You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alamu sun nuna kai tsaye suna fita ne daga zuciyar ta?.

Sai daya tsayar da jordan cikin motar ya daidaita kansa,ya kalli
fuskarsa yaga ta koma ainihin mode dinta sannan yace suje. Bayason yaje da wani
sauyi ko kadan saman fuskarsa,don yasan abune da tana masa kallon farko zata
karanci hakan,shi kuma duka yau din yana buqatar kyakkyawan yanayi shida
duniyarshi,wadda yayi missing nata tsahon kwanaki biyar kenan.

Cikin hukuncin Allah JADDA MAJESTY JET ya sauka a filin tashi da saukar
jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake abuja.

Mintuna kadan kafin jirgen ya sauke matakalarsa a hankali,tsakanin
wasu mintunan kuma mutanen dake da iko da jadda majesty din suka fara fitowa.

Da farko wasu matane guda biyu masu baqar fata,giant dasu,sanye da
baqaqen abayas da mayafinta wanda sukayi rolling,sannan kuma suka manne idanunsu da
baqaqe glasses.

Mata biyun dake bayansu su dinma abayanne a jikinsu,saidai tasu ruwan
wine color ne. Daya janye take da wata qaramar luxury luggage,yayin da dayan ke
dauke da wata kyakkyawar jaka.

Kyakkyawar halittar dake takowa daga tsakiyarsu ta dushe kowacce diya
mace dake tafiya tare da ita.

Mistress ameenatu ahmad mrs muhammad jadda......the lady of the
house itace ke takawa d'ai d'ai cikin wani yanayi da zai tabbatar maka da cikar
kamala da nutsuwa gami da kammaluwar hankali da nutsuwarta waje guda.

Sanye take cikin wata Turkish gown ta wani lafiyayyen
material,rigar ta bude sosai daga qasa,armless ce butter color me adon gray color
da wasu manyan flowers masu ban sha'awa,wadda aka yiwa top gray color me dogon
hannu da kuma sarqarta a jikin rigar ta yadda basai ta buqaci wata spare sarqa ba.

Tayi rolling kanta da gray color din wani exclusive veil,qafarta na
sanye da wani high hill daya kasance mahadin qaramar handbag din hannunta da batafi
taci qananun abubuwa ba sai tsananin tsada da jakar ke dashi.

Rungume take da wata baby girl wadda ke sanye da gown armless fara
qal data kasance mahadin takalmin qafarta da kuma dan crown din dake saman kan
yarinyar wanda ya hana sassalkan dogon gashinta bazuwa zuwa sassan fuskarta.

Wani irin kamanni ne tsakanin ta da yarinyar na sak da sak.......abinda
kawai ya banbanta su shine kasancewar yarinyar 'yar kululluba da ita.

Ameenatu muhammad jadda kenan IFFA......shalelen family din
jadda....diya mace qwaya daya da suke da ita cikin villa din tasu. Chubby din
abbee......chubby din anni......kuma chubby din triplet da twins na jadda villa.

Cikin kyakkyawar nutsuwar nan tata Madame kuma duniyar muhammad jadda
wato ameenatu ahmad ke sauka da takalmin ta me tsini wanda zakayi tsammanin ba zata
ita tafiya dashi ba,saidai caf caf take takawa da abinta cikin sani kan ado da gayu
daya ratsa jini da jikinta gaba daya.

Wani fitinannen qamshi take fiddawa wanda ya huda jikinta,irin
qamshin da sai kazo kusa da ita kake iya jinsa a duk wani motsi da zatayi.

Dawowarta kenan daga qasar saudi Arabia,bisa gayyatarta da sukayi don
su karramata da lambar yabo da kuma girmamawa ta musamman kasancewar gidan
marayunta gida na farko da kaf nahiyar africa dama wasu qasashen qetaren babu koda
kwatankwacinsa.

Gida ne daya fara bawa yara feature me kyau......ya fara inganta
musu rayuwa da inganta mafarkansu bisa jagorancin me gayya me aiki muhammad fu'ad
jadda mamallakin kamfani guda daya da baida kishiya dake sarrafa gold da Diamond a
qasash kusan arba'in cikin qasashen da muke dasu a duniya sama da guda dari biyu.

"Karbeta najma.....tayi bacci" Sabreen ta fadi a nutse tana miqawa nanny dinta ita
gami da gyara rolling dinta daya dan cukuikuye.

"Sarkin rigima" Nanny din nata ta fada tana rungumeta a kafadarta

"Kunfi kusa,fadanki dana iffa ko waye ya shiga ma kunya zaiji" Sabreen ta fada tana
murmushi.

Murmushin daya samu isa ga idanuwan Muhammad fu'ad dake zaune cikin
mota,ya kuma kori Jordan ya saita madubinsa yana qarewa duniyarsa kallo abinsa.

Sam bata ganshi ba,bata kuma san yana mata kallon qurillar nan tashi
ba,duk da cikin jikinta tana jin kamar wani kusanci yana wanzuwa tsakanin zukatan
guda biyu.

"Welcome maa" Shine abinda dukka ma'aikatan da suka rako boss jadda suke fada cikin
rusunawa da girmamawa,yayin da ita kuma take amsawa cikin nuna kulawa da tambayarsu
aikinsu.

Abun yana bawa fu'ad mamaki sosai.....gaba daya ta zama tamkar wata uwa
tsakanin kowanne ruhi dake rayuwa cikin jadda's villa. Ba iya yaran gidan su huda
amna dasu saddiq ba......tsakanin kowa da kowa ma,muddin kana kwana kana tashi a
jadda's villa.

"Wannan tsadajjen murmushin rabonshi da akeyi ya isa haka please" Ta tsinci
lallausan sautin nan nasa cikin kunnuwanta a sanda ya fito daga motar yana bude
mata murfin motar yana kuma gyara babbar rigarsa da daya hannun.
"Wow" Ta fada da wani boyayyen sautin da labbanta ne kawai zasu gaya maka abinda ta
fada,tana fidda idanunta waje dukka a kansa.

"Muffin......ka koma exactly ranar da ka zama angon ameenatu sabreen.......sak irin
shigar".

" Har yau har gobe har kullum ma cikin taya kaina murna nakeyi da mallakar mace
irinki......ki taimakeni ki sakayamin kanki cikin motar nan kafin mazan dake
airport dinnan kaf su qarasa kallemin ke" Kai ta girgiza tana dariya sanda ta fara
takowa cikin jan aji.

"Hammana yaushe xai canza ne?baya kallon madubi yaga yadda ya fara zama babban
mutum?,babban mutum din daya ajiye yaran da sati me zuwa zasu kammala secondary
school dinsu?"

"Fu'ad bazai taba canzawa ba.....kishinsa da soyayyarsa game da Sabreen suna nan
kaman yau aka ginasu" Ya amsa mata yana rufe motar,ya zagaya ya shiga nasa side
din.


_wacce addua kuka yimin littafinnan yaqi kammaluwa a yau?_πŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯Ή


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽

*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*

*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*πŸ˜‚πŸ˜‚

Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*
*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*

*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin
aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ
wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN

08103155915𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 173


*_HUGUMA CLOSET ON TIKTOK_*

*follow us diaries*πŸ₯°πŸ₯°πŸ‘πŸ½πŸ‘πŸ½

https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1


173




Wani ajiyar zuciyar numfashi ya sauke yana lumshe ido gami da sauke
nannauyan ajiyan zuciya.

"Sai yanzu zuciyata zata koma aiki daidai......welcome home your royal highness" Ya
fadi cikin salo na girmamawa yana hada hannuwansa guri guda. Murmushi tayi tana
girgiza kai,kullum sabuwa ce a wajensa kaman yadda yake sabo a wajenta.

"Giya nake roohi......hayaty kulliha" Ido ya fidda waje yana tashin motar tasa.

"Wannan ranks din nifa bana gane musu sosai yanzu.......jira nake naga nan gurin ya
tasa" Ya fada yana taba lafaffen cikinta kaman bata taba daukan ciki ba.

Itama waro idon tayi tana kallonsa. Mamaki yake bata yadda har yanzu
'ya'ya basu isheshi ba,yara goma cas tara dukkaninsu maza mace daya?,me kuma yake
da buqata?.

"Muffin......fauzan fawwaz da fawad ba graduation dinsu next week immediately ana
gama bikin nadra da haneefa?". Dubanta kadan yayi sannan ya tada motar hankalinsa
kwance.

"What's that supposed to mean? And what's the point?......kin daina haihuwa?".
Ganin yadda yayi maganan yana nuna da gaske yake fadi,saita karya wuyanta tana
narke masa.
"Hamma......yanka sau hudu fa?...."

"Yanka hudun yana nufin kin gama?" Ya sake tambaya yana tsume fuska. Sosai tayi
calming down kanta tana saukar da kanta.

"Ni na isa?" Ta fada a sanyaye. Wani abu data lura dashi yana da bala'in son tara
yara,Allah ya taimaketa ya dinga bata bibbiyu har sau uku bayan ukun farko da
tayi,iffa ce kawai tazo ita daya abinta,shi yasa idan suka tashi tsokanarta suke
cemata me baqinjini,ita ba wanda ya rakota,su kuwa saida suka rako juna,duk da cewa
a zahiri kusan farinjininta daban yake,kowa yasan wannan,farinjinin diya mace cikin
yara maza.

Shurun da tayi ya sanyashi satar kallonta kadan sannan ya kauda
kai,bayason damuwa a tare da ita sam sam,don ta gama yi masa komai a rayuwa.

"Bani labari.....How'd the trip go?". Numfashi ta sauke tana son wadata fuskarta da
murmushi,saidai kafin tace komai ya sake magana.

"Banga mamana bafa.....a ina kika barta?"

"Tana hannun Nan najma(kaman yadda iffa din take kiranta)" Kai ya gyada

"I missed her so much......da safen nan abinci sam bayamin dadi idan na kalli gurin
xamanta naga bata nan". Baki Sabreen ta tura tana bata fuska.

"I don't know me yasa kakeson min kishiya da iffa ne.......zan bayar da ita fa?".
Ido ya waro kaman zai saki steering motar yana dubanta.

" What?,yarona ko daya bazan iya badawa ba koda cikin gari ne dani......in fact ma
ni koda mutuwa nayi ban yarda a rabamin yara ba bare ina raye".

"Mu ajiye batun mutuwar nan hamma....." Ta fada tana maida aljihun motar data bude
ta dauko mint sweet ta saka a bakinta.

"Komai ya tafi daidai hamma......kuma dukka lambobin yabo dana karramawar da suka
bayar naka ne....kaine ka cancancesu......ni 'yar tayi ce,Allah yakai kadan kabarin
abba.....sun saka kudade masu yawa a asusun gidan,duk da nace bamu da buqatar
wannan,amma sunce zasuyi don neman lada,sannan cikin daliban da muke yayewa duk
shekara,a dinga ware mutum goma,maza biyar mata biyar yearly zasu dauki nauyin
karatunsu har zuwa degree,har masters ma idan suna buqata har sama da hakan". Kai
yake jinjinawa,ya jima yana ayyukan lada dana alkhairi kala daban daban,amma wannan
din yafi kowanne yi masa dadi da qara masa walwala da nishadi. Uwa uba kuma wani
abu daya lura dashi,tun daya sanda gidan ya fara aiki dukiyarsa kaman amai
take,wani irin mahaukacin hauhawa takeyi,wani irin bangajejen budi yake qara samu
da shi kansa kai tsaye yanzun bazaice ga adadin abinda ya mallaka ba.

Ci gaba sukayi da tattaunawa shi da ita da wani irin yanayi da zai gaya
maka zallar soyayya da tausasawa da jin qaine ke wanzuwa tsakanin ruhi da zukatan
wadannan masoyan.

Suna isa ya karbi mamarshi ameenatu iffa,don ta farka a sannan. Ita
dinma da gudu ta nufoshi tana fadin.

"Miss you abbee...."

"Mamana.....My incomparable mother.....a mother without equal" Ya dagata yana
juyata abinsa,ba ruwansu shi da ita da al'ummar dake farfajiyar gidan,wadanda kusan
dukansu sun fito ne saboda tarbar Sabreen din,wanda wasu lokuta suke mata title da
THE MISTRESS OF THE VILLA.

K'ananun shekaru gareta amma ta zama babbar qarfi da yaji cikin gidan,duk
da ta tasamma shekaru arba'in daidai a duniya......amma tsananin kula da kai da
gyara jiki da kuma shan natural abubuwan gyara ga diya mace ya sanya zaka yita
daukanta a shakarunta ashirin da biyar ko da takwas take. Bugu da qari idan ka
kwatantata da su anni da suka kasance manya a gidan,ba laifi idan ka kirata da
yarinya. Kusan duk wani dawainiya da matsaloli da zaa kaiwa annin ta hana isarsu
Gareta,ballantana maamah da ba cikakkiyar lafiya gareta ba,yau da lafiya gobe babu.

Girman ya karbeta da kyau,yadda ta tafi dashi kuma cikin adalci da
mutuntawa ya sanya kowa yake biye da ita da tarin qauna.

Ko a wajen bata wuce ba sai data duba lafiyar duka ma'aikatan,fuad na
biye da ita dauke iffa yanata shan surutu,daya hannun nasa kuma handbag dinta ce.
Wannan dabi'ar tasa kowa dake jadda villa ya santa,tun suna kunya har ya zame musu
jiki. Ko zaman kwana uku kawai kayi cikin villa din zakasan cewa akwai wata
mahaukiyar soyayya irin ta hanta da jini a tsakaninsu.

Tare suka jera cikin gidan bayan gamawa da ma'aikatan yana tsokanarta.

"Hajjaju da kanta......yau masu gidan sun dawo kowa ya shiga saitinsa" Yayi maganar
yana maqalewa a bayan fuskar iffa yana mata gwalo. Murmushi ta saki tana mintsinar
hannunsa.

"Ka daina mantawa fa da cewa yanxun baban samari ne kai.....in suka ganka kana
tsokanar ummensu tabbas xakaji kunya".

"Suma sun jima da sanin cewa ba'a raba hanta da jini......yadda nakeso susan zallar
madarar soyayyar dake tsakanin abbeensu da ummeensu alhamdlh sun fahimta" Kai ta
gyada,ita kanta tasan da hakan,hakan kuma ya taimaka sosai wajen bawa yaran
qwaqwalwa da rayuwa me kyau,hakanan kuma suma sai suka tashi da qaunar junansu
sosai.

"Banga kowa ba cikin dukka yaran gidan nan ba.....sauban dai ancemin yana gurin
anni".

"Kin rigani fade ne......duk da kaman su nadra sun tafi siyayya dasu sahl samr
suhail duka sun bisu". Murmushi ta danyi tana jinjina kai,tana sake jin rayuwarta
tayi mata dadi idan ta tuna yau zata aurar da nadra da haneefa gaba daya,ragowar
abinda ya rage mata kenan take addu'ar Allah yakai mata ranta.

"Kaman yaushe zaku fara bikin nan?" Fuad ya tambaya sanda suke dab da isa sassan
maamah. Umarnin anni ne,duk sanda suka dawo daga wata tafiya ko kuma suka tashi da
safe zasu shiga su gaisa ita ta yafe zuwan farko,su fara zuwa wajen maamah tukunna
su dubata.

"Don itace me lalura,tafi buqatarku a akaina,ni da lafiyata har yanzu da sauran
qarfina.....kuma alhamdulillah zan iya yiwa kaina komai"

"Hamma abubuwa kadan zasuyi fa......zasuyi the day of qur'an da dalibai da
malamansu na mu'assas.......then zasuyi bridal shower.......sai waleema da anni ta
shirya shikenan,dukkansu suda mazan basason dogon biki". Kai ya jinjina,yana
jinjinawa yaran,suna da wani irin hankali da nutsuwa na daban,komai nasu moderate
ne,shi yasa ya yuwa rayuwarsu wani tanadi na musamman da ba wanda ya sani sai ranar
da aka daurawa kowaccensu aure.

"Ma sha Allah.......Allahumma barik" Ya furta suna sanya qafa makekiyar balcony din
da zata sadaka da falon.
Idanunta akan tashar saudi sunnah da suke hasko masallacin ma'aiki
tare da karanto hadisansa masu tsarki girma da alfarma,zuciyarta takejin tana
tsananin kewa da qishirwan gurin,kaman bata taba zuwa ba tunda take a rayuwarta.
Sukanje tana bin jama'ar gidan da suke da kebantattun lokuta da jirgin jadda
majesty jet yake jigilar kowacce halitta dake birnin jadda villa din bayan kowanne
hutun makaranta da za'ayiwa yaran. Wannan damar suke amfani da ita suke ziyartar
fauzan fawad da fawwaz dake karatunsu a madeena king Abdul'azee international
School wadda suka kammala kuma za'ayi bikin yayesu sati me zuwa.

Kaman saukar nannauyan dutse daga qirjinta haka taji sanda sukayi
sallama a tare,ta motsa bakinta tana amsa musu da sautin da ba'a fahimtar abinda
take fada sosai sai wadanda suke da matuqar ganewa kaman sabreen din,don shi kansa
fu'ad din sometimes sabreen ce ke gaya masa abinda tace din.

Idanunta ta janye a kansu tana maidawa kan yarinya ta biyu da Allah ya
jarabceta da masifar son yarinyar......yarinyar da duk gidan kowa qaunarta yakeyi
saboda kasancewarta jika diya mace qwaya daya kaf cikin jikokin gidan ashirin da
wani abu. Ameenatu iffa ta sakarwa maamahn murmushi tana zamewa daga jikin fu'ad ta
tsallako da gudu tayo wajen maamah.

"Har yanzu baki tashi kin fara tafiya ba?,kikace zaki fara tafiya kafin mu dawo?"
Ta fadi cike da quruciya cikin maganarta. Murmushi kawai maamah din ta
sake,yarinyar ta tattaka qafafun maamahn ta haye cinyarta tayi dare dare tana bata
labarin su hamma fauzan suna gaisheta.

Tayi kewar 'yan ukun sosai,su na dabanne a zuciyarta,duk da gidan cike
yake da tagwaye amma nasu qaunar daban yake. Har yanzu suna iya kira video call su
dukka ukun su sakata a gaba da hirarraki har sai sun sakata dariya sanna,har zaman
jiran kiransu takeyi kulli yaumin,koda basu kira ba zata sanya a kira mata su.

"Barka da warhaka maamah.......ya qarfin jikin?".

" Alhamdulillah " Yau sautin amsa gaisuwar sabreen din ya fita da kyau har sai da
sabreen ta daga kai ta kalleta a mamakance.

"Ya taro?" Ta fada da sarqaqqen harshenta.

"Alhamdulillah.....mun kammala cikin nasara"

"Allah ya taimaka" Ta sake fada da qyar tana fuffusgo kalmar.

"Ameen" Sabreen ta amsa tana sadda kanta tana tattalin hawayen farincikin dake son
ballewa cikin idanunta.

Kamar yadda maamah ta zata din,sabreen din saidata tabbatar komai yana
tafiya daidai a sashen,daga masu kula da ita har kalar abincin da ake bata sannan
suka wuce sassan anni.

Suna zaune da mutuminta sauban a courtyard din da ya zamana shuru
saboda fitar duka yaran da rashin motsinsu wanda anni batasan me ya kawo hakan ba.

Murmushi ya sakarwa ummeen nasa da abbeen nasa,ya zare headphones din
ya ajiye ya tako da nutsuwar nan tasa yana fadin.

"Sannu ummee.....abbee sannu" Ya fada yana kamo iffa wadda tayi tsalle ta daneshi.
Akwai sabo sosai tsakaninsu,don wani irin sassanyan kulawa yake bata ta hankali.

"Anata karatun sauban?" Sabreen ta fadi bayan ya gama gaidasu,fu'ad ya dora
hannunsa saman kansa. Yana jin yaron sosai a jininsa saboda yadda yake da maitar
karatu,yana da buri sosai akanshi,kowanne yaro nashi yana bashi karatu daidai da
abinda ya fuskanci yafi karkata akai.....kaman yadda ta fannin neman kudi ma yayi
alqawarin zaibar kowa yayi kalar neman kudin da yafi sha'awa muddin bai sabawa
addini ba.

Da wani irin alfahari qauna da soyayya anni ke kallonsu a gabanta,har
suka gama gaisawa suka fara taba hira

"Kije ki huta takwara,anjima akwai general dinner a babban dining room na gidan
nan,sai a qarasa hirar a can" Murmushi tayi a kunyace sannan ta miqe,fu'ad ya
tayata da jakar suka rankaya dukkaninsu wannan karon har sauban suka fice.

Tun kafin sukai ga bude qofar sassan taga kaman parlor din farko yayi
duhu da yawa,bangaren sitting room ba ba wani wadataccen haske. Tanata so tayi
magana amma kuma Allah bai bata iko ba har sai da suka shiga parlor din.

Duduun ba wani haske,abun da ya basu mamaki kenan daga ita har fu'ad
din,ta bude baki zatayi magana fitilan farko ta kama. Harafin H ne tafkeke,mamaki
ya cikata,zatayi magana A ta bayyana,da wani irin sauri P ta bayyana a jejjere
ragowar suka kama suka bada cikakken sunan HAPPY WEDDING ANNIVERSARY.

Baki sake take kallon harufan,ta juya a hankali da zummar yiwa fu'ad
magana ko yaga abinda take gani,sai gaba daya wutar falon ta kunnu hade da wasu
abubuwa masu walwali da suka soma bude kansu da kansu daga jikin fitilun suna
watsuwa a kansu,lokaci guda kuma muryoyin zuria'ar yara na jadda din ta hadu wajen
fadin

"Happy wedding anniversary" Sai a sannan suka ankara da komai da tsananin mamaki.
Ameen,Amaan,hilal dan huda na fari,naseem dan amna na fari,sai yaron wajen farouq
na farko shima Aleem,sai tagwayen sabreen na biyun masu bin su ameen Aabid da
Aadil,sai wasu twins din masu binsu Aadil din,irfan da farhan wadda ameenatu iffa
ita ta zama cikon ta gomansu.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA
KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA
IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE
SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA
A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*



*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
*_BGAWO'S KITCHEN_*


ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 174

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



174



Yara ashirin da daya ne idan ka dauke mutum biyar dasu nadra suka fita
siyayya dasu.......sai fannah da huda dake tsaye a bayan yaran da alama su suka
tayasu hada wannan surprise din. Inda Allah ya kawo ma sauqin abun amna bata
nan,tare suka fita siyayyar dasu nadra tabbas da abun sai yafi haka.

Kasa magana sabreen tayi,harga Allah tana sane da yau dinne suka cika
shekara goma sha shida da aurensu,amma bata kawo zatayi wani abu da wani zai gane
ba illa tsakaninsu ita dashi,sai gashi yaran sun rigata aiwatar da komai.

"Ku ko?" Sabreen ta fada tana nuna fannah da huda,fanna din da amnar da dukkaninsu
zuwa yanzu tana jinsu tamkar uwa daya uba daya suke. Tana nunasun da yatsa tana
murmushi sai kuma kukan farinciki ya barke mata,ta aza kanta saman kafadar fu'ad
din tana matsar qwalla.

Irin wannan soyayya da suke gwada mata batasan wacce iri bace,bama ita
ba.....kusan dukkaninsu ba zaka tantance wane da wane ga daga inda suka fito ba.
Rankatakaf jikokin gidan dama iyayensu kallon uwa suke mata,kuma hakan baya rasa
nasaba da yadda ta riqesu kaman ciki dayan suma fito.

A cikin yaran ba wanda bata taba rainonsa ba,duk itama tata
bataliyar,duk kuma da cewa kusan kowanne yaro yana da nanny dinsa a gidan,sai wanda
suka kai shekarun girma irinsu ameen sannan ake barinsu su koyi rayuwa da hidimar
rayuwar data zamewa kowa ya koyi yiwa kansa.

Idanun yara kawai ya hana ya rungumeta,amma qasa qasa yake fadin.

"Karki bata fuskarki,karki kashe mana farincikin yau" Ya fada yana dan bubbuga
bayanta.

"Kita fatan muci gaba da irga wadannan shekarun tare" Abinda ya rada mata kenan.

Qaramin walima akayi a gurin da kayan maqulashe kala kala,kuma abunda
ya bata mamakin shine,koda autar gidan iffa wadda tare suka shigo gidan sun tanadar
mata gift din da zata bawa daddy jadda (yadda gidan suke kiransa kenan in general
idan ba'a sassansa bane).

Farinciki da walwala ne kawai ya wanzu a gurin,inda daga qarshe dai
bata haura samanta ba kota wuce sassanta ta lalace a nan tana tsakiyar family din
nata suka zarce da hirarrakin bikin da zaa fara jibi jibi.

Wayarta ta ciro da zummar kiransu nadra taji inda suka dade haka da
yawa sai taci karo da tarin miscal din jadda. Ta zaro ido tana mamakin tun yaushe
yaketa kira bataji ba?,saiga shigowar wani kiran nasa.

"Sabrrrr" Kawai ya fada a narke,take ta fahimci yana buqatarta a kusa dashi.

"Banda abun hamma.....awa daya kawai ya rage ayi magriba fa?" Ta fada cikin mita
tana tura katafariyar qofan master bedroom dinshi.

Bata gama ajiye qafarta taji an ficikota ciki,a zafafe ya manne
bakinsu guri daya ba tare daya jira komai ba.

Har kullum har ko yaushe har kuma abada mantawa takeyi da shekarun
dake wuyansu idan suna tare da jadda din. Wani irin mutum ne

Please Login or Register in order to submit comment