You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dukka number dinsa taci gaba da gwadawa,number ta qarshe data kira taji
alamun kiran ya soma tafiya,saita samu gefen kujera ta zauna tana furzar da iska me
zafi daga bakinta ranta yana tafasa.

Kaman jira ake ya gama wayar wani kiran ya shigo. Kamar ko yaushe
bayyanar sunanta saman screen din fargaba da kokwanto yake sanyashi. To amma ba
yadda ya iya,dole ya daga kiran ya mata sallama kaman yadda yake a dabi'arsa.

"Wa'alaikumussalam.......me yasa har yanzu baku shigo bane fuad?,ka manta da
alfarmar dana nema kenan?" Ta fadi tana qoqarin tausar zuciyarta ta yadda kalaman
zasu fita da taushi daga bakinta.

Komai qanqantar motsi tsakanin anni da maamah sai yaga tarin banbance
babance. Da fari anni lafiyarsu kawai takeso taji kafin komai......amma ita nata
uzurin su shigo suci abinci shi ta fara gabatarwa,abincin da ta tabbatar koda
basuci a wajenta ba zasuci ako ina nema,amma kuma lafiya fa?.

"Ayyukane suka tsaremu yau dukkaninmu,yanzu haka ma wani guri zan qarasa......amma
in sha Allah i will do my best". Shuru ta danyi wuta tana dauke mata,yanzun qarfe
tara harda rabi na dare,yaushe yaje wani waje,yabaro gurin kuma yazo wajenta?.

" Okay,ina jira" Abinda ta fada kenan tana jin kamar ta bude masa abinda ke ranta.
Bala'i da masifa takeson lullubeshi dashi,to amma ko dazun suna waya da hajja
harira sai data gaya mata

"Me garaje ba kasafai ya fiya cin nasara ba a dukka lamuransa,saikin saka haquri
juriya da kauda kai kaman bakiga komai ba". Wayar ta cillar gefe,ta hada tafukan
hannayenta cikin fuskarta.

Wata irin tsanar anni da alhaji hamza tana mata masauki a zuciya tana
kuma qara samun hauhawa cikin ranta. Inama ace yau zata budi idanu taga babu su
cikin rayuwarsu?,da kowacce dama tazo mata yadda takeso.

Iya tafiyar da sukayi cikin motar bawai zaman shuru kadai yayi
ba,zuciyarsa ta gama nisa akan matsalar iya balla shingen asusun ajiyarsu har kuma
a debi wani abun?. Ba shakka koma waye ya aikata hakan yana da alaqa me qarfi da
kamfaninsu,yana kuma da alaqa ta kusa kusa da mika'il. Dole ya zamana yana da alaqa
da mikail.....ko shi kansa mikail din ma gaba daya.

Dalili......dukan abinda zai basu daman yin kutse kai tsaye da samun
nasara haka a sauqaqe yana tare da mikail din. Dazu dazu ya danqa masa komai,cikin
qasa da awa biyu kacal kuma ace komai ya faru?.

"Muje gida" Ya bawa driver din umarni,wanda ba wanda ya binciki dalili tsakaninsu
ukun suka sauya akalar tafiyar tasu.

A tsaitsaye ya leqa anni sannan ya wuce zuwa sassanshi. Ya samu sassan
nasa neat kamar ko yaushe kaman kuma yadda yake buqata. Ba duhu ba kuma haske me
yawa sai matsakaicin hasken da bai fiya takurawa idanuwa ba. Ko ina qamshi yake
fiddawa da wani irin moderate yanayi.

Takalmanshi ya sabule daga bakin qofa yana sauya wasu lausasan flip
flops,daya daga cikin hadimansa ya sunkuya ya daukesu yana adanasu cikin wani
qawataccen ma'ajiyar takalma me daukan hankali.

"Ku ajiye komai ku tafi,na sallami kowa.....sai da safe" Ya fadi musu yana takawa
zuwa hanyar da zata sadashi da wani dan corridor da zai bashi daman isa bangaren
dakunan baccinsa.

Daga zuciyarsa har gangar jikinsa basu da wani karsashi ko qwari,to amma
kasancewar zuciyar jaruma ce ya sanya bata gaza ba,sai daya tabbatar yayi wanka
yayi sallah ya sauya kayan jikinsa sannan Kai tsaye ya dawo falon da babu kowa a
cikinsa,saidai ya tabbatar security tako ina suna kai kawo cikin gidan dama wajen
gidan.

A nutse yake ratsa falon hannunsa zube a aljihun boxers din daya sanya
tamkar wanda ya boyeshi saboda jin sanyi ko baya buqatar aga hannun nasa. Light
blue kalan kayan sun masa wani irin kyau,saidai kuma fuskarsa tadan fada kadan
wanda baya rasa nasaba da stress din yau daya tsinci kansa a ciki.

Dining ya wuce kai tsaye,komai yana shirye cikin tsafta. Bayajin a
duniya bayan anni akwai wanda yakai ameh sanin tsarinsa akan abinci.

Yasan duk abinda ya bude cimarsa ce,kuma abinda yakeso ne,saidai kuma
bayajin akwai wani sauran space da cikinsa zan dauki abinci,wannan ya sanya ya bude
royal glass bowl din da tun bai bude ba yana iya ganin abinda yake ciki.

Lafiyayyen fruit salad ne da aka samar dashi daga dukkan nau'in kayan
marmari na nan qasar dama wanda bamu dasu a nan din. Baya rabo da fruit sam,don
haka masu shirya masa store da fridge dinsa sunsan duk inda zasu samar masa da
nauin fruit da cimar da yakeso din.

Yadan diba da yawa,sai ya sauka a hankali ya duba ma'ajiyar shayinsa.

Bayashan coffee sai idan dole ta kama,amma yasan sirrin shan black tea
da ake masa hadi na musamman da abubuwa masu amfani ga lafiya irinsu cinnamon
cardamom scent leaves da sauransu.

Da kansa ya shirya komai saman tray ya nufi wata yar kyakkyawar books
shelves ta ainihin gogaggen katako dake bangon gabas na parlor din. Hannu daya ya
sanya ya murza wani abu da ba lallai ka iya lura da zamansa jikinta ba,sai ya
sakeshi yasa hannu ya juyashi take qofa ta bayyana daga baya abinda ba zaka taba
tunanin samuwarsa a wajen ba,ya taka ya shiga a hankali yana maida qofar yadda
take.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 76


Daki ne da yakan jima bai shiga cikinsa ba sai muhimmin aiki irin haka
ya taso. Saidai duk da haka komai a tsaftace yake.

Wani irin table ne na musamman ya jawoshi gaban main table dake dauke da
nau'ikan na'urorin computer iri daban daban,ya aza tray din hannunsa a kai,ya taka
a hankali ya kunna kowanne lantarki dake dakin,ya bada haske sosai. Komai na dakin
bisa tsari yake,da nau'o'in kalolin green masu qarawa idanu qwarin gani.

Idanunsa saman systems din daya kunna guda biyu yana jiran su gama
saituwa. Kadan kadan kuma yana kurbar black tea din da qamshinsa ke qara masa
nutsuwa,kafin ya ajiye ya soma shan fruit salad din,daidai sanda komai na system
din ya daidai ta,sai ya sake jawo kujerarsa gaba yana bata dukkanin hankalinsa.

Cikin tsananin nutsuwa da qwarewa yake bin komai. Ya kusa kashe a
qalla awa biyu cikakku kafin ya dakata,ya tura kujerarsa baya yana zubawa allon
computer idanu yana duba abinda ya samu a tsahon zaman da awannin da ya kashe.

Iska kawai yake furzarwa daga bakinsa,mamaki yana sake cikashi da samun
bayanan duk da bai qarasa samun ragowar baya nan ba,amma ko iya wadannan bayanan da
zaman da zaiyi da mikail sun isheshi samun kan komai. Ya dinga murza tafin hannunsa
cikin na juna tamka ma jin sanyi,kanshi yana sake cakewa.

"Jibril usman" Ya maimaita sunan idanunshi nakan sunan da bai samu damar
samun ainihin fuskar me sunan ba. Tabbas ko wayeshi din mayen computer ne,kuma
qwarrare a sanin fanninta,saidai duk da haka qwarewar tasa akwai saura,don akwao
gurare da abubuwa daya gani wanda shi Jabril din da ya samu rufesu to ba shakka shi
kansa yanzun bazaikai ga isa ga bayanan ba. Qaramin masanin computer zai iya
saluting jibril,amma shi da mutane ire irensa zasuyi murmushi ne kawai,a karon
farko kuma su fahimci saura taqi kadan yakai inda ya dace yakai din.

Gefe daya ranshi ya sake ninka baci,duk wanda yaga aka zare kudin
zaiyi tsammamin manyan hackers gagarumai wanda suka gagari duniya system dinsu ta
hadu dashi......wannan kadai ya isa ya sake zaburar dashi lallai lallai yana
buqatar yin garambawul wa security team dinsa,amma kafin sannan mikail shine mutum
na farko daya dace ya dauki mummunan mataki a kansa,saboda shi da kansa ya yiwa
tsaron company dinsu aiki,ya saka abubuwan da duk qwarewarka idan ba samun wani
information mutum yayi ba zai wahala ya samu isa ga inda suka samu isa din.

"Ina yaje?,waye ya bawa sirrinmu?" Wadannan sune tambayoyi guda biyu da yake
buqatar ji daga bakin mikail din. Kodai yaci amanar company......ko an nemi
rayuwarsa an masa barazana....kota dalilin sakacinsa bayanan sun fita.

Washegari kaman kullum,yabi tsarin jawadalinsa na kullum tun daga gida
har zuwa office. Qarfe shida da rabi yake kammala motsa jikinsa ya wuce wanka,idan
ya fito yakan dan bar bathrobe jikinsa ya karbi newspaper da magazines ya
duba,yadan duba saqonnin email da WhatsApp dinsa ya hada da shan ruwan duminsa ko
dafaffiyar madarar shanunsa me tumeric. Sai bayan kammala dukka wadannan hidindimun
sannan yake shiryawa,yayi breakfast ya wuce office.

Kamar ko yaushe yau dinma bakwai da rabi ya fito daga toilet daure da
bathrobe dinsa. Yanaso yau ya fita da wuri ne fiye da yadda ya saba fitan. Don ko
da safe daya tashi ya sami missed calls din maama din kusan guda goma,wanda ya
tabbatar tun na daren jiya ne.

Yawan kiran nata kadai da takeyi yana sake bashi tabbaci ne a kanta. Ya
jawo wayar ya turawa musaddiq text akan zuwa takwas ya shirya zai aikeshi wani
guri,sai ya cire toilet slippers din ya sanya wasu tausasan rufaffun takalma ya
soma takawa yana fita don riskar parlor ya duba newspapers din yau.

Ba kowa parlor din sai ameh daketa zirga zirgar shiryawa ogan nasa
dining,sai me sunan malam dake zaune saman lallausan turkey carpet din da aka
qawata tsakanin kujerun. Me sunan malam din na daya daga cikin amintattunsa da basu
da shamaki wajen samun daman isowa parlor dinsa.

"Good morning sir" Ya fadi yana rusunar dakai
"Morning me sunan malam.....mun tashi lpy" Ya amsa masa yana zama saman wata sofa
guda daya data banbanta da sauran duka kujerun parlor din yana kai hannunsa saman
dan qaramin table din da aka zube masa sabbin newspaper din bayan an kwashe na
jiya.

"Lafiya alhamdulillah sir"

"Ma sha Allah" Ya furta yana bude page din farko na jaridar ba tare daya tsaya
karanta bangonta dake dauke da title na labaran ciki ba.

Labarin farko suka wafci idanunsa. Ya sake dawowa da baya bayan ya
karanta layin farko da akayi da manya manyan zane. Bai tsaya bata lokaci ba ya koma
bangon don sake duba title din da ya tsallakeshi a dazu. Tabbas duka abu guda suke
nunawa cikin harshen turanci

*_GAGARUMAR SATA.....AN WAWASHE KOMAI DAGA ASUSUN JADDA DIAMONDCHORE
RESOURCES/AKWAI YIWUWAR DURQUSHEWAR COMPANY DIN NAN DA WANI DAN LOKACI_*.

Jaridar ya juya tamkar ma ya manta wanne gidan jarida ne suka kafe
labarin. Sai ya maidata ya ajiye yana dauko newspaper ta gaba.

Ita dinma kaman wancan,bangon farko abinda yake rubuce kenan a jiki,ya
sake juyawa shima ya duba gidan jaridar sai ya maidata itama din ya ajiye,ya sake
daukan ta uku.

To ita dinma babu wani canji,duka dai labari guda daya ne,abinda ya bashi
tabbaci da yaqinin wannan shine labari na farko da zaiyi trending kenan yau a
duniya kasuwanci.

Idanu kawai yaci gaba da zubawa rubutun kamar wanda kwanyarsa ta kasa
gano komai,ya daga idanunsa a nutse da suka fara sauya launi ya kalli ameh daketa
goge dining din da kyau don kawar da qura datti ko maiqo komai qanqantarsa daga
muhallin cin abincin boss din nasa da ya sani da tsananin tsafta da rashin son qura
ko datti komai qanqantarsa

"Ameh......dauki waya ka kira sassan saddiq.....i wanna see him yanzu yanzu".

"Yes sir" Ameh ya amsa masa yana sakin komai,sannan ya gangara a hankali yana nufar
inda wayar take girke.

Daidai sanda ameh ya gama shaidawa saddiq saqon fuad farouq yayi
knocking daga can first door sannan ya turota a hankali ya shigo. Yana sanye da
kayan motsa jiki da alama fitowarsa kenan daga dakin motsa jiki na gidan,wanda dama
kusan kullum shine qarshen shiga,fuad kuma na farko,saddiq da musaddiq ke binsa
daga baya.

Dauke yake da jaridu har guda uku a hannunsa,kallo daya fuad yayi masa
ya karanci shima labarin ya gani kuma shi ya shigo dashi. Fuskarsa a dinke ba
walwala ya samu kujerar dake fuskantar fuad din,wannan ya sanya me sunan malam
ficewa ba tare daya gabatar da abinda ya kawoshi ba,hakanan ameh shima ya wuce ta
kitchen ya bulla ta baya yabar sassan.

"Tun jiya naketa qoqarin ganinka.....duk da dare yayi sanda kuka dawo nayita
nemanka ban samu ganinka ba........yanzu da safe kuma sai naga wannan" Ya fadi yana
zube masa jaridun hannunsa. Binsu yayi da kallo sannan ya maida dubansa kan fuskar
farouq

"Nima haka na tashi na gansu farouq"
"How comes fuad?" Ya furta tsananin bacin rai yana cin zuciyarsa. Kanshi ya motsa
kawai yana girgizashi kadan

"A lot of things farouq......bansan ma ta inda komai ya fara ba......na kuma rasa
ta inda zan kamoshi......inajin kamar ana warwaremin tunani na ne......da farko
wawashe asusun kamfani ta sigar da ba wanda zai iya yinta sai na kusa ko wanda
yasan sirrin asusun......ina cikin aikin kamo zaren kuma sai ga wannan......wannan
fantsamar labaran tabbas shiryayyen abune koda kwashe kudin ba shiryayye
bane.......zakafi kowa fahimtar anyi ne don a yiwa kamfanin illa......ta yaya
babban kamfani kamar namu da yake da hannuwan jarin manyan 'yan kasuwar duniya ace
saboda tsananin rashin tsaro har za'a iya kutsa kai ciki a debe kudin
mutane?......wanne tabbacin tsaro muke dashi da zamu baiwa dukkanin wanda yake da
buqatar kasuwanci damu?,wannan shine tuhumar da xamu fara fuskanta daga wajen
al'umma......waye ya fidda labarin cikin qasa da awanni uku,har ya zamana labarin
da kowanne shafin jarida suka maida bangon labarinsu?". Kai farouq ke gyadawa cikin
zuzzurfan nazari,ya daga Idanunsa ya sake duban fu'ad

"Shi kansa kwashe kudin nan baka tunanin aike ne?,ture ne?,kuma suna da alaqa da
wanda ya fidda labarin?". Mintuna kusan uku fu'ad din baice komai ba,kansa yana
sake qullewa,sanda ya bude baki zaiyi maganar sadiq ya shigo sanye da jallabiyya
hannunsa riqe da system.

Kallo daya dukansu sadiq din yayi musu ya fahimci sunga komai,tun da
sassafe kiraye kirayen wayoyi suka tasheshi,kusan fitar labarin su suka hanashi
fita motsa jiki tun daga sallar asuba daya koma. Yana tunanin ta yadda zai iya
sanarwa da fu'ad din abun,amma kuma yasan zai wahala awannin safiya su wuce bai
sani ba tunda shi din ma'abocin bin shafukan jarida ne.

"I hope abba baiji komai ba ko bare anni?" Fu'ad yayi tambayar tsananin fuskar
farouq da sadiq. Junansu suka kalla kafin farouq ya amsa

"Zai wahala abba bai sani ba,tunda kasan yana bibiye da kafafen yada labarai,annin
dai ita zaka zatarwa haka" Kai ya girgiza yana yin qasa da kan nashi,yasa hannunsa
yadan shafi qasan wuyansa.

"Yanzu mene abunyi?" Farouq ya tambayeshi yana kallonsa.

"Dole komai ya kasance cikin hikima da kuma tsanaki,hakanan for now dole mu zama
cikin takatsantsan da sanya ido akan kowa,faruwar wannan kadai ya sake gayamin
tabbas akwai wasu qofofi dana bari a bude......akwai wasu bayanai namu tabbas da
suke fita.....akwai wanda kuma yake dauka yakai din......sadiq " Fu'ad ya fadi yana
dubansa

"Na'am hamma"

"Inaso kabar kowa a haka,kada ka sake amsa waya ko maganan kowa.....amma ka
shiryamin meeting na sirri,koda me sunan malam banason yasan da zaman.....ka tsara
awannin da zamu zauna din zuwa tashi,zai fara daga goma na safe har sai sanda na
buqaci tashi......general meeting nake buqata"

"Okay hamma" Ya fadi yana sauke system din saman cinyarsa cikin qoqarin duba
schedule dinsa na yau yayi cancelling wasu ya kuma gyara time na wasu koda akwai
yiwuwar zai iya gabatar dasu.

Sun jima da farouq a wajen suna tattaunawa kafin farouq din ya miqe ya
wuce nasa sassan da zummar shiryawa,don yanason ya bishi zuwa kamfanin.

Sai qarfe tara saura suka fito,kaman ko yaushe ya taka zuwa sassan
anni. Kowacce safiya takan zauna a parlor har sai taga ficewar kowa zuwa wajen
sana'arshi. Yau dinma tana zaune cikin riga da zani na lallausar atamfar super
exclusive me ruwan sararin samaniya da ratsin ruwan ganye. Ta lullube jikinta da
tattausan mayafi dan turkey daya dace da atamfar,dukka hannayenta siraran awarwaro
ne masu daukan idanu da suka dace da fatarta da batayi komai na darajar kulawa
nutsuwa da kwanciyar hankalin da take ciki.

Kamar kullum kuma kaman ko yaushe ya duqa gabanta suna gaisawa. Yau din
bata ja zance dashi ba saboda ta karanci kaman gaggawar fitar sukeyi.

"Muhammadu" Ta kirashi sanda suka gama sallama ya juya zasu fice


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 77


A nutse ya waiwayo sannan ya amsa

"Na'am anni......akwai wani abunne?". Kai ta girgiza tana jin tausayinsa hakanan
yana tsarga mata. Tasan cewa akwai abubuwa da yawa da suke damunshi cikin
zuciya,amma shi din wani irin mutum ne me masufar zurfin ciki. Zai wahala kaji ya
b'ara ko kaji kukanshi.

"Kaman akwai wani abu ko?" Ta jefa tambayar gareshi don batason fitowa kai tsaye ta
Qureshi da tambayoyinta

"Ba komai anni" Ya fada cikin bata tabbaci,don yayi imani ya nuna mata akwai
damuwar,to yinin yau gaba daya haka zasu barta cikin rashin sukuni.

Kai ta gyada ba don ta yarda ba,sai don tasan koma meye idan ya dace ta
sanin shine mutum na farko da zai fara gaya mata

"Ubangiji ya kauda dukkan abunqi,Allah yayi jagora"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu anni,na gode" Daga haka ya juya yana fita. Har cikin
ransa yakeji irin wannan addu'o'in nata,duk kuwa da cewa bawai shi daya takewa
adduar ba kowannensu ne,amma yakanji a ransa kamar tasa ta dabance.

Bai shiga mota daga parking lot na gidan ba,sai yace su fiddo
motocin su sameshi waje. Ya soma takawa a nutse suna jerawa shida farouq suna
tattaunawa kadan kadan har suka fito a gidan.

Sanda suka doshi gidan nasu yayi tsammanin farouq zai dakata daga yi
masa rakiya amma sai yaga yaci gaba da binsa har suka isa bakin gate. Sun gaisa da
malam saidu cikin girmamawa sannan suka kutsa kai ciki,guards dinsa guda biyu dake
biye dashi suka dakata suna jiran fitowarsa.

Tunda ta wayi gari ta kasa tabuka komai,tana kwance kawai a daki tana
kwancewa da saqawa bayan doguwar wayar da sukayi da hajja harira. Anya kuwa nasarar
da take sanya ran samunta zata cimmata?,zata ma iya haqurin kwana ukun da bokan ya
deba mata kuwa ba tare data koma ta sanar dashi komai ba?.

Maida tunaninta tayi tana sarrafa shawarar da hajja hariran ta bata.
Bata jin cewa shawarar zatayi aiki har ta lanqwaso mata me babban suna yadda
takeso?.....anya bazai zama doguwar hanya me wahala ba?.
"Waye ne?" Tayi tambayar cikin izza sanda taji an nace da knocking mata qofar
bedroom

"Nice hajiya.....yallabai ne yazo" Me aikin ta furta a qasqance

"Yallabai?,fu'ad kenan?" Ta tambaya a mamakance tana duba lokaci

"Eh shine" Ta sake amsawa a ladabce. Cike da mamaki ta kalli agogo. Wannan ba shine
lokacin da suma saba shigowa gareta ba,me ya kawoshi yau da safe?,ko dukka cikin
dabaru da salon son kauce mata ne?.

"Ina zuwa" Ta amsa mata sannan ta fara yunqurin saukowa daga saman gadon.

Tun daga nesa ta zuba idanunta a kansu,hira suke qasa qasa da wani irin
kusanci da emotion da zaka tsammaci su din tagwaye ne da ska rayu qarqashin mahaifa
guda daya. Bata ga wani banbanci ba ko kadan tsakanin danta muhammad jadda
mamallakin kamfanin haqa da sarrafa diamond ba.....da kuma farouq hamza kibiya me
kamfanin saida tsabar abinci da taki ba!.

Meye ribar suna da yayi?,meye amfanin salon banbancin kasuwanci
tsakaninsu muddin a idanu zaka dinga hangar yanayin sukunin rayuwa iri daya
tsakaninsu?. Kamata yayi ace ana hangen tazara tsakaninsu,kwatankwacin tazarar dake
tsakanin bawa da uban gidansa.

Wani irin abu yayi mata tsaye a wuya,amma dole ta saita yanayin
fuskarta sanda ta isa gabansu

"Wato farouq kayi wuyar gani,har gwara sadiq ya fika kirki anfi ganinka" Dukkaninsu
ba wanda zancanta ya kwantawa,saidai kawai sun bita da irin yanayin da tazo musu
dashi. Wannan faran faran sa sabuwar maraba da iyalan Alhaji hamza kibiya sabuwa a
idanunsu da basu taba ganinta ba.....koda kuwa sanda ta dawo ta iske iyalinta cikin
kyakkyawan rayuwa qarqashin jagorancinsu da tallafawar rayuwarsu.

"Wanne irin aiki ne ya riqeku jiyan kaida dan uwanka kuka saka halartar kira na?"
Tayi masa tambayar daketa cin ranta,don har xuwa lokacin bata gamsu wai aiki ne ya
riqeshi ba

Yana murza yatsun hannunsa idanunsa samansu,zuciyarsa na wani irin motsa
cikin yanayi maras dadi. Koda yaushe maganarta babu komai ciki sai zallar son kanta
a ciki......ba wani sauti alama ko yanayi na kulawa ko nuna damuwa......ba wannan
shaquwar da maganadisu dake tsakanin uwa da danta da har zata iya karantar yanayin
damuwa walwala ko farinciki da yake ciki,abinda dukka ta rasasu anni kuma ta haye
kansu ta zauna sosai.

"Yanayi ne na aiki da zai iya rutsawa dakai ako wanne yanayi ko lokaci" Ya amsa
mata a taqaice don bawa kansa kariya .

"Yau kuma fa?" Ta sake fadi tana tsareshi da dukka idanunta

"In sha Allah" Kawai ya fada shima nan a taqaice.

Duka duka zaman bai wuce na mintuna goma zuwa sha biyar ba suka wuce.
Mintuna goman da suke da matuqar tsada da daraja a wajensa......don ita din
itace.....yana jin ya wajaba ko yaya ya bata wadannan mintunan don tserewa tuhumar
ubangiji.

Fadin ma yanayin daya kwana a cikinsa a wannan ranar dare har ya zuwa
safiya bata baki ne. Duk sanda ya waiwaya ya sake duba wayarsa sai ya dinga jin
abun kamar mafarki......kaman baccin daya kwanta shi yakeyi,kaman har yanzu idan ya
farka zai samu komai ba gaske bane.

Daga sallar magariba har ishai saida safe ya hada da asuba ya ramasu.
Gaba daya ya wani firgice ya fita hayyacinsa a tsakanin. Ba abinda yake iya tunawa
sai wanene Muhammed jadda da kuma irin hukuncin da zai iya dauka a kansa.

Duk yadda yaso ma ya yiwa kansa hasashen ta inda zai fara kare kansa a
gaban mutumin da a fagen aikinsa baida maraba da zakin daya fito farauta sai yaga
sam zantukan daya tsara ko kadan basu hau kan saiti ba,basu kuma dace da hankali
ba. Tsananin tsoron da firgicin ya sanyashi kashe wayoyinsa gaba daya,saishi kadai
cikin dakin tamkar tsohon mahaukaci.

Ba abinda kunnuwansa ke gaya masa sai sautin sallamar talauci cikin
rayuwarsa,an debi kudin da ya tabbatar baida abun biya koda kuwa zai saida komai
daya mallaka shi da danginsa su koma yawo tsirara.

Taku biyu yayi don shiga toilet ya rage gudawar da yake fama da ita
tun faruwar abun idanunsa suka fada kan dan kunnen.

Gabansa yayi wani mummunar faduwa

Please Login or Register in order to submit comment