You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaman baya wajen,haka fuskarsa ta nuna kaman baisan me
ake magana akai ba.

"Fu'ad" Farouq ya kirayeshi sanda suka isa farfajiyar asibitin,guards dinsa kuma
nata kai da kawowa wajen tabbatar da tsaron wajen kafin fitowarsa.

Idanunsa dinnan masu bala'in kwarjini ya daga ya zubewa farouq su.
Yanayin kallonsa yana da matuqar kaifi da saukar da dafi,idanun suka so yiwa farouq
din kwarjini,saidai wannan din ba baqon abu bane a wajensa,abune da ya riga ya saba
dashi tuntuni.

"Ako yaushe ka dinga tuna cewa taci albarkacin kalmar UWA.....zata kuma ci gaba da
cin wannan Al Farmar koda meye tayi maka" Idanunsa yadan ragewa kaifi kaman zai
lumshesu sai ya fass,ya sake budesu sosai saman fuskar farouq din. Wannan maganar
inda farouq din yasan mugun famin da ya yiwa ciwonsa da baiyita ba,har maqogoronsa
sai da yaji yawu yana neman daukewa,ya tattara dukka wani yaqi da yakeyi da
yanayinsa sannan ya bude bakinsa

"Inda ace a yau za'a zare wannan kalmar tsakanina da maamah......da har abada ba
zata sake ganin fuskar muhammad fu'ad ba muddin kuwa ya haifu daga tsatson
jadda.....a lokacin daya miqa mata dukkan soyayya da yarda......a lokacin ta nuna
masa cewa DIYA MACE MAYAUDARIYA CE.....BA KUMA ABAR YARDA BACE,bata barshi haka ba
har sai da tayi silar......." Ji yayi bazai iya qarasawa ba.....ji yayi wannan
sirrin bazai iya furtashi ga kowa ba,sai kawai ya sanya hannu ya bude murfin motar
ya zura qafafunsa yana fitowa ba tare daya jira me budewar ya bude masa ba.

Tun bai qaraso bakin qawatacciyar balcony din da aka yiwa dakin ba
musamman saboda shan iska da hutawar me lalura da me jinya ba ya hangeta zaune ta
hasken fitilun da aka wadata wajen dashi. Kanshi ya dauke sarai,yana jin har qasan
ransa ya washi matar. Ba zaya gaya mata gogayya da duniya ba.....kaman yadda bazai
gaya mata sanin takan duniya ba. Bata tunanin akwai wani yanayi da zai nuna mata a
yanzun da zai tunzurata ta janye rayuwarta daga cikin tasu har sai ta cimma nata
gacin.

"Sannu da zuwa.....ashe ka qaraso" Hajja harira ta furta cikin tsananin nuna kulawa
tana miqewa daga saman kujerar da take kai.

Kanshi ya dauke yana maidawa ga Musaddiq daya taroshi tun daga farkon
balcony din

"A nemo likitan......yazo da gaggawa don ina da abunyi" . Sosai maganar ta daure
kan hajja harira wadda kwarjininsa ya hanata sake cewa komai. Lallai ya kamata
kafin ta zurma kanta da yawa ta sake karantar kowanne taku da motsi nasa domin
samun isar muradinta cikin sauqi.

"Waye a cikin dakin?" Ya sake jefa tambayar ga Musaddiq. Saidai kafin wanda aka
yiwa tambayar ya amsa hajja hariran ta rigashi amsawa cikin matuqar alhini

"Basu barin kowa ya shiga don har yanzu ma bata farfado ba". Duba daya tak ya yiwa
hajjan yayi taku uku ya isa gaban dakin,ba tare da jiran umarni ko bada dama ga
kowanne likita ba ya murza handle din ya tura kansa ya shige.

Daga bakin qofa ya fara tsaiwa,ya harde hannayensa a qirjinsa yana
qare mata kallo. Tana kwance cikin lallausan blanket da aka rufeta dashi har zuwa
qirjinta. Ba qarin ruwa babu na jini.....baiga oxygen ba,saidai akwai canola daya
kula da ita a hannunta.

Idanunta a rufe suke,a haka tafi kama da me bacci. Sake nutsa idanunsa
sosai yayi saman fuskarta yana karantar fuskar bayan wucewar kowacce daqiqa har ya
samu matsaya cikin zuciyarsa dangane da ita,ya sauke hannayen nasa yana sake
qarasawa ciki,takun likitan kuma sai ya biyo nasa takun.

Fasa qarasawa yayi bakin gadon,ya zube hannayensa cikin aljihun
wandonsa ya waiwayo a nutse yana amsa sallamar likitan gami da zube masa idanunsa.

Dan tsamurmurin likita sanye da lab coat,hannunsa kuma riqe da wani
file,yayin da wuyansa ke rataye da abun auna gudun zuciya.

Ta cikin farin gilashin idanunsa ya kalli fu'ad. Kallo qwaya daya tak
daya mamayi zuciyar likitan da wani irin mahaukacin kwarjini tare da zallar mamakin
wanzuwar muhammad jadda cikin asibitinsu.

"Meye ya kawo mamallakin jadda diamond chore resources asibitin?" Ya tambayi Kansa
da kansa tsoro da kwarjini suna cikashi.

"Kada dai ace da gaske suke da suka gaya masa ita din mamarsa ce?" Wannan maganar
ta sake tsarga masa wanda hakan ya sake sakashi jin rudani yana mamayarsa. Yasan
waye muhammad jadda,bazaiso kuma fadawa matsala dashi ba,ba zayaso fadawa hurumin
da ba nashi ba da karatunsa daya samu yake riqe kansa da iyalansa.

"Shine likitan?" Fu'ad daya gama qarewa likitan kallo ya furta yana duban musaddiq
daya qaraso daga ciki yayi tsaye gefan fu'ad din

"Shine hamma" Ya amsa masa shima yana maida dubansa kan likitan.

Duk wani qoqari nasa ya tattaro,ya kalato yawun bakinsa yana dora
murmushi saman fuskarsa

"Barka da zuwa asibitinmu yallabai.....munyi farinciki da shigowarka yau
asibitinmu......hakan ba qaramin qarin kima da martaba bane ga asibitinmu damu
kanmu gaba daya". Hannayensa zube a aljihun wandonsa,kamar yadda idanunsa suke a
Kan likitan.

"Madalla.....inason magana dakai if possible"

"To......ba damuwa.....ba matsala hakan,muje ne ko a nan zamuyi?" Yayi tambayar
yana raba idanunsa tsakanin fu'ad din da musaddiq.

"Qaraso ka duba patience dinka".

"Aah yallabai..... Ai ba za'a barka a tsaye kana jira ba.....hasalima ban jima da
fita a dakin ba ai". A nutse ya debe dubansa daga kan likitan,sannan ya fara takawa
a nutse yana fita a dakin musaddiq ya mara masa baya.

A hankali yaci gaba da takawa yana fita a asibitin. Bai dakata ba har ya
isa inda motarsa ke ajiye. Kafin ya qarasa daya daga cikin guard din ya zabura ya
bude masa sannan ya jira isowarsa

"Kada ka rufe.....zanga baqo"
"Yes sir" Ya fadi yana barinta a bude kaman yadda ya buqata. Budewar data bash
daman kallon likitan da kuma karantar kowanne motsi nasa cikin wani kallo da ba na
kai tsaye ba wanda ke cike da hikima.

Wani irin bugu zuciyarsa keyi musamman sanda ya tsinci kansa tsamo tsamo
tsakanin Jordan da abdulbasit da suka kusa rufa tsahonsa. Ya daga kansa yana duban
fuskokinsu da suke manne da baqin gilashin idanu.


*D U N I Y A T A*

*_D U N I Y A T A_*

Page 89
________________________
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz

*_assalamu alaikum warahmatullah_*

*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada
ko rashin ingancin kaya?_*

*_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_*

*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke
iya bada kayansa akan hakan ba_*

Shadda
Laces
Atamfa
Kayan yara English wears dana jarirai
Qawatattun handbags
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
Huluna na maza da mata yara da manya socks
Takalma na maza da mata yara da manya
Lafayas
Sarqoqi agoguna banguls da rings

_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_

_bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_

*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?
_*

*_masu manyan qarfi da matsakaita?_*

*_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda
zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_*

*_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_*

*MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA*

*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU
RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*
*_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_*

*_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*✌🏽 ✌🏽 ✌🏽 ✌🏽 ✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽
✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
_________________________

PAGE 89


"Enter" Jordan yace dashi yana jiyowa sosai gareshi gami da nuna masa
cikin motar. Bashi da abunda zai ce don shi kansa yasan nan din ba wajen wasa
bane,ya daga qafafunsa da yaji sun fara masa nauyi yana sanya jikinsa cikin
motar,yana kuma jin yadda gumi yake tsargo masa daga kowacce kafa ta jikinsa.

Set din dake opposite nasa ya masa nuni,hakanan ya zauna yana qoqarin
gyara lab coat dinsa yana hadiye wani miyau me kauri. Idanu kawai fu'ad din ya sake
zuba masa duban daya sanyashi kasa nutsuwa ya dinga gyare gyare,daga gyara agogo
zuwa gyara rigar jikinsa da kuma hannun rigar.

A nutse ya janye masa idanun,sannan ya motsa bakinsa

"Ya sunan doctor din?"

"Ni....Dr kamal......sunana Dr kamal". Kai fu'ad ya jinjina yana lumshe ido gami da
budesa sanan ya maimaita sunan a hankali

"Good Dr kamal,ina maka murnar samun damar zama likita ga
mahaifiyata......am.....inaso nasan da meye da meye suka ce ka gaya mana a matsayin
cutar dake damunta?". Sosai maganar ta rudashi saboda tazo masa a bazata,ya dubi
fu'ad yana qoqarin nuna masa gaskiyarsa

"Su waye?.....Ni ba wanda yacemin ga abinda zan fada sai abinda bincikena ya gano".

"Kamal!" Fu'ad ya kira sunansa da wata irin deep voice dake dauke da amo me
tsoratar da wanda ake magana dashi.

"N...na'am"

"Lookat me......" Ya sake fadi masa yana tsareshi da idanunsan nan da suke sanya Dr
kamal jin kamar zaya narke.

"Kayi haquri yallabai" Dr din ya sake fada kansa tsaye ba tare da fu'ad din ya sake
cewa komai dashi ba. Wani irin rudani da firgici suna ratsashi.....gaba kura baya
sayaki,yasan hajja harira ba sanin shanu ba,amma ta yaya zai yadda yayi jayayya da
mutum irin muhammad jadda din?,wanda yayi imanin ita kanta inda hajja harira ta
gama sanin wayeshi da kyau ba zata saka kanta cikin wannan wasan ba.

"Yallabai......sunce zasu biyani bayan barazana da hajja harira tayimin......sunce
na kwantar da ita kawai na saka mata ruwa wanda zai qara mata kuzari ne
kawai...........sunce tabbas zakazo...idan kuma kazo din na kambama ciwo da kyau,na
nuna muku zaman kadaici da kewa ce take damunta,wanda muddin ba'a kula da ita da
kyau ba.....an samu wani cikin wadanda sukafi kusa da ita take kuma yawan ambatarsu
su zauna tare da ita ba to tabbas zuciyarta zata iya bugawa ayi
hasararta......sunce idan.....". Dakatawa yayi ba tare daya qarasa fadin abinda zai
fada din ba saboda daga masa hannu da fu'ad yayi. Shuru ya ratsa motar,abinda ya
sake ruda Dr kamal,ya sanya hannun rigarsa yana goge gumin fuskarsa bayan ya cire
gilashin idanun nasa.
"Sauka kaje....kaci gaba da riqeta.....zaka sallameta,but sai daidai lokacin da na
baka umarnin yin hakan"

"Okay sir" Ya fada da gaggawa yana juyawa gami da laluben hanyar fita daga
motar,don zaman motar duk da laushin kujerunta da sanyin Ac da wani ni'imtaccen
qamshi da yake fita......amma ji yakeyi kaman yana zaune ne cikin qabarinsa.

"Dr" Ya sake kiran sunansa dab da zai sanya qafafunsa a qasa. Adan zabure ya
waiwayo yana qoqarin saita kansa.

"Banda wannan harqallar.....ka tabbatar babu wata sauran haramtacciya ko miyagun
harqalloli da kakeyi a boye......don idan hakan ta kasance ka tabbata ba zaka tsira
a hannuna ba"

"Wallahi ranka ya dade ba ruwana......ni din mutumin kirki ne ka tambayi kowa ma"

"In kuwa hakane ka kyautawa kanka".

"Sauko malam" Jordan yace da Dr kamal din a dake cikin rashin son wasa.

Jinsa ya dinga yi kaman zai kifa sanda yake komawa cikin asibitin.
Inda ace yasan da gaske take ita din mahaifiyarsa ce ta yaya zaiyi wannan kasadar?.
Fadan giwa da damusa waye yake shiga?,sai wawa sai mahaukaci,shi kam qaura zaiwa
asibitin bazai sake shigowa ba sai gobe,duk da yasan bashi da inda zaije yace ya
guje masa.

Duk wani mamaki da maamah zata bashi a yanzu ya biyo bayan wanda ya
gani a yanzu da shekarun rayuwarsa ta baya. Ko daya bai sake komawa asibitin
ba,saidai kuma bai hana kowa zuwa ba. A kwanakin ma gaba daya yana qoqarin ganin ya
gyara wasu abubuwa da yake ganin suna qoqarin tasowa can qasan kamfanin,wanda idan
har ya bari matsalar tayi girma zata iya jawo asara mafi muni fiye data kudadensu
da suka zirare.

A cikar ranar lahadi kusan kowanne bayani ya kammala samunsa,ya shigar
da komai cikin documents,sai la'asar ya kammala,don haka daga nan alwala yayi ya
wuce masallaci. Daga masallacin ya sake dawowa gida,ya leqa anni da bata jima da
dawowa duba maamah ba,sai ya zauna falon bayan ta sanya amna ta dama masa yoghurt
da fura.

"Muhammadu" Anni ta kirasa,sai ya dauke idanunsa daga tasha alhadath dake nuna
yadda bani Israel ke dake ragargazar Palestinian,hankalinsa ya fara nisa kan hanyar
da zai aika musu tallafi ya kuma isa garesu kai tsaye

"Na'am" Ya amsawa annin yana dubanta

"Jiya abbanku ke complain....ko sau daya ance ba'a ganka a asibiti ba......ni kaina
ko sau dayan banji kace zaka je ba,sai zama da kaketa yi a sassanka?".

Hannu ya sanya ya karbi kyakkyawan tray din da amna ta jero cups da
bowl me kyau dake dauke da dammen yogurt din,ya aje gabansa yana cewa

"Thanks lovy dovy". Qaramin murmushi ta saki,ta juya tana komawa kusa da anni ta
zauna.

"Jikin nata da sauqi ai anni......infact ma tun ranar ta samu lafiya.....yau ma
zasu sallameta". Ya amsa ba tare daya kalli annin ba,don yasan yana yin hakan zata
dago wani abu

"Duk da haka muhammad wannan din baiyi kyau da tsari ba....."
"Yanzu daga nan can zanyi anni kiyi haquri". Kalmar haquri idan ya fadeta da
gaggawa haka to tabbas baison bacin ran annin ne,ta gama karantar hakan.

Jujjuya furar yayi sannan yayi bismillah yakai bakinsa. Fuska yadan
bata ya daga kai yana duban amna

"Yaushe kika koma sakamin sugar a abin sha?". Kai tadan langabe

"Hamma.....kadan fa na saka maka wai don bakinka yayi taste"

"Zoki dauke abarki" Ya fada yana dan ture bowl din. Da sauri ta miqe tana fadin

"Ayyah hamma.....kayi haquri kada magauta suji kanmu....bari na hada maka wani
wannan sai BB farouq yasha"

"Kayi zaton amnan taka tayi hankali ne?,kaima kai ka sowa kanka wannan
gallafirin......wai sai yaushe zaka fidda mace ne Muhammadu?,bakasan duk girman
namiji aure shike cikashe wani gibi ba?,gibin da babu abinda zai cikeshi face
auren?......ita kanta amna yaushe ta fara iya riqe abinda ya dace da itama
ballantana ta riqe abinda ya dace da waninta?". Waiwayowa tayi tana duban annin
kamar zata saki kuka

"Wayyo anni.....yanzu duk qoqarin da nayi baiyi ba?,hamma don Allah ban canza ba?"
Wani sassanyan murmushi ya kubce masa,ya maida kallonsa ga anni

"Tsokanarki fa anni takeyi.....kin canza sosai amna ta,kinyi kuma hankali,yauma
nasan akasi aka samu,ki dama min wata ki sakamin apple a ciki da grapes ki
ajiyemin,idan na dawo zan sha".

Tabe baki anni tayi tana kauda kanta

" Ai daman.....indai abu da laifin amna duk girmansa saika maidashi qarami......da
tashi kayi kaje ka shiryadinma da zaifi maka". Murmushi ya saki ya miqe a nutse.
Duk wani jini na anni girmansa yake gani martabarsa yake gani hakanan qaunarsa
yakeyi.

"Hamma na shirya na rakaka?" Ta fada tana tallafe da tray din.

Bayason zuwa da ita,saboda ya tabbatar ba zata samu marabtar data dace
da ita ba,amma bazai iya cewa bazaije da ita ba,don haka yace

"Ki shirya.....but be fast....banson jira"

"Yanzun nan hamma" Ta fadi tana qara hanzarin barin wajen.

Suna hanya tana cikashi da labarai kala kala wanda hakan yake masa dadi
da debe masa kewa. Don amna din wajen quruciya da sakalci irin na autanni ba daga
baya take ba.

Koda suka isa cikin asibitin sai ya kalleta

"Ko ki zauna a nan,ko na yiwa Jordan magana ya kaiki ki zabi duk abinda
kikeso.....kina da 30 to 40minutes"

"Yay!.....thank you hamma na" Ta fada da tsananin murna.

Zaune take daga bakin gadon da kwata kwata cikin kwanaki ukun a duniya
taji ba abinda ta tsana sama da kwanciya a kansa. Kwanciyar da babu alamun nasara a
tattare da ita,kwanciyar da bata amfaneta da komai ba saima sake haska mata rashin
nasararta muraran da ake sakeyi.

"Ba alamun nasara hajja......zuciyata tafi karkata akan na tafi plan C.....a plan C
ne kuma nakejin cewa koda sharadina zai zama silar rugujewar fu'ad wannan karon
basan sassauta masa ba......a wannan karon a shirye bake na gindaya masa sharadin
da nayi imanin bazai iya tsallakeshi ba.....a wannan karon hajja......ban yarda
koda da darsawa a rai ba zuciyata ta darsamin wai bazanyi nasara ba.....dole dole
dole nasara ta kasance a tsagina.....hajja a yau zan bar asibitin nan,ina da
buqatar na huta saman gadona nayi bacci me lafiyar da zai bani damar tsara komai da
kyau cikin kwanyata.....na kuma wayi garin litinin da wannan shirin".

Kai hajja ke gyadawa tana kuma sake juys Plan C din maamah data
tabbatar zaiyi wahala idan ba abinda take hasashe bane ba.

"Hakan ma yayi,abun ni kaina ya soma shallake tunani na.....amma mariya anya shima
baida hatsabiban da suke masa aiki?" Shuru maamah tayi,ko qwalqwalwarta bata kama
muhammad yana biye biyen nan ballantana hankalinta. Tun daga haihuwarsa zuwa
tasowarsa kawai tasan ya banbanta da sauran yara,quruciyarsa ma ta daban ce a cikin
yara,zuwa sanda ya cika shekara goma cas a sannan ta sake ganin banbanci mabayyani
a kanshi.

Shigowarsa dauke da cikakkiyar sallama sai ta zama tamkar amsa ga
tambayoyin hajja harira. Bakinta yana dan rawa tana kamo amsar sallamar da qyar ta
hada kalaman tana amsa masa.

A nutse ya tako ciki idanunsa akan maamah din data dauke kanta daga
gareshi gabanta tana ji yana faduwa. Haka kawai ita kanta sau tari sai taji ya mata
kwarjini,fargabar kada dai ace yaji wani sashe na tattaunawarsu yana cikata.

Duk yadda hajja ke qoqarin ankarar dashi tana wanze a dakin ta hanyar
jera masa sannu da zuwa amma ta gaza samun hankalinsa. Bawai kuma don baijita
ba,aah haka kawai yakejin wani abu na daban game da matar,sannan kuma kwanyarsa a
kullum idan ya ganta takan yawaita qoqarin tunata cikin jerin sahun mutanen da yaga
gilmawarsu a shekarun da abbansu yake raye.

Kaman bai lura da sauyawarta ba,yaja kujera gaban gadon ya zauna yana
gaidata. Ta amsa masa tana hadiye bacin ranta. Fada takeson masa sosai ko zata samu
sassauci amma kuma idan ta tuna a gobe akwai nata plan din dai ta danni
zuciyarta,saidai duk da hakan sai data b'ara

"Kasan ina nan amma fu'ad ka banzatar dani?,ko ka manta ba'a canzawa tuwo suna?"

"Kiyi haquri" Ya jefeta da kalmar nan da har ta fara tsanarta saboda yawan fitarta
daga bakinsa.

Shuru yaci gaba da ratsa dakin ba tare da kowa yace da dan uwansa
komai ba,kafin daga bisani aka turo qofar.

Dr kamal ne,ya qarasa shigowa cikin takatsantsan da tsantseni,wanda
dukkan me hankali yana kallonsa zai fahimci hakan.

"Kwanciyar haka ta isa?,xaki iya komawa gida?" Ya tambayeta a tausashe saidai kuma
kalamai ne masu harshen damo da yawa a ciki.

Juyowa tayi tana dubansa maganar tana qoqarin fassara kanta da kanta
cikin qwalqwalwarta. Ta zargi wani abu,amma kuma yanzun ba muhallin wannan bane,don
haka ta dauke dubanta ta maida kan Dr kamal
"Ina buqatar sallama Dr,naji qwarin jikina".

" Yanzu in sha Allah" Ya fadi yana bude file dinta. Hannunsa yana dan rawa yayi
rubuce rubuce ya maida ya rufe,sai fu'ad ya miqa masa hannu Kai tsaye,yadan
kalleshi sannan ya miqa masa file din salin alin.




*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 90



*_MONDAY_*
*_Tushen aiki,ko nasara na tsoronki_*


Cike da confidence take shiryawa cikin tsadaddiyar dubai abaya budaddiya
data lullube jikinta ainun.

Wine color wadda aka qawata qasanta da kuma qasan wandon abayar da wasu
irin stones da zare ruwan gold masu daukan hankali.

Gaban madubi ta matsa tana saka brush tana sake kwantar da doguwar
sumarta me yauqi da rashin cika sannan ta ware madaidaicin mayafin abayar tayi
rolling dinsa saman kanta,abinda ya bawa kyakkyawan fuskarta daman fita tarwai ta
kuma haska da wine color din abayar jikinta.

Siririn agogo ta sanya gold me dan adon wine,wanda yake suwa set da
komai nasa,ta taka a hankali ta matsa ta dauki purse dinta da wayarta ke ciki
tanata haske.

Kiran ta daga ta sanya a kunnenta tana aza idanunta kan huda dake zaune
gefan gadon,kai kace mata ket ta zura da gudu

"Okay.....gani nan fitowa" Ta furta tana maida wayar jaka sannan ta maida kallonta
kan huda. Suna hada idanu boyayyun hawayen dake qasan idanun hudan suka yiwa kansu
hanya.

"Adda.....ina tsoro" Ta fada tana jin zuciyarta tana nauyi. Taku biyu Sabrina ta
isa gabanta,ta kuma kamo hannunta

"Duk duniya.....duk wanda yace zai tabaku bazan qyaleshi ba muddin ina da iko da
qarfin hakan......ba yau ba,ba kuma sau daya ba ina jan kunnen Naseer yayi qoqarin
fidda rayuwarsa daga kaina......ya sanyawa ranshi bai taba haduwa da wata basma ma
ba amma baiji ba........a wannan karon ya kamata nayi masa general hukuncin da zai
sanya a rage ire irensa baragurbi cikin mutane......kada kiji tsoro,babu abinda zai
faru" Ta bata tabbaci tana matsa hannayenta.

Iska me zafi maamah ta furzar daga bakinta sanda suka kammala zama
saman qawatattun kujerun da aka zuba saboda zaman cin abinci ko shan wani abu ga
baqi maziyarta wajen.

"Wai nikam mariya.... Meye hikimar tattaunawarmu a nan?" Hajja harira ta tambayi
maamah tana kallonta.
"Harira.....gani nakeyi kaman akwai wani information nawa da yakeyin
leaking.......yadda fu'ad yake samun damar kaucewa kowanne tarko nawa abun yana da
matuqar daure kai......inaso mu koma gida da wuri don a yau nakeso A YITA TA QARE!"

"Ina saurarenki" Hajja ta furta tana hade yatsunta guri daya tare da bawa maamah
hankalinta.

"Hajja......aure zanwa fu'ad!" Sosai maganae ta zowa hajjan a bazata,wanda hakan
yaso hautsinata tare da haifar mata da fargaba......fargabar yiwuwar rushewar plan
nata da rashin cimma interest dinta tsakanin wasan da ake murzawa yanzun.

"Aure kaman yaya mariya?,ya samo matar auren kenan?" Kai ta girgiza tana sake
matsowa kaman hajja din bata jinta sosai

"Ya akayi kanki ya kulle hajja?,zanwa fu'ad aure da yarinyar da duk na zaba masa
don ta zamemin tsanin MALLAKARSA".

Shuru hajjan tayi wuta tana neman dauke mata. Ba wai kuma mamaki ta
shiga ba,aah tanason adan taqin tayi tunanin amsar da zata bawa maamah wadda zata
bayu ga tafiyar lissafinta daidai. Duk yadda taso kuma ta kwalkule maganar ta
fiddata a daidai ta gaza,don harbuwar maganar zuwa kwanyarta tazo mata ne da wani
irin katsuwar hanzari da gajere kuma tsukakken lokaci

"Yimin bayani dalla dalla qawata".

"Yanzun nan" Cewar mamah tana komawa ta zauna sosai.

"Zan nema yarinyar da na tabbatar babu soyayya a zuciyarta sai soyayyar
kudi......zan nema yarinyar da zata iya aikata komai indai akan kudi ne.....zan
nema yarinyar da ba kasafai namiji ke burgeta ba kaman yadda kudinsa yake burgeta
ba......za muyi contract da ita na auren fu'ad zuwa wani lokaci.......zata
shayarmin dashi ta ciyarmin dashi daga dukkan wani abu da akeso yaci ko yasha da
zai jawo min hankalinsa.......daga sanda buqata ta biya zan sallameta daga dukkan
adadin kudaden da takeso tayi kuma nesa da rayuwarsa.....a sannan ne kuma tayimin
tawa shimfidar da zan soma tawa tafiyar".

Idanu hajja ta zubawa maamah sosai.....ga bikin zuwa kuma babu zanin
daurawa.....tabbas wannan tsari nata yayi.....kuma komai zai iya tafiya ya kuma
wanzu kaman yadda ta tsara din muddin akayi katari da kalar yarinyar da zatayi
aikin.

A jikinta takejin wannan aikin nata ne,wannan kuma su za'a
yiwa.....wannan aikin JANAN dinta za'a yiwa ba kowa ba......zata soma tata
shimfidar ne itama a sanda mariya ke tunanin zatayi tata.....a sannan zata wanzar
da nata tsarin da zai kauda na mariya,dole ta tsaya kai da fata ta taya mariya
fafutukar wannan tsarin ya tabbata,to amma ta yaya zaiyi accepting?. Yaron da yake
da tsananin kafiya da tsaurin da bokansu ma ya gaza juya akalarsa?.

"To amma ta yaya kike zaton zai karbi maganarki ta

Please Login or Register in order to submit comment