You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauran lokacin batawa tayi sa'insa da yaranshi,don haka
ta juya a mugun fusace zuwa cikin gidan. Tana tafe da dan sassarfa tana neman
number kawu Rufai,abinda ta manta rabonta dayi kenan,saidai shi ya kirata idan
neman abun duniyarsa ya motso,shima din ba kasafai ba,don yafi ganewa yayo tattaki
suyi ido da ido.

Wata muguwar guda taji an sake mata data ratsa har tsakiyar kanta
sanda take taka tsakar gidan nasu,ta runtse ido gudar bibo tana sake birkita mata
kwanya,tana so taji da matar nan,amma kuma wani sashe na zuciyarta yana gaya mata
tukunna dai ba yanzu ba,wannan qurar data taso miki a yanxu ita tafi cancan ta a
kasheta.

"Yar arziqi irin albarka......kiranki alheri ne.....yanzu haka ina cikin layin naku
ai,gidan zanzo akwai bayanin da zan miki"

"Basai kazo ba kawu... .Amma inaso ka kira wancan mutumin da kake iqirarin ka bashi
aurena......ka shaida masa yayi gaggawar janye wadancan gumakan daya dasa mana a
qofar gida da zummar hanani fita sabgogina"

"Kajimin shashasha.....macen da aketa tattali amma ta kasa gane hakan......banda
abun ki wacce macace kaf unguwar bama gidan ba ta samu darajar samun masu tsaron
lafiyarta idan bake ba?,ke wannan kawai bai isheki alfahari ba?"

"Kawu!" Yau din ta kirashi da dan tsauri a muryarta saboda yadda ranta yakai maqura
a baci

"Fadi abinda kikeso ki fada......gani nan ma na shigo gidan" Ya qarasa fada yana
datse kiran.

Da kallo bibo data maida yanzu zaman tsakar gida sana'arta qarfi da
yaji ta bishi dashi

"Allah ka rabamu da mutuwar zuciyar da 'ya'yan cikinmu zasu dinga juya mu" Ta fada
qasa qasa,yaji tana magana amma bai fahimci me take cewa ba,don shi a yanzu
hankalinsa nakan lamarin sabreen da me jadda,bazai samu cikakken bacci ba sai ranar
daya tabbatar an miqa musu ita.

A tsaye take don ta kasa zama,ba abinda zuciyarta ke maimaita
mata sai kalmar

"Wai waye wannan muhammad jaddan?,me ya dauki kansa?,wa yafi?,wa ya damu dashi?".

Koda kawu ya shigo kallo daya yayi mata ya tabbatar lallai abubuwa
sun fara cabewa. A yadda yayi mata farin sani fuskarta kawai ta gaya masa lallai ta
fara cika,kuma dab take da fashewa,fashewar kuma da yayi imanin ba zata taba zame
masa alkhairi ba musamman shi,bata da tsoro,tana iya yin komai idan har ta tsara
zatayin,gwara tun wuri yayiwa tufkar hanci......ya gayyato masu tayashi yaqinnan
don ya samu ya tsira da mutincinsa da sauran 'yan canjinsa.
"Ka kirashi ka gaya masa......idan ba haka ba zan gaya masa ta hanyar da bazata
yiwa kowa dadi ba kawu!" Ta sake maimaita maganar da sautin da zai tabbatar maka
kai tsaye daga zuciyarta maganar ke fita.

"Oh.....Allah na gode maka" Abinda kawai ya iya fada kenan. Tako ina yana jin gumi
yana tsatsafo masa,tsakanin me jadda da sabreen baima san wanda yafi wani sakashi a
masifa ba.

Hannun kujera ya samu ya zauna yana share fuskarsa da hannun babbar
rigarsa,yana jin gaba daya duniya ta juya masa baya cikin qanqanin lokaci. Number
da a kullum kiranta yake yawan sakar masa da fargaba da kuma faduwar gaba ya
kira,duk da ya fuskanci cewa mamallakin number mutum ne me tsananin sauqin kai da
kuma fahimta qwarai,hakanan kiran number wayarsa yafi masa sauqi akan kiran wancan
mutumin da yake jinsa tamkar wani mala'ikan daukan rai a wajensa.

Daidai lokacin da yake tsaye cikin malam aminu kano international
airport,zagaye da guard nasa,gefe daya kuma farouq ne da yayo masa rakiya.

Kusa da kusa suke tsaye sosai shi da farouq din,da alama akwai magana
me muhimmanci da sukeyi shi dashi din. Hannunsa ya zura kawai cikin aljihun kaftan
dinsa ya zaro wayar,ya maida dubansa ga fuskar fuad dake qoqarin sanya wayarsa a
silent,don ba kasafai ya fiya son kiran waya ba

"Surukinka ne yake kira" Yayi maganar qasa qasa ta sigar zolaya da muryar da iya su
kadai zasu iya jin maganar. Kadan yadan daga fararen idanunsa ya jefa masa
harara,sannan ya maidasu kan wayar yana ci gaba da abinda yakeyi din ba tare daya
ce dashi komai ba.

Idanunta suna lumshe,amma kuma yadda kawun yake wayar cikin matuqar
girmamawa kai kace sune sama dashi sai bacin rai ya sake zuwa mata wuya......ba
wannan bane a gabanta,abu mafi muhimmanci shine ya sanya wannan qattin su janye
daga qofar gidansu,don haka ta saka kunne sosai tana sauraron muryar farouq dake
fita tar tar ta speaker din wayar kawu,wanda ya sakata ne a speaker don ta samu
tabbaci kan duka hukuncin da ya yanke a kanta.

Haka kawai cikin ranta takejin bashi bane yake magana,daga yadda
farouq din ke magana adan sake ya sake baya yaqinin haka.

"Yallabai din yana kusa?,akwai saqo da aka bani zan isar masa....."

"Yana jinka uncle......bari na saka a speaker......though dai zaiyi kusan two weeks
idan ya wuce.....zai dawo one week before the wedding". Kansa fuad ya sake dagawa
ya watsawa farouq wata harara,don me zai zauna yana bayani musu akan abinda shi
kadai ta shafa

"To ma sha Allah......ma sha Allah.......dama sabrina ce ke neman izinin rage masu
tsaronta......sannan kuma a yau din tana buqatar ya bata izinin fita.....".

"Ban yarda taje ko ina ba....koda kuwa qofan gida ne". Wannan dakakkiyar muryar
tasa dake cike da ginshira ta ratsa wayar ta kuma samu kyakkyawan damar isar da
saqo ga kunnuwanta.

Kaman ya yarfa mata ruwan zafi haka taji. Tsam ta samu kanta da
miqewa,ta zauna sosai tana zubawa kawu rufai idanu wanda zuwa sannan har ya fara
haramar rufe maganar hanyar fadin

"To in sha Allah.....in sha Allahu ba damuwa......". Bai ankara ba,baisan kuma ta
yaya ba sai tsintar wayar yayi a hannunta,kai tsaye ta zare wayar daga hannun kawun
ta maidata kunnenta cikin wata fusatacciyar murya

"Ina fatan kana kan waya!" Sautin da yaja hankalin farouq da wayar ke hannunsa,da
kuma shi kansa fuad daya soma takawa zai wuce ciki don ya isar da saqon da yakeson
isarwa din.

Taku uku farouq ya cimmasa,sai ya zura masa wayar kawai a aljihun gaban
rigarsa yadan matsa gefe yana karantar yanayin fuad din

"Ban nema izini ba......hakanan bance a nema min izinin komai daga wajenka
ba......umarni ne kawai kan ka janye wadancan halittun da babu sanin kimar dan adam
ko daya a tattare dasu......kafin su tafi kuma ka tabbatar sun karbi komai naka
daka bada da sunan dukiyar aure"

"Au haba?" Ya fada da wani irin calmness zuciyarsa da kwanyarsa na qidddige wasi
cikin halayenta.

"Ashe bayan qwamushe girman kai harda rashin kunya kika hado?.......abun yayimin
daidai......i salute you ma'am........zaki ci gaba da zama cikin gida har na tsahon
sati biy cur ba tare da kin taka koda qofar gida ba.......wannan shine punishment
mafi sauqi a gareki".

"But....who are you?" Ta tambayeshi a zafafe tana jin zallar rainin wayo cikin
maganganunsa.

"Relax mana.......so soon haka?,saurin me kikeyi nason jin waye muhammad
fuad?,bayan sanin nasa suine babban barazana a rayuwarki?". Yakai qarshe yana ajiye
numfashi,bai kuma barta ta sake cewa komai ba yace

"Kina zaton zan barki ba masu tsaremin ke.....don nasan kadan daga aikinki ki
fecemin da dukiyar aure na.......wannan wasan zaiyi dadi sosai.......but......kisan
dawa zaki bugashi......idiot!". Qit ya katse wayar,ya kuma zarota a gaggauce daga
aljihun nasa. Abu daya zai sanya ya buga wayar a qasa,ta fito daga wajen mutum me
matuqar girma da mutunci a rayuwarsa.

"Don't ever never try it.......kasan bana shiri ko jituwa da mara
kunya......wayarka taci saa data kasance taka ce,da daga yau ba zata sake amsa
sunan waya ba" Sai ya sake masa wayar shi kuma ya cafe,yayin da ya qara gaba yana
wucewa cikin kaman yadda yayi niyya.

Yadda ya qara zafin nama cikin tafiyarsa kadai zai gaya maka zuciyar
'yan maza ta motsu sosai,ya bishi da kallo sosai. Yadda yayi doguwar magana haka
yau cikin fada,ya tabbatar koda ya bishin bazaice komai dashi ba.

Kasa bawa kawu wayar tayi har sai daya sake kwatsa mata tsawa

"Bani wayata nace!" Saita miqa masa wayar wanda miqawar ya hadu da silalowar
siraran hawaye daga fuskarta. Da gudu gudu ta qarasa shigewa dakin,tana jiyo
sababin kawun da yaketa yarfa ruwan masifa kamar xai ari baki

"Kinsan wayeshi?,kin kuma san matsayinsa da har kika gaggaya masa magana
haka?,kinsan idan ran mutumin nan ya baci ya kama duka danginki ya kulle basu da
saidan me fiddasu?".

Maganganun kawu ba sune suke dawo mata akai ba,yadda ya dinga yaba mata
magana kalma bayan kalma kuma murya a kwance.....hankalinsa ma a nutse shine yafi
mata matsanancin ciwo.

Wunin ranar haka ta dinga juyi cike da baqinciki da takaici,tanaso tayi
kuka amma tana hana kanta,tana ganin tafi qarfin tayi masa kuka(ni kuwa nace anya
sabreen?,ba girin girn ba tayi mai).

Tana daga kwancen tana irgen yadda awanni suka shuda suka kuma zama
silar tafiyar ayshatu india ba tare data yiwa yarinyar kallon qarshe kamar yadda
taso ba. Da wannan juyin ta qarar da wuninta kaf da tunaninta na yadda zata samu
zullewa tsakanin qattan garadan nan ta fice a gidan,ta kuma nisanci kowa ta yadda
zai kasance kafin zuwan sati biyun da ya ambata saidai ya dawo ya tarar ta zama
tarihi a garesu gaba daya.

********"kai jama'a,qalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un,mudai mun hadu da
masifa,wannan bala'in har ina?,kai da gidan mijinka amma duk shiga ko fita wani
qato yana tsaye,shi xai bude maka qofa shi xai rufe maka?". Muryar bibo kenan dake
sakin buhun data dawo dashi daga kasuwar saitin dakinsu sabreen din,don tana so
dukka maganganun da zata fada ya samu wajen zama na din din din a kunnenta.

A kwanakin sam bata da aiki sai fadin baqaqen maganganu da kuma tarin
habaice habaice,tana neman duk wata hanya ne da sabreen zata kulata ta lanqaya mata
sharrin da har masu gadin nata zasuji su kuma isar dashi ga uban gidan
nasu,wataqila hakan ya zama silar fasa auren. Sosai auren ya tsaye mata a rai,ta
laluba ta kuma bincika inda zata sake ganin matan nan don ta sake jaddada musu 'YAR
BARIKI fa dansu zai aura.....amma bata samu ma wanda ya gansu ba ranar da sukazo
unguwar ballantana ya tayata neman su. Ita din a yanzu tsoron taba sabreen din
takeyi,duba da iya mutanen da suke gadin gidansu ma gaba daya ba ita sabreen din
ba,wannan dalilinne kawai yake taka nata birki akan abubuwan data qulla aiwatar
mata. Abu daya take jira shine ranar da zaa ce zaa kawo lefe,tana sanya ran ranar
ta zame mata ranar nasara tunda ba wani daya danganci sabreen,a ranar sai tayi mata
tonon silili cikin jamaar kawo lefen,ta tabbatar za'a tafi da ita a baki,kuma dole
saqo zaikai kunnen wadanda suke da iko da hana abun ko aiwatar dashi.....randa
zasuzo karbar kayan aurensu kuwa tasan dukka yadda zatayi.....koda tsiya koda
bala'i ta juya abun ya koma kan hadiyyarta.105


A wannan lokacin sabreen din na kwance saman doguwar kujerar falon nasu,a
kwance take rigingine tana kallon ceiling,saidai kuma manyan idanunta dukkabiyun a
rufe suke kai kace bacci takeyi.

Banda yar qaramar fankar dake bada iska me dadi a falon ba zakace
akwai wutar nepa ko sola cikin dakin ba. Ta kashe tv ta kashe dukkan wani qwai da
zai iya bada haske.

Kwanakinta shida kenan tana irin wannan kwanciyar,musamman lokaci irin
wannan da yara suka wuce makaranta. Zuwa yanzu kwanyarta da tunaninta dukka sun
gajiya kan yadda zata sanya wadannan qattan subar qofar gidan,abinda zai bata damar
sakewa kenan ta qarasa aiwatar da plan dinta. Ta lura daidai da second basa gusawa
daga qofar gidan bare ta samu wata qaramar dama ma da zata gifta. Dukkan wani
tunani nata ya soma gajiyawa,hakanan ta fara gajiya,bataga wani alamu na samun
cikar nasararta na nesantasu da wannan gidan ba.

Kulli yaumin Allah shine da kullum sai kawu ya shigo dakin ya sameta a
haka,qarfi da yaji ya zama me wa'azi yayin da ita kuma ta zama kurmar dole. Ta sake
qaranta magana da wawalwalarta,ta sake zama miskila sosai,sai yayi maganarsa ya
qare ya tashi kan wa'azin biyayyar na gaba da muhimmancim aure bata ma bude idonta
ba bare tace dashi ta tafasa a sauke ba.

Wannan abun da take masa yana sake razanashi,yasanta cikin miskilai ma
nata halin na daban ne,wannan ya sanya ya dauki matakin da bata taba zato ko kawo
cewa zai dauka din ba......don a daidai sannan kunnuwanta suka jiyo mata sallama da
wata murya da take kyautata zaton ta santa......ta mata kyakkyawan sani ba in
general.

Daga sallamarta ta farko har zuwa ta biyu dukansu suna ji,amma tsananin
mamaki ya saka suka kasa amsawa har sai data sake bayyana sosai a gabansu.

Bahijja........matar da a yanzu haka suka shafe shekara goma sha daya
basu sanyata a idanaunsu ba.....haihuwar haneefa......haneefa daa yanzu girma da
shekaru suke bayyana kansu a tattare da ita.

Kasa kowanne motsi tayi,saboda tana jin komai ne a mazaunin mafarki,sai
kawai idanuwanta data bude ta zubawa qofa idanu tana sauraren isowarta don taga da
gasken itace?.

Daga cikin al'ummar gidan da suka shaidata suma kallon mamaki suke
binta dashi. Fuskar da ta bace musu tun wani zamani baya. Da idanu take qarewa
gidan kallo kawai tare da al'ummar gidan da ba wanda ya iya fusgar sunanta sai
daada.

"Ikon Allah.......kina nan bahijja?". Murmushi ta saki

"Ina nan daada...." Ta amsa mata dashi tana ji a jikinta lallai akwai tarin
qalubale masu yawa.

Kasa daidaita nutsuwarta tayi lokacin da take sallama zuwa cikin falon
nasu. Ta sauko gaba daya daga saman kujerar cikin wani irin hanzari tana dosarta. A
murya tana jin tamkar ummenta ce ta dawo,haka nan wani sashe na kamanni,duk jikinta
rawa yakeyi,hawaye kuma suka balle mata,irin hawayen nan da suke zama tilas zubarsu
a idanu. Cak komai nata ya tsaya sanda ta fada jikinta tana sakin kuka lokacin da
muryar uncle abdulk'adir. Muryar data sake sanya kowanne sashe na jikinta rawa,ta
zare jikinta daga na bahijja ta daga kanta kaman me ciwon wuya tana ware fararen
idanunta da suka sauya kala akan uncle abdulk'adir din dake takowa zuwa cikin
dakin.

Yana nan dai kaman yadda suka sanshi,giant dashi me yawan daurewar
fuska. A wancan lokutan basu da shekaru sosai,wannan ya sanya basu fiya fahimtar
rashin sakin fuskar nasa ba saboda yana da fara'a ga yara. Sai ta riqe bahijja
sosai wadda suke kira da didi,itama ta kama nata hannun tana shirin zaunar da ita.

◦•●◉✿ "Oh.....Allah na gode maka" Abinda kawai ya iya fada kenan. Tako ina yana jin
gumi yana tsatsafo masa,tsakanin me jadda da sabreen baima san wanda yafi wani
sakashi a masifa ba.

Hannun kujera ya samu ya zauna yana share fuskarsa da hannun babbar
rigarsa,yana jin gaba daya duniya ta juya masa baya cikin qanqanin lokaci

✿◉●•◦𝘽𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙖𝙬𝙖 𝙪𝙠𝙪 ✿◉●•◦


Dukkanin wani kuka a yanzu a kuma wannan lokacin ta yishi,kukan faduwa da
rashin nasararta da kuma rashin hango galaba qarara daga kaucewa wannan birkitaccen
auren da yafi kama da auren bauta.

"Ba abinda zaki mana.....ba abinda zakiwa kanki ki kyautatawa kanki da rayuwarki
sai aure......a wannan shekarun zaman me kike tunani zakiyi?,har kice bakison
aure?,idan bakison aure me kikeso sabreen?.....kisa a ranki idan har bakiga afkuwar
auren nan ba to daya ne a cikin ku biyu ya mutu.....ko ke ko shi".

"Ya Allah......kasa ya mutu.......ya Allah ka sanya wannan tafiyar da yayi ya yita
kenan" Ta samu kanta da furtawa a zahiri. Adduar data baiwa kowa mamaki a wajen
banda kawu rufai dake zaune daga gefe. Gigitacciyar tsawar da uncle abdulk'adir ya
sake mata ya sanyata runtse idonta kawai ba tare data motsa ba tana sauraren bugun
zuciyarta,ko qas zuciyarta bata rusuna ko ta canza ba game da adduar data
masa,saita dinga ninks wata can qasan zuciyarta tana maimaitawa akan Allah ya kawo
duk wata sila ko hanyar da zaiyi nisa da rayuwarta ya barta ta huta kamar kowacce
'yantacciyar d'iya.

"Wai ina amanar da nake yawan tambayarka akai rufai game da yaran nan?,ya akayi ka
bari sabreen ta zama haka?". Wani lafiyayyen gumi ne ya yanko masa,baisan iya
adadin qaryar sunan nan lafiya qalau da ya yiwa abdulk'adir ba......baisan iya
adadin saqon da ya aikowa yaran ya handame ba ba tare da yabar kowa yasan ma anyi
aiken ba.

Idanunta kawai taja ta rufe lokacin da didi keson jin ko tana da
wata matsala ko kuma damuwa ne game da auren bayan kasancewar ita ce batason
mijin?.

"To ta cewa didi me?,ta gayawa didi mamarsa tana da manufar aurawa danta shi?,while
shi kansa batasan me yasa ya nemi aurenta ba da kanshi?. Tana jin bata da sauran
option a yanxu illa ta tsaya ta zuba idanu kawai a buga wannan wasan da
ita.......waye zai zama WINNER?.....WAYE KUMA LOSER a tsakanin mutum ukun?.

𝐒𝐚𝐛𝐫𝐞𝐞𝐧
𝐌𝐮𝐡𝐚𝐦𝐦𝐚𝐝 𝐟𝐮𝐚𝐝
𝐌𝐚𝐚𝐦𝐚𝐡 𝙜𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖
𝐇𝐚𝐣𝐣𝐚 𝐡𝐚𝐫𝐢𝐫𝐚

Daga gefe da nata shirin da KO MEYE SHI?.


Abu daya ne zata ce ya sanya wani dan siririn haske da sanyi cikin
mummunan yanayin da take jin kanta a ciki.....shine samun wani haske a dakin da ya
zama tamkar makwafin uwa a garesu. Yadda haneefa huda da nadra suka sanya didi a
gaba tamkar ummensu ce ta dawo. Ita kuma tana tsakiyarsu,hira sukeyi tamkar xasu
kwana a zaune ita dasu,su din kamar zasu koma cikinta,yayin data rungumesu da kyau
itama kasancewar Allah bai bata haihuwa ba.....dangin mahaifinsu ko a wancan
lokacin na rasuwar yayarta musamman kawu rufai su sukayi tsayin daka suka hanata
koda haneefa da take qarama a sannan,sai haqura tayi badon zuciya bata so ba.

Kwana da wunin da sukayi da sabreen ba wani abu daya canza daga
yanayinta. Ta riga tayi giving up tun bayan da kawu abdulk'adir ya wuce yabar didi
bahijja da zummar zata zauna dasu a nan har sai lokacin biki yazo za'a share biki
da ita sannan ta koma.....komai ya qare kenan!,abinda ya rage mata daya ne
shine......ta maida kanta kan tsara yadda zata maidawa kowa aniyarsa......amma har
yanxun tana jin abun kamar ba gaske bane.....tana jin kamar a mafarki ne.....yaya
akayi wadannan mutanen suka mamayeta har haka?,suke shirin juya rayuwarta dare daya
daga wani bigiren zuwa wani......bigiren da bata taba tunanin zata tsinci kanta a
ciki ba har abada.

✿◉●•◦𝙎𝙖𝙣𝙣𝙪 𝙨𝙖𝙣𝙣𝙪 𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙣𝙖 𝙯𝙪𝙬𝙖......✿◉●•◦


Isowar akwatinan auren muhammad jadda zuwa gidansu sabreen ahmad kadai
ya sake gigitar da tarin jama'a na cikin gida dana waje. Wasu irin qasaitattu kuma
lafiyayyun luxury akwati kala daban daban da suka tasamma jimillar akwatuna talatin
da shida wato dozen hudu dalla dalla inji munafukai da 'yan gaza gani akwatina d'ai
d'ai har arba'in da takwas kenan.

Iya kwati set qwaya daya tal kawai idan aka fiddata aka saidata banda
kayan cikinta sun isa musulmin jarin cikakke ga mutum a qalla goma sha kyan kyan.
Wasu sabbin designers akwatuna da sabreen din ta zama mutum na farko cikin jerin
ahalin iyalan masu arziqi data mallakeshi.

Fadin irin tarin dukiya da suturun alfarma dake ciki ma bata baki ne.
Lefe ne da aka zubawa kayan ado na gold da diamond a ciki kamar yadda yake shine
ainihin sana'ar muhammad jadda,wanda duk wanda ya gani sai ya tabbatar lallai sun
cika kayan aure daga wajen mamallakin kamfanin diamond da gold.

"Anya bayan wannan sana'ar kuwa baya yankan kai?,suna kyautar mota kaman suna
kyautar sweet.....bayan motar da aka hado mata da ita a kayan aure yanzun guda biyu
suka sake sakawa akai kayan lefen fa,wai kyautar uban ango da uwar ango.....nabeela
wannan wacce irin baqar rana ce?" Hadiyya da labarin lefen ya hanata zaune ya kuma
hanata tsaye cikin dakin hostel din nasu ta fada da idanunta da sukayi jajur don
kuka.

Wadda ke zaune a gefensu ta saki murmushi

"Kina wasa da bariki.....ai indai kin cika macen bariki me wayo to tabbas kafin ta
bare dake kike kama kanki.....ki samu wani alaj din kiyi wuf dashi ki shige daga
ciki abinki....."

"Muffy.......motocin millions of naira fa kaman ana bada biscuit?" Hadiyya ta sake
maimaitawa. Tsaki wadda suka kira da muppy din ta saki tana jawo kwalbarta

"Har yanxu na yarda da sauranki baki waye ba.......wai shin kinsan waye muhammad
jadda kuwa indai da gasken shi zata aura?.....to bari kuji.....ni ina samun
labarinsa ta bakin mata da 'yammatan dake cudanya cikin manya manyan Billoniers din
da muke dasu.....kusan burin kowacce mace a cikinsu ta samu kutsawa koda gefen inda
yake......amma inaa....saidai hange daga nesa,baya shan koda taba ballantana akai
ga giya......bai daga idanu ya kalli d'iya mace ballantana har ta burgeshi akai ga
batun nemanta.......abu me tsananin daure hankali da tunani kenan. Koda kyau ne da
namiji a yanzun irin na jadda zai wahala kaga baya neme nemen mata ko shaye
shaye.....ballanta shi ya hada duka,ga kyau ga masu gidan rana baja baja tamkar
ganyen bishiya.......bai shaye shaye ba neman mata,ya rufe wadannan hanyoyin guda
biyu wadanda sune suke saurin sawa a cimma d'a namiji.......budaddun qofofi masu
saurin isar da sharri rayuwar d'a namiji" Tayi zancan da confidence dinta ganin
yadda dukkansu suka bata hankalinsu. Ita kanta tana jin dadin106

Ita kanta tana jin dadin bayar da labarin qwarai.....don har a qasan
zuciyarta tana jin muhammad din winner ne na gaske daya tsallake tarakunan da
matasan masu kudi da yawansu basu iya tsallakewa,idanma basa yin duka to zaka samu
sunayin daya daga ciki tabbas!.

"To.....ko muna da rabon samun irin wannan mazan ko sai a aljanna?" Maganar daya
daga cikinsu kenan data bawa kowa dariya duk da suns taya 'yar uwarsu ne jimami. Su
kansu a karan kansu sun sani.....samun irin muhammad din sai mace me tsananin
sa'a,kowacce cikin zuciyarta kuma ba tare data bayyanawa hadiyya ba ji takeyi dama
itace sabreen din,duk da cewa hadiyyan ta gaya musu cikakkiyar KARUWA CE.

Duk yadda bibo ke fama da habaici a ranar kasa komai tayi. Wani irin
baqinciki ke nuqurqusarta kaman ta hadiyi zaciya. Inda tasan lalacewar sabreen ba
wani abu bane da zai zame mata illa ba ya hanata auruwa da tuntuni ta dade da sanya
hannu a lamuranta ta kadata tayi nesa dasu bare yau taga wannan abun takaici. Lefe
ya kasa dauke qasan?,sai babban falon marigayi mahaifinsu na sama aka kaishi aka
zube a can?. Didi ta sanya muqulli ta rufe don sunyi yawan da za'a ce wai anzo
kallo an zauna an bisu daya da daya an kalla kamar yadda aka saba ganin lefe. Wanda
gulma ta qarewa kuwa saidai ya leqa ta windo ya kalla,iya Kalllon bayan akwatin
kawai ba tare da ankai ga budesu ba wani abu ne me qayatarwa a idanun me kallo.
Tana kwance kamar kullum har akayi didifniyar ajiye lefen dama komai da
komai,idanu take budewa kawai lokaci bayan lokaci ta kalli su huda.

Ba wata damuwa sam sam a tattare dasu,sai take hangowa ma kamar
farinciki suke ciki. Sun samu didi da yanzu duk inda ta motsa suna wajen ta zame
musu uwa na wucin gadi. Tausayinsu takeji qwarai,a ina zata barsu randa aka maqala
mata wannan maqalallen auren?. A yanxu kam akwai walwala me yawa tare dasu saboda
qishirwar UWA da suke kasheta tare da didi din.

"Anata hidima anata hidima......amma mu har yanxu bamuga qyallin ango ba,bamuga
yazo gaisuwa ko ganin amaryarsa ba bare akai ga batun gaidamu iyaye" Irin lafazin
da ya fita daga bakin me biwa bibo kenan bayan ta yaye labulen dakin suna

Please Login or Register in order to submit comment