You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rufin asirin mace".

Shuru kawu rufa'i yayi tamkar me shakka ko kokwanto akan shawarar
rabi'u.

"Har yanzu rabi'u bakasan yarinyar nan ba,kafaffiya ce me shegen taurin kai da
rashin tsoro,idan ta kafe akan abu babu wanda ya isa ya tanqwarata,bata tsoro
shakka ko kuma shayi.....ba irin Sabrina bane ake zuwa musu da magana haka kai
tsaye a hada da wa'azi da shawara ba kuma su dauka.......Sabrina rinduna ce da sai
an fuskanceta da gayyar jama'a....amma dai kafin sannan zan gwada wannan din rabi'u
"

"Zata aminta in sha Allah,kuma komai zaizo da sauqi"

"To Allah yasa" Kawu rufa'i ya furta ajiyar zuciya tana subuce masa. Shi kadai
yasan kalar tashin hankalin da yake ciki,yayi nadamar sanin duk wani dan caca tun
daga haihuwarsa kawo yau bare kuma har ta zame masa sana'a.

*****Shi daya ne tal tsaye cikin kitchen din,sanye da fararen tanks top da joggers
masu taushi. Kunnensa daya yana maqale da earpiece yana amsa waya. Daga gefe guda
kuma yana tsaye ne gaban wani qaramin cabinet yana ciro ganyen zaitun,ginseng
wolfberry da zai dafa tea dinsa na musamman dasu,sannna ya jawo wai qaramin plate
din daban ya zuba dabino teen da busashen inibi da ake kawo masa shi tun daga china
bayan anyi packaging nasa a wata jar leda mai kauri.

Hankalinsa yayi nisa sosai wajen amsa wayar da dafa tea din,har baiji
shigowar farouq ba,wanda ta qaraso dab dashi ya kumayi tsalle ya haye saman kitchen
cabinet din kusa da plate din da fuad din ya zuba friut din,ya soma miqa hannu yana
tsinta daya bayan daya yana jefawa a bakinsa gami da cilla qafafunsa yana duba
wayarsa rabi da rabi,yayin da kuma lokaci bayan lokaci yakai kai dubansa ga fuad
din.

Daidai sanda ya gama amsa wayar tea din nasa ya gama dahuwa,ya
jawo kebantacciyar ma'ajiyar kyawawan kofunan shan shayi na tangaran.

"Nayi zaton baka shigo ba ai". Fuad dake zuba musu tea din ya furta ba tare daya
kalli farouq ba.

"Na shigo tun dazu......na tsaya duba wasu baqi ne da abba yace na sauraresu don
yayi nisa". Kai kawai ya jinjina,yayin da farouq ya maida dubansa kan cups din da
fuad ke zuba tea din

"Amma dai bani ka zubawa ba ko?" Ya fada yana dan yamutsa fuska. Sai a sannan ya
daga kai ya kalli farouq din.

"Ba dole bane sai ka sha......" Yayi maganar shima yana hayewa saman kitchen
cabinet din tare dakai cup din bakinsa a nutse hankali kwance yana sipping.

Sosai farouq yake kallonsa kafin murmushi da yafi kama da dariya ya
subuce masa

"Ina mamaki idan na ganka a kitchen......zai zamewa 'yan jarida babban labari idan
sukasan muhammad jadda dinnan yana shiga kitchen da kanshi time to time"

"It's my hubby.........inason dafa tea dinnan da kaina.......na tabbatar bakasan
amfanin wadannan ganyayyakin a jikinka ba da bazakayi wasa dasu ba". Yakai qarshen
maganar yana sake maida cup din bakinsa.

"Inaso na koya......but bakina yanason dadi.....harshena ba irin naka bane" Yayi
maganar yana nuna damuwa akan fuskarsa. Sake cire cup din yayi yana balla masa
harara

"Ka zauna dadi ya kasheka......you know baka fini son girki me dadi ba......but
lafiyanka a matsayinka na d'a namiji sama take da komai.....wait.....wai meyasa ma
zan zauna inatayi maka wannan bayanin,do what you want,amma sanda kayi aure kada ka
nemeni da shawaran komai". Murmushi ya sake kubcewa farouq,yana so yana kuma
farinciki yaga ya sanya muhammad magana har haka,wannan dalilin ne ya sanya baya
gajiya da tsokananshi,duk da ba kasafai yake biye masa ba.

"Kaine na hannun daman ango.....so that kai ya kamata na fara nema kuwa......"

"Baka da wani abu me muhimmanci ne da zaka fada?" Fuad din ya fadi yana kafe farouq
da idanu. Dariya sosai farouq ya saki harda sunkuyawa kadan

"Da alama aljanar amaryarka ta iso,taji batun aure....."

"Farouq" Fuad yadan kirashi da husky voice dinsa.

"Times up" Farouq ya furta yana daga hannayensa sama

"I have something to talk about.......very serious" Farouq din ya fada yana gyaran
murya kadan sannan ya maida fuskarsa serious,abinda ya sanya fuad shima ya bashi
hankalinsa ganin ya koma umarul farouq dinsa na asali.

"Tun jiyan zuwa yau nake zuba ido da kunnen ka nemeni ko kayimin qarin bayani...."

"Akan me?" Fuad din ya tari numfashinsa.
"Akan yarinyar daka nema aurenta ta hannun kawunta a office dinka......kwata kwata
ban fahimci meye shirinka ba......in fact ma duk wanda ya sanka dole abun ya
sanyashi mamaki......how and when ka fara sassautawa ra'ayin riqau akan aure?,when
kasan yarinyar har soyayyar da za'a iya aure ta shiga?,.....anya auren tsakani da
Allah zakayi kuwa dude?"

Sassauta zamansa fuad din yakeyi,baisan murmushi ya subuce saman
kyakkyawar fuskarsa ba. Murmushin da ya sanya farouq ya sanya masa qatuwar ayar
tambaya ya sabbaba masa kafe fuad din sosai da ido.

Bayaso fu'ad din yaje ya aikata wani kuskure,yanason koma meye su bishi
a sannu

"Banda kai dan rainin hankali ne dama ana auren wasa ne?.....da gaske aurena zaa
daura mata,aure zan nema kaman yadda kuka nema kuke kuma neman naku....already ma
gayawa wancan tsohon nata...two weeks ma nace masa badon ina nufin nan da 2weeks
din nake buqata ba,zan daura mata igiyata kaman kowanne mutum......but....." Ya
katse maganar yana durgowa daga saman cabinet din,sannan ya fara takawa zuwa bakin
sink din kitchen din ya kunna tap yana wanke cup din. A mugun qagauce farouq yake
kallonsa yana son jin qarshen labarin,ya sani tsaf zai iya qin qarasa masa ya
barshi da guntuwar magana a ciki

"But what fu'ad......tell me mana?" Farouq ya furta cikin damuwa,danuwar data taba
zuciyar fu'ad din har ya waiwayoshi bayan ya gama wanke cup din.

"I want her to lern the hard way.......she made a mistake data zabi taba kudin
jadda company"



𝗗 𝗨 𝗑 π—œ 𝗬 𝗔 𝗧 𝗔

𝙃 𝙐 𝙂 𝙐 π™ˆ 𝘼

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 96


Yayi maganar yana zube idanunsa akan farouq da mamaki ya fara saukar
masa

"To learn what?fu'ad?......sai ka aureta ne sannan zata koya darasin rayuwa?". Wani
dan qaramin murmushi ya saki,ya miqe tsaye sosai yana goye hannayensa har yanzu
idanunsa akan farouq din

" Ba wata hanya me sauqi da zan sanyata ta barwa sauran mata masu irinta darasi sai
ta wannan hanyar.....dole ta fuskanci hukunci.....dole ta gane yadda ta dauki kanta
batakai can ba......dole ta karbi sakamakon mutanen data dinga sanyawa a masifa
saboda rabasu da dukiyarsu data dinga yi ba dalili.....inason ta san meye
rayuwa......tasan kokai waye kana da iya limit dinka a rayuwa.......abdus salam na
tura mata amma tayi avoiding nasa........kaga inda tayi accepting dinsa da hukuncin
zaizo da sauqi" Yakai qarshen zan can yana sakin hannayen nasa gami da juyawa yana
nufar inda ya ajiye wayarsa.

"Let her fu'ad......"

"Am sorry bro....Definitely sai na nuna mata kuskurenta......na dauki wannan
alwashin" Ya sake fada yana bude wayarsa.

Shuru farouq din yayi yana wani gajeran tunani.....yafi kowa sanin
waye fu'ad.....yafi kowa sanin halin tsaiwarsa da kafiyarsa akan komai ma.....idan
yace zaiyi ba gudu ba ja da baya

"Amma ta yaya zaka tunkari su abba da wannan maganar?".

" Kaman yadda kowanne me neman aure yake sanar da iyayensa mana......akwai wani abu
sabo ne a ciki?" Yayi zancan kanshi tsaye hankalinsa kuma kwance ba wani haufi.

Duk da yasan waye fu'ad amma wannan karon mamaki yake sake bashi,yayi
tsai da ranshi yana kallonsa kamar yadda shima shi yake kallo.

"Da wani abu?" Fu'ad ya furta yana dage dukka girarsa biyun. Kai farouq kawai ya
girgiza,yama rasa me zaiyi?,murmushi ko takaici?.

"Idan naji wani abu daban daga wajen anni ko abba tabbas kaine" Fu'ad ya fadi ba
tare daya kalli farouq ba daya sauko daga saman cabinet din shima.

Harara ya watsawa fu'ad din kaman zai idanunsa zaso fado

"Saika hanani fada din" Daga haka ya soma tattaki zai fice daga kitchen din

"Karka damu,koda ka fada din ai ba wani abun bane.....zan koya mata tarbiyya ne na
kuma koya mata wadatar zuci da kame kai daga dukiyar al'umma......kaga ko ba komai
zan samu ladanta ko?"

"Kai ka sani" Farouq ya fada yana qarasa fita a kitchen din,yanayin yadda yayi
magana kuma ya sanya fu'ad sakin wani lallausan murmushi.

*****Tamkar tsakanin hajja da maamah din babu wani me sauran abun fada sanda driver
ke wulwula saura dasu cikin baqar range Rover din mallakin maamah.

Ba wanda yace komai din har zuwa sanda maamah ta gaji da shurun ta
gyara zamanta.

"Amma hajja abun yazomin a bazata,ya kuma dauren kai matuqa". Juyawa gefanta hajja
tayi tana duban maamah data tsinke mata zaren nata lissafin da take hadawa tare da
qoqarin ganin amsar lissafin ya fito daidai.

" A yadda bayaninta ya nuna......zata iya aikata komai muddin akan kudi
ne.....hakanan kudin sune abu mafi daraja cikin idanunta......ya akayi ta wofantar
da buqatarmu ta watsa mana qasa a ido?......duk da cewa ido ba mudu ba ai yasan
kima.....duk wanda ya kallemu zai shaida irin daula da ni'imar da muke ciki". Wata
ajiyar zuciya hajjan ta saki itama,ta zubawa waje daya idanu kafin tace

"Ni kaina abun ya dauren kai,kuma iyakar tunani na bamu shiga mata da wani abu da
ba daidai ba" Tayi maganar cikin 'yar damuwa. A wannan gabar ita kanta nasara take
buqatar a samu.....nasara takeso tazo musu......yarinyar zata zame mata tamkar wani
tsani me tsananin sauqin da zai ciccibata ya zuwa matakin tata nasarar.

"Ba wani abun damuwa bane ba hajja......ita iya nata hasashen ta dojewa
buqatarmu.....kina tunanin zan barta?" Ta jefawa hajja tambayar.

Duk yadda hajja ta saka idanunta cikin na maamah din don hango plan dinta
akan yarinyar ta gaza ganowa,don haka ta dora da tambayar

"Wanne mataki kenan zaki dauka?".

"Matakin da shine mafi dacewa da ita,ki zuba idanu kawai ki jira cikar kwanaki ukun
dana bata.....da kanta zata budi baki tace ta amince" Ta furta sanda motar ke
tsayawa a farfajiyar gidanta,don haka ta saka hannu da kanta ta bude murfin tana
fita hajja ta mara mata baya zuciyarta cike da wasiwasi.

Sun samu zuwaira ta kammala komai,ta cika table da kalolin abinci iri
iri na alfarma,wanda duka cikin izzar maamah dince. Ba'a abinci kala daya a
gidan,bata yarda wannan ba,daga breakfast lunch har zuwa dinner ana mata varieties
of food ne taci wanda ranta ke ra'ayi tabar sauran.

Daki na musamman da aka kebe ta sanya aka shigar da hajja don ta huce
gajiya kafin itama ta watsa ruwa ta sauya wasu kayan ta fito. Kamanninta da
musaddiq suna fitowa sosai sanda take fitowa daga dakinta sanye da wata bubu gown
me tsananin laushi.

"Yau nake sake ganin kamanninki da musaddiq fa...." Hajja ta fada tana murza
awarwaro hannunta.

Murmushi kadan ta saki tana jan daya daga cikin Kujerun dining din ta
hau ta zauna

"Tun duniya na kwance akance kamannina da musaddiq yafi yawa......shi wancan
babanshi ya dauko.....ni kuwa ba?" Maamah ta hade zancan duka tana qoqarin daukan
cup da zuwaira ta fara zuba musu lemo

"Uhmmm" Hajja ta fada tana kallon maamah,can qasan ranta tana jin wani abu.....tana
kwatanta irin izza gadara da mulkin da maamah din zata zuba a duk sanda haqarta ya
cimma ruwa
"Waya sani ma ko ta rufe idanu ta manta dake ta canza qawaye?" Wani sashe na
zuciyarta ya jefo mata wannan tunanin.

"Ni kuma bari zanyi hakan ta faru?" Ta bawa kanta da kanta amsa

"Kinsan wani tunani da nayi" Maamah ta sake fada tana juya cokalin cikin abincin
bayan barin zuwaira waje. Zuwairan da a yanzu tsananin kishi da tsanar hajja ke
ruruwa qasan ranta,ganin farat daya hajjan ta rushe gwamnatinta,gwamantin da da ita
aka fara fafutuka aka kuma dasa harsashin gininta.

"Zanyi magana da fu'ad a yau ko gobe.....zan sanar masa ya fara shirin aurensa nan
kusa". Kallo hajja ta bita dashi

"Da wuri haka?,har yanzu bamu samu tabbacin amincewar yarinyar ba". Wani murmushi
maamah ta saki tana saka lomar abinci na farko a bakinta.

"Sabrin qaramar alhaki ce a wajena.....bata isa ta tsallakewa tarko na
ba......amincewar fu'ad tafi zama abu me wahala a gareni akan amincewar
sabreen.....na rantse miki da Allah.....muna nan zaune dake zata kira da kanta ta
furta ta amince". Maganganun maamah din a yanzu daure kan hajja sukeyi. A kafe
yarinyar take,ba wata alama ta amincewa a tattare da ita har suka baro gidan,to
wanne abune haka zai sakata sauya ra'ayi da gaggawa?.

"Indai kina da wannan tabbacin to tabbas tsarinki yayi". Hajja ta bata qwarin
gwiwa,daga wannan kuma sai suka zarce da wata hirar ta daban.

******A hankali suke takowa ta tsakanin kyawawan shuke shuken da aka qawata kusan
kowanne sashe na gidan. Baqin wando ne a jikinsa wanda bai qarasa idon sawunsa ba
da kadan,sai shirt itama baqa me gajeran hannu,hakan ya bayyana murdadden
damtsensa,kalar rigar kuma daya kasance baqa ta haska farara lafiyayyar fatarsa
dake sulbi tamkar ta mace. Kadan kadan iska ke wasa da sumarsa daga hagu zuwa
dama,wani lokaci yasa hannu yadan shafeta kadan. Ko daga ina kake muddin a daura
dasu kake to tabbas hancinka zai iya dauko maka lallausan qamshinsa daya zauna
sosai a jikinsa,ya kuma kama komai da yake mu'amala dashi,kama da wayarsa keys
dinsa briefcase da sauransu.

Shi da farouq ne bayan fitowarsu daga ainihin parlor din abba wato
alhaji hamza kibiya. Karo na farko kaf tsahon rayuwarsa daya gabatar da wata d'iya
mace a matsayin macen da yakeso ya aura. Har a sanda suke takawa yanayin anni ya
kasa barin idanunsa,can qasan zuciyarsa sai yakeji anya ya kyautawa wadannan
dattawan guda biyu da suka karbi lamarin auren hannu bibbiyu da zallar farinciki?.

"Alhamdulillah.....alhamdulillah,Allah na gode maka daka gwadamin wannan ranar da
raina da lafiyata.....wacce me sa'ar ce?,a ina take?,ya kuma sunanta?" Anni da
qananun hawaye suma maqalewa ta fada tana kallonsa.

Sunkuyar da kansa yayi,sam bai dauka lamarin aurensa ya zaune musu a
rai ba har haka saida wannan maganar ta taso,ko da wasa bai taba qiyasta zasuyi
farinciki har haka da zancan aurensa ba,tunda duk sanda farouq ya sanyashi a gaba
game da lamarin auren cewa anni take

"Ka shiga hankalinka fa......matar mutum kabarinsa.....komai komai nada nasa
lokacin.....kar ka sake kiransa mijin aljana......yarona yana da ibadar da ba wata
halitta data isa ta cutatar min dashi".

"Sunanta sabreen......kuma marainiya ce" Abinda yaji kawai farouq ya fada kenan.
Kallon gefan ido ya yiwa farouq din,a nasa zaton zai tona asirin plan
dinsa......sai baiyi hakan ba......amma ya jishi kuma yana isar da wani zance da
baisan sanda suka yishi da farouq din ba.

"Dukkaninmu ya fimu iya shiri anni......yanason aje nema masa auren,kuma sati uku
kawai yake buqata". Shuru suka danyi dukansu,don abun yazo musu a bazata. Sun dauka
zaya jera ne tare da 'yan uwansa ayi komai lokaci guda?.

"Anni......komai na gininku ya kammala......da bude company da tarewarku duka duka
sati biyu ne ya rage......ayimin afuwa idan abun yazo muku a gaggauce......inason
ku zama wakilai akan komai kafin mubar nan din". Yayi maganar cikin sunkuyar da kai
tare da mamakin me yasa farouq yin hakan?. Bazai iya qaryata farouq din ba ko yace
ba haka bane a gabansu annin,dole ta sanya ya dora da nasa bayanin. Baida wani plan
na a daura auren sam a yanzu,yanason ya fara sanya mata shamaki ne ta hanyar
maidata property dinsa. Shiga ko fita saida izininsa,hakanan yana buqatar kowanne
motsi nata ya kasance qarqashin umarninsa,matakin quntatawa na farko kenan da
yakeso ya fara aiwatar mata wanda zai sanyata jin ta qasqanta,kuma ita din batakai
inda take tsammanin ta kai ba.

Murmushi abba ya saki yana cewa

"Banda abinka ko a yau iyayenta suka baka ita ai bai haramta a daura muku aure da
ita ba......zan samu mamanka a sanar mata ko akwai wanda zai zama nata wakilin
wajen zuwa neman auren......zanyi magana da bangaren mahaifinka suma,in sha Allah
bazai wuce wadannan satikan ba".

Har suka isa sashensa baice da farouq ci kanka ba,sai da suka isa
falon. Qarasawa yayi gaban freezer a nutse ya bude,ya ciro ruwa me sanyi abinda
yadan jima baisha ba,yau dole zaisha din saboda yadda tsarin farouq yazo masa a
bazata,ya kuma busar masa da maqoshinsa.

Sai daya gama sha ya dire robar saman dining,ya kuma fara saukowa daga
steps din dining din cikin tafiyar nan tasa me cike da ginshira.

Ba zato ba tsammani farouq yaji saukar waya sama cinyoyinsa,sannan
fu'ad din ya tako gabansa ya tsaya hannunsa zube a aljihun wandonsa.
"Tunda kai ka tsara komai ai sai ka qarasa aikinka......ka kirayi wancan tsohon ka
gaya masa yadda ka tsara din,don bani da lokacin masa bayani......lokacin kawai
nace ka shaida masa.......sadakin aure kudin sanya rana da sauran bidi'o'i ya
lissafa ya cire cikin kudadena da suke kwasa,canjin ya rubutasu aci gaba da lissafi
har zuwa ranar da zan fashesu gaba daya......don ba wanda zaici kudin jadda ta
wannan hanyar ya tsira".

Da idanu farouq yake binsa,dariya nason kamashi amma yana dannewa

"Amma malam ya kamata ka koyi ladabin magana zuwa yanzu,ko ka manta yanzun suraki
yake a wajenka?" . Harara ya watsa masa da fararen idanunsa yana zama saman sofa

"Kaci gaba da gayamin haka,wataran zaka wayi gari da haqoranka a hannu" .

"Zaka aikata.......ai gwara da aka saka ranar auren 3weeks,kafin aljanarka ta dawo
ta sanyaka kace ka fasa.....kaini koma wanne irin aure ne fa gwara kayishi,a qalla
addu'ata bata fadi qasa banza ba,zaa yiwa aljana kishiya.....naci nasara" . Duk da
baijin dariya ko wani raha sam a ransa.......amma saida maganganun nan na farouq
suka sanyashi sakin wani miskilin murmushi kafin kuma ya waske kaman bashi ba.

Yana tsaka da cin abincin dare kiran ya shigo masa,ya daga wayar
ya sanyata a hands free yana adduar koma waye ya kirashi Allah yasa alkhairi ne.

Tunda farouq ya gabatar masa da kansa gumi ya fara yanko masa,gaba
daya yaji abincin ya gundureshi ya fita a kansa,sai ya tsame hannunsa daga ciki ya
miqe tsaye yana sauraron farouq jikinsa yana kyarma



*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 97


"To.....to shikenan......in sha Allahu zan shaidawa dangin
uwarta.....to Allah ya nuna mana....to godiya nake a gaida alhajin". Ya qarasa fada
jikinsa yana rawa wayar kaman zata sulale ta fadi

" Na shiga uku na lalace ni rufai" Ya fadi a sarari yana zama dabar saman Kujerun
da kwana uku kacal da zubasu sumame daga jadda company ya riskeshi. A da mugun
laushin Kujerun yake ji,amma a yanzu yana jjnsu tamkar kujerun da aka sarrafa da
bishiyar qaya.

Kansa kawai yake mirginawa daga hagu zuwa dama. Duk da ya iya tijira
ya kuma iya tubura,amma wannan karon sai ya tsinci kansa da tsananin shakkar yadda
zai tunkari sabreen din ya gaya mata ya bada aurenta a madadin kudin cacar wasu da
yaci,da kuma nata kudaden data kwasa.

Bata iya doguwar magana ko rashin kunya irin na 'yan uwanta ba.....amma
idan tayi maka wani abun har sai ka gwammace baki ta bude ta gasa maka rashin
kunyar.

"Yanzu meye mafita?" Ya fada a sarari yana juya hannaye irin na wanda ya banu ya
lalace,daidai nan matarsa umma asabe tayi sallama ta shigo dakin.

Kusan duka wayar da farouq din keyi da kawu nashi hankalin yana kan
news da suke hasko faduwa da tashin hannuwan jari a kasuwa a yau din. Yaji suna
sallama da kawu rufai din,sai wayarsa dake ajiye a gefe ta dauki ruri.

Kamar kowanne lokaci da bayyanar sunanta saman fuskar wayarsa ke
sanyashi jin wani iri haka ma yanxun. Ya miqe ya zauna sosai yana sauke qafafunsa
dake harde a dazun,ya daga wayar ya saka a kunnensa yana yin sallama.

"Wa'alaikumussalam..."

"Barka da dare" Ya fadi a nutse yana qoqarin saita kanshi.

"Barka kadai......idan kana gida ka shigo yanxu inason yin magana da kai". Dan
shuru yayi kafin ya amsa a taqaice da

"Okay" Amsawar tasa ya bata daman katse kiran,ta ajiye wayar tana sake hada kalaman
da zata tunkareshi dasu.

Kaman bazai motsa ba sai kuma ya miqe,farouq ya miqa masa dayan wayan
tashi

"Mun gama magana......"

"Ba wani abu me muhimmanci a ciki da saika sanarmin......ka riqe duk bayanansa
zasuyi maka amfani wajen qarasa plan din daka tsara". Dariya farouq ya saki yana
lumshe idonsa,ya kuma sake relaxing abunsa sosai cikin kujera

"Hakanma ni yayimun.....zakaga kalar tawa ja'irartar". Bai amsashi ba ya soma
wucewa inda flip-flops dinsa ke jere nau'i daban daban cikin wata ma'ajiyar takalma
dake bakin qofar shigowa falonsa,ya miqa hannunsa kan wanda ya fara gani,ya zarosu
ya sanya a qafarsa ya buda qofa ya fice yana jin wata fargaba haka kawai tana
saukar masa wadda baisan dalilinta ba.

Yau ma gidan ba kowa,banda malam saidu daya bude masa qofa suka gaisa
ya wuce ciki.

Ita daya ce hakimce saman lafiyayyun kujerunta,falon bai cika hask
sosai ba sai haske fitilun da aka qawata ginin POP din dake saman falon.

Da murmushi a Fuskarta ta amsa sallamarsa tana tashi daga
kashingidar da tayi ta zauna sosai. Ya zare takalmansa ya barsu daga nan sannan ya
qaraso ciki.

Kaman kowanne lokaci,ba kasafai ya fiya zama saman kujera ba idan ya
shigo falon yauma haka,sai ya samu daura da inda take zaunen ya zauna yana
tanqwashe qafafunsa kamar me shirin fara cin abinci.

"Bari na samo maka ruwa tukunna". Ta fada tana miqewa sannan ta wuce cikin kitchen.
Bai dakatar da ita ba don gudun ballo wata rigimar daban kuma,saidai bayajin ko a
gabansa akayi aikin ruwan zai iya aminta yasha shi. Kansa ya daga kadan yana kallon
falon da ainihinsa nan din dakine na mahaifinsu ciki da falo......dakin da ya rayu
yasha jiyya a cikinsa har ya koma ga mahaliccinsa.....dakin da nan ne waje na
qarshe data sanya qafafunta ta tsallakesu ta fice......dakin da anan sukaci gaba da
zama shi musaddiq da jadda cikin talauci har itama jadda ta tafi ta barsu. Yau ga
dakin ya zama wata qawatacciyar duniya.....saidai wadanda suka cancanci suci
arziqin abun sunyi qaura sun barwa wani sashe da basu da alhakin samun gajiyar
abun.

"Bismillah" Ta fada tana dire masa tray din sannan ta koma saman kujera ta zauna.
Idanunsa ya lumshe da suke masa wani irin radadi sannan ya budesu,ya miqa hannu ya
dauki gorar ruwan swan ya balleta ya tuttula a cup ya dauki cup din kawai ya riqe a
hannunsa

"Tashi ka koma saman kujera ka zauna sosai magana nakeso muyi dakai me matuqar
muhimmanci" Tayi maganar tana soke yatsunta cikin na juna tana sassauta sakin
Fuskarta zuwa daurewa.

Kallo daya tak yayi mata,sai ya dire ruwan ba tare daya ce komai ba
ya miqe din ya zauna saman kujerar dake fuskantarta.

"Muhammadu" Ta kirashi kai tsaye da zallar sunansa,kiran da ya saka gabansa faduwa
abinda ya mance rabonsa da yajishi

"Na'am" Ya motsa tausasan labbansa ya amsa da wata murya can qasa.

"Wacece ni a wajenka?" Ta jefa tambayar a gareshi tana kafeshi da idanuwa.

Jin abun yayi yayi masa banbarakwai kawai,yana ganin amsace bayyananniya
ai da ba sai anyi dogon neman amsa ba.

"Mene ya kawo wannan tambayar maamah?" Ya fada a sanyaye

"Akwai.....amma kafin sannan inaso naji amsa daga bakinka.....don komai da zai taso
daga baya din yana da alaqa da kalar amsar daka bani" Qasa yayi da kansa ransa da
zuciyarsa suna sake jaddada masa tabbas akwai wani abu.

"Mahaifiyata ce ke" Kai ta jinjina tana jin alfahari,tana jin kalmar har tsakiyar
ranta,zamowa mahaifiya ga mutum irin Muhammad jadda ba qaramar takar sa'a bace ga
kowacce mace.....ba qaramin zamowa riba bace ga kowacce uwa me haihuwa.....ribar
qafa ce ta kowacce bangare.

"Shikenan......akwai buqatar da nake da ita daga gareka.......kuma umarni ne zan
baka,bawai roqo ko neman alfarma nakeyi ba......ina magana

Please Login or Register in order to submit comment