You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yayi abun ba'a cewa komai,mutane da dama ya fidda da
prison,mutane masu yawan gaske ya biyawa bashi,mutane masu yawa ya siyawa gidajen
zama,mutane masu yawa ya dauki nauyin aurar da 'ya'yansu,a cikin dangi kuma ya sake
ninka adadin mutanen da ake bawa kujerar hajji da adadin ninki uku. Mutane da yawan
gaske ya dauka nauyin maganinsu da samar musu lafiya,hakanan ya qara yawan adadin
marayun da nauyinsu ke wuyansa. A sannan sai ya ke qara jin yana da kyau idan
sabreen ta koma hankalinta su zauna,foundation yake da sha'awar ya bude mata saboda
taimakon iyayen marayun da marayun kansu.

Yayi kyautar kudaden da shi kansa baya lissafawa. Duk duniya sai
data shaida muhammad jadda an haifa masa abinda yafi so.....muhammad jadda ya samu
abinda yafi qulafuci,duka kuma yayi ne saboda nunawa ubangiji godiyarsa a gareshi.

Kwanaki uku kawai da suka rage suna suka baro birnin madeena da
boundles of joy dinsu,suka sauka kanon Nigeria.

Tun a airport tasan lallai haihuwa wata baiwa ce,wata abace ta daban
dake cike da ni'ima baiwa da kuma tarin albarka da bata da iyaka.

Tamkar tawagar matafiya haka sukayi zuga zuwa gida,ko dama fu'ad din
idan yana qasar motocinsa sukan kasance ne cikin convoys koda yaushe......saidai a
yanxun yawan adadin ya ninku.

Sanda suka isa gida ma mutane 'yan sannu da zuwa da barka suka
samu,saidai kusan duk wanda ke cikin gidan me fada aji ne,don haka cikin gayu da
nutsuwa komai ke gudana,don sai data shiga daki ta sake wanka ma,aka warware yaran
suma aka sakeyi musu wanka aka shiryasu cikin wasu lausasan kaya masu zuwa complete
set dinsu ruwan sararin samaniya me haske. Nannys ya dauka musu qwararru tun daga
madeena din,wadanda raino suka karanta gaba daya. Salwa da sameena,ba cikakkun
larabawa bane,saidai acan aka haifi iyayensu suma aka haifesu,har kuma suka soma
girma a yanxun,don kowacce tayi shekara kusan talatin da biyar biyar. Asalin
kakanninsu 'yan nigeria ne......mata ne kamilallu da suka san rayuwa,sukasan kuma
raino da abinda ake nufi da tarbiyya.

A iya rayuwarta idan aka gaya mata akwai ranar da rayuwa zata sadata
da manyan mutane irin wadannan zata qaryata.....mummunar qaryatawa kuwa,don tasan
tabbas wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa idan har ba ta dalili ko silar fu'ad din
ba.

Allah ya zuba mata wani iri kwarjini da cika ido sabreen din tun
asali,tana kuma da wata irin nutsuwa da kamewa......wannan ya sanya ta saje sosai a
cikinsu.

Irin gifts din data karba a ranar kadai sai daya sanya kanta ya kusa
kullewa. Da gaske masu kudi suna sha'aninsu,da gaske masu arziqi suna
sha'aninsu......da gaske rayuwa mataki mataki ce. Gifts data samu a yau idan a
rayuwarta ta baya aka gaya mata ana kyauta da irin wadannan kudaden ko kayan zata
qaryata,zata kalli wanda ya bata wannan labarin tace masa ya rage qarya......ya
kuma ji tsoron Allah,sai gasu zube a wani daki daban,wanda ma'u tace a nan zata
tarawa yaran komai nasu.

Ana magariba ta rufe ganin kowa don tanaso ta bawa fu'ad
lokacinsa.......tanaso ta bashi kulawa kaman yadda ta soma tsarawa rayuwarta. Yaran
ta sama su salwa suka sake daukewa,aka sake fesa musu wanka da wasu baby set din da
akayi musu order dinsu musamman daga wani babban kamfani dan qasar turkiyya. Akwai
wani tambari na musamman jikin rigunan dake dauke da THE JADDA'S jikin rigar
Kowannensu,hula da takalmi da safan hannu dana qafa duka irin guda sak da kayan da
abun daukan nasu dake da adon gold a jiki.
Daga wanka ta fito itama,wanda take lullube wajen dinkin da wani
leather haka tayi wankanta sannan ta tsane jikinta da kyau kafin ta bude.

Tururin zazzafan ruwan dake tashi da wani sassanyan qamshin turaren
wanka na incense by kabo daughter jikinta yake fiddawa. Wani irin nishadi
takeji......tana masifar son qamshi har batasan waye yafi wani ba tsakaninta da
fu'ad din. Duka gidan a dumame yake da qamshin incense by kabo daughter,wanda
kowanne sashe da daki na gidan qamshinsa daban yake fiddawa.

Manyan mahaukatan botikai tasa akayi mata kusan kala goma,kowanne kuma
qamshinsa daban yake fiddawa.

Kanta ta busar ta kuma turareshi da kabbasar gashi duka daga
kamfanin incense by kabo daughter,ta tajeshi tana qoqarin kameshi da banda taji an
riqe hannayenta a tausashe ta baya.

Murmushi ya subuce mata jin yaqi magana,ya kuma tsaya cak yaqi ya bata
alamun da zata gane shine. Motsa labbanta tayi a hankali tana dora hannunta ta baya
saman nashi.

"Koda bayan na dauki shekaru da mutuwa ne......koda bayan na zama qasusuwa ko qasa
cikin qabarina......muddin zaka wuce ta gurin zan fahimci cewa kaine ka wuce,don
takun takalmanka zai zama ya fita daban dana kowa". Wani irin abu yaji yana
ratsashi,sabreen dinsa ta fita daban da kowa.......ta iya kalaman da suke sanyashi
kullum kwanan duniya yake jin kansa yana sake kumbura,kullum kwanan duniya yakejin
yafi kowanne d'a namiji sa'ar mace.....kullum kwanan duniya yakejin ba za'a sake
haifan mace kamanta ba.

Juyo da ita yayi suna fuskantar juna,idanunsa cikin nata yana ganin ta
sake masa wani ajiyayyen kyau.

"Na dauka zaki tsorata ai" Ya fada a tausashe yana sanya hannunsa ya matsar mata da
wani siririn gashi daya fito ta gefen fuskarta gefe. Murmushi ta kuma sakar masa
tana juya idanunta.

"Tsoro?" Ta tambayeshi tana murmushi,sai kuma ta miqa hannunta gefan fuskarsa tana
shafa kwantacciyar sumar dake wajen.

"Wannan jarumin mazan......wannan uban na 'yan ukun nan masu sunaye masu
daraja......ya fidda kalmar tsoro kwata kwata daga rayuwar marainiyar nan.....ya
cikata da qauna da aminci da soyayya.....ya sanyata cikin wata masarauta dake cike
da tsaro......ya kewayeta da amintattun mutane......ya kuma sake bata wasu ruhikan
har uku da zasu rayu da ita" Kasa magana yayi illa jawota da yayi ya rungumeta
tsam cikin jikinsa.

"Me zan mallaka miki my world......me zan miki da zai sake fahimtar dake girman
matsayinki a raina.....me zan miki?".

"Kaci gaba da sona saboda Allah,kaci gaba da qaunatata don girman zatin Allah,ka
kula dani......ka kula da yayana da rayuwata.....sannan ka rayu dani ni kadai".
Dagata yayi.yana murmushi gami da duban fuskarta,kafin yace komai ta rigashi.

" Ina da.tsananin kishi.....amma akanka kadai.....banajin zan iya rabaka ko sharing
dinka da wata".

"Kin riga kin sameni.....kin sameni har abada ke kadai sabreen.....xanta maimaita
miki hakan har sai ranar da kika gamsu dari bisa dari".

"Na yarda dakai" Ta furta tana kallon tsakiyar idanunsa
"Na yarda dake fiye da yadda kika yarda dani" Ya fadi yana sauke mata tattausan
kiss.

Knocking din qofar shi ya maida hankalinsu kan qofar.

"Xan iya shigowa hamma?" Muryar amna ta qaraso dakin bayan tadan buda qofar kadan

"Bismillah" Ya fadi yana takawa zuwa qofar dakin.

Babies biyu ne rungume a kafadarta,ya miqa hannu ya karbi daya yana
tayata dashi. Tare suka shigo dakin,ya qarasa gaban sabreen ya tsugunna zai miqa
mata shi,kaman yasan an iso gaban mamanshi ya saki kuka.

Murmushi ya saki yana bude fuskarsa,ya kalleshi da kyau sannan ya daga
kansa yana dubanta.

"Farouq ne......" Murmushi itama tayi tana maida kallonta kan fuskarsa.

"Gyara zaman na baki shi". Saman cinyarta ya dora mata shi sannan ya saka mata
pillow yadda zata jita comfortable. Baya ya koma ya zauna sosai yana kallonsu cikin
burgewa,yadda take shayar dashi hamza yana gefanta hannunta saman sumar kan hamzan.

"Hamma" Ta kirashi a shagwabe.

"Giwar hamma" Ya amsa mata har cikin ranshi yana jin ta cancanci wannan sunan.

"Nifa na shirya"

"Zuwa ina?" Ya tambaya yana kallonta.

"Zamuje ni dakai mu kaiwa maamah yaran nan ta gansu......bata gansu ba bata sansu
ba". Shuru ya danyi yana juya maganarta,hakan ya kamata suyin,to amma shi yana
tsoron dabi'ar maamah,baisan da wanne irin kallo zata dubi yaran ba,yana tsoro kada
kallonta kadai ya cutar masa da yaran. Saidai kuma ya tabbatar sabreen din tana da
zurfin tunani da hangen nesa,ba zata yi abinda zai zamewa yaran cutarwa
ba......hakanan ya yarda da ita dari bisa dari.....161


"Is okay" Ya fada a taqaice yana miqewa

"Bari na watsa ruwa kafin lokacin ki sallami sojojina ko?abbana ne kawai ba'a kawo
ba" Ya fada yana kashe mata ido daya. Rolling nata idanun tayi tana murmushi.

"Ba laifi"

"Wannan abun yana kasheni my world......anya zaki taimakamin na barki har ki
warke?" Ya fada yana karya wuya. Yadda yayi wani kalan tausayi ya sakata sakin
dariya

"Eh to,ai anni tana nan dai......sannan momma ma gobe zata iso". Sarai ya fahimci
me yake nufi,sai yadan bata rai,ya tako zuwa kusa da ita.

"Karki yadda a zame mana katanga tsakaninmu......bazan iya jurewa ba,idan kuma har
na gaza jurewar komai ma zai iya faruwa" Ya qarasa maganar yana aje mata wannan
zazzafan kallon nasa da taji ya tsarga mata itama tun daga tsakiyar kanta har tafin
qafafuwanta. Daidai sanda kira ya shigo wayarta,ya matsa a hankali ya dauko mata
wayar.
"Bibo da yarinyarta sunzo,saidai na hanata ganinki,don har yanzun ban gama nutsuwa
da ita ba,bazan kuma bari kowanne abu da ban gama nutsuwa dashi ba ya iso gareku"
Ya furta yana saka mata wayar a hannunta.

"Na tabbatar maka bibo tayi nadama zuwa yanzu,don ba komai yake damunta ba tuncan
baya sai kishi da hassada"

"Zan duba na gani" Ya amsa mata yana takawa a hankali zai fita a dakin,ta maida
kallonta kan wayar.

Kawu rufa'i ne,ta dan saki murmushi tana daga kiran.

"Sannu d'iyar arziqi......sannu d'iyar albarka......wadda aka haifa tsiya tana
bacci". Dariya sosai kawun ya bata.

"Ina wuni kawu barka da dare"

"Barkanki kadai,an samu kai qalau?"

"Alhamdulillah kawu"

"Ubangiji ya rayasu yayi musu albarka......ai nace kinyimin daidai da kika bugo
yara uku tun a karon farko......wa yaqi arziqi?,waye zaiyi sanya a gidan
arziqi?,ina me miki wasiyya,duk sanda kika tashi haihuwa dinga ajiye masa hudu hudu
uku bibbiyu,idan da hali karkiyi d'an d'aya ma sam". Dariya ce taso kubce mata,amna
ta danneta,saidai hakan ya nuna a muryarta.

"To ai kawu abun na Allah ne,shi yake bada iya adadin da yakeso".

" Eh amma ai yace ku roqeni zan amsa muku ko?,qarshen watannan zamu shiga qasa me
tsarki,farouqu xai fara cika alqawarinsa.......zam zage nayita roqo miki.haihuwar
haka haka din" Wannan karon saida tayi dariya sosai.

"Kawu Allah ya bamu masu albarka wadanda zamu iya dasu".

"Ke!,kana da wadata da arziqi irin na mijinki harka dinga tunanin kalar yaran da
zaka iya dasu?,yo ko yawan taron arfa kika haifa masa ai yana da abinda zaiji
dasu". Kai ta girgiza tana murmushi.

"Kawu......tarbiyya ba'a nan take ba,kace ameen kawai"

"To ameen sarkin tsari......nace ba?" Ya fada yana komawa serious.

"Ina jinka kawu"

"Ina iya tahowa zaman dab'aro?". Idanu sosai sabreen ta bude dariya tana son qwace
mata.

"Kawu kaifa kawuna ne,kuma namiji ne kai,ai mata suke zaman dab'aro,inama laifin
ace inna A'i?(matarsa)".

"Ke komai yanzu a zamanance akeyinsa,ta yaya zan turo A'i gani?,bayan ba abinda
bazan iyayi miki ba?,ni damuwata na kula da d'iyar ahmadu,na rama halascin da ya
yiwa rayuwata" Ta fuskanci da gaske kawu yake,saita gyara muryarta.

"Kawu kada ka damu,mun dauko masu kula da yaran musamman,sannan kuma ga masu aikin
gidan na ainihi".

"Duk da haka ba za'a barki haka ba,xan aiko A'in ta zauna miki kona kwana arba'inne
na al'ada"

"To kawu Allah ya saka da alkhairi ya qara zumunci" Ta fada tana jin dadi qasam
ranta. Ko ba komai zata ce ga wani daga dangin mahaifinta,duk da zuwa yanzu 'yan
uwa ne kowa keta kutsowa da b'arkowa don nuna kulawarsa da bajintarsa akan
haihuwar,tun suna madeena ma kafin sukai ga dawowa.

Wayar ta sauke tana murmushi sanda take tuno baya,drama dinsu da kawu
wadda kusan kullum sai an yita,rayuwa kenan.....komai yayi farko said qarshe,kuma
dukkan tsanani yana tare da sauqi tabbas.

Farouq yayi bacci,saita ajiyeshi kusa da dan uwansa hamza,ta miqe
ta soma shiryawa,tana yi tana duban fuskokinsu. Ita kadai murmushi yana subuce
mata,tana jin qaunar yaran har a cikin jininta. Duk sanda ta kallesu su ukun a jere
reras saita samu kanta cikin mamakin yanzu wadannan din daga jikinta suka
fito?,yanxu wadannan din 'ya'yanta ne?,mallakinta ne?,yanzu wadannan din jininta
ne?,jinin muhammad fu'ad ne?.

Sanda ya shigo tsaiwa kawai yayi yana qare mata kallo,tayi wannan
sassanyan kyau cikin shigar atamfar data yafawa mayafi onion color. Sautin sauke
ajiyar zuciyarsa shi ya dawo da hankalinta,tadan juya ido a shagwabe

"Ka tsoratani hamma.....ka iya sanda ka tsaya kayita qaren kallo.....so kake kyauna
ya qare?". Bai amsa mata ba har sai daya iso inda take,ya rungumeta ta baya
sassanyan turarukansu suna gauraya waje daya.

"Bakisan kina sake qara shekaru kina sake qara kyau a waje na ba?,tsarki ya tabbata
ga ubangijin daya qagi wannan halittar ya kuma mallakamin ita a matsayin
halaliyata......kuma uwar 'ya'yana" Luf tayi itama a jikinsa,tana jin yadda
soyayyarsa take hudata tako ina.

Mota uku kawai tayi musu rakiya zuwa gidan maamah din,wadda tun a
bakin gate masu da guards na gidan suka taso,kowa barka yakeyi masa da nuna
farincikinsa.

Shi ya dauki farouq da hamza,ita kuma abba ne a hannunta wato
almustapha. Yana gaba yayi sallama tana biye dashi. Mutum daya suka samu a parlor
din wato saratu,ta miqe tana musu sannu da zuwa,ta kuma karbi yaro guda daga hannun
fu'ad din tana musu barka da addu'o'i sosai.

"Yanzu muka kai hajiya ciki,munga kaman ta gaji da zaman bacci takeso tayi"

"Har yanzu ba batun magana?". Kai saratu ta girgiza cikin jimami.

"Ba abinda ya canza har yanzu" Shuru kadan yayi yana juya al'amarin,a irin kulawar
da take samu physically and mentally yaci ace an samu ci gaba sosai,amma yana
mamakin yadda komai yaqi canzawa koda qanqani kuwa.

Daga saman gadon da take zaune jingine da fuskar gadon ta daga
idanunta sanda suke sallama cikin dakin. Idanunta ta zube fes a kansu kowanne dauke
da yaro guda. Saratu ce ta fara isa gefanta ta aje hamza tana juyawa ta fice a
dakin.

Da wani irin kallo taci gaba da binsu ba tare data dora idanunta
akan yaran ba da takejin ba zata iya kalla ba,zuciyarta ta fara zafi tana jin gumi
yana fara keto mata.

Kaman hadin baki suka isa gabanta a tare,fu'ad ya ajiye mata farouq a
gabanta,ya karbi almustapha ya ajiyeshi shima kusa da farouq,ya dawo da hamza kusa
da yan uwansa still idanunta akan fu'ad din yake. Yatsarsa ya sanya ya nuna hamza.

"Ga hamza......wanda ya zamemin tsanin zama muhammad jadda din da ake kirana dashi
a yanzu,hamzan daya bani dakin kwana......ya bani sabuwar rayuwa,ya bani sabon
ahalin da zan rayu dasu,na kuma kallesu a mazaunin nawa,ya kashemin kudinsa,yayi
amfani da lafiyarsa don sama mana abinda zamu rayu dashi cikin aminci.......ga
farouq,wanda ta sanadinsa nakai ga hamzan daya zama qashin bayan ilimina da
tarbiyyata gaba daya........ga kuma abbana..." Ya nuna almustapha yana tsagaitawa
wanda da alama wani abun ya hadiye.

"Abbana.....sanadi na......abbana da bani da wani abban daya haifeni wanda zai sake
maimaituwa irinsa sak" Yana kaiwa nan ya miqe,ya damqi hannun Sabreen

"Gasunan maamah.......gasunan ki kallesu,kiga waye bakiso a ciki?,waye yayi miki
wani laifi na rashin kyautawa?.....ki.kallesu jikokinki ne......yaran da suka fito
daga tsatson fu'ad.....dan da kika dauki cikinsa wata tara,d'an da kikayi naqudarsa
tsakanin mutuwa da rayuwa" Yana kaiwa nan ya fara jan sabreen din suna fita a
dakin.

Bugawa kawai zuciyar sabreen takeyi,don tace akai mata yaran ba hakan
yana nufin su fita a dakin subar mata su ba,zuciyarta ta kasa nutsuwa ko amincewa
da hakan

"Hamma......"

"Shshshsh" Kawai yace da ita da qarfi.

"Hamma yara na....." Ta sake fadi a gigice wanda sautin da reaction din yakai
kunnen maamah dake zaune a dakin.

Suna fita a dakin ya kama kafadunta dukka biyun ya riqeta da qarfin
gaske.

"Relax sabreen.....ba abinda zai faru......ba zata iyayi musu komai ba......inason
zamansu a dakin ya wanke duk wani daci da tsanarsu da zata iya ji a nan
gaba......ban isa na sanya ta soki ba kota soni......amma
definitely!.....dole!......dole taso wadannan yaran" Qwarin gwiwar da take gani
tsakiyar idanunsa shine ya bata relief,ta bishi xuwa falon suka zauna.

Tana iya jin zaman yaran kusa da ita har cikin jikinta,tana iya jin
wanzuwarsu sosai a tattare da ita,saidai kuma ta gaza daga idanunta ta kallesu.
Zafi takeji a ranta,zafin sabreen sosai takeji,tana ganin kamar itace silar komai
da komai.

Sun dauki mintuna masu yawa a haka,iyayen basu dawo sun daukesu
ba,abinda ya dinga bata mamaki kenan. Me yasa suka iya dauke idanunsu akan
yaran?,me yasa suka iya bar mata su suka fice abinsu?. Motsin da hamza ya fara yi
shine ya fusgi hankalinta ba tare data sani ba takai dubanta kansu.

"Subhanallahi" Ta fadi a ranta tana mamakin zallar kamannin dake fuskar yaran.
Kamannin da suka tuna mata da fu'ad din sanda yake tsumman goyo kaman haka. Idanu
ta zuba masa shi kuma yana ci gaba da motsinsa,a hankali har ya fara qushin qushin
din kuka,abinda kuma ya tashi sauran 'yan uwansa kenan.

Mutsu mutsu suka fara yi su duka ukun,kafin kuma a hankali su kece da
kuka.162
Hannun fu'ad ta riqe da kyau tana ji kaman ana matsa zuciyarta sanda
sautin kukan nasu ya isa ga kunnuwanta. Jikinta duka ya dauki rawa,ta daga idanu
tana kallon fu'ad. Qin kallonta yayi,kuma kaman ta fahimci yana sane yaqi kallon
nata,sai kawai ta sadda kanta qasa tana sake jin yadda zuciyarta ke tsananin
bugawa.

Cika mata kunne sosai kukan nasu yayi.

"Ya isa....kuyi shuru" Ta fadi tana jin ciwon yadda furucinta baya fita a sanda ta
yishi,saidai kuma ga mamakinta sai almustapha ya fara rage sautin kukansa,a hankali
dukkaninsu suka rage kukan kafin kuma suyi shuru. Mamaki taji ya kamata,ta sake
xuba musu idanu wanda kaman sunsan da hakan sai hamza ya soma bude idanunsa. Tarwai
qwayar idanunsa,kai ba zakace jariri bane dan sati biyu kacal,tana waiwayawa ga
sauran suma duk idanunsu sun bude,kuma ita suke kallo.

Batasan me yasa ba ta samu qaramin murmushi ya subuce daga
fuskarta,ta samu kanta da yunqurin miqa hannunta ta kamo hannun koda d'ayane a
cikinsu.

Cikin wani irin ba zata da mamaki sai ga hannunta ya motsa,ta maida
dubanta ga hannun,ta sake gwada dagashi xuwa gaba,ga tarin mamakinta sai hannunnata
ya isa ga almustapha ta riqe yatsunsa hannun nata yana wani irin kakkarwa.

Wani abu da batasan meye ba ya soma ratsa zuciyarta,hawayen da batasan
daga ina suke ba suka tsinke mata.

Wacce irin baiwa ko hukuncin Allah ne tattare da yaran?,abinda ta dinga
maimaitawa kanta da nacewa da tambaya kenan idanunta akan fuskokinsu dukka su ukun.
Sun zame mata waraka daga wani bangaren ciwon ta kenan?. Tambayar da tana ajiyeta
fu'ad ya murza qofar ya shigo a hankali shidaya,don gaba daya sabreen ta gaza
miqewa bare tayi jarumtar biyoshi,kawai zuciyarta tana gaya mata shikenan,shurunsu
wani abun ne maras kyau ya samesu.

Hannun nata yabi da kallo yana mamaki shima wanda har yanxu yana cikin
yatsun almustapha,ya qarasa gabanta ya tsugunna yana duban hannun yana kuma duban
yaran.

"Hannunki ya motsa yau?" Ya tambayeta,saita gyada kai a hankali hawaye yana silmiyo
mata daga idanunta. Qasa yayi da kansa yana tasbihi ga Allah,sun jima a haka sannan
ya fiddo wayarsa.

"Ubangiji ya tabbatar da lafiya" Ya fadi a taqaice yana kiran sabreen zuciyarsa ta
nauyaya da girman zatin Allah.

Tana kallo suna ficewa da yaran a dakin,sai ta samu kanta da gaza
dauke idanunta a kansu har suka kammala ficewa. Tafi qarfin awanni uku bacci bai
dauketa ba,tana jin kamar dakin nata ya koma kango bayan fitar tasu,kamar ba wani
abu daya rage a dakin sai ita kadai.

Abun mamakin shine,kwana tayi tana mafarkin yaran,cikin mafarkanta na
daren gaba daya sune kewaye da ita,harda wanda suke magana da ita,saidai ta kasa
bambance me suke fadi.

Ajiyar zuciya kawai ta dinga saukewa sabreen din tana tariyo abinda
fu'ad ya gaya mata na yadda ya shiga ya samu maamah din.

"Ya Allah.....ka jefa matsananciyar soyayyarsu a zuciyarta ninkin ba ninkin yadda
ta tsani mahaifiyarsu" Ta samu kanta da wannan addu'ar.
*_NAMING CEREMONY_*


Katafaren kuma qawataccen guri ne na alfarma,aka aka shirya sannan aka
tsarashi musamman saboda gabatar da radin sunan. Komai na gurin kusan fari ne,farin
ma irin qal dinnan me daukan hankali da kuma daukan idanu. Tun daga farkon shiga
gurin har zuwa ciki wasu irin manyan hotunan ne na jiraran design daban daban suke
welcoming naka.

Kana shiga gurin zakasan guri ne bana wasa ba.....guri ne da akayi
barin dukiya,irin barin da zai gaya maka ba'asan zafin kudin ba,don an nemesu a
sanda ya dace an kuma tarasu.

Komai a tsare yake,don guri na musamman aka tanada saboda ajjiye yaran.
Kowa xai qarasa ya gansu,me buqatar basu gift ko wani abu makamancin hakan amna da
huda suna kusa,don sune iyayen yaran gaba daya.

Cikin tsari aka soma gudanar da taron,sabreena maman yaran wadda ta
koma hajiya sabreen,tayi wani irin razanannen kyau cikin wani dan banzan lace da
aka warewa milliyoyin kudi aka bada order saqashi a india. Ba iya lace din jikinta
kawai ba......hatta da lace da atamfofi da manyan luxury warmers da aka raba a
gurin duka container guda akayi musu.

Tun kana lissafa adadin kayan ciye ciye da shaye shaye da aka tanada a
wajen zaka gaji ne kawai,don kuwa tsarin serve yourself kawai akayi,debi da
kanka,kaje ka zaba ka zuba koka aika a debo maka,ko ka kira daya daga cikin
ma'aikatan dake wajen ka bashi order din abinda kake da buqatar ci.

Guri na musamman aka tanadarwa jama'ar DUNIYATA,don a idanun sabreen
mutane ne masu kima mutunci da daraja,wadanda suka taimaka qwarai wajen bawa
dangantaka dama soyayyarsu gudunmawa.

A gurinne fannah ta gabatar da kyautar da BB ya yiwa takwaranshi,wato
kyautar sabon company dinsa na sarrafa auduga da fiddashi qasashen waje.....daukan
nauyin duka wani abu da ya shafi rayuwarsa,tun daga karatu lafiya sutura da
sauransu,yace kawai abbanshi ya zuba masa idanu,don shi aka haifawa umar din. Bama
umar duka ba.....dukkanninsu yana jinsu a zuciyarsa,saidai yace bazaiyi qarya ba
umar din na dabanne a wajensa.

Abba baiyi qasa a gwiwa ba shima ya aiko da nashi saqon ta hannun
amna,estate guda ne me dauke da gidaje dari ya mallakawa nasa takwaran. Ihu aka
dinga yi a wajen,saboda yadda abun ya qawatar da mahalatta taron,wato dai gasa ce
ta gasken gaske tsakanin kowa da takwaranshi. A sannan fu'ad din yana daga can
gidan hutawarsa,yana kallon yadda taron yake gudana kamar a gabanshi,ta hanyar
cameras da ya saka aka zuba sosai a wajen,aka kuma miqa ragamar monitoring dinsu a
hannun qwararrun security dinsa. Saidai duk da haka yaji yana sha'awar

Please Login or Register in order to submit comment