You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikinsa komai daya kama na neman lafiyarta zaiyi mata
shi,bayan ya tanqwara zuciyarsa wadda kowanne taqi tana tuna masa da yanayin nata
action din akan mahaifinsa sanda yake jinyar ajali. Ya sani idan zai biya ta wannan
ko paracetamol maamah bata cancanci tasha ba ta hannunsa.....to amma har yanzu
huduba da tarbiyyar anni tana yawo a jininsa.

"Uwa uwa ce fu'ad,duk lalacewarta ba wata madadinta" Wannan maganar ya jima da
haddaceta daga bakin annin.


★Cikin sati guda komai ya kammala na fitar da maamah din qasar Egypt.
Fu'ad da kansa yace musaddiq yayi zamansa su samu hutu sosai da amna,don itama amna
din har yanzu yana ganin kaman bata gama sakin jikinta ba bata warware gaba daya
ba. Sanda yake shirin tafiyar sabreen ta sameshi a daki,ya daga kai daga abinda
yakeyi yana dubanta. Sosai cikinta yake sake bayyana kanshi kowacce rana. Sosai
cikin ke qara mata wani kyau,shi kansa zamanta a jikinta kyau yake mata. Hannuwansa
ya harde yana kallonta da sassanyan murmushin nan nasa. A kwanakin gaba daya ta
sake sauya masa,wani abu me sunan tattali da kulawa da bai sanshi ba yake samu daga
gareta. Wani irin respect take bashi,bai taba jin bashi respect yana burgeshi ba
kaman a kanta,ta maida kanta qasansa sosai,komai zatayi tana nuna ita din a
qarqashinsa take,ita din mallakinsa ce.

"Sun hanaki bacci halan so abbee dinsu suke jira yazo tayasu hira" Ya fada yana
bude mata hannayensa. Bata tsaya wani bata lokaci ba ta taho ta fada ciki,ta kuma
lafe abinta. Ba wani guri da takejin tsananin aminci kaman qirjinsa,ba wani guri da
take ji take kuma samun cikakkiyar nutsuwa irin qirjinsa,wani guri ne na musamman
da takejin duk duniya bata da kamarshi.

"Na gama shirya nawa kayan fa hamma" Ta fada a shagwabe. Dan dagata kadan yayi daga
jikinsa yana duban fuskarta.

"Zuwa ina kenan adda?".

" Egypt mana" Ta fada a shagwabe tana maqale kafada. Kai ya girgiza yana sakinta
sannan ya fara takawa yana barin wajen

"No.....zaki zauna a nan har mu dawo,kinsan yanayin da kike ciki ai ko?,ko kin
Manta wani hutun nake shirin baki ma?". Batace masa komai ba har ya qare
zancen,saita sauke hannayenta data harde a qirjinta tana takawa a hankali zuwa inda
yake zaune yana basarwa ta hanyar qirqirar wani aikin.

Dab dashi ta zauna har jikinsu yana gogar na juma,tasa hannunta ta jawo
fuskarsa zuwa inda take kaman yadda shima yakeyi mata.
"Nasan me kake tunani,nasan abinda yasa ka fadi haka kuma.....amma kada ka
manta.....har yanzu maamah uwa ce.....kuma nidin nayi alqawarin riqe hannunka
gam,zamuyi tafiya bisa tafarkin rayuwa a tare,da dadi ko babu dadi right?". Kansa
ya daga a hankali yana dubanta,ya rasa wadanne irin mutane haka Allah yayi masa
rahama da ni'ima dasu?,sam basa duba sharri sai alkhairi a tare dashi,duk da irin
uwar da Allah S W T yayi masa jarrabawa da ita.

"Koda maamah zata kasance me laifi a waje na.....nikam na yafe mata,har abada babu
wata uwar da zata iya haifamin muhammad jadda sai ita.....ta kuma haifamin din,ina
da abinda zan iya saka mata dashi?". Idanunsa ya lumshe kawai yana jin yadda
soyayyarta ke tsatstsaga jikinsa. Addu'ar mace ta gari da yayi Allah ya bashi ma
sama da abinda ya roqa din,yana jin kunyar idanun kowa......yana jin kunyar sanyasu
su yiwa maamah wani hidima bayan dukka tarin sharrance sharrancenta a garesu,wanda
har zuwa yanzu shikam yana ji a a jikinsa maamah din bata hau sirad'al mustaqeem ba
da gasken gaske.

Hannunta ya riqe sosai cikin nasa da wani irin taushi.

"Na gode sosai my world......na gode duniyata". Murmushi ta sakar masa

"Ba godiya tsakanina dakai.....kome nayi maka kafi qarfinsa a wajena".

Tafiyar sai ta kasance me sassauci a tare dashi,don kasancewar
sabreen a tare dashi cikin kowanne motsi a rayuwa ba qaramin qarfafa masa gwiwa
yakeyi ba. Sun isa Egypt bisa jagorancin Dr awwab,an kuma gabatar da maamah ga
qwararrun likitocin asibitin,wadanda suka dauki kwanaki suna dukkan bincike da
gwaje gwaje.

To sakamakon dai guda daya ne,hawan jini ne me tsanani da har a Egypt
dinma dai bai sauka ba,sai kuma wani abu data qulle a zuciyarta da suke ganin kaman
shima yana barazanar taba lafiyar zuciyarta.

Sabreen ta girgiza matuqa,jikinta kuma ya sanyaya,ta qara cika da
mamakin maamah,ta kuma sake sallamawa lamarinta,ta qara yarda da imani da yaqinin
lallai wanda Allah ya shiryayye......ba wanda kuma ya isa ya shiryar da wanda Allah
ya batar. Daga idanun maamah da kallon da take binta dashi duk da kalar hidimarta
gareta ta karanci ba wani rusunawa ko nadama a tattare da ita......qaddararren
ciwon daya zama jarrabawa game hankali ne kawai yayi mata cikas ya hanata duk wani
sukuni.

Daga qarshe sun yanke zasu ci gaba da bata kulawa har na tsahon wata
guda suga abinda hali yayi. Da taimakon qwararun nurses dake kula da maamah din aka
soma dorata akan magunguna da therapy kala kala. Duk da akwai masu kula da ita din
sabreen bata zauna ba,saidai ko yanzun sabreen ce zata bata abinci ba zata karba
ba. Da idanu take kafeta,wani abu yana sake mata ciwo,duk sanda ta kalleta
zuciyarta tana gaya mata.

"Yarinyar tayi winning a kanki,ke gaki a zaune saman wheelchair ko yatsarki baki
iya dagawa". Rana ta farko da zuciyarta ta gaya mata haka bayan sun gama zama da
ita ne sun wuce masaukin da suke kwana.

Kuka sosai ta dingayi,hawaye shabe shabe daya na bin daya,hawayen zallar
baqinciki faduwa da kuma asarar da tayi.

Hakanan nurses din dake kwana da ita suka taru a kanta suna
lallashinta,amma taqi tsaida hawayen tamkar ma suna tunzurata. Haqurin da suke bata
ma sake bata mata rai yakeyi,ta rantse inda bakinta yana magantuwa su kansu da sai
sunji magana iya magana.
Jirigi guda musaddiq da amna,farouq da fannah......saddiq da huda
wadda ta soma murjewa ta fara qiba suka shigo Egypt duba maamah din.

A ranar taga baqar ranar da zata iya cewa kaf fadin rayuwarta bata
taba ganin irinta ba. Kowa yana zaune da qugunsa......yana takawa da
qafafunsa....hannu kai da qafufuwansu dama bakunansu gaba daya suna aiki amma banda
ita?,banda nata?,ita kadai dai komai a kanta ya qare?. Wannan tunanin ya sake
sakawa ta dinga fitar da hawaye,har numfashinta ya sarqe saida likita ya shigo ya
mata allurar bacci.

"Har yanzu akwai wata danqararriyar damuwa a ranta.....kuma indai bata cireta ba
treatment dinmu bazaiyi aiki ba,jininta bazai taba sauka ba.....tana da ciwon tun
asali tayi wasa da magungunanta har sai daya zame mata haka,qodarta ta fara nuna
alamun failure.....duk yadda zakuyi ta cire damuwa a ranta". Bayanan da likitan
yayi musu kenan. Dukkaninsu sunsan wani abune me suna gaibu tilasta maamah ta cire
damuwa a ranta,damuwar da dukkaninsu suka kasa gane ta meye idan ka dauke fu'ad
sabreen da musaddiq.

A nasu hasashen it's high time ace maamah ta cire komai a ranta,so ba
damuwar dabi'unta bane na baya,saidai fu'ad sabreen da musaddiq sunsan cewa HALI
ZANEN DUTSE......BARIN HALI KUMA SAIDAI MUTUWA.

*_TURQASHI.....WAI ME KARATU NACE BA.....WAI SAI YAUSHE NE MAAMAH ZATASAN ANNABI YA
FAKU?,SAI YAUSHE NE HALINNAN ZAI CANZA?_*155


★Cikin wata gudar nan da suka dauka mata ba wani kalar treatment da
ba'ayi mata ba. An kashe kudi sosai anyi amfani da engine da fikira da fasahar dan
adam a kanta amma ba wani canji ko qanqani da aka samu. Duk wata lalurarta saidai
ayi mata,bata tsinanawa kanta komai don ko yatsanta bata mallaka ba,bata isa ta
juyashi ba bare sauran sassa na jikinta. Idanu da kunnuwan ne kawai suke aiki,banda
su za'a iya cewa komai a jikinta ya tsaya a aiki idan ka cire ZUCIYA.

Wannan zuciyar dai da annabi yake mana gargadi da jan kunne a
kanta,wannan zuciyar dai da yake gaya mana idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan
ta baci dukkan jiki ya baci. Wannan zuciyar dai wadda da ita ake gwada nagartar
bawa.....wannan zuciyar dai wadda da ita ake ganin qarfin mutum,ba qarfi na jiki ba
ko qarfi na dukiya ko qarfi na mulki ko qarfin iko ba.

(Ubangiji don girman al'arshinka kasa mufi qarfin zuciyarmu,ya Allah kasa mu
mallaki zukatanmu don hasken fuskar manzan Allah,wallahi wallahi duk wanda kaga
yayi qarko to tabbas ya mallaki zuciyarsa ne......yafi kuma qarfinta,ya haneta
aikata abubuwa masu yawa daba daidai ba,dukkaninmu kowa yasan daidai yasan kuma ba
daidai ba,kubutacce a cikin mu shine wanda ya mallaki zuciyarsa yaji tsoron
Allahnsa akan komai na duniya da lahira,yake kuma aiki da nasa hankalin).

Dole hakanan don ba yadda za'ayi mata suka tattara suka koma gida
nigeria da sauran tarkacen kayan therapy din da za'a iya siya mata,wadanda zasu
dinga motsa mata gabbanta,kaman yatsun hannu da sauransu.

Ma'aikata dole ya sanya aka samo masa ya dauka,wadanda zasu kula da
ita da komai nata. Wankanta,cin abincinta,sallarta tsaftar kanta data jikinta.
Already tana da masu aiki dake tsaftace gidan suyi girki,akwai guard kuma a gaban
gida da farfajiya masu kula da gidan gaba daya.

Rayuwa duk yadda kayi haka za'a yi maka,Allah da kansa yace wadancan
kwanakin sune muke juyasu tsakanin mutane,kwatankwacin karin maganar bahaushe da
yake cewa YAU GAREKA GOBE GA DAN UWANKA.
Wata babbar dama ce ta samu ga wadannan ma'aikata da aka dauka,sabbi
da kuma wasu daga cikin wadanda suke cikin gidan. Bude cin karensu babu babbaka
sukayi,kowa yayi abinda yakeso a sanda yakeso,a kuma yanayin da yaga dama. Bata da
bakin magana sai idanu,sai tarin baqinciki da takeji kaman zai kasheta.

Idan tayi bayan gida ko fitsari,muddin fu'ad ko musaddiq basa nan
sai ta gane kurenta. Don zasu barta da abinta sai sun gama sharafinsu sannan suzo
su wanke su gyarata bayan sun gama tsaki toshe hanci da harara da baqar magana.
Tanaji tana gani duk wani abu da yake mallakinta ita keda iko dashi sunayin yadda
sukaga dama,da sunji alamun zuwan musaddiq ko fu'ad harma da sabreen......yanzun
nan zasu dawo gabanta su zauna suna nan nan da ita. Takan yawaita kallon fu'ad
din,tanason gaya masa irin abinda suke aikata mata amma ba wannan damar,ba bakin
magana,tana ji tana gani zasu gama abinda zasu yi mata su fice,su kuma su dora daga
inda suka tsaya.

Duk abinda mutum yake akwai ranar da dubunsa zata cika,khairan au
sharran......muddin kaga ka dade to Allah yana qara maka lokaci ne yaga ko zaka
tuba?,ko zaka gyara kurenka?.....ko zaka gano kanayin ba daidai ba?....kaman yadda
bahaushe yace komai nisan jifa qasa zai fado.....komai girma gona akwai kunyar
qarshe.

A irin wadannan ranakun Allah ya kawo sabreen katsam. Basuyi zaton
zuwanta ba,don ba lokacin zuwan nata bane. Yanayin da taga sun watsar da maamah din
ya daga hankalinta sosai. Hawaye kawai ta dinga yi tsoron Allah ita kanta yana sake
shigarta,wato dan adam ba kowa bane.....kaman yadda yake ba'a bakin komai ba.
Girman kai dagawa da mugunta dukka idan kaga mutum yana yi Allah ne ya ara masa
lokaci,dama ce wadda idan yaga dama ya qwaceta shikenan ta tafi kenan har gaba da
abada.

Ko a mafarki akace mata maamah din zata dawo haka ba zata gasgata
ba......ko da wasa aka ce mata akwai lokaci me zuwa kaman haka ba zata yarda
ba......matar dakeji da dukkan wani izza taqama da gadarar qarfin iko,yau gata
zaune waje daya,ko ruwa bata isa ta bawa kanta ba idan ba'a bata ba.

Kaf ma'aikatan gidan ta tattara,bayan ta gama jin ta bakin amintaccen
malam sa'adu,wanda ya gama karantar halin kowa. Da kanta ta yanke hukunci ta
sallami dukkan wanda lambarsa ta fito na baqin hali da mugunta. A ranar tayi kuka
tayi kuka,kukan tausayin kanta a matsayinta na 'yar adam wadda itama haka tana iya
kasancewa a kanta. Tun fu'ad na lallashinta har ya rasa ta ina zai bullo mata. Ya
dafe habarsa kawai yana kallon yadda tasa ciki a gaba tana kuka. Kuka akan
maamah?,duk sanda ya tuna da wannan abun yana bashi mamaki.

Baiyi zaton koda mutuwa maamah tayi ba hakan zai d'a d'a sabreen da
qasa ba

"Ya ilahi......wacce irin zuciya ce da ita?" Ya tambayi kansa da kansa yana sake
jinta har cikin qasusuwansa. Ya tabbatar kyakkyawar zuciya kawai baiwa
ce......baiwa ce da ba kowa Allah yake yiwa ita ba,baiwar da tafi duniya da abinda
yake cikinta alkhairi.

"Ya isa haka sabrrrr.......ya isa.....babies dinki karsu dauka nina taba musu
maamah fa" Ya fada cikin damuwa. Shi kansa ba jin dadin ganin maamah a haka yakeyi
ba,to amma yasan cewa duk wani abu daya dace suyi mata sunyi mata shi,hukuncin
Allah ne kawai yake aiki a kanta.

Duk runtsi duk yanayin aikinsa sau biyu shida musaddiq suke zuwa,da
safe da kuma yamma wani kuma yaje da dare. Har yanzu wannan ruhin da wannan
zuciyartata basu gama yin laushi ba,abinda yafi komai dagawa fu'ad din hankali
kenan. Idan kaga tana gumi sosai to musaddiq yaje shida amna,ko ta ganshi tare da
sabreen ko kuma ta zubawa cikin jikin sabreen din idanu.

A yadda sabreen ta damu da maamah yayi tsammanin zuciyarta zata
sanyaya da dukkan komai. A yadda ta wahal da amna ta nemi rayuwarta ya zaci yanzun
zatayi nadamar aikata mata abinda ta aikata mata. Kai tsaye ya hana musaddiq zuwa
da amna kwata kwata,don itama 'yace me cikakken 'yanci da iyayenta ke matuqar
qaunarta,bai kamata a dinga razana rayuwarta da qananun shekarunta ba ta hanyar
zuwa da ita inda takeji kullum bata da security.

Wannan karon saida sukayi bincike sosai kafin daukan masu mata
hidima,asalin garinta na haihuwa suka shiga tushenta,suka samo amintattun mata da
suke da dangantaka da maamah din. Wasu ma cousins dinta ne......amma yanayin rayuwa
ya sanya duk suke kaman sun girmeta. A asali nutumin karkara mutum ne me karamci
mutunci da kuma martaba dan adam......mutum ne me juriya da amana,har yanzu akwai
ire irensu.....cikin taimakon Allah suka samo mutum shida a cikinsu. Uku mata uku
maza,da farko ma sunce kyauta zasu kula da ita,saboda Allah saboda kuma girman
zumunci. Basuyi fushi ko zuciya da yadda ta watsar dasu ba,saidai fu'ad bai yarda
ba,ya yankawa kowannensu albashin da iyalinsa zasu rayu cikin wadata da nutsuwa.

A duk sanda yaje dubata,ya cire duk wani shiga nashi na office don
gyarata ko mata wata hidima mamaki sukeyi. Babban mutum kamarshi?,wanda bai rasa
komai ba?,amma yana iya tsaftace qazantar mahaifiyarshi?,ko yayi mata brush?,ko ya
azata saman keken dake mata massage da sauran exercise na jiki?.

Abu daya da yakan tuna a ko yaushe a kanta shine girman haqqin
uwa......uwa uba kuma maamah din a yanxun abar tausayi ce ita,koda ita batasan
hakan ba,koda har yanzu zuciyartata batayi laushi ba.

Daya daga cikin ranakun da suka sake sanyaya jikin sabreen game da
maamah. Ranar wata Wednesday ne,ranan kwanaki biyu suka rage ita da fu'ad din su
koma madeena umra da kuma duba lafiyarta dana babies dinta,a asibitin da fu'ad yayi
mata register na komai. Burinsa a duniya a haife masa yaran a garin manzon rahama
annabi Muhammad,garin da jikin masoyi farin haske farin jakada yake kwance a ciki
wato madeena.

Tazo ta samu masu kula da ita sun gama mata komai. Ta qarasa kujerar
dake gefan wheelchair dinta suna gaisawa da ma'aikatan,idanunta yana kan maamah
din. Ta rame sosai,duka idan ka kalleta ba zakace mariya bace.

Kwanakinnan da cikinta ya sake turowa ya fito sosai bata kallon nata.
Kallo daya tak idan tayi mata to koda awa nawa zatayi da ita ba zata sake daga
idanunta a kanta ba.

Zama suke na kaman qawaye da masu aikin,don haka yawancin lokuta
idan tazo cewa take su zauna ayi hira,a nata lissafin wai ko hirar zata daukewa
maamah din kewa.

Yanzun ma hira sukeyi lokaci lokaci suna kallon wani hausa film. Sunason
kallo sosai,kuma bata hanasu ba indai sun gama duka ayyukansu.

Musaddiq ne yayi sallama,suka amsa masa,ciki harda sabreen cikin mamakin
jinsa a irin wannan lokacin. Kwata kwata ba lokacin zuwansu bane,saidai kafin ta
dauke idanunta amna ta biyo bayansa.

Doguwar riga ce a jikinta da qaramin hijab,kallo daya tayi mata taga
kaman ta fada.

Yau din ba wannan tsoron sosai a tattare da ita,ta tako kaman yadda
mijinta yayi ta qaraso gaban maamah ta gaisheta ta kuma dubata sannan ta matsa gefe
kusa da sabreen ba tare data damu da ko idanu maamah din bata daga ta kalli amna
ba.

Sun gaisa da sabreen kafin amnan tayi shuru. Sabreen ta daga kai ta
kalleta da dan mamaki. Amna ba kasafai zata zauna tayi shuru haka ba,abune me
wahala musamman idan akwai sabo tsakaninku. Dan tabota tayi,ta daga kai ta
kalleta,sai ta sake mata murmushi,itama amnan ta maida ma sabreen

"Lafiya kuwa auta?" Sabreen ta tambaya. Kaman jirar tambayar aman da ya taso mata
yakeyi sai ya qarasa fitowa zuwa sarari.

"Subhanallah" Sabreen ta fada a rude ta miqe tana riqe amna din dake sake
galabaicewa.

Kaman ya mance a inda yake,gaba daya yayo kan amna din yana
rungumeta ta baya hadi da riqeta sosai hankalinsa yana tashi. Sannu kawai yake jera
mata,har zuwa sanda ta kammala aman,daya daga cikin masu aikin maamah din tuni
harta dauko kayan aiki tahau gyara gurin,sauran kowacce sai jera mata sannu suke
cikin kulawa da tausayawa.

Idanu maamah ta zuba mata tana jin qwayar idanun dama kewayenta gaba daya
sun budade da yaji,tamkar an damqi garin yaji an watsa mata. Wani lafiyayyen gumi
ya soma karyo mata,ta kasa dauke idanunta daga kanta zuciyarta na wani irin
mahaukacin bugawa.

"Da ka sani musaddiqu ai baku fito haka nan ba"

"Daga asibiti muke......tun shekaran jiya bata da lafiya taqi kuma yarda aje
asibitin saboda tsoron allura......ganin ban samu shigowa da safen ba sai nace bari
mu shigo mu gaida maamah saimu wuce gida" Ya amsa mata yana goge mata jiki da
tissue.

"Allah ya sawwaqe.......Allah ya inganta......mu saidai mu tayaku da addu'a
ai,shekara ashirin rabona da haihuwa yanzu haka" Ta fada cikin raha tana murmushi.

Murmushi sabreen ta saki,sai a yanxun ta gano bakin zaren,wato shima
musaddiq yayi nashi aikin. Murmushin da yazo wuyan maamah ya tsaye mata,sai taga
kaman dariya sabreen take mata,kaman sabreen tana gaya mata KE DIN LOSER ce,kowa
yaci nasara a kanki,abinda ya sanya wani tari ya sarqeta ta soma qoqarin zamowa
daga saman wheelchair din saboda yadda zaman ya gagareta.156


"Subhanallah" Musaddiq ya fadi da sauri yana isa gareta ya tareta kafin
takai qasa. Hawaye ne suka qwace mata,inama ace tana da ikon tureshi,ba shakka da
sai tayi masa mummunar turewar da bazai sake sha'awar zuwa kusa da ita ko kawo mata
dauki ba.

Ciccibarta yayi yana maidata saman wheelchair din sannan ya daureta da
belt din da suke jiki. Komawa yayi gabanta ya zauna yana duban fuskarta yana kallon
gumin da yake tsatstsafo mata. Ba ita ba.....shi kansa radadi zuciyarsa take
masa,saidai akwai banbancin radadin da yakeji da kuma wanda ita yakeji. Ita nata
radadin na baqincikin rayuwar wasu ne,qyashi da kuma baqar hassada. Yayin da nasa
radadin ya ta'allaqa ne da yadda kullum zuciyarta ke sake gurbacewa,duk da irin
yanayin da take ciki,duk da irin qalubalen da take fuskanta amma hakan bai sanya ta
haqura ta ajiye koma meye da yake zuciyarta ba.

"Maamah" Ya kira sunanta kai tsaye da wani irin sauti bayan ya yiwa masu aikin
alamar su fita. Jajayen idanunta ta daga ta kalleshi dasu,tana da magana fal
bakinta saidai ba damar hakan.

"Kiyiwa Allah.....kiwa manzon Allah......na roqeki ko meye muka yi miki a
rayuwa.....ba domin kanmu ba don lafiyar jikinki ki manta da komai........ki duba
girman Allah ki sassautawa zuciyarki......haba mana!" Ta furta da wani irin bacin
rai da yakeji yana taso masa.

Idanu tsaf ta zuba masa,abinda ke nuna inda bakinta a bude yake tabbas
da yaji maganganu,saidai ko a iya kallonta a kansa kawai ya shaida masa maganarsa
ta shigeta da wani kalar mamaki.

"Ba wanda ya isa ya canza qaddarar wani.....ba wata qaddara da zata sauya kanta da
kanta sai wadda ubangiji da kansa yaso sauyata.......ba wani dan adam da zai
tsarawa wani rayuwarsa......kowa da yadda Allah ya tsara masa.... Me yasa ba zaki
hutar da zuciyarki ba?" Ya sake fadi yau din yana jin zuciyarsa takai
maqura.......a yau din yana jin yana yanke dukkanin tsammaninsa da sauyawar halaye
da dabi'un maamah.

"Ki yafe mana idan mun miki wani abun.....me zaki ragu dashi?" Ya qara tambayarta
yana kallonta. Ba amsa,amma still hawayen basu daina fita ba

"Ko bayan an cuceka ka yafe.....ba zaka ragu da komai ba sai qaruwar daraja a
gunka......ki yafe mana indai mun miki laifi muddin kedin ke kika haifemu" Ya qara
fada yana hade hannayensa waje daya alamun roqo.

"Indai kun yadda ni din nice na haifeku me yasa ba zaku yimin abinda nakeso
ba?,indai kun yarda nice na haifeku me yasa ba zakubi umarnina ba?,me yasa ba zaku
kwanta nayi muku mulki irin na isassun iyaye ba?,me yasa ba zaku fahimci asiri
akayimin ba?,me yasa ba zaku gane ba hawan jini bane wannan?!" Wadannan sune
kalaman da suke ta kokawa a qirjinta suke koma neman hanyar da zasu fidda
kansu,saidai kuma ba wannan damar,illa hawayen baqincikin rashin samun damar magana
da batayi ba da suka sake wanke mata fuska.

Tsam ya miqe kawai,ya kama hannun amna da jikinta ya sakeyin laushi
qwarai bayan aman da tayi,ya miqa mata takalminta ta sakawa qafafunta suka fice a
parlor din sabreen da maamah na binsu da kallo,kowa da mabanbancin yanayi cikin
zuciyarsa.

Tausayin musaddiq da hammanta kullum take kwana take tashi,bata
tunanin duk yadda sukaso maamah ta shiryu idan har ubangijin daya halicceta bai
shirya mata hakan ba saidai kowa yayi haquri. A zuwan da take dubata da duba
yanayin gidan da masu kula da ita.....ba kalan lokutan da bata kebe ba zaune da
ita,daga ita sai maamah din ta karanta mata dukkan kalar wata nasiha me ratsa jiki
da zuciya......amma bata taba ganin alamun rusuna ko sanyi daga idanuwanta ba.

★"laila" Hajja harira ta sake kiranta karo na biyu. Daga kai lailan tayi wadda
ke zaune qasan carpet din dakin ta kalli mahaifiyar tata.

"Na'am hajja" Ta fadi dukkanin wani lungu da saqo na zuciyarta dama gangar jikinta
suna azalzalarta,tana jin kaman wuta ake hurawa sassan jikinta dama zuciyarta.

"Wacece ni?"

"Mamana ce" Ta amsa mata Kai tsaye idanuwanta kafe a kanta.

"Alhamdulillah" Hajja ta fadi tana sakin murmushi. Cikin zuciyarta cike fal da
godiya ga bokan da yayi mata aikin farraqu tsakanin maamah da laila,ya gaya mata
cewa wannan din qaramin aiki ne da zai iya aiwatarwa,ya mata alqawarin sai yazo duk
duniya ba wanda laila taqi jini taji koda sunansa sama da hajiya mariya.
"Zaki koma wajen maamah mariya?" Hajja ta gwada tambayar laila. Shuru ta danyi na
wasu sakanni,sai kuma ta girgiza kanta da qarfi.

"Bana so,bazan koma ba,ina wurin hajja na". Ta fadi bawai don tana nufin abinda

Please Login or Register in order to submit comment