You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Da fari tsakaninsa da amna idanu ne kawai,baya ma zama.inda take
bare daukarta,ta fahimci kaman wata kakkaifar gaba ce tsakaninsa da jinsin mata,ita
kadaice mace cikin miliyoyin mata da take samun kulawa da qauna daga gareshi wanda
ita dinma sai da suka debi shekaru yana dari dari da ita. Bata tsananta tuhuma
ba,tasan incident din daya faru dashi a baya akan mariya da mariya sune suke
hunting dinsa.

Wannan abun bai karye ba tsakaninsa da amna din har sai sanda ta fara
laulayin haqori. Kashin haqori matsananci daya sanya mata amai da zawo da yaso
wucewa da rayuwarta. A ranar a kuma daren har sun fidda rai da ita,tayi wani suma a
hannunsa. A ranar taga gigicewa mai tsanani a tattare dashi,shi daya ne yake da
qwarin gwiwar daya dinga mata wasu abubuwa don dawo da mumfashinta,sai gashi cikin
ikon Allah ta dawo.

Tun daga wannan ranar kulawarsa a kanta ya zama na dabanne,sabo ya
shiga tsakaninsu,ta tashi ta ganshi a matsayin yaya kuma uban da bata da kamarshi.

"Kamar akwai inda zakaje ko?" Anni ta tambayi musaddiq da suke hira da farouq


*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*
*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 46
____________________________
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

*_assalamu alaikum warahmatullah_*

*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada
ko rashin ingancin kaya?_*

*_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_*

*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke
iya bada kayansa akan hakan ba_*

Shadda
Laces
Atamfa
Kayan yara English wears dana jarirai
Qawatattun handbags
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
Huluna na maza da mata yara da manya socks
Takalma na maza da mata yara da manya
Lafayas
Sarqoqi agoguna banguls da rings

_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_

_bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_
*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?
_*

*_masu manyan qarfi da matsakaita?_*

*_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda
zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_*

*_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_*

*MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA*

*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU
RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*

*_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_*

*_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*✌🏽 ✌🏽 ✌🏽 ✌🏽 ✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽
✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽
_____________________________


Tana tsareshi da ido. Duba daya ya yiwa annin ya fahimci tambayar ta yita
ne kawai bawai don tana son sanin amsa daga bakinsa bane....aah,ta yita ne don
tanason tunasar dashi wani abu

"Kamar zan fita din......amma kuma banason fitar" Ya fada yana kallon qatoton
agogon dake manne a bango.

"Amma dai ina fata kana sane da girman umarnin uwa ko?,sannan kana sane da girman
alqawari......haka kuma uwa uba baka manta dashi ba?" Dukka jikinsa ne yayi
sanyi,sai yadan sadda kansa qasa kadan. Lallai ba shakka inda ace dukka iyaye haka
suke tamkar anni da zaiyi wuya.....za'a tirza,hakanan za'a sha fama kafin a samu
baragurbin yara cikin al'umma.

Kai ya jinjina,sai ya soma ture plate din gabansa,ya dauki wayarsa ya
sanya gaban aljihunsa ya miqe yana fadin

"Sai na dawo"

"Allah ya kiyaye......" Anni ta bashi amsa tana satar kallonsa. Tako ta ina ba
alamun jin dadin zuwan da zaiyin,ba wani sukuni walawala ko farinciki irin na da a
sanda zai hadu da iyayensa.

Da kallon tausayi ta bishi dashi har ya bacewa ganinta. Ta janye
idanunta tana sauke zazzafar ajiyar zuciya,sai suka hada idanu da farouq dake zaune
yana cin abinci a hankali.

"Daga musaddiq har muhammad tausayi suke bani har yanzu,har yanzu wannan tabon da
aka barwa rayuwarsu yana tare dasu bai goge ba". Kai farouq ke gyadawa yana duban
anni

"Gaskiya kika fada anni......musaddiq nashi me sauqi ne,ba wanda abun ya yiwa illa
matuqa yake kuma taba halayensa da dabi'unshi har yanzu irin fu'ad......akwai fushi
saurin daukan zafi da yawa cikin halayensa......shariya rashin son yin magana ko
hira da kowa,wanda yawancin lokuta idan irin hakan ta faru nasan abinne ya motsa
masa,shi yasa sau da dama nake maida kaina wani iri a wajensa saboda na sama masa
farinciki duk qanqantarsa". Kai kawai anni ke jinjinawa,har cikin zuciyarta tana
jin ba dadi,abun kuma yana tabata.
Wani gauron numfashi ta sauke tana ajiye wayarta data dauko wadda ta
kasa juriya tana shirin kiranshi kenan. Kacokam ta aza idanunta ga bakin qofa tana
tsumayin qarasa shigowarsa tana jin yadda yake gaisawa da ma'aikatan gidan faran
faran. Irin sakewa da ta tabbata idan ya shigo ciki baya iya irinta da ita.

Da sallama ta yaye kakkauran curtain din dake bakin qofar ya shigo.
Ganinsa kawai da tayi,zuciyarta kuma na ayyana mata cewa wannan din d'anta ne halak
malak sai taji wata izza ta sake daduwa cikin kanta

"Kina da wannan kadarar.....kina da wannan damar don me yasa zaki bari a qwace miki
su cikin sauqi haka?" Ta yiwa kanta da kanta wannan tambayar.

Gyara zamanta tayi sosai sanda ya iso ciki,ya zauna saman daya daga
cikin kujerun yana dan tsagaita dubansa daga inda take

"Barka da dare" Ya furta a nutse,har yanzun baya jin wani sabo shaquwa ko soyayya
nata a tattare dashi,yana jinta kamar kowacce baquwa......yana kuma jinta kamar
kowanne baqon abu na rayuwarsu.

Qoqarin wadata fuskarta da fara'a tayi kaman yadda zuwaira ta
shawarceta don samun isa ga burika da muradanta cikin sauqi

"Ai na cire tsammani da zuwanka musaddiq......wai dama haka duniya take?,......na
zaci komai girman laifin uwa d'a yana iya yafeshi ko?" Ta fada murya a sanyaye.
Idanunsa kadan ya daga yana kallonta,ya kasa gamsuwa da ita har yanzu,yana jin
inama ace yadda ta furta wadannan kalaman a bakinta haka suke har cikin zuciyarta?.

"Kibar wannan maganar maamah,abune daya riga ya shude,kin wuni lafiya?" Ya maida
maganar da tambayar lafiyarta

"Alhamdulillah.....saidai yayanka ya watsar dani musaddiq,ya barni cikin buqatar
rayuwa da abubuwan da a zahiri ya cancanci ace nafi qarfinsu amma suna neman fin
qarfina" Ta fada a karye.

Mamaki sosai ya sake lullubeshi har ya gaza jurewa sai daya daga
idanunsa ya qarewa suturar jikinta da kuma falon da take ciki kallo. Tana cikin
ni'ima da wadatar da babu abinda ta nema a rayuwarta ta rasa amma tana kiran
abubuwa da dama sunfi qarfinta?. Anya kuwa da kyakkyawa da kuma tsakakkiyar zuciya
ta dawo cikin rayuwarsu?,anya wannan tsohon maqalallen halin baya tare da ita?.
Shine mutum na farkon da yafi kowa sanin cewa hammansa baya wasa da ci sutura sha
muhallinta da lafiyarta,bayan ya dauke duka wannan kuma da wani ajiyayyen salary na
dubu dari duk wata,duk da aqa'ida ba wata qwaqwarar buqata guda daya da ashekarunta
ta yima rayuwarta saura. Hatta da man fetur da ake zubawa motocinta guda biyu bai
daukewa kansa ba,to me take nema sama da wannan cikin dukiyar da aka sameta a sanda
ta nisancesu?,cikin dukiyar da aka sameta a sanda ta gujesu?,cikin dukiyar da aka
sameta a sanda take can cikin duniya tana kalar rayuwar data zaba?,kalar rayuwar
data fifita sama da ta rayu dasu?.

"Bana jin akwai sauran abinda hamma ya rageki dashi maamah" Ya gaza jurewa sai daya
fadi mata idanunshi tsar a kanta zuciyarsa kuma cike da mamakin furucinta. Idonta
itama takai kansa tana kallonsa

"Yanzu a naka tunanin a matsayina na mahaifiyar mutumin da ya mallaki kamfanin
sarrafa diamond......mutumin da yake da harqalla da manyan kamfanoni da suke a
qasashen waje.....qasashen wajenma manyan qasashen da suka tumbatsa ta fannin
tattalin arziqi da qarfin mulki da iko.....mutumin da yake noma kaso mafi tsoka na
dukka abincin da Nigerian dama Africa gaba daya suke ciyar da al'ummarsu amma ace
abinda zai iya cira ya bani na zallar kudi shine dubu dari?" Ta aje masa tambayar
ranta yana fara mata zafi amma tana danneshi.

Ci gaba yayi da kallonta yana fahimtar abubuwa da dama tattare da ita,a
yau kuma a yanzun sai yaji shima ya shirya tambayarta

"Idan har ya miki kadan kuma hamma bai kyauta ba......wacce buqata kike da ita da
zakiyi da kudi?" Tambayar sak irin ta dan uwansa kenan......amsar kuma da ba zasu
taba samunta a bakinta har abada

"Musaddiq......yanzu bayan ci sha sutura da biyan duka sauran buqatu da zasu taso
Shikenan iya abinda nake da buqata a matsayina na 'yar adam?,bayan ina da d'an da a
kullum idan zai bani kyautar million daya bazaiji komai ba a jikinsa daga abinda ya
mallaka?"

"Maamah......kin taba zuwa da wata buqata kinaso ayi miki kaza?,ko a yiwa wane kaza
wanda ba zallar kudi zaki amsa ba da hamma ya taba qinyi miki?" Ya jefa matar
tambayar yanason gane ainihin gaskiyar da takeson lullubewa

"Kai musaddiq.....kalleni nan......dukkanku ke da fu'ad nina haifa abuna......banyi
lalacewar da don zaku yimin wani abu sai na zama tamkar almajira a wajenku ba....."

"Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki" Ya fada kawai don kawo qarshen zancan. Can
qasan zuciyarsa babu gasgatawa ko yarda da ita ko kadan. Idan yayi rantsuwa ko
kaffara bazaiyi ba,ba haka siddan hammansa yaqi yarda ya sakewa maamah tsurar kudi
ba,ya yadda dashi dari bisa dari,yana komai bisa bayyananniyar hujja da kuma
dalilai. Kawai dai mutum ne shi me tsananin zurfin ciki da miskilanci,wannan ya
sanya idan ya aiwatar da abu babu lallai ka fahimci don me yayin?,kuma bazai taba
zama yayi maka wani bayani ba game da hakan.

Shuru ne ya biyo baya na wasu mintuna,tanata qoqarin controlling kanta
don har yanzu bata kai ga cimma burinta na abinda takeson taji ba. Ta furzar da
iska kadan sannan ta fara kiran daya daga cikin masu aikinta.

Kamar ko yaushe da sassarfa ta iso saboda tsoro da gudun sabawa
umarninta.

"Ki sauke kayan abincin nan a nan....ko dining din zaka hau kaci?" Ta tambayeshi
tana dubansa.

A zahirance so yake ya gaya mata ya qoshi,baya buqatar cin komai,amma
ya tabbata fadin ba abinda zai haifar sai wani rigima da tashin hankalin,don haka
yadan gyara zamansa

"Ta kawo nan din" Sai ta juya ta watsa mata kallo

"Kinji ai abinda yace". Suna zaune ta dinga sauke kwanukan abincin. Warms na
alfarma masu tsananin tsadar da ko a gidajen masu sukuni sai wane da wane.

Da kanta maamah din tayi serving nasa don buqatarta shine ya saki jiki
yaci sosai ta yadda zata samu daman yin magana dashi ta kuma samu duka information
din da takeso.

"Bismillah sauko" Ta fada da salon bada umarni nakai tsaye. Bai musa mata ba ya
zamo ya sauko din,sai ya fara kai hannunsa ya dauki glass cup na lemo yana juyashi
a hannunsa.

Spoon ta dauko ta qara a plate din,ta kalleshi da murmushi

"Muci tare ko?" Kai ya gyada kawai yana duban kwanon. Komai yayi masa banbarakwai.
Ko a shekarun baya da suke da qananun shekaru ya iya abinda qwaqwalwarsa zata iya
riqewa baya jin sun taba zama kwano daya,sai yanzun da ya zama cikakken mutum?. Ko
a baya sanda bai kammala iya cin abinci ba idan ta zuba musu ta tura musu ta shiga
sabgar gabanta hamma ne ke zama ya bashi komai zafinsa har sai ya qoshi.

Hira take sako masa a hankali a hankali,tana cin abincin yana juya
cokalin kawai a ciki bayan ya dire cup din lemon.

Sai bayan data soma karantar kamar sakin jiki tattare dashi sannan ta
aje nata spoon din tana dubansa cikin murmushi

"Ya akayi kai da dan uwanka musaddiq wanda duk duniya bashi da kowa bayan kai amma
ka nesanta


*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 47


"Ya akayi kai da dan uwanka musaddiq wanda duk duniya bashi da kowa bayan kai amma
ka nesanta kanka da kalar sana'arsa ka maida kanka baya ta hayar sanya jikinka a
al'amura ta harkar gona?,bayan sana'ar ba taka bace,gadon gidan Alhaji hamza kibiya
dinne zasu daukeka su cusa ka?,sannan su raba dansu da fu'ad kai su tsigeka daga
gareshi?,wanne irin ragon azanci ne wannan shirme da shashanci?,sannan wannan kadai
ya isa ya nuna akwai mummunar manufa da qulli cikin zuciyar amina da manufa aka
shirya wannan".

Maganganunta sunyi masa girma qwarai,mamaki kuma ya lullubeshi har sai
daya tsaya kawai yana duban yadda maamah din ta haqiqice.

".....bazan yarda ba a rabamin kan yarana,bayan a mahaifa guda suka kwanta......don
wannan zalunci ne kawai,duk yadda zakayi ka nema komawa sashen da dan uwanka yake
aiki,shima kuma zan masa magana kaji?" Sai ta qarashe kuma cikin kwantar da harshe
saboda magana ta gaba da takeson yi.

"To" Kawai ya iya cewa da ita,ya sani basai an gaya masa ba,maamah din tayi nisan
da batajin kira,hakanan dukkan wani bayani da zaice zaiyi mata yana zaman bata
lokaci ne kawai a wajenta.

"Yanzu bayan kamfanin diamond ai ina sanya ran zuwa yanzu addu'ata ta cicciba
Muhammad izuwa mallakar wasu boyayyun mafanunnukan ko?" Ta fada tana murmushi tare
da tsare musaddiq da kallo.

Dubanta yayi sosai,yana ji har cikin zuciyarsa da gangar jikinsa bai
gamsu xa yanayin tambayar tata ba,don haka girgiza mata kai kawai yayi

"Bansan komai a kanshi ba maamah tunda ba sashe daya muke dashi ba" Wani abu ne ya
tsaya mata a wuya,amma sai tayi qarfin halin danneshi ta amsa masa da

"Haka ne......amma dai baka ce bakasan qarfi da nauyin kudaden da suke shigo masa
ba ko?" Sake daga kai yayi yana dubanta zarginsa yana sake tabbata

"Bana ce ba maamah.....abune da ya shafi sirrinsa kuma ba a qarqashinsa nake aiki
ba.....ni ina qarqashin farouq"

"Eh to.....maganar gaskiya sai yanzu na fahimci kimiyyar da ta sanya amina tayi
kutin kutin din cusa danta wa Muhammed kai kuma ta rabaka dashi.....kana jininsa
wanda bashi da na biyunsa a duniya amma bakasan komai nasa ba?.....wanda ni nayi
imanin a yanzun inda zan zaunar da shi saddiqun nayi masa ire iren tambayoyin da
nayi maka din yana da amsar kowacce fes?.....wannan itace hanya mafi sauqi da zata
samu salwantar da fu'ad da dukka abinda ma ya mallaka". Idanunsa ya runtse yana jin
zafin mummunan zaton da maamah din ke jifar 'yar tahalikar dashi.....matar data
zame musu bango majingina,matar data zabi farincikinsu akan nata.....matar da
silarta ne a yau suka zama dukkan abinda suka zama din.....suka kawo izuwa matakin
da suke kai a yanzu......matar da banda ita da yanzu shi da muhammad din duka da
take taqama dashi ba'asan a wacce shiyya nahiya ko yanayi suke ba.

"Maamah..." Ya fada yana bude idanunsa a kanta ba tare da ya shirya tsaida
maganarta ba.

"Duk yadda kike tunanin anni fa ba haka take ba.....idan baki godewa anni ba bai
cancanci ki jefeta da mugayen zato ba......kamfanin nan da rayukanki suke baci akai
asalin diamond din da aka samu ba hamma bane kawai ya sameshi ba.....a lokacin suna
tare da BB farouq......"

"Amma shi ya haqo shi kuma ya samu nasarar tsira dashi.......ka dauka bansan dukka
wannan ba?" Tayi maganar tana tsareshi da idanunta da suka cika da bacin rai.
Lallai sai sun nuna mata fifikon matar can akanta?,bayan bata da masaniya akan
sanda ta dauki cikinsu bare kuma haihuwarsu?.

"Eh hakane.....amma shi BB farouq baida sha'awar harkar diamond noma yafi so shi
yasa......"

".......shi yasa aka fidda haqqinsa aka bashi nasa kason......dukiya ta zama ta
muhammad sh kadai......amma duk da haka basu qyaleshi yana amfana da abarsa shi
kadai ba.....saboda nasa kason da nasa bangaren na haqar ma'adanai yafi noma
albarka da kawo samu,shi yasa suka tattare shi suka kuma dora masa dukan lalurarsu
suna zuqeshi sannu a hankali.....suka kuma nesantaka dashi.....suka haramta maka
sanin komai daya shafeshi ta cusa danta" Ta qarashe maganar da wani irin ciwo da
emotiona daga zuciyarta

"Maamah....." Ya kira sunanta yana son dakatar da ita. Baya qaunar ko kadan
wadannan kalaman marasa dadin sauraro suna fita daga bakinta zuwa kawunan mutanen
da suka yiwa rayuwarsu tsaiwar da babu wani mahaluki daya taba yinta

"Ni na zabi fannin noma da kayan abinci......basu suka sani ba....ba wanda ya bani
shawara....."

"Musaddiq!.....ina fada kana fada duk akan mutanen can?,to waishin ko zaka koma
cikin aminatu ta sake haifarka a matsayin danta bani mariya ba?". Maganar yaji tayi
tsauri da yawa,kuma ya sani uwa uwa ce komai lalacewarta,hakanan ba'a canzawa tuwo
suna,don haka ya miqe tsam,don dama a qagare yake da wannan zaman da baiga
ma'anarsa ko alfanunsa ba. Ya dauka zasuyi hira ne irin ta d'a da uwa?,ya dauke
zata tambayeshi bayan ta barsu yaya suka rayu?,ya dauka zata nuna nadaman barinsu
da tayi sun basu gama zama mutane ba?,sai gashi gaba daya hasashenta da hangenta
ba'a nan yake ba?,da gaske ne abinda zuciyarsa take raya masa ta biyo DAUKAKARSU DA
DUKIYARSU NE?.

"Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki,sai da safe.....na barki lafiya" Ya fada
yana juyawa a hankali yana fita daga falon zuwa farfajiyar gidan.

Da kallon takaici ta bishi,shi kansa me sukuni da wadata ne wanda zai
iya kashe mata ko nawa take buqata ballanta a gangaro kan muhammad,mahaukatan
kudade ke shigo musu daga harkar noma kayan abinci da sauran kayan masarufi da
sukeyi,kuma su rabasu cikin qasashen Africa dama qasashen qetare. Tana da dukka
information daidai gwargwado a kansu.....amma sai gashi wadatar kowannensu yanason
zame mata hoto.

Yadda ranta yake a bace sai zama ya gagareta,takai ta kawo kusan sau
uku tana ji har cikin zuciyarta ya dace ta gaggauta daukan mataki,ya kamata tayi
wani abu akai kada komai yaci gaba da tafiya a haka. Daidai sanda takai dab da
qofar taji horn na mota da kuma shigowarta farfajiyar gidan,bata bi takai ba amma
zuciyarta tana mamakin baqon daren da sukayi.

Mintina uku kawai tayi sallama cikin falon. Sallamar data sanya maamah
din waiwayowa tana amsa mata fuskarta babu walwala.

Sanye take cikin wani lafiyayyen lace ruwan zuma. Kallo daya tak zakasan
cewa ba na qananun mata bane,ba kuma qananun kudi aka sanya aka mallakeshi ba haka
dinkin boubou din da aka zuba masan. Zagayayyen dauri ne saman kanta da zai gwada
maka adadin wayewarta da kuma zurfinta a sanin data yiwa duniya. Mayafinta na yafe
a kafada daya,daga hannayenta har zuwa wuyanta adon sarqa zobe da bangles ne da
babu ko tantama da shakka na gold dinne. Ita din idan ka kalleta baifi ka bata
shekaru arba'in da biyar ba,saidai kuma ta dara hakan,don a yansu tana dosar cika
shekaru sittin ne a duniya.

Daga bayanta wata macece wadda duka ba zata haura shekara arba'in ba.
Riqe da wata kyakkyawar handbag wadda babu ko tantama jakar matar dake gaba ne
saboda dacewa matuqa da tayi da kayan jikinta.

Maimaita sallamar tayi a karo na biyu tana duban maamah fuskarta a
sake. Wannan ya sanya maamah din tayi qoqarin sakin tata fuskar gami da sakaya
damuwarta a gefe,cikin mamaki da tarba me kyau ta matsa gareta tana tararta

"Hajiya......isowar yaushe?" Ta tambayeta tana murmushi

"Tun shekaran jiya fa?,gajiya nayi ma na gudo,amma ason dan ahalan sai farkon sabon
wata zamu dawo" Ta furta tana neman wajen zama.

Zaman itama tayi a kujerar dake fuskantar tata

"Da kyau.....ai ya kyauta wallahi,ko yanzu aikin huta ko?"

"Yadda ya kamata kuwa.....wai nikam musaddiq nake gani yana fita sanda nake shigowa
da mota?". Dan tabe baki kadan maamah din tayi sannan ta amsa cikin salon rashin
bawa maganar muhimmanci

"Shine mana"

"Hala bai ganeni ba,don baiyimin magana ba"

"Ko ya ganekin ma babu lallai ya miki magana ai harira" Ta amsa mata boyayyar
damuwar fuskarta tana bayyanar da kanta.

Kallon tsanaki hajiyar mamallakiyar sunan harira ta yiwa maamah kafin
tace

"Ban gane me kike fada ba mariya" Qarasa bawa sauran boyayyar damuwarta qofa tayi
ta fallasa kanta,don tambayar sa harira tayi mata ta zama tamkar susa ce tayi mata
akan ciwonta
"Ina da damuwa harira.....ina da damuwar da har kwanan gobe na gaza gano
maganinta".

A nutse hajja harira ta waiwaya ta dubi 'yar aikinta,wadda ke tsaye
daga gefe,tunda suka shigo taketa faman gaida maamah din amma bata ma jita ba bare
ta amsa

" Ajiyemin jakar ki fita daga waje ki jirani" Ta fadi mata. A ladabce ta ajiye
jakar sannan ta juya da hanzari tana ficewa,abinda ya bawa hajja harira damar maido
hankalinta ga maamah

"Nayi tunanin kawo yanzu kinyi nisa daga dukkan wani abu me suna damuwa daga randa
dan cikinki ya zama mamallakin kamfanin diamondchore?"

"Daga sannan sabuwar damuwa ta fara hajja harira" Maamah din ta furta ranta yana
matuqar quna

"Idan na kalli yadda kike fantamawa hajja sai na sake tabbatarwa kaina lallai akwai
aiki a gabana......aikin kuwa shine YADDA ZAN MALLAKE 'YA'YANA". Wani irin duba
hajja hariran take mata,sai kuma ta kyabe baki

"Keda wanne baccin kikeyi da baki aikata hakan ba mariya?,wanne gangancin ya
kaiki?,bakisan daga ranar da Allah ya yiwa 'ya'yanki arziqi ba.....akwai tarin
mutane da dama da suke marmarin juye matsayinki su haye kai ba?.......kin ganni nan
mariya?,kaf 'ya'yana babu wanda ya isa ya aiwatar da wani abu komai girmansa kuma
komai qanqantarsa ba tare da sanina ko yardara ko sahalewata ba.....ke koda matansu
ko 'ya'yansu zasu yiwa kuwa sai da sanina da yardaya,a cikinsu babu wani gida da
bansan me yake gudana a cikinsa ba 24hrs......yanzu haka katafaren gini na sanya
sukeyi na bai daya duka zamu zamana a muhalli guda....." Kai kawai maamh ke
gyadawa,a yau ta yarda ta miqa wuya ta kumayi surrender kan cewa harira ta fita
shu'umanci,iya yadda tae bada.labarin cike da izza da alfahari kawai ya isa gaya
maka gaskiyar haqiqanin zahirin abinda ke faruwa kenan......jikinta ya isa ya sake
qarfafa maka zancanta.....tsanin alfahari da takeyi yayin bada labarin kuma zai
gaya maka yadda take jin dadin yadda take tafi da rayuwarta.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 48



"Inaso na zama uwa mafi gata a duniya harira,inason na zama uwa mafi izza akan
yaranta......inason na zama uwa mafi zama abar alfahari abar nunawa a
duniya....inason 'ya'yana su dawo qarqashina.....na mulkesu kaman yadda ubangida
yake mulkar bawansa......su zamana a tafin hannuna kamar yadda jariri sabuwar
haihuwa yake zama a hannun mahaifiyarsa".

Wani murmushi hajja harira ta saki tana duban maamah

"Lallai mariya burinki me girma ne......amma dai kinsan ki baro kari tun ran tubani
ko?,ko mu da muka raini yaran

Please Login or Register in order to submit comment