You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaisawa
da didi.

Dan murmushi didi da tasaki,duk da itama abun yana ranta,bata taba
ganin ya kirayi sabreen din ba duk da tasan zai wahala ta daga wayar a yadda ta
kafe dinnan bataso......bata taba jin ance gashican yazo ba koda ba zata fita ba

"Danku ne fa?,me kike ci na baka na zuba?,ai har sai kun gaji da ganinsa"

"Aiyo to......naga mun aurar amma ba haka mu muka saba gani ba,koda yake sha'ani me
arziqi daban dana talaka" Daga haka ta saki labulen tana wucewa don saqo ne takeson
ta isar ta kuma tabbatar ya kai inda take da muradi.

Sanda didi ke zaune saman kanta tana jefa tambayar kanta,sai ta
mayar da idanunta kawai ta rufe tana cewa

"Ki tambayi kawu" Tana ganin shike da cikakkiyar amsar bada ita ga wulaqantaccen
aure irin wannan. A duniyar auren hadi.....a kuma duniyar auren dole bata taba
ganin kalar nata auren ba......ki sau daya bai taba tako qafarsa unguwarsu bama
bare akai ga isowarsa qofar gidan mahaifinta da zummar nemawa kansa ita kamar yadda
kowanne d'a namiji yakeyi. Sai damunsu akeyi da kawo dukiyar data tabbatar tamkar
magana ce a fakaice ake gaya mata na sun zabi kudi ga kudi nan.......kawu yayi mata
abinda ba wani mahaluqi daya isa yayi mata shi,hakanan ba wanda ya kwatanta yi mata
hakan sai shi. A kullum kalmar UBA da Allah yabashi wannan take dubawa take dauke
masa qafa da idanu akan wasu abubuwan,banda haka bata tunanin akwai wanda zai mata
hakan ta lamunta.



ð˜žð™Ąð™ð™–ð™Ÿð™ž 𝙝𝙖ð™Ēð™Ŋ𝙖 𝙠𝙞𝙗𝙞ð™Ū𝙖 ð™Īð™Ąð™™ 𝙧𝙚ð™Ļ𝙞𝙙𝙚ð™Ģ𝙘𝙚


"Alhamdulillah" Ta samu kanta da furtawa tana shafa hannunta saman
fuskarta bayan ta kammala sallar ishai a ranar. Rana ce data zama ta hidima sosai a
garesu kai kace bawai lefe kadai aka kai ba......tamkar bikin ake gudanarwa a
ranar. Gefe guda kuma cikin hidimar tashi suke daga gidan,akwai 'yan uwa sosai da
abokan arziqi da kowa ke zaban furniture din da yakeso a sassan nata.

Har qasan ranta takejin farinciki idan ta tuna kwanaki bakwai kacal
suka rage muhammad dinta ya zama magidanci kamar yadda kullum take da mafarkin
wannan ranar. Abu daya ne ya tsaye.mata a rai,yake sake sanyata a shakka da
kokwanto duk kuwa da abba hamza yayi qoqarin nusasheta tare da yi mata bayanin ta
fidda abun a ranta wato batun mariya.

Komai da mariya akeyi,ayyukanta duka suna gwada yadda take dama dama da
auren nan. Ta yiwa mariya farin sani,ba sanin jiya ko yau ba kawai......banza bata
kai zomo kasuwa,hakana nan mariyar ungulu ce bata jewar banza......ta kasa aminta
da haka siddan mariya keson abun nan ba wata adawa kaman yadda ta saba.....uwa uba
kuma neman yazo daidai dana fuad din. A haka dai take kallon abubuwa amma kuma
tanata qoqarin gamsar da kanta all is well kaman yadda abba ya shawarceta.

Sallamar musaddiq da farouq bayan sunyi knocking ta basu izinin
shigowa su saka sanyata gyara zamanta yadda qafafunta zasu miqe sosai. Kaman ko
yaushe tana dubansu bisa alfaharin samun 'ya'ya irinsu suka qaraso.

"Larai keson magana dake akan dakincan,tana tambaya shima zaa fitar da kayan
ciki?,nace mata dai su kwashe kawai" Farouq ya fada yana shafar sumar kansa hadi da
zama gefan annin musaddiq kuma ya yiwa kansa mazauni saitin qafafunta. Haka suke
duk sanda suka sameta zaune koda su hudunne sai su sakata gaba a tsakiya kamar wasu
yayayyu ko masu shan maama,sa. Basa ganin girmansu gaba dayansu indai suna gabanta
ne.

"Eh yayi hakan....tashin nan ina jinsa kamar wasa wallahi" Anni ta fada tana
alhinin bari muhallin da suka dauki shekaru a cikinsa,duk da cewa bawai sun barshi
kenan ba.....nan dinma zaa sake zuba sabbin furniture da komai da komai cikin satin
nan,idan sun gaji da waccan unguwar sai ta taho nan ta zauna......saidai ko kusa ko
alama wannan gidan bai isa ya hada kafada da wannan din ba.

"Lokaci anni.....zakiso wancan gidan fiye da wannan fa" Kai ta kada

"Kayya.....ku yara kune qyale qyalen rayuwa ke mugu gardi.....faruqu......inason
magana da surukata,ko zaka kiramin ita?" Ta tambaya farouq.

Zamansa ya gyara ya ciro wayarsa yana budeta

"Banajin ina da number surukar nan taki anni...." Ya fada a ransa yana tunanin fuad
dinma baida ita,bayason kuma su fahimci hakan

"Amma bari nasa a turo sai na kira miki".

Kawu kawai ya kira kanshi tsaye ya nema number daga wajensa.

ð™Žð˜žð˜―ð™ð™€ð™€ð™‰ð™‰


Jujjuya wayar kawai takeyi a hannunta tana cije lips dinta zuciyarta
na sake quntata. Tunda suka gama waya da matar da har yanzu ta kasa yarda wai ita
din mahaifiya ce ga wancan dan rainin wayon ma'abocin girman kan mamaki yake sake
cikata. Wayar mintuna talatin amma ta sanyata zaman minti ashirin tana tariyar
kowacce magana data fita daga bakinta

"Duk abinda kikaga baiyi ba kiyi magana.....duk kudin da kike buqata ki nemesa a
wajena zaki sameshi........burina guda daya tal shine ki cikamin burina da kuma
manufar da ta sanya na nema miki auren d'ana.......wannan shi zai baki damar zama
cikin jerin sahun masu kudi masu arziqi.....kuma shine zai zama kariya daga rayuwar
'yan uwanki.....domin har yanzu suna a hannun mu duk da kuwa mun sake miki su".

Kai ta jinjina tana sake cije lebe.....har yanxu matar bata santa
ba......batasan wacece Sabrina da iya adadin abinda zata iya aikatawa ba......inda
ace ta sanya harsashin wasan tsakanin ita da ita ne data nuna mata tata zallar
qwarewar......to amma inaaaa......bisa rashin sa'a ta sanyo da rayukan da suka zama
sune K'ARFINTA kuma sune RAUNINTA dole tayi komai bisa lura da kuma tsari.

Bataji nauyin gaya mata kai tsaye ba.....ta shaida mata cewar

"Bani buqatar ku nunawa duniya ni.....duk wani events bani da sha'awar
zuwa.....koda kin tsara hakan dani ki cireni a ciki" Amsar data bawa maamah sanda
ta bata daman shirya duk kalar events din da take da buri ko mafarkin gudanarwa
koda kuwa wasu qasashen take so ayi jigilar qawayenta don gudanar da komai a can.
Ta bude mata komai ne don a nata karatun.....gogaggiyar mace kaman sabreen da tasan
dadin kudi da bariki.....tabbas zataso cikin manyan burika dama mafarkanta tayi
kalar bikin daya zarce na kowacce yarinya dake tashe ko kuma take jin kanta ko
ubanta wani ne.

"Ma sha Allah.....alhamdulillah,to Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa....gata
bari na bata" Muryar didi kenan data shigo dakin riqe da wayarta

"Ga surukarki.......karbi mana" Didi ta fada tana miqawa sabreen wayar. Kanta ya
daure,wacce surukar tata kuma?,wata dabance bayan wadda ta gama tumasanci yanzu ko
kuwa?. Yadda didi ta tsareta da ido......ba wani sauran abinda zatayi saita saka
hannu ta karba din.

"Assalamu alaikum warahmatullah" Anni tayi cikakkiyar sallamar da wannan muryar
tata data cika da nutsuwa da dattako,muryar data tsarga tun daga zuciyar sabreen
din ta sace wani nauyi da fushi daketa kai kawo a qirjinta cikin mintuna qalilan ba
tare data ankara ba

"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Ta samu kanta da amsawa da wata nutsuwa data
sameta ba tare da tasan daga ina bane.

"Allah yasa zaki iya shaida wannan mamar taku,ina fatan ya gaya miki komai a
kaina?" Anni tai maganar da sautin murmushi a muryarta. Dif tayi don batasan me
zatace mata ba.....me zai gaya mata mutumin da ko fuskarsa bata gama tantancewa ba
bare duk wani abu daya shafeshi.

A taqaice anni ta yiwa sabreen bayanin matsayinta. Bayanin daya dinga
zillo saman zuciyar sabreen yana sake rikita mata lissafi,iyayensa biyu?,masu
mabanbantan dabi'u da halaye,wadannan sune kawai abinda tafi riqewa tanason kuma
tantancewa amma kawo yanzu kanta ya tsuke gaba daya.

"Ki daukeni tamkar mahaifiyarki sabreen.......duk wani abu da uwa kewa 'yarta zaki
sameshi a tare dani in sha Allah". Kalmar data daki qirjinta ta kuma saukar da wani
abu me sanyi saman ranta

"Suna da banbani" Taji ana gaya mata daga can saman kanta bayan ta sauke wayar da
suka gama da ita. Tana tariyar maganganun data gaya mata cike da harshe me hikima
da fasaha.....sam babu hadi ko a iya kalamai tsakaninta da waccan dake iqirarin ita
ta haifesa

"Zanso nasan wacece uwar ta gaske" Ta fada qasa qasa tana duban didi dake shigowa.

"Saiki kintsa kanki.....don tace zatayi aiken me gyaran jiki da zasu fara aikinsu
daga gobe har zuwa ranar da zaa daura aure.......amma sabreen" Didi ta fada tana
neman wajen zama gefan sabreen din ba tare data damu da damuwar da batun gyaran
jikinta ya saukar mata ba.

"Mamarsa nada kirki har haka?.....me yake tsananta damuwarki......duk wani motsi
nasu yana alamta su din mutanen kirki ne.......wanda dukiyarsu bata rufe musu idanu
ba.....don Allah ki kwantar da hankalinki......tabbas ina kyautata musu zato"

"Ba zaki gane ba didi,abinda kike gani a zahiri ba shine a badini ba.......to waima
wanna jikin zaa gyara?" Tayi dukka maganar ne idanunta a kulle,amma wannan ta
qarshen ta ware idanunta ne akan didin.

Kallonta didin takeyi tana jin kamar sabreen din bayan matsalar
miskilanci da yake damunta harda matsalar jinnu.

"Wanne jikin kike dashi bayan wannan nakin?,ko kinaso kiyi ma dattijuwar matar me
tsananin karamci gardama?" Ido ta tsurawa didi tana jin kamar fa bai kamata tace
mata bataso ba ko?,to amma ai sam gyara jiki ma baihau ba a wannan bigiren da take
kai ita,don haka ta mayar da idanunta ta rufe tana motsa labbanta

"Da zaiyiwu shine abunda nafiso ta janyemin". Didin ta jima a zaune tana kallonta
mamaki yana sake kamata,sai data gaji don kanta kawai ta miqe tana cewa

"Allah ya kyauta" Ta fice a dakin.

"Anni da suruka.......Muryar nan kamar na santa anni" Musaddiq ya fada yana
kallonta. Sai a sannan ta iya dauke kanta daga fuskar wayar kamar sabreen dince a
gabanta,batasan me yasa ta jarabtu dason yarinyar da bata taba ganin fuskarta ba
hakanan

"Ba mamaki ka taba rakiyar zance a boye ko jinsu suna waya da hamman naka" Dariya
ta subuce masa

"Anni wannan soyayyar waye yasan sanda aka qullata?,banda ansan gidan su da sai
nace mijin aljana ya bishi da gaske aljanar xaya aura"

"Ungo nan.....wato wannan dan kaniyar yayan naka ya koya maka ko?,maza ka fadi
yaji,idan shi yasha a hannunsa kaidai kasan sauran"

"Tuba nake" Ya fada yana rufe bakinsa da hannunsa yana qoqarin boye dariyarsa.

********Tana kukan zuci qwarai da gaske wanda ke tattare da zargen abubuwa masu
yawa data tanadi tunkarar kowa da komai......amma hakan bai hana zuwan me gyaran
jikin da take aikinta da wata irin qwarewa tamkar zata sauya fatar jikin ta ta
ainihi da wata ta daban ba.

Komai ta kawo idanu ta xuba masa kamar dai komai nata ya daina
aiki.....saidai fa wannan kwanyar......wannan zuciyar suna nan suna aikinsu daidai.


auren da zai zamewa rayuwarsu ð™ˆð˜žð˜―ð™ð˜ŋ𝙄n tafiya bisa wata turba da basu taba kawowa
A daidai sanda komai yake tafiya,shirye shirye suna nisa,kwanakin qulla

zata bude musu......a wannan lokacin shirye shiryen maamah sukayi nisa itama.

Ta narka kudaden da batasan adadinsu ba wajen bokanta.....wanda ta
saida tsaffin kadararrta ta narkasu zuwa kudin da zasu isheta aiwatar da komai.

Kowacce rana da gari zai waye,yana waye mata ne da tsananin farincikin
ganin kusantuwar cikar burinta........sanin wacece yarinyar wacece SABREEN adan
gamayyarsu ta qididdigaggun lokuta ya sanya ta gabatarwa da boka SUNANTA don tana
buqatar aiki a kanta na musamman.

𝙏𝙊𝙧ð™Ķ𝙖ð™Ļ𝙝𝙞......𝙞𝙙𝙖ð™Ģ 𝙠𝙞ð™Ģ𝙖 ð™Đ𝙊ð™Ģ𝙖ð™Ģ𝙞 𝙝𝙖ð™Ģ𝙜𝙚 𝙠ð™Ī 𝙝𝙖ð™Ļ𝙖𝙝𝙚ð™Ģ 𝙖𝙗𝙞ð™Ģ𝙙𝙖 ð™Ŋ𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙊 ð™Ĩ𝙖𝙧ð™Đ
2 ð™Ģ𝙖 ð™Ąð™–ð™—ð™–ð™§ð™žð™Ģ ð™Ģ𝙖ð™Ģ ð™Đð™Ī 𝙠𝙞 𝙜𝙖𝙜𝙜𝙖𝙎𝙖𝙧 𝙖𝙟𝙞ð™Ū𝙚 𝙝𝙖ð™Ļ𝙖ð™Ļ𝙝𝙚ð™Ģ𝙠𝙞.....𝙙ð™Īð™Ģ 𝙗𝙖 ð™Ąð™–ð™Ąð™Ąð™–ð™ž 𝙗𝙖ð™Ģ𝙚
𝙘 𝙖ð™Ģ ð™Ē𝙊𝙠 𝙖 ð™Ģ𝙊𝙛 𝙖 😁😄

𝙄𝙙𝙖ð™Ģ 𝙗𝙖𝙠𝙞 ð™Ļ𝙖ð™Ē𝙊 𝙠𝙖𝙧𝙖ð™Ģð™Đ𝙖 ð™Ĩ𝙖𝙧ð™Đ ð™Īð™Ģ𝙚 𝙗𝙖 𝙠𝙞ð™Ū𝙞 𝙝𝙖ð™Ģð™Ŋ𝙖𝙧𝙞ð™Ģ 𝙠𝙖ð™Ē𝙖ð™Ļ𝙝𝙞 𝙠𝙞
𝙗𝙞𝙗𝙞ð™Ū𝙚ð™Ļ𝙝𝙞 𝙙𝙖 𝙠ð™Ū𝙖𝙊......𝙙ð™Īð™Ģ 𝙜𝙊ð™Ģ𝙙𝙖𝙧𝙞ð™Ģ ð™Ąð™–ð™—ð™–ð™§ð™žð™Ģ ð™Ū𝙖ð™Ģ𝙖 𝙖 𝙜𝙖𝙗𝙖

𝙕𝙖ð™Ŋð™Ŋ𝙖𝙛𝙖ð™Ģ ð™Đ𝙊𝙜𝙜𝙊
𝙈𝙖𝙠𝙞𝙧𝙘𝙞
ð˜ŋ𝙖 𝙎𝙖ð™Đ𝙖 𝙞𝙧𝙞ð™Ģ 𝙗𝙖𝙝𝙖𝙜𝙊𝙎𝙖 𝙠𝙊ð™Ē𝙖 𝙗𝙞𝙧𝙠𝙞ð™Đ𝙖𝙘𝙘𝙞ð™Ū𝙖𝙧 ð™Ļð™Īð™Ū𝙖ð™Ūð™Ū𝙖
𝘞𝙠𝙎𝙖𝙞 ð™Ąð™–ð™Ļð™Đ ð™Ĩ𝙖𝙜𝙚 𝙙𝙖 ð™Ģ𝙖𝙠𝙚ð™Ļð™Ī ð™Ģ𝙖 ð™Ļ𝙖𝙠𝙖𝙧 ð™Ē𝙊𝙠𝙊 𝙎𝙖ð™Ģ𝙙𝙖 ð™Ŋ𝙖𝙞 𝙭𝙖ð™Ē𝙖 ð™Ē𝙊𝙧𝙛𝙞 𝙜𝙖
ð™Ąð™–ð™—ð™–ð™§ð™žð™Ģ
𝙏ð™Ī 𝙖ð™Ēð™Ē𝙖 𝙞𝙙𝙖ð™Ģ 𝙙𝙖ð™Ē𝙖 𝙗𝙖ð™Đ𝙖 𝙗𝙖ð™Ģ𝙞 𝙙𝙖ð™Ē𝙖 𝙗𝙖 ð™Ŋ𝙖ð™Ē𝙊 𝙝𝙖𝙙𝙚 𝙗𝙖ð™Ū𝙖ð™Ģ ð™Ļð™–ð™Ąð™Ąð™–ð™
ð˜ŋ𝙊𝙠 𝙙𝙖 ð™Ŋ𝙖ð™Ģ ð™Ķð™Īð™Ķ𝙖𝙧ð™Đ𝙖 ð™Ģ𝙖 𝙝𝙖𝙙𝙖 ð™Ē𝙊𝙠𝙊 ð™Ļ𝙝𝙞 𝙞ð™Ģ ð™Ļ𝙝𝙖 ð˜žð™Ąð™Ąð™–ð™,𝙙ð™Īð™Ģ ð™Ŋ𝙖𝙞 ð™Ŋ𝙖ð™Ē𝙚
ð™Ē𝙊𝙠𝙊 𝙈𝘞𝙉𝙐𝙉𝙄𝙔𝘞.

𝙃𝙐𝙂𝙐𝙈𝘞𝙉𝙆𝙐 ð˜ū𝙀.




𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2

ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ

𝙋𝘞𝙂𝙀 1



𝘞ð™Ē𝙗𝙞ð™Đ𝙞ð™Īð™Ģ & ð™Ļ𝙊𝙘𝙘𝙚ð™Ļð™Ļ

𝙈𝙊𝙝𝙖ð™Ēð™Ē𝙖𝙙 𝙛𝙊'𝙖𝙙 𝙟𝙖𝙙𝙙𝙖

"Hustle until you no longer need to introduce yourself,push your self because no
one else is going to do it for you". Kalamansa na qarshe kenan da tarin mayan
attajiran da sukayi meeting na qarshe dasu wanda keson saka share dinsu cikin sabon
kamfanin da kwanaki bakwai suka rage masa ya budeshi. Kalamai ne da suka dauki
hankulan mutanen dake wajen,wanda dasu aka kammala zaman.

Sanda yake sallama dash fiye da rabin hankalinsa yana kan wayarsa da
tun dazun ya lura tana haske. Sai da gurin ya rage saura shi daya da hudu daga
cikin guard dinsa da wannan karon dasu yayi tafiyar wadanda ke nesa da inda yake,ya
miqa hannu a nutse yana jawo wayar gami da fesar da iska me dumi daga bakinsa.
Cikin kowanne motsi yana jin farinciki na yadda al'amuran bude kamfanin ke gudana
da dukkan wani haske qyalli da kuma alamu na nasara,bai taba qwallafa rai akan wani
abu kaman haka ba,baisan me yasa dukka tunaninsa da hankalinsa suka raja'a wajen
son ganin cikar wannan mafarkin nasa ba. Tunda yazo samu cikakken zama na awa biyu
cur ba,saidai idan dare yayi ya wafci wasu awanni ya tilastawa kansa kwanciya ya
huta. Kowanne minti idan ya shude da amfaninsa a wajensa,ko baya din dama shi mutum
ne me girmama lokaci tare da bashi muhimmanci qwarai.

Sunan farouq kawai daya gani ya sakashi gyara zama yana furta

"Ya salam" Qasa qasa fuskarsa nason fidda wannan sihirtaccen murmushin nasa da ba
kasafai ake samun dacen ganinsa ba. Wani sirri ne kwance cikin murmushinsa dake
qara masa haiba da kwarjini da fitar asalin kyan da ubangiji ya huwace masa. Yasan
zayasha qorafi ne kawai wajen farouq din......don yace masa zai kirashi har baisan
adadi ba......hakanan bazai ma iya tuna awar qarshe da sukayi waya ba.

"Hala baka da wani abu me muhimmanci cikin rayuwarka sama da business dinka?"
Kalmar da farouq ya fara jera masa kenan. Boyayyen murmushi ya saki yana daga
dogayen qafafunsa ya aza saman dunqulallen table din gabansa me azabar kyau. Wani
irin shaquwa da fahimtar juna ce tsakaninsu dake sanyasu iya fahimtar mode din juna
koda basa kallon fuskokin juna. Yasan zaiji fiye da haka ma a bakin farouq din,don
muryarsa a dake take da alama har kan fuskarsa akwai alamu na qosawa

"Idan ka cire ku family na.......tabbas ba abinda ya fishi muhimmanci cikin duka
kaf rayuwata".

"Aurenka da yarinyar su a wanne muhalli ka sakasu?....." Ya sake masa tambayar
kansa tsaye cikin salo na kaiwa maqura da son masa titsiye.

"Aure?....yarinya?" Ya maimaita maganar har ga Allah cikin son neman qarin haske.

"Eheeennn" Farouq ya fada a taqaice,cikin ransa yana jin rainin hankalin jadda yana
neman fin qarfin tunaninsa muddin ya gaya masa ya manta da lamarin auren dake
gabansa.

"Mmtsewww......au" Fuad ya furta wani siririn murmushi yana sake qwace masa. Sai a
yanzun kwanyar tayo masa tariyar karatun baya na abinda ya baro a nigeria. Kusan
gaba daya sabgar ta shafe daga tunaninsa,abinda ya sanya a gaba ya mamaye tunanin
komai daga kansa.

"Am sorry......kasan halin......"

"......halin mijin aljana.......zata sakashi ya aikata fiye da haka ma,saidai
alhmdlh.....duk abinta a wannan karon munci qarfinta,kuma in sha Allah dan uwana
bazai mutu babu aure ba". Dariya sosai ta qwace ma fu'ad din ganin yadda farouq din
ke maganar very serious,abinda ya jima baiyi ba,ya rasa abinda yasa suka damu da
auren nan......ya fuskanci gaba dayansu murna suke dashi.....ya karanci dukkaninsu
sun daukeshi serious kuma da gaske suke lamuran baki daya.....ciki harda MAAMAH duk
da akwai qatotuwar ayar tambaya a kanta......don ya sani,koda yaushe ita ungulu
bata jewar banza.

"Ka duba email dinka na sauke maka saqo......ka duba urgently"

"Alright" Ya amsa masa suna katse wayar dukansu.

Yasan tsaf xaya iya mancewa idan bai duba saqon yanzu ba kaman yadda
farouq ya buqata. Don haka kanshi tsaye ya bude email dinsa. Baibi takan sabbin
saqonni da ya fahimta kaman akwaisu ba,kanshi tsaye ya bude saqon farouq din.

Daya bayan daya yake bin hotunan daya turo da kallo ba don yana fahimta
can can ba. Hotuna ne na style readymade na kayan maza masu azabar kyau da aji da
wani fitaccen kamfanin fidda readymade suturu ke samarwa. Company ne da sanya
suturar data fits daga cikinsa sai wane da wane......sai mutanen da suka amsa sunan
shegu ne su ta fannin kudi da dukiya.

A idanu kayan sunyi kyau,saidai shi baisan me zaiyi dasu ba,don haka
ya jawo daya wayar tashi ba tare daya dauke dubansa daga kan hotunan kayan ba ya
dannawa farouq din kira.

"Am coming" Abinda yaji farouq din ya fara fadi kenan da alama yana magana da wasu
ne daga gefe

"Have you seen it?" Idanunsa ya lumshe kadan sannan ya budesu

"Yes I have.....but bansan me zanyi dasu ba......hala ka fara preparation na bude
garment company ne?". Wani qululun takaici ya tsayewa farouq a wuya,seriously
mutumin nan da gasken gaske yake ya fara mantawa da cewa aure zaiyi. Duka ya sakar
masa ragamar komai a hannunsa ba tare da damuwa ko tambayar ya ake ciki ba ko meke
faruwa ba.

"Na rantse da Allah sa'arka daya baka kusa dani......shin wai ka manta yarinyar
mutane da zaka aura wadda ka kaiwa sadaki?,in all likelihood ka samu memory
formation right?" . Wannan karon ma saida sautin dariyarsa ya isa har kunnen farouq
''Calmdown mana dude......abun yayi zafi ne har haka?"

"Yama fi haka zafi" Ya fada yana jin ya tuqewa halin fu'ad din.

"To am sorry......amma dai ka sani......ina da abubuwa masu muhimmanci da yawa a
gabana.....kai din kuma wakili nane a ko ina......duk abinda ya dace ka zartar ka
zartar....na baka wuqa da nama" Ya fada calmly,don bayason ya sake tunzura farouq
din,tunda yana ganin yana iya bakin qoqarinsa a abinda shi a nasa ganin baikai
muhimmanci da suke bashi ba. Dan shurun da farouq din yayi da yadda ya sauke
numfashi ya tabbatar masa fushinsa ya sauka,dama ko can basa wani dogon fushi da
juna,da farouq ya zazzage abinda ke cikinsa shikenan,shine dama me yawan kauda
kai.....zaka jima kana masa abu amma miskilancinsa bai bari ya nuna maka har kasan
kana masa ba daidai ba,har sai sanda ya gama taraka tukunna.

"Kayi magana dasu abdulghafar......for now ya kamata su sassauta tsaronsu akan
yarinyar"

"For what reason?" Fu'ad ya maida masa kanshi tsaye yana gyara zamansa sosai saman
lallausar kujerar da yake zaune akai.

"Ina ganin kaman ya kamata ta sake.....duk da dama dole ka bata security da
guard,ko don yanayin halin tsaro da qasar ke ciki,sannan zuwa yanzu ta zama part of
us......wanda duk xai d'amfara da sunanmu dole a bashi tsaro"

"Forget about it farouq......she's gonna be able to do what you....." Sai kuma ya
fasa qarasawa yana jan siririn tsaki. Shi sam sam koda sau daya bai taba jin wani
abu da yayi kama da yarda ko gasgata yarinyar ba.....akwai abubuwa da yawa da uake
suspecting a kanta,wanda ya sake qaruwa tun daga lokacin data bayyanar masa a
mazaunin ZABIN MAAMAH.

"Do you have concern about her actions?" Farouq ya tambayeshi yana tattara masa
hankalinsa.

"Manta kawai......mu ajiye wannan,baka tambayeni akan komai ba dude?". Yayi maganar
calmly kaman zancan business din yafi bashi peace akan batun auren.

"Akan komai?,akan business dinka?,wannan shine kadai damuwarka?"

"Wani abu daban daya kamata na damu dashi sama da haka?". Numfashi sosai farouq
yaja,yana tsoron yadda fu'ad gaba daya baya bawa harkar nan muhimmanci,yana tsoron
faruwar wani abu......careless din yayi yawa har haka,yana jin kamar ya kashe wayar
kawai,to amma ya sani wannan shine abu na qarshe da zaiwa fu'ad ya bata masa rai,ya
tsani a kashe masa waya sam sam.

Yadda yake masa bayanin nasarorin da sauran abinda ya rage ya sake bashi
tabbacin business dinsa shine gaba da komai. Sunyi magana har ta kusan awa guda
kafin su yanke sadarwar dake tsakaninsu.

Sanda yake qoqarin minimizing email din idanunsa suka sauka kan wani
sabon adreshin email din dake dauke da sabbin saqonni guda uku,kamar zai share ya
wuce sai baiyi hakan ba,ya danna ya budeshi ya fara bin saqonni da kallo.

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2

ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ
𝙋𝘞𝙂𝙀 2


Kallon farko zaka fahimci ya bada dukka hankalinsa akan abinda yake ganin
gilmawarsa cikin wayar tasa. Saqonni ne kusan guda uku,kala daban daban,saidai kuma
kowanne saqo daya yakeson isar masa.

_mr muhammad jadda,You hereby warned to stop all activities related to lunching
your company_ saqon farko kenan.

A nutse ya sauke idonsa zuwa ga email na biyu

_Not heeding this warning may put your personal and professional assets at risk_ .
Sake matsawa yayi zuwa saqo na uku shima still dai kakkaifan jan kunne ne zalla a
cikinsa.

_Ignoring this warning may lead to financial losses and reputational damage_ still
dai qasansa shima wani saqonne

_Proceed with caution,as this may have unintended consequences_.

Tsam yayi da ransa,yana sake bin saqonnin daki daki yana bitarsu.
Wannan wanne irin barazana ce haka me girma?,daga wanne sashe ta bullo?,su waye
keda alhakin aiwatar da hakan?.

Ya jima da sani......ba sanin jiya ko kuma yau ba.....sana'arshi sana'a
ce dake dauke da tarin hamayya gogayya da kuma abokan adawa na sarari dana
boye,wani irin matsayi ne da Allah ya bashi wanda bai taba tunanin samuwarsa a
qananun shekaru irin nashi ba. Akwai tarin mutanen da suka fishi jimawa cikin
harkar.....saidai har yanzu basu samu irin nasibin daya samu ba.

Gyara zamansa ya sakeyi da kyau yana furzar da iska daga bakinsa. Ya
sani,zai iya bincike akan ainihin adreshin,saidai kuma yasan zai wahala ya iya
reaching komai akai koda yaso samun haka. Beside ma,isn't the first time daya fara
samun ire iren wadannan saqonnin,wanda daga qarshe yake cimma daga wanne waje
suke?. Ba abinda ya taba girgizashi ko ya daga masa hankali kwata kwata,amma kuma
hakanan yaji wannan saqon ya tsaye masa a rai. Bai sani ba.....ko don saqon yazo
masa ne a daidai sanda yake da burin aiwatar da abinda ya qwallafawa ransa na cikar
burinsa?.

Yadda yake a tsaye a siffa da zati me taba zuciya,haka zuciyarsa take a
tsaye. Ba komai ke bashi tsoro ko firgitashi ko sanyashi yaja baya akan abinda ya
fuskanta ya kuma qudira zai aiwatar ba.....don haka wannan saqon ma sai ya sanyashi
cikin sahun sauran saqonni marasa muhimmanci,wadanda ba komai bane a ciki face
zallar barazana maras muhimmanci a wajensa.

"Hasbiyallahu wa ni'imal wakil,hasbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wa
huwa rabbul arshil azeem" Ya furta a nutse,take taji zuciyarsa tana sake samun
nutsuwa da aminci.

Komai ya tattare yana duba lokaci,cikin jikinsa yake jin ya gaji,yana
buqatar cikakken hutu kafin gobe,so samu yabar qasar nan da kwanaki biyar,to amma
ya fahimci zai wahala dama ta bashi hakan.

Sanda suke takawa da guard dinsa zuwa mazaunin motocinsa guda biyu
kira ya shigo wayarsa. A gajiye ya zura hannunsa a side pocket dinsa ya zaluqota.
Taku biyu baya sukayi dukkaninsu,wanda wannan kuma sabonsu ne,don basu tsaiwa a
waje muddin zai amsa waya,saidai idan shine ya buqaci hakan.
Sosai ya zubawa sunan ido yana kallonsa,yayin da zuciyarsa ta cika da
wasi wasi da saqe saqen abinda kunnuwansa zasu iya jiye masa daga bakinta. Yaci
gaba da irga bugawar da wayar keyi,wanda yake jinsa kamar daidai da bugawar
numfashinsa. Ko a tarihi,ko kuma a labari yana kyautata zaton shi din yana cikin
mutane sahun farko da idan labarinsu zai fita a kundin littafin al'ajabi zai ja
hankalin mutane da dama. Kiran uwa na daya daga cikin kiran dake sanya dukkanin
yaro alfahari.......kiran uwa na daga cikin kiran da kowanne yaro ke fatan gani a
kowacce rana.....kiran uwa kira ne dake iya juya zuciyar kowanne yaro daga
baqinciki zuwa farinciki.....amma banda su......banda tasu mahaifiyar......banda
kuma nasu kiran wanda ba komai a cikinsa face zallar ko kwanto da didibniya
tsakanin lalubo alkhairi ko sharrinsa.

Yana daga cikin motor qafafunsa suna waje ya zauna,yana qoqarin lalubo
nutsuwarsa da yakan rasa a duk sanda kiranta ya riskeshi ya daga

Please Login or Register in order to submit comment