You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani abu ta kasa maidashi daidai inda
yake hakan ya nuna masa alamar tayi masa bincike. Hatta da biro dake ajiye qwaya
daya tal saman teburin sai data karanci a yadda yake ajiye din,ta dauka ta kuma
gwada maidawa ta tabbatar ya zauna kaman yadda aka ajiyeshi. Wayarta ta fidda,ta
sake yiwa office din qaramin video komai da komai sannan ta maida wayar jakar,ta
kuma shiga aikin bincika komai daki daki.

Baya ga abinda suke nema taga abubuwa da yawa cikin office din,irinsu
condom dake nuna mata lallai riqqaqqen dan bin mata ne,taaba irin masu tsadar nan
da sauran abubuwan maye. Abinda ya sake darsa mata mugun tsanarsa kenan,wutar kuma
ta tabashin ta hanyar kwakwashe masa komai tana sake ruruwa cikin ranta. Ya zama
dole ta durqusar dashi,durqusarwar da bazai sake tashi ba.

Maida komai tayi kaman ba wani abu daya faru a office din,ta tattare
duk abubuwan da take nema din tayi musu ajiya ta musamman cikin jakarta. Hatta da
wani qaramin ledar cake da akaci aka barshi sai data tabbatar ta maidashi yadda
yake,ta gyara rolling dinta da kyau tana sauke numfashin samun nasarar kammala
komai ba tare daya dawo ba.

Maqoshinta taji ya bushe tana da buqatar ruwa,sai ta taka tana nufar
kyakkyawan fridge din dake girke waje daya.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 70


Turus tayi tana kallon yadda aka maqare gidan farko na fridge din da
wasu kalan kwalabe da bata saba ganin irinsu ba. A hankali take dubasu har ta
fahimci kwalaben na meye?.

Kwalaben giya ne tabbas,ta maida idanunta ta lumshe tana furta

"Innalillahi" Can qasan harshenta. Sai kuma taja jikinta baya a hankali tana
matsawa daga jikin fridge din don batajin zata iya shan wani abun sha daya fito
daga fridge din komai halascinsa.

Zuciyarta ke qara bugawa da tsanarsa haushi da kuma takaici.
Shikam mikail dame zaiji?,abubuwan ai sunyi masa yawa,sun masa yawan da batasan
wanne a ciki zai iya dauka ba. Kaman ana son bata amsar tambayarta sai qofar tayi
qaramar qara alamun ana budeta ne,ba jimawa ya bayyana cikin office din yana
dubanta da murmushi

"Am so sorry dear......ina fata banyi keeping naki da yawa ba......boss ne idan ya
tashi aikinsa tamkar engine.......baya gajiya,na samu na kubota da qyar".

Idanunta ta dauke daga kan files din da yake rungume dasu,wanda ta
tabbatar a cikinsa sauran bayanan da take nema suke. Ta kalato dukkan dauriyarta ta
jefeshi da qaramin murmushi

"You deserve it ai....."

"Wow......serious?" Ya fada da wani irin zumudi da zakwadi yana qarasowa gabanta
dab da ita ya zauna har yana neman hade gwiwoyinsu guri guda. A dabarance ta miqe
da sauri,sai ya bita da kallo. Taji a jikinta yana kallonta ne don haka ba tare
data juyo ba tace

"Bari nayi fitsari kadan"

"Oh....okay to dear" Ya fada yana dora files din saman table din cikin ransa yana
qissima yadda a yau din zai gwangwaje,a yau din zai kashe duk wata qishirwa tasa
dake damunshi a rai.....a yau zaiyi morewar da bayajin ko daren amarcinsa zaiyi
wannan.

Gaban madubij toilet din ta tsaya tana sauke numfashi idanunta akan
fuskartata. Muryarta can qasa tace

"Please jib.....muyi komai mu gama da sauri......banason ganin fuskarshi kwata
kwata"

"I know.....zanyi iya qoqarina......amma please kada kice zakiyi halin hawainiyar
nan taki" Dan murmushi ta saki,yasan halinta sarai,koda nawa aikin zai basu idan ta
motsa mata tana iya cancel dinsa

"Zanyi qoqarin nima" Ta amsa masa tana kunna famfo sai ta bige da daura alwala.

Mutum hudu ke biye dashi sanda yake takowa cikin veranda din idanunsa
saman takardar dake hannunsa yana sake karanta abinda take dauke dashi. Can qasan
zuciyarsa akwai wani kokwanto da mamaki,kusan zaman yau da suka fara yi da mikail
wanda ba'a qarqareshi ba saboda quracewar lokaci ya karanci kamar hankalinsa ba
gurin yake ba sam sam. Yana karance da kuma bibiye da motsinsa. Duk muhimmanci da
girman takardar a wajen kamfanin gaba daya amma har ya iya mantota cikin dakin
taron,wannan ya sanya ya yanke biyoshi da kanshi ya kawo masa don ya sake alamta
masa muhimmancin takardar.


"Wait here" Ya fadi a nutse ga mutanen dake bayanshi yana sanya code na qofar
office din Mikhail din ta bude ya murza handle din yana turawa can qasan ransa yana
jin kamar bai kamata yayi hakan ba ba tare daya nema izinin shigar ba. Duk da
kowanne office a qarqashinsa yake amma bai shiga office din kowa,hakanan baya taba
bada damar a bude maka office muddin baka nan,amma haka kawai yau din yaji yayi
hakan.

Sanda ya murda handle din yake shigowa da sallama cikin husky and deep
voice nashin nan,dai dai sannan itama ta bude qofar toilet din ta fito tana qoqarin
maida rolling na mayafinta.

Idanunsa kan mikail daya miqe a rude cike da tsananin mamakin ganin
boss din nasa yau da kanshi a office dinsa gabansa yana faduwa,yayin da nata idanun
suke kan fu'ad fuskar fu'ad din tana dubansa qasan ranta tana jin kamar tasan
wannan fuskar.

Baikai ga lura da ita ba ya miqa masa takardar

"Keep it......." Ya furta da wani irin yanayi idanunsa cikin tsakiyar qwayar idanun
mikail wanda hakan kadai ya isa ya gaya masa wani gargadi yake aika masa da kuma
muhimmancin da takardar ke dashi

"In sha Allah sir" Ya amsa yana karbarta da hannu biyu. Juyawa yayi da zummar
ficewa a office din,dai dai sannan idonsa ya sauka a kanta. Idanunasu suka gauraya
waje daya,sai tayi saurin zare dubanta daga kan fuskar tashi gabanta yayi wani irin
faduwar da batasan meye dalili ba.

Dan zuba mata ido yayi na sakanni tamkar zaiyi magana,sai kuma ya
fasa,ya juya ya kalli mikail sannan ya maida dubansa kanta sai kuma ya juya yana
ficewa a nutse daga office din.

Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke. Allah ya sanya ba zuwa yayi ya
samesu cikin wani yanayi ba da dukka sauran gaskiyarsa da yakeson tabbatarwa boos
din a yau babu ita.

Yasan an jima ana kai masa tsegumin halinsa,amma kasancewar shi din
ba mutum bane me daukan qananun maganganu ya sanya abun bai wani tasiri ba.

A yadda yake jinsa a dan rude sai yaji yana buqatar giya don daidaita
nutsuwarsa. Ya tafi zuwa fridge din yana fadin

"Boss......bashi da sauqi kwata kwata,idan har wani kuskure ya faru tsaf zaka rasa
aikinka,a wajensa wannan din ba wani abu bane me wahala".

Batace dashi komai ba kaman yadda bata kula da abinda ya dauko yakw
sha ba,ta qarasa wani sashe na dakin ta tayar da sallah kawai don lokacinta ya
shiga.

Tunda ta tayar da sallar har ta idar yaba zubawa cikinsa barasa.
Sanda ta sallame din saita kafeshi da idanu kawai. Ranta cike fal da mamakin yadda
dan adam da hannunsa zai dinga durawa cikinsa abinda yasan zai cutar dashi?.

Waiwayowa yayi sai suka hada ido. Ta hade fuska da kyau tana miqewa

"Banason wannan abar sam... Muddin kanason mu kasance tare kuwa saidai ka rabu da
ita" Tayi maganar duka tana jin wani iri har cikin ranta

"Am sorry dear.......indai wannna ne kada ki damu na ajiye".

Tana maida takalmin qafarta tana tunanin yadda zata samu ta duba
takardar da boos din nasa ya kawo masa yanzu?.

Ta kalleshi tana gyara zamanta bayan ta gama saka takalmin

"No water no drinks?" Murmushi ya sake mata

"Akwai mana.....gasucan a fridge sai kalan wanda kikeso" Kai ta girgiza
"Ba wani abu da zai fita a fridge dinnan na sha shi"

"Why?" Ya tambayeta yana zare ido

"Na tsani shaye shaye" Ta bashi amsa kai tsaye,amsar data sakashi sake zaro idanu

"Duk kyan nan naki babe?,kinsan yanzun macen bariki bata gama cika ba sai ta hada
da cakewa?". Ido ta dan rufe kadan tana budesu,kalmar MACEN BARIKI da yayi amfani
da ita a kanta tana mata quna sosai cikin rai

"Cikar wannan kyan naki babe ki dinga taba wani abun da zai sanya ki dinga jin
kanki very high......Ni zan dauki nauyin baki komai mai tsada wanda ba kowacce
yarinya ce ta isa ta samesu ba......sai irinku matan da kuke da gata a wajen
partner dinsu......like kaman wannan giyar.....bata bugar dani,saidai nayi bacci na
awa daya shikenan idan na farka zan jini fresh......please ki koya sha ko kadanne
akwai dadi,saikin gwada zaki gayamin" Yayi maganar yana qoqarin sake zuba wata a
cup da alama kuma ita yake da niyyar baiwa idan ya zuba din.

Tsam ta miqe tana jawo jakarta dake a gefanta tana ratayawa

"Ya haka kuma?" Ya tambaya yana dubanta

"Zan wuce gida" Da sauri ya diro daga saman kujerar da yake kai

"Haba babe.....me yayi zafi?,bayan baki cikan alqawari na ba......kinsan dakin nawa
na kama mana a Bristol kawai saboda yau?" Idanunta ta juya tana ajiye numfashi

"Banga alamun ka dauko wannan hanyar ba......kana yimin maganar abinda babu shi a
tsarina.......baka iya saukar baqo ba sam......na nema abun sha kana min sharhin da
lokacinka yake ci maka......idan lokacin dana diba ya cika zan tafi koda ba komai
daka samu"

"Ba za'ayi haka ba" Ya fada da hautsine jin zaiyi asaran abinda ya qwallafa rai a
kai,ya ajjiye komai na hannunsa ciki harda takardar da yanzu yanzu aka jaddada masa
muhimmancinta yayi hanyar fita daga office din.

Wannan shine ya bata cikakkiyar damar qarasawa,ta fidda wayarta tayi
snapping takardar ta turawa JIB kai tsaye ta share komai ta koma mazauninta tana
jiran dawowarsa.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 71

Kai tsaye ya wuce saman sofan dake ajiye bangare daban na office din yana
zame takalman qafarsa. Already sunyi sallan azahar bayan fitowarsu daga hall
din,don haka ya maida bayansa kadan ya jingina da sofa din.

So yake ya huta kadan kafin ya fita yaje yaga baqinsa,to amma tunani
ya hanashi hutawar,don maamah ce ta fado a ransa,sai ya fidda waya yana kiran
musaddiq idanunsa akan agogo yana qirga yawan awannin da suka rage da zasu maidasu
gida su duka. Ko kadan bazai bari musaddiq yaci gaba da mu'amala da gidan maamah
haka kai tsaye ba,ko mu'amala da dukkan wani abu daya shafi gidan game da abinci ko
abun sha ba. Don sam hankalinsa bai kwanta ba bazai kuma taba kwanciya ba,don ta
kashe dukkan wani abu da zai bashi nutsuwa tattare da ita.
Bugu daya ya daga,muryarshi ta fita cikin girmamawa.

"Qarfe nawa zaku bar company yau din?".

"Zamu dan jima yau,saboda akwai sabbin fertilizer da aka muka fitar,zamu gabatar
dashi ga manoma"

"Yayi kyau,idan kun kammala kafin ka fita a company din ka sanarmin"

"In sha Allah" Ya fada a girmame.

Katse wayar yayi yana sanya hannu zai jawo file din daya shigo dashi sai
kuma abun ya fado masa. Ya tsaya cak yana juya ganin da yayi mata. Daga toilet ta
fito,jikinta duk damshi da lema da yake nuna ta taba ruwa,to me yakai mace office
din mikail?.

Ya jima yana jin maganganu iri iri akan mikail din,to amma shi din ba
mutum bane ke daukan qananun maganganu shi yasa bai taba bi takai ba. Hakanan bai
fiya zafafa bincike da bin al'aurar mutum ba. Amma yau haka kawai yaji maganganun
da yakeji a kanshi din yana dawo masa.

Muqamin da Mikhail yake dashi a company din bashi da alaqa sam da hada
hadar jama'a karbar baqi ko mu'amala dasu ballantana yace harkar kasuwanci ne ya
kawota wajensa.

Qaramin tsaki yaja yana qoqarin watsar da maganar. Ta iya yiwuwa irin
watsatsun 'yammatan nan ne dake yawon bin maza office office dinsu don kawai son
abun duniya. Muddin ko haka ne shi bazai bari wannan ta faru cikin kamfaninsa ba.
Dukiya yake nema ta halal me cike da albarka,dole duk wanda yake qasansa ya kiyaye
dokar Allah lokacin mu'amalarsu,bayan kuma mutum ya fita daga kamfanin saura ya
rage nashi.

Zancen ya maqale a ransa duk da ya bude file yana dubawa,qananun
shekarun daya fuskanta tana dasu su sukafi tsaye masa a ido duk da ba qare mata
kallo yayi ba,yana tsoron kada ya zamana yaudarota yayi ya kawota office dinsa?.
Wayarsa ya zaro ya laluba number saddiq da ya baro a first floor yana ganin
ma'aikatan da suke da buqatar dauka kafin shi ya gansu yayi final interview dasu.

Ringing biyu ya daga,sai ya zauna sosai ya sake tambayarsa inda yake
duk da yasan a inda yake din

"Muna qasa.....na kusa kammalawa dasu"

"Alright......kasan me nakeso da kai?" Ya tambayeshi yana shafa baqar kwantacciyar
sumar dake gefan fuskarsa zuwa habarsa

"Aah hamma"

"Mikail......ina buqatar kowanne motsi nasa daga yanzu ya zama ana min monitoring
nasa"

"Done hamma" Saddiq din ya fada cikin qwarin gwiwa.

Sosai wannan aikin da hamman ya bashi yayi masa dadi,don ya jima yana
ganin abubuwan zargi masu yawa tattare da mika'il din,to amma baida cikakkiyar
hujja da zai gabatarwa da hamma,shi kuma hamma koda kana da hujja sanda zaka gaya
masa magana sai ya bincika ya tabbatar da gaskiyar maganarka.

Minti talatin ya sake duba agogonsa. Yana shirin miqewa saddiq din ya
shigo,ya gabatar masa da komai ya ajiye masa duka takaddun

"Well done" Fu'ad ya fadi bayan ya tabbatar da komai ya tafi daidai.

"Kira me sunan malam.....wanne time ya bawa mutanen nan?" Ya gayawa saddiq daya
kasance executive assistant dinsa wani lokaci ya juya ya zama P.A dinsa,har muqamin
me sunan malam dinma yana hawa wato scheduling coordinator ma gaba daya.

Hularsa ya dauka da agogonsa daya jiye a gefe,ya qarasa ya sanya
takalmansa daidai sanda executive Porter dinsa ya shigo

Shi ya dauki sauran kayan da yasan zai iya fita dasu din,yabi
bayansa,yayin da musaddiq ya tsaya don ya qarasa killace komai ya kashe sauran
electronics dake kunne,don yasan ba lallai su sake dawowa ta kamfanin sai kuma
gobe.

Yana fita suka hadu dame sunan malam din,sai yabi bayansa suna
takawa a nutse yana gaya masa sauran schedule dinsa na yau duka

"Amma sir.....sai nakega kaman abubuwan sunyi yawa.....ko akwai abinda zaa rage ko
a sauyashi a kaishi gobe?".

Kansa ya girgiza sanda saddiq ya matso yana scanning keycard jikin
designated elevator din da shi daya yake amfani dashi cikin company din.

"Kada ayi cancel komai.....zamu kammala in sha Allah komin dare.....make sure
kowanne ka sanar masa da exact time da zamu hadun"

"Yes sir" Me sunan malam ya fada yana bawa guards dinsa waje,daya daga cikinsu yayi
gaba don tabbatar da lafiyar elevator din duk da anyi keeping nata waje daya kuma
don saboda shi,muhammad jadda yabi bayansa sauran guards din suka shiga hadi da
saddiq.

Cikin ransa ya shirya sake maida kanshi busy fiye da kima,bama wai shi kadai
ba,hadda musaddiq don kaucema duk wani tsari da plan na maamah har sai yaga iya
inda gudun ruwanta zai kaisu. Ya shirya sadaukar da dukka lokacinsa ya tafi dashi a
aiki fiye da yadda yakeyi a baya,duk da ko a bayan shi din ba wani cikakken lokaci
gareshi ba. Sau tari anni tana yawan yi masa fadan yana tsaurarawa rayuwarsa da
yawa,ya kamata ya fiddawa kansa lokaci da zai dinga hutawa. Bashi da wani time
qwaqwara daya ware don yaje hutu,idan ka ganshi yana hutawa to tabbas umra yaje
wadda duka duka baya haura sati daya yake dawowa.

Suna yawan ware qarshen kowacce shekara suje dukansu suyi umra,daga nan
abban ya zaba musu qasashe guda biyu dake da wani tarihi cikin addini ko rayuwa
suje su qarashe qarshen shekararsu a can. Sau tari shi din baya tafiya tare
dasu,saidai ya biyosu daga baya,wanda ana kammala umra dinsa yake dawowa kan
kamfaninsa,bai fiya binsu tafiye tafiyensu da suka tsara ba.

Direct suka nufi private parking garage dinsa wanda aka tanada kawai saboda
ajiye motocin da yake kai kawo da kuma hidima dasu. Wajene da yasha banban da
sauran duka parking lot na company din,wanda aka qawatashi aka kuma cikashi da
tsaro na cctv da kai kawon security.

Dukka sauran guard nashi suna tsaye suna jiran qarasowarsa. Isowar nashi
yasa da sauri CSO dinsa ya qaraso ya bude motor din da zai tafi a cikin ta ya matsa
yana bashi guri,ya shiga saddiq yabi bayansa.

Sanda motocin ke motsawa suna barin wajen zuwa ainihin hanyar da zata
sadasu da gate na farko na kamfanin,daidai lokacin ya gyara zamanshi yana bude wani
guri a side na kujerar da yake kai don ciro earpiece da zaiyi using nasa wajen amsa
kiran daya shigo wayarsa.

Kaman fitar kibiya idanunshi suka fada parking lot na sauran staff da suke
da matsayi na biyu cikin kamfanin. Kan mikail idanunshi suka fada,ya bude mata
murfin motar yana jifanta da wani mayen murmushi,yayin da nata fuskar yake kadaran
kadaham tana sanya jikinta cikin motar

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 72


Zare Idanunshi yayi daga kansu yana jin wani quna a ransa.

"Tun yaushe mikail yake irin wannan abun?" Yayi maganar a hankali ba tare da yayi
tunanin saddiq zai jishi ba. Dan dubansa sadiq din yayi kafin ya rusunar da
idanunsa

"Hamma yana dan taba harkokinsa dama,amma kuma banajin a cikin company,yanayin
komai ne a wajen company"

"Idan har a wajen company yakeyi in zanyi wani abun bazai wuce tunasar dashi kawai
da gyara masa kuskurensa da take wuyan kowanne musulmi,ya kuma wajaba a kansa ya
zama dole a addini da wajen ubangiji yayi akan dan uwansa musulmi a sanda ya
fahimci kuskure ko gyara cikin al'amarinsa.....amma kuma muddin yana shigo min da
wasu abubuwa da basu dace ba muhallin neman halal dina.....lallai lallai zan dauki
mummunan mataki ne a kansa". Yayi maganar da sound din da zai nuna maka da gasken
gaske yake.

Tunda suka shiga motar take jifanta da wani irin narkakken kallo. Yanaji
jikinsa yana macewa kasala yana saukar masa kamar ko yaushe idan yasha barasa,shi
yasa yaso ta bashi hadin kai ko hannunshi yadan fara kaiwa jikinta guraren da suka
tsone masa idanu amma ta qiya. Yana kuma tsoron suna isa Bristol zaiyi wahala baiyi
baccin nan nasa ba na wajibi,wanda muddin baiyishi ba bazai iya hasala komai ba
yadda ya kamata.

Ta gaya masa tana da qa'ida da kuma dokokin da dole ya kiyayesu muddin
yanason rakiyarsu tayi tsaho. To sai yaga hanzarin ma na meye?,ya qyaleta mana?,don
dai jiran awa daya kacal me zai cishi?,shi da ta tabbatar masa a yau din wuni guda
tana tare dashi?.

"Babe......muddin a yau kika bani hadin kai yadda na jima ina mafarki.....zan baki
fara sheet da ba komai a ciki ki rubuta komai da yazo kanki kike burin
mallaka......idan nace komai ina nufin komai fa,komai tsadarsa ko yawansa.....ina
tare da lalitar jadda diamondchore" Ya fadi yana sakin qaramin shu'umin
murmushi,don ya hango irin barnar da ganimar da kwasa cikin account din.

Kadan tadan dubeshi sai ta dauke kai,tana maimaita sunan kamfanin da
tun shigarta ta tabbatar ba qaramin kamfani bane gama gari da kowa ya saba gani
ba......to amma sai taji ba abinda ya burgeta tattare dashi. Ta tabbatar tunda har
mamallakin kamfanin zai danqawa mutum irin mika'il ragamae tasarrufi da dukiyar
kamfanin duk kanwar ja ce,ba yadda za'ayi mikail din ya dinga irin wannan
fantamawar yana wasa da kudadensa ba tare da masaniya ko daurin gindinsa ba.

Ta yaya ma cikakken namiji kamar wannan daya mallaki dukiya ke dimbij
yawa,kadarori kala daban daban ciki harda private jet amma ya gagara aure?,bayan a
shika shikan aure bai rasa komai ba?.

Qaramin tsaki taja qasan ranta hoton fuskarsa yana dawo mata tana jin
kimarsa da haushinsa suna kwaranyewa daga idanunta,saboda haka batajin daga shi har
mika'il sun cancanci tausayawa.

Saidai ta sani,kudaden da suke da zummar kwasa din ba qananun kudade
bane.....kudade ne da ta tabbatar ita kanta sunfi qarfinta dama duk wanda yake tare
dasu,saidai kuma yawan masu buqatan kudi da muke dasu suke kuma kewaye da idanunta
sun isa su lashe komai cikin zama mawadata da zasuci gaba da gudanar da rayuwarsu
cikin salama,ta soma hango wasu daga cikinsu suna rayuwa irin rayuwar da takeson
ganinsu sunayi,wannan tunanin ya sanyaya sakin sassanyar ajiyar zuciya.

"Bakice komai ba" Mikail ya fadi yana dan waiwayowa ya dubeta kadan,don tsananin
rudewa da firgicewa cikin farinciki da dimuwa da yake ganin wasu matan a ciki idan
ya musu irin wannan albishir din sam sam baiga koda kamannin haka a wajenta ba

"Idan kuma hakan baiyi miki ba ki zabi kome kikeso a rayuwa......indai zaki bani
rayuwarki zan baki komai da kike da buri" Ya sake fada cikin qoqarinsa nason gamsar
da ita kalamansa.

"Baka da damuwa" Ta amsa masa cikin salon miskilancin nan nata,don maganganunsa sun
fara isarta,bata fiya son doguwar magana ba.

Juya kalmar ta bashi rayuwarta takeyi cikin ranta. Har yanzu ta kasa
sabawa da kalaman maza 'yan bariki,har yanzu mamakin wannan halittar ta d'a namiji
ta kasa sakinta,su koda yaushe kansu sukeso?,kansu suka sani?,ko yaushe yaya zasuyi
su samu jin dadinsu daga wajen 'ya mace?,ba tare da sun damu da yadda tata rayuwar
zata kasance ba?. Basu da wannan asarar,suna iya sanya qafa suyi fatali dake duk
sanda wannan halin nasu ya motsa na BUTULCI,aurenki sukeyi ko zaman bariki kuke?.

Tayi imanin halin D'A NAMIJI A JININSA YAKE,dan kunama ne shi da
gaske,tana kyautata zaton babu wani d'a namiji da bashi da wannan halayyar,saidai
na wani ne ya d'ara na wani kamar yadda take gani take kuma kan gani din. Wannan
hasashe da karatun da tayi musu shike nesanta zuciyarta kullum daduniyarsu,takejin
ba abinda yafi dadi a wajen mace irin ta rayu ita kadai ba tare data raba kowanne
namiji cikin rayuwarta ba bare ta bashi wani matsayi da zai zameta lalura qunci ko
quna nan gaba cikin rayuwa.......gwara ta rayu ita daya shine zata zama me cikakken
'yancin da bata dame bata mata rai.

Nisa da zurfin da tayi a tunani ya sanya har suka iso Bristol bata
sani ba. Yayi parking na motar ya fito yana takawa da qyar saboda yadda jikinsa
yake qara nauyaya,ya zagaya side din da take zaune ya bude mata qofar sai ya miqa
mata hannu alamun ta taho.

Hannun nasa ta kalla sannan ta kalli

Please Login or Register in order to submit comment