You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sabodashi shi kadai.

Hannunsa ya sanya ya riqo qugunta bayan ya fiddota daga bathtub din.
Idanunta yake kalla sosai wadanda suka rine saboda azabar kuka. Taqi kallonsa ta
kuma sanya duka hannuwanta biyu tana turashi baya,amma ko motsi baiyi ba bare tasa
ran zai matsa. Yadda takejin dumin fitar numfashinsa a rarrabe yana sake dasa mata
matsanancin tsoronsa,shigen wannan yanayin taji daga gareshi dazu,a yanzun idan
yace zai maimaita abinda yayi dazun ta tabbatar saidai ta taqaitawa kanta wahala
kawai tayi sallama da duniya......ita kadai tasan abinda takeji,ita kadai tasan
radadin da takeji yana ratsata a duk wani motsi da zatayi.

"Sabrrrrr....." Ya fada da sautin dake kama da rad'a,wani irin narkakken sauti dake
da amo na can qasan maqoshi,idanunsa cike fal da wata irin mahaukaciyar soyayya da
baiyi zaton cikin zuciyar tasa akwai wani space daya ragewa wata halitta ba.

Kanta ta dauke gefe,maganganu takeson gasa masa amma tana jin idan ta
tsaya ta maida masa koda kalma daya ma yana da wannan darajar ashe?.

"Sabreeennn" Wannan karon ya kira sunanta full da wani irin sassanyan kuma
kwantaccen sauti. Idonta ta lumshe tana mamakin jin sunan yau radam saman
bakinsa,kiran sunansa a bakinsa daban yake da yadda kowa ke kiranta,kaman yadda
komai nashi yake daban haka furucin sunanta a bakinsa.....amma kuma zuciyarta saita
ture hakan,haushinsa ya taso ya maye gurbin wannan.

"I know.....nayi abubuwa masu yawa......na bata miki rai da yawa......na gaya miki
maganganu masu yawa......i hurt you.....i really hurt you even...." Sai ya kasa
qarasawa saboda yadda zuciyarsa take rauni.

"Na bata miki da yawa.....na sani,but dukan abinda nayi shine akan hujja da
evidence da binciken da nayi wanda yazo da negative reviews......sabrrrr" Ya sake
kiranta a karo na uku yana sake zube qwayoyin idanunsa dake cike da shauqi a
kanta,yana jin kamar ya dauketa ya bude qirjinsa ya boyeta,yana jin kamar ya
hadiyeta ya huta da abinda yakeji qasan zuciyarsa.

Ganin da gaske ba zata kalleshi ba sai ya sanya hannu qasan habarta
yana juyo da fuskarta. A zafafe ta qwace tana hadiye kukan daya taso mata,ba abinda
take muradi a yanzun irin ya sake mata qugunta tayi nesa dashi,ya gama kalle komai
da komai nata.....wannan laifin nasa batasan yadda zata gogeshi ba.

Sake kamo fuskar yayi ta qwace,sai kawo ya jawota cikin jikinsa ya
mata wata kyakkyawar runguma. A karo na biyu fatar jikinsu ta sake haduwa guri
daya,wani qaton numfashi ya qwace mata,kaman yadda qaramin yaron da yasha kuka kan
saki ajiyar zuciya sanda ya samu kyakkyawar runguma da lallashi daga wajen mamansa.

"My heartfelt apologies" Ya sake fada da wani sassanyan sauti me tada tsigar jiki
yana miqa hannu ya sake musu ruwa saman kansu shi da ita. Saukar ruwan ya sake
tayar masa da abinda yakeji ninkin na dazu,abinda ya qarasa gigitashi kenan,ya
dagata yana hadeta da bangon toilet din,ya fara abubuwan da yasan zai samu sauqi da
sassaucin abinda yakeji.

Wani irin tsoro ne ya sake kamata,takaici da baqincikin yadda yake
sarrafa jikinta yadda yaga dama,sai ta sake sakin kuka me sauti tana sake tureshi
dakai masa duka da siraran tafin hannunsa. Ba abinda yaji saiji da yayi ma kaman
tana sake zugashi,sautin kukanta kawai yake iya ji daya sake zame masa kaman zuga
zugi,don sai ya dinga jin kaman kukan wani abu daban takeyi bana baqinciki ba,deep
inside yasan na baqinciki ne,but bazai iya qyaleta ba ko yaya......yana buqatar
samun sassauci koda baiyi me gaba daya ba,yanajin zuciyarsa da rayuwarsa tana sake
mannuwa da ita,yana jin kamar duk wani fitar numfashinsa ya ta'allaqa da ita ne.

Sai daya tabbatar ya samu nutsuwar da yake da buqata sannan ya jata
jikinsa yana fitar d wani zazzafan numfashi,ya gama kashe mata jiki da tsoro
itama,dole ta jingina da jikin nasa tana jin yadda zukatansu ke wani irin
gudu,musamman shi da bugun zuciyarsa ke shiga cikin kunnenta sosai saboda kan nata
dake kwance a qirjinsa.

Duk da ruwan dake zuba saman kansu yana kwaranyewa a sassan jikinsu gaba
daya amma hakan bai hanashi tantance dumin hawayenta saman fatar jikinsa ba. Ya
gaza bude idanunsa,sau hannunsa guda daya yake shafar sassalkan gashinta daya watsu
har gadon bayanta,ya kuma manne sosai saboda ruwan dake zuba

"Am sorry......I'm genuinely sorry,My apologies from the bottom of my heart" Ya
fada yana kissing goshinta softly.

Ture fuskarsa tayi tana sake qayyade adadin rashin imaninsa......tadai
san saboda itace kawai ya gwada mata wannan rashin tausayin,banda haka ta tabbatar
inda duka mata haka sukeji ba abinda zai sanya su zauna ko suci gaba da yin aure.

"Leave me" Ta fada tana qoqarin tashi daga jikinsa. Hannunsa ya sanya ya damqota
sosai yana cewa

"I can't......ko mutuwa bata isa ya rabani dake ba sabrrrrrr.....zan yita baki
haquri har ranar da numfashina ya fita daga gangar jikina......zanta baki haquri ko
sau dubu a rana kikeso.....karki wahalar damu gaba daya ta hanyar cewa na barki ko
na nisanceki.....don wallahi wallahi wallahi bazan iya ba......i can't do it" Ya
qarasa fada yana sake matseta jikin bango sosai sannan ya fara tsarkake jikinsa
idanunsa a kanta.

So yake qarfi da yaji sai ya cire kowacce kunya daga
idanunta,tsaiwarsa haka a gabanta tana jin shine abu mafi girma firgici da razani
da suka taba gani. Cikin mintuna kadan ya gama ya kashe shower din,ya jawo babban
towel ya wareshi. Ta dauka zai rufa ne ko ita ya bata daman rufawa.....maimakon
haka sai ya jawota jikinsa ya bude towel din ya nadesu su biyun a ciki.

Shi da ita ba wanda numfashinsa baiso yin qaura ba saboda yadda
jikinsu ya sake gauraya dana juna

"Shshshsh" Ya fada yana qoqarin daidaita numfashinsa,don bayason tace
komai,hannunsa ya sanya a gadon bayanta ya matseta cikin jikinsa gami da rabata da
qasa kaman yadda zaka rungumi yaro a haka suka fita a toilet din.

Batasan da gangan yayi ba?,oho.....amma gaba daya suka zube a gadon
yana fadawa samanta. Ya aje mata nauyinsa sosai har sai da numfashinta ya fara
nauyi

"Oh....sorry" Ya furta yana dagata gami da bar mata towel din a tare da ita. Rintse
ido tayi tana qin dubansa,bai damu ba ya jawo boxer dinsa dake yashe a gefe tun
dazun ya saka,ya sanya hannu ya sauketa zuwa sofa bed ya fara tattare comforter da
bedsheets din harma da pillow case din,don bayason anni ta sake dawowa idanunta su
gani. Toilet ya koma ya shiga sheqa musu ruwa,jikinsa yayi wani irin sanyi ganin
yadda ruwan ke wanko jinin. Da gaske ya shigeta ne da tabbaci da yaqinin ta riga ta
saba......ya kuma samu qofar a kulle gam....dole taji ciwo koma wanne iri akace
masa taji. A yadda yakejin cikakkiyar lafiya a jikinsa ya sani,koda bazawara ce
yaje mata da irin yanayin jiya lallai saita yabawa aya zaqinta ballantana ita din
da take sabon hannu.

Luggage dinta ya bude,ya fidda mata kaya bayan ya saka wata sassauqar
riga a jikinsa over sized shirt da wandonta. Fara ce qal data dace da black trouser
dinsa. Sama sama yake jinsa shima,saidai abinda ke gabansa ya shafe komai.

Da rinannun idanunta ta dubeshi sanda ya aje mata kayan,tana so ne ya
matsa ya bata waje ta shirya amma bataga alamun xai matsa din ba,hasalima tsaye
yake a kanta ya zube duka hannayensa a aljihun wandonsa kaman zai lasheta,ya zube
mata nauyayan idanunsan nan yana jin kamar ya buda qirjinsa ya fiddo mata
mahaukaciyar soyayyar data sakar masa.

"Ka fita zan shirya" Ta fada a taqaice ba tare data kalleshi ba,hannayensa ya fidda
daga aljihunsa ya juya a hankali ya fita.

Duk yadda taso ta miqe sosai don ta shirya amma hakan ya gagareta,ba
zata iya tsaiwa normal kaman kowa ba,abinda ya sanya hawaye yaci gaba da zuba a
idanunta,saita dinga jin data sani ta barshi ya taimaka mata,amma kuma batason
komai da zai dinga hadata dashi. Da qyar ta lallaba ta saka underwears dinta ta
maida rigar,sannan ta lallaba hannun damanta ta kwanta tana ci gaba da fitar da
ruwan hawaye.

A nutse anni ta murda qofar tana shigowa da sallama,wata kunya ta taso
ta lullubeta,saita rufe idanunta tamkar me bacci,tana fata annin taji kaman baccin
takeyi ta juya ta barta.

"Sannu....." Anni ta fada a hankali da alama ta fahimci ba baccin takeyi ba.

"Zaki iya tashi?,doctor zata shigo ta dubaki". Kai kawai ta gyadawa anni ba tare
data iya furta komai ba,ta motsa a hankali tana tunanin yadda zata tashi din.
Matsawa annin tayi ta kamata a nutse tana cewa

"Yi a hankali" Tausayinta yana kama annin. Yanayin yanayine bame dadi ba,iya yau
kawai ta fahimci yaron nata yadda jikinsa ke agine hakama komai nasa

"Allah ya baki ikon jurewa" Annin ta fada cikin ranta. Sai a yanzu ta fahimci
dalilin da yasa yake kaucewa abubuwa da dama,azumin litinin da alhamis akai
akai,harma wani lokaci yakanyi azumin annabi dawud,yau yayi gobe ya huta. Wani
lokaci takance

"Ka dinga hutawa mana me babban suna......ga azumi ga aiki,shi kansa aikin busy din
da kake sakawa kanka pressure din tana yawa". Sau tari murmushi kawai yakeyi ko ya
kafa mata hujja da



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³
π™‹π˜Όπ™‚π™€ 78


78


"Ba isashen time na tsayawa cin abincin,wani lokaci azumin yafi,idanma
banyi ba coffee ne sai ruwa sai fura ko yoghurt ". A yau ta fahimci ainihin
dalilinsa,saita dinga furta

" Alhamdulillah" Qasan zuciyarta. Da gaske Allah ya tsare mata yaranta gabansu da
bayansu kaman yadda take yawaita addua a dukka salllolinta na nafila ko na farilla.
Tayi imanin inda wani ne ya samu cikakkiyar dama irinta fu'ad din,tarin dukiya kyau
ilimi da suna da yayi a duniya ba irin haramtattun ayyukan da bazai aikata ba,ta
sani akwai dubban mata dake a shirye su bada kansu ga irin wadannan mutanen,koda ba
zasu samu komai ba a wajensu daukaka ce ace yau suna tare dasu.

Sai data zaunar da sabreen yadda zataji dadin zaman sannan ta juya a
hankali tana fita parlor din.

Minti daya ta dawo tare da baquwar fuskar. Dr fadwa siririya fara
tas,duba daya zaka fahimci shekarunta duka duka ba zasu haura arba'in ba zuwa da
biyu. Anni tana gaba dauke da tea tray,Dr fadwa na biye da ita.

Qasa sabreen tayi da qwayar idanunta,ba zata iya kallonsu ba dukka su
biyun,har Dr fadwa dake matsayin baquwa a idanunta. Ajiye tea tray din anni tayi
tana duban Dr fadwa. Kai Dr fadwa ta gyadawa anni,sai annin ta maida dubanta ga
sabreen

"Ga likita na.....zata dubaki in sha Allah,ki saki jikinki.....itama 'yar gida ce"
Kai ta dagawa anni a hankali,tana jin takun anni da fitarta a dakin,ta kuma ja
qofar ta rufe musu.

Dubanta Dr fadwa take tana kuma karantarta. Ko ba'a gaya mata ba ta
fahimci ita din bame saurin sakewa da mutane bace,ta miqa hannu a nutse ta kama
hannunta ta sanya a nata,abinda ya sanya sabreen daga kanta ta kalleta da
risunannun idanunta. Da sassauqan turanci take tambayarta da sakakkiyar murya.

"Kinci abinci?" Kai ta girgiza mata a hankali. Ba zata iya tuna wani abincin kirki
da taci ba,tun na dazun kafin su fita,ko acan wajen cin kifi ma bata saki jiki taci
komai ba,kasancewar ita ba ma'abociyar cin abinci cikin jama'a bane. Kai tsaye Dr
fadwa ta jawo tea tray din zuwa saman cinyarta tana matsawa dab da sabreen

"Ki saki jiki kici abinci......sai na dubaki,kada ki damu da yawa......hakan yana
faruwa ga 'ya'ya mata da yawa,musamman da yake yadda kowacce mace halittanta
daban,haka kowanne namiji shima nashi halittan daban......fashewar budurcin mace
yana iya kawo fitar jini.....amma komai zai zama daidai kinji?" Kai ta daga a
hankali,ta kuma miqa hannu tana karbar mug din da anni ta hada mata tea me dumi
sosai da kauri.

Ita kanta tasan ba komai a cikinta,ballantana kuma da abun ya faru sai
taji kamar anyi mata yasa,kamar an kwashe 'ya'yan hanjinta gaba daya,kamar iska
tana turata zuwa gaba.

Kadan kadan take shan tea din,dr fadwa bata matsa wajen kallonta ko yi
mata wata tambaya ba ta daban,ta bata time sosai tana duba wayarta har taga ta
ajiye. Wayar ta bari ta daga kai tana kallonta,batasha da yawa ba amma saita
qyaleta don tasan lallai yanayin bame dadi bane.
Kauda tray din tayi ta matso kusa da ita tana dubanta

"Sunana fadwa kefa?"

"Ameenatu" Ta furta idanunta suna dan lumshewa

"Sabreen sunan inkiya?" Kai ta gyada,saita fidda takarda fara ta rubuta sunan akai.

"Eheennn......ina ne yake miki ciwo yanzu?" Shuru tayi don tamabayar tayi mata
nauyi da yawa,uwa uba ma gurare da yawa ciwon suke mata,tun daga lips
dinta......qirjinta....hatta da tafukan hannunta da suka sha murxa zafi zafi takeji
suna mata.

"Ki sake sosai kiyimin bayani,shi yasa madam ta fita ta bamu guri......zai iya zama
ciwo me zafi nan gaba idan baki bayani ba". Hannu tasa ta nuna mata wajen ba tare
data iya kallon idanun fadwa ba.

"Alright......zan duba wajen idan ba damuwa?" Ta fadi da nufin neman izini. Dif
tayi abun yana mata wani iri,shikenan ita kuma jikinta ya zama wani budadden guri?

"Kiyi haquri....saboda lafiyarki,bazai dauki lokaci ba" Ta fada da sigar lallashi.
Kai ta gyada mata a sanyaye.

"Kin shirya?" Dr fadwa ta fada tana kallonta sanda ta kwanta kamar yadda ta
kwatanta mata. Kai ta gyada mata tana rufe idonta saboda kunya.

A hankali ta fara dubata cikin qwarewa da nutsuwa yadda ba zata fama
mata ba.

"Oh my god.......subhanallah" Abinda ta fada kenan tana maida mata doguwar rigarta.

"Kin masa gardama ko musu?" Dr fadwa ta fada tana kallon fuskar sabreen din da
tuntuni ta canza kala zuwa red. Tambayar sai ta zama kaman ta bata license din
sabon kuka,ita me zata ce mata?,batasan ma me tayi ba.....musu ko taurin kan
batasan wanne ne tayi a ciki ba,batasan wanne ne ya faru ba.

"Irinsu sir.......ba kasafai za'ayi musu musu a irin wannan lokacin a wanye lafiya
qalau ba.....next time kada ki qara musu ko gardama,mijinki yana da duk wani
personality da kowacce 'ya mace zatayi alfaharin samunsa a matsayin
miji,.....kulawa da tattali yake buqata,ko don gaba kada ki sake matse jikinki da
hana masa kanki haka". Sanda take fadin next time din ji take kaman ta ture Dr
fadwa,itakam wacce irin sauna ce da zata yarda taci gaba da zama da mutum
irinsa?,wanda bisan ciwo ko darajar dan adam ba?,balle ma har hakan taci gaba da
faruwa wai a gaba?.

Daidai nan anni ta tura qofar ta shigo,da murmushi take tambayar Dr
fadwa

"Kin gama?" Kai ta girgiza tana dan murmushi itama

"Aah fa......madam yaronki aiki ya baro.....bleeding din data dinga yi ta samu tier
ne.....so dole sai an mata stitches..." Idanu kadan anni ta fiddo,har jikinta tana
jin wani iri. Lallai Allah kadai yasan azabar da tasha tunda har an kai ga batun
dinki.

"Gurin yayi ciwo sosai gaskiya.....harda bruises banda tier din,dole a dinki
wajen,inda first degree tier ne da sauqi....so amma yanzun ma idan kina ganin a
bari......"
"No.....a dinke Dr" Anni tayi saurin dakatar da Dr fadwa din. A yadda taga yanayin
fu'ad din da idanunshi ba yadda zata bari a bar sabreen din a bude,tun sanda momma
ta gaya mata marainiya ce takejin kamar kula da sabreen din wani haqqi ne daya
rataya a wuyanta.

"Kiyi haquri a dinke sabreen kinji?,wannan gurin shine mutuncin duk wata d'iya mace
a wajen mijinta.....akwai zafi amma zai wuce kaman bai faru ba,wannan shi ake kira
da cikakken mutunci mijinki ya zamana shi ya karbi wannan abun ba wasu shashashai a
waje ba.....nayi alfahari da hakan......na kuma yi alfahari dake kaman yadda nasan
yake a wajen mijinki" Anni ta fada a tausashe hannunta saman kan sabreen da kunya
ta hanata koda motsawa bare ta bude idanunta.

Sake fita anni tayi ta basu waje don sabreen din ta sake sosai. Dr
fadwa kuma ta shirya komai,ta kuma yi mata allurar da sai data zubda qwalla kafin a
gama,batasan azaban yana gaba ba sai da aka fara dinkin.

Neman sakayya wajen Alla data dinga yi har batasan sau adadin nawa ta
fadi ba,saidai duka cikin ranta takeyi,bakinta baya iya furta komai sai ruwan
hawaye dake fita Dr fadwa na mata sannu.

Kasa zama yayi a falon,sai kawai ya tura qofar dakinsu saddiq ya
shige. Kwance yayi kawai saman gadonsu,ya kasa tuna komai sai hankalinsa dake can
dakin inda ya barosu,yaji shigar dr fadwa da anni da fitowar annin duka,baisan me
yake faruwa ba don haka ya kasa samun nutsuwa. Gefe guda wani irin sarqaqiya ya
shiga.

"KARUWA" Sunanta ma farko kenan daya fara zuwa kunnensa,yaci gaba kuma da zuwa masa
daga bakunan mabanbantan mutane. Kenan dukka wadannan bincike da shaidun duka
shaidan zur ne?,duka shaidan qarya ne?. Idan har hakan ya kasance kuma ganin da
yayi mata a hotel fa?,mashkur dake hannunsu a yanzu haka yana nemanta afujajan da
sunan wadda ta kwashe masa komai nasa?,ganinta da yayi fa tare da mika'il?,a cikin
kamfaninsa tana fitowa daga toilet dinsa?,binciken daya tabbatar kuma ita ta kwashe
kudaden asusun kamfaninsa fa?,wannan kuma mene?. Ta yaya zai fahimta?,ta yaya zai
gane?,waye zai warware masa?.

"Ka nutsu fu'ad.......diban kudi yasha banban da bada mutunci.....don tana kwashe
kudaden maza.....don kana ganinsu tare hakan ba yana nufin tana basu kanya
bane,kowanne matsayinsa daban,cakudasu waje daya kuma shine zai sanya ka kasa
banbance inda komai ya dosa" Wani sashe can qarqashin lungun zuciyarsa ya gaya
masa.

Sau uku yana leqa parlor din ko zaiga ko yaji motsin anni ko wani abu da
zai bashi haske amma baiji ba. Kunyarsa da kawaicinsa duka suka qare,sai kawai ya
buda qofar dakin ya fito kai tsaye yana tunkarar dakin.

Itace ta farko da idanunsa suka fada kanta bayan bude qofar da yayi. Ta
wani sake fadawa farat daya saboda masifar dinkin. Ko baka santa ba tsakanin a
wannin nan idan ka kalli fuskarta zakasan tayi kalar kukan da bata taba irinsa ba.

Idanunsa ya maida kan Dr fadwa,likitan da sai da tazo ya tuna ya taba
saninta a Egypt,ta taba dubashi da yayi wani zazzabi,hankalinta kuma da nutsuwarta
shine abinda ya sanya ya bata daman bashi magani.

"Welcome sir" Ta fada cikin girmamawa. Kai ya gyada yaja kujera yana zama
hankalinshi a kanta. Daga kallon da yayi mata ta fahimci qarin bayani yake nema.
Dama kuma dole akwai buqatar masa qarin bayanin don ta fahimci kaman yana cikin
mazan nan marasa haquri akan abinda ya shafi janibin auratayya.

"Mun kammala,anyi mata stitches.....but please sir,tana buqatar hutu na koda 3to 4
weeks kafin a sake tabata,saboda a bawa dinkin daman warkewa yadda ya kamata". Ido
ya lumshe sannan ya bude yana jinjina kai.

"Mun gode....ta yaya zaa biyaki?".

"Madam ta biya sir.....Allah ya qara lafiya" Kai ya jinjina yana girmama qaunarsu
da anni. Tsantsar kulawa da qauna irin wadda akasan uwa kadai take da wannan
zuciyar. Komai idan ya kama qoqari takeyi tayi musu shi ba tare data jira yin kowa
ko cewar kowa ba.

Tatttare kayanta tayi ta fice taja musu qofar.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 79


79


A hankali ya dauke dubansa daga kan qofar zuwa inda take zaune. Idanunsa ya zuba
mata yana jin akwai wani boyayyen abu ciki rayuwarta,wadanne irin masharrantan
mutane ne tattare da ita haka?,wadanda ba zasu iya fadin alkhairi a kanta
ba?,wadanda ba zasu iya suturta aibunta ba a sanda akazo bincike a kanta ba?. Idan
bai manta ba,ya samu tabbacin cikin wadanda suka bada shaida a kanta harda matar
babanta,sanda yake jaddadawa abdul haleem bayason fake bincike,baya son kuma
gurbataccen shaidu.

"Wacece a cikinsu?" Ya tambayi kansa da kansa yana takawa gabanta,tausayi da wata
irin mahaukaciyar qauna tata tana hudashi. A yanzun yana jin a shirye yake da duk
wani mutum da zai taba rayuwarta,a shirye yake ya bada dukkan abinda ya mallaka a
kanta.....in fact a yadda ta zame masa mahadin numfashi a yanxun......ba dukiyarsa
kadai ba.....hatta da rayuwarsa a shirye yake ya bata ita. Yana jin ya shirya kame
duk wani wanda ya bada shaidar banza a kanta,ya shirya tuhumarsu ko su
waye....komai yawansu.....komai kuma kusancin dake tsakaninsu da ita.

A jikinta takejin wanzuwarsa a wajen,wannan ya sanya ta sake zabar ci
gaba da rufe idanunta,har ya iso gefanta,ya zame kan gwiwoyinsa yana aza qarfinsa
akai. Hannusa ya miqa ya kamo tattausan tafin hannunta,ta motsa da sauri ta nufin
zamewa amma ya rigata,ya kamo hannun nata da daya hannun ya saka tsakiyar
hannayensa yana duban rufaffen idonta. Dukka kalamansa sun gama qwace masa,komai ya
auno sai yaji bai hau mizanin bada haquri ba....amma hakanan zaici gaba da gwadawa
don ya shirya karbar ko meye daga gareta hannu bibbiyu.

" Can you feel any pain or discomfort?" Ya tambayeta kaman zai maida idanunshi
cikin fuskarta. Shuru ne ya zame masa amsa,bata ko motsa ba ballantana ta nuna
tasan da ita yake. Sake matsa hannunta yayi kadan a tausashe,ya motsa labbansa
yace

"Sabrrrrr" Nan ma shuru ba wani motsi ko amsa. Jawo hannun nata yayi kadan,ya kuma
matso dashi ya dora tafin hannun nata saman qirjinsa saitin zuciyarsa.

Tabbas har cikin jininta taji bugun zuciyarsa.....kaman yadda dumin
cikin hannunsa da wanda taji cikin qirjinsa ya tabbatar mata da zazzafan zazzabin
da yakeyi,amma ko daya sai taji bataji tausayinsa ba.

"Im filled with regret for what i did,am truly sorry......please kice wani abu man"
Ya fadi cikin zaquwar ji daga gareta,amma still ba wani canji. Shurunta sai yaji
yana kasheshi har cikin tsokar zuciyarsa,shirunta sai yaji yana masa wani irin
ciwo......baya fatan ta zama me hukunci da shuru wanda kusan halinsa kenan,ya kuma
san ciwon hakan.

"Sabrrrr......I'll do everything to prevent it on the future nayi alqaw....."
Future din daya fada shi ya sanyata janye hannunta sa wani irin sauri,saidai kuma
kash zafin namansa ya qure nata,kafin ta samu daman boye hannun ya sake kamoshi
yana jin wani nisa da takeson haifarwa tsakaninsu. Cikin yanayi na karaya ya sake
aza tafin hannun nata saman kuncinta,ya kuma dora kansa akai kaman wanda ya samu
pillow

"My heart was beaten past sabrrrrr........zata iya bugawa wallahi......please sabr
say something mana......"

"Ka qyaleniiiiii....." Ta fada cikin daga murya tare da wani irin sautin kuka wanda
yayi daidai da shigowar anni. Tsaiwa tayi cak tana dubansa,kaman zata koma sai kuma
ta tuna da zancan Dr fadwa,don haka ta qaraso cikin,amma ta dauke kai kaman bataga
abinda ya faru ba. Idanunsa ya aza kan annin,sai ya janye jikinsa daga wajen yana
komawa inda dr fadwa ta tashi wajen data ajiye documents din da tayi rubutu a ciki.

"Daughter" Ta kira sabreen a hankali wadda ke qoqarin boye hawayenta da mode na
fuskarta.

"Naam" Ta amsa tana murmushi

"Akwai ciwo ko ya ragu?,idan akwai tace tayi prescribing wasu magunguna,ta tura ta
pharmacy dinsu zaa karbo ko a kawo miki".

" Akwai ragowa" Ta fadi tana jin yadda gurin ya daddaure mata

"Zai daina in sha Allah" Maida kallonta tayi kansa.

"Ka hada mata kayanta da duk zata buqata......zatayi matsa zuwa dakina,zan kula da
ita zuwa sanda ciwon zai warke" Anni ta fada adan dake. Da mamaki ya kalli annin
yana jin rashin dadi yana saukar masa,abun sam bai masa ba,yana ganin kamar shi
yafi cancanta a bari yayi jinyarta,yayin da sabreen taji kamar an mata rahama,wani
sanyi ya fara sauka saman zuciyarta.....zata matsa daga kusa dashi......zata bada
rata me yawan gaske kuwa tsakaninsu,tana jin sai taso ma zata bari idanunsa ya hadu
da nata,tabbas da wannan damar zatayi amfani tayi nesa dashi,nisan da zai fara tun
daga yanzu har kuma abada

_uhmmm.....sabreen,anya me jadda zai bari kuwa?,to dai zami gani_


Kaman yadda ani ta

Please Login or Register in order to submit comment