You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da rayuwa ta kawosu inda suke a yanzun ya nema malam sa'idu.
Kyautata rayuwarsa yayi da gasken gaske ba tare da mutane sunsan da hakan
ba......amma sai ya ajeshi a mazaunin me gadi bisa shawararsu da amintarsu shi da
malam sa'idu din,kuma hakan bai hana ya bashi albashi ba duk wata,saidai ba irin
albashin da ake jifan gamagarin masu gadi ba. Malam sa'idu baisan wace maamah ba
bare anni,tun a baya wajen sana'arsa yake lazimtar zama,bai tara jama'a bare gulma
dayi da gidajen alumma ya shigo ciki har yasan abinda gidan wani ke ciki,abu daya
ne dai da har yau bai fahimta ba,jaddada gadin gidan da kula da shige da ficen
matar gidan daya kasa tantance matsayinta a wajensa. Da yake bame damuwa da abinda
bai shafeshi bane bai taba tambaya ba,yana dai aikinsa yadda akace,duk kuma abinda
muhammad din yake da buqatar sani yana sanar masa.

"Mu zauna daga nan" Fuad ya fada yana neman wajen zama saman bencin da malam
sa'idun kan dan kashingide akai wani lokaci.

"Aa haba yallabai.......ai sai ka bata kayanka kuma......bari a dauko maka kujera
daga cikin gida kafin mutanen gidan su qaraso"

"Yi zamanka" Ya fada cikin ko in kula. Mamaki ya sake kashe malam sa'idu. Duk uwar
dukiyar daya mallaka,kyau....ilimi duk basu sanyashi jin ya bambamta da sauran
jama'a ba.

"Ita kadai ta fita?" Fuad din ya tambayeshi yana zaro wayarsa

"A'ah....su biyu ne" Ya amsa masa kai tsaye,don ba tambayar da zaiyi masa da zai
boye masa wani abu. Kai ya daga yana duban malam sa'idu din jin ya ambaci ita da
wata.....Allah yasa abinda yaketa qoqarin kaucewa da fatan kada ya faru ba shine ya
soma faruwa ba

"Sun jima da fita?"

"Eh ya kusa awa biyu zuwa uku haka" Ya sake amsa masa. Idanu yadan zubawa malam
sa'idu din kamar yanason fahimtar wani abu daga gareshi,sai kuma ya janye idon yana
fesar da iska daga bakinsa,sai ya samu kanshi da Maida wayar aljihunsa kawai ya
miqe daga zaman da yayi niyyar yi da,ya dawo gaban gidan ya tsaya sosai jikin
realer da aka yiwa gaban gidan adon flowers da ita,idanunshi bisa hanya zuciyarsa
na karanta masa abubuwa iri daban daban.

Tun dazun tunani da hankalin maamah yana kan hajja,har zuwa lokacin da
mintuna kadan suka rage musu su isa ga unguwar

"Yarinyar can fa hajja kin kaita wata unguwar tana jira". Murmushi hajja ta saki da
qaramin tsaki a hade

"Bari ki gani" Ta fada tana daukan wayarta daga saman cinyarta.

A hands free ta saka wayar,bugu daya ta daga. Akwai qaguwa sosai cikin
muryartata,amma kuma bata isa ta nuna hakan ba koda da wasa kuwa

"Hajja na qaraso"
"To yayi.....na bar wajen,zan turo miki address na inda zaki sameni,na gaji gida
nakeso na wuce,kada ki wuce minti biyar baki iso ba"

"To hajja" Ta amsa mata a sanyaye. Katse kiran tayi,murmushi na subuce mata ta
kalli maamah

"Yanzu nan zata zo cikin minti biyar?" Maamah ta tambaya cikin mamaki

"Kuma mijinta shi zai maidani gidanma a gabanta ba....da kai da kaya ai duka
mallakar wuya ne". A gajarce ta tura mata adress din,sannan ta fara qoqarin kiran
yahaya daidai sanda suke karyo kwanar da zata sadasu da shimfidadden jadda street
din dake rubuce jikin wani qaramin allo dake kafe a farkon layin.

Tunda ya hangi motar ya ganeta kafin takai ga isowa. Yaci gaba da bin
motar da idanu har ta qaraso qofar gidan,tayi kuma yi tsaiwar bawa malam sa'idu
umarnin bude mata hanyar shigewa,sai a sannan ya sauke hannayensa yana duban
tayoyin motar da sukayi bududu abinda zai shaida maka ba qaramar tafiya akayi da
motar ba,tafiya me tsaho kuma cikin guraren da basu da shimfidadden titi ya saka
kai yana wucewa ciki kafin malam sa'idu ya kammala bude musu gate din.

Kansa a qasa yake takawa cikin gidan,haka kawai zuciyarsa yakejin bai
gamsu da yanayin fita da kuma shigowar motansu a yanzu ba. Cikin falon ya yiwa
kansa gurin zama. Ba kowa a ciki,don dama muddin idan bata nan din bata aminta da
masu aikin nata su kusanci falon har sai ta dawo.

Tun tsaiwarsu bakin gate din ta ganshi,wannan ya sanya driver yana
aje motar qasan rumfar aje motocin ta bude ta fito

"Ya da sauri haka ko duk gajiyar ce?" Hajja ta tambayeta sanda take tattaro jakarta

"Yaroncan Muhammadu na gani,yana ciki yana jira,bansan tun yaushe ya shigo gidan
ba.....banyi zaton jirgin safe zasu biyo ba" Ta fadi hankalinta yana yin cikin
gidan. Da kallo hajja tabi maamah din ganin yadda duka hankalinta yayi cikin
gidan,sai kawai ta jinjina kai ta soma yunqurin fita a motar itama tabi bayanta.

Qafafunsa na harde cikin juna yayin daya jingina bayansa da makarin
kujerar,ya zube idanunsa duka a bakin qofa yana jiran ganin shigowarta. A wannan
yanayin ta murda qofar ta shigo,tanata qoqarin azawa fuskarta rashin sukuni da
gasken gaske. A wannan karon batajin zatayi masa da wasa akan dukka buqatun da zata
bijiro masa dasu.....dole yayi yadda takeso wanda shine zai zama cikamakin burin
MALLAKAR 'YA'YANTA.

Duk yadda taso tayi diban watsin tsiya dashi amma sai kwarjininsa
yakeson bugar da ita. Hausawa sukace kuma wanda yayi me kyau ya sani haka wanda
yayi maras kyau. Idanun da yake binta dashi sai ta dinga jin kamar yanason karantar
daga ina take?,me kuma taje yi?.

"Sannu da zuwa" Ya fada a nutse yana zare qafafunsa daga cikin na juna daidai sanda
take aje mayafinta da jakarta

"Ai kaine da sannu" Ta fada a taqaice tana ta tattalin fushinta da bacewar fara'a
daga fuskarta,saidai kuma wani bangaren na zuciyarta yanata saka mata tsarguwa da
kuma shakku.

Hada ido sukayi a karo na uku,sai ta kasa jurar kallon da yake binta
dashi din

"Kana mamakin na baka umarni baka bi ba kazo na sameni a raye ban mutu ba ko?" Ta
fake da wannan,don batasan da abinda zata iya qalubalantar kallon nasa dake mata
wani irin nauyi da kwarjini ba. Idanun nasa ya sauke a qasa yana girgiza
kansa,baikai ga cewa komai ba ta sanyo kai da tata sallamar.

Ita dinma dashi suka fara hada idanu,saidai nata kallon yafi na
maamah tsini a nata idanun da zuciyar. Kwarjininsa ya cikata fal,hakanan alfaharin
ganin farko wa mamallakin jadda diamondchore resources ya cikata.

Sunansa ya jima da shiga kundin nata lissafin,saidai a dukka
hasashenta bata taba tunani ko zaton samunsa a nan kurkusa ba.....bata taba kawowa
cewa yana da wata alaqa ta jini me kusanci irin haka da tsohuwar qawa kuma
aminiyarta mariya ba.....bata taba hasashen mariyan tana da nasibin haifar babban
mutum har kamar Muhammad jadda ba.

"A'ah.....yaron namu ya iso kenan......maraba" Ta fada tana sauya reaction na
fuskarta cikin qasa da second biyar tare da takowa cikin falon a hankali. Akaikaice
yake dubanta da wani irin kallo,sam baisan fuskarsa ba......bai kuma tuna ko yaya a
inda ya santa ba,ta yaya ita din akayi tasan wayeshi?,yaya akayi tasan daga tafiya
ya dawo?.

"Bana jin zaka iya shaidani.....shi ya sanya banyi mamakin musaddiq daya kasa
ganeni ba.....ga yayansa ma ya gaza shaidani?" Ta fadi tana sakin fara'ar da bata
kai ga qarasawa ainihin zuciyarta ba,yayin da kwarjininsa ke barazanar hanata samun
abun fadi. Still dai baice komai ba yana ci gaba da dubanta. Ko dis baiji matar
tayi masa ba,bai hangi dattako ko kamala da sukayi daidai da shekarunta ba a
tattare da ita,sai kawai ya dauke kallonsa daga kanta don baiga amfanin maida
hankali tare da son qoqarij fahimtar abinda ya tabbatar daga qarshe bame amfani
bane,amma ina suka fita har na tsahon awannin ita da maamah din?. Tambayar data
maqale masa kenan,bashi kuma da amsa.

Qafarsa kawai ya miqa ya zira takalmansa ya miqe

"Lokacin sallah ya kusa,zanyi salla na dawo" Ya fadi yana juyawa a nutse yana fita
a falon.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 57
_________________________
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy


Assalamualaikum

Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma
Kuma kina tunanin chake kudi kisaya a dunkule??
Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen??
To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT
KITCHENUTENSILS* (Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki
ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin kayan kitchen.
Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide
kudinki.
Ba iya nan muka tsayaba, farashin kayanmu daban yake a ko ina.
Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da
Kuma ganin yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode

https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
____________________________

"Yaa huda.....yaa huda?" Muryar haneefa ta ratsa kunnuwanta dai dai
sanda take kwance qudundune cikin bargonta. Kusan idan bawai dare ne yayi ba hakan
ba dabi'arta bace,amma a yanzun yana neman ya zame mata dabi'ar da sabreen ta fara
karantar hakan.

Batakai ga ce mata komai ba,don ba abinda ta gani behind kwanciya din
da take yawan yi,sai ta barshi kawai a zuwan yanayi ne da yakan sauyawa kowanne dan
adam. A yanzu ma gaba daya hankalinta yana kan ayshatu.....ciwonta gaba yake qara
yi,ga mika'il a gefe,ga mashkur shima daya sanya wuta da yawa a kanta. Ya'aqoub ne
kawai me dan sauqi saboda bai cika zafafawa ba. Dukkansu batason kowa ya subuce
mata a daidai wannan lokacin da shirinta ke qara zurfi a kansu,kuma tafi hangen
samun nasara da wuri akan mika'il da mashkur,don shi ya'aqoub a yanzu tunaninsa
yafi karkata kan yadda zai shawo hankalinta ta aminta ta aureshi,abinda kuma bataga
ranar yiwuwarsa ba. Wai mema zata tsinta ne a auren?,bayan tana ganin yadda su
mazan suke?,tana ganin kuma yadda matan ke komawa?,ko hanyan aure yanzu mutum yayi
mata ai bai qaunarta ballantana ace mata tayi. Duka tsari da halayyar mazan baiyi
mata ba ballantana ta cusa kanta a sabgarsu da nufin zama tsakaninta da waninsu
zama na din din din?.

Miqewa tayi a dole tana duban haneefa,sai haneefa din ta miqo mata
takarda tana cewa

"Wani ne wai a waje yace a baki...." Da sauri ta fiddo mata idanunta waje sanda
muryar sabreen wadda ke amsa waya take dosowa cikin dakin. Yadda suka daga kai suka
kalleta duka su biyun ya sanyata janye wayar daga kunnenta tana kallonsu

"Lafiya?" Tayi tambayar tana sauya yanayin fuskarta. Wani faduwa gabanta yayi,cikin
tsoro tsoro ta girgiza kanta tana qaqalo murmushi tace

"Ba komai.....ina kwance haneefa ta tsoratani,na dauka wani abune da naji tanata
tashina". Idanu ta sake zuba mata na daqiqu sannan ta amsata tana zama gefan nata
gadon

" Ko bata tsorataki ba dama ai yaci ace kin tashi,an kusa kiran sallah.....uniform
dinku nadra ta wanke tunda kin koyi laziness......kije kiyi alwala ki dawo ki
kwashe abincin tukunya a flask a wanke sauran abinda ya rage".

"Tom" Ta fadi tana matse takardar a tsakiyar hannunta tare da tunanin yadda zata
miqe da takardar ba tare data lura da ita ba,to amma kuma ci gaba da zama dinma
tunanin mafita tamkar tana bata damar dora ayar tambaya ne a kanta.

Aljihun skirt dinta ta tuna dashi,cikin dabara ta cusa a ciki,sannan
ta zame ta sauko tana gyara inda ta kwanta din,ta daura dankwali saman doguwar
sumarta ta juya tana fita a dakin. Dauke idonta tayi daga kan tab dinta ta bita da
kallo. Haka kawai ta gagara samun nutsuwa kwanaki biyun nan,duk motsinsu a kan
idanunta yake,kuma da gaske tana ganin dan sirkawar wani abu kadan tattare da huda
din.

Bandaki kawai ta wuce kai tsaye tana fata da zumudin budewa taga meye
a takardar?.

Sai data samu guri cikin toilet din ta zauna sannan ta ciro takardar
ta kuma warwareta.

Kaman yadda ta zata shi dinne,sunansa kawai data gani sai bugun
zuciyarta ya qaru da kaso hamsin cikin dari.
Yau kwanaki uku kenan,ya rakota daga hanyar makaranta har dab da
gidansu kamar yadda ya saba a kowacce rana......tun tana gocewa har ya fara zame
mata sabo ba tare da sanin nadra ko haneefa ba wadda yanxun aka banbanta musu
lokutan tashi qarfi da yaji ba tare da kowa yasan dalili ba. Ya zame mata kamar
abokin rakiya a yanzun.....tun tana dari dari da tsoro har hakan ya fara gushewa
daga zuciyarta.

A ranar alhamis tayi matuqar mamaki yadda ya tsaya suna tsaka da
tafiya,ya kuma kafeta da idanu

"Lafiya kake?" Ta tambayeshi da mamaki

"Ke kyakkyawa ce" Ya fadi yana jin wutar sha'awarta na ruruwa a ransa tamkar yadda
ya dinga jin ta 'yar uwarta. Yana jin kamar ya dauketa a yanzun ya wuce da ita ya
aikata abinda ya tanadi aikatawa,saidai kuma bazaiyi haka ba,yanason komai ya
kasance a daidai sanda zatafi jin ciwo da radadin da zai iya zama ajalinta,ya kuma
tarwatsa farincikin da take musu tattali. Yanason idan ya tashi ya tarwatsata
tarwatsewar da ba zata taba dawowa ta gyaru ba ballantans ta koma yadda take.

Idanu ta waro tana dubansa,yadda yake yawan kambata da kurantata ya
sanya kusan kullum sai ta kalli madubi......kusan kullum sai ta kalli kanta da
kanta taga wannan kyan da yake magana a kai......wannan budurwar da yake yawan
kiranta dashi. Tun bata ganin abinda yake fada din har ta fara ganin,amma tana
ganin kaman bata ca canci kowacce rayuwa ba a yanzun......karatu shine yafi da cewa
dasu kamar yadda yaa sabreen ke gaya musu

"Ina sonki huda.......ina tsananin qaunarki tun daga ranar dana fara
ganinki.......zuciyata tana miki wani mahaukacin so da bansan iya adadinsa
ba......wallahi inaji a zuciyata tamkar zanyi hauka saboda ke huda......ki soni don
Allah......ko baki sona ni zan koya miki yadda zaki soni din". Kalaman da suka
tsoratata suka kuma razanata kenan. Kalaman kuma da Naseer din ya shiryasu ne kawai
don ya soma wasa da tunaninta da qwaqwalwarta,plan na biyu kenan daga cikin
tsarikansa.

Baya taja tana girgiza kai,tana jin tsoro yana shigarta. Wacce irin
soyayya a shekarunta?,duka duka nawa take?,koda yaa sabreen bataga ta kawo kowa
tace shi zata aura ba,bataga wani yazo qofar gidan da sunan zance wajenta
ba.....koda abinda ake maganarshi a kanta da nasu idanun basu taba ganinta cikin
motar wani ko tsaye da wani ba har zuwa yanzun da take tsaye a gabansa. Ko rakota
da yakeyi kullum kwanan duniya a tsorace take......wani lokaci zuciyarta tana raya
mata idan sukayi kacibus da yaa sabreen fa?,sai kuma zaqin bakinsa da daddadar
hirarsa ta yaudare tunaninta da kunnuwanta.

Tayi mugun tsoratar data dinga ja da baya da baya tana girgiza kai.
Yana tsaye ya kafeta da idanu,abun yana masa sugar sosai. Irin hakan yafi buqata
don ta haka ne sabreen din zata fuskanci girman nasa aikin. Ya samu sabon ruhi
sabon gangar jiki da baisan komai ba game da rayuwa......zai hurewa zuciyar
kunne,sannan ya mori gangar jikin yadda yaso ya kuma watsar da ita tamkar wani
yasashen abu maras amfani. Yana tsaye harta gudu a layin ta bacewa ganinsa,sai ya
bushe da dariya.

Hakan da tayi ya tabbatar masa qwaila ce,ya kuma bashi tabbacin baa
taba gaya mata kalmar so ba sai a kansa

"Allah sarki......gashi baki fara da jin kalmar ba a sa'a......anyway......ko mene
ya faru dake 'yar uwarki ce taja miki" Ya fada yana juyawa don barin layin ya
qarasa inda yaransa ke cikin mota suna jiransa.

Hannunta har rawa yake sanda take warware takardar. Tsakanin alhamis
jumaa asabar da kuma yau lahadi ba wasu mintuna biyar kyawawa da suka wuce ba tare
da tunanin abinda ya faru tsakaninsu ya dawo kanta ba. Duk juyin da zatayi sai
kalamansa sun dawo mata,kallonsa murmushinsa da kambamawarsa. Fuskarta kam ta
kalleta yafi sau adadi tana sake duba kyawun surarta da yake yawan jaddadawa. A
yadda take gani ba mace me kyan yaa sabreen dinsu......ashe itama to tana da kyau
dinne da gaske?,ko kuma yana fada ne kawai?.

*_Hello me kyau,fadin azabtuwar da idanuna da zuciyata sukayi saboda rashin tozali
dake ba abu bane me sauqi......ina fata zaki daure a gobe ki barni naga wannan
kyawawan idanun da zuciyata ta mutu a kansu.....idan ba haka ba.....zan iya rasa
numfashina_*

Da sauri ta duqunqune takardar ta kuma jefa a toilet ta bita da
flushing zuciyarta na bugawa sosai. Tsoro zumudi fargaba da mamaki dukka suka hade
mata har ta rasa wanne tunani ma zatayi.

Bugun qofar bandakin da akayi ana jiranta ya sake rudata,sai kawai taja
qofar ta bude ta fito ba tare da tayi komai ba,taja burki bakin famfo ta daura
alwala tayo dakin nasu.

Gaba daya tunaninta ya karkata ga saqon,har ta mance da batun kwashe
abinci tayi zaune saman kujera tana bitar saqon da ya riga ya rubuta kansa da kansa
a kwanyarta. Fitowar sabreen din ya sanyata tunawa,ta miqe da hanzari ta nufi
kitchen.

Yanzunma da kallo sabreen ta bita har ta shige kitchen din. To wai me
yake samun huda take wasu wasi haka?. Bata sani ba,sai ta girgiza kai ta taka
hannun kujerar tana dauko babbar dardumar da sukan shimfida suyi magariba da ishai
akai suyi bitar karatun makaranta ta taimaka musu da wanda zata iya.

Da ruwan zafi sosai tayi wanka bayan wucewar hajja saboda ciwo da
jikinta yake mata sakamakon zaman mota data jima batayishi kaman haka ba. Ta shirya
kanta cikin fafi indian abaya me laushi,ta yane kanta da mayafin abayar daya
kasance medium cotton kaman yadda jikin dogon rigar yake.

Cikin falon tayi zaune bayan ta kirayi me aikinta ta canza mata channel.
Qafafunta a miqe saman side glass table din,hannunta dauke da glass cup dake cike
da lemon raspberry tatacce me asalin tsadar. Babu wani abu da zata ci ko tayi
amfani dashi cikin gidan da yake da qaramin kudi. Komai nata me tsada take
zaba,hatta da ruwan da zata sha kuwa ballantana akai ga sutura ko wayar hannunta.

Ko a yanzun haka ta gaya masa tana buqatar ya sauya mata iPhones din
hannunta guda biyu. Iphone 15 da wata tsaddadiyar waya sabuwar qira da kamfanin
Samsung's. Duka duka wayoyin ba wadda tayi wata uku,to amma garin gane ganenta ta
hangi wasu sabbin fitar,su kuma takeso ta riqe.

A komai tafison ta zama cikin sahun mutane na farko da ake ganin komai
sabo a wajensu. Inda tana da iko komai zai zamana ana ganinsa ne ta wajenta,sanda
zai soma zagayawa hannun masu kudi irinta ita ta dade da cin zamaninta. Ta sani,a
dukiyar da d'anta yake dashi yana da qarfin kudi da mulkin da zai iya sanyawa a
qera mata duk abinda take buqatar ya kasance nata ita kadai daga kowanne kamfani a
fadin duniya,to amma ta fahimci rayuwarsa baya daidaitata dai dai data sauran masu
kudin irinsa. Ba kuma haka takeso ba.....ba haka take muradi ba......tanaso ta
gansu suna rayuwa daidai da matakin arziqinsa. Ta fahimci yana cikin sawun mutanen
da ba kasafai suke bayyana arziqinsu ba,sai abinda ya riga ya bayyana ba yadda
zasuyi dashi.

Aka idar da magariba akayi ishai shuru. Tun tana tattalin maganganun
da zatayi dashi har wasu suka fara bace mata. Ta daga kai ta kalli agogon dake
shirye saman tv din falon takwas da rabi na dare,to shin sai yaushe zai shigo?,sai
yaushe wannan abun zaizo qarshe?.

Sannu a sannu sanda taga an doshi tara na dare babu
alamunsa,wayoyinsa dukka a kashe shida musaddiq din da zata sanya ya kira mata shi
a duk inda yake.

A ranta ta dinga jin cewa hadin baki ne......a ranta kuma ta dinga ji
aminatu ce ta hanasu.....a yanxun haka qila suna can gabanta......ta zaunar dasu
sai abinda tace musu.

Wannan tunanin ya dugunxuma mata zuciya,har taji bata da wani sauran
zama cikin gidan. Dakinta ta wuce kawai bayan ta ajiye kofin lemon,ta shiga zaro
takalmi cikin jerin takalman alfarma dake adane a shoe rack dinta. Cikin zuciyarta
takeji yau din Alhaji hamzan zata tunkara......tanaso taji shine yayi mata cikin
yaran ko ubansu?,tana so taji da ita dasu wai waye ahaqqu dasu?.

"Nazo muje ne?" Zuwaira ta tambayeta sanda taga tana dosar qofar fita daga falon

"Zauna basai kinje ba" Ta amsa mata a gaggauce tana fita a gidan.

Mugun bugun da takewa tafekeken gate din gidan ya fusata securities din
gidan,saidai kuma lokacin da suka duba wadda ke bugun ta na'uarar tsaro dole
kowannensu fusatarsa tayi nata guri.

Basusan ainihih matsayinta ko ita wacece ba......amma yadda suka
fahimci girmamawar da take samu daga mazauna gidan ya basu alamar cewa tana da nata
matsayin na daban.

Ko kallo security din daya bude mata qofar bai isheta ba ballantana
tabi takan welcoming nata da yakeyi tare da bude mata qofa ta biyu da zata sadaka
da farfajiyar gidan. Daga nan wasu security din su sake marabtarka kashi na uku
kenan kafin kakai ga ainihin cikin gidan ka zarge qofar da zata sadaka da babban
falon anni na farko.

Bata taba tunanin zata sake takowa cikin gidan ba karo na
biyu.......don duk lokacin data tako din alatun gidan yakan zame ma idanu da
zuciyarta barazana. Tana jin kamar kowanne abu idan ta kalla a gidan yana mata
izgili ne tare da gaya mata da dukiyar danki aka samar dani......baki kuma da wata
izza ko power ta mallakata.

Kowanne taku daya idan tayi cikin gidan ranta quna yake......sak
fasalin yadda takeso gidan da zata rayu ya kasance sai gashi kacokam a yau din irin
wannan dream house din nata mallakin aminatu ne.. Wasu mutane da basu da
masaniyar sanda ta dauki cikin fuad har ta haifeshi.

Qofa ta qarshe da zata bata daman shiga falon annin nanma sai data
jinkirtawa na'ura sannan ta bata izinin shiga,ta dauke kanta ranta yana suya da
wani irin fushi. Tafi qarfin ta tako gidan alhaji hamza har abada.....inda sun bata
girma da martabarta da a yanzun ba shakka ita ake zuwarma haka neman gindin zama.

Tana sane da yadda mabuqata ke yawan ziyartar gidan karbar taimako a
duk sati......taimakon da ta tabbatar daga fuad ake rabashi.......sai gashi ita duk
yadda taso ta dinga cina farfajiyar nata gidan da mabuqata,tana raba musu kudi a
envelope yadda taso abun bai samu yadda takeso ba. Bai hana taimako,amma saidai ta
rubuta list na mabuqatan ya hadasu dana gidan alhaji hamza a raba musu taimakon
tare.

Bata samu yin sallama ba,sai Allah ya sanya tana sanya qafafunta a
falon idanun anni dake kashingide cikin lausasan sofa ya sauka a kanta.

"Ikon Allah" Anni ta furta tana miqewa daga kashingidar da tayin tana sauke
qafafunta qasa idanunta akan maamah

"Da kinyi zamanki ma.....don ni ba wajenki nazo ba kaman yadda na alqawarta zuwa na
na qarshe gidan nan......wajen hamza nazo" Maganar tata tazo qarshe dai dai sanda
amna ke fitowa daga kitchen ta zuba abincin dare,don tace yau

Please Login or Register in order to submit comment