You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qishirwarta. A kanta yakejin komai kuma ita kadai zata
iya sama masa da wannan nutsuwar.

Saidai kuma ya karanci hakan wani abu ne da bazai taba samunsa
ba.....don haka gwara yayi daukan fansan da zata gwammace bashi rayuwarta yayi
yadda yaga dama da ita.

"Don Allah me kyau kice wani abu mana" Ya fada yana marairaice mata

"Nayi kewarka mana....." Ta samu kanta da furtawa. Yadda ya fidda idanu yana gwada
mata mamakinsa ya sanyata jin kunya gami da mamakin kanta. Wani abu ne da yake
faruwa da ita karo na farko a rayuwarta da bata taba tunanin zuwansa a nan kusa ba

"Da gaske kike?" Ya fadi har yanzu idanunsa a waje,sai tasa hannunta kawai ta
lullube fuskarta dasu tana sakin qaramin murmushi,abinda ya sake fidda kamanninta
sosai da sabreen.

"Don Allah yau daya ki bani aron mintunanki biyar" Ya fadi yana hade hannayensa
waje guda. Mintunan biyar din da yake sanya ran a cikinsu zai qarasa dashen da ya
dauko.

"Don Allah karkice aah,bazan sake neman wata alfarma ba daga wajenki ba daga
wannan" Ya sake maganar yana qara marairaicewa da kyau.

Rabuwa biyu zuciyarta tayi,wani sashe na zuciyar tata yana cewa ta
bashi damar.......yayin da wani sashen kuma yake cike da tsoro,tsoron da kusan
kullum a cikinsa take.

Batasan yadda akayi ya shammaci rayuwarta har ta soma sabo dashi
take kuma jin wasu baqin abubuwa a kansa ba,irin abinda bata taba jinsa akan kowa
ba,koda kuwa cikin duniyar mafarkinta ko kuma hasashe.

Cikin qasa da mintuna biyar din daya dauka ya qarasa wargaza duk wani
tunani nata. Sanda take takawa zuwa gida dauke da kalamansa masu nauyi.......ji ta
dinga yi duniyar tamkar ita daya ce mace a ciki......dama haka zukatan dake da masu
furta musu kalamai masu dadi sukeji?. Yau daya ta gasgata kalaman daya taba furta
mata

"Har yanxu ke yarinya ce.....ba zakisan dadin rayuwa ba sai kinso kin kuma bada
dama an soki......kowacce rai tana da buqatar wanda zai sota.....a lokacinne zaki
karanci martaba da darajarki da kuma zamowarki cikakkiyar mace duk da qarancin
shekarunki.

Hannunta takai tana shafa qaramar wayar daya bata wadda ke dauke da
layi da kuma number dinsa. Ita kanta batasan adadin yawan roqon da yayi mata ba
kafin ya karya zuciyarta ta aminta da karbar wayar ba

"Zanyi tafiya me nisan xango,a qalla zanyi watanni biyu ban saki a idanuna
ba......bazan iya jurar rashin ganinki ba......" Kai take girgizawa a tsorace

"Yaa sabreen......"

"Ita kike tsoro?,zanje na nema dama a wajenta,kada ta rabani da abinda raina
yakeso,zan roqeta ta barni na dinga jin muryarki....."

"Baka da hank......" Taji bakinta ya subuce da fadi.....sai kuma ta yiwa kanta
waigi daga furta abinda tayi niyyar fada din a mugun tsorace. Yaa sabreen din da
kullum kwanan duniya cikin kwatanta mata ta kaucewa sauraren kowanne d'a namiji har
sai ta isa minzali?,yaa sabreen din da bata lamuncewa kowa mu'amala dasu ba komai
kusancin dake tsakaninsu?,shine a yanzun yake neman kai kansa da kansa gabanta?.

"Huda......zan iya komai a kanki.....zan kuma iya komai saboda ke,ni kadai nasan
zafin sonki da nakeji a raina.....don Allah ki karbi wayar nan......muryarki kawai
xanji,daga gaisuwa idan kinso ki kashe wayar" . Ido ta zuba masa a mamakance
jikinta kuma yana yin sanyi,wai dama haka soyayyar take?. Qwallar data gani
shimfide a idanunsa suka karya duk wani qwarin gwiwa nata,kafiya da kuma dagiya,ta
karbi wayar ba tare da tana da masaniyar ta karbi shiryayyen abu da zai wargaza
musu rayuwa ba dukkaninsu......

Sake dafa wayar tayi sosai,qasan ranta tana jin qarin tausayinsa yadda
yake faman marairaice mata,da alama soyayya ba qaramin kamu tayi masa ba. Dama
wannan itace soyayyar?,dama haka akeji?,dama haka take iya canza mutum daga ainihin
yadda ka sanshi?.

Ita kanta mamakin kanta takeyi yadda ya iya canzata gaba daya cikin
qanqanin lokaci haka,amma kuma hakan fa yana nufin nan da shekara daya ko biyu
kenan aure zatayi?. Tayi aure kuma yana nufin tabar yaa sabreen?,tabar nadra tabar
haneefa?.

To wai ta yaya ma zata fuskanci yaa sabreen din da shi?,tace mata
me?,bayan tsahon tasowarta idanunta basu taba gwada mata yaa sabreen din tana
soyayya ba da kowa ma ballantana aure?,kullum zancanta yadda zasuyi zuzzurfan
karatu kuma su zama wasu a gaba......wannan qudurin zai cika kuwa?.

Eh.... Wata zuciyar ta bata amsa daga wani gefan

"Shi karatu ai baya hana aure......kaman yadda aure baya hana karatu" Ta tuna da
wata hira data jiyo 'yammatan ajinsu sunayi,abinda ya sanyata sakin murmushi kenan
dai dai sanda take sanya qafarta cikin falon nasu.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 61

Dai dai lokacin sabreen din ke aje wayar mashkur wanda ya sanyata a
lissafin yadda komai zaya kasance.

Shine mutum na farko daya matsanta mata da son ta bishi wani guri
wajen garinsu. Da fari yaso ace dubai suka wuce,saidai tayi duk wata hikima tata ta
kansile tafiyar da a baya ya tayar dayi musu shirinta gadan gadan. Baisan wace
ainihin sabreen ba.....shi yasa ya gaza fahimtar dukka wadannan shirmen basa
gabanta. Taqi kadan take jira ta yasar da qwallon mangwaro ta huta da quda.

A matse take.....kuma cikin matuqar buqatar kudaden saboda aikin
ayshatu data tabbatar gab zuciyarta take ga kaiwa ga matakin da zata daina moruwa.
Ko a jiya data ziyarci gidan jikinta yayi sanyi.......ta kuma sare sosai da yanayin
jikin nata,har sun fidda rai da ita a wunin ranar,amma da yake shi rai idan yana da
sauran shan ruwanshi a gaba to tabbas fa sai ya sha.

Motsin shigowarta ba tare da sallama ba ya sanyata daga fararen
idanunta ta zubesu a kanta.

"Meye hakan kuma yau?" Tayi mata tambayar tana duban fuskarta wani abu yana darsuwa
a ranta.

Fuskarta da fara'a ta juya tana fadin

"Au.......mantawa nayi wallahi" Saita tsaya daga qofar tana yin sallamar kamar
yadda suka saba.

Sai data danyi jim kadan sannan ta amsa mata,ta bude labulen ta
shigo,sabreen ta bita da kallo can qsan rabta wani abu yana kai kawo

"Sannu da gida" Ta fada tana nufar hanyar dakinsu,don sam ba'a sake take ba,Allah
Allah take ta samu waje ta yiwa wayartata ajiya me kyau. Tasan halin yaa sabreen
din qwarai da gaske,tana da mugun fikira da saurin dago wani abu dake a boye,a
yanzun haka kallonta da takeyi din gani takeyi kaman tana kallon wayar ne tarwai
bisa idanunta.

Bata iya amsa mata ba,tadai bita da kallo har zuwa sanda ta wuce
dakin. Janye dubanta tayi daga bakin qofar dakin tana sauke numfashi. Bataso taji
kokwanto ko shakka ko kadan akan 'yaruwarta......to amma haka kawai jikinta yake
bata wani yanayi daban wanda bata saba jinsa ba akan huda din.

Duk da tasan ba kowa a dakin amma hakan bai hanata kallon gabas da
yamma hagu da dama na dakin ba kafin ta ciro wayar daga aljihunta,ta kuma daga
katifarsu daidai inda tafi kwanciya ta jefa wayar. Tana dagowa sabreen na daga
labulen dakin ta shigo hade da sallama.

Wani mummunar faduwa gabanta yayi,ta amsa da sauri tana kuma
waiwayawa,sai suka hada idanu da ita. Tsoronta ya qaru,ta dinga ji kamar ta ganta
ne sanda take ajiyar.

Kanta da taga ta dauke shine abinda ya bata relief,ta sauke boyayyar
ajiyar zuciya ta fara fidda uniform din jikinta.

"Huda" Tayi kiran sunanta sanda ta zauna bakin gadonta.

"Na'am" Ta sake amsa mata tana sakin rigar uniform dinta data kama zata fidda.

Idanunta ta zube mata,kafin tace komai haneefa da nadra sun
shigo,wanda already sun rigata dawowa harma sun sauya uniform dinsu zuwa kayan gida

"Gashi yaa" Nadra ta fada tana miqa mata Leda

"Kuje falo a samu plate a juye yasha iska,gani nan fitowa" Ta amsa musu tana binsu
da idanu har suka fice kafin ta maida dubanta ga huda
"Zo nan huda" Ta umarceta tana ci gaba da karantarta. Ba musu ta ajjiye dan kwalin
hannunta sannan ta tako ta zauna a inda sabreen din tayi mata nuni.

Zuba mata idanu tayi tamkar yau ta fara ganin fuskarta,abinda ya sake
sanya ma huda fargaba da shakku

"Kinsan na tsani nayi tambayar meke faruwa?,akwai matsala?......a bani amsa da babu
komai....bayan kuma da matsalar.....akwai kuma abinda yake faruwar" Ta qarashe
maganar idanunta har yanzu cikin na hudan.

Har cikin qashinta taji tambayar tata tamkar taba hango komai tar
tar,saidai kuma wani sashe na maganarsa ya bata qwarin gwiwa tare da hikimar
kaucewar tuhumarta

"Tunda har akwai tsoron yaa sabreen a ranki,bai kamata ki bari a yanzu tasan muna
tare ba,har sai mun sake shaquwa da junanmu.....ta yadda koda ta tashi
rabamu,tausayin yadda mukeson junanmu zai sanyata ta haqura......akwai lokacin da
na ware da zamu sanar mata......kinga koda kuwa na girme mata nesa ba kusa
ba.....amma dole nayi mata biyayya kema na tayaki yi mata biyayya ko ba haka ba?"
Wasu daga cikin kalamansa da a yau suka sake sanyawa ta sake masa. Yadda ya mutunta
mata yayar da duk duniya bata da abu mafi girman daraja irinsa.....bata jin zata
kasa sonshi a ranta.

"Me yake faruwa huda......kome qanqantarsa kada ki boyemin" Ta furta tana kallonta.

Kanta ta girgiza tana narke fuskarta

"Me kika gani yaa sabreen......?" Itama kanta ta kada zuwa gefe guda gami da cije
lips dinta na qasa,daga qasan zuciyarta ana gaya mata lallai akwai wani abu da ba
dai dai ba.

"Canji nake hangowa dan kadan huda......wanda kowanne canji cikin rayuwa daga kadan
kadan yake farawa" Ta amsa mata kai tsaye ba wani kwana kwana.

Zama tayi sosai hudan tana dubanta

"Ba komai yaa sabreen fa.....idan ma akwai din ni bazan boye miki ba"

"Kin tabbata?" Ta jefa mata tambayar da wani nannauyan sauti dake tabbatar mata
tambayar me girma ce dake dauke da tarin fassarori da ma'anoni.

Kalamansa sukaci gaba da bata confidence,har ta daga kai cikin
tabbatarwa

"Na tabbatar" Ido ta lumshe tana gyada kai

"Shikenan" Sai ta miqe itama tana daukar daya wayar tata wadda ita ta shigo da ita
dakin.

Mika'il takeson tabowa.......tana da buqatar fara kawar dashi daga
layin,koda kudin visa passport da bill na asibitin ta samu daga gareshi,idanma so
samu ne ya zamana komai ya fita daga jikinsa,ta yadda duk abinda zai samu daga
bangaren mashkur din zai zamana tamkar ribar qafa ce.

Akwai abubuwa da yawa da yake list dinta wannan karon da takeson
yi,wanda kuma yana da buqatar muquden kudade. Akwai mutane da yawa data kwana biyu
bata gansu ba,tanason a wannan karon ta jiqa kowa yadda ya kamata.
Kaman yadda ta saba kebe kanta a dukkan lokaci irin haka da ya
shafeta. Yanzunma can farfajiyar gidansu ta wuce bayan ta rabbatar ta sallamesu da
dukkan abinda ya kamata. Me home work yana yi,me bita da hada haddar da zaya bayar
a islamiyya ma yana nashi.

JIB ta kira,kamar ko yaushe layinta layine na musamman da ita kadai ke
kiransa dashi,hakan ya sanya baya missing call,don muddin yaga kiran yasan akwai
abu me muhimmanci.

Gaisuwar ban girma yayi mata kaman yadda suka saba sannan suka shiga
tattaunawa kai tsaye akan ayyukan da takeso ta gama dasu

"Ka sani,ba kasafai nakeson dadewa da mutum ba.....nafison nayi na gama a wuce
gurin ya sake sabon lale.....ciwon aishatu shine abinda yafi dagamin hankali
najeeb......banason sanadiyyar wani ayshatu ta rasa ranta......inason sama mata
lafiya tare da mata tanadin rayuwa da zata manta abinda ake kira da tsanani talauci
ko wahala". Can qasan ransa yake hadiye wani abu,yana cika da mamakinta ako
yaushe,tana yawan sanya ranta da kanta a risk,bawai don saboda jin dadinta ko
walwalarta ba......aah......tana yin komai ne kawai don jin dadin wasu.

"Zamu kammala da izinin Allah......amma a wannan karon indai komai yayi kyau,adadin
kudaden an samesu daidai ya kamata kema ki inganta rayuwarki sama da yadda kike a
yanzu". Dan qaramin murmushi ne ya subuce mata,har jib yana iya jiyo sautinsa kadan

"JIB.....kune a gabana......har yanzu inajin mutanen dake tare dani ban kaisu
matakin daya dace sukai ba". Zuciyarsa ce ta karye girmanta na dada qaruwa a ranshi

"Ko yanzun ma me ya rage?,kinyi mana komai,tunda muna iya tsaiwa da
qafafunmu......mu ya kamata mu tallafeki kikai inda ya dace kikai din.....kusan
dukkanmy burinmu ki samu nagartaccen miji......"

"Mubar wannan maganar jib yanzu" Ta katse numfashinsa. Murmushi kadan ya saki,shima
kansa yasan ya taba inda batason aje. Sau tari yakanyi mata uzuri......koda shine
yaga abinda ta gani,yaji kuma abinda taji ba shakka iya hukuncin da zaima rayuwarsa
shine nisantar kowacce diya mace,saidai kallo daga nesa,indai ba qaddara me qarfi
da zata hada tarayyarsu guri guda ba.

"Zakibi mashkur abuja bayan mun gama da mika'il" Ya furta a nutse bayan shurun daya
gifta a tsakani na wasu 'yan mintuna

".....banason tafiyar nan jib"

"Itace hanya guda daya mafi sauqi da zamu kammala komai hankalinmu kwance......na
sani baki taba bin kowa ko ina ba......amma a yanzun zakije,na miki alqawarin ba
abinda zai faru,zan baki kariya da support harki dawo,zan bi bayanku idan ta
kama......kwana daya tal zaki bani zan kammala aikinsa.....mashkur din nada
tsananin wayo fiye da yadda kike tunani......amma kuma kinsan kutsa kai asusun
mika'il yafi na mashkur hadari da kuma tsauraran matakai da sai an masa shiri na
gasken gaske?" Shuru tayi tana son fasa maganganunsa daya bata su a cure. Kanta har
ya soma dan hargitsewa,sai ta gyara zamanta kadan tana cewa

"Ka rudar dani jib......mashkur nada wayon da lallai sai an bishi qafa da qafa
kafin cimma nasara......mika'il sassauqan wayo ne dashi......amma nasu account din
yana tattare da tsaro sosai haka ne?"

"Exactly boss lady" Ya fada yanason jefa raha cikin zancan. Ya jefawa fuskarta
murmushi kadan kuwa,sai taja dan qaramin tsaki

"A ajjiye wasa jib.....na soma gajiyawa da wadannan hadarurukan......inason muyi
babban aikin da zan huta nima hakanan na kula da rayukan dake gabana da kyau"

"Haka nakeso miki nima......bari na qara miki wani bayani kadan......mika'il yana
riqe da ragamar babban account din dake mallakin wani kamfanin sarrafa
diamond......kamfani ne ne matuqar qarfin jari da huldodin kasuwanci da qasashe
daban daban.......kusan rabin kudin wannan kamfanin asusunsa mika'il yana da access
dashi.....hakanan duk wani kudi da zai shiga ko ya fita yana da access da
hakan.....a bincikena na lura yana wadaqa da kudin yadda yakeso,saidai kuma yana bi
ta hanyar lura da saka tsantseni ta yadda ba lallai a gane hakan ba,saboda
mahaukaciyar riba da matsiyatan manya manyan kudaden da kamfanin ke samu a kowacce
rana....."

"Matsiyata.....manya manya?" Ta jefawa jib tambayar. Qaramar dariya ya saki

"Sorry......maqudan kudade"

"Okay......naji kana amfani da wasu kalmomi ne.....eheeen......kaga kenan komai
zaizo mana akan daidai?"

"Haka nake tunani......amma ki bani kwana uku,zan duba yadda zamu kutsa cikin
asusun.....amma shima dole ku hadu a ranar Koda na awa daya zuwa mintuna
talatinne......ki sassauta riqon tsaurinki kiyi kaman kin sakar masa komai....."

"Mtseewww....ya isa don Allah" Ta dakatar dashi,don zuwa yanzun abubuwan sun fara
barin kanta,tana ji kawai lokaci ya tunkarota da zata maida kai sosai ga 'yan
uwanta. Dukkansu girma suke qara yi,kuma suna da buqatar attention dinta sosai fiye
da wanda take basu a baya.

Jib na 'yar dariya yace mata

"Shikenan......cikin kwanaki ukun zaki iya jina koda wanne lokaci,kibar wayar a
bude,ki kuma fara shirin zuwa abujan.....nima zanyi nawa shirin"


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 62



"Yayi" Ta amsa masa a taqaice tana katse kiran.

Shuru kawai tayi tana jin yadda iska ke kai kawo a farfajiyar wajen.
Yadda iskar ke kadawa sai take jin kamar kwatankwacin yadda tata rayuwar ke garawa
kenan,daga hagu zuwa dama,daga dai dai zuwa rashin daidai,amma a yanzun cikin ranta
takejin lokaci yayi da zata tsaida komai.....ko a iya haka ta tabbatar tayi qwarin
da rayuwarsu ba zata tagayyara ba.

Tunda ta tabbatar ta fita zuwa farfajiyar gidan ta rufe qur'aninta,ta
kuma miqe da hanzari ta wuce zuwa cikin dakinsu.

Cikin mintuna qalilan ya cire dari darin da take na amsa wayarsa da
takeyi cikin dakin. Tun tana a tsaye tana kai kawo da kuma leqe tsakanin labulayen
dakin har ta koma ta zauna sosai a gefen gadon tana sauraren kalamansa dake da wani
irin dadi suke kuma sake samun matsugunni me kyau a zuciyarta.

Yadda dukka kalamansa suke a tsaftace,ba wani kalma ko furuci maras
kyau ya sanya take sake jinsa sosai cikin ranta,wani bangaren na zuciyarta kuma
yana yabawa kamalarsa da kamewarsa.

Ba wani abu me muhimmanci da zaman zaiyi mata,don haka ta yanke duka
tunanin tana miqewa daga inda take din tana nufar cikin gida don komawa dakinsu.

Tun daga nesa kadan dab da qofar da zata sadaka da ainihin tsakar
gidansu ta hangi hadiyyan. Ta ganta sarai zance takeyi,wanda dama takanyi din
lokaci bayan lokaci.

So samu tabi ta wata hanyar da bazata hada numfashi da ita ba,to amma
kuma babu hanyar,saidai tabi zabi guda daya daya rage mata,ta koma ta zauna ta
jirata har ta gama zancan tabar wajen. Wannan abunne kuma takejin ba zata iya
ba,duk abinda ta niyyaci ko nufaci yi ba kasafai take bari dalilin wani ko wata ya
sanyata ta juya da baya ba.

Tunda ta doso gurin ta fuskanci hankalinsa ya dauku a kanta. Ba baqon
abu bane a wajenta saurin gane motsi ko manufar d'a namiji a kanta daga kallo daya
tak. Dauke hankalinta da idanunta tayi daga wajen kamar bata san da zamansu ba tana
wucewa ciki.

"Wannan 'yar gidanku ce itama kenan?" Ya maida hankalinsa ga hadiyya yana
tambayarta wadda tuntuni idanunta suna a kanshi,cikin wani irin banzan kallo da
bacin ran yadda yake kallon sabreen din

"Eh 'yar nan dince.....sai akayi yaya kuma?" Ta bashi amsa a matuqar fusace har
sabreen dake gab da wucewa tana ita jiyota.

Kanta ta girgiza kawai tana sakin siririn murmushin nan nata maras
sauti me dauke da tarin ma'anoni masu yawa. Itakam daga hadiyya har dukkan wani
gajan baqo da zayazo wajenta bata tunanin akwai wanda ya isheta kallo a cikinsu.

"Ina kuma hudan?" Sabreen ta tambaya tana kallon sararin da tabar hudan a zaune
kafin fitarta

"Ta shiga daki" Haneefa ta bata amsa. Labulen daya sakaya qofar shiga dakin tabi da
kallo

"Daki kuma?,me takeyi a ciki?"

"Ban sani ba wallahi.....naga dai ta shige" Nadra da aka miqawa tambayar ta amsawa
sabreen cikin rashin taqamaimen amsa

"Tun yaushe ta shiga din?" Ta sake tambayar nadra wannan karon qasa qasa.

"Baki jima da fita ba" Ta bata amsa itama da yanayin yadda tayi mata tambayar. Bata
son saka ko darsa wani abu a ransu,don haka tadan sake rantabrana kallon nadra

"Rufe littafin data bari a bude din" Batayi gaggawar shiga dakin ba don kada ta
barwa zuciyar yaran wani hasashe,saita koma ta bude fridge ta dauko ruwa,ta qarasa
gaban first aid box dinsu dake ajiye cikin falon t dauki paracetamol ta taka zuwa
dakin.

Daidai sanda ta shaqi wani sassanyan numfashi daya cika fal da
farinciki da kuma shauqin soyyayya,daidai lokacin ta daga labulen dakin tana takowa
zuwa ciki.

Mutuwar kwance tayi sanda idanunta suka ga shigowarta,sai ta kasa ci
gaba da maganar da taso ci gaba da yi. Tana iya jinsa yana cewa
"Hellooo.....my love.....hello" Amma ta kasa kowanne motsi. Duk sautin maganarsa
qwaya daya ji takeyi kamar zata saki fitsari,don tana ganin yadda sabreen din ke
matsowa tsaf zata iya jin sautinsa.

"Me kikeyi a kwance bayan sallar magariba?.....kuma na barku ne kuna karatu?" Ta
mata tambayar tana kafeta da idanu,gami da zama saman drawer dake tsakanin gadajen
nasu. Shuru yayi daga inda yake zaune yana bin sakannin da suka kwashe da ita akan
waya suna qara gudu,yana kuma sauraren sautin muryar sabreen dake ratsowa ta cikin
wayar zuwa kunnuwansa tare da sake tuna masa abubuwa masu yawa da suka shude
tsakaninshi da ita.

Numfashi taja ta sauke,lokaci daya yadda zata sauya daga ainihin
yanayinta yazo mata,saita bata fuska

"Banajin dadi ne". Inda hankalinta cikin jikinta yake a lokacin ba shakka babu
abinda zai hanata jiyo sautin fitar murmushinsa.

Ko iya hakan yana gwada masa samuwar matakin nasara daga gareshi. Ta
yadda ya bibiyi diddigin rayuwarsu.....a yadda bincike ya fito masa.....basa iya
boye mata komai.....komai girman laifinsu ko gaskiyarsu.....komai tsanani ko
maslaharsu.....ba wani abu da suke iya lullube mata shi,yau gashi ya fara taka
matakin nasara......ta koya qarya saboda shi.

"Me yake damunki haka nan da nan?" Cikin qwarewa wajen iya bankado abinda ke
lullube ta tambayeta. Tambayar data sanyashi jingina bayansa da kujera yana jiran
jin amsa ta biyu

"Kaina ne yake ciwo" Sai ya tsinci muryar sabreen din tana bada amsar da hudan ce
ya kamata aji haka daga bakinta.

Yadda ta bada amsar ya sanya huda daukewar numfashi daga jikinta na
wucin gadi,tare da sanya Naseer tattara hankalinsa akan wayar,kadan kadan fargabar
kada ya zamana ta gano meke lullube tana son saukar masa.

"Ga magani tashi kisha" Ta sake cewa da huda tana miqa mata kofin ruwan dake
hannunta tare da satches na maganin.

Ruwan da maganin duka tabi da kallo,ta fara motsawa kadan sannan ta
miqe da sauri ta zauna tana sakin wayar. Santsin pillow din ya sanya ta zame ta
kuma sulale ta sauka a gefen cinyarta saita matsa kadan tana qarasa danneta.

Ci gaba tayi da dubanta har zuwa sanda ta balla maganin tasha,sai ta
miqa hannu ta karbi rayuwar ruwan da maganin itama ta balla ta sanya a bakinta tabi
da ruwa

"Ba abu mafi sauqin fade irin ciwon kai.....amma ki sani,yawan kiran sunansa yana
iya jawoshi koda babu shi a wajen" Ta fadi tana qarasa sauke idonta a kanta.

Tsoro da fargaba ya sake cikata,saita lumshe idonta tana son dasa
gaskiyarta a zuciyarta

"Nima zamana kenan na jishi ya saukar min,na dauka nadan lokaci ne xai sauka idan
na kwanta"

"Allah ya sawwaqe" Ta fada a taqaice tana takawa a hankali hadi da ficewa daga
dakin.

Wata ajiyar zuciya ta sauke tana fidda idanunta waje,tana iya jin yadda
bugun zuciyarta ke kai kawo wanda ta tabbata tsoro razani da kuma firgici ne ya
haifar mata dasu.

*****Tsakanin asabar da kuma lahadin yana da isashe lokacin da zaiyi shirin komawa
bakin ayyukansa zuwa litinin,wannan ya sanyashi maido da dukan ayyukansa da suka
tsaya sakamakon tafiyar da yayi.

Shi kansa yasan satin da zasu shiga din ba satin zama bane,babu hutu
sam a tattare dashi. Aikine me yawan gaske,don bayajin zai zauna ya huta har sai
yakai ga gacin kammala komai ya kuma bude kamfanin da a yanzu shine cikar burinsa.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 63


Sassanyan yammaci

Please Login or Register in order to submit comment