You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da cin abincinsa yana kuma morewa kallon duniyarsa. Kaman
bazaice komai ba....kaman bazai amsa ko ya sake magana ba......har ambassador ya
fara sarewa gami da fidda rai kafin yace.

"Zabin dawowar dukiyarka qwaya daya ne tak........tsaffin kudaden qasar nan da ka
danqaresu a France.......zamuyi yarjejeniyar dawo dasu gida kuma qasata Nigeria don
amfanin al'ummar qasar". Wani razani ya sake kama ambassador,wanne irin mutum ne
fu'ad din?,kamar wani maye me gani har hanji?,kudade ne masu ciwo nauyi da yawa da
yayi imanin koda iya su kadai iyalinsa suka tsira sun rabauta,amma har ya akayi ya
ankara dasu?.

"Ina fata kana saurarena?" Fu'ad ya tambayeshi yana cirar tissue yana goge bakinsa
don abincin ya isheshi haka.

Sai daya goge gumin fuskarsa da habar rigarsa sannan yace.

"Ina jinka......na fahimta"

"Good......secondly diyarka......rashin kyautata tarbiyyarta wannan matsalarka
ce.....damuwarka ce.....haduwarka da Allah kadai ya isheka barazana.......tayi
attempting kasheni......inaso ta gaggauta fita da kanta media television da
magazines ta tabbatarwa duniya da tayi yunqurin aikata hakan,tayi apologize
nawa......tayi na matata.....ta tabbatarwa da duniya cikakken mutunci da darajar da
iyalina ke dashi.......wannan muqulli ne kawai na budewar daskararru da kuma
qwatattun dukiyoyinka......hukuncin yunqurin kisan kai kuma ita da
hukuma.....sunsan matakin da yafi kamata su yanke a kanta".

Ba fareeda kadai ba.....hatta da sabreen hukuncin ya mata nauyi,tayi
zaton iya hakan da zatayi ya wanke duk sauran laifukanta...

"Amma sir.......na dauka duka hakan zai wakilci kowanne laif......"

"Khaleed!" Fu'ad ya kirashi a tsawace cikin fushin da har sabreen dake zaune a
wajen sai data daga kai tana kallonsa,tana kallon yadda kamanninsa ke sauyawa
alamun bacin rai ya fara tasiri a zuciyarsa.

"Magana ake ta kisan kai bisa ganganci da niyya......magana ake ta bata mutunci da
daukan hayar gidajen jaridu suyi batanci ga iyalina......kasan nawa ta kashe don
kawai a buga sunan matata ta sunna da sunan KARUWA?,waye yake bata kudin?,a ina
take samosu?,a gaban waye take dukka kalan rayuwar da taga dama?......wannan
hukuncina ne ba wai shawara bace ko alfarma.....kana da right na cewa ba zatayi ba
gaba daya......wannan ya rage naku.....dont contact me again indai akan wannan
issue dinne.....i finalized the matter"

"Please sir......please....."

"Khaleed,Not my problem to solve......Could you please stop calling me?". Shuru
ambassador yayi,ya tabbatar ba wani abu da zai sanya fu'ad canza wannan hukuncin
nasa,abinda ya bawa fu'ad daman yanke kiran yana jan wani dogon tsaki kaman zai
tsinke harshensa.

A tausashe ta karbe wayar,ta sakata a DND mode ta ajeta gefe. Kamo
lallausan tafin hannunsa tayi ta saka cikin nata tana lalubar qwayar idanunsa,cikin
nasara ta samosu,saita kafeshi da idanunta tana kallonsa tana kuma murza tafin
hannun nasa.

Cikin minti biyar ya sauke wata nannauyan ajiyan zuciya,abinda ke
tabbatar mata ya samu relief na bacin ransa. Hannunta ta dora saman cikinta tana
nake fuska a shagwabe.

"Suna tsorata sosai idan abbee dinsu yana cikin irin wannan fushin......sunce na
bashi haquri,na gaya masa komai me wucewa ne,komai watarana zai zama sai labari".
Murmushi ya subuce masa yana lumshe idanunsa,ya saka hannunsa ya dagota,ya dorata
saman cinyarsa,tura hannunsa yayi saman cikinta a nutse ya aza tafin hannunsa akai.

"Dukiya jarrabawa ce me zaman kanta....kaman yadda talauci take shima jarrabawa
ne,duk wanda Allah ya jarrabi bawa dashi akwai nasa kalan qalubalen.....ki fadi
musu daddynsu yana nan yana fighting akan yadda zasu rayu cikin aminci ba tare da
sauran qaya ba akan hanyarsu.....i love them more than i love myself....."

"I hope I'm still your number one?" Ta fadi a narke tana kyabe baki. Dole ta sanya
wani murmushi me sauti ya subuce masa,ya kama kumatunta yadan riqe yana girgizawa.

"You're filled with jealousy......madam.....ke din DUNIYATA ce fa gaba daya".
Murmushi tayi yana boye fuskarta a kafadarsa.

" Kiraminsu Musaddiq" Ya fada yana komawa normal mode dinsa. Zamewa tayi a jikinsa
a hankali ta miqe,ta taka tana fita zuwa parlor din.

Dukkansu suna zaune,kowa kusan wayace a hannunsa yana dannawa. Farooq kuma
ya koma amsa waya. Rusunawa sukayi suka gaidata cikin girmamawa,ta amsa musu da
danjin kunya da nauyi sannan tace musu.

"Hamma yana kiranku" Miqewa sukayi suna wucewa ciki,banda farouq daya daga musu
hannu alamun yana zuwa. So samu su shiga ciki duka ta zauna ita a nan,don wala'alla
wata magana zasuyi data shafesu,to amma farouq yana nan,ita kuma yanzu kunyarsa
takeji,dole ta juya ta koma dakin.

Yana zaune still saman kujerar,ya miqe qafafunsa hannunsa da cup din
ruwa yana sha. Gaidashi sukayi shima cikin girmamawa kaman yadda suka saba,ya jiye
glass cup din yana amsa musu.

"Anni bata shigo ba?" Ya tambaya yana dubansu.

"Eh sai zuwa anjima kadan,abba ne yadan tashi da ciwon kai".

"Subhanallah,amma ba wanda ya gayamin a cikinku?" Ya fada cikin dan nuna bacin rai.
Idanu kawai suka hada kowa ya sadda kansa,kota yaya zasu gaya masa bayan ko ganinsa
basu samu yi ba.

waya ya dauka ya kira abban,suka gaisa yaji jikin bawai tsanani ko yawa
yayi ba,yace suyi xamansu yau su huta,tunda komai yana tafiya lafiya
alhamdulillah,sannan sukayi sallama ya aje wayar yana dubansu.

"A cikinku akwai wanda yayi magana da wani cikin abokai ko 'yan uwa sanda zamu baro
madeena mu sauka a nigeria?". Daga kai sukayi suna dubansa,don tambayar tashi ta
musu wani iri. Kai ya jinjina musu.

" Eh ina nufin ko a hira ba wanda ya bawa wani full details na ranan dawowarmu da
inda zamu sauka?"

"Full details?" Musaddiq ya tambaya yana kallon hamman nasa. Kai fu'ad ya jinjina
yana maida hankalinsa a kansa.

"Eh" Fu'ad ya jaddada masa.

"Akwai hamma" Musaddiq ya fada abinda ya faru a wancan ranar yana dawo masa. Ido
fu'ad ya lumshe sannan ya budesu.

"Waye?" Ya tambayeshi kai tsaye.

"Maamah ta bani wani number na tura mata details din.....ban kawo komai a raina ba
hamma......ban kuma yi tunanin akwai wata matsala da hakan zai haifar mana ba" Ido
sosai ya zubawa musaddiq din,yana jin kanshi ya masa nauyi da ambatar sunan maamah
a lamarin. Tsoro ya kama sha da fargabar kada sunanta ya fito cikin jerin sahun
sunayen mutanen da suke da hannu a faruwar al'amarin fa.

"Me yasa zakayi haka musaddiq?......me yasa baka kiyaye wasu abubuwa?,kana tunanin
ni dakai saddiq farouq amna dama duk wanda yake under jadda family ordinary human
ne?" . Shuru yayi jikinsa yana yin sanyi. Tun sanda abun ya faru wannan abun yake a
ranshi,jiki da zuciyarsa duka suna gaya masa akwai alaqa tsakanin abun da kuma
wancan address din daya bada,wannan ya sanyashi tilastawa kansa zama tuno digits
din daya turawa address din,ya kuma sake zaunar dasu tsaf cikin kansa.

"Baka riqe name din dake jikin contact din ba....koda bincike ne ta yaya kake
tunanin za'a iya yinsa?" Fu'ad dake kallonsa da takaici ya fada.

"Na riqe digits din...." Shuru ya danyi yana ci gaba da kallonsa

"Really?" Kai ya jinjina masa,sai ya waiwaya ga saddiq.

"Ya baka digits din ka turawa saleem.....kace masa injini" Ya fada yana maida
bayansa jikin kujera yayi relaxing.

Wani irin bacin rai ne yake ratsashi,maamah itace silar faruwar wannan
abun?,to hadin baki sukayi da fareeda kenan wajen kasheshi ko goyon baya ta
bata?,hakan yana da alaqa da hallarar kowa a asibitin da nuna zallar damuwarsa a
kansa amma banda ita?. Kanshi ya samu da girgizawa,yana jin cewa sam maamah din ba
zata aikata haka ba.

"Amma ta taimaka wajen kauda abbanku daga duniya?" Tambayar da tazo daga qasan
zuciyarsa kenan,ta kuma sake taso masa da wani irin bacin rai.

β˜…A hautsine take duban mahaifin nata bayan ya gama gaya mata hanyar mabudin
arziqinsa da yake hannunta,bisa tsari da kuma dokar da fu'ad ya bayar.

"Yanaso yayi humiliating dina ne abba......ta yaya zan fita gaban 'yan jarida na
tonawa kaina da kaina asiri?....hakan kuma ba yana nufin na wanke kaina da kaina
bane?,tamkar kenan na bawa shari'a daman yankemin hukunci da daukan mataki a kaina
ta sassauqar hanya?" Ta fada tana jin cewa aikata hakan wani abune da bazai yuwu
ba.

"Kina tunanin kina da wani sauran amfani a wajena ne fareeda muddin dukiyar dana
kwashe shekara da shekaru zata salwanta ta sanadinki?......ruwanki kimin hanyar
dawowar arziqina nasan hanyar xa zaki samu Sasaaucin hukunci.....ruwanki kiqi ni
kuma da hannuna zan miqawa hukuma ke......daga rana irin ta wannan lokaci kuma ki
tabbatar na cireki daga jerin 'ya'yana.....sunan.Khaled mustapha kuma ya saraya
daga wuyanki.....na haramta miki amfani dashi haramtawa na har abada".

"Bazanyi abinda yace ba daddy.....hakanan kaima dukiyar ka zai dawo hannunka" Ta
fada tana rarumar wayarta.

Number maamah take nema,hanya guda daya tilo da take tunanin zatabi don
samun warwarewar komai.

Daidai lokacin da mota ke tsula gudu da ita saman kwalta,hankalinta
yayi nisa yayi kuma zurfi a tunanin tun sanda ta baro wajen boka. Kora yayi mata
fata fata akan kada ta sake zuwa masa muddin da maganar data shafi taurari biyu ne
sabreen da fu'ad. Ya gama aiki a kansu har abada saidai ta nemi wani.

Sanda ta lallabashi da batun wata buqatar daban tazo da ita ba irin ta
baya ba.....buqatarta dankwafar da cikin sabreen yayita zama a mararta ba tare daya
girma ba bare a haifeshi,wannan kuma zai zama silar da zai zama karo na farko kuma
na qarshe data samu ciki da fu'ad din,a sanya masa shakka kan qaryar ciki tayi dama
tun asali.....maganar rabuwarsu kuma ita zataji da sauran.

Har ya soma buga qasa yayi wani zabura da saida qoqunan gabansa gaba
daya suka hantsila,yaja baya yana gurnani da wasu surutai kafin daga bisani ya
dubeta.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 131


https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX


131


"Kinsan aikata hakan daidai yake da kiran mutuwarki da kuma gaggauto da
ajalinki tu lokacin mutuwarki baiyi ba?" Sosai abun ya daure mata kai itama,tana
kuma buqatar qarin haske.

"Kamar yaya?,ban fahimta ba?". A fusace yake.magana wannan karon fiye da fusatarsa
ta dazu.

"Wannan yaran da suke cikinta......bake bama......duk wanda keda qudurin cutar
dashi to tabbas ajalinsa yake kira......fiddasu daga mahaifarsu ko hanasu wanzuwa
suyi rayuwa irin ta kowanne jariri kuwa,daidai yake da kiran ajali yayin da yake
nesa da ruhi.....ki fita daga harkar wadannan taurarin......suna dab da karo da
naki taurarin.......tazarar dake tsakaninku kadance,faruwar hakan kuma daidai yake
da LALACEWAR RAYUWARKI!.......SAURA QIRIS!.....KI KAUCE KI BASU HANYA.....BA WANI
ABU ME CUTARWA DA YA ISA YA TARE HANYAR SHAWAGINSU!" ya fada a tsawace yana nunata
da yatsa.

Tashin hankali!,kanta taji ya wani irin sarawa.....muddin ya kasa
mata wannan aikin duk duniya bata jin akwai wanda zai iya yinsa

"Kayimin rai.....zan ninka maka abinda ya kamata a......"

"Dakata!" Ya fada a gigice.

"Wannan aikin ba kudi yake buqata ba.......aiki ne na tsira da rai........ran da
muddin aka barshi ya dulmiya babu me iya fitowa dashi........KIBAR DA'IRATA HAR
ABADA....KARKI SAKE DAWOMIN DA MAGANAR TSARARRUN TAURARI BIYU".

Wannan tunanin yana mata shawagi kiran fareeda ya shigo,ta saka
idanunta akan kiran da wani irin yanayi,mamaki ya sanya batayi wani dogon nazari ba
ta daga kiran tana sakawa a kunnenta.

"Ina kika shiga fareeda..... Ko kina shirin janyewa ne saga qudurinki?" Ta fadi
tanajin kamar idan ta hada kai da fareeda din nasara zata zo mata da gaggawa cikin
sauqi,dole tana da buqatar me tayata wannan yaqin.

Ba kalar neman da bata yiwa zuwaira ba amma ta kasa samunta......duk
inda take tunanin idan taje zata sameta ta aika ba labarinta,abun yana daure mata
kai.

"Ban fasa ba.....kuma sauka daga kan nufina ba.....hasalima tsakiyar aikin da
nakeyi aka samu matsala da kuskure". Kanta ya sake sarawa,ta zauna sosai tana riqe
wayar a kkunnenta sosai.

" Me ya faru kuma?". Sai data gyara muryarta da kyau sannan tayi magana.

"Nasa anyi attacking na matarsa.....cikin rashin sa'a aka sameshi.....yanzu haka
anyi freezing komai na dukiyarmu......yasa kuma an dakatar da dad daga
muqaminsa......yana maganar saina fito nayi iqirarin nina aika a kasheshi.....na
bada haquri a media sannan zai sakar mana komai.....abinda yasa na kiraki.....inaso
ki sakashi ya warware komai......ya janye kuma komai.....muddin wani abun ya sameni
duk wani mmuradinmu zai tsaya cak.....don ina da babban shirin da zai kauda mana
damuwoyinmu ni dake gaba daya".

Dif maamah din tayi,kwanyarta suna juya mata maganganun fareeda. Haka
kawai taji hankalinta kamar ya kasa kama maganganun fareeda din,kaman akwai wani
abu da ba daidai ba.

"Fareeda.....bansan qasar da suka kaishi ba.....yanzun haka matarsa ke dauke da
cikin da nakejin gwara na nakasa da wanzuwarsa a tare da ita.......bansan inda suka
ajeshi ba".

"Taiwan......yana wani asibitu na Taiwanese a taipei......ki kirashi tabbas zaki
sameshi".

" Ki dakaceni tukunna.......fu'ad baya cikin mazan da akewa gaggawa haka kuma su
karba da sauri".

"Me kike fada mariya?!" Fareeda ta fada a tsawace,a yanayin da take ciki bata
qaunar sharhi qarin bayani ko dako......isar da saqonta da cimma burinta kadai take
da buqata.
"Kinsan a wanne yanayi muke ciki da har zaki saka bataun JIRA a wannan
zancan?......kinsan kowacce daqiqa guda da zata shude muna sake shiga hadari ne
nida duk wanda ya dangancemu?......buqata ta gaggawa ce......kiyi hanzarin dakatar
da d'anki daga aikata abinda yayi niyyar aiwatarwa......idan kuma ba haka ba to
tabbassss bazan shiga uku ni kadai ba......zan shaidawa duniya da hannunki a cikin
komai......dollars dina da kika karba kuma.....kada ki manta akwai evidence na
amount account details date da time na yadda na saka miki komai.....saiki shirya
maidosu" Daga wannan fareeda ta yanke kiran.

Wani sarawa kan maamah taji yayi......lallai idan fareeda ta ambaceta a
wannan badaqalar ba abinda zaya hana mutane aminta dasa hannunta.....musamman
mutanen dake da issue da ita irin ameenatu da sabreen.....sabreen din da har yanzu
tana qarqashin awa saba'in da biyun data bata,awannin da batasan ta yadda zata
fiddo fu'ad ba banda yanzun da kiran fareeda ya sanya tasan inda yake.

Karasashinta ya dawo da wani irin sanya ran lallai tana da
dama.....damarmaki har guda biyu.....damar sanyashi ya janye kaman yadda fareeda ta
buqata,a yadda duk wata kadara tata data mallaka ta narke daga auren fu'ad da
sabreen......da kuma neman hanyoyin da zata rabasu batajin tana da adadin dollars
din da zata maidawa fareeda kudinta.

Lalubar number dinsa ta fara yi tana jin yadda kanta yaketa sara mata
da ciwo. Kira uku tayi,ana hudun sabreen data dauke wayar don ya sake samun nutsuwa
taga kiran.

"Maamah" Da sunan yayi serving ba kaman sunan anni da yake suna na daban cikin
wayar tasa ba. Qaramin murmushi ta saki,sannan ta taka zuwa bandaki a hankali ta
maida qofan ta kulle.

"A yanzun yana buqatar hutu daga dukkan wata takura da zullumi na rayuwa.....yana
buqatar yin nesa da kowacce kalar damuwa" Kalaman sabreen kenan da suka sauka a
kunnenta suka sanya wayar hannun nata kusan subucewa daga hannun nata,kanta kuma
yayi wani dummmm na wucin gadi kafin ta tattara qarfin halinta waje daya.

Magana takeson mata amma ta kasa furta komai,wacce irin HATSABIBIYA ce
yarinyar?,a yanzun haka kenan tana taiwan tare dashi ta barta bata cikakken bacci?.

"Duk yadda kike tunanin cin nasara.....kina yiwa kanki qarya ne.....ni mariya a duk
sanda nayi nufin cimma nasara akan wani abu.....ba wani wanda ko wani abu daya isa
ya dakatar dani daga wannan nasarar....."

"Sai ubangijin da yayi ni yayi ki,ya kuma halicci nasarar........shin da gaske ne
kuwa?.....anya ke kika haifi muhammad da musaddiq?" Sabreen tayi mata tambayar da
bata taba tunanin zata iya mata ita ba....amma yau ta tsinci kanta da tambayar
tata.

Wutace tsaf ta daukewa maamah tana jin jiri yana kamata daga zaune.

"Idanma ya tabbata ke dince.....to ki saka a ranki kin haifawa masoyansu ne
su.......sun tashi daga mallakinki.....sun tashi daga ababen kulawarki,ubangji ya
musu musaye da masoyansu na haqiqa....."

"Ki dakata da wannan shirmen......ki hadani da d'ana dashi nake buqatar magana"
Sabreen bata tsaya sake sauraronta ba ta kashe kiran,ta kuma kashe wayarma gaba
daya.

Iska me zafi ta furzar daga bakinta,mamakin maamah yana sake kasheta,a
yanzun dai ya tabbata dari bisa dari......dukiya takeso......arziqin take da buqata
bawai 'YA'YAN BA.
Mummunan tashi hankalin maamah yayi,ta soma sake gwada kiran number
amma a kashe.

"Allah ya tsine miki......muddin banyi sanadinki ba a rayuwa nayi asara" Shine
abinda maamah take maimaitawa sanda take yunqurin sake maimaita kiran number fu'ad
din ana gaya mata a kashe layin yake.

Sam Allah ya dauke mata basirar kiran musaddiq......tunaninta yafi
karkata ga ME ZAI FARU bayan awannin da fareeda ta debar mata tana jiranta?.

*_Hajja_*


Tun sanda suka gama wancan wayar da maamah ko sau daya taqi bawa
kwanyarta hutu na neman mafita da hasashen abinda zai wakana......hakanan ta gaza
dauke kunnuwanta daga jiran isowar jami'an tsaro gareta suyi awon gaba da ita kaman
yadda take hasashe,duk kuwa da bokanta ya shaida mata ba wanda ya isa ya shigo ya
kamata muddin ta tabbata a cikin gidanta,saidai idan qafa ta sanya ta fita.

Ta sake amanna da maganarsa ganin kwana dayar har biyu shuru,sai wannan
ya bata daman zama tana tunanin matakin da zata dauka akan maamah.

Laila itace burinta......laila da ita take kwana take kuma
tashi,yantuwar laila shine muradinta kafin ta waiwayo ga hanyoyin tozarta mariya.

Tsai tayi da ranta tana bitar kalaman da sukayi musaya a wayarsu ta
qarshe,ta tsinci tsoro kadan da razana a muryar mariyan,ta yiwu akwai wani abu
daban da batasan dashi ba.....ta yiwu ba mmariya bace ta fidda hotonsu.....ta
tabbatar tunda hoton maqale yake da nata....duk da fuskarta bata fito sosai ba amma
zai wahala mariyan tabari ya fita. Wata shawara ta tsirga mata.....taji a wannan
karon ta shirya ayi tone tone tsakaninta da mariya muddin autarta zata dawo cikin
hayyacin rayuwarta,wayarta ta dauka kanta tsaye ta fara kiran layin wayarta.

Kamar ana jira ta tsagaita da kiran fu'ad wani kiran ya danno mata
waya. Hajja harira,ko kadan kiran bai sakata fargaba ba har sai data daga wayar
suka fara musayar magana.

"Da baki wahalar da kanki kina tambayata meye yasa nayi kiranki ba......fuskata da
sunana sunyi tambari a bakunan al'umma da kuma kowacce jarida......kina tunanin
akwai wani faruwar abun kunya da zanyi shakkar fitarsa?....abun da koda ya fita
tawa kunyatar qarama ce akan ta mahaifiyar data sadaukar da mutuncinta da rayukan
'ya'yanta saboda ta mallaki abun duniya?". Kaman babu jini cikin jikin maamah haka
takeji......a yanzu takeson solving wannan issue din batabataso hajja ta afko cikin
wannan da'irar.....tanaso a sanda hajja zata buqaci a fafata yaqin ta gama da issue
din fareeda dana sabreen harma da ameenatu,a sannan zata gwadawa hajja yadda ake
wasan kura da rayukan dan adam.

"Hajja......karki tunkari.fadan da bazaki.iya qarasashi ba......ki lallaba
masarautar cikin gidanki dake gareki,ki qarasa mulkinki sannu a hankali,ki kuma
jirayi randa naga damar 'yanta miki d'iyarki"

Wata dariya data saka numfashin maamah tsaiwa na wucin gadi ta
saki,sai da tayi me isarta sannan tace.

"A a'ah......mariyatul kibdiyya......wai ni bakisan abokin mutuwa nake nema
ba?....,to bari kiji.......daga yau zuwa gobe na baki ki maidomin da d'iyata gaba
na,ko kuma wannan boyayyar fuskar dake gefena a bugun shafin farko na jarida da
kowa keson ganinta ta bayyana kanta da kanta.....aikin fahimta ko?" Daga wannan
hajja bata jira komai ba ta kashe kiran.

Daga zaunen da take amma sai taji tana jin jiri.......me yasa komai
yake neman ya kwabe mata lokaci guda?,kowa adadin awanni yake deba mata cikin
umarni da kuma gadara?,wai me yake faruwa ne?.

Daidai nan taji muryar driver dinta yana fadin.

"Mun iso gida.hajiya" Kanta ta daga tana kallon gidan,batasan sanda suka iso ba
kaman yadda batasan sanda suka shigo gidan har ya iso parking lot ya tsaida motar
ya kuma kasheta ba.

Hannu ta saka ta bude murfin motar,a hankali taja jikinta tana fita a
motar,saidai ko Cilakken tsaiwa batayi ba ta yanke jiki ta fadi a wajen hankalinta
yana gushewa.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 132


https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



132


Da sallama farouq ya shigo,sabreen dake tsugunne gaban fu'ad din tana
gyara masa nails dinshi na qafa duk da fes suke.....amma tsabar bayason tayi nesa
dashi ya tsiro mata aikin ta matsa kadan tana amsawa.

"Sannu da aiki addanmu" Ya fada yana jawo kujera ya zauna yana dubanta. Murmushi
tayi a kunyace tana amsawa.

"Yauwa BB....sannu da qoqari....Allah y qara zumunci.....ya saka da alkhairi".

" Ameen dai.....dama wani abun saboda ke akeyinsa ai ba don mutum ba" Ya qarasa
fada yana jifan fu'ad da harara wanda yayi relax abinsa jikin kujera kaman badashi
yake ba.

Miqewa tayi da zummar basu guri.

"Kin gama ne?" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi. Kai ta girgiza tana satar kallon
farouq tana masa alama dashi. Ya fahimci me take nufi amma ya basar,don haka ta
buda baki.
"Zanyi waya dasu huda kafin ku kammala". Agogo ya kalla da narkakkun idanunsa.

" Minti goma ki dawo ki qarasamin"

"Okay sir" Ta fada a girmame ta qarasa tana daukan wayarta ta fice.

Farouq bai jira ta kammala fita din bama ya soma fesar da abinda ke
ransa.

"Zuwa nayi na maka sallama". Dariya ya taso ma fu'ad amma ya danneta,sai ya miqe
sosai ya zauna yana ware idanunsa akan farouq

"Ina zaka kuma?"

"Gida zanje ayimin aure.....bazan zauna na mutu na tashi a gafiyar lahira ba".
Wannan karon dariya ta gasken gaske ya bawa fu'ad,har wanda ke parlor din zai iya
jin sautinta,kalan dariyar daya jima rabonshi da irinta.

"Bafa inda zakaje dude.....ko zaka hadiyi zuciya saika gama jinyata ka cikasa
ladanka".

"Lada irin naka ne banaso......ina samun ladanka kaima kana samun naka ladan
ko?....bazan iya ba....ni yanzu wallahi kafi qarfina" Kai ya jinjina yana shafa
sumarsa. Da gaske yasan farouq aure yakeso.....kuma koda shine yake a matsayin
farouq din yana sanya auren mace kaman sabreen bayajin zai iya haqurin da yayi
ma.......baiga abinda zaiwa farouq ba sama daya tabbatar da aurensu a daidai date
din da aka saka.....baya jin zai yarda ya zama silar daga bikin farouq koda na
kwana daya ne.

"Ka yiwa pilot nassar magana......ayi booking barinmu taiwan zuwa
Nigeria.......inaso larabar nan mu koma gida". Waiwayowa farouq yayi yana kallonsa
da mamaki.

"Ina zakaje kana jinya?,ina zakaje bincike kuma bai kammalu ba?". Murmushi ya saki
me taushi yana duban farouq din,duba irin na 'yan uwantaka ta jini me cike da
dumbin qauna.

"Bincike ya gama kammala farouq......fareeda keda alhakin komai......ta samu
nasarar aiwatar da komai dinne ta silar maamah data bata full details din......abu
daya da ban sani ba shine.....bata da masaniyar abinda fareeda zatayi dashi?,ko
tana da masaniya?,tayi hakanne dukka cikin tsare tsarenta data dauki shekara da
shekaru tana gudanarwa?" Ya qarasa maganar duk wata walwala da yake ciki tana
sulalewa daga jikinsa. Ba farouq kadai ba,hatta sabreen data dawo da niyyar daukan
slipper dinta ta zagaya koda veranda din dakunan saita tsaya tana komawa da baya.
Wani irin tausayinsa yana sasuqar zuciyarta. Yadda walwala tayi qaura daga fuskarsa
karo daya ya tabbatar mata a yanzu a rayuwarsa bashi da sauran wani ciwo daya wuce
MAHAIFIYARSA. A jikinta ta dinga jin cewa......She has to put in effort to help him
overcome his past,ya kamata ta sake matsawa sosai cikin rayuwarsa.....yana
buqatarta fiye da yadda take hasashen zai kasance.

"No dude.....no.....kada kayi wannan tunanin.....ko yaya ne.....ko yaya kuke da
maamah uwa ce.....bana tunanin kowanne kalan hali ne da ita zata iya bada qofa ko
daman rabaka da rayuwarka". Idanunsa da suka sauya kala ya maida kan farouq yana
dubansa.

"Farouq.....duk yadda zan gaya maka abinda ke nan gurin..." Yayi nuni da qirjinsa
da yatsansa.

".....ba zaka fahimta ba.......mun rasa MAHAIFIYA.....MUN RASATA RASHI NA HAR
ABADA......saidai na yadda nayi kuma imani,yana cikin rashin cikar kamalar ni'imar
mutum cikin DUNIYARSA......cikakkiyar ni'ima tana lahira".

"Duk da haka dude please......ka ajiye wannan a side"

"Na ajiye farouq......fareeda zata girbi duk abinda ta jima tana shukawa.....she
must pay.....bawai iya kaina kawai ba". Kai farouq ya jinjina,wani aikine daya
shirya gudanarwa da kansa,sai gashi fu'ad din ya rigashi.

"But dude.....inaga kaman

Please Login or Register in order to submit comment