You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanda kwanyarsa ta haska masa wani abu
lokaci guda tamkar haskawar walqiya cikin duhun dare.

Tsugunnawa yayi ya dauki dan kunnen.....sai yanzu ma ta dawo
kwanyarsa,sai yanzu tunaninsa ya soma haska masa wani abu

"Fateema?" Ta maimaita ainihin sunan da shine nasa STAMP din data bashi.

Komawa yayi ya zauna saman kujerar dake daura da qofar bandakin
yanason tuna yininsu na jiyan a tare.

Yayi dukkan wani flash back daga qwaqwalwarsa zuwa zuciyarsa da kuma
idanunsa,ba wani motsi nata guda daya daya bashi alamun rashin gaskiya a tattare da
ita

"To amma me yasa na farka na nemeta na rasa?" Ya jefawa kansa tambayar data
sanyashi miqewa ba shiri,ya jawo wayarsa da baiyi shirin kunnuwa ba ya
kunnata,cikin ransa yana jin gamsuwar tabbas ita ta aikata ko kuma tana da hannu
wajen afkuwar komai.

Sanda wayar ta daidaita sai ya fara yunqurin kiranta,saidai a duk
sanda zai kirata din sai computer ta datse kiran ba tare da an masa bayanin komai
daga danganci network ne babu a area din da take?,ko kuma wayarce dungurun gum a
kashe?.

Ci gaba yayi da gwada kiran babu qaqqautawa,har sai daya sare,energy dinsa
yayi qasa,ya tabbatar bazai cimmata a waya ba.

"Sai kayi tattaki ka sameta a inda take" Wannan shawarar ta sakashi zabura ya
miqe,ya zura takalman qafarsa a gaggauce,saidai yana daukan key din motarsa komai
ya tsaya masa cak

"A ina take?,a ina kuma zaka sameta din?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar data kusa
tsaida numfashinsa

"Na shiga uku" Ya fada yana jin dukka jikinsa yana rawa

"Bansanta ba,bansan komai a kanta ba" Ya fadawa kansa da kansa idanunsa suna tara
hawayen da babu makawa sai da suka yiwa kansu qofa
"Garin ya akayi haka?" Ya sake tuhumar kansa da kansa,abinda ya sanyashi sulalewa
ya zauna a wajen.

Yafi qarfin awa biyu zaune ya kasa hasalawa kansa komai,kafin daga baya
wata zuciyar ta bashi wata guntuwar shawarar data dan bashi nutsuwa kadan,har ya
iya miqewa ya gyara rigar jikinsa ya maida hularsa ya lalubi qofar fita.

Dukkan wani muhalli da yasan sun taba haduwa,cin abinci,shan ice
cream,shopping da sauransu ba wanda baije ba. Saidai duk inda yaje din dogon bayani
ne maras fa'ida ko kuma alfanu,domin ba wanda ya ganeta. Abinda bai sani ba
shine......ita din tamkar tarwada take a cikin ruwa......tana da matuqar santsi da
idan taje waje zai wahala ka sake samunta a nan... Muddin taje waje dakai sau daya
ta kansile wajen kwata kwata cikin jadawalin rayuwarta,ba guri bane da take
mu'amalantarsa ba a koda yaushe ballanta fuskarta ta zama sanniya a wajen mutanen
dake yawan xiyartar wajen ko kuma ma'aikatansu ba.

Tun yana zagayawa da qarfin gwiwarsa har ya sare. Zuwa sannan yanajin
zai haukace ne idan bai gayawa kowa halin da yake ciki ba,don haka yana isa Bristol
baiko koma dakinsa ba ya kira mato a waya.

Tazarar minti ashirin kacal ya iso,ya shigo dakin yana cewa

"Kai matsala ne dakai,wani lokacin sai ayita faman kiranka baka dagawa,tun jiya
nake danna maka kira kaqi dagawa......gobe ne za'a zauna cacar nan fa......"

"Shut up mato!" Ya dakawa mato din tsawa,don maganarsa a sannan daidai take da yana
buga masa abu me qara a kunne.

"Lafiya uban gidana?,me kuma ya faru?"

"Mato na hadu da 'yar damfara......na hadu da gagarumar barauniyar data yasheni
tas......bama ni ta yasheba tukunna......ta taba dukiyar kamfanin jadda ne!".

Zaro idanu mato din yayi waje yana janye jikinsa baya da sauri kaman
yaga wani abun tsoro tattare da mika'il din

"Anya yau bakasha barasar da kanka baya dauka ba?,kasan maganganun da
kakeyi?,barauniya fa kace,kuma macace?,sannan data tashi dukiyar Muhammed jadda ta
kwashe?" Ya qarasa maganar kaman zaiyi ruku'u. Ba kuma ruku'u din zaiyi ba,kawai
yayi hakanne don ya samu damar ganin fuskar mika'il dake zaune sosai,yanason kuma
samun tabbacin maganar haka take ko kuma akasinta.

"Duk yadda kaji ka sake kuma fada hakanne" Ya fada a galabaice yana tsananta fatan
samun mafita daga wajen mato.

Ga mamakinsa sai yaga mato ya juya yana neman hanyar fita daga dakin. Da
wani irin hanzari mikail ya miqe ya damqo rigarsa yayi qarfin halin jawoshi baya
sannan yasha gabansa

"Ina zakaje kuma?" Kicin kicin yayi da fuska

"Ka dauko bala'in da yafi qarfinka ai me gida,ni kuma bani da wani gatan da zan iya
tareshi,kaga gwara na yiwa kaina qiyamulallaili nasan nayi". Sakinsa mikail yayi
har yana taga taga kaman zai fadi. Cikin fusata da fushi yake duban mato,yayi taku
biyu a gabansa sannan ya tsaya yana sake kallonsa

*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*

PAGE 78


"Kai butulu......na dade da sanin alaqar bariki bata da riba.....kuma
bata wanyewa lafiya qalau.....amma inaso ka sani.....ni mikail baka isa ka gwadamin
wannan halin ba saboda yadda kaci a jikina,komai ka zama ta silata ne.....to ga
hanya nan......kana iya tafiya......amma ka sani,wallahi.....wallahi duk abinda zan
shiga zan bada sunanka da tabbacin tare mukayi komai".

Ji mato din yayi kaman ya debo qarfe ya jibga masa saman kanshi,sai ya
koma ya sulale ya zauna

"Ya zakayimin haka oga?,kasan tun safe naga qishin qishin abun?,ya baza jaridu da
jafafen yada labarai?,amma ban taba tunanin kaine a ciki dumu dumu ba?"

"Mune dai a ciki,kuma zanyi maka haka muddin kaima kayimin hakan". Ya bashi amsa
kai tsaye yana duban tsakiyar idonsa.

Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana yin collapse. Nadama da dana
sanin taba sanin mikail a rayuwarshi tana sauko masa. Shikam ina zai iya tarar case
da Muhammed jadda?,wanne ganganci ne ma zaiyi saken da koda sunansa zai shiga list
na sahun wadanda ake tuhuma.

Shuru yaci gaba da wanzuwa a dakin tamkar dukkaninsu ba xasu sake
magana ba kafin mato ya magantu

"Ita yarinyar wacece ita?,zaifi kyau kabi sawayenta ka bincikota ka damqawa jadda
ita a sauqaqe su tuhumeta". Wani banzan kallo ya watsawa mato

"Inda nasan ita din wace da ta yaya ma zan batawa kaina lokaci ina neman shawarar
butulu irinka?......tun haduwata da yarinyar na karanci tasha banban da sauran
yammata dama mata gaba daya.....tun daga yanayin kyau siffa da kuma jan
ajinta......bata sake shallake tunani ba sai a yau dana karade dukkan guraren da
muka saba haduwa ko na saba ganinta amma na kasa zaqulota,......ta shafe dukkan
wani footprint nata,bani da sauran hanyar da zan iya lalubota".

Shuru mato yayi abun yana tsimashi shima. Duk iya yawan duniyarsa bai
taba cin karo da abun mamaki irin wannan ba.......duk budewar idanunsa da kuma son
duniyarsa baiga gangancin da zai sanyashi tunkarar fada ko jayayya da mutum irin
muhammad jadda ba.....hakan daidai yake da saida rai.....daidai yake kuma da
Rungumar mayunwacin zaki. Amma irin wadannan maquden kudaden kuma ace diya mace ce
ta diba?.

"Me afkuwa ta afku yallabai.......yanzu lokaci ya qure ya kuma matse da zaka tsaya
nemanta da bayyanar da gaskiyarka.....don koda ka samota dinma ka gabatar musu da
ita to ba shakka dole saika rasa aikinka.....na tabbatar zasu sallameka ne". Wannan
maganar ta mato ta sanya gumi tsatstsafowa mika'il. Ya koma baya yana zama sosai
tare da kamo habar rigarsa yana sharce gumin goshinsa.

"Don ubanka mafita nace ka bani bawai ka dinga haskomin makomata ba" Ya fadi da
mugun tsaron ci gaba da jin sautin xai rasa gurbin aiki da kamfanin jadda diamond
rashi na har abada,bayan a nasa mafarkin yana hangoshi ne wataran a kujerar CEO din
ma gaba daya yana juya nasa kamfanin diamond din.

"Mafita kam na samota......amma sai idan ka amince.......zaka juya hankalin kowa
kayi wasa dashi.......ka kuma binne batun kwashe kudin asusu ba tare da kowa ya
fahimta ba".
Kaman an watsa masa ruwan sanyi haka yaji rahama tana sauka a
zuciyarsa,baisan sanda ya kama hannun mato ya riqe qam qam ba abinda bai taba yi ba
tsakaninsu

"Dama za'a samu irin wannan hanyar na kasa yarda da ita mato?,maza
gayamin......gayamin don Allah".

Hannunsa ya zame yana mamakin yadda yau masifa da bala'i suka sanya
ubangidan nasa zama maqasqanci a gabansa.

"Caca......a caca ne kawai zaka ciyo maquden kudaden da zaka iya cike babban gurbin
da zai sauke fushin me jadda daga kaso dari zuwa ashirin". Ido ya zubawa mato
alamun me gama Fahimtarsa ba.

"Nasan baka gane ba ko?,me gida......kana da nasibin da muddin ka zauna teburin
caca saidai ka kwashe badai a kwashe ka ba,tunda kake baka taba zama teburin caca
an cinye ka ba tsahon shekarun daka dauka,saidai ma ka tashi da gwagwabar ribar
dake lunka arziqinka.......wannan zaman da za'ayi a gobe babban zama ne......akwai
manyan gidadawan masu kudin da basu gama wayewa a sabgarba.....basu kaika qwarewa
ba,sun sanya mugayen kudade masu nauyi cikin cacar saboda romon bakan shigowarka
cikinta da nayi musu da yawan kudade masu nauyin gaske.......kudin da kowanne zai
zuba ba qarami bane me gida......kuma ina da tabbacin kaine zakayi nasarar
wawashesu......ka zuba kudade sosai ka saki jiki don ka sarqafo dukkan abinda zasu
zuba.....bana jinka.....nasan da qwarewarka.....na kuma yarda dakai".

"Nima na yarda da kaina" Ya fadi kai tsaye cikin confidence da kuma yarda da cewa
lallai ba shakka waraka tazo. Rungume mato yayi yana jin tsananin farinciki kafin
ya sakeshi yana cewa.

"Muddin muka gama da wannan,na rantse da sarki Allah saina nemo yarinyar
nan......saina nuna mata cewa ita din ba komai bace cikin duniyar bariki,sai na bar
mata tarihi,saina sanyata tayi danasanin zuwanta duniya!!".

Tunda gari ya waye yake kwance kawai lamo,ita bame bacci ba hakanan ita
ba idanunta biyu ba. Su biyu ne a dakin tun bayan wucewar nadra da haneefa
makaranta,tana daga parlor huda na cikin uwar dakin qudundune a bargo da sunan bata
da lafiya ba zata samu daman zuwa makaranta.

Ta shirya hakanne don tana sanya ran sabreen din zata fita ta barta a
dakin kamar jiya,tasha hirar soyayya da hameed dinta,wanda a yanzu duk duniya bata
jin akwai sauti ko muryar da takai tasa dadi da daraja.

Amma ga sabanin mamakinta yadda taga sabreen din kwance yana gaya
matane ba lallai bane ta fita ba yau din. Tayi tsaki cikin bargon yafi a qirga,tayi
juyi daga hagu zuwa dama sau ba adadi. Tana iya ganin yadda wayarta dake qasan filo
keta haske alamun kiran hameed wato naseer ne yake shigowa amma tsoro ya hanata
dagawa.

A hankali a hankali ta dinga jin duk wata juriya tata tana
qarewa,muradinta da burinta kawai shine yadda zata samu taji muryar hameed dinta.
Sannu a hankali ta dinga jin hirarsu ta jiya tana dawowa

_akan sonki bana tsoron kowa,zan kuma iya komai a gaban kowa saboda ke....zan iya
sadaukar da komai a kanki,zan kuma iya rabuwa da kowa,kefa?,zaki iya?,ki gwadamin
wataran_.

Kalaman Hameed kenan ko yaushe a kanta. Muddin zai sadaukar har haka
ita me zaya hanata ta sadaukar?. Tambayar data yiwa kanta kenan,abinda kuma ya cire
sauran dan tsoron dake ranta ta jawo wayar ta daga ta kara a kunnenta.

Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sakar mata kamar qaramin yaro

"Har na fidda rai.....huda kina azabtar dani,kullum kafin na samu jinki sai nasha
baqar wuya?,sai na shafe awanni ina lalubenki?,bayan ni ko agaban waye bana iya
wofantar dake huda?,koda waye a wajen zan ambaceki zan kuma yi waya dake.....me
yasa huda ni bazakimin wannan sadaukarwar ba?". Yadda yayi maganar sai ya bata
tausayi sosai,harma taji tana zargin kanta daqin daga wayar tasa tun dazu

"Allah huda idan aka wayi gari na mutu sonki ne ya kasheni" Duk wata tsiga ta
jikinta sai data zuba......son da yake mata wai da gaske ne har yakai haka?.

"Kina mamaki kuma kina musu ko?,kinason tabbatarwa?" Cike da quruciya da rashin
sanin kan rayuwa ta furta masa

"Eh"

"Nan da kwana uku xan dawo ya kama ranar Monday,zaki yarda na shigo makaranta na
daukeki?.....zan kaiki inda zan nuna miki zallar soyayyata a gareki ki ganta quru
quru.....kin yarda kinaso ki gani tawan?". Sai ta narke wuya zuciyarta na karkata
gason ta gani din. Can qasan ranta kuma fal mamaki,tadai kusa ganin wannan soyayyar
da yaketa faman zuguiguita mata ita......ta kusa ganin soyayyar nan dai da takeji
anata magana a kanta.

"Zan miki tanadi na musamman,zaki gani da idanunki.....daga ranar nasan ba zaki
sake musu shakka ko kokwanto ba". Janta yayi zuwa cikin hirar sosai duk da sama
sama take amsa masa a darare amma hakan bai dameshi ba,sake jan ra'ayinta kawai
yakeyi,yana kuma sake dulmiyata cikin kogin qaunarsa.

Kadan kadan takejin motsi daga dakin,to amma sai kunnuwanta sukafi
tafiya zuwa tsakar gidan gidan nasu. Don ta tabbatar huda bacci takeyi ko sanda ta
fito,ta share wannan maganar tana dauko wayarta ta lalubi number jib.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 79


"Allah dai yaja kwana hajjaju......our young hajiya" Jib din ya fadi cikin
fara'a.

Karamin tsaki taja tana kauda zancan,haka kawai ita batajin komai akan
kudin,bata kuma jin wata walwala. Duk wani tsari da jib din yakeyi mata tana jinsa
ne kawai,don nata lissafin duka ba'a wannan bangaren yake ba.

Uwa uba shi Kansa jib din bataji ya tsarawa kansa komai ba,ita kuma
yanzu su dinne a gabanta da sauran yara marayun nan da take kwana dasu ta kuma
tashi dasu cikin ranta.

"Ka sameni gidan marayun nan,zamu qaraso nida busari" Ta bashi saqon a taqaice

"Okay to ba damuwa.....amma ke me kika warewa kanki?"

"JIB....ajiye maganarnan haka a gefe,kada kabarmu mu jiraka please"
"In sha Allah" Ya fada mamakin halayenta suna sake ninkuwa a ranshi.

Kafin ta ajiye wayar tahau ta daya sim din data saba neman busari,ta
tura masa saqo sannan ta ajiye wayar tana dan furzar da iska daga bakinta gami da
zubawa labulen qofar falon idanu kamar me nazari akan yadda aka sarrafashi.

Kadan kadan ta dinga jin kamar dai motsinne daga dakin da kaman sautin
murya a can qasa. Tun tana basarwa har ta miqe,ta taka a hankali ta soma nufar
dakin.

"Eh" Kalmar da aka fadi qasa qasa ta shiga kunnenta sanda ta yaye labulen dakin.
Hasken daya ratso falon zuwa uwar dakin ya ratsa blanket din da take ciki ya kuma
alamta mata wanzuwar wani a dakin,sai tayi wata mutuwar kwance zuciyarta tana
tsananta bugawa ta latse wayar tana turata tsakanin katifar da bagon gadon. Daqyar
take iya hadiyar yawu saboda tsoro,tun yaushe nema aka shigo bata sani ba,kada dai
ace ta jima a tsaye tana jinta?,wannan tunanin kadai ya sanya jikinta jiqewa da
gumi kamar an watsa mata ruwa.

Hannu ta sanya ta yaye bargon,sai ta runtse idanunta

"Keda waye kike magana?" Sabreen ta jefa mata tambayar tana zube mata idanun nan
nata masu kaifi.

"Magana kikaji yaa sabreen?" Shuru tayi dajin tambayar datai matan,sai ta girgiza
kai alamun aah bayan ta gama qare mata kallo

"Wannan gumin fa?,ko zazzabi kikayi ya sauka?" Ta sake jefa mata tambayar amma
wannan karon da salon son kamo abun farauta

"Eh.....eh nima haka naji" Idanunta ta maida ta lumshesu sannan ta bude. Ta gama
bata hint,ta kuma gama hada dukkan wasu abu da takeso,ta sanyata a ajujuwa kuwa tun
daga sauyawarta zuwa yau,kuma ta fadi a kowanne aji......tana jin sunzo matakin
qarshe ita da ita,sai ta sake mata blanket din,ta juya tana takawa a nutse zuwa
inda take adana kayan wankanta ta diba tana fita a dakin.

Da wani malalacin kallon ta bita har ta gama ficewa,haka kawai taji kaman
akwai wani abu ba daidai ba

"Idan ma akwai.....idanma kuma ta gane aiba wan sabon Allahn kikayi ba" Wannan
tunanin ya bata qwarin gwiwa ta tabe baki,ta maida kanta filo tana jin yadda
zuciyarta ke bugawa sosai,daga bisani kuma ta koma tunanin hirarrakinsu da hameed
kaman yadda ta saba.

Cikin qanqanin lokaci suka isa babban gidan kula da marayu,wanda yana
cikin gidajen da suke karban kaso mafi tsoka daga dukkan abinda ta samu.

A yau din kabakin arziqin data kai musu ya faranta ran kowa. Hakanan
list da tayi na abubuwan da zata aiwatar musun ya sanya kowa kokwanton anya da
gaske take?. A duka shekarunta ina taga adadin wadannan kudaden?. Ayyuka ne da zasu
canza fasalin gidan gaba daya ya canza cimarsu harma karatun yaran gidan. Tsari ne
kuma data dauki sunayen 'yammatan ciki da suka isa aure suke da buqatar tallafin
kayan daki da kayan kitchen harma da suturar fitar biki. A ranar gaba daya gidan a
yamutse yake da tsananin mamakin ayyukan da tace zatayi din. Saidai daga bisani
shigaban gidan ya basu nutsuwa ta hanyar fadin

"Ta iya yiwuwa 'yar wani hamshaqin attajirin ce mu bamu sani ba ta bad da sawu,ko
daga suturar jikinta da fatarta zakasan cewa kaman hakan zai yuwu,kudai godewa
Allah daya turo me dauke mana damuwarmu koda yaushe,gashi a wannan karon bayan
tallafin data saba bayarwa zata mana aikin da mutanen dake da ikon yi masu yawan
gaske suka gaza yi mana......zata mana aikin dana tabbata muddin ya tabbata
matsalolinmu masu yawa zasu kauce".

Ta yita share qwalla me yawa a hanyar komawa gida,yaran suna mata gizo
cikin idanuwanta. Wato maraya a wannan zamanin daidai yake da wani abu maras alfanu
cikin al'umma muddin ba dukiya aka mutu aka bar masa ba?,hankula da idanuwan
al'umma duka sun toshe?,me arziqi shine mutum?,me arziqi shike da amfani?,idan yau
kana da abun hannu kowa qoqarin rabarka yakeyi?,kowa so yake ya hada dangantaka
dakai komai qanqantarta?,kowa so yake ace kuna da alaqa kunsan juna?.

Anya mutane a yau kuwa sunsan iya adadin bala'i da masifar zubar ruwan
hawaye a idanun maraya qwalli daya tak a garesu?,anya suna tunawa da girman
haqqinsa da ma'aiki yayi gargadi da jan kunne akai?. Bibo ta fado mata a rai,saita
dinga juya kai kawai,matar tana daya daga cikin mutanen da zasu azabtar dasu
tsananin azaba inda Allah ya qaddari mutuwa ta dauke ummeensu a sanda suke
dukkaninsu qananu......arrahmanu arraheem ubangiji da baya hadawa bawa abu
biyu......sai ya dauke musu sanyin idaniyarsu a sanda ita nata hankalin da qarfin
ya fara kawowa. Ya sanya mata qarfin zuciya da kuma qarfin halin iya tare musu
tashin hankali da masifa komai girmanta,ya sanya rainonsu da kulawa dasu a hannunta
tun bata wuce itama a raineta ba.

(YAKE BAIWAR ALLAH!....tabbas riqo yana da wahala.....riqo yana da daci yana da
nauyi,amma kisani......DA KI RIQE YARO KI AZABTAR DASHI GWARA KI TUN FARKO KICE BA
ZAKI KARBA RIQON BA yafi miki sauqi da mafita har a wajen Allah muddin kikasan
zuciyarki ba zata iya jure da kiyaye wannan amanar ba.....AMMA WALLAHI
WALLAHI
WALLAHI kikayi kuskure kika karbi riqo don ki burge ko kada a zargeki,to wallahi
idan nace KINA CIKIN MASIFA ma kadan ne.....ba zaki san girman bala'i da kike ciki
ba sai ranar gobe qiyama......hatta ubangiji bayason kuka maraya shi da yayi kowa
yayi komai ya kuma qaddara hukuncin maraici a kansa
IDAN KINSAN akwai maraya yanzu haka da kike banbanta riqonsa dana 'ya'yanki.....to
ki gaggauta yiwa kanki hisabi tun kafin ranar zuwan hisabin na gaske.......idan har
kinsan akwai maraya yanzu haka a hannunki.....to ki gaggauta gyarawa kafin ki barwa
'ya'yanki masifa da bala'in da zaiyita bibiyar rayuwarsu,kiyi qoqari kifi qarfin
wannan tsokar dake qirjinki wadda ake kira da ZUCIYA.....kiyi qoqari kifin qarfin
wannan maqiyin naki wato SHAIDAN.....Allah ya bamu ikon fin qarfin wadannan ababe
guda biyu ameen summa ameen).

"Kaini gidan malam" Ta fadiwa busari a nutse,wanda bai musa ko ya tambayi ba'asi ba
ya karkata akalar motar. Zuciyarsa shima cike take da farinciki,don yana cikin
alherin tashi daga dan adadaita sahu,zuwa mamallakin shago sukutum da guda a babbar
kasuwar kantin kwari nan da sati uku kacal.

Kusan duk wanda ya kwana ya tashi a kamfanin yasan da faruwar komai.
Yayin da sake fitar labarin boyayyar badaqalar data afku qasa da wasu awanni ya
sake sanya mutane da yawa na kamfanin mamaki musamman wadanda basu san komai
ba,basusan kuma abinda ake ciki ba.

Kowa da kansa da kansa ya yiwa hisabi,don shigowar boss Muhammad
kamfanin ya sake sanya kowa shiga taitayinsa. Masu zuba kunnen abinda zai faru da
kalar matakin da zai dauka suka ci gaba da sanyawa,yayin da a nasa bangaren ya
nutsa cikin bincike tare da tattaunawa da taimakon dan uwansa kuma shaqiqinsa
farouq.

Ganawa ce takai tsaye kuma da mutum na farko bayan shigarsa kamfanin
da sukayi da manager din banking da yake mu'amala dashi,wanda suka iso su uku da
biyu cikin nasu ma'aikatan. Hankalinsu kusan yafi na fuad tashi,don sun sani ba
qaramar nasara bace ace kamfani kamar wannan yana da asusu dasu,hakanan
kuma....gagarumar asara da faduwa ce ace a yau ya rufe account dinsa dasu
sanadiyyar wannan.

"Baku da laifi sir......coz kusan sai aka shigar da komai da ake buqata da zai bawa
mutum damar accessing da account din sannan kuka bada damar fitar kudin......inda
kuskuren yake shine......amount din da aka fidda din ya cancanci ace anyi alerting
namu kafin a bada daman fiddashin.....saboda akwai hanyoyin da mukebi wajen fidda
kudade masu nauyi irin haka........kuma kun san da hakan......anyway...sakacin
security team namu yafi na kowa.......sai kuma ma'ajij company da yake number one"
Ya qarashe maganar yana komawa ya zauna sosai yana gyara wuyan suit nashi.

Matsowa sadiq yayi dab dashi a nutse ya rada mishi

"Hamma......mun gaza samun mikail har yanzu mu shaida masa zaman da za'a yi yau
din". Kansa ya gyada

"Kar damu dashi......idan inason ganinsa ko ina ya shiga zan sanya ne a kawomin
shi.......but nafison ya kawo kansa da kansa in a legal way.....ka rabu da nemansa"

"Okay" Ya fadi cikin gamsuwa. Ya yadda da hamman nasa,ya sani ba ordinary mutum
bane tuntuntuni......bayajin a yanzu ko farouq zai gaya masa wayeshi saboda kaf
gidan yafi kowa kasancewa dashi cikin awanni masu yawa. Fara aiki dashi ya sanya
kullum kwanan duniya yake sake shiga ransa. Baisan haka hamman nasa yake da shiga
rai ba sai yanzu......baisan haka kyakkyawar mu'amala take yawo a jininsa ba sai
yanxu da aiki yake hadasu adadin awanni masu yawa.

Hannu ya miqa ya karba file din da suka iso masa dashi na dukka bincike
da nasu bibiyar da sukayi. Kusan wasu guraren abubuwan da suka bincika yazo daidai
da nasa,wani gurin kuma sun kasa accessing information din jibril wanda shi a yanzu
haka yana da komai. Abu daya ya kasa yarda dashi shine......jibril bashi kadai yayi
wannan aikin ba.....dole akwai wani a tare dashi......wanin kuma yana qarfafa
zargin muddin ba mikail bane da kanshi ya dauki duka information din ya miqa musu
da zummar cin amana ba......to na jikin mikail ne wanda yake tare dashi.

Hannu ya bawa manager din sukayi musabaha

"Mr Joshua mamallakin bankin yana miqa jajensa......yanzu haka yana hanyar zuwa
kowanne lokaci,da fatan zaa karbi baquncinsa". Wani abu me kama da murmushi kawai
yayi yadan dage kafadarsa,sukayi sallama dashi ya fice.

Iska me zafi ya fitar a bakinsa,ya miqe yana zare suit din jikinsa na
saman ya ratayeta a muhallin da aka tanada don ratayewar. Ya duqa yana zare
takalmin qafarsa hadi da magana da saddiq

"Awa nawa ya rage mu shiga meeting?"

"Thirty minutes hamma"

"Good......yanzun security team kawai nakeson gani,kayi cancel sauran
staffs......infact ma banason susan da zaman.......ina da buqatar binciken sirri a
kansu don dole mu nemo me fidda mana information......ka gayawa me sunan malam
immediately after meeting inason ganinsa"
*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 80




Please Login or Register in order to submit comment