauti ya saki

"Sun gudu......they can't wait to see" Fuska ta tabe ta kyabe baki kaman zata saki
kuka

"Kaga irinta ko?"

"Wayyo Allah hannuna" Ya fada shima yana karyar dakai gami da riqe hannun da daya
hannun. Tuni ta watsar da komai tayi wajen tana riqe masa a rude.
"Sannu.....da zafi ko?,fama maka nayi?,yi haquri.....ko a kira Doctor" Yadda ta
fadi doctor din sai labbanta suka masa wani mugun kyau. Lallausan kiss ya saukar
mata saman lips din yana dariyar yadda ya cita wasan,ya samu hanya mafi sauqi na
sake kusantar da kanshi da ita.

Sai kusan dare can sosai sannan su anni sukayi niyyar wucewa masaukinsu.
Ya tsareta da ido ganin tana hada jakarta da tarkacenta,a ransa yakejin muddin tace
zata wuce tabi su anni saidai su tafi tare,don kuwa bazai zauna ba shima tana wani
gurin yana wani muhallin na daban.

Kamar anni tasan abinda yake tsarawa,ta ciro wani babban envelope ta
aje mata a gefanta.

"Ga magungunanki nan.....kada ki kwanta baki sha ba.....mun wuce gida mu,sai gobe
idan Allah ya kaimu.....saiki kula dashi....muhammad Allah ya qara afuwa,sai da
safe". Har baisan sanda murmushi ya kubce masa ba,yasa hannunsa me lafiya ya shafi
kansa.

"Ameen anni,na gode sosai,Allah ya qara girma" Ita kanta annin tasan godiyar da
biyu ake mata ita,batace komai ba dai ta shanye,har sunkai qofa ta waiwayo.

"Ki kula da kanki da kyau,kada ki manta da abinda likita ya fada" Ta qarasa maganar
tana sauke dubanta kan fuskar fu'ad. Ko batayi maganan kai tsaye ba ya fahimci shi
anni ke ajiyewa saqon,saboda haka suna fita ya jawota jikinsa yana cewa.

"Ni za'a yiwa gulma?,wai anaso ana kaiwa kasuwa......kinsa anni ta tsareni da
warning,wannan maganar da biyu aka yita,kuma dani ake nasan......ita anni ta
jikokinta kawai take bata ta d'anta" Ya fadi yana sansana kunnenta,abinda ya sanya
tsigar jikinta xubawa,ta yunqura da niyyar gocewa a jikinsa,sai ya fake kaman yadda
ya saba.

"Wayyo hannuna" Dawowa tayi da sauri ta zauna tana masa sannu.

"Muga hannun.....idan yana ciwo a kira likita mana" Ido daya ya kashe mata yana
kallonta.

"Kece likitan ai.....jeki kulle qofan da key ki dawo na nuna miki abinda zakimin ya
rage zugin da nakeji" Ya fada yana karya wuya kaman da gaske zugin yake. Da zuciya
daya taje ta rufe din ta dawo,saidai kafin ta ankara ya jawota jikinsa ya matseta
da kyau,kota ciwon ma bayayi.

"Kada ka fama

Please Login or Register in order to submit comment