You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ringing biyu wayar tayi ya daga yana sakata a kunnensa

"Ya kamata ka qaraso wajen walimar fa.....akwai mutanen da zaku gaisa dasu"

"Bana kusa"

"Kaman yaya?" Farouq ya tambayeshi a mamakance

"Eh.....kaman yadda kaji bana kusa,uzuri ya kamani nadan fita"

"Why.....you know......"

"Anni zata fahimceni idanma kai baka fahimta ba.....sai na dawo" Ya amsa masa yana
katse wayar ya maidata ya ajiye. Shi a yanzun kasuwancinsa shine abinda yafi
damunsa shine kuma gaba da komai,bai takurawa kowa ya matsawa kowa ba,don hatta da
saddiq daya Kamata ace a yanxun suna tare suna duba al'amuran da suka taso musu bai
masa magana ba,bai kuma ce komai dashi ba saboda yaga ya sanya kanshi cikin hidimar
bikin sosai,ya bashi lokaci ya qare ya dawo hayyacinsa.....tafiya ce dai dasu
tsakanin jibi da gata,kuma bazai dage masa qafa ba dole ya shirya su wuce. Girgiza
kai kawai farouq din yayi,halin fu'ad saishi,baisan ma yaushe ya fita din ba bayan
sun shigo cikin gidan tare. Ya sanshi sarai ya kuma sani,wani irin mutum ne shi da
kasuwancinsa ke gaba da komai idan ka dauke shi anni abba da su saddiq,amma koma
meye yana ji a jikinsa,yana Kuma fatan duk yadda yakai ga gujewa auren da bashi
wani rashin muhimmanci ya zame masa silar shiryuwa da saituwa kaman kowanne
magidanci.

A nutse farouq ya ratso cikin mutane ya yiwa anni rada. Kai kawai ta
gyada sanda idanunta suke kan sabreen dake zaune waje daya bata ko qwaqwaqwaran
motsi. A iya haka tana iya hangen nutsuwa a tare da ita,sannan haka kawai takejin
qaunar yarinyar cikin ranta.

Tana iya hangen wasu abubuwan ta cikin mayafin dake lullube saman
kanta,a sanda walima tayi nisa..... Kai kawo na mutane ya qara yawa tata zuciyar
cike take da lissafe lissafe kala kala. Lumshe idonta tayi sanda aka fara gabatar
da miqa gudunmawa ga amarya,wato kowa zaizo ya zube mata tasa gudunmawar adan wani
babban qwarya dake ajiye a gabanta maimakon yin liqi,wanda daga nan za'a fara
gabatar da lectures akan zaman aure. Numfashi ta sauke daga can cikin hunhunta,duk
cika da batsewar mutanen dake a wajen bata hangi wani nata ko mutum daya ba. Sai
takejinta bare a wajen da wani irin rashin sukuni da takura.

*DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 21


21
A nutse aka fara zuwa daya bayan daya ana zube sabbin 'yan dubu dubun fil
a miqe cikin bundles dinsu a gabanta. Ta rasa tsakanin burgewa da rashinsa wanne
takeji cikin zuciyarta?,duk da ta hangi tarin nutsuwa da kamala a komai na taron.

Idanunta ta sake dagawa a hankali ta cikin mayafin tana kallon bakin
qofar shigowa gurin dake facing dinta......tamkar abinda ake jira kenan saita hangi
huda na shigowa. Da farko ta dauka kaman gizo idanuwanta sukeyi mata ko kuma me
kama da ita ne,saidai shigowar nadra da haneefa ya qarasa kore mata dukka shakkun
data soma ji cikin ranta. Wannan bai saketa ba taga abinda ya kusa doka zuciyarta
saboda firgici.....maamah ce.......tana biye dasu da dukkan alamun da zasu gwada
maka tare suke......tare suka shigo,don waiwayawa haneefa tayi da alama kiran
sunanta tayi,sai taga ta riqe hannunta haneefa na mata murmushi tana maida mata
sukaci gaba da takowa wajen tare.

"A ina ta gansu?,a ina ta daukosu?,ya akayi taje ko sukazo wajenta?,tun yaushe?,me
kuma take gaya musu?" Tayi tambayar sanda taga ta tsaidasu duka su ukun kuma
kowacce ta tattara mata hankalinta.

Sanye take cikin wata 'yar ubansun super embellished me asalin tsadar da
jikinta ke bada wani irin santsi tamkar ba atamfa ba. Tun daga yanayin shigar zaka
tabbatar da gaske ta dauki duniyarta dama rayuwarta gaba daya.....hakanan da gaske
komanta yana mata dadi yana kuma tafi mata yadda takeso. Daga bayanta hajja harira
ce data shirya kanta itama cikin applique lace ruwan sararin samaniya. Ita dinma
duba daya zakayi mata ka tabbatar da halin yazo daya kamar yadda abotar tazo daya.

Kai tsaye ta daga yatsa tayi musu nuni da kujerar da sabreen ke zaune
a kai,sai dukkaninsu suka maida idanuwansu kanta. Fuskokinsu suka cika da farinciki
duk da basa iya ganin fuskarta sosai,suka motsa kamar zasu taho zuwa wajenta,amma
sai taga ta sunkuya tana magana dasu. Cikin qasa da second talatin taga sun maida
hankalinsu gareta.......sun kuma juya suna binta a baya zuwa hanyar data
nufa,daidai lokacin da me gabatarwa ke bada sanarwar

"Mahaifiyar ango ta shigo......uwarsa kuma zata marabceta" Maganar data finciko
hankalin sabreen daga shingen tunanin data afka sanda take binsu da kallo suna biye
da maamah sau da qafa.....kai kace ummeensu ce ta dawo duniya.

"Uwa?.....mahaifiya?,wacece?" Ta samu kanta da shiga wannan rudanin tare da fatar a
yau ta samu warwarewarsa,don haka ta buda dukka idanunta tana bin kowanne kusurwa
da kallo tanason samun warwarar rudaninta.

Cikin nutsuwa da girmamawa anni ta miqe tana dosar inda maamah ke a
tsaye,fuskar annin shimfide da fara'ar data ratsa har qasan zuciyarta. Har yanzu
gangar jikinta da ruhinta basu daina jin farinciki da alfaharin aurar da fu'ad
ba......wani abu guda daya daya zamewa maamah tamkar dafi tsakiyar tsokar zuciyarta

"Ameenatu ce ta aurar dashi" Kalmar da inda tana da ikon gogeta tsaf saita gogeta
daga dukkan wata ma'adana ta kalamai.

"Barka da zuwa......sannunku da zuwa......"

"Uwa kuma mahaifiyar muhammad fu'ad jadda ba,ai haka ya kamata ne gabatarwarki ta
fadi" Hajja harira dake tsaye gefan hannun hagun maamah ta furta da wata irin izza.

Kallo daya anni tayi mata ta watsar da ita gami da bawa banza
ajiyarta,idanunta suna sauka akan fuskar 'yammatan su uku da take ganin tamkar ta
taba ganin fuskar a wani waje. Kallonsu kawai tayi suka fara gaidata daya bayan
daya,ta amsa musu tana dafa kan kowaccensu da madaukakiyar fara'a da kuma
kulawa,kulawar da ta sauka har cikin idanun sabreen wadda ruhinta gaba daya yana a
wajen,saidai babban qalubalenta bata iya jin me aka tattaunawa akai.

Tun daga tashin anni har tsaiwarta a wajen sabreen na tuna guraren
data taba ganin fuskar matar ne. Indai da gaske itace anni......itace uwa ga fu'ad
ba shakka ta santa......amma ta yaya haka ta kasance?,ya akayi yake da uwaye
biyu?,me yasa anni data taba sani duk da alkhairi ya hadasu ba ita ta nema masa ita
ba?,sai waccar baquwar fuskar da bata taba ganinta ba kafin faruwar wannan abun kaf
tsahon rayuwarta?.

"Barkanki kade Ameenatu.......sannunki da hidima" Maamah ta maida mata da wani irin
salon murmushin da ya sanya anni tajishi har cikin jinin jikinta.

"Ina tayaki murnar aurar da fu'ad da kika samu damar yi......wannan babbar dama ce
da zata zame miki tarihi kuma abun tunawa watan watarana.......ina aka tanadarwa
mahaifiyar fu'ad domin ta zauna ita da qannen matarsa?" Tayi tambayar kai tsaye
cikin isa......

"Ai albarkacin kaza qadangare kansha ruwan kasko mariya....muhalli har sai kin
baiwa wani" Anni ta fadi duk da rabin hankalinta yana kan yaran abubuwa masu yawa
suna yawo a ranta. Waiwaya tayi ta yafito muhsina inna uwaisha dake shirin wucewa

"Itace mariya.......a cikata da irin karamcin nan da aka gada,koda zata cika hall
dinnan da jama'arta.....a tabbatar an gamsar da buqatarsu,a nuna mata dattako da
dattijantaka" Dukka anni tayi maganganun da kai da bakasan komai ba zaka dauka
zallar magana ce kai tsaye,saidai gasu hajja da maamah din dukkaninsu sunsan magana
ce akayi musu me harshen damo. Juyawa abinta anni tayi tana komawa cikin
jama'arta,maamah tabi bayanta da kallo tana jin zafin jirwayen datayi musu me kama
da wanka. Zafafan baqaqen maganganun data fahimci kowaccensu,amma kuma saiga
murmushi yana subucewa daga saman fuskarta

"Kwanaki kadan suka ragewa izzarki ameenatu.....na rantse koda pant din dake
jikinki da kudin muhammadu aka siyeshi saikin zareshi kin miqomin.......na rantse
sai na sanya fu'ad ya gaya miki maganganun da zasuyi silar ajalinki......maganganun
da zasu zame miki dafin da zuciyarki zata buga ta tarwatse pieces " Tayi dukka
maganganun ita da zuciyarta tana me cike da alwashi.

Duk da wadannan abubuwan data samu ta kuma aiwatar zuciyarta ta kasa
samun nutsuwa ko qanqani.......sam farincikinta har yanzu rabi ne......daga sanda
ta iso bakin qofar mansion House din Alhaji hamza kibiya duka sai taji ta raina
nata gidan kwata kwata. Batajin akwai wani gida ko gini da fu'ad zaiyi mata komai
kyau da dukiyar da aka narkar ya zauna mata a rai muddin zai zamana muhallin Alhaji
hamza kibiya yafi nata......indai zai zamana matsugunnin ameenatu zai d'ara nata.

Daina fahimtar komai tayi......daina fuskantar duk abinda ake gudanarwa
tayi,dukka idanunta dama hankalinta suna kan 'yan uwanta,suna kan kowanne motsi da
kai kawo nasu. Hankalinta taji yana tashi,bata qaunar kowacce mu'amala ko alaqa
kome qanqantarta tsakanin maamah dasu,saidai yadda taga tana jansu a jiki,ta
wani.mugun sake musu ko ita batajin ta sake musu haka. Haneefa duk girmanta tana
saman cinyarta tana wani lallabata,irin lelen da haneefa din keso a matsayinta na
auta take kuma qishirwarsa.

Cafko hannun amna tayi wadda ta zuge tata jakar ta fara fiddo sabbin
'yan dubu dubu kaman ba'asan ciwo da zafinsu ba.....kamar ba wasu abu masu
muhimmanci ba tana zubewa sabreen din.

"Kiramin su nadra.....kice suzo yanzu yanzu injini". Dubanta amna tayi duk da bata
iya ganin fuskarta sosai.

"Su waye?" Ta tambayeta don bata gane ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana qoqarin saita
kanta,sai sannan ta tuna amna din bata sansu ba

"Sun shigo yanzu su da......." Ta dakata tanason tuna sunan da ake kiranta dashi

"Su da maamah" Kai amna ta daga tana hangensu daga nan inda take,kwata kwata bata
qaunar abinda zai hadata da matar,bata qaunar kallon da take binta dashi irin
kallon dake fita daga idanuwanta zuwa kanta,amma zuwa aiken sabreen ya zame mata
dole

"Okay" Tace da ita

"Na gode" Sabreen ta fadi da sauri saboda jin dadin zatayi mata abinda takeso a
sanda bata da damar tashi.

Da ido take bin amna sanda take nufarsu,duk wani taku dake qara kusancin
ama dasu bugun zuciyarta qaruwa yakeyi,ta kasa dauke idonta daga kansu daidai da
second guda har zuwa sanda ta qarasa gabansu. Taga amna ta mata magana,ita kuma ta
waiwaya tayi magana dasu kafin ta sake dubanta still ta gaya mata wani abu daya
sanya amna din juyowa ta dawo mata.

"Me suka ce?" Ta fara da tambayar amna din tun bata gaya mata komai ba

"Zasu zo.....zasu taho tare da maamah din wai". Idanunta ta maida ta lumshe tana
girgizawa amna kai kawai. Wani irin rikitaccen yanayi yana sauko mata,kada dai ace
suna jin wani sauyi na daban akan maamah kamar yadda takejin wajabcin bin umarninta
tako ina yana ratsata?.

Tun daga wannan sa'ar nutsuwa tayi mata qaura,ta kasa debe idanunta
daga kan 'yan uwan nata,duk wani motsi murmushi da kuma fara'ar fuskarsu ya
tabbatar mata suna jinsu ne cikin sukuni da farinciki,har zuwa lokacin da aka bada
sanarwar isowar mahaifiyar ango zuwa inda surukarta take.

Tamkar mejin tsoron wani abu haka zuciyarta taci gaba da bugawa sanda
maamah ke kusantota tana takowa wajenta dasu nadra gaba daya. Idonta ta lumshe da
sake budesu akansu gaba dayansu tana me kyautata zaton saisun iso gareta ne kai
tsaye kafin aiwatar da komai......saidai kuma akasin haka ne ya faru. Kamar kowa
suma wajen zuba kudin suka nufa,kowacce ta dire rafas na dubu dubu sabbi guda uku
dake hannunsu huda kuma ta zuba biyar. Bin kudin tayi da kallo,suka kuma tsaye mata
a rai.

"Wai ina momma bahijja?" Tambayar da bata da amsarta batasan kuma wanda zai gaya
mata amsar ba. Ta tabbatar daga kansu har zuwa momma ba wanda zai basu wannan
kudaden son suzo su zuba a wajen.....amsarta ta fito sanda maamah ta cire wani
rafas din ta bawa nadra da zummar ta qara a ciki.

"To kuje ku gaisa" Maamah ta basu umarni sanda ta fara zube nata kudaden da suka ja
hankalin mutane da dama.

"Waye ya kawoku?, yaushe kukazo?,ina momma?" Ta damqe hannun nadra da tafi kusa da
ita tana jera musu tambayar a gaggauce daya bayan daya.

"Momma ta tafi yau....tun da safen mukazo,mun dawo gidan maamah......"

"Tana da kirki adda.....kuma tace kema kina nan,zamuci gaba da ganinki.....kayanmu
ma tace basai mun taho dasu ba......kawu yace muyi zamanmu zamufi samun kulawa".

"Baki da hankali huda?" Ta fada da sauti me qarfi tana qoqarin janye lullubinta don
ta samu damar saka idanunta cikin na huda.
"Yi a hankali......idanun jamaa suna kanki" Maamah data sunkuya saman kanta tana
maida mata lullubinta ta fada da murmushi akan fuskarta kamar wani abun arziqi take
gaya mata.

"Ku tafi mu zauna daughters" Ta fada da kulawa sosai a muryarta da cikakkiyar
fara'a.

Tana jin takunsu sanda suke sauka a wajen,ba damuwa ko wani abu cikin
muryoyinsu,tana jin tafiyar nasu na buga zuciyarta sosai,tanaso qwalla ta fita daga
idanunta komai qanqantarta ko zataji sanyi,amma ko daya bata samu wannan damar ba.

Koda aka kirayi anni saita aike amna da wani qaramin akwati da ba
wanda yasan meye a ciki aka ajiye cikin wani salo na siyan girma.


*DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 22


22


Kafin a tashi tsaf ta rasa sauran nutsuwarta,wani irin tashin hankali
takeji maras misali daga kowanne lungu da sashe na zuciyarta. Ba abinda ke gilmawa
ta idanu da zuciyarta sai huda nadra da haneefa......ina momma bahijja?.....ina
momma bahijja?,.....da gaske ne sun bawa maamah yaran?,ya akayi haka ta kasance?,ya
akayi ta tafi ba tare da sunyi sallama?,ya akayi ta tafi ta barsu bata cika mata
alqawarin data dauka akan 'yan uwanta ba?......zata sakene ta kalli rayuwarsu ta
balbalce?,ko xatayi dukkan abinda ya kama tayi don ta tseratar da rayuwar yaran?.
Wadannan sune tambayoyin da ta dinga yiwa kanta har a sanda take cikin kebantaccen
qaramin parlor din da amna ta kawota bayan tashi daga taron,tace ta zauna zasu gana
da anni.

Dogayen yatsunta da suka sha lalle kawai take murzawa kanta a
qasa,zuciyarta na wani irin zafi tare da jin qaguwar su koma gida ta lalubi maamah
suyi magana ta sosai da ita.....koda tana jin kamar ta samu ikon sarrafa zuciyarta
da bin umarninta cikin wani irin takura da takeji ana yiwa zuciyarta,.....to amma
sam bata samu lago akan abinda takeji a zuciyarta game da 'yan uwanta. Qaunarsu
darajarsu martabarsu da kuma soyayya da shaquwar data ginu tsakaninsu ba abinda ya
sauya.

"Assalamu alaikum" Muryar anni ta ratsa falon tana murza qofar ta shigo

"Wa'alaikumussalam" Tada daga kanta kadan tana duban qofar gami da amsa sallamar.
Kallon kallo suka yiwa junansu,kowanne a cikin su yanason tuna inda yasan fuskar
dan uwansa. Sabreen ce tayi saurin watsar da qoqarin lalubo inda tasan fuskar
annin,saboda gaba daya hankalinta ba'a nan yake ba,sai ta samu kanta kawai da
zamewa daga saman kujerar tana gaidata,wata dabi'a data manta rabon data
aikatata,amma a yau ta samu kanta da yin saboda wani kwarjini da taji matar tayi
mata.

"Koma ki zauna abinki daughter" Ta fada da kulawa amma saita kasa hakan,saita samu
kanta da zama sosai tana tanqwashe qafafunta.

"Na tsaidaki ko?,ga dare yana qara yi,duk da me babban sunan bai qaraso ba,uzuri ya
taso masa daya saka dole ya fita" Kai ta sakeyin qasa dashi ba tare da tace mata
komai ba,batasan me yasa matar take mata kwarjini haka sosai ba.

"Bari muyi magana a taqaice a gaggauce......da farko ina miki maraba da shigowa
cikinmu da kikayi,ina fatan Allah yasa ku zama abokan arziqin junanku.....Allah ya
hada hankalinku waje daya......bani bace mahaifiyar fuad,amma idan na kira kaina
uwa a gareshi nasan banyi laifi ba,ni din uwar riqonsa ce tun daga quruciyarsa har
kawo yau.....hajiya mariya wato maamah itace mahaifiyarsa". Dole bata shirya ba
maganar ta sakata daga kai da hanzari ta dubi anni,sai kuma ta maida ta sunkuyar

"Baiyi sa'ar uwa ba.....ke kuma bakiyi sa'ar d'an riqo ba" Abinda ta fadi kenan
qasan zuciyarta tana jin kamar a tsakaninsu annin ta fita daban. Anya ba halinsa
Allah ya duba ba ya hadashi da uwa daidai da halinsa?. Zaren tunaninta ya katse
sanda anni ke magana

"Yana da kirki.....yana karamci,yana da tausayi yana da tausasawa amma fa.......ga
mutumin daya fahimceshi. Bashi da sauqi ya fiya tsauri,bashi da tausayi ga wanda
bai fahimci shi waye ba,bayason qarya.....bayason saba alqawari,bayason yaudara
baya son ha'inci......sannan uwa uba baya daukar raini. Abu na gaba muddin zakayi
wasa da addini taku ba zata taba zuwa daya ba.....muddin ba zaka kasance karimi
kamar yadda yake ba ba zasu taba daina sabani ba,wadannan sune kadan daga
halayensa.......ameenatu" Ta kirata da sunanta na ainihi,abinda ya motsa zuciyar
sabreen kenan sosai

"Ban gaya miki duka halayensa ba don na tursasaki kula da yarona.....na gaya miki
ne don na sauqaqa miki qofofin zama dashi....na gaya miki ne don kiyi hanzarin
mamaye zuciyarsa......na kuma gaya miki ne don na rage miki wahalar
fuskantarsa......naso ace na samu zama da wasu mutane mafi kusanci dake don na
tambayi naki halayyar na isar masa dasu a shimfide.....domin cikar mafarkina
shine......gidan muhammadu yafi gidan dukkanin wani magidance zama aljannar
DUNIYA......gidansa ya zame masa kaffara akan kowanne abu daya fuskanta a rayuwarsa
a baya" Anni ta qarashe maganar har tsakiyar zuciyarta tana fatan mafarkinta ya
tabbata. Miqa hannu tayi a nutse ta kamo hannun sabreen ta sanya cikin nata

"Idan har zaki bashi dukkanin kulawa......idan har xaki nuna masa zallar soyayya
irin soyayyar da uwar kewa danta.....idan har zaki kasance me addini tsafta da
kwalliya.....xaki kula da abincin muhammadu tabbas kin gama samunsa a tafin
hannunki......yana cikin yunwar soyayya da kulawa.....muddin ya samu isashiya da
zata qosar dashi babu ko haufi kin gama mallakar zuciyarsa dama rayuwarsa gaba
daya".

Ta saurara ta kuma fahimci duka zantukan annin,saidai cikin nata
zuciyar wani magana takeyi na daban

"Inama ace zaki fahimci waye danki sani na zahiri ba fuska biyunsa ba......inama
wata daban kike budewa sirrikansa wadda ta shirya xama dashi ba SABREEN me zaman
wucin gadi ba".

Dole ta sanyashi kashe duka wayoyinsa tun a hanya a sanda abdussabur
yake tuqashi zuwa gidan anni.

A cikin jikinsa da zuciyarsa yakejin wata irin galabaita da bai taba
jin irinta ba saboda zurfafa da tunanin da yayi. Yana da kyau yaci gaba da tafiya a
gabar da yake na sanya idanu akan kowanne motsi da abinda dukka yake da alaqa da
maamah. A zarginsa me girma da qarfi ya sake hawa kan yarinyar.......ya sake samun
gamsuwa da cewa akwai shirin daya shigo da ita gidan,tunda har qarfin alaqarsu
yakai girman da zata kebanceta da wata number wayar ta daban wadda shi kansa baisan
da ita ba. Wunin yau gaba daya fiye da rabin tunaninsa yau duka ya tafi ne akan
hakan.

Bazaice maamah maqiyayarsa ce ba.....hakanan bazaice bata sonshi
ba,amma ta fifita kudi dukiya da abun duniya sama da tasu soyayyar.......kusan yayi
mata fari kuma cikakken sanin da dan adam kan iya yiwa zanen tafin hannunsa koma
fuskarsa......bazaiyi wasa da rayuwarsa ba.....hakanan bazai barwa maamah kowacce
irin dama ba.....hakanan zai saka yarinyar a wasan da zata qara fahimtar batasan
komai ba cikin duniya.....zai dafata da ruwa da kuma jinin jikinta.

Yayi sallama ya shiga parlor dinne a sanda anni ke miqa mata wata
irin takarda me daukan idanu dake qunshe da littatafai na addu'o'i

"Akwai tsaftatattun addu'o'in mallakar miji a ciki,wadanda basu da wani aibu illa
ko shirka a ciki,saidai suna matuqar tasiri wajen kama miki zuciyar mijinki a
gareki" Ko alamun fa'ida bataji cikin bayanin anni ba......wannan mallkar da take
fadi inda zata yiwu ta bawa maamah ita ta mallaki dan nata kamar yadda tace,ita
kuma ta sakar mata 'yan uwa tabbas shine zatafi farinciki.

Yana zaune yana sauraren anni tana jaddada mata

"Ki raqe addu'a da kyau.....a yanzun kece garkuwan mijinki,garkuwar gidanki ma gaba
daya" Baki ya tabe yana siririn tsaki qasan ransa. Inda anni tasan wacece ita
tabbas da bata wahalar da kanta wajen mata wannan dogon jawabin ba,da tayi saving
energy dinta kawai saboda gaba,a sanda zata fahimci wala'alla ko haruffan baqin
dake cikin littafin ba zata iya hadawa ba ballantana ta karanta,don shi kam daidai
da karatun sallarta bashi da tabbaci akai,don ya sani cewa Allah ya fada cikin
qur'ani me girma

_haqiqa sallah tana hana alfasha da duk wani nau'in abunqi_. Ya tabbatar da
nutsatsiya kuma cikkiyar sallah takeyi bata yadda za'ayi ta kasa rabuwa da dabi'ar
karuwanci da bin maza.

Ko a motar kamar ba wanda yasan da zaman juna. Kusan nasa tunanin ma na
tafiyar dake gabansa ne daga yanzu zuwa kowanne lokaci,yayin da nata tunanin
ya.lula duniyar yadda zata fidda 'yan uwanta daga wannan wasan da bata shirya
shigarsu ciki ba.

Sanda suka isa gidan sam bata wani jira guard sun bude mata qofa
ba,gurds din da take mutuwar jin haushinsu tun daga sanda suka hanata rawar gaban
hantsi a gidansu. A yanzu kuma a wannan gidan ta fahimci dasu ake kowanne
motsi,wannan wacce irin masifa ce kamar raqibu da atidu da buwayin sarki ya saukar
maka da suka zama lallai ka rayu dasu don su dauki dukkan ayyukanka,masu kyau ko
akasin haka.

A gaggauce ta wuce duka falukan ta zarce hallway zuwa bedroom
din,burinta kawai ta isa ga gallababbiyar wayar ta hadu da maamah.

Da zafin nama ta birkita inda ta aje wayar kafin su fita,saidai kuma
sama ko qasa ba wayar ba dalilinta. Cak ta tsaya tana gwama numfashi,sai kawai ta
bude jakar data dawo da ita ta fidda asalin wayarta da take kiran kowa da kowa da
ita.

Asalin layin maamah din ta kira,wanda bugu biyu ta daga,saidai bata
jiyo komai ba sai muryar haneefa daga gefe da alama hira take mata ita kuma tana
fadin

"Allah auta?" Idanu ta runtse,ta lura da gaske ta shiryawa wasan...... Ta ruwan
sanyi takeso ta cutar da rayukan da basuji ba basu gani ba.

"Me kikeso?,me kike buqata?" Ta tambayeta kai tsaye ba tare data damu ta amsa
sallamar data mata ba. Wani shu'umin murmushi ta aje,sannan ta jita tana cewa

"Haneefa jeki kwanta kema,idan na gama zanzo na daukeki mu wuce daki tare"

"Tom" Ta amsa mata kamar yadda yawanci haka maganarta take,abun kuma daya sake
sokar zuciyar sabreen kenan.

"Mallakamin d'ana nakeso kiyi.....ni kuma zan mallaka miki 'yan uwanki ta ruwan
sanyi,dama naki ne". Tayi mata bayanin hankali kwance. Suya sosai taji zuciyarta
tanayi,tanason fadin maganganu da dama......tanason tayi abubuwa da dama amma kaman
an danne harshensa sai zallar bacin ran dake mata zullo

"Why ni?,me yasa saini ne?" Ta fusgi kalmar daga harshenta ta watsawa maamah ita.

"Saboda ni a wajenki kawai na hango irin zarrar da nake buqata......a aikinki na
gano abinda zaisa aikina ya cimma gaci.....uwa uba kina da wani irin kyau da zai
iya saurin rusunar da zuciya ya kuma narka zuciyar kowanne d'a namiji". Qit kawai
ta kashe wayar tana jifa da ita gami da cusa dukka yatsunta goma cikin sumarta.

Maganganun maman sun isheta haka,a yanzu basu take da buqatar ji ba.
Kowacce tsiga ta jikinta ta miqe,taji wani irin matsuwa da fatan isowar kayan aikin
maamah din hannunta. Inama ace zai yuwu ta danneshi tayita dura.masa abincin?,daga
safe zuwa yamma ya zame mata mallakakke kaman yadda takeso ita kuma ta samu yancin
'yan uwanta. Tabbas! Inda babu 'yan uwanta da maamah din tayi garkuwa dasu,babu
abinda zai hanata nuna mata ainihin kalarta da kuma ainihin yadda wasan zai gudana.


*DUNIYATA LITTAFI KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862


ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 23



23


Har wani nauyi idanunshi ke masa saboda tsohuwar gajiya da sabuwar gajiya
dake a jikinsa,ga kuma wadda ke jiransa a gaba. Wanka ya fara yi,sai kawai ya sauya
pyjamas dinsa ba tare da yabi takan abinci ba don baijin gajiya zata barshi yayi
hakan yabi lafiyar lallausan gadon nashi dake gewaye da kyawawan pillows daa luxury
bedsheet din dake qarawa bed din zama

Please Login or Register in order to submit comment