You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi da kallon wayar,batayi yunqurin dagawa ba har zuwa
sanda wayar take dab da tsinkewa.

A kunnenta ta kara wayar,sannan ta maida idanunta ta rufe gami da
jan bakinta ta tsuke.

"Hi" Ya furta cikin zamudi tamkar ya mance gurin da yake a zaune. Qaramin tsaki
taja qasan zuciyarta,ta motsa labbanta a hankali

"Assalamu alaikum" Ta fadi a nutse.....sallamar da ta sanyaya masa jiki,ta kuma
jefa shakku a cikin zuciyarsa. Itace macen da yakewa kallon bariki ta farko da take
matuqar masa kwarjini. Itace ta farko da yake hangen wasu kalan dabi'u da suke jefa
shakku da kokwanto cikin zuciyarsa. Baisan kala da adadin matan da yayi mu'amala
dasu cikin rayuwarsa ba,amma sai take neman zame masa ta daban.

Dan gyaran murya yayi sannan ya amsa mata da

"Wa'alaikumussalam.....afuwan.....banyi sallama ba ko?,na matsu da naji muryarki
ne.....na kwana da kewa na kuma tashi da ita......ina fatan kin tashi lafiya?" Sai
da tasha qamshin nan nata da yake a halittarta sannan ta amsa masa

"Lafiya qalau......"

"Naji dadi dajin hakan.....yaushe za'a bani damar sake ganinki?" Yayi mata tambayar
abinda yafi damunsa kuma cikar burinsa a kanta.

"Sai lokacin yayi......idan yayin da kanshi zai kawoka gareni". Sam ba haka yaso
ba,sai kuma yake ganin kaman daga gareshi ne,ya kamata ya gyara wasanshi.

"Zan iya haqurin jiranki koda na shekara nawa ne......amma inaso kisan akwai
zuciyar da tayi matuqar mutuwa a kanki take kuma da buqatar soyayyarki....."

"Mika'il......" Aka kira sunanshi daga gefe,muryar ta fusgi hakalinsa,yadan waiwaya
kadan ya dube kamilar fuskar nan,daya daga cikin fuskoki biyu dake masa kwarjini
cikin kamfanin
"Am sorry......zan yanke kiran,ina fatan samun wayarki a bude zuwa anjima,ba kamar
yadda nasha wahala jiya ba" Boyayyen tsaki ta saki tana yanke kiran hadi da zame
wayar daga kunnenta. Ta wurga fararen idanunta gefe tana sauke qaramar ajiyar
zuciya. Wato namiji akan mace tamkar mayen qarfe ne da qarfen kansa?,musamman idan
zaki bashi abinda yakeso?,ko kuma yana hasashen samun wata riba ko ganima a kanki?.

A nutse ya zuba masa idanunsan nan yana kallonsa lokacin da yake jefa
wayarsa a aljihu yakuma iso bakin zagayayyen table din da yake zaune a kai.

Muhammad fuad jadda CEO abinda ke rubuce kenan jikin wani dan siririn
katako dake zaune sosai saman table din daga gaba gaba. Saidai a maimakon muhammad
jaddan,farouq hamza kibiya ne zaune saman kujerar yana duban mika'il da kyau har ya
zauna kujerar dake fuskantarsa.

"Sassaucina fiye da oganku kamar yana son jawo sakaci da aikinku ko?" Ya jefawa
mika'il tambayar yana debe dukkan wani wasa da haba haba da ya saba yi dasu dake
saman fuskarsa. Shafar kansa kadan mika'il yayi cikin rusunawa

"Sorry sir.....urgent call ne shi yasa....but hakan bazai sake maimaituwa ba"

"Mituna nawa nayi ina kallonka ba tare daka sani ba,hankalinka baya jikinka?,ka
kuwa san girma da matsayin position da kamfani ta baka mika'il?" Ya sake masa
tambayar yana riqe habarsa da yatsarsa guda gami da kafeshi da idanunsa sosai.
Yanayin ya tabbatarwa mika'il na gaske ne,a irin wannan lokacin da yake buqatar
kusanci na sosai da JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES bai kamata ya bari BOSS muhammad
ya dawo ya samu wani shaidan banza a kansa ba

"Sorry sir.....it will never happen again" Kaman bazai daina kallonsa ba sai kuma
ya fesar da iska daga bakinsa,ya tura masa wani folder yana cewa

"Ruwanka ka riqe aikinka da kyau,ruwanka kayi wasa dashi.....daga rana ita yau ba
zaka sake ganina a company dinku ba,wataqila saidai ziyara......ka kuma fini sanin
waye boss dinka" Ya qarashe maganar yana tashi daga saman kujerar.

Yadda hankalinta yayi kan zuwa duba aysha yasa gaba daya ta manta da
batun wayar da ta bada address din aje a karba. Gaba daya ta manta ma da zaman
wayar cikin dakinta. Sai data tabbatar su huda sun dawo daga boko sun wuce
islamiyya sannan ta shirya cikin wani dinkin atamfa doguwar riga data bude sosai
daga qasa ta zauna mata daga sama cas jikinta,ta kuma lullube kanta da Chantilly
veil,takalmi da jakan D&G su suka zama cikamakin adon nata.

Kamar ko yaushe tsakar gidan nasu zuwa farfajiyar gidan bata rabo da
kai kawon jama'a jifa jifa. Kamar kullum haka ta ratsasu a nutse ta fice ba tare
data damu da idanun dake zube a kanta ba.

Kamar dai kowanne lokaci,abinda ta baro cikin gidan shine a waje. Yawan
idanun jama'a dake kanta ko kadan basu dadata da qasa ba. Tun asali mutum ce me
damuwa da lamarin gabanta.

Abubuwa da dama da suke cikin zukatan mutane a kanta bata isa ta
gogeshi ba. Abune da tun yana damunta ya zame mata jiki. Suna mata kallon biri ne
tana musu kallon ayaba. Anyi walqiya me hasken data haska mata abubuwa masu tarin
yawan da suke boye cikin hijabin idanuwan jama'a da wani irin shamaki da tsinkaye
da idanuwa basu kaiwa wajen.

Wasu mutanen a riga kawai suke mutane.....wasu dattawan a suna ne
kawai kuma a baki.......wasu jama'ar da ake tunanin suna gyara ko bada gudunmawar
gyaruwar al'umma su din GUBA ne,guba ce wadda bata da magani,guba ce me d'aid'aita
komai da wargaza komai.
Daidai sanda takai qarshen tunaninta sai ta fidda eye glasses dinta da
ba kasafai ta fiya amfani dashi ba ta manne qwayar idanunta. Daya daga cikin abinda
ya sanya suke mata mummunan kallo da mafi munin fassara. Eye glasses ne me duhu
dake qarawa fuskarta kyau da kuma kwarjini,yake kuma iya hana mutane ganin ainihin
qwayar idanunka.

A nutse takai bakin titi,saidai yanayin kai kawon abun hawa kadai zai
gaya maka akwai qarancin motocin haya

"Ki siya mota kawai ki huta sabreen" Ta tuna kalamin qawarta qwaya daya da take da
ita duk duniya wato haseena. Karon farko tun wayewar garin ranar ta saki murmushin
da batayi niyya ba,abinda ya sanyashi tsaiwa da motarsa cak. Duk da cewa ta daki
zuciyarsa tun daga nesa daya hangeta,amma sai gashi farat daya ta sanyashi tsaiwar
da baiyi niyya ba.

Taga gilmawar farar motar amma saita dauke dukka wani hankalinta zuwa
wani sashen,qasan zuciyarta tana fatan bawai ya tsaya bane saboda ita,don a yanzun
bata da buqatar qaruwar kowanne namiji cikin rayuwarta. Tana da tarin matsalolin da
takeson ta kammala dasu tukunna,mazajen dake cikin rayuwarta kuma a yanzun ta
sallami kowa da kalar sallamar data dace dashi kafin ta sake sabon zubi.

A hankali motar ta dawo daidai gabanta ta kuma tsaya cak,sannan aka
sauke glass din motar,abinda ya bawa sassanyan sanyin ac din dake gauraye a motar
damar fitowa waje ya kuma daki fuskarta.

Sallamar da yayi mata ta tilastata waiwayowa ta dubeshi. Nutsatse
kuma kamili a ido,wankan tarwada wanda ko bai miqe tsaye ba ta tabbatar dogo ne.
Zagayayyar Fuskarshi da gemu ya yiwa qawanya,sai idanunsa dake saye a cikin glass.

"Bai dace ace zafin rana yana dukan wannan kyakkyawar fuskar ba.....shigo don Allah
na rage miki hanya". Jin kai da miskilanci cikin jininta yake,duk daga yanayin
kamalar data gani a fuskarta ya mata kwarjini amma saita sake dauke kai ba tare da
tace masa kanzil ba.

Murmushi ya saki,ya miqa hannu yana bude mata motar

"Ki shigo domin Allah". Ya furta yana tsareta da idanu har zuciyarsa yana jin tayi
masa. Duk da cewa akwai wani irin kwantaccen kwarjini akan fuskarta wanda bayajin
cewa ita kanta tasan tana dashi.

Kaman yadda magiyarsa ta dauki hankalinta haka bullowar kawu ta dauki
hankalinta. Duk da cewa daga nesa yake amma ta zuba masa idanu da kuma wannan komar
tata dake saurin karanto lissafin me lissafi. Cikin qasa da minti daya ta gama
karantarsa,zaiyi wuya ace ba ita yaje nema gida ba bai sameta ba ya fito. Batayi
shawara ta biyu ba ta juya a hankali ta kama murfin motar ta bude ta shige ta maida
ta rufe,daidai sanda motar ke tashi ya iso gurin.

"Kaga shegiyar yarinya?,ni zaki gudarwa?,don ubanki ai duk tantirancinki dai idan
dare yayi gidan adamu kike dawowa ki kwana ko?,to mu zuba dani dake.......meye
amfaninki muddin ba za'a moreki kudi ba?,ai amfaninki kiyita kawo mana kudi tunda
hanyar da kika zabawa kanki kenan" Ya fada yana yarfe hannuwa shi daya a gefen
titi,kai kace ya samu matsalar kwanya.

Juyawa yayi da zummar barin wajen,saidai taku biyu rak yayi wayarsa
keypad dake aljihunsa ta dauki kururuwa.

"Kai jama'a......Allah yasa ba bala bane.....kash.....shine wallahi" Ya fada yana
qoqarin danna madannin wayar da yayi tsananin tauri saboda ganin rayuwa da yayi.
"Hel.....helo bala.....don Allah kar ka damu.....ai in sha Allahu ina me tabbatar
maka damu za'a shiga wannan cacar.....yo ta ina zamuyi wasa?,bayan kai da kanka ka
tabbatar min mutumin nan attajiri ne......ai ina maka rantsuwa da Allah baka bina
bashin rantsuwa wannan karon arziqi ne yake kiranmu....inata buga buga naga na samu
adadin abinda akeso a shiga cacar dasu....kada ka damu,zuwa nan da dare in sha
Allahu zaka jini,yauwa na gode" Ya fada yana sauke wayar,ya soma laluben aljihunsa
don maidata ciki yana sake magana a fili.

"Idan ma Allah ya taimakeni na haye da wadannan kudaden ina zaki sake jina?,ai nima
na zama attajirin kaina don ubanki" Sai yaja qwafa sannan tsaki ya biyo baya,ya
juya yana sauya hanya.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 38


Sau biyu yana sake juyawa yana kallonta. Tun bayan sallamar da tayi
yayin shigowa motar bata sake cewa wani abu ba.

A nutse take da dukkan nutsuwarta,nutsuwar data sake janye ra'ayinsa a
kanta matuqa.

"Erhmmm" Ya danyi gyaran murya kafin ya dora da

"Na gode qwarai da baki wofantar da magiyata ba.....hakan ya nunamin kinsan darajar
dan adam....." Maganarsa ta sanyata dawowa tunaninta tare da tunasar da ita a inda
take. Batace masa komai ba,tadan dai motsa kadan alamun tana saurarensa,hakan ya
bashi damar ci gaba da magana.

"Da farko dai sunana alhassan.....ko zan iya sanin sunan malamar?" Sunan daya kira
kanshi dashi ya sanyata juyawa kadan ta kalleshi sannan ta maida dubanta ga kwaltar
da suke bisa kanta. Kaman ba zatace komai ba sai kuma ta motsa bakinta

"Sunana....." Sai tayi hanzarin dakatawa. Shima kaman sauran?,yana buqatar a bashi
stamp?,yana buqatar personal suna nashi tamkar dai sauran 'yan uwansa jinsinsa?. Eh
yana buqata,saidai shi din bata jin zatayi wani doguwar mu'amala dashi da har zai
buqatu ya zuwa stamp na musamman

"Da alama sunan nan me tsada ne ko?,sai na siyeshi?" Ya fadi yana dan satar
kallonta kadan fuskarsa dauke da murmushi. Kai ta girgiza a hankali

"Sunana sawwama"

"Nice and good name.....me azumi kenan?" Ya fadi yana dubanta kadan. Kafada ta
daga,koma meye ma'anar sunan bai zame mata damuwa ba,kawaidai ta bashi sunan ne don
shine sunan da yazo kanta.

"Ma sha Allah......gashi mun iso inda kika cemin,kuma ina da tarin abubuwan fadi
don inason alaqar tamu tayi nisa,tafi haka zurfi,za'a bani wani abu kaman number
waya ko adress nazo na sameki?"

"Wayata bata da guarantee adress kuma bani da" Ta bashi amsa ta kai tsaye daidai
sanda yake tsaida motor din a inda ta nuna masa.
"Waya ba guarantee adress aishi zai zama babban guarantee ko?....me yasa kikace
baki da adress?"

"Saboda bamu da gida" Ta sake bashi amsa kai tsaye sanda take dubansa da fararen
idanunta masu sheqi da hasken rana ya qara musu qyalli,abinda ya sake daukan
hankalinsa kenan. Murmushi ya saki yana jin tana sake burgeshi

"Alright.....nasan dai ba dan adam din dake rayuwa a titi.....amma bazan takurawa
zabinki ba......zaki iya bani dama ta uku?,damar yin magana dake a nan?" Numfashi
ta sauke a hankali tana jin ya takurata da yawa,ta daga hannunta dake daure da
agogo ta kalla sannan ta sauke tana juya idonta daya sashen alamun qosawa

"Mintuna biyar kawai"

"Na gode" Ya fada yana gyara zamansa sosai.

"Bari na tafi kai tsaye kada na cinye mintunana ko?" Ya furta yana sake sakin
murmushi. Batace masa komai ba still,saidai ta kafe idanunta ne saman qofar gidan
dake gabansu kadan. Tunaninta yafi karkata akan gidan,tana tunanin me zataje ta
taras?,wanne abu zata samu cikin gidan.

"Tunda na ganki sawwama naji zuciyata ta kwanta dake.....ta kuma kamu da
sonki......naji kuma a raina na samu matar aure.....ina fatan zaki bani dama....."
Statement dinsa na qarshe data samu fahimta kenan.

Waiwayawa tayi ta dubeshi,shima idanunsa yana kanta,da alama ya gama
dukkanin bayanansa ita yake da buqatar jin ta bakinta. Dauke duban nata tayi,sannan
ta saka hannu ta bude murfin motar ta zura qafafunta ta fito. Da mamaki yake binta
da kallo har zuwa sanda ta maida masa murfin motar ta rufe,tadan rage tsaho kadan
tana dubansa da shiny eyes dinta

"Na gode da karamcinka......amma kayi haquri.....babu aure a rubuce cikin
rayuwata.....na barka lafiya" Ta motsa labbanta a hankali sannan ta janye jikinta
daga motar.

Soma takawa tayi a hankali tana barin wajen,AURE na daya daga cikin
abinda take mantawa dashi a rayuwarta. Aure yana cikin abinda yake a lissafin
qarshe cikin abubuwan da suke ba dole ba a rayuwarta. Aure yana daya daga cikin
abinda take masa wani irin kallon da batasan ajin data zubashi ba.....babu shi ko
kadan a dictionary dinta,idanma anyi zancensa,tana masa kallon wani baqon abu wanda
batasan ranar da zata saba da ji ko ganinsa ba,bare azo da batun wanzuwarsa akan
kanta.

Ko kadan bata damu da tsaiwarsa a wajen ba,abu daya ta sani.....kaman
sauran mazan,yadda basu da masaniyar daga inda ta fito......hakanan bata basu qofa
ko qanqani game da sanin inda zata ko inda zata shiga. Don haka bata kutsa kanta
cikin gidan ba sai data kadar masa da hankali,ta kuma tabbatar ya bar layin.

Da sallama a bakinta ta shiga madaidaicin tsakar gidan dake shimfide da
sabon simintin da bata jima da sanyawa ayi musi shi ba saboda jin dadinsu.

Yara ne aqalla kusan guda biyar wadanda shekarunsu bazai haura goma
zuwa sha uku ba. Biyu daga cikinsu wanki sukeyi,daya kuma tana wanke wanke,yayin
da guda dayar take jawo ruwa a rijiya tana zubawa a babban mazubin ruwan da suke
amfani dashi a gidan.

Sallamarta ya sanya kowacce ta watsar da abinda takeyi,suka kuma rugo
da gudu suna rige rigen isa inda take. Kyakkyawar fuskarta ta fadada da fara'a
itama ta buda hannunta tana tarbarsu,daidai sanda muryar matar ta iskesu
"Ku da waye haka?" Ta bayyana tare da qarashen tambayarta tana qoqarin daura
dankwali saman kanta.

Murmushi ne ya wadaci fuskarta itama,kakkaurar matar ma'abociyar
tsaho da qiba,saidai alamu sun nuna yanayi na rayuwa ya sanya qibar zubewa sai
saura data zama halittarta ce ba zata iya rabuwa da ita ba. Baqace wannan ya sanya
dukka kamanninta sukafi karkata ga kamannin babarbariya.

"To ku barta ta qaraso mana" Ta fadi tana juyawa cikin dakin da ta fito,dukansu sai
suka bi bayanta harda sabreen daketa jefawa yaran tambayoyi.

Tare suka zauna da yaran saman shimfidaddiyar dardumar da matar ta
shimfida saboda sabreen din,daya daga cikin yaran ta miqe ta fice sai gata da ruwa
adan qaramin jug da cup,yayin da sauran sukaci gaba da zama a kewayenta.

"Ina Ayshatu?" Tambayar farko da sabreen tayi mata bayan sun gama gaisawa,tambayar
data sanya yaran suka miqe daya bayan daya suna fita a dakin.

Bata ce komai ba matar saita miqe tana dosar wata qofa dake maqale a
falon,itama batace komai din ba ta miqe ta biyo bayanta.

Yalwataccen daki ne dake wadace da tsafts,ba komai a qasan sai wata
lamusashiyar katifa guda daya yashe a qasa. Daga samanta idan ka duba da kyau mutum
ce a kwance data lulluba duka jikinta. A sanyaye sabreen ta qarasa gaban katifar,ta
saka hannu ta yaye rufar bakinta yana rawa ta kira sunanta

"Aishatu?" A hankali ta ware idanunta akan sabreen din,sai kuma wani busashen
murmushi ya subucewa kyakkyawar fuskar yarinyar

"Aunty....kece kika zo?" Ta tambayeta da siririyar muryarta. Kasa riqe kanta
tayi,sai kawai tayi qasa da kanta hawaye yana diga daga idanunta. Tana jin tausayin
yarinyar kamar zai fasa zuciyarta,tana jin kamar zata narke a wajen,tana jin inama
ace tana da ikon fidda ciwo ta farat daya daga jikin mutum a yanzu yanzu basai
anjima ta cisgeshi daga jikin ayshatu

"Ko baki da ikon cire mata shi yanzu yanzu.....kina iya sama muku dama ke da ita na
samo mata lafiya a duk inda lafiyar take a fadin duniya" Wani sashe na zuciyarta ya
bata amsar data motsa mata wani qwarin gwiwa daga can qasan zuciyarta. Wannan ya
sanya ta sake daga idanunta tana kallon aysha. Allah ne kadai yasan bila'adadin
mata da yaran da suka shiga irin yanayin da ayshatu ke ciki duka sanadin TAIMAKO.
Lalacewar al'ummarmu abune me matuqar ban mamaki da daure kai. FYADE ba'a daukeshi
da wani muhimmancin da me aikatashi zai fuskanci hukunci mafi tsananu ba a tsarin
doka. Tana iya tuna yawan kudaden data kashe,shige da ficenta da kai kawo data
dinga yi kafin ta samu ayiwa azzalumin hukuncin da doka ta tanada. A abinda ya yiwa
aisha,ba hukuncin daurin shekaru take da buqata ba......lahira yafi kamata ya
baqunta yaje ya hadu da hukuncin mafi iya hukuncin masu hukunci.

Sosai ta bawa zuciya da gangar jikinta qwarin gwiwa,ta zauna sosai
ta yiwa yarinyar komai. Ta bata abinci ta kuma dinga hilatarta,har suka dinga hira
tana saurarensu murmushi yana subuce mata. Hakan ya sanyaya ranta kafin su kebe da
ummaa ta sake mata bayanin data yi mata a waya.

"Waje nakeson a fita da ayshatu,inason ta warke sumul taci gaba da rayuwarta,duka
duka shekarunta sha uku,ya kamata ta rayu kamar kowa" Ta fada zuciyarta tana mata
zafi. Allah ya dora mata tausayin yaran da matar kanta da batasan asalinsu ba,amma
dukka dawainiyarsu kusan kaso tamanin cikin dari tana a wuyanta,hatta da hayar
gidan da suke zaune a ciki kuwa,banda abinci da ma karantarsu rayuka shida.
Da idanu ummaa take bin sabreen. Tasan cewa dukkaninsu babu wanda suka
hada dangantaka a tsakaninsu,amma suna jin juna kamar 'yan uwa,suna kuma ci gaba da
tsananin shaquwa da juna.....kuma a yanzun sune 'yan uwan kawunansu.

"Sabreen......kiyi iya abinda zaki iya mu barwa Allah sauran.....samun maganin
ayshatu a gida Nigeria ma miliyan nawa ya kama bare ayi batun fita da ita
waje?,kinsan miliyoyin kudin da za'a cajemu?,daga visa passport masauki abinci da
zaman asibiti zuwa kudin magani?" Shuru sabreen tayi tana saurarenta,tana jin
zuciyarta na wani irin ciwo,irin ciwon da mutum kanji a duk sanda yake tsananin son
abu amma babu ikon samuwar wannan abun gareshi. Numfashi taja sosai ta aje tana
duban maama

"Allah zaiyi cikin iko da isarsa......na tabbatar Allah bazai taba wofantar da
bayin da aka zalunta ba" Kai ummaa ke jinjinawa tare da yaba tauhidi da yaqinin
sabreen.

Ta jima dasu saidai hankalinta yana kan asibiti,don haka lokaci kadan
ta qara akai tayi musu sallama bayan ta aje musu kudi kaman yadda ta saba da basa
wuce cefane da zirga zirgar makarantar yaran.

Tana hanya zuciyarta kamar ta fashe,hakanan ta sake jinta a rikice
bayan fitowarta daga asibitin bayan taji bayani daki daki na yadda zata fita da
ayshatu waje ayi mata aiki.

Kudade ne masu kaurin da a yanzun bata dasu bata kuma bawa wani
ajiya ba. Batasan tayi farautar kudi don ta ajiye ta tara abun duniya ba......tana
farautarta ne don ta raba a tsakanin mabuqata marasa galihu irinta,yanzun ka buqata
ta taso mata wadda take da girma da muhimmanci a rayuwarta. Sai taja numfashi mai
nauyi,tabbas a yanzun zatayi FARAUTA ta ainihi,tsakanin MIKA'IL YA'AQOUB da kuma
MASHKUR waye zaiyi aman wadannan maqudan?.

_tofa zamuji waye,komarta zatayi kamu ko kuma wannan karon ita zata shiga komar?_


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 39


Tun a hanya har takai gida zuciyarta na karakaina ne tsakanin sunyen
mutum ukun MIKA'IL MASHKUR KO KUMA YA'AQOUB.

Da sallama ta shiga parlor din bayan ta tsallake tarin idanun da a
kullum suke da tuhume tuhume da zarge zarge a kanta masu tarin yawa. Ta samesu suna
hada uniform dinsu guri guda nadra zata wanke. Huda kuma na kokawar kammala abincin
dare,don da alama basu jima cancan da dawowa islamiyya ba.

Takan samu cikakkiyar nutsuwa a duk sanda ta dawo gidan ta samesu
lafiya lau kaman yadda ta fita ta barsu. Haneefa ta zaburo da gudunta ta daneta
tana mata sannu da zuwa

"Auta na gaji.....mu zauna". Ta fada tana direta saman kujera itama ta zauna a
gefanta.

Jakarta ta bude ta fiddo alawa cikin wadanda ta siyawa su aishatu ta
musu tsaraba ta miqawa nadra da haneefa
"Karbi huda" Ta furta sanda huda din ta gama goge qasan tiles din inda suka zubda
ruwa.

A nutse ta tako,ta zauna a hannun kujera ta miqa hannu tana karba din
idanunta akan fuskar Sabreen.

"Komai lafiya ko?" Sabreen din ta tambayeta tana kallonta ganin kallon da huda din
ke binta dashi.

Kai ta gyada tana kauda dubanta daga kanta

"Lafiya lau anty" Da idanu sabreen din ta rutsata tana kallonta,kamar ba zata ce
komai ba sai kuma ta buda baki a hankali

"Ko yauma kunnuwanki sun sake ji miki wani magana daga bakunan mutanen gidan nan da
kika sakashi a ranki?" Ta mata tambayar tana tattara hankalinta a kanta.

A hankali ta girgiza kai alamun aah

"Huda" Sabreen ta kirayi sunanta kanta tsaye. Daga kai tayi ta kalleta sai kuma ta
qara sadda kanta qasa

"Dawo nan ki zauna" Ta fada tana nuna mata gefanta zuciyarta tana bugawa fiye da
yadda ya kamata ace ta buga din. Ko kadan bata qaunar taga sauyawar yanayi daga
motsin kowannensu. Duniya da mutanen cikinta tsoro suke bata matuqa.....irin tsoron
da babu shi a cikin FARAUTARTA amma tana dashi cikin DUNIYARTA data 'yan uwanta.
Sune dukka rauninta a rayuwa,sune tsoronta kuma sune kwanciyar hankalinta.

Kamar yadda ta buqata haka ta zamo ta zauna a gefanta,saidai har yanzu
bata yarda sun hada idanu ba

"Huda.....kalleni nan" Ta fada tana kausasa muryarta. Yadda ta bata umarni kadai ya
gaya mata bada wasa take ba,ta furta umarnin ne tun daga tsakiyar zuciya da kuma
ruhinta,don haka ta dago din ta dubeta kai tsaye kaman yadda tace

"Zan maimaita tambayar dana miki,kuma ina buqatar ki bani amsarta kafin nadra da
haneefa su sake dawowa dakin nan......mene a ranki?,meye damuwarki?"

"So nake ki daina fita yaaya......ki zauna a gida kaman kowa" Ta fadi muryarta tana
rawa. Idanunta sabreen ta maida tadan lumshe kana ta budesu. Fargaba tadan saukar
mata,yau huda ce ta fara tararta da wannan maganar,gobe sai nadra jibi sai
haneefa?. Tambaya ta yiwa kanta amma kuma tana baiwa kanta yaqinin abinda zai faru
kenan a zahiri.

"Kina zargi na ne kema huda?" Tayi mata tambayar takai tsaye tana kallon qwayar
idanunta. Kamar maganar ta daketa sosai hakan ya sanyata daga kai da hanzari ta
kalleta tana girgiza kai,sai kuma ta sake sauke kan nata qwalla tana gangaro mata.

"Yaushe kika soma zare audugar dana baki ki sanyawa kunnuwanki akan zancan
mutane?,yaushe kika samu cikakken zaman saurara da fahimtar maganganun
mutane?,yaushe hankalinki ya fara kaiwa nan huda?" Ta furta idanunta suna
qanqancewa,wanda hakan zai nuna maka zallar radadin da takeji a zuciyarta.

"Ina nan yadda kika sanni huda.....babu kuma abinda zai canzani......gwagwarmaya da
fadi tashin da nayi a

Please Login or Register in order to submit comment