You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciyarsa.



Daga saman balcony din da zata sadaka da ainihin falon suka sameta a zaune ta
hakimce. Faruqee ne a gaba,musaddiq yana biye dashi,sai me babban suna da ko qaunar
hada idanu da ita bayayi. Zuciyarsa yadda take a zafafen nan tana ayyana masa
abubuwa masu dama a kanta.



"Idan ka kuskura ka qaraso na saina sanya an maka dukan tsiya......baka isa ka
shigamin gida ba tunda kai din tantiri ne mara kunya.....nan gaba kadan shaye shaye
zaka farayi da daba,kaga kenan ka samu hanyar da zaka hallakani a banza" Ta fada
tana miqewa tsaye.
Dukka su hudun sukayi carko carko suna dubanta da jin kuma wani sabon bala'in daya
tunkarosu kuma bayan na dazu da safe.



"Kai har ka isa na fadi magana ka sabamin bare ka maidamin?,don an zagi uwarka da
ubanka,su su waye da ba za'a zagesu ba?,wato gaka kai me zuciya ko,to an zagesu din
na kuma zagi banza da wofi".

Da qarfi ya damqi hannun saddiq ya kuma soma ja da baya yana janye jikinsa daga
wajen



" Yauwa gwara daka fahimta,don wallahi kabar gidan nan kenan,tun yanzu kana
tsayarmin ina ga nan gaba idan ka gama zama balagagge?".



Da sassarfa Faruqee da har ya isa bakin qofar falon ya soma saukowa yana takowa
zuwa garesa ganin suna nufar gate din fita daga gidan yana qwala masa kira da
niyyar tsaidashi



"Aisai ka bishi kaima don ubanku,na fiku iskanci qananun balagaggu" Ta furta tana
komawa saman kujerar ta zauna



"Bar nan gurin" Ta kwatsawa musaddiq daya mace a wajen saboda tsoro da mamaki
tsawa,baiyi wata wata ba ya juya shima yabi bayan 'yan uwansa.



Bai iya tsaidashi ba har sai da suka isa qofar gidansu dake garqame. Sai sukayi
carko carko suna kallon kallon shi dashi. A yadda ya hangi kwantaccen fushi da
bacin rai akan fuskar me babban suna sai ya rasa da wadanne kalmomi zai iya shawo
kan me babban suna?,wacce kalma ce zatayi masa aiki?.



"Kayi haquri kazo mu koma,tunda gidan abba ne ba nata ba bata isa ta hanaka zama
ba,yau ko kasheni zatayi saidai ta kasheni" Wani irin kallo ya yiwa Faruqee,ga
mamakinsa murmushi ya gani ya subuce masa.



Da wani irin zafi ya waiwaya ya dauko dutsen dake yashe gefan malalen simintin dake
gaban gidan nasu,har tsoro ya kama Faruqee yaja da gefe,sai yaga ya doshi qofar
gidan,ya kama kwadon dake jiki ya fara bugeshi baji ba gani.



Tsakiyar azahar ne,wannan ya sanya ba yawaitar jama'a a layin bare a samu me
dakatar dashi. A yanayin da yakejin zuciyarsa da kansa a ciki,bayajin akwai ma
wanda ya isa ya dakatar dashi din sai MUTUM DAYA TAK A DUNIYA.....ALHAJI HAMZA
KIBIYA.



Zare kwadon yayi ya watsar gefe,kansa tsaye kuma ya soma cusa kai cikin gidan ba
tare daya damu da yana datti ko qurar data lullube qofar ba.



Wannan shine mafarin komowarsa gidansu......tushensa......asalinsa da yaji yafi
masa kwanciyar hankali sau dubu akwan kwanansa cikin babban bedroom din gidan alhj
hamza dake dauke da wuta 24/7 da kayan alatu na rayuwa.



Tun a asalin halittarsa shi jajirtacce ne tsayayye da bai yarda da faduwa
ba......sanda komai ya dinga faruwa kuma daki daki,sai zuciyarsa ta qara qeqashewa
ta kuma tsaya kyam......ya karantawa kansa da kansa cewar shine uwa kuma uban kansa
da dan uwansa sadiq.......shine gatan kawunansu,ya fidda kowa daga cikin zuciya
rayuwarsa dama hasashensa. Wannan ya sanya tun rana ta farko da suka dawo gidan bai
kuma karbar koda ruwa daga gidan alhj hamza ba. Duk da yadda ran Faruqee ke baci da
yadda yake wofantar da komai da ya kawo musu din kuwa koda ruwan sha ne. Da kansa
ya tsaya,sadiq na debo ruwa shi kuma yana wanke komai da yayi saura na gidan wanda
zasu iya amfani dashi. Cikin kwanaki uku kacal ya fara Qwadago.



Duk wani aiki da zai samar masa kudi......komai wuyarsa kuwa muddin halas ne yana
karba yayishi hannu bibbiyu. Da wannan din ya dogara.....da dan abinda yake samu
din ya dauke musu abinci dama abin sha......idan faraga ta samu harda kudin
transport na makaranta koda na zuwa kadai ne banda na dawowa.



Sauyawar yanayi da kuma tsarin rayuwarsa ya sake canxashi gaba daya. Yana tsananin
son karatu kowanne iri ne,na addini dana boko gaba daya


*_TURQASHI_*

*_BIGI SAI BIGI_*

*_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_*

*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE
A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*

*_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_*

*_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_*
*QAMSHI IYA QAMSHI 24HR*

*HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA*

*NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER*

*_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_*

Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Original musk tahara
Multipurpose spray

*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*

08032119803

Ko ki lalubeta ta nanπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ

*Instagram handle_incense by kabo daughter*

*Facebook_kabo daughter*

*Twitter_kabo daughter*
________________________________


_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯°


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997



PAGE 10


Baya wasa da islamiyya,amma wahala da nauyin kansa dana saddiq ya sanya
ya sallamawa zuwa islamiyya. Duk da haka bai sare ba,ya lalubi makarantar magariba
ta manya ya soma zuwa don karantar litattafan addini,duk kuwa da nisan zangon
tafiya dake a tsakaninsu.

Su kansu ba 'yantattun 'ya'ya bane cikin gidan mahaifinsu......amma
duk da wannan ya gaza barin me babban suna yakuma qyaleshi kamar yadda ya fuskanci
yana da muradin hakan. Duk da basu da 'yanci ko fada aji a gidan......amma hakan
baya hanashi dauko abinci daga cikin nasa kwanon data qayyade musu cikin gidan ya
kawo don suyi tarayya suci tare,amma koda wasa me babban sunan bai taba dangwala
yatsarshi a ciki ba.

Abun yana ma Faruqee zafi da ciwo matuqa,har daga qarshe hakan ya
sanya suka samu sabani

"Don mama tayi maka laifi ai ba abincinta bane,abincin abba ne wanda har yanzu a
nasa zaton kuna cikin gidansa ne cikin aminci bisa kulawarta,iyakarta da abincin
nan tazo ta diba itama taci,don ko dafawa ba ita ke dafawa,larai ce......kuma ita
ke qaramin yawan abincin a boye ba tare da saninta ba,to indai bawai nima gaba da
fushi kakeyi dani ba banga abinda zai hanaka ci ba.....idanma kai ba zakaci
ba....kada ka sake hana saddiqu yaci,kai ka zauna haka can ta matse maka". Busashen
murmushi ya saki yana jin yadda cikinsa ke qugin yunwa,don yau ba wani abun kirki
ya samo a aikin ba,wannan ya sanya basu wani qoshi ba wunin ranar sur.....ga kuma
tafiya makaranta a gabansu gobe juma'a.

Yadda Faruqee yayi fushi ya kuma dauki zafi da abun ya sanya yake
barin saddiq din suna hadaka dashi. Shikam yasan bazai taba iya sanya abincin cikin
bakinsa ba. A duk sanda yayi yuqurin hakan sai maganganunta su dawo musu kar kar
cikin qwaqwalwa

"Tunda uwarka ta zube ku ta tafi ta barku,banga uban da zai iya zama daku
ba......uwarku ma ta barku ballanta wani?" Aduk lokacin da zai tuna da irin wannan
maganar a take yakanji komai ya fita a kansa ne,tsananin baqinciki ya mamaye
walwalarsa,wata irin wuta me zafi na taso daga qasan zuciyarsa da ruhinsa dangane
da imaninsa. Ta wani fuskar da mama da sauran 'yan unguwa dake jifansu da muggan
kalamai sai yaji sam baya jin zafinsu ko kadan,da uwa da uba da kuma dangi ake
ado,su kuma basu da ko guda daya!. Ya tabbata lallai su din cikakkun marasa gata
da galihu ne,kuma kowanne suna aka kirayesu dashi sun cancanta.

Yayi imani inda har jadda tana raye.....koda sunfi kowa talauci da
matsin rayuwa......to babu shakka zasu zamo na sahun gaba gaba wajen zama yaran da
sukafi kowa samun gata na kulawa da soyayyar kaka. Saidai Allah baya barin wani don
wani yaji dadi,ya tabbatar haka ubangiji ya tsara musu tasu DUNIYAr,haka kuma yaso
ganinsu a cikinta.

A wannna tafiyar abba yayi nisan kiwon da ya jima baiyi irinsa ba.
Yana rayuwa bisa yaqinin lallai gidansa da marayun Allahn daya dauka riqo suna
lafiya,tunda duk sanda zaya kirata hakan take gaya masa,sannan lokaci bayan lokaci
tana hadashi da musaddiq,shima kuma

"Lafiya qalau muke abba" Shine amsar da yake bashi bisa jagorancin mummunan gargadi
da idanuwa da maman take aike masa duk sanda suke wayar. Faruqee ne bata taba yarda
ta bawa wayar ba,sai a wani yammaci da abban yace ya jiyo muryarsa ta hadasu.

"Lafiya amma ba qalau ba amma.....muna buqatar ka dawo a kusa abba" Bata iya
barinsa ba ta fusge wayar daga hannunsa cikin hanzari ganin yana niyyar sauka daga
layi.

Maganar ta tsayewa abban a rai,ta kuma sanyashi yaji dukkan hankalinsa
yana tarkatowa yana yowa gida. Duk kuwa da akwai sauran abu daya tsara zaiyi a can
din,amman sai yaji komai ya fita a kansa tahowarsa gida ce abu na farko da yake
kwana yana tashi dashi.


*******Kusan dukkansu jan qafafunsu sukeyi,zafin rana yunwa ga gajiya dake tattare
dasu. Akwai nisan tazara me dan dama tsakaninsu da makarantar wanda suke shanyeta
a qasa daga tafiya zuwa dawowa. Babu ranar hutu a garesu idan ba asabar ko lahadi
ba. Ga me babban suna kuwa,baya gane asabar ko lahadin cikin rayuwarsa da
DUNIYARSA. Rayuwar tasa gaba daya a birkice take,bashi da wata dogon hutu daya wuce
makaranta zuwa neman kudin abinci.

Yayi wani irin duhu,dukkan hasken fatar nan da suka gado babu
shi,ya rame daga ainihin halittarsa zuwa wata halitta ta daban.

Tun daga nesa ya soma hangen wani abu da yayi matuqar girgiza hankali
da kuma tunaninsa,ya sanya dukkan wani tunani nashi ya fara sauka daga kan layi,ya
kuma daina gane me Faruqee daketa faman bashi labari yake fadi.

Wata qurace take tashi daga wani sashe na gidansu gami da qarar
zubewar bulalluka. Gefe guda akwai tsaiwar tsirarun mutane da kuma yara wadanda
basa raina abun kallo,hakanan basa bari abun kallon ya wucesu kamar qanqantarsa.

Zame hannunsa yayi daga jikin na Faruqee,a gaggauce da kuma hanzari ya
soma tattaki har zuwa inda aikin ke gudana.

"Gidanmu ne fa.....me yayi ake rusheshi?" Ya furta bayan ya tabbata ya tsaya gaban
mutanen dake gabatar da aikin futu futu cikin qasa da qura.

Dukkansu suka waiwayo suna dubanshi,kafin daga bisani wani dan
tsamurmurin mutum dake sanye da milk riga da wando na shadda,da kuma babbar riga ta
koriyar shadda gami da baqaf hula daya karkatata gefe ya qaraso gabansa yana
dubansa. Bakinsa cike da gashin baki,kai kace daya daga cikin qabilun da suka shude
ne shekaru aru aru.

"Yaro me kake cewa?" Ya fadi yana saba babbar rigar da a zahiri an tafka babbar
asara wajen ware shaddar aka masa rigar da ita gaba daya,don kuwa yadin ya masa
yawa,alamu ma suna nuna kamar rinjayarsa takeyi

"Gidanmu ne nace,me yasa kuke rushe mana gida?" Ya sake jefa tambayar ga mutumin
yana tsareshi da ido da zummar jin ba'asin maganar.

Qaramar dariya yadan saki yana sosa gashin bakinsa da alama qaiqayi yake
masa.

"Yaro man kaza......kai!bakasan tsohuwarka ko ince uwarka ta karbi rabin kudin
gidan daga hannun matata ba sanda zata bar garin?". Fuska da idanu gaba daya me
babban suna ya yamutse yana duban mutumin cike da zallar mamakin da kwanyarsa ta
gaza dauka.

" Ko da yake ma.ba fahimta ai zakayi ba,wannan zancan na babanka ne inda yana
raye,ba abinda zaka gne yaro" Yana kaiwa nan sai ya juya yana dubaΓ± mgainan

"Kuyi ku raba ku zagaye mana haqqinmu" Da hanzari yasha gaban mutumin jin kalaman
da yake sake maimaitawa

"Kada su sake taba mana gida,don nan vidan ba gudan mamata bane da zata
saidashi,gidan mahaidinmu ne daya ginashi da guminsa,ta nemeta ta biyata kudinta
amma mu ba ruwanmu" Tsaiwa yayi yana qanqance idanu hadi da duban me babban suna

"Kai wannan yaron da alama zakayi tsaurin idanu,da alama dai abinda ake fadi a
kanka gaskiya ne......to ai ko kai yanzu ba zakace ga inda uwar data haifeka take
ba,tunda ta bazama yawon duniya ta watsar daku.....". Kalmar ta sokeshi qwarai
kamar kowanne lokaci. Duk a iya adadin fadar da akeyi bai taba yunqurin kare musu
jifan da ake musu da kalmar ba,amma a yau din sai yaji koda sau daya yana da
sha'awar huce musu wannan takaicin shi da saddiq.......yana da marmarin maida
martani koda sau daya ne tak......amma baya sha'awar bata kariya ko wanketa daga
muggan kalaman mutane a kanta,don bashi da abun cewa a kanta,kwata kwata dukkan
wata soyayya qauna ko tausayi na fil'azal a tsakaninsu yanxun baya jin akwai
burbushinsa,abinda ya sani kawai ya kare kansa ya kare saddiq dinsa

"Ba abunda ya shafemu da inda taje ko inda take.......kaman yadda ba ruwanmu da
karbar kudinku da tayi don nan gidan mallakin mahaifinmu ne mallakinmu......abinda
muka sani kawai shine mu din halastattun 'ya'yane da aurar ya samar......"

Daya daga cikin ma'aikatan wanda kuma gidan su yake ta qarshen
layinsu wanda ke tsaye gaban tsani ne ya bushe da dariya

"Dame kwado yafi gaya ku da shegun?,dame kuka fisu?" Yana kaiwa nan ya dauki
qatuwar gudumar da suke dukan saman ginin da ita ya soma taka matattakalar tsanin
yana hayewa da zummar ci gaba da aikinsa na ragargazar ginin da mahaifinsu ya
kwashe lokaci yana zuba kudadensa wajen qawata musu shi. Ya sadaukar da kudi da
qarfinsa wajen samar dashi,ya sanya burinsa akai na ganin sun rayu a cikinsa cikin
aminci da kwanciyar hankali.

Kwata kwata kasa jurewa yaji yayi da mummunar kalmar da yaji ya
jefesu da ita. Sanda ya daga gudumar zai doka......daidai lokacin ba tare daya
ankara ba ya sanya hannu ya fusgoshi sai gashi qasa warwas!. Abinda ya sanya dukka
jama'ar dake tsaitsaye a gefe tun dazun basuyi magana ba yunqurowa,masu salati
sunayi masu yunqurin tayar da babba magini sunayi.
Wani irin mamakin sauyar rayuwa da mutanen dake rayuwa a cikinta ya
kamashi. Da idanu yake binsu


*_TURQASHI_*

*_BIGI SAI BIGI_*

*_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_*

*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE
A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*

*_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_*

*_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_*

*QAMSHI IYA QAMSHI 24HR*

*HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA*

*NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER*

*_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_*

Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Original musk tahara
Multipurpose spray

*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*

08032119803

Ko ki lalubeta ta nanπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ

*Instagram handle_incense by kabo daughter*

*Facebook_kabo daughter*

*Twitter_kabo daughter*


*D U N I Y A TA*

*_H U G U M A_*
PAGE 11
_____________________________

*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*

*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*

*_NA GWADA NA GANI_*

*_YA SUBHANALLAHI_*

*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*

*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*


*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*

*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*

*_ME KIKE JIRA?_*

*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*

*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*

*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER*

*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME
SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*

*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON
QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO
NE?_*

*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*

*_zaki dariya za kuma ki godemin_*

*_gani ya kori ji_*

*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
___________________________




Daga sanda ya jawoshi ya maidoshi qasa......daga sannan yaga iya yawan
adadin mutanen dame wajen wanda sam baiyi zaton sunkai haka ba,bai dauka suna da
yawa haka ba.....amma duk da wannan yawan nasu babu wanda yayi yunqurin yin wani
anu guda daya sanoda ceton rayuwarsu da cetin ginin gidan dashi kadai suma!mallaka
a rayuwarsu wanda zasu nuna suce ya fito daga jini da gumin mahaifinsu?. Me yasa
al'umma ta sauya?,ya dinga duban fuskokin masu luguiguita zancan da kambama abinda
ya aikata din,dukkansu suna tsaye sanda ake himmar rugurguza mafaka guda daya tasu
da tayi saurs,ba wanda ya tallafa,ba wanda ya dakatar. Kusan dukkansu fuskokinsu
bayyanannu ne a idanunsa,fuskokin daya saba gani sunzo neman taimako wajen
mahaifinsu,wanda bai taba gazawa ba da taimaka musu da abinda Allah ya hore
masa,amma yau tsantsar butulci irin na dan adam sune suka juye suna masu tsaiwa
suna kallon wasy na shirin zaluntarsu.

A sanda yayi nisa da wannan tunanin a lokacin babba yayi amfani da
wannan dama yakai masa duka,dukan da yazo masa a bazata banda jin hucin wucewarsa
da yayi da hucin hannun Faruqee daya tare masa dukan. Yaja baya yana maida
hankalinsa jikinsa,sai ya taka dutse ya kuma yi taga taga ya fadi da baya,wannan ya
sanya babba ya sake yunquro masa da nufin turmesheshi cikin baraguzan ginin gidan
da suka fara saukewa,sai Faruqee shima ya taso ya rufa masa baya da zummar baiwa me
babban suna din dauki.

Cikin zafin nama fushi da kuma taurin kai gami da kafiya da taurin
zuciya Shima ya yunqura ya miqe yana jiran qarasowar babba. Idanunsa a lullube suke
da bacin rai,baya hangen nisan tazarar shekaru da kuma girman jiki dake tsakaninsa
dashi.

"Kai.....kai......dakata.....meye hakan?" Muryar nan me cike da kamala tausayi da
dattako ta ratso gurin. Kowa ya tsaya ya waiwaya yana duban saukowarsa daga motar
zuwa takowarsa cikin fusassun duwatsun gurin. Alhaji hamza kibiya ne idanunsa na
kai kawo tsakanin Faruqee me babban suna da kuma ginin gidan nasu.

Mutum ne me cikar kamala da dattako,wanda ya riqe mutuncinsa da kyau.
Yana daya daga cikin dattijan unguwa dake bada Umarni ko shawara abi,musamman da
yake yana da abun hannunsa wato kudi abokan tafiya.

Kunya tadan kama manyan dake wajen da basu hana ba sai tsaiwa kallo
da sukayi,wanda sun tabbatar idanuwansa sun gansu gaba daya.

Bai tsaya sauraren barka da zuwan da suke masa ba,sai qoqarin
qarasawa gabansu kawai da yakeyi bayan yace da saddiq da musaddiq su tsaya daga
baya,wanda dukansu suka tsorata tun farkon rigimar,to amma basu dame kawo musu
dauki bare suyi hanzarin garzayawa su kirashi ko zai cecesu.

Ta gefan babba dake tsaye yana kade jikinsa cikin jin nauyi yana kuma
huci qasa qasa ya wuce,ya qarasa inda me babban suna ke zaune warwas ya miqa masa
hannu ya tasheshi tsaye.

Yana tsaye a gabansa ya bashi handkerchief yana karkade jikinsa.
Idanun alhaji hamza a tsaye sosai jikin uniform din nasa da suka fara alamta masa
wani abu.

"Me yake faruwa a nan ne?" Ya watsa tambayar ga tsamurmurin mutumin daya lura kusan
shine baquwar fuska a wajen.

Baiyi qasa a gwiwa ba ya kwararowa alhaji hamza bayani kaman yadda
ya yiwa me babban suna,bayanin da maimaicinsu yake sanyashi jin kamar ya rufe
idanunsa ya budesu ya ganshi ba'a wajen ba,kamar ya rufe idanu ya kuma budesu ya
tsinci kansa haihuwar wata uwar daban ba maama ba......kaman ya tsugunna qasa ta
hadiyeshi ya huta.

Sai daya kammala bayaninsa gaba daya sannan alhaji hamza ya gyada
kai

"Nine a matsayin wakilin yaran nan,kuma bana nan,yanzu haka shigowata garin
kenan,inaso a dakatar da aikin nan,ka kuma sameni gobe mu zauna muyi magana akan
batun da kazo dashi,ina da buqatar qwaqwarar shaida da hujja ka taho da ita,idan ya
tabbata da gaskiyarka,zaku fadi iya kudin data karba zan biya na fansarwa yaran
gidan da suka gada,idan kuma aka rasa daya daga ciki kasan qarshen case din basai
na qarasa ba" Abba yayi magana yana janye hannun me babban suna sunayin gaba. Ko
daya bai amsa maganar mutanen ba,wanda ba abinda ransa keyi game dasu sai baci da
soyuwa. Rayuwa ta lalace,DUNIYA ta zama wani abu na daban?,babu me kawar da
barna?,babu me rungumar dan wani?,kowa nasa ya sani.

A baya suka bishi yana riqe da hannun me babban suna ba tare da yace
komai ba.

Motarsa ya qaraso da ita bakin gate din gidan nasa sannan ya
kulleta,ya soma takawa zuwa ciki yana kiran Faruqee. Cak ya tsaya daga gate din
gidan shida saddiq suna kallon abba Faruqee da musaddiq suna wucewa zuwa ciki.

"Me babban suna" Abba ya ambata sanda ya sanya qafarsa ta farko cikin gidan

"Abba baya shigowa gidan mu yanzu" Musaddiq ya fadiwa babban qasa qasa yana tsoron
kada mama dake can ciki ta jiyoshi. A mamakance ya kalli musaddiq sannan ya waiwaya
ya kalli me babban suna dake tsaye daga baya kansa a qasa.

Yana jin nauyin abba qwarai,yana kuma jin nauyin saba
umarninsa,amma bayajin qafafunsa zasu sake taka wannan gidan har abada kamar yadda
yaci alwashi.

"Faruqee meye haka?" Abba ya tambayi farouq cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa

"Abba ya koma gidan su,mama ta koreshi". Wani abu yaji ya sauka tsakiyar kansa har
kaman qafafunsa suna neman yin rawa.

" Ya salam ya Allah" Ya fada a fili,tun yaushe ta aikatawa.marayun Allah haka?,ashe
shi yasa hankalinsa yayi qololuwar tashi sanda ake taba ginin gidan nasu tunda yana
kallonsa a mafaka guda daya duk duniya data rage musu?,ashe shi yasa yaji ya kasa
samun nutsuwa kwata kwata a kwanakin?.

"Muhammadu" Abba yakirayeshi kai tsaye da cikakken sunansa da ba kasafai yake
kiransa dashi ba.

Kansa ya daga,suka hada idanu da abban da idanunsa da suka jajur

"Zoka wuce muje ciki" Ya sake bashi umarni nakai tsaye.

Umarninsa dai dai yake da umarnin mahaifinsa da yayi silar kawoshi
duniya,tabbas idan zaiyi musu da gardama wa mahaifinsa to la shakka zai yi wannan
wa abban. Amma fa tabbas inda ya san abban zai ankara d wuri akan baya biye
dashi,allai da yayi nisa da gurin tunda wuri,tun gabanin yayi masa umarnin shiga
gidan irin haka.

A gaba ya jeresu yana biye da bayansu har zuwa sanda suka isa
ainihin falon gidan. Daidai sanda take fitowa daga kitchen hannun ta dauke da jug
data tanadarwa abban lemo,haka kuma tasha ado da lace bakinta ya cika taf da
lipstick ja shar dashi.

Har cikin zuciyarta takejin bala'i da masifa suna tsarga mata. Yau kam
dukkan juriyarta da karar da take masa ta qare muddin dai yace dawowa yayi da yaran
nan masu zubin mayu. Iya zamanta da yaranshi ma ya isheta jarrabawar rayuwa bare ya
qaro mata yaran da batasan matsayinsu a gidan ba,suba agololi ba,su kuma ba yaran
masu gida ba.

A gaggauce ta isa dining ta ajjiye jug din idanunta bisa fuskarsu
"Ku kuma daga ina?,daga dawowarsa shine kuka biyoshi saboda tsabar maita?" Ta furta
tana zazzare idanu hannuwanta riqe da qugunta.

"Ya isa da Allah asama'u" Abba ya fada da hanzari yana daga mata hannu,don wasu
maganganun bai dace ace an yisu gaban yaran ba,koda saddiq da musaddiq basu da
shekaru sosai,ai Faruqee da me babban suna zuwa yanzun sun fara kammala hankalinsu
tunda sun shiga shekara ta goma sha biyar.

"Ku wuce dakinku ku canza uniform"

"Ba inda zasu a gidannan dai wallahi,basu da daki kuma basu da matsugunni tunda dai
bakai ka haifesu ba.....danginsu ma sai watsar dasu wai ballantana kai abba?" Ta
fada tana sake matsowa hanyar da zasu wuce zuwa dakin

"Abba babu kayansu

Please Login or Register in order to submit comment