You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Done" Ya fada kaman yadda ya saba. Daga kai farouq yayi ya kalli saddiq
din

"Kalleshi kaman mutumin kirki........ya addabemu cikin gida......sai yazo company
sai ya zama wani me biyayya.....thank god da Allah ya hadaka da fu'ad......da nine
da tuni ka kusa sakamin hawan ruwa" Ya qarashe maganar yana daukan gorar ruwan da
fu'ad ya dauko musu saman table yana mamakin yadda qananun hidima na cikin office
yake yi da kansa,duk da cewa yana da qarfin ikon da ko taka qasa yace bazaiyi ba
akwai masu yi masa.

"Bakasan mutane da yawa da suka fiya wasa ba suna da wani boyayyen talent?".

"Talent a wajen wa wai?,wannan?,kawai dai Allah ya tattaro mana shi da taimakonka"
Ya fadi yana bude murfin ruwan. Bai amsa ba fu'ad,yadai saki siririn murmushin da
ba lallai ka iya fahimtarsa ba yayi bismillah can qasa ya soma zuqa a hankali.

Kafin yakai ga dire cup din kira ya ratso wayarsa,saddiq yafi kusa da
ita don haka yace

"Hamma amna ce"

"Kai dauki kace mata lokacin aiki ne yanzun" Kai fu'ad ya girgiza da sauri yana aje
ruwan. Wayar ya miqa masa,ya sake duba kiran sannan ya daga

"Good morning hamma"

"Mornin lovy dovy". Qaramin murmushi ta saki

"Hamma ka tashi lafiya?,yau ka fita early kuma anni tace baka tambayeni bama" Ta
qarashe fada da shagwabar nan tata data zame mata jiki. Murmushi ya saki

"Ban tambayeki ba amma kina raina amna.....wani muhimmin abune ya taso.....kiyimin
addua,ki gayawa anni ma idan tazo sallan dhuha tayimin addu'a.....but karkice mata
wani abu ne ya taso,just kice munyi waya nace tayimin addu'a during salat of
dhuha".

"In sha Allah hamma.....Allah ya kula ya tallafa" Ta fada cikin kulawa

"Ameen autan anni" Murmushin jin dadin sunan ta saki

"Hala rival dina baya kusa hamma......yaji da kunnensa sunan dai nawa ne"

"Karki bari na dawo gida na iskeki....." Saddiq dake gefan fu'ad ya fadi da sauri.
Kai ya daga fu'ad din ya jefa masa harara

"A gaba na?"

"Sorry sir" Ya fadi yana shafa kansa. Abun ya yiwa amna dadi,yana iya jiyo qaramar
dariyarta har ya katse kiran.

"Baka hasko komai game da mikail ba?" Farouq ya jefa masa tambayar sanda yake
qoqarin duba wani saqo daya shigo system din nasa daga department na wanke dukka
diamond din da aka haqo don tabbatar da kyansa da ingancinsa.

Fararen idanunsa kewayayyu da hasken system din ya qara haskewa ya daga
ya dubeshi na wasu sakanni sannan yace

"Kai me ka hango?".

"Guy din bashi d gaskiya kwata kwata.....and ina kyautata zaton yana da masaniya
akan komai koda bada saninsa akayi ba".

"Na fahimci haka......but akwai wani abu ko wani behind him....."

"It's true.....ni tun tafiyarka South Korea na karanci abubuwa masu yawa game
dashi,bamu samu zama bane yadda naso har wannan abun ya faru......amma bari mu fita
a meeting dinnan"

"Yayi" Ya amsa masa yana duba lokaci.

Wata irin zazzafar tattaunawa ce ta wanzu tsakaninsa duk wani dake under
security team. Jiki da zukata sunyi laqwas da wani irin tsoro da kuma firgici.
Bacin ran da suka gani a fuskar boos din nasu ya sanyasu cikin tashin hankali,domin
kuwa wani abune da basu taba ganinsa a tattare dashi ba.

Dukka bayanan da suka bashi kusan yazo iri daya akan nasa da wanda
baki suka bashi,saidai akwai wasu sauye sauye cikin nasu

"Na baku 2days to find full details na dukka team din da sukayi wannan
aikin......na tabbatar ba aikin mutum daya qwal bane......team work ne tabbas!" Ya
fadi yana doka file din saman table din da yake kai.

Zuciya da qwaqwalwarsa duka a zafafe ya dawo office,yayi nufin yin
alwala don yayi salat dhuha kaman yadda ya saba sai yaga lokaci ma duka ya
qwace,duk da haka bai fasa daura alwalar ba saboda ita kadai tana saka masa sanyi
cikin zuciyarsa

"I need rest please.....duk meson ganina ka gaya masa sai after one hour......kayi
shutting komai saina nemeku" Yayi magana da mutanen dake tare dashi. Da daya da
daya kowa ya fice har saddiq. Farouq ya miqe a hankali

"Ina zaka kai kuma?"

"Zan bar CEO ya huta haka nan......da gaske brain dinka yana buqatan shuru na wasu
lokuta".

"Ko zan huta da ganin kowa banda kai farouq" Ya amsa masa yana jingine bayansa
jikin sofan da ya canza mata siffa daga kujera ta koma qaramin gadon hutawa cikin
sakan talatin.

Murmushi farouq ya saki,sai ya kalli agogonsa sannan yace

"Na sani.....but now dai dole farouq yadan matsa kadan Shima.....zanje nayi waya da
fanna......yau duka ban kira naji lafiyarta ba". Kiran sunan fanna kawai da yayi ya
sanya ya daga masa hannu ba tare da yace masa komai ba,sai ya sake sakin qaramar
dariya yana takawa

"Anyi zancan SOYAYYA zaka birkice.....bari na qara matsawa da hanzari......hala
daya cikin matan naka ne ma zasu kawo maka ziyara". Yayi zancan yana kaiwa qofa.

Maganarsa ta sanya fu'ad sakin murmushin dole duk da bai shirya ba,sai
ya bude idonsa a hankali yana bin bayan farouq da kallo har ya qarasa ficewa,ya
maida idon ya rufe bayan ya saita security na qofan nasa da wani qaramin remote a
gefansa ta yadda babu me iya damunsa,duk da ya bada warning ma reception nasa da
kuma saddiq. Shi a wannan ire iren situation dinma idan har yace soyayyar zaiyi
baisan ta yadda zai fuskanceta ba.....baisan ma ta inda zai kwasota ba. Yasha ji
daga bakin farouq rashin bada kulawa da bada lokaci yana kawo macewar
soyayya.....shi kam ya tabbatar wannan shine dalili na farko da zai saka tasa
soyayyar mutuwa murus. Ya tuna 'yammata biyu da farouq ya takura ya
hadasu.....abinda dukka ya rabasu dashi shine lack of caring. Sometimes ma mantawa
yakeyi da babinsu,koda kuwa ta hanyar tura tex bare kira bare aje gayin tattaki
zuwa gidajensu. Da kansu suka fahimta baida lokaci,suka kuma samawa kansu salama
zancan ya mutu murus,shima suka shafa masa lafiya.

A hankali kekenapep din ke gangarawa da ita layin gidan malam din,ya
kuma tsaya daidai gidan.

"Na gode......kana iya tafiya,gobe idan Allah ya kaimu zan nemeka saimu qarasa
komai,ka gaida ummaah da kyau"

"Zataji in sha Allah....tace zatayi tattaki da kanta don miki godiya". Murmushi
kawai ta saki tana sauka daga napep din,idanunta kan muhallin da malam ke bada
karatu. Ba jamaa wajen,ta kalli agogon hannunta,da sauran lokaci akan lokacin daya
saba xama,sai ta taka a nutse tana wucewa cikin gidan.

Kamar kullum ta taras da rumasa'u tana aikace aikacen gida,matar
malam na daga rumfarta a zaune tana tsince busashen zogale.

"Maraba da diyata" Ta fadi cikin fara'a da murmushi tana sauke farantin zogalen
daga cinyarta gami da karkade zaninta da ya d'an baci da kadan. Har qasan zuciyarta
kuma tana jin dadin dawowarta da wuri,ba kaman wancan karon ba data tafi ta jima
bata waiwayosu ba.

Itama tata fuskar da murmushi tare da jin dadin yadda aka samu wasu
halittu da suka damu da rayuwarsu ta qarasa shiga cikin rumfar,bayan ta zame
halfcover din qafarta

"Aah.....ina sauran jikokin nawa?" Ta furta tana duban bayan sabreen. Murmushi ta
saki tana zama saman shimfidaddiyar daddumar da matar malam din ta shimfide mata

"Ba daga gida nake ba gwaggo" Ta fada Kaman yadda taji rumasa'u tana kiranta wani
lokaci.

"Kash.....to ai naso ganin kishiyata haneefa ne ai" Ta furta tana dariya tare da
yunqurin miqewa

"Itama kullum zancanta kenan.....amma zan kawosu na kusa in sha Allah"

"To Allah ya yarda" Ta amsa mata tana bude fridge din dake ajiye a rumfar gaban
falonta ta ciro mata ruwan pure water me matsakaicin sanyi da lemon zobo,rumasa'u
ta hado da kofi ta shigo mata dashi.

"Nima inata sanya ido naga huda" Ta fada tana murmushi. Kiran sunan hudan ma ya
sanya hankalinta dawowa kan huda din data barosu gida.

"Zasuzo in sha Allah rumasa'u" Ta amsa mata cikin kulawa.

Zama tayi suna dan taba hira,tana son su sabreen yarinyar,wanda su
kansu basusan dalili ba,saidai ba ruwan ubangiji shi yakan sanya qauna da jituwa
tsakanin bayinsa a duk sanda yaso hakan ya kasance.

"Hala malam baya nan?" Ta tambayi gwaggo

"Yana nan,yadan fita ne kasuwa,amma da wuri yau din zai dawo,yana da karatun dare
na manya da yakeyi". Kai ta jinjina,tana jin dole zata jirashi har ya dawo,duk da
tanason komawa gida da wuri,don a yanzun hankalinta bai bata ta dinga nisan kiwo
ba.
Jikinta da zuciyarta sun gaza samun nutsuwa sam sam akan huda,cikin
jikinta takejin akwai wani abu ba daidai ba.

Iya yadda tayi magana da ita dazun kawai ya isa gaya mata akwai wani
abu,saita rufe babin wannan tunanin tana maida hankalinta tsakar gida hadi da taya
su gwaggo amsa sallamar malam din.

*Tsaye yayi kawai gaban madubi yana duban fuskarsa da kyau tare da son
bawa kansa qwarin gwiwa. Yana buqatar cikakkiyar nutsuwa da kuma qarin tattara
dukkan wani tsohuwar fasaha da qwarewarsa wajen ganin ya cimma nasara a cacar.
Tunda yake bai taba caca mafi hatsari ba irin wannan. Caca ce da zata iya zuwa masa
da sakamako guda biyu......nasara wadda zata wankeshi daga dukkan wani rudani da
tashin hankali.....ko kuma faduwa wadda daidai take da daukan guduma ta kuma
tarwatsa rayuwarsa gaba daya.

Hasashen sunan faduwa kawai sanyawa zuciyarsa wani irin mugun bugu
yakeyi,tuna sunan FADUWA kawai sai yaji kaman qirjinsa zai tarwatse,don haka a
yanzu da yake tsaye gaban madubin ya daga murya don baiwa kansa da kansa tabbaci
tare da qwarin gwiwa

"Ba faduwa a hanyata,tabbas nike da nasara......ni zan cinye!" Ya fadi da wani irin
qaraaji yana sake sanyawa ransa nasarar da gaske tasa ce.

Qofar aka dan qwanqwasa,ko ba'ayi magana ba yasan waye,don haka ya
waiwaya yana fadin

"Gani nan,tayar da mota" Sai ya juya ya dauki waya da maqullansa ya fito.

Baice da mato komai ba ya bude gaban motar ya shige,mato kuma ya
bawa motar wuta,ya danna hon me gadi ya dage musu gate din suka fice.

"Ina fatan yau baka shawu ba" Mato ya fada yana sake bawa motar wuta saman kwalta.
Harara ya waiwaya ya maka masa kafin yace

"Mahaukaci ne ni?,idan nasha ta yaya zan samu isa ga abinda nakeso?,......zan shawu
iya shawuwa bayan mun dawo da talin himilin kudin da zan cike gibin asarata". Kai
mato ya jinjina yana dan dukan steering

" Inaji a jikina kam wannan nasarar tana hannuwanka......munkaila me da'ira?.....ka
manta sunan naka ne?". Wata wawiyar dariya ya saki,sunan da mato ya tuna masa ya
sake jinsa cikin alfahari......wani rubutaccen suna ne daya samoshi daga wajen
abokan cacarsa. Muddin zai hau tebur din caca to ko kai waye ka zama nama,baisan
iya adadin abinda ya tara ba da dukiyoyin al'umma shekara da shekaru,sai yau gashi
dare daya wata qaqqarfar guguwa tanason yin gaba da tsohon
arziqinsa?......inaaaa......ai bazaya bari ba,sai inda qarfinsa ya qare. Iya sunan
da mato ya gaya masa ya sanya masa qarin karsashi tare da jin dokin isa wajen.

"Ni kaina inaji a jikina lokacin nawa arziqin ya gabato,don gagarumar caca ce ina
gaya maka me gida.......tsaffin 'yan caca za'a zuba wadanda suka sanya kudi masu
ciwo......don Allah banda ganganci ina tsohon hannu zai kara da sabon jini?,yaro
masanin dabaru da siddabarun kayar da mutum?"

"Tsautsayi ne mato" Ya bashi amsa wani murmushi yana subuce masa,don nasararsa
kawai yake hanga muraran.

Tafiyar mintuna kadan suka isa gidan cacar,tun daga waje ya fahimci
gidan a cike yake,abinda ya sake tabbatar masa da maganar mato. Ya fito a motar
yana murmushi suka jera da mato zuwa ciki yana sake bashi bayani akan komai.
"Amma me gida......nayi mamaki da me jadda bai nemeka ba".

"Har gwara ya nemeni da wannan shurun da yayimin......shirunsa yana nufin komai
mato......shi yasa nake bidar nasara a wannan karawar.......daga nan wajensa zankai
kaina ayi a gama......bani da tabbacin a yanzun baida masaniyar inda
nake.......tsaf yana sane da motsina duka zai iya yiwuwa". A mamakance mato ke
duban mikail,tsoron girman izza da qarfin ikon Muhammed jadda tana sake saukar
masa,saidai bai samu cewa komai ba suka qarasa ciki.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 81



Daga yadda yaga wajen ya sake amanna da maganganun mato din. Duba daya ya
fahimci tabbas masu tsohon arziqi da kudin caca ne,kuma da alama a yau din kowa
cikin buri yake,hakanan kowa yayi guzurin dukka wata dukiya da yake alfahari da
ita.

Saura kadan dariya ta fashe masa,don dukkaninsu shi a nasa idanun
kallon gidadawa yake musu,kuma cinyayyu da zasu qare wasan cikin hasara da rashin
nasara.

Su biyu rak ke zaune daga wata kwana cikin farfajiyar wajen. Kawu
kenan,wato kawu sama'ila shi da nasa aminin barau.

Cikin nutsuwa da shegen kwanyar da yake dashi yake karance mikail da
idanunshi sunkai kan kawo amma banda kan kawu din. A nutse yake karantar mukail,har
zuwa sanda suka zauna da'irar da za'a zuba caca ta farko.

"Me ka karanta ne sama'ila?,kayi shuru ko ka fasa ba zaka buga wasan ba?" Murmushi
kawu ya saki yana tura hularsa gaba.

"Tun bayan mutuwar yaya daya haramta min yin caca,ban qara zama gagarumar caca irin
wannan ba.....inaji a jikina silar arziqina ne yazo.....bazan zauna ba har sai naga
iya nashi takun......baka ruftawa wasa baka san yanayin hannun kowa ba"

"To me ka fahimta sama'ila?" Barau ya sake tambaya idanunsa akan yadda wasan ya
fara tafiya

"Dan zamani ne fa wannan da zai kara da tsaffin 'yan wasa......gogagge ne kana
kallonshi,kuma shima qwararre ne da irin tasa qwarewar,wanda idan kowa baiyi
takatsantsan ba komai zai iya faruwa"

"Shege sama'ila" Barau ya fada yana qyaqyacewa da dariya

"Ka zuba ido kawai kayi kallo" Ya amsa masa yana maida hularsa daga gaban goshi
zuwa qeya.

A duk sanda yakeson samun nutsuwa ta qwaqwalwa da ruhi sararsa shine
kwanciya,ya rufe idanunsa yayi kuma shuru a waje da muhallin da ba hayaniya ko kuma
motsin kowa. Ko yanzun hakan yayi cikin office din,saidai qarar wayarsa ya sanyashi
miqa hannu ya lalubota don yasan ring din na daban ya sakawa kiran don kirane da
yake buqatarsa
"Sir........yana gidan caca na green card"

"Good" Ya fada a nutse yana bude idanunsa

"Don't let him go.....ina buqatar information na wuninsa na yau gaba daya"

"Yes sir" Ya furta cikin girmamawa. Wayar ya ajiye,sai ya miqe a nutse ya zauna
ranshi na wani mahaukacin baci. Ga wani zargin ya sake shigo kasa akan mikail
yanason kore uzurin da zuciyarsa keson bashi. Muddin ya kuskura bincike yazo masa
caca yayi da kudinsa na halal tabbas!,zai nuna masa ainihin kalarsa......zai gane
waye zahirin muhammad jadda. Dukiyar da aka tarata da gumin halak?,dukiyar da ake
takatsantsan wajen jefa haram a ciki komai qanqantarsa?,kudin ruwa da ruba
dukkaninsu haramtattu ne a cakudasu cikin dukiyarsa,amma yau din zanyi ganganci ko
kuskuren zarar halalinsa ya jefa a qazantaccen guri irin wannan?.

Tsam ya miqe,sai ya koma saman table dinsa ba tare daya sanya takalma
a qafarsa,ya kunna system dinsa ya tattara hankalinsa akai.

Karo na kusan goma barau ya kalli kawu sama'ila kaman yadda mato ke
zaune yana murmushi daga gefan mikail yana kuma tayashi lissafin maquden kudade da
dukiyar da yaketa cinyewa ta abokan bugunsa.

"Sama'ila?,dama wannan shine hasashen naka?". Murmushi kawu ya saki yana karkacewa
kaman abun ya masa dadi

"Gaskiyar kenan barau.....amma barshi ya gama iya tasa dabarar......uwayensa na nan
zuwa su koyar dashi darasi" Wata dariya barau ya saki bayan ya gama fahimtar abinda
kawun yake nufi

"Yanzu naji batu,amma ta yaya muna da kai zaka bari wannan jaririn yazo gidanmu ya
cimu wasa?" Murmushi ya sake saki idanunsa akan mikail daidai sanda ya cinye alhaji
wada miliyoyin kudi

"Talala ce me kaman sake.....barshi ya gama karbarmin kudaden tukunna da gidajen"
Dariya barau ya sake saki harda buga qafa.

Cikin awa uku ya daurewa kowa jijiya a wajen. Cikin tumbatsa da izza
mato ya miqe

"Akwai wani sauran wanda zai kara da sarki?" Yayi shela yana ji a ransa sun gama da
kowa,babu me sauran motsi. Shuru ne ya biyo baya,sai ya sake maimaita tambayar yana
duban kowa d'ai d'ai

"akwai" Barau ya fada da qarfin murya. Mato da mikail din duka suka waiwaya suna
duban kawu dake qurya,sai suka dubi juna tsakanin mato din da mikail

"Waye kenan a cikinku zai shiga?" Tsam kawu ya miqe yana nuna kansa

"Nine" Ido suka hada sai suka bushe da dariya tsakanin mato da mikail

"Qaraso mana dattijo....koda yake ba dattijo a nan......inajin akwai rabona a
jikinka ne kaima.....ko giya ta kwana daya na sha da canjinka". Boyayyen dariya
kawun ya saki,ya fara takowa zuwa wajen kowa ya zuba masa idanu yana mamakin qarfin
halinsa,kamar ba'a gabansa aka cinye kowa ko ba amma shi zai jefa kansa?.

"Dame zaka shiga?" Ya jefa masa tambayar a raine. Karkacewa yayi ya zaro wasu
takardu yana dubansu. Takardun dake dauke da sunan alhaji aliyyu ahmad
zaki......mahaifi ga sabreen..... Takardar dake matsayin mallakin magadan kuma
marayan yaran da yayi Qundumbalar shiga cacar da ita,cikin jin cewa zata ciyo masa
tarin maquden kudaden da zasu zame masa silar arziqinsa gaba daya.

Saman teburin ya aza takardar yana kallon mikail,hannu ya sanya ya
dauka ya duba ya karanta ya kuma tabbatar original ce wanda gidan ya haura
miliyoyin kudi

"Ashe.....kudinka baaba ai ya haura 'yan canji ma ai.......idan na samu nasarar
cinye gidan nan ko?,rusheshi zanyi na maidashi gidan shaqatawa,ayita shigomin da
'yammatan unguwa ina hutawa dasu ina biyansu".

Wani abu ne ya cakewa kawu a rai,ya tsani zina,ya tsani harkar neman
matan banza,kaman yadda ya tsani shaye shaye,barshi kawai da cacarsa data zame masa
masifa wanda dama tana da shiga jiki. Kai tsaye yaji tsantsar cin fuska ce ya
tanadeta zaiyi musu wannan ya sake aza wutar qaimi a zuciyarsa,ya karkace kaman
yadda yakanyi a yanayi irin wannan,ya kalli Mikhail da kyau

"Idan dai har ya zama mallakin naka kana da wannan damar" Ya bashi amsar da wani
irin kakkaifan kallon dake gaya masa kai tsaye na SAI NA BAKA DAMAR CINYE GIDAN
SANNAN ZAKA AIKATA HAKAN.

Izza da jin cewa zai samu nasara akan kawun ya sanyashi ninka abinda
kawun ya zuba shima ya zuba cikin cacar aka fara buga wasan. Tashin farko kawun ya
maido takardun gidan yayi tafiyar ruwa da kudaden da mikail ya zuba,abinda ya jawo
hautsinewar wajen,hankula dukka suka komo wajen,aka fara yo dafifi,wadanda aka
cinye suke alhini dukansu karsahinsu ya dawo,sai aka fara zuba sabon wasa.

Da daya da daya ya dinga zuba abinda ya ciyo kawu sama'ila yana
kwashewa. Duk abinda ya zuba kawun ya cinye shaidan zuciya da kuma mato saisu gaya
masa ya sake zuba wani,zai iya yuwuwa ya samu nasarar dawo da abinda aka cinye masa
a baya.

Tafi tafi cikin qasa da awa biyu sai gashi yana tashi daga Mikhail me
manyan kudi yana komawa asalin mikail dinsa kaman yadda ya shigo wajen. Cikar awa
biyu cif komai ya qare!.kawu sama'ila ya wawushe duk wata kadara daya cinyo daga
wajen wasu ya zuba!,ya koma tsurar yadda ya shigo musu a wajen!.

Sowa ihu murna da tafi ya cika wajen,ainihin sunan kawu sama'ila na
teburin ya soma dawowa bakunansu wato DA BANBANCI!.

Kowacce tsiga ta jikin mikail zubawa takeyi. Idanunsa sun kada sunyi
jazur,jijiyoyin kansa sun fito rada rada. Sosai yakejin ya muzanta,ya toxarta. Ta
yaya zai bari wani qaramin alhaki tsohon daya bashi shekaru masu tazara ya kafa
tarihi a kansa?,tarihin da muddin ya bari ya tabbatu a haka.....to ko shakka babu
ya xubar da kimarsa da kwarjininsa a idanun abokan cacarsa dake bashi wani irin
girma. Karon farko a rayuwarsa da wani yayi nasara a kansa,shi kuwa ta yaya zai
bari haka ta tabbata?.

"Ga wasu kudaden na zuba.....azo a sake zama!!" Ya furta da qarfi,sautin daya sanya
wajen yin dif aka zuba masa ido.

Da sauri mato ya kalleshi,ya kuma ja hannunsa da qarfi yana dubansa
qasa qasa

"Wanne kudi kuma ya rage maka indai ba motar da mukazo a ciki ba zaka saka?"

"Qyaleni mato.....bakajin habaicin da suke yada min?,dole na aje musu tarihi,dole
sunan mikail suma yaci gaba da wanzuwa a kunnuwansu da bakunansu da wajen cacarsu".

"Wanne kudi ya rage maka?!"
"Ragowar abinda aka bari a asusun jadda" Ya fada yana jin zuciyarsa ta qeqashe,kuma
tabbas wannan kudin xai dawo da sauran kudin da duka narke,duk kuwa da yasan mugun
gangancin dake cikin aikata haka.

"Kada kayi haka!" Mato ya fadi a gigice.

"Anma yi" Ya amsa masa ba fargaba ko shayi saboda ya bawa kansa tabbacin shine keda
nasara.

Wayarsa ya fidda yabi dukkan process yayi transfer kudin da suka rage
zuwa account din wanda zai ajiye kudin,idan nasara tasa ce ta dawo masa,idan ta
kubce kuma dukka kudi sun tabbata mallakar KAWU!.

Daidai lokacin da akayi alerting mutum biyu fitar kudin,sai fuad dake
zaune yana bibiyar komai ya lumshe ido yana sauke siririyar ajiyar zuciya,daidai
sannan kuma kira ya shigo masa. Ko daya duba sai yaga daga department din da aka
kira ya daga yana cewa

"Just keep an eye on it,naga komai" Sai ya kife wayar yana maida dubansa ga allon
system din yana qoqarin tracking account na wanda aka sanya kudin.


*_TURQASHI....QAQA QARA QAQA,BAZANCE KOMAI BA😂😂.....amma akwai ZAZZAFAR TURKA
TURKA FA.....MUJE ZUWA_*

*HUGUMANKU CE*


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

Page 82

A wannan karon......daga shi har kawu samaila sai da aka basu hutun
mintuna ashirin,don kowannensu yayi iya shirin da zai qara yi. Magoya baya kuma
jingima kawun ya samu,wanda kusan dukkansu suna murna ne da nasarar daya samu,don
sun tabbatar cewa koda basu maida dukkan abinda Milakil yaci nasu ba,to tabbas
kawun zai maida musu wasu abubuwa kasancewar shi din nasu ne.

"Me gida......ka tsaya iya waccar asarar da kayi......kada kayi kuskuren sake yin
wani ganganci......ka fini sanin waye muhammad jadda"

"Sosai kuwa mato.....amma jikina yana bani nasarata tana tare dani wannan
karon......bazan bari nayita asara ba" Ya amsawa mato cikin yanayin da yake
alamtawa mato cewa mikail din yayi nisan da bazaiji kira ba.

Cikar mintuna ashirin aka sake zama,zaman daya dauki sabon salo ya kuma
dauki hankulan kowa dake wajen. Tsahon wasu mintuna ana fafatawa,inda daga qarshe
komai yazo qarshe. Kawu samaila ya sake wawushe kudin,ya kuma bar mikail cikin wani
irin yanayi tsakanin mutuwa da rayuwa.

Dukka kururuwar murna da muryoyin abokan kawu samaila dake tashi a
wajen baya iya fayyace komai. Abu daya kwanyarsa ke iya fahimta gami da maimaita
masa

"An qarasa cinye kudin jadda diamond resources,ba abinda yayi saura".
Kowanne sashe na jikinsa ya dauki rawa da wani irin kalar tashin
hankali mara misali. Yana jin komai ne tamkar yana mafarki.....yana ganin kamar xai
farka ko zai tashi,yana ganin kamar ba haka bane har sai daya damqi hannun mato

"Mato da gaske ne?,ko mafarki ne?"

"Da gaske ne maigida......ai na gaya maka dama". Taga taga mikail din yayi zai fadi
mato ya taroshi,jama'an dake kusa suka kuma karanci hakan suka kawo masa dauki ta
hanyar tallafe masa mikail din suka zaunar dashi suna masa sannu

"Kaima banda abinka oga ai kayi wauta.....hausawa sukace idan bakasan gari ba
saurari daka......na tabbatar rashin sanin waye sama'ila ya sanyaka sakin jiki
dashi kan teburin caca......amma ita dama yau gareka ne gobe ga dan uwanka,idan an
sake wani zaman ta yiwu ka samu nasarar maido wani abun naka"

"A wajen wa?......lallai garba ka manta waye sama'ila ne" Dan uwansa da suka

Please Login or Register in order to submit comment