You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

balle tasgaro to tabbas dukka mutanen can akwai daga inda suka
bullo,akwai kuma mabanbantan dalilai da suka shigo da ita rayuwarta. Me suke
buqata?,wanne dalilai ke garesu?.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 82



_Manzan Allah S A W yace: Bawa zaizo ranar qiyama da tarin ayyuka da kuma tarin
lada,yana murna zai shiga aljanna sai Allah ya dakatar dashi,ga tarin mutane da
baisan daga ina suke ba.....dukansu masu neman haqqinsu ne a kansu a wajen
Allah,yaci dukiyar wancan.....ya zagi wancan.....ya zalunci wannan,ana biyansu da
haka da haka sai ya wayi gari bashi da komai cikin ayyukan ladansa,bayan ayyukansa
sun qare za'a koma ana diban zunubin mutanen a maimakon biyansu da ladansa ana
lafta masa,daga qarshe sai ya tashi baida komai sai tarin zunubai,sai Allah yayi
umarni wa mala'iku su jefashi a wuta( Allah ka tsaremuπŸ™πŸ½)_

_bukhair da muslim_
82


Tun yana daga cikin motar idanunsa suka sauka akan fuskar fu'ad din. Wani
irin murmushi da ya fito tun daga qasar zuciyarsa ya wanzu a fuskarsa. Tabbas aure
rahama ne kaman yadda mata suke rahama ga rayuwar wanda ya dace dasu. Daga inda
yake yana iya hangen wani annuri na musamman na fita daga miskilar fuskar nan da
ba'a lamunce mata murmushi ba a kowanne lokaci sai lokaci lokaci idan shi da kansa
kuma yaso hakan,amma a yau yana ganin wani sakewa akan fuskar daya tabbatar koshi
me fuskar ba lalllai yasan da ita ba.

"That's my bro muhammad fu'ad jadda" Ya fada qasan ransa yana taya fu'ad murna gami
da kama murfin motar ya fito. Ci gaba yayi da kallonsa ba tare dashi ya sani
ba,idan har za'a tambayeshi mutum na farko dake bashi mamaki a duniyarsa fuad
dinne.......mutum na farko da rayuwarsa tamkar madubi ce a wajensa.....mutum na
farko da tausayinsa bai taba raguwa a ransa ba fuad dinne. Yana da sauqi kayi masa
mummunar fassara idan bakasan halinsa ba,bakasan wanene shi ba,amma kuma kuna wuce
wannan level din dashi zaka fahimci mutane irinsa a duniya qalilanne.

"Ka kama kanka farouq.....banda tsokana da yawa,kafi kowa sanin wayeshi" Ya gayawa
kansa da kansa saboda yadda yakejin wata dariya nason fara taso masa tun bai qarasa
wajen da fu'ad din yake ba

"Ka wuceshi kawai kaman baka ganshi ba indai kasan ba zaka iya riqe dariyarka ba"
Wani sashen na zuciyarsa ya bashi shawara don da gaske dariyar nan bayajin zata
riqu. Yafi yarda da shawarar zuciyarsa ta biyu,don haka ya zaro wayarsa yahau kiran
fannah ba tare daya shirya ba,a sannan harsu amna sun wuce cikin gidan.

Baisan adadin sau nawa murmushi ya kubcewa fuskarsa ba. Duk da waya ce
a hannunsa amma ba abinda yake gilmawa idanunsa sai ita din. A wannin da suka shude
masa sunyi masa wani irin tasiri da har ya mutu ba zasu taba goge masa ba. Wasu
irin mintuna na musamman da suka fara cikin fushi suka kuma qare da wani abu me
matuqar ban mamaki da bai taba kawoshi ba a ransa.

Bai lura da saqon ba don haka cikin sauqi hannunsa ya danna saqon
ba tare da ya shirya ba

*_Kada ka taba tunanin zaka subucemin.....kada ka taba tunanin zaka
kubcemin........a shirye nake nayi komai don na mallakeka.....ciki kuwa harda taba
alaqar dake tsakaninka da KARUWAR da kake kira matar aure a gareka,fareeda khaleed
mustapha_

Wani irin kallo yakewa saqon yana sake karantashi daga farkonsa zuwa
qarshensa,

"Karuwa?" Ya maimaita sunan da wani irin yanayi da yakejin kaman ana yankar naman
zuciyarsa.

"Fareeda?" Ya sake maimaita nata sunan yana jin wani irin fushi yana taso masa.
Fareeda da ire irenta baya jin zai dagawa waninsu qafa da kalmar KARUWA ta fita a
bakinsa muddin suna nufin kalmar ne akan SABREEN. Zaiyi shari'a da kowa a
kanta......zai kuma tsaya mata akan duk wanda ya jefeta da wannan kalmar. Har ya
fara laluben number fareeda din kai tsaye Muryarshi kawai yaji ya daga kai yana
kallonsa. Farouq ne,shi kuwa da gasken gaske wai bai ganshi ba,ya daga hanci sama
yana amsa wayar kanshi a sama yana duban qofar gidan.

Ganinsa kawai sai yaji fushinsa ya soma sassauta,dan uwa kuma abokin
kuka tun daha quruciyarsa har kwanan gobe bai fasa ba. Tsaf ya gama karantar farouq
din,sanin da yayi masa sani ne ba na yau ko na jiya ba,ya gama karantar abinda ya
shirya,don haka har ya gotashi ya sanya hannu ya fincikoshi baya gami da zaunar
dashi a gefansa.

"Zauna kayi dariyarka yadda kakeso" Ya fada yana shan mur gami da dage girarsa
dukka biyun sama tare da qoqarin danne abinda ya taso masa game da saqon fareeda.
Maganar fu'ad din sai ta zama kaman tsokana ga farouq din,take kuwa kowacce dariya
dake cinsa ta fashe,ya soma qyaqyatata,harda sauka daga kan concrete chair din ya
zame yayi Zaman dirshan cikin grass carpet din yana dariyarsa abunsa.

"Kayi me isarka,don wallahi muka shiga ciki kayimin a gaban yaran nan saina faffasa
maka baki" Ya sake fada yana hade ranshi

"Aah...me yayi zafi?,bani na kar zomon bafa,wallahi ko ratayar ma ba'a bani ba" Ya
fadi yana qoqarin danne dariyarsa. Wani kallo ya watsawa farouq din yanata qoqarin
maintaining girmansa.

"Farouq?"

"Allah ya taimakeka" Farouq ya fada yana daga masa hannu da shigen gaisuwar sarakai

"Kada ka batamin mode dina" Ya fada yana ware masa idanunsa duka a kansa.

"Ango ai baka laifi koka kashe dan masu gida......girmanka ne,Allah ya taimakeka
tuba nake....." Naushi ya kawo masa Allah ya rufa masa asiri ya kauce ya samu
iska,farouq din ya sake komawa da baya yana sassauta dariyar tasa,don magana yakeso
suyi me muhimmanci.


β˜… *FAREEDA*

Da qyar ta tattara kanta tana laluben hanyar fita daga dakin. Tunda take
a rayuwarta bata taba jin ta muzanta irin na wannan ranar ba,don ko data koma daki
kasa hada idanu tayi da lubna qawarta.

"Ke da zaki bude wuta kuyi spending night din gaba daya kya dawo haka da wuri?" Ta
tsareta da tambaya sanda ta hautsina kayanta tana laluben inda take ajiye kayan
mayenta ko zata samu wani abu da zai dauke mata baqincikin da takeji. Bata samu
komai ba,abinda ya sake hautsinata kenan,ta kama gashin kanta ya damqe da qarfi
sannan ta sake tana dakawa lubna tsawa

"Get out of my sight.....idiot" Tabe baki lubna tayi tana matsawa gefe. Ta sani
indai muhammad jadda ne ta qwallafa rai a kansa yanzun ma ta fara wahala da
sonshi,bata taba jin wadda a tarihi ta taba samun koda alamu alamun nasara ba a
kansa. Da qyar ta iya hada abinda ya bugar da ita ta zube tana bacci ruhinta cike
da cin alwashin cikin mutuncin maamah idan ta farka,tare da shaida mata ta dawo
mata da kudadenta da dukka taci muddin ba zata iya mallaka mata d'anta ba. Ta dauka
duniya ba wadda take da iko dashi sama da ita....ta kuma dauka mallaka mata shi
shine abu mafi sauqi da zata iyayi mata.

*MAAMAH*


Tun saukarta a qasar ba zata ce ga wata cikikakkiyar ibada data iya samu
ta aiwatar ba,dukka hankalinta da tunaninta yana a kansu. Me dame yake kashewa
ameenatu?,me dame sabreen ki shiryawa a kanshi?,ta bayyana masa sirrinta ne kaman
yadda taci alwashi ko.kuwa?. Babban a binda yafi damunta da tsaya mata a rai batun
fareeda,gashi har yau din ba taji komai daga gareta ba,bata kirata ba ita kuma bata
da number wayarta bare ta fara nemanta. Abu daya ta sani
shine.......tabbas.....kofa zatayi yawo tsirarara.....koda malami ko babu.....koda
boka ko babu saita nunawa SABREEN DA AMEENATU girman isarta akan danta. Idan har
bata sanya fu'ad ya auri fareeda ba ba shakka ita din ba diyas halas bace.

Bayan sallar la'asar kawai saita kasa sukuni,tsakanin jiya da yau
kawai saita dinga jin kaman wani abu zai faru ko ya faru,wannan ya sanya ta lalubi
number wayarsa ta soma kiransa cikin jin isar mallakinta ne shi ya kamata ya
zamanto sai yadda tace ko ta lamunce sannan ayi.

Qarar wayar fu'ad din ta sanya hankalinsa ya koma kan wayar daga kan
farouq da ya fahimci iya shege kawai yakeson samun dam yayi masa......baisan yadda
zuciyarsa ta tumbatsa da wani irin yanayi akan yarinyar ba?. Komai bai dameshi ba
irin yadda zai maidata mallakinsa fiye da yadda ya maidata a yanzun......yanaso ita
kanta a jikinta ta sallama cewa ita din mallakarsa ce har abada,sai ya kalli farouq
ya daga masa yatsa alamun zai amsa wayar. Kai ya jinjina masa,saidai kafin yakai ga
dagawar wayar ta yanke. Qoqarin lalubota yakeyi ya kira sai tex ya fado masa

_"Duk wanda kayi gangancin kamawa ko hukuntawa cikin mutanenmu dake
hannunka.......ba shakka labarin matarka zai zama labari na farko da zai zama
fitaccen labari kowacce safiya saman jaridun qasar mu da qasashen dake huldar
kasuwanci dakai,suke kuma ganin kima da daraja a tare da kai_

Wani irin fusgar hankalinsa saqon yayi,saidai kuma kafin ya sarrafa
kwanyarsa ya fahimci komai kiran maamah ya danne saqon,dole ya kauda abinda ke taso
masa ya daga kiran yana sawa a kunnensa,bakinsa dauke da addu'ar

"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa'anta taj'alal hazna iza shi'ita
sahla". cike da fatan ba wani abu bane na daban zata baro dashi ba bayan abubuwan
dake dabaibaye dashi ba.


*_Da sauran masu bibiye da rayuwarsa kenan_*

*_Ya zafafa da gaske wajen yin campaign na samun soyayyar ta,xaiyi nasara ko kuma
zata zille masa?_*

*_shin fareeda zatayi nasara ta hannun maamah kuwa?,kaman yadda tayi nasarar
sanyashi auren sabreen a wancan lokacin?_*

*_munata gangarowa da MAFARIN warwarar kowanne qulli da tonuwar binnannun asirai_*

*_sai ince muje zuwa dai_*


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862




𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 83
_An rawaito daga manzan Allah S A W yace: Daga cikin mutane ukun da baxasu shiga
aljanna ba,kuma Allah bazai musu duban rahama sune 1_ _"WANDA YAKE ZINA TUN YANA
YARO HAR YA TSUFA YA MUTU BAI TUBA BA_

_2 _TALAKA ME GIRMAN KAI_

_Bukhari da muslim_


83



Cikin cikikakkiyar nutsuwarsa yayi sallama,zuciyarsa bata fasa neman
dauki da ambaton sunan Allah ba.

"Wa'alaikumussalam" Ta amsa masa a dake,tanaso ya fahimci cewa lallai shi din me
laifi ne a wajenta.....wannan fahimtar tata da zaiyi ya zama sila kuma jagora zuwa
ga wanzuwa da amsar babban burinta a yanxu na auren fareeda.

A nutse ya fara gaidata,ta amsa masa a dake kaman dazun. Shuru ya ratsa
na wasu sakanni kafin tace.

"Baku hadu da fareeda bane?" Mamaki kadan ya kamashi,mamakin yadda akayi maamah din
tasan da zuwan fareeda Maldives.

"Mun hadu" Ya amsa mata kai tsaye,kasancewar mutum ne shi da wahala ko tsanani basa
sakashi yayi qarya.

"Amma me ya hanaka zama me masaukinta?......tunda kana da tabbacin ba don kowa tazo
ba sai don kai". Mamaki ya sake kamashi,ya lumshe idanunsa yana jin takaicinsa yana
sake daduwa. Gaba daya maamah din kowacce rana sake jirkita takeyi tamkar
wahainiya,wasu abubuwan nata da takeyi sai ya dinga ganin tamkar ba cikin
hayyacinta take ba. Maamah ke magana,uwar data kawoshi duniya,inda wani ne ya masa
magana makamanciyar wannan yana da amsoshi masu yawa da zai bata.

"Bansan da zuwanta.....batayi shawara dani ba kafin ta taho.....and a yanzun ina da
iyali maamah,bani da wata alaqa da ita ta kusa ko ta nesa,banda dangantaka da ita"
Ya amsa mata da kwantacciyar murya duk da tarin quna da bacin ran da yake ji na cin
zuciyarsa.

Idanunta ta qanqance cikin jin tashin hankali yana ratsata a hankali a
hankali. Meye yake shurin faruwa?,meye yake faruwa da har yau din fuad da bakinsa
ke ambaton INA DA IYALI?. Yaushe ne ta samu wannan matsayin a wajensa?,wata kalma
da bata taba jin ta fito daga bakinsa ba?.

Tarin masifa da wani irin tsanar sabreen tana ratsata,batasan wanne
kalar abu ya kamata ta yiwa yarinyar ba......a yanzun a dukka illar da aka mata a
rayuwa bayan ameenatu sabreen din itace ta biyu,koda ta raba sabreen da fu'ad bata
jin taci riba idan tabar yarinyar haka siddan taci gaba da rayuwarta,tana jin ya
kamata ta ajewa rayuwarta wani babban tabo ko miki da zai sanya koda a gaba zata
zamewa wasu izina a kanta. To amma babban qalubale da barazanarta a yanzu shine TA
WACCE HANYA ZATA RABASU?. Haka kawai take jin matsanancin faduwar gaba da fargaba
idan ta tuna kalaman sabreen akan auren fu'ad,bawai ta fara son fu'ad bane
matsalarta,idan hakan zata kasance ma zai zame mata daidai,tsoron shine shi fu'ad
din......yana da wata irin zuciya da bata iya soyayya ba kaman yadda bata iya
qiyayya ba......yana da wata irin zuciya me riqe abinda takeso da gasken gaske.....
Wata irin zuciya da idan tana so tana so.....idan bataso bataso,zuciyar da zata iya
sadaukarwa da abinda takeso komai data mallaka.....ta zamewa abinda take qauna
kariya daga dukkan wata iska ko kuma guguwa.

"Wanne iyalin kake magana akai fu'ad?,iyalin da nice silar wanzuwarsu a
rayuwarka?.....ko kuma iyalin da babu wata kima ko martaba a tattare dasu?.....ko
kuma ni da aka tsinceni daga ayarin tafiya aka wofantar dani saboda kun nunawa
duniya bani da wata daraja a wajenku?,ni din ba kowa bace a wajenku?". Wani ciwon
kai dukka maganganunta sukaso tasar masa lokaci daya,ya sanya tafin hannunsa ya
dafe goshinsa yana murzashi a hankali tare da lalubo me ya kamata yace mata?,gefe
guda kalmar IYALIN DA BASU DA WATA KIMA KO MARTABA tana masa zillo cikin kwanya.
"AKWAI WANI ABU A LULLUBE" yaji wani saqo na zuciyarsa yana gaya masa. Idan har
maamah ta aura masa sabreen ne saboda ta yarda da tarbiyyarta kaman yadda tace da
farko......me ya kawo wannan maganar a kanta a yanzu?. Bayajin akwai wani abu qwaya
daya da zai iya tunawa wanda ya taba hadasu koda cikakkiyar magana bare yayi
tunanin akwai abinda ta taba yi mata.

"Fareeda ta taso qafa da qafa.......ta sameni har muhallina......ta girmamani
matarka ta tabamin haka?,fareeda tabar qasarta ta biyoka har inda kake,bata da kowa
batasan kowa ba saboda tana sonka.......me matarka ta taba yi me kama da wannan?".
Kanshi yaji ya sake qullewa......a yau din duka me ya kawo maganganu akan
sabreen?,me yahau kan maamah duka akan sabreen din?.

"Ina me baka umarni a matsayina na uwar data haifeka.......nan da kwanaki goma zan
bar qasar nan......ba wani jirgi da zanbi,ba wanda zaizo ya daukeni....kai da kanka
nakeso kazo ka daukeni ka kuma kawoni Maldives......ka kuma soke barinku qasar ka
daidaitashi da nawa barin har sai na kammala uzurina sannan mu tafi......daga
qarshe ina me baka umarni kaje kaga fareeda......ka kuma marabceta kaman yadda
kowanne baqo yake marabtar baqonsa......wannan umarni na ne indai nice na haifeka"
Daga haka ta yanke kiran ba tare data jira cewarsa ba.

Shima wayar ya sauke daga kunnensa yana kallonta,kafin ya sakata a tafin
hannunsa yana dan dokata kadan kadan. Kallonsa farouq yayi kafin ya aje dubansa ga
wayar hannunsa. Ya fahimci wadda tayi kiran ya kuma ji wani abun da take cewa
saboda magana take da qarfi da kuma fushi.

A abinda yake lisssfawa zaiwa fareeda kowanne ya debo sai yaga yayi
masa kadan. A hankali maganganun maamah din sai yaji kamar suna tafiya da
farincikinsa suna son rushe duk wata walwala daya samu.

Idanunsa ya bude kan farouq yana hadiye kowanne bacin rai da maamah ta
sanya masa da rudanin saqon daya shigo wayarsa a dazun.

"Ina jinka......kaman magana kakeso muyi ko?" Yace da farouq. Idanu yadan zubawa
fu'ad din,sai yaji tausayinsa yana kamashi. Kowacce ni'ima da baiwa ta rayuwa Allah
yayi masa......amma ya rasa UWA TA GARI. Ya sake yarda tabbas rayuwa jarabawa
ce,hakanan kowanne dan adam akwai inda tashi jarabawar take,ba wanda yake samun jin
dadin duniya dari bisa dari.

Murmushi farouq ya sakar masa,sai yaji bazai iya kowacce magana dashi a
irin wannan yanayin ba,don haka ya sauya akalar zancan yana yin murya qasa qasa

"Wai yaya akayi wannan gingimarin ta iya hawa saman keke?,karaya nawa keken ya
samu?,duk da ni shaida ne akan yadda keken ya kusa komawa akwala sabod......"
Naushi yakai masa cikin sa'a ya daki iska. Ya fahimci lallai da gaske farouq so
yake ya maidashi birin wasanshi. Gefe farouq ya koma yana dariya,can qasan ransa
yana jin dadin hararar da fu'ad yake watsa masa,yasan tabbas ko bai nasarar gusar
da baqincikinsa ba zai rage masa wani abu.

"Wallahi ka iya bakinka akan iyali na......kada ka yarda mu saka qafar wando daya
dakai" Yayi maganar yana nunashi da yatsansa.

Ido farouq ya zaro yana daga hannuwansa sama

"Ya salam.....kace me?,iyalinka?,unbelievable.....wazai tayani jin wannan
kalmar.......sabreen won the battle" Qaramin dutse ya dauka zai jefeshi ya kwasa da
sassarfa ya wuce cikin gida yana cewa

"Wallahi ta haukatashi......ya zama madoki" Tilas dariya ta subuce saman labbansa.
Sai da farouq ya bacewa ganinsa sannan ya maida hankalinsa kan wayarsa. Kai tsaye
ya kira jordan sukayi magana ta wasu mintuna sannan ya kashe,ya kalli agogonsa yana
lissafin awannin da suka rage su kaishi gurin target dinsa.

β˜…K'arfe takwas na dare agogon Maldives ya gama shiryawa cikin wasu
lafiyayyun trouser da t.shirt. ta fidda sigarsa sosai da wani sassanyan kyau ke
tsayawa a zuciyar dukkanin 'ya macen data Kalleshi. Wani irin mutum ne da zai
wahala ka kalleshi ka kauda kai,koda baka furta komai a kanshi ba amma zai tsaye
maka a zuciyarka da idanuwanka. Jikinsa yabi ya feshe da turarukansa,sannan ya
sanya sau ciki a qafarsa,ya dauki wayarsa da maqulli ya nufi qofar fita daga dakin.

Dukkaninsu suna dining area suna cin dinner. Kusan tunda suka iso garin
tare suke cin abincin safe dana dare,na rana ne kowa da tsarin cin abincinsa bai
yuwu suci lokaci guda. Ire iren wadannan abubuwan sune suke qarawa iyalan anni
hadin kai qaunar juna shaquwa tare da fahimtar juna.

A kanta idanunsa suka fara sauka,wani irin abu ya tsarga masa tun daga
kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa. Tun jiya bai sake sanyata a idanunsa ba,suna
dakin annin ita da amna. Bazaice ga abinda sukeyi ba,amma lokaci lokaci yana jin
muryar amnan da motsinsu,ita kanta amnan bata sake fitowa ba. Ita da amna suna seat
din kusa da juna,kaman magana suke qasa qasa,baka iya ji saboda musaddiq da saddiq
da suka cika gurin da musunsu da bai gane ma akan meye suke musun ba.

Kaman wadda aka umarta,nata fararen idanun da a kwanakin yaga kaman sun
qara girma ta daga ta watsa masa cikin rashin sanin shi dinne ya is wajen. Qwayoyin
idanunsu suka gauraye da wani irin mabanbantan feeling. Da sauri ta janye qwayar
idonta yayin da nata kallon a gareshi ya zame masa kamar wani irin dafi daya
sabbabba mutuwar dukkan wasu gabbai a jikinsa. Tsigar jikinsa ta zuba sanda ta soma
motsa wadannan siraran lips din nata tana tauna Chip's din dake gabanta. Bazai taba
manta abinda yaji daga kowanne sashe na jikinsa ba a ranar farko daya soma tsotsar
tausasan lips dinta ba......wani mahaukacin saqo da suka aike masa da baisan inda
zai iya adana yawansu a kwanyarsa ba. Yanzun da take juyasu tana tauna sai ya
zamana tamkar tsokanarsa takeyi haka yakeji tana aika saqo kowanne sassa na
jikinsa.

Fitowarsa ya sassauta tashin muryar saddiq da musaddiq din,kowa ya
maida hankalinsa jikinsa,kasancewar sunsanshi mutum ne da baison ire iren musunnan
nasa. Yakance

"Shashanci ne wannan,kuna da abubuwan yi da yawa a gabanku cikin rayuwarku,shi ya
kamata ku fuskata" Sau tari musaddiq yakanyi dariya idan bai wajen

"Shifa hamma ya dauka kowa irinsa ne.....ba baki nayi mana ba,amma ba zamu iya
achieving abinda yayi achieving ba.....we are doing the best,amma ba zamuyi kaman
nasa ba". Kujerar dake opposite dintata ya zauna,sam table din baida fadi
sosai,wannan yana iya sawa idan ka zura jiki da yawa gwiwarka ta iya taba ta abokin
zamanka.

Zamansa a wajen sai taji kaman gaba daya ya cika wajen.....kwarjininsa
da qamshin sassanyan turarensa gaba daya ya gauraye wajen. Nauyin idanuwansa takeji
har tsakiyar kanta,abinda bata taba ji ba a kansa tsahon tarayyarsu.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862




𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 84



_Allah S W T yana cewa "lallai sallah tana hana alfasha da munkari_

_Duk wanda salla bata hanashi qarya ba,zina sabawa iyaye,zuwan gidan boka shirka
kenan,cutar da maqota da sauransu,to tabbas ya tuntubi sahihancin sallarsa_




84


"Barka da fitowa hamma" Amna ta fada wadda sun hadu yau kusan sau uku sun
riga da sun gaisa already.

"Lovey dovey.....barka da dare" Ya fada cikin wani irin aji kaman me qididdige
adadin kalamansa na ranar. Murmurshi amna ta saki qasa qasa.

"Hamma.....kada ka saka adda sabreen taji kishi fa.....sunan nan for now ya kamata
ace nata ne". Daga shi har ita nauyi maganan ya musu musamman da anni ke a
wajen,wadda tayi burus kaman bataji ba tana qarasa shan black tea dinta. Amnan ya
kalla sannan a dabarance ya saci kallon sabreen din. Bayajin akwai wani suna daya
cancanci ya kirata dashi......har yanzun duk sunan daya bata sai yaji tafi gaban
wannan sunan. Daidai lokacin tana jefawa amna harara da fararen qwayar idanunta
ne,wani irin kyau yaga ta sakeyi masa,tsigar jikinsa yaji ta zuba sosai har sai
daya lumshe idonsa.

"Ka maida hankalinka fa.....aiki zaka fita kayi" Wani sashe na zuciyarsa ya gaya
masa ganin tana neman dagula dukkanin lissafinsa.

"Yi serving hammanku takwarata" Anni data kammala shan tea din ta yiwa sabreen
magana. Hakan ya masifar yi masa dadi,sai ya ajiye mug din daya dauko da farko yayi
relaxing bayansa jikin kujera yana jin jikinsa yana sake mutuwa gaba daya....wani
irin feeling yana taso masa yana sake kashe masa duk wani kuzari nasa.

Sai data ji gabanta ya fadi da anni ta fadi haka,amma dole ta ajiye
fork din hannunta ta miqe,fork din yabi da kallo,gaba daya ya gama karantarta,bata
qaunar abinci ko kusa ko alama....bayajin zai iya bari taci gaba da hakan,dole ta
dinga cin abinci me inganci tana qoshi,bayajin indai zata dinga zama ba abincin
kirki zata iya dauke lalurarsa yadda yakeso. Shi kansa wani lokaci yana tsoron
kansa,tun a lokacin da yake shi kadai ma.....shi da kansa yasan yana da buqatar
mace me juriya kafin ya samu abinda yakeso. Faruwar abunnan kuma ya tabbatar masa
sa zarginsa,bai taba kawowa ma zata iya dauke buqatarsa.....duk da abinda ya farun
yasan akwai aikin gaggawa da kuma rashin sabo a tattare da ita,amma yasan cewa
lallai akwai aiki a gabansa,dole sai ya horar da ita yadda zata dace da muradi da
tsarinsa.

Kwata kwata ya mance ya samu farouq a wajen,ya shagala wajen qare mata
kallo ta qasan idanunsa. Zaka dauka sam ba ita yake kallo ba,amma kowanne motsi da
zatayi idanunshi suna kanta sanda take zuba masa abincin. A cikin qaramin hijab
take,amma shi ba hijab yake gani ba,wannan kyakkyawar surar tata yake
gani,kyakkyawar surar da yakejin koda zata shekara a yana ganinta zallarta bazai
gaji ba......kyakkyawar surar data kusa qwace kowanne tunani tasa,ta kusa sanyashi
manta waye muhammad jadda gaba daya. Wani sashe na zuciyarsa dake danqare da
mahaukacin kishinta ya soma masa zafi,gani yakeyi musaddiq saddiq da farouq dake
zaune a wajen suma suna iya ganin abinda yake gani.....yana jin kamar duka suma
qare mata kallo sukeyi.

"Gyara kintsi yallabai.....anni fa na wajen nan kada a tafka abun kunya" Cikin
kunnuwansa ya tsinci muryar farouq yana fada. Cikin dakiya ya gyara zamansa yana
basarwa,abinda ya kusan sawa farouq ya fashe da dariya.

"Shi yasa ake cewa bawa yaji tsoron Allahnsa koda yaushe" Farouq ya kuma fada sama
sama. Tunu fuad ya gama karantar abinda yake fada,so amma yanzun baida energy din
kulashi. Hannu yasa don karbar mug din da take miqo masa,cikin dabara ya hade da
zara zara yatunta da suka ja hankalinsa sosai,ya kuma motsa hannun nasa yana
lullube bayan hannunta da tafin hannunsa.

"Thank you" Ya fada da wani irin sauti can qasan maqoshinsa yana karbar mug din.

Kaman an yarfa mata ruwan sanyi haka taji sanda dumin tafin hannunsa
yake ratsa kowacce jijiya ta jikinta,ta koma ta zauna tana jin cikin ta duka ya
gama cushewa ta qoshi da chips din,sai ta koma juya cokalin kawai.

Tana jin hirarrakinsu amma ita din ta gaza cewa komai,kaman yadda
shima ta fahimci jifa jifa yake cewa wani abu. Kanta da idanunta cikin

Please Login or Register in order to submit comment