You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sukuni da
arziqin rayuwa. Parking lot din ya cika gaba daya da motocinsu,ta wannan tana wane
wannan,a haka ya qaraso gurinsu da natsattsen takun nan nasa kamar namijin talo
talo.

Daya bayan daya yake basu hannu suna gaisawa,wasu su zolayeshi wasu
suyi masa qorafi. Da yawansu bashi da abun cewa,musamman yadda yaji gabbansa sunyi
sanyi da ganin mutanen da farouq din ya tara masa duk kawai dondai su shaida daurin
auren da bai gama gamsuwa da yiwuwarsa ba. Ba wanda shigar fuad din bata dada da
qasa ba,don ya dace da shigar ainun,harma tafi karbarsa sama da farouq din.

A nan suka kashe wasu mintuna kusan sha biyar ana rudu irin na
abokai,gaba daya wajen ya dumame da qamshin turaruka masu tsananin tsada,daga
bisani suka fara shiga motocinsu suna tashi daga wajen. Convoy sosai suka hada da
jerin gwanon motoci masu tsayi,kusan daurin auren sanannen labari ne daya karade
kowa,don haka duk inda zasi gifta sai ya zamana kamar suna sake bada sanarwar
afkuwar abun. Duk inda suka gifta saisun wafci hankula da kyawun motocin,kowanne
traffic suka je ba jinkiri ake daga musu qafa motocinsu su wuce tas,don haka basu
wani kashe lokaci sosai a hanyar ba suka isa inda suka nufa.

Bai sake ji a jikinsa komai da gaske bane sai sanda suka isa alu
avenue dake nasarawa,masallacin alfurqan inda acan aka tsaida don shaida daurin
auren. Jikinsa yayi wani irin sanyi sosai,yana ganin da gasken gaske komai yake
wakana lallai.

"Ya salam.....ya subhanallah" Kawai yake fada a ranshi. Irin taron dafifin al'ummar
daya gani bai taba zaton zai samu irinsu a gurin ba........manyan mutanen daya samu
a wajen bai taba koda kawowa zai samesu a wajen ba.....duba da ba wani mutum daya
daya gayyata da bakinsa. Manyan 'yan kasuwar duniya daga qasashen duniya daban
daban......manyan 'yan siyasa da qusoshin gwamnati......shugaban qasa da attajirai
gami da duk wani me fada aji,don kusan kowa qarin martaba ne a tare dashi halartar
daurin auren.

Basu ma kai ga samun damar isa cikin masallacin ba saboda yawan
al'ummar dakeson ganinsa tare dayi masa fatan alkhairi. Baisan iya dadin yawan
manyan mutanen daya jima bai gani ba amma yau daurin auren ya tattarasu waje guda
ba.....baisan kuma adadin su nawa ya gaisa dasu ba,har zuwa sanda kunnuwansa suka
jiye masa ta lasifiqan cikin masallacin data fito waje tana fadin.

"Mun shaida daurin auren matashin attajirin dan kasuwar gold MUHAMMAD FUAD JADDA
da amaryarsa AMEENATU AHMAD MU'AZZAM".

"AMEENATU?.....why?. Me yasa aka sanya mata wannan sunan?" Ya furta can qasan
ransa. Ta yaya zai zamana tana da suna me matuqar martaba da mutunci a idonsa irin
wannan?,why..... Full name din da aka kirata dashi bai tuna masa komai ba sai kawun
nata rufa'i,ranar daya samu fill details nashi da wannan sunan ya sameshi. Ya saki
siririn tsaki yana jin ranshi yana baci. Inda mutane sunsan ko su waye su da basu
bata kudadensu ba wajen siyan ticket na jirginsu sun cika jingim wajen shaida
daurin auren ba,ya sake jan qaramin tsaki yana juyawa tare da neman nesanta kansa
da hayaniyar wajen,guard dinsa da duk hautsinewar wajen basu yarda sun matsa ba
suka biyoshi a baya.

Can wajen motocinsu ya koma,sai daya shiga ya zauna sannan yace musu

"Don't.....karku gayama kowa ina ta nan idan ba farouq bane ya tambaya".

"Yes sir" Suka amsa a matuqar ladance suka maida murfin suka zuge masa.

Rawanin duka da babbar rigar ya cire ya ajiye gefe,sannan ya koma ya
zauna sosai yana nazarin wajen ta cikin motar. Abinda ya lura dashi,bawai farouq
kadai ba,hatta da abba ya dauki abun very serious,yaga mutanensa a wajen har baisan
adadinsu ba......haka anni,yaga familynta sosai,tamkar tana auren farouq ne,sai ya
maida idonsa ya kulle yana son tuno waye da waye ya gani daga bagaren maamah?.

Bai samu nasarar kaiwa qarshen tunaninsa ba knocking da aka yiwa glass
din motar ta sakashi bude ido,ya ganshi farouq ne,yana daga kwancen ya danna remote
ya bude mass murfin.

Dubansa yayi sanda yake qoqarin shigowa

"Reception zamu wuce.... Already wasu sun fara yin gaba,musaddiq da saddiq tun dazu
suna ta wajen". Shi sai a sannan ya tuna ma.baiga kowa cikin su ba,ason ranshi
farouq din ya barshi ya koma masauki ya kwanta ya rama baccin dake.kansa,ya kuma
rage hayaniyar mutane da yakeji har cikin kansa,saidai kuma ya sani koda yace zai
masa bayani ma farouq din ba fahimtarsa zaiyi ba,yadai fadi abu daya

"Ina fatan daga can duk wata hidima ya qare baku qirqiri komai ba kuma......don
bazan iya jure zuwa wajen komai ba".

" Wanda baisan halinka bane zai wahalar da kansa shirya wani abu......walimar.ma
saboda cika sunna ne da neman albarkar auren" Farouq ya amsa masa yana daga kiran
abokinsa da yake gaya musu sun isa wajen

"Muma muna dab......ka jirani" Yace yana sauke wayar. Siririn murmushi kawai fuad
ya saki,farouq.....farouq..... Idan ba farouq babu shi.......kaman yadda yasan idan
babu shi babu farouq din.

Tunda momma bahijja ta tilastata tayi wanka,ta kuma shirya cikin wata
sabuwar atamfar Hilton wax. Cikin kayan da momma ta zare cikin lefen ta bayar aka
dinka ba tare da sanin sabreen din ba. Tun tana shiryawa taji shigowar uncle
abdulhakeem da tun jiya suka iso suka kwana a tahir guests palace. Zancan duka ya
shafi aurenta ne,wanda duk kalma daya da zata fita daga bakin uncle din nata sai
taji kanta ya wani sara mata. Zazzafan mutum ne da ta jima bataga mutum me zafi da
kafiya akan gaskiya ba irinsa. Ta jima tana tunanin idan ta kammala deal dinta ta
tashi matsawa daga gurbin da take zuwa wani ta yaya zata bacewa idanunsa?,ta kuma
zullewa duk wata tuhuma tashi?. Taji ya ambaci sunan su huda da nadra da tafi sati
tana tunanin ina za'ayi da rayuwarsu?,amma tasan tayi kadan ta tsaya gabansu ta
musu wannan tambayar,bata kuma samu jin abinda suke cewa ba sanadiyyar hayaniyar
yan tafiya daurin auren data qaru. Ta gama shiryawar taji wani zazzabi ya sauko
mata bayan ciwon kanta daya dinga gaba gaba saboda tunanin data matsawa kanta
dashi,sai kawai ta lallaba can gadonsu nadra dake qarshe ta haye can ta qudundune.


𝐃ðŪ𝐧ðĒðē𝐚𝐭𝐚 𝐧𝐚 ðĪðŪ𝐝ðĒ 𝐧𝐞
𝟎𝟖𝟏𝟖𝟕𝟐𝟓𝟓𝟖𝟔𝟐

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
ð˜Ąð˜Ē𝘧ð˜Ē𝘧ð˜Ēð˜Ģ𝘊𝘚ð˜Ēð˜ģ

ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2

ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ

𝙋𝘞𝙂𝙀 10


Page 10


Can cikin tsakiyar kanta maganganun mutane ke mata yawo sanda motar ke
tafiya cikin nutsuwa saman lafiyayyar kwaltar dake shimfide a kanta. Muryoyin
mutane daban daban da sukayi mata fadan shiga gidan miji wai a cewarsu

"Allah yasa dai ki iya zama......don zaman aure daban da zaman bariki,zaman gidan
miji daban da yawon bariki" Muryar bibo kenan da nata salon fadan da yafi kama da
turun mutuwa

"Da dadi ba dadi kiyi haquri ki zauna......Allah yasa mutuwa ce zata raba,kiji kiqi
ji,ki gani kiqi gani" Muryar daada kenan wadda ta kama hannuwanta tana fada
muryarta a sanyaye. Ko da can ba zatace ga wani mummunan abu da daada ta taba musu
ba,ita dai barta da shariya da rashin shiga lamari da sabgar kowa cikin gidan. Idan
ka ganta kuwa a ciki to tabbas abu yaci tura,amma bibo da yaabi koda dan wani akeyi
suna iya ara su yafa tun usul.

"Mommaa......nadra.....haneefa.....huda" Sunayen data iya kirawa momma kenan sanda
take yunqurin sakata a cikin motar da zata yi musu jagora zuwa inda zasuje.

"Ina sane dasu......kuna su din ba nauyinki bane" Ta amsa masa a tausashe.

Ta cikin lafayar jikinta take iya hangen yadda motar ke tsala gudu
abinta,amma saboda lafiyar motar da irin tsarin da akayi mata zaka rantse ba gudun
takeyi ba.

Ta maida idanunta ta lumshe,wasu hawaye da batasan sanda suka taru ba
suka biyo kuncinta suka diga bayan hannunta dake ajiye saman cinyarta. Har yanzu
dai ta kasa gasgata abinda take gani,har yanzu ta kasa gasgata abinda kunnuwanta da
zuciyarta ke nanata mata.

Da gaske mutumin nan yaci galaba a kanta da dukka tsarikansa.....da gaske
shike da nasara ba ita ba.......da gaske ya cinye wasan a wannan gabar.....saidai
kuma hakan baya nufin zaita nasara kenan a kanta,hakan baya nufin ta fadi kenan har
abada.....lallai zata canza labarin......zata canza qaddarar da dukkan iyawarta.

"Gidan mamarshi zamu fara shiga.......sai gidan riqonsa,kamar haka matar data shigo
dazu tace ko?" Daada ta fadi tana dan duban momma bahijja da hannun sabreen yake
cikin nata.

"Eh haka ne" Ta amsa mata idanunta sauke kan faffadan sabon gate din gidan maamah
dake nuna zallar dukiyar dake narke cikin gidan.

A nutse jerin gwanon motocin suka cusa kai makekiyar harabar gidan data
kasance mafarkin maamah na shekara da shekaru,gidan daya dauki hankula da bakunan
dukkan jama'arta dake hulda da ita. Gidan da a cikin ranta ita kanta ta gamsu da
dukiyar daya lashe,amma zuciyarta bata gama nutsuwa da hakan ba saboda har yanzu
gidan alhj hamza kibiya da iyalinsa yafi nata girma yalwa da kuma tsari,ba tare
data duba yawan da suka darata dashi ba,da kuma yawan al'umman da gidan ke dauka
suke riqo a yanzu haka.

Tunda motar ta tsaya a parking lot na gidan gabanta yake wani irin
faduwa,ta maida idonta ta lumshe tana sauraren bugun da zuciyarta keyi da bata taba
jin irinsa ba,sai taji bugun har kusa da maqogoronta. Sake runtse idanunta tayi
sanda momma bahijja ke fadin ta fito,tana jin bugun zuciyar na sake daduwa amma
kuma ta rasa me ya kamata ta karanta?,wacce addu'a ce ta dace da irin wannan
yanayin da takejin kanta a ciki?.

Riqon hannunta da momma din tayi shine ya sassauta mata abinda takeji
kadan,ta sake riqe momma din itama da kyau ba tare tasan ta yadda zata gaya mata
abinda takeji cikin qirjinta ba.

A dan hanzarce ta shigo dakin nata,sannan ta maida qofar ta kulle ta
kuma murza key. Da dan hanzarin still ta isa gaban madubin nata dake manne da wasu
lafiyayyun lockers. Ta murza daya daga ciki ta bude ta,sannan ta saka hannu ta ciro
baqar ledar dake a ciki ta dora saman madubi. Ko ina a jikinta amsawa yakeyi da
wani irin doki da son fara aiwatar da nata aikin,a yau batasan sau dubu nawa tana
addu'ar samun wannan sa'ar ba......batasan sau nawa ta roqi samun nasara a wannan
ranar ba,nasarar da indai ta rasata kamar wadancan kwanakin ta tabbatar komai zaizo
mata da wahalar gaske.....batasan kuma ta yadda zata tari abun ba.

Kusan leda shidda ce,kowacce sai data kunceta sannan ta saka hannu ta
fara ciro kayan ciki. Kusan tarkace ne a idanun me kallo,amma a wajen maamah gwara
rashin million dubu da rasa daya daga cikin kayan. Wasu kwalabe ne masu dauke da
wani irin baqin abu a ciki,wani kuma kore kore ne,saidai yana da dan qamshi qamshi
kadan a ciki mara qarfi. Ta bude kowanne ta tsiyaya cikin tafin hannunta,ta kuma
mulke hannun nata da kyau kamar yadda aka umarceta da tayi,sannan ta maida komai
muhallinsa kamar bata taba komai ba cikin dakin.

Gaban madubin ta tsaya tana qoqarin controlling kanta da daidaita
nutsuwarta. Idanun ta fes cikin fuskarta tana maganar zucci da kanta da kanta,wanda
batayi wani nisa ba knocking din da ake mata ya isa kunnuwanta. Adan fusace tace
tambaya don bata buqatar doguwar mu'amala da kowa har sai wadda tayi shirin saboda
ita ta iso

"Zuwaira ce" Ta bata amsa a tsanake.

"Sun iso,suna falon qasa sun......."

"Gani nan" Ta tari numfashin zuwairan ba tare data jira sauran bayaninta ba. Ba
sauran bayaninta take da buqatar ji ba,tunda taji abinda take buqatar jin,ta
waiwaya tana zura takalmanta data cire tare da kallon tsadajjen mayafin data
lullube jikinta dashi ta tabbatar ya zauna a jikinta......ya sanyata tayi kwarjini
da wata irin kamala da sam zai wahala ka kawo wani abu me muni a kanta. Kyanta ya
bayyana.....kamanninta da musaddiq sosai,yanayin jin dadin da kulawar data samu
wadda take rainawa ta sake sanyawa jikinta ya murje sosai,hutu da quruciya sun
bayyanar mata.

Murmushi ta sakarwa kanta da kanta,sannan ta juya a hankali tana fita a
dakin.

Tun daga saman stairs din take raba idanunta tana son hangota. Bata
wani sha wahala ba,ta hangeta zaune saman lallausan carpet din da aka qawata
tsakiyar falon dashi. Qafafunta a tanqwashe suke,kanta a qasa cikin shigar laffayar
da tazo mahadin lace din da aka zauna akyi dukka adon jikinsa da hannu(handmade
lace),kamar yadda lafayar jikinta itama duk wani zare da duwatsun jiki da hannu aka
gameshi. Abune na masu dashi,ba wani cikar jama'a masu yawa ko cinkoso,kowa yana
zaune a nutse,yayin da gaisuwa ke wakana tsakaninsu momma da jama'ar da suka samu
cikin falon.

Da wani irin kirki na gasken gaske saman fuskarta,faffadan murmushi da
fara'a me nuna tsantsar maraba da baqo ta iso rukunin kujerun tana furta

"Lale maraba......sannunku da zuwa......sannunku da qoqari" Da murmushi a fuskar
momma ta amshe maraban tana duban maamah tsaf tare da karantar yanayinta.

"Bari na zauna kusa da diyata" Ta fadi tana zama kujerar dake kusa da sabreen din.

Gaisuwa akayi cikin mutunci dason nuna ainihin zallar kirkinta,suka
gabatar mata da amanar sabreen tare da dan qaramin jawabin girmama kowa ga sabreen
din

"Itama diyata ce ai tunda yarona take aure,kuma in sha Allah zakuyi alfahari da
hada alaqa damu,Allah ya bada zaman lafiya,shi kuma Allah ya tayashi riqo" Maamah
ta furta cikin zaquwa da gajiya da bayanan. So take kawai ta isa ga muradinta.

"Am nace ba.....idan ba damuwa inason ganin diyata a kebance,minti biyar don Allah"
Maamah ta fada tana murmushi. Ba tare da tunanin komai ba ko kawo komai ba momma
bahijja tace

"Bismillah mana......haba hajiya ai diyarku ce" Daada ta fadi yadda momma din ta
karbi sabreen yana burgeta.

Duk da tayi gaba zuwaira ke mata jagora zuwa wani daki na daban a saman
benen.....amma saita dinga jin wani irin yanayi yana bibiyar gabobinta.

Kasa zama tayi,tana a tsaye sanda taji zuwaira taja musu qofar ta fice.

"Zauna mana.....ki yaye wannan lullubin kan naki......don fahimtata nakeso kiyi
sosai tamkar yau ne karon farko da kika fara fahimta ko haddace wani abu a
rayuwarki" Tayi maganar cikin jerarrun kalmomin da kana jinsu zakasan ko meye zata
fada yana da matuqar muhimmanci a wajenta.

Sai data fara janye lullubin nata baya,sannan ta sulale a wajen ta
zauna. Tana jin kamar babu wani sauran qwarin gwiwa daya rage mata a rayuwa,duk da
yadda take kokawa da zuciyarta da qoqarin qarfafawa kanta gwiwa.

"To alhamdulillah.......komai ya kammala,kuma komai yazomin da sauqi fiye da yadda
nayi zato ko kuma tsammani........ina fata baki manta meye manufar aurenmu ba?" A
nutse sabreen din ta daga kai sannan ta zube mata idanunta saman fuskarta. Kallonta
tayi na second kusan goma sannan ta gyada kai

"Da kyau.....da farko abinda zan fara gaya miki shine abinda na maimaita miki a
baya.......qaidar contract dina na farko shine sirri.......inason sirri,don muddin
aikin nan ya fita daga da'irar sirri zuwa wata da'ira ta daban.....to tamkar kin
wargaza rayuwarki da hannunki ne......bayan taki rayuwar da kika wargaza
kuma......kin wargaza ta 'yan uwanki suma...." Daga ma maamah hannu tayi da hanzari
tana zare idanunta daga kanta

"Ki tsaya iya kan ameenatu kawai......huda,nadra da haneefa,tabasu ko sako sunansu
cikin sabgarki da ameenatu tamkar ganganci ce"

"Da kyau!" Maamah ta furta tana sakin murmushi,abubuwa biyu zuwa uku suna jan
hankalinta. Gyara zamanta tayi tana ci gaba da murmushi

"Ashe ameenatu ce....abu yayi kyau..ameenatu ta bata,wata ameenatun zata
gyara,wannan abun yayimin dadi.......qwarin gwiwarki da rashin sarewarki ya
burgeni......kariyar da kike bawa qannenki tana da yawa,kuma ita dai ta isa ta bani
yaqini da tabbacin ba zaki bari a samu failure ba ko don saboda su......."

"Shiga maganarki kai tsaye" Sabreen ta fadi mata tana kauda kanta zuwa wani sashe
na daban. Idanu maamah tadan zuba mata har yanzu tana murmushi,sai kuma ta miqa
hannu ta zaro wata paper da abun rubutu ta ajiye a gabanta.

"Inaso ki rubuta adadin kudaden da kike da burin mallaka a rayuwarki......ni kuma
zan mallaka miki su a madadin sadakin aikinki,zan kuma qara miki kwatankwacinsu
muddin komai yayi daidai".

Fararen manyan idanunta ta daga ta watsawa maamah su,karon farko da
idanun suka yiwa maamah din wani kwarjini da bata taba jin irinsa ba. Murmushin da
ya subuce kuma a fuskar sabreen ya sanya mata kokwanto

"Ki fadi magana me muhimmanci saboda mutanen dake zaman jiranki a qasa" . Maganar
tata tadan daure mata kai,a nata ganin ba wata magana da zata zama me muhimmanci a
wajen sabreen sama da maganar kudin aikinta,wanda take ganin shi kadai ya isa ya
bata azama akan aiwatar mata da komai. To amma akance......shi yaqi dan zamba
ne,don haka ta gyada kai



𝗗𝘂ð—ŧð—ķ𝘆ð—Ū𝘁ð—Ū ð—ŧð—Ū ð—ļð˜‚ð—ąð—ķ ð—ŧð—ē
𝟎ðŸī𝟭ðŸīðŸģðŸŪðŸąðŸąðŸīðŸēðŸŪ


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

Ėķ𝗕Ėķð—ĒĖķð—ĒĖķ𝗞 ĖķðŸŪ

ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ

𝙋𝘞𝙂𝙀 𝟭𝟭


ð—Ģð—Ūð—īð—ē 𝟭𝟭


"ð—Ąð—Ū𝗷ð—ķ ð—ąð—Ūð—ąð—ķ ð—ąð—Ū ð—ļð—ķð—ļð—Ū 𝘇ð—Ū𝗚ð—Ū 𝗚ð—ē ð—đ𝘂ð—ŋð—Ū ð—Ūð—ļð—Ūð—ŧ ð—ļ𝗞𝗚ð—Ūð—ķ,𝘄ð—Ūð—ŧð—ŧð—Ūð—ŧ 𝘇ð—Ūð—ķ 𝘀ð—Ūð—ŧ𝘆ð—Ū ð—ļ𝗞𝗚ð—Ūð—ķ
𝘆ð—Ū𝘇𝗞 ð—ąð—Ū 𝘀ð—Ū𝘂ð—ūð—ķ........ð—Ūð—ķð—ļð—ķð—ŧð—Ū 𝗚ð—ē 𝘀ð—Ū𝘂ð—ūð—ķ ð—ŧð—ē ð—ķð—ąð—Ūð—ŧ ð—ļð—ķð—ŧð—Ŋð—ķ 𝘆ð—Ūð—ąð—ąð—Ū ð—ŧð—Ū𝗰ð—ē 𝗚ð—ķð—ļð—ķ,𝗰ð—ķð—ļð—ķð—ŧ
𝘄ð—Ū𝘁ð—Ūð—ŧð—ŧð—ķ ð—ļð—Ūð—ąð—Ūð—ŧ 𝗚ð—Ū ð—ļð—ķð—ŧð—Ū ð—ķ𝘆ð—Ū ð—ļð—Ū𝗚𝗚ð—Ūð—đð—Ū𝘄ð—Ū ð—ļð—ķ 𝘄𝘂𝗰ð—ē ð—Ūð—Ŋð—ķð—ŧð—ļð—ķ,ð—Ūð—ļ𝘄ð—Ūð—ķ ð—ŧð—Ū 𝘀ð—Ū𝘄ð—Ū ð—Ū
ð—Ūð—Ŋð—ķð—ŧ𝗰ð—ķ,𝘀ð—Ūð—ķð—ŧð—Ū ð—ŋ𝘂𝘄ð—Ūð—ŧ 𝘄ð—Ūð—ŧð—ļð—Ū,𝘀𝘂 ð—ļð—ēð—ŧð—Ūð—ŧ ð—ąð—Ū ð—ŧð—Ūð—ļð—ē ð—ąð—Ū ð—Ŋ𝘂ð—ūð—Ū𝘁ð—Ūð—ŋ ð—Ū ð—ļ𝗞𝘄ð—Ū𝗰𝗰ð—ē ð—ŋð—Ūð—ŧð—Ū ð—ļð—žð—ąð—Ū
𝘀ð—Ū𝘂 ð—ąð—Ū𝘆ð—Ū ð—ŧð—Ū𝗰ð—ķð—ŧ 𝘆ð—Ū 𝘀ð—ĩð—ķð—īð—Ū 𝗰ð—ķð—ļð—ķð—ŧ𝘀ð—Ū,ð—ŧð—Ū 𝘄ð—Ūð—ŧð—ļð—Ūð—ŧ ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū 𝘆ð—Ū ð—ļð—Ū𝘀ð—Ūð—ŧ𝗰ð—ē ð—Ū 𝗰ð—ķð—ļð—ķð—ŧ ð—ŋ𝘂𝘄ð—Ūð—ŧ
𝘄ð—Ūð—ŧð—ļð—Ūð—ŧ𝘀ð—Ū,ð—ķð—ąð—Ūð—ŧ ð—ŧð—Ū 𝘀ð—Ū𝗚𝘂 𝘄ð—Ūð—ŧð—ŧð—Ūð—ŧ 𝘀ð—Ū𝘂 ð—ąð—Ū𝘆ð—Ū 𝘁ð—Ūð—ļ ð—Ū ð—ŋð—Ūð—ŧð—Ū 𝗚ð—Ū 𝘆ð—Ū 𝘄ð—Ūð—ąð—Ū𝘁ð—Ūð—ŋ. 𝗜ð—ŧð—ąð—Ūð—ķ
ð—ĩð—Ūð—ļð—Ūð—ŧ 𝘆ð—Ū 𝘀ð—Ū𝗚𝘂 ð—ķð—ŧð—Ū 𝗚ð—ē 𝗚ð—ķð—ļð—ķ ð—Ūð—đð—Ŋð—ķ𝘀ð—ĩð—ķð—ŋ ð—ąð—ķð—ŧ ð—ļ𝘄ð—Ūð—ŧð—Ū 𝗰ð—Ū𝘀ð—Ū'ð—ķð—ŧ 𝘄ð—Ū𝘁ð—Ūð—ŧð—ŧð—ķ 𝘂ð—ļ𝘂 ð—ļð—Ū𝗰ð—Ūð—đ
ð—ļ𝗞𝗚ð—Ūð—ķ 𝘇ð—Ūð—ķ 𝘀ð—Ū𝘂𝘆ð—Ū ð—ąð—Ūð—ķð—ąð—Ūð—ķ ð—ąð—Ū 𝘆ð—Ūð—ąð—ąð—Ū ð—ŧð—Ūð—ļð—ē𝘀𝗞......ð—ąð—Ūð—īð—Ū ð—ŋð—Ūð—ŧð—Ūð—ŋ ð—ļð—ķð—ŧ 𝘇ð—Ū𝗚ð—Ū
'𝘆ð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū𝗰𝗰ð—ķ𝘆ð—Ū.....ð—Ūð—ļ𝘄ð—Ūð—ķ ð—ļð—Ū𝘆ð—Ūð—ŧ ð—Ūð—ķð—ļð—ķð—ŧ,ð—ī𝗞ð—Ŋð—ē ð—Ŋð—Ū𝘀ð—Ūð—ķ 𝗷ð—ķð—Ŋð—ķ ð—Ŋð—Ū 𝘇ð—Ūð—ŧ ð—Ūð—ķð—ļ𝗞
ð—Ū𝗚ð—ķð—ŧ𝘁ð—Ū𝗰𝗰ð—ķ𝘆ð—Ū𝘁ð—Ū,ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū 𝘇ð—Ū𝘁ð—Ū 𝘁ð—Ū𝘆ð—Ūð—ļð—ķ 𝘇ð—Ū𝗚ð—Ū ð—ŧð—Ū 𝘄ð—Ūð—ąð—Ūð—ŧð—ŧð—Ūð—ŧ ð—ļ𝘄ð—Ūð—ŧð—Ūð—ļð—ķð—ŧ ð—Ū 𝗚ð—Ū𝘇ð—Ū𝘂ð—ŧð—ķð—ŧ '𝘆ð—Ūð—ŋ
ð—Ūð—ķð—ļð—ķ ð—ĩð—Ūð—ŋ ð—ļð—ķ ð—ļð—Ū𝗚𝗚ð—Ūð—đð—Ū ð—Ūð—ķð—ļð—ķð—ŧð—ļð—ķ ð—ļð—ķ𝘆ð—ķ ð—īð—Ūð—Ŋð—Ū........𝘆ð—Ūð—ąð—ąð—Ū 𝘇ð—Ūð—ļð—ķ 𝘇ð—Ū𝘂ð—ŧð—Ū ð—ąð—Ū ð—ģ𝘂ð—Ūð—ą ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū
𝘄ð—Ūð—ŧð—ŧð—Ūð—ŧ 𝘇ð—Ūð—Ŋð—ķð—ŧð—ļð—ķ ð—ŧð—ē.......𝘀ð—Ūð—ķð—ąð—Ūð—ķ ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū 𝘇ð—Ūð—ŧ ð—ī𝘂𝘁𝘀𝘂ð—ŋð—Ū 𝗚ð—ķð—ļð—ķ ð—ļð—Ūð—ąð—Ūð—ŧ ð—ąð—Ūð—īð—Ū ð—ĩð—Ūð—đð—Ū𝘆ð—ēð—ŧ𝘀ð—Ū
ð—ąð—žð—ŧ ð—ļð—ķ ð—ļð—ķ𝘆ð—Ū𝘆ð—ē ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū ð—ļ𝗞𝗚ð—Ūð—ķ 𝘆ð—Ū𝘇𝗞 𝗚ð—ķð—ļð—ķ ð—ąð—Ū 𝘀ð—Ū𝘂ð—ūð—ķ......"

"𝗕ð—Ūð—Ŋ𝘂 ð—Ŋ𝘂ð—ūð—Ū𝘁ð—Ū" 𝗧ð—Ū ð—ģð—Ūð—ąð—Ū ð—ļð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū 𝘁𝘀ð—Ū𝘆ð—ē,𝘀ð—Ūð—ŧð—ŧð—Ūð—ŧ 𝘁ð—Ū 𝗚ð—ķð—ūð—ē 𝘁𝘀ð—Ū𝘆ð—ē 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū ð—ī𝘆ð—Ūð—ŋð—Ū
ð—đ𝘂ð—đð—đ𝘂ð—Ŋð—ķð—ŧ𝘁ð—Ū. 𝗊ð—Ūð—ŧð—ķ ð—ķð—ŋð—ķð—ŧ 𝗚ð—Ū𝗚ð—Ūð—ļð—ķ ð—ļð—ē ð—ĩð—Ū𝗷ð—ķ𝗷ð—ķ𝘆ð—Ū ð—ąð—Ū 𝘇𝘂𝗰ð—ķ𝘆ð—Ūð—ŋ𝘁ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ŧð—ąð—Ū 𝘁ð—Ūð—ļð—ē 𝘀ð—Ū𝘂ð—ļ𝗞𝘄ð—Ū
ð—ąð—Ūð—īð—Ū 𝘀ð—Ū𝗚ð—Ūð—ŧ,ð—Ŋð—Ūð—ŧð—ąð—Ū 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū ð—ļð—Ū𝗚ð—Ū ð—ūð—Ūð—ŋð—ģð—ēð—ŧ 𝘀𝘁ð—Ūð—ķð—ŋ𝘀 ð—ąð—ķð—ŧ 𝘄ð—Ūð—đð—Ū ð—Ūð—đð—đð—Ū 𝘇ð—Ū𝘁ð—Ū ð—ķ𝘆ð—Ū ð—ĩð—Ūð—ŋð—ąð—ē𝘄ð—Ū.
𝗔ð—ŧ𝘆ð—Ū ð—ļ𝘂𝘄ð—Ū 𝘄ð—Ūð—ŧð—ŧð—Ūð—ŧ ð—ąð—ķð—ŧ ð—Ļ𝗊𝗔 𝗖𝗘?,ð—Ļ𝗊𝗔 𝗖𝗘 𝗰ð—ķð—ļð—ķð—ŧ ð—ĩð—Ūð—đð—ķ𝘁𝘁ð—Ūð—ŋ ð—Ŋð—ķð—đ'ð—Ūð—ąð—Ū𝗚ð—Ū?,ð—ļ𝗞 ð—ļ𝘂𝘀ð—Ū
𝘂𝘄ð—Ū 𝗰ð—ē 𝗰ð—ķð—ļð—ķð—ŧ 𝘄ð—Ūð—ŧð—ķ 𝗷ð—ķð—ŧ𝘀ð—ķ ð—ļ𝗞 ð—ĩð—Ūð—đð—ķ𝘁𝘁ð—Ū 𝘁ð—Ū ð—ąð—Ūð—Ŋð—Ūð—ŧ?. 𝗕ð—Ū𝘁ð—Ū𝘀ð—Ūð—ŧ 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū ð—Ŋð—ķ𝘆ð—ē ð—ąð—Ū ð—ķ𝘁ð—Ū ð—Ŋð—Ū
𝘀ð—Ūð—ķ ð—ąð—Ū𝘁ð—Ū𝗷ð—ķ 𝗚𝘂ð—ŋ𝘆ð—Ūð—ŋ𝘁ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ŧð—ąð—Ū 𝘁ð—Ūð—ļð—ē 𝘁𝘀𝘂ð—ī𝘂ð—ŧð—ŧð—Ū𝘄ð—Ū ð—īð—Ūð—Ŋð—Ūð—ŧ 𝗚𝗞𝗚𝗚ð—Ū ð—Ŋð—Ūð—ĩð—ķ𝗷𝗷ð—Ū ð—ąð—žð—ŧ 𝘁ð—Ū𝘀ð—Ūð—ŧ
𝘁ð—Ū ð—ūð—Ūð—ŋð—Ū𝘀𝗞. 𝗕ð—Ū 𝘇ð—Ū𝘁𝗞 𝘁ð—Ū 𝘁𝘀ð—ķð—ŧ𝗰ð—ē𝘁ð—Ū ð—Ū ð—īð—Ūð—Ŋð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū ð—ģð—Ūð—ąð—ķð—ŧ

"𝗟ð—Ūð—đð—đð—Ūð—ķ 𝘆ð—Ūð—ŋ𝗞ð—ŧð—Ū 𝘆ð—Ū ð—ąð—Ū𝗰ð—ē,ð—ŧð—Ū𝘆ð—ķ ð—ģð—Ūð—ŋð—ķð—ŧ𝗰ð—ķð—ļð—ķ ð—ąð—Ū 𝘀ð—Ū𝗚𝘂ð—ŧ 𝘀𝘂ð—ŋ𝘂ð—ļð—Ū ð—ķð—ŋð—ķð—ŧ 𝘄ð—Ūð—ŧð—ŧð—Ūð—ŧ....𝗔ð—đð—đð—Ūð—ĩ
𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ 𝗚ð—ķð—ļð—ķ ð—Ūð—đð—Ŋð—Ūð—ŋð—ļð—Ū" 𝗧ð—Ū ð—ūð—Ūð—ŋð—Ū𝘀ð—Ū ð—ģð—Ūð—ąð—Ū 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū ð—Ū𝘇ð—Ū ð—ĩð—Ūð—ŧð—ŧ𝘂ð—ŧ𝘁ð—Ū 𝘀ð—Ū𝗚ð—Ūð—ŧ ð—ļð—Ūð—ŧ 𝘀ð—Ūð—Ŋð—ŋð—ēð—ēð—ŧ ð—ąð—Ū
𝘀ð—ķð—īð—Ūð—ŋ 𝘀ð—Ūð—ŧ𝘆ð—Ū ð—Ūð—đð—Ŋð—Ūð—ŋð—ļð—Ū.

𝗎ð—Ū𝗚𝗚𝗚𝗚 𝘁ð—Ū𝗷ð—ķ 𝘄ð—Ūð—ŧð—ķ ð—ķð—ŋð—ķð—ŧ ð—Ūð—Ŋ𝘂 𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū ð—Ŋð—ķð—ŧ ð—ļ𝗞𝘄ð—Ūð—ŧð—ŧð—ē 𝘀ð—Ū𝘀ð—ĩð—ē ð—ŧð—Ū 𝗷ð—ķð—ļð—ķð—ŧ𝘁ð—Ū.
𝗖ð—ķð—ļð—ķð—ŧ ð—ļ𝗞𝘄ð—Ūð—ŧð—ŧð—ē ð—ĩð—Ūð—ŋð—Ŋð—Ū𝘄ð—Ū 𝗷ð—ķð—ŧð—ķ ð—ąð—Ūð—ļð—ē 𝘇ð—Ūð—īð—Ū𝘆ð—Ū𝘄ð—Ū ð—īð—Ū 𝗷ð—ķ𝗷ð—ķ𝘆𝗞𝘆ð—ķð—ŧ𝘁ð—Ū 𝘄ð—Ūð—ŧð—ķ ð—ķð—ŋð—ķð—ŧ 𝘀ð—Ūð—ū𝗞 ð—ąð—Ū
𝘀ð—Ū𝘂𝘆ð—ē 𝘀ð—Ū𝘂𝘆ð—ē 𝘀𝘂ð—ļð—Ū ð—ģð—Ūð—ŋð—Ū ð—Ūð—ģð—ļ𝘂𝘄ð—Ū ð—ąð—Ū 𝘄ð—Ūð—ŧð—ķ ð—ķð—ŋð—ķð—ŧ 𝘀ð—Ū𝘂ð—ŋð—ķ ð—ąð—Ū ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū ð—īð—Ūð—īð—īð—Ū𝘄ð—Ū 𝗚ð—ē
𝘆ð—Ū𝘄ð—Ūð—ŧ ð—īð—Ū𝘀ð—ļð—ē

"𝗔ð—đð—đð—Ūð—ĩ 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ 𝗚ð—ķð—ļð—ķ ð—Ūð—đð—Ŋð—Ūð—ŋð—ļð—Ū" 𝗧ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ļð—ē 𝗚ð—Ūð—ķ𝗚ð—Ūð—ķ𝘁ð—Ū ð—ļð—Ūð—đ𝗚ð—Ūð—ŋ 𝘀ð—Ū𝘂 𝘂ð—ļ𝘂 ð—ąð—žð—ŧ 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū𝘀𝗞ð—ŧ
ð—Ūð—ąð—Ūð—ąð—ķð—ŧ 𝘀ð—Ūð—ļð—Ūð—ŧð—ŧð—ķð—ŧ 𝘀𝘂 𝗰ð—ķð—ļð—Ū ð—ļð—Ūð—ģð—ķð—ŧ 𝘁ð—Ū ð—ąð—Ū𝘂ð—ļð—ē ð—ĩð—Ūð—ŧð—ŧ𝘂ð—ŧ ð—ŧð—Ū𝘁ð—Ū ð—ąð—Ūð—īð—Ū 𝘀ð—Ū𝗚ð—Ūð—ŧ ð—ļð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū

"𝗔𝗚ð—ēð—ēð—ŧ 𝘆ð—Ū 𝗔ð—đð—đð—Ūð—ĩ......ð—Ū𝗚ð—ēð—ēð—ŧ 𝘆ð—Ū ð—ŋð—Ūð—Ŋð—Ŋð—Ūð—đ 𝗔ð—Ūð—đð—Ū𝗚ð—ķð—ŧ" 𝗠𝘂𝘁ð—Ūð—ŧð—ēð—ŧ 𝘄ð—Ū𝗷ð—ēð—ŧ ð—ļð—ē ð—Ū𝗚𝘀ð—Ū𝘄ð—Ū
ð—ąð—Ū𝘀ð—ĩð—ķ.

𝗛ð—Ūð—ŧð—ŧ𝘂ð—ŧ 𝘁ð—Ū ð—ąð—Ū𝘂ð—ļð—ē ð—ąð—Ūð—īð—Ū ð—ļð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū,𝘁ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ŧ𝘆ð—Ū ð—ĩð—Ūð—ŧð—ŧ𝘂𝘄ð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū ð—ąð˜‚ð—ļð—ļð—Ū ð—Ŋð—ķ𝘆𝘂ð—ŧ
𝘁ð—Ū ð—ąð—Ūð—ī𝗞𝘁ð—Ū 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū ð—ģ𝘂𝘀ð—ļð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ūð—ŋ𝘁ð—Ū

"𝗧ð—Ū𝘀ð—ĩð—ķ ð—ļð—ķ 𝘄𝘂𝗰ð—ē ð—īð—ķð—ąð—Ūð—ŧð—ļð—ķ......ð—ąð—Ūð—īð—Ū ð—ŧð—Ūð—ŧ ð—ļ𝘂 ð—ļð—Ūð—ķ𝘁ð—Ū ð—īð—ķð—ąð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū ð—ļð—Ūð—ķ 𝘁𝘀ð—Ū𝘆ð—ē......ð—ąð—Ūð—īð—Ū
ð—Ŋð—Ū𝘆ð—Ū ð—ąð—Ū ð—ļð—Ūð—ŧ𝘀ð—ĩð—ķ 𝘆ð—Ū ð—ŋð—Ūð—ļð—Ū𝘁ð—Ū ð—ķð—ŧð—ąð—Ū 𝘆ð—Ū ð—ąð—Ū𝗰ð—ē 𝘁ð—Ū𝗷ð—ē ð—ąð—ķð—ŧ.....ð—ļð—ķð—ŧ𝗷ð—ķ ð—ąð˜‚ð—ļð—ļð—Ū ð—Ŋð—Ū𝘆ð—Ūð—ŧð—Ūð—ķð—ŧð—Ū
ð—ļ𝗞?" ð—Ķð—Ū𝗚𝘂ð—ŧ ð—ļð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū 𝘁ð—Ū𝘆ð—ķ ð—ąð—Ū ð—ī𝘆ð—Ūð—ąð—Ū 𝗚ð—Ū𝘁ð—Ū ð—ļð—Ūð—ķ ð—ąð—Ū 𝘄ð—Ūð—ŧð—ķ ð—ķð—ŋð—ķð—ŧ 𝗚𝘂ð—ī𝘂ð—ŧ 𝘀ð—Ūð—ŧ𝘆ð—ķð—ŧ 𝗷ð—ķð—ļð—ķ ð—ąð—Ū
ð—Ŋð—Ū𝘁ð—Ū 𝘁ð—Ūð—Ŋð—Ū 𝗷ð—ķð—ŧ ð—ķð—ŋð—ķð—ŧ𝘀ð—Ū ð—Ŋð—Ū,𝘀ð—Ūð—ķ𝘁ð—Ū 𝗷ð—Ū𝘄𝗞𝘁ð—Ū 𝘁ð—Ū ð—ŋ𝘂ð—ŧð—ī𝘂𝗚ð—ē𝘁ð—Ū 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū 𝘀ð—Ūð—ļð—ē 𝘀ð—Ūð—ļð—ē 𝗚ð—Ū𝘁ð—Ū 𝘄ð—Ū𝘀𝘂
ð—Ūð—ąð—ąð˜‚'𝗞'ð—ķð—ŧ,ð—Ūð—Ŋð—ķð—ŧð—ąð—Ū 𝘆ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ŧ𝘆ð—Ū 𝘁ð—Ū𝗷ð—ķ ð—ļð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ 𝘄ð—Ūð—ŧð—ķ ð—ķð—ŋð—ķð—ŧ 𝘀ð—Ūð—ŋð—Ū𝘄ð—Ū,𝘁ð—Ūð—ļð—ē 𝗰ð—ķ𝘄𝗞ð—ŧ ð—ļð—Ūð—ķ 𝘆ð—Ū
𝘀ð—Ū𝘂ð—ļð—Ūð—ŋ 𝗚ð—Ū𝘁ð—Ū.

ð—Ķð—Ū𝘂ð—ļð—ē ð—đð—Ūð—Ŋ𝘂ð—đð—ē ð—Ū𝗚ð—ŧð—Ū 𝘁ð—Ū𝘆ð—ķ ð—Ū ð—ļð—Ūð—ŋ𝗞 ð—ŧð—Ū ð—Ŋð—Ūð—Ŋ𝘂 ð—Ūð—ąð—Ūð—ąð—ķ,𝘀ð—Ūð—ŧð—ŧð—Ūð—ŧ 𝘁ð—Ū 𝗚ð—Ūð—ķð—ąð—Ū
ð—ąð˜‚ð—Ŋð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū ð—ļð—Ūð—ŧ ð—Ūð—ŧð—ŧð—ķ 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū ð—ŧð—Ūð—ŋð—ļð—ē ð—ģ𝘂𝘀ð—ļð—Ū ð—ļð—Ū𝗚ð—Ūð—ŋ 𝘇ð—Ū𝘁ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ļð—ķ ð—ļ𝘂ð—ļð—Ū

"𝗔ð—ŧð—ŧð—ķ ð—ąð—Ūð—ŋð—ē ð—ģð—Ū 𝘆ð—Ū ð—ŋð—ķð—īð—Ū 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ,ð—ĩð—Ūð—ŋ 𝘆ð—Ūð—ŧ𝘇𝘂 ð—Ŋð—Ū𝘀𝘂 𝘀ð—ĩð—ķð—ī𝗞 ð—ąð—Ū ð—ķ𝘁ð—Ū ð—Ŋð—Ū.....ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū 𝘆ð—Ūð—Ū
𝗚𝘂𝘀ð—Ūð—ąð—ąð—ķð—ū 𝘆ð—Ū𝗰ð—ē 𝘀𝘂ð—ŧ 𝘀ð—ĩð—ķð—īð—Ū 𝘄ð—Ū𝗷ð—ēð—ŧ 𝗚ð—Ūð—Ū𝗚ð—Ūð—ĩ....ð—ąð—Ūð—īð—Ū 𝗰ð—Ūð—ŧ ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ķ ð—ŧð—Ūð—ŧ". 𝗔
ð—ŧ𝘂𝘁𝘀ð—ē ð—Ūð—ŧð—ŧð—ķ 𝘁ð—Ū ð—ąð—Ūð—īð—Ū ð—ļð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū ð—ąð—Ūð—īð—Ū 𝘇ð—Ūð—ŋð—ē 𝘄ð—Ūð—ŋ𝘄ð—Ūð—ŋð—Ū𝘆ð—ēð—ŧ ð—ĩð—Ūð—ŧð—ŧ𝘂ð—ŧ𝘁ð—Ū ð—ąð—Ū 𝘁ð—Ūð—ļð—ē𝘆ð—ķ 𝘁ð—Ū 𝗚ð—Ūð—ķð—ąð—Ū
ð—ļð—Ūð—ŧ ð—Ū𝗚ð—ŧð—Ū

"𝗠ð—ē ð—ļð—ķð—ļð—ē 𝗰ð—ķ ð—ŧð—ē ð—ŧð—Ū ð—Ŋð—Ūð—ļð—Ū 𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū 𝘇𝘂ð—Ŋð—Ū ð—Ū𝗚ð—ŧð—Ū?,𝗰ð—ķ ð—ąð—Ū 𝘇𝘂𝗰ð—ķ?,𝘆ð—Ū𝘆ð—Ūð—ŋð—ļð—ķ 𝗰ð—ē ð—ģð—Ū?,ð—ĩð—Ūð—ŋ 𝘀ð—Ūð—ķ
ð—ļð—ķð—ŧ ð—īð—Ū𝗷ð—ķ ð—ąð—Ū ð—īð—Ūð—ŧð—ķð—ŧ𝘁ð—Ū 𝘄ð—Ū𝘁ð—Ūð—ŋð—Ūð—ŧð—Ū.....𝘄ð—Ū𝘁ð—Ūð—ūð—ķð—đð—Ū ð—ąð—Ūð—ŋð—ē ð—ŧð—ē 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ 𝗚𝘂𝘀𝘂 𝘀𝘂ð—ļð—Ū 𝘄𝘂𝗰ð—ē ð—ąð—Ū
ð—ķ𝘁ð—Ū,ð—Ū𝗚𝗚ð—Ū ð—ļ𝗞𝗚ð—Ū 𝗚ð—ē𝘆ð—ē ð—ŧð—Ū𝘀ð—Ūð—ŧ ð—ĩð—Ū𝗚𝗚ð—Ūð—ŧð—ļ𝘂 𝘇ð—Ūð—ķ ð—ļð—Ū𝘄𝗞𝘁ð—Ū 𝘁ð—Ūð—Ŋð—Ŋð—Ū𝘀 ð—ļð—žð—ąð—Ū ð—ąð—Ūð—īð—Ū ð—Ŋð—Ū𝘆ð—Ū
ð—ŧð—ē" . 𝗧ð—Ū𝘆ð—ķ 𝗚ð—Ūð—īð—Ūð—ŧð—Ūð—ŋ 𝗰ð—ķð—ļð—ķð—ŧ 𝘀𝗞ð—ŧ ð—ļð—Ū𝘄ð—Ūð—ŋ𝘄ð—Ū ð—ąð—Ū ð—Ū𝗚ð—ŧð—Ū 𝘁𝘂ð—ŧð—Ūð—ŧð—ķð—ŧ ð—ļ𝗞𝗚ð—Ūð—ķ,ð—ąð˜‚ð—ļ ð—ąð—Ū ð—ķ𝘁ð—Ū𝗚ð—Ū
𝘁ð—Ū𝘀𝗞 ð—ū𝘄ð—Ūð—ŋð—Ūð—ķ ð—Ū 𝘀ð—ĩð—ķð—ī𝗞 ð—ąð—Ū ð—ķ𝘁ð—Ūð—ŧ,ð—ąð—žð—ŧ ð—Ūð—ļ𝘄ð—Ūð—ķ 𝗚ð—Ūð—īð—Ūð—ŧð—īð—Ūð—ŧ𝘂 𝗚ð—Ū𝘀𝘂 𝘆ð—Ū𝘄ð—Ū ð—ąð—Ū 𝘁ð—Ūð—ļð—ē𝘀𝗞 𝘁ð—Ū𝘆ð—ķ
ð—ąð—Ū ð—ķ𝘁ð—Ū.
"𝗔𝗚𝗚ð—Ū ð—Ūð—ŧð—ŧð—ķ 𝘆ð—Ū𝘂𝘀ð—ĩð—ē?,ð—ŧð—ķ ð—ļ𝗞 ð—ī𝗞ð—Ŋð—ē ð—ŧð—ē ð—īð—Ūð—ŧð—ķ ð—ŧð—Ūð—ļð—ē𝘆ð—ķ 𝘁ð—Ū𝘆ð—ķ ð—ŧð—ķ𝘀ð—Ū"

"ð—Ķð—Ūð—ķ ð—ļð—ķ𝘆ð—ķ ð—ģð—ķð—ģð—ģð—ķð—ļð—ē ð—ļð—ķ𝗷ð—ē ð—Ūð—ķ 𝘀ð—Ūð—ŋð—ļð—ķð—ŧ ð—īð—Ūð—ŋð—Ū𝗷ð—ē" ð—Ķð—Ūð—ąð—ąð—ķð—ū ð—ąð—Ūð—ļð—ē 𝘀ð—ĩð—ķð—ī𝗞𝘄ð—Ū ð—ŋð—ķð—ūð—ē ð—ąð—Ū ð—đð—ēð—ąð—Ū ð—Ū
ð—ĩð—Ūð—ŧð—ŧ𝘂ð—ŧ𝘀ð—ĩð—ķ ð—ąð—Ūð—ļð—ē ð—ąð—Ū𝘂ð—ļð—ē ð—ąð—Ū 𝘁ð—Ū𝗚ð—Ŋð—Ūð—ŋð—ķð—ŧ 𝘄ð—Ūð—ŧð—ķ ð—Ŋð—Ūð—Ŋð—Ŋð—Ūð—ŧ ð—ļð—Ū𝗚ð—ģð—Ūð—ŧð—ķ ð—ąð—Ū 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ 𝘀ð—ĩ𝘂ð—ĩ𝘂ð—ŋð—Ū
𝘄ð—Ū𝗷ð—ēð—ŧ ð—ģð—ķð—ąð—ąð—Ū 𝘀𝘂𝘁𝘂ð—ŋ𝘂 ð—ŧð—Ū 𝗚ð—Ūð—ŧ𝘆ð—Ūð—ŧ 𝗚𝘂𝘁ð—Ūð—ŧð—ē. 𝗝𝘂𝘆ð—Ū𝘄ð—Ū 𝘁ð—Ū𝘆ð—ķ 𝘁ð—Ū ð—ąð˜‚ð—Ŋð—ē𝘀ð—ĩð—ķ 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū 𝘀ð—Ūð—ļð—ē
ð—Ŋð—Ū𝘁ð—Ū ð—ŋð—Ūð—ķ,𝘀ð—Ūð—ķ 𝘁ð—Ū 𝘁𝘀𝘂ð—ļð—ē ð—Ŋð—Ūð—ļð—ķ ð—ļð—Ū𝘄ð—Ūð—ķ 𝘁ð—Ū ð—ļ𝗞𝗚ð—Ū 𝘁ð—Ū 𝘇ð—Ū𝘂ð—ŧð—Ū ð—Ŋð—Ū 𝘁ð—Ūð—ŋð—ē ð—ąð—Ū𝘁ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ļð—ē 𝗰ð—ē𝘄ð—Ū
ð—ļ𝗞𝗚ð—Ūð—ķ ð—Ŋð—Ū,ð—ąð—žð—ŧ 𝘁ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ŧ ð—šð˜‚ð—ąð—ąð—ķð—ŧ 𝘁ð—Ū𝗰ð—ē 𝘇ð—Ū𝘁ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ļð—ē 𝗚ð—Ūð—īð—Ūð—ŧð—Ūð—ŋ 𝘇ð—Ū𝘀𝘂 𝘆ð—ķ𝘁ð—Ū 𝘀ð—Ū'ð—ķð—ŧ𝘀ð—Ū ð—ŧð—ē
ð—ļð—Ū𝘄ð—Ūð—ķ ð—ąð—Ū 𝘀ð—Ūð—ąð—ąð—ķð—ū,ð—ąð—Ūð—īð—Ū ð—ūð—Ūð—ŋ𝘀ð—ĩð—ē 𝘆ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ļð—Ū𝘁ð—Ū ð—ļ𝘂ð—ļð—Ū.

"𝗔ð—ŧð—ŧð—ķ ð—ļð—ē𝘆 ð—ŧð—Ū 𝘀ð—Ū𝘀𝘀ð—Ūð—ŧ 𝗕𝗕 ð—ģð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū,𝘆ð—Ū𝗰ð—ē ð—ŧð—Ū 𝘀ð—Ūð—ļð—Ū 𝗚𝘂𝘀𝘂 ð—ļð—Ū𝘆ð—Ūð—ŧ ð—ŧð—Ūð—ŧ ð—Ū 𝗰ð—ķð—ļð—ķ,ð—ĩð—Ū𝗚𝗚ð—Ū
𝘇ð—Ūð—ķ𝘇𝗞 𝘆ð—Ū 𝘀ð—ĩð—ķð—ŋ𝘆ð—Ū". 𝗊ð—Ūð—ķ𝘄ð—Ū𝘆ð—Ū𝘄ð—Ū 𝘁ð—Ū𝘆ð—ķ 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū ð—Ŋð—Ū𝘄ð—Ū ð—Ū𝗚ð—ŧð—Ū 𝘂𝗚ð—Ūð—ŋð—ŧð—ķ 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū 𝗚ð—Ū𝘁ð—Ū ð—ŧ𝘂ð—ŧð—ķ ð—ąð—Ū
ð—ķð—ŧð—ąð—Ū 𝘁ð—Ū ð—Ū𝗷ð—ķ𝘆ð—ē𝘀ð—ĩð—ķ.


"𝗕ð—Ū ð—ķð—ŧð—ąð—Ū 𝘇ð—Ūð—ļð—Ū𝗷ð—ē ð—ģð—Ū 𝘀ð—Ūð—ķð—ļð—Ū ð—ļð—Ū𝗚𝗚ð—Ūð—đð—Ū 𝘀ð—ĩð—ķð—ŋ𝘆ð—Ū𝘄ð—Ū ð—ŧð—Ū ð—ŋð—Ūð—ļð—Ūð—ļð—Ū ð—ļð—Ū 𝘆ð—ķ𝘄ð—Ū ð—Ūð—ŧð—ŧð—ķ
𝘀ð—Ūð—đð—đð—Ū𝗚ð—Ū......ð—ąð—žð—ŧ ð—Ŋð—Ū 𝘇ð—Ūð—ļð—Ū ð—ĩð—Ūð—ŧð—Ūð—ŧð—ķ ð—ļ𝘄ð—Ūð—ŧ𝗰ð—ķ𝘆ð—Ū ð—ąð—Ū 𝘄𝘂ð—ŋð—ķ ð—Ŋð—Ū 𝘆ð—Ū𝘂......𝘆ð—Ūð—ąð—ąð—Ū ð—ŧð—Ū
ð—īð—Ū𝗷ð—ķ ð—ąð—ķð—ŧð—ŧð—Ūð—ŧ ð—Ŋð—Ū𝗰𝗰ð—ķ ð—ŧð—Ūð—ļð—ē ð—Ŋ𝘂ð—ūð—Ū𝘁ð—Ū 𝗚ð—ē 𝘁𝘀ð—Ūð—ĩ𝗞.....ð—ļ𝗞 ð—ģð—Ūð—ŧð—ŧð—Ū ð—ĩð—ķð—ąð—ķ𝗚ð—Ūð—ŋð—ļð—Ū 𝘁ð—Ū ð—ĩð—Ūð—ŧð—Ū𝗚ð—ķð—ŧ 𝗷ð—ķð—ŧ
𝗚𝘂ð—ŋ𝘆ð—Ūð—ŋ𝘁ð—Ū" 𝗙ð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū ð—ąð—Ū𝘆ð—Ū ð—ŋð—ķð—ū𝗞 ð—ģ𝘂ð—Ūð—ą 𝘄ð—Ūð—ŧð—ąð—Ū ð—ļð—ē ð—ū𝗞ð—ūð—Ūð—ŋð—ķð—ŧ 𝘄𝘂𝗰ð—ē𝘄ð—Ū ð—ļð—Ūð—ķ 𝘁𝘀ð—Ū𝘆ð—ē 𝗰ð—ķð—ļð—ķð—ŧ
ð—īð—ķð—ąð—Ūð—ŧ 𝘆ð—Ū ð—ģð—Ūð—ąð—Ū.

𝗊ð—Ūð—ķ𝘄ð—Ū𝘆𝗞𝘄ð—Ū 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ 𝘆ð—Ū ð—ļð—Ūð—đð—đð—ķ ð—ģð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū ð—ąð—ķð—ŧ

"𝗗𝘂ð—ļð—Ū ð—ļð—Ūð—ķ ð—ļð—Ū𝘀𝗞.....ð—ļð—Ū ð—Ū𝘇ð—Ū𝗚ð—Ū ð—ļð—Ūð—ŧð—ļð—Ū ð—ĩð—ķð—ąð—ķ𝗚ð—Ūð—ŋ ð—ąð—Ū ð—ļ𝘄ð—Ū𝘁ð—Ū ð—ļ𝘄ð—Ū𝘁ð—Ū ð—Ŋð—Ū𝘁ð—Ū ð—ąð—Ū 𝘄ð—Ūð—ŧð—ķ
𝘁𝘂𝘀ð—ĩð—ē ð—ļ𝗞 ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū ð—Ū𝗚ð—ģð—Ūð—ŧð—ķ.....𝘄ð—Ūð—ķ 𝘄ð—Ūð—ķ𝘁 𝗚ð—Ū......𝘁𝘂ð—ļ𝘂ð—ŧð—ŧð—Ū ð—ļð—Ūð—ŧð—Ū ð—ŧ𝘂ð—ģð—ķð—ŧ ð—ŧð—ķ 𝘇ð—Ūð—ļð—Ū
𝘀ð—Ūð—ļð—Ū ð—Ū ð—īð—Ūð—Ŋð—Ū ð—ļð—Ūð—ļð—Ūð—ķ 𝗰ð—Ūð—ŧ ð—īð—ķð—ąð—Ūð—ŧ?"

"𝗊ð—Ūð—đð—đð—Ūð—ĩð—ķ 𝘄ð—Ūð—đð—đð—Ūð—ĩð—ķ 𝘀ð—Ūð—ķð—ļð—Ū 𝘀ð—ĩð—ķð—ŋ𝘆ð—Ū ð—ļð—Ū𝗚ð—Ūð—ŧ ð—ļ𝗞𝘄ð—Ūð—ŧð—ŧð—ē ð—Ūð—ŧð—ī𝗞,ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ķð—ŧð—Ū ð—ļð—Ūð—ķð—ļð—Ū ð—ĩð—Ūð—ŋ
𝗰ð—ķð—ļð—ķ" 𝗎ð—Ū𝘆ð—ķ ð—īð—Ūð—īð—īð—Ū𝘄ð—Ūð—ŋ 𝘆ð—Ūð—ŧð—ļð—Ūð—ŋ 𝗚ð—Ū𝘀ð—Ū ð—Ŋð—Ū𝘆ð—Ū ð—ąð—Ū ð—ŋð—Ūð—ŧ𝘁𝘀𝘂𝘄ð—Ū,ð—ąð—žð—ŧ ð—ŋð—Ūð—ŧ𝘁𝘀𝘂𝘄ð—Ūð—ŋ 𝗰ð—ē
ð—ļð—Ūð—ąð—Ūð—ķ 𝘆ð—Ū𝘀ð—Ūð—ŧ 𝘇ð—Ū𝘁ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ļð—Ū ð—ģ𝘂ð—Ūð—ą 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ ð—Ūð—Ŋð—ķð—ŧð—ąð—Ū 𝘆ð—Ūð—ļð—ē𝘀𝗞 ð—ąð—ķð—ŧ ð—Ŋð—Ū 𝘁ð—Ūð—ŋð—ē ð—ąð—Ū 𝗷ð—Ūð—ŧ 𝘇ð—Ūð—ŧ𝗰ð—ē
ð—Ŋð—Ū,ð—ļð—Ū𝘀ð—Ūð—ŧ𝗰ð—ē𝘄ð—Ūð—ŋ ð—ąð˜‚ð—ļ 𝘄ð—Ūð—ŧð—ąð—Ū 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ ð—ŋð—Ūð—ŧ𝘁𝘀𝘂𝘄ð—Ū ð—Ū 𝗰ð—ķð—ļð—ķð—ŧ 𝘀𝘂 𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū ð—ū𝗞ð—ūð—Ūð—ŋð—ķð—ŧ ð—ģð—ķð—ąð—ąð—Ū ð—ąð—Ūð—ŧ
𝘂𝘄ð—Ūð—ŧ𝘀ð—Ū ð—ąð—Ūð—īð—Ū ð—ŋð—Ūð—ŧ𝘁𝘀𝘂𝘄ð—Ūð—ŋ.

ð—œð—ąð—Ūð—ŧ𝘂 𝘆ð—Ū 𝘇𝘂ð—Ŋð—Ū 𝗚ð—Ū𝘀ð—Ū,ð—ļð—Ū𝗚ð—Ūð—ŋ 𝘇ð—Ūð—ķ𝘆ð—ķ 𝗚ð—Ūð—īð—Ūð—ŧð—Ū 𝘀ð—Ūð—ķ ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū 𝘆ð—Ū ð—ģð—Ū𝘀ð—Ū,𝘆ð—Ū 𝗷𝘂𝘆ð—Ū
𝘇𝘂𝘄ð—Ū 𝘀ð—Ū𝘀ð—ĩð—ēð—ŧ ð—ģð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū ð—ąð—ķð—ŧ 𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū 𝘁ð—Ūð—ļð—Ū𝘄ð—Ū 𝗰ð—ķð—ļð—ķð—ŧ ð—ŧ𝘂𝘁𝘀𝘂𝘄ð—Ūð—ŋ ð—ŧð—Ūð—ŧ 𝘁ð—Ū𝘀ð—Ū. 𝗖ð—Ūð—ļ 𝘆ð—Ū
𝘁𝘀ð—Ū𝘆ð—Ū ð—ąð—Ūð—Ŋ ð—ąð—Ū 𝘇ð—Ūð—ķ 𝘀ð—ĩð—ķð—īð—Ū,𝗚𝘂ð—ŋ𝗚𝘂𝘀ð—ĩð—ķ 𝗚ð—ē ð—ūð—Ūð—ŋð—Ū𝗚ð—ķð—ŧ 𝘀ð—Ū𝘂𝘁ð—ķ 𝘆ð—Ū 𝘀𝘂ð—Ŋ𝘂𝗰ð—ē 𝗚ð—Ū𝘀ð—Ū,𝘆ð—Ū
𝘄ð—Ūð—ķ𝘄ð—Ū𝘆ð—Ū 𝘆ð—Ū ð—ąð˜‚ð—Ŋð—ķ ð—ģð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū ð—ąð—ķð—ŧ

"𝗊ð—Ūð—đð—đð—Ūð—ĩð—ķ 𝘆ð—Ūð—ŋ𝗞ð—ŧ ð—ŧð—Ūð—ŧ ð—ļð—Ū ð—ŋð—Ūð—ķð—ŧð—Ūð—ŧð—ķ ð—ąð—Ū 𝘆ð—Ū𝘄ð—Ū,𝘄ð—Ūð—ķ ð—ļð—Ū 𝗚ð—Ūð—ŧ𝘁ð—Ū ð—ļ𝘄ð—Ūð—ŧð—Ū ð—ą'ð—Ūð—ķ ð—ą'ð—Ūð—ķ ð—ĩð—Ūð—ŋ
ð—Ŋð—Ūð—ļ𝘄ð—Ūð—ķ ð—ŧð—Ū ð—Ŋð—Ūð—ļð—Ū.....𝘁𝘂ð—ļ𝘂ð—ŧð—ŧð—Ū 𝗚ð—Ū 𝘄ð—Ūð—ķ 𝘄ð—Ū𝘆ð—ē 𝘆ð—Ū𝗰ð—ē 𝗚ð—Ūð—ļð—Ū ð—ĩð—Ūð—ļð—Ū ð—ŧð—Ū 𝘁𝘀ð—Ūð—ŋð—Ū ð—ļ𝗞𝗚ð—Ūð—ķ
ð—ŧð—ē?,ð—Ū𝘂ð—ŋð—ēð—ŧ ð—ąð—Ūð—ŧð—Ū 𝘁𝘀ð—Ūð—ŋð—Ū ð—ąð—Ūð—īð—Ū ð—ąð—Ū𝘂ð—ŋð—Ū𝘄ð—Ū 𝘀ð—Ūð—ķ ð—ŋð—Ūð—ļð—Ū𝘁ð—Ū ð—īð—ķð—ąð—Ūð—ŧ 𝘁ð—Ūð—ŋð—Ŋð—ķ𝘆𝘆ð—Ū ð—ąð—Ū 𝘇ð—Ū𝘀𝘂𝘆ð—ķ?"

"𝗚ð—ķð—ąð—Ūð—ŧ 𝘁ð—Ūð—ŋð—Ŋð—ķ𝘆𝘆ð—Ū?" 𝗙ð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū ð—ąð—ķð—ŧ 𝘆ð—Ū ð—ģð—Ūð—ąð—Ū 𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū ð—ąð—Ūð—ŧð—ŧð—ē ð—ąð—Ūð—ŋð—ķ𝘆ð—Ūð—ŋ𝘀ð—Ū,ð—ąð—žð—ŧ 𝘁𝘂ð—ŧ ð—ąð—Ūð—īð—Ū ð—ŧð—Ūð—ŧ
ð—ĩð—Ūð—ŋ 𝘀ð—Ūð—ŧð—ąð—Ū 𝘇ð—Ūð—ķ ð—Ŋð—Ūð—ŋ𝗞 ð—ģ𝘂ð—Ūð—ą ð—ąð—ķð—ŧ 𝗰ð—ķð—ļð—ķð—ŧ ð—īð—ķð—ąð—Ūð—ŧ𝘀ð—Ū ð—Ŋð—Ū𝘆ð—Ū𝘀𝗞ð—ŧ 𝘆ð—Ūð—īð—Ū 𝘄ð—Ūð—ŧð—ķ ð—Ūð—Ŋ𝘂 𝗚ð—ē ð—ļð—Ū𝗚ð—Ū ð—ąð—Ū
𝘄ð—Ū𝘀ð—Ū 𝘀ð—Ū𝗚.....𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū𝘀𝗞ð—ŧ ð—ķð—ąð—Ūð—ŧ𝗚ð—Ū 𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū ð—ąð—Ū𝘂ð—ļð—Ūð—ŧ ð—Ūð—Ŋ𝘂ð—ŧ ð—Ū 𝗚ð—Ū𝘇ð—Ū𝘂ð—ŧð—ķð—ŧ 𝘄ð—Ū𝘀ð—Ū 𝘀𝗞 𝘆ð—Ūð—ļð—ē
𝘆ð—Ū𝗷ð—ķ 𝘀𝗞𝘀ð—Ūð—ķ ð—Ū ð—ŋð—Ūð—ŧ𝘀ð—Ū ð—Ū𝘂ð—ŋð—ē 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ ð—ļð—Ū𝗚ð—Ūð—ŋ ð—ļ𝗞𝘄ð—Ūð—ŧð—ŧð—ē 𝗚ð—Ūð—īð—ķð—ąð—Ūð—ŧ𝗰ð—ķ.

"𝗧𝗞 ð—ļð—Ū 𝘀ð—Ūð—Ŋð—Ū ð—đð—ķ𝘀𝘀ð—Ūð—ģð—ķ 𝘆ð—Ūð—đð—đð—Ūð—Ŋð—Ūð—ķ" 𝗎ð—Ū ð—ģð—Ūð—ąð—Ū 𝘁ð—Ūð—ŧð—Ū 𝗷ð—Ūð—ŧ ð—ĩð—Ūð—ŧð—ŧ𝘂ð—ŧ𝘀ð—Ū 𝘀𝘂ð—ŧð—Ū ð—ūð—Ūð—ŋð—Ū𝘀ð—Ū𝘄ð—Ū 𝗰ð—ķð—ļð—ķ.

𝗗ð—Ūð—īð—Ū ð—ūð—Ūð—ŋ𝘀ð—ĩð—ē ð—ąð—Ūð—ķ ð—ąð—žð—đð—ē ð—ķð—ąð—Ūð—ŧ𝘂 𝘆ð—Ū 𝘇𝘂ð—Ŋð—Ū𝘄ð—Ū ð—ģð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū ð—ąð—ķð—ŧ,𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ 𝘄ð—Ūð—ŧð—ļð—Ū
ð—ąð—žð—ŧ ð—ąð—Ū𝗚ð—Ū 𝘀ð—Ūð—Ŋ𝗞ð—ŧ𝘀ð—ĩð—ķ ð—ŧð—ē ð—ąð˜‚ð—ļ ð—ąð—Ūð—ŋð—ē,ð—Ŋð—Ūð—ŋð—ē 𝘆ð—Ū𝘂 ð—ąð—ķð—ŧ ð—ąð—Ū 𝘀𝘂ð—ļð—Ū 𝘄𝘂ð—ŧð—ķ 𝘇ð—ķð—ŋð—īð—Ū 𝘇ð—ķð—ŋð—īð—Ūð—ŋ ð—ąð—Ū
ð—Ŋð—Ūð—Ŋ𝘂 ð—īð—Ūð—ķð—ŋð—Ū ð—Ŋð—Ūð—ŋð—ē ð—ąð—Ūð—đð—ķð—đð—ķ ð—ąð—Ū ð—ģð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū 𝘆ð—Ū ð—Ū𝘇ð—Ū 𝗚ð—Ū𝘀ð—Ū. 𝗎ð—Ū𝗷ð—ķ ð—ąð—Ūð—ąð—ķð—ŧ 𝗷ð—ķð—ļð—ķð—ŧ𝘀ð—Ū
𝘀𝗞𝘀ð—Ūð—ķ,ð—ģð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū 𝘆ð—Ū ð—ģð—ķð—ąð—ąð—ž 𝗚ð—Ū𝘀ð—Ū ð—ļ𝗞𝗚ð—Ūð—ķ. 𝗞ð—Ū𝗚ð—Ūð—ŧ ð—ąð—Ū𝘇𝘂 ð—ĩð—Ūð—ļð—Ū 𝘆ð—Ū ð—ąð—ķð—ŧð—īð—Ū 𝗚ð—ķð—ūð—Ū 𝗚ð—Ū𝘀ð—Ū
ð—ļ𝗞𝗚ð—Ūð—ķ 𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū 𝘀ð—ĩð—ķð—ŋ𝘆ð—Ū𝘄ð—Ū,𝘀ð—Ūð—ķ ð—īð—Ū𝘀ð—ĩð—ķ 𝘆ð—Ū ð—ģð—ķ𝘁𝗞 ð—ģð—ē𝘀 𝗰ð—ķð—ļð—ķð—ŧ 𝗞ð—đð—ķ𝘃ð—ē 𝗰𝗞ð—đ𝗞ð—ŋ,𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ ð—Ū𝗚ð—ģð—Ūð—ŧð—ķ ð—ąð—Ū
ð—ĩ𝘂ð—đð—Ū ð—ąð—Ū ð—ĩð—Ūð—đð—ģ 𝗰𝗞𝘃ð—ēð—ŋ 𝘀ð—ĩ𝗞ð—ē ð—ąð˜‚ð—ļð—Ū ð—ļð—Ūð—đð—Ūð—ŧ ð—―ð—Ūð—đð—ē 𝘀ð—Ūð—īð—ē ð—ąð—Ū𝘆ð—Ū ð—ąð—Ū𝗰ð—ē ð—ū𝘄ð—Ūð—ŋð—Ūð—ķ ð—ąð—Ū 𝗞ð—đð—ķ𝘃ð—ē
𝗰𝗞ð—đ𝗞ð—ŋ ð—ąð—ķð—ŧ ð—ąð—Ū 𝘄ð—Ūð—ŧð—ķ ð—ķð—ŋð—ķð—ŧ 𝗚ð—Ū𝘁𝗰ð—ĩð—ķð—ŧð—ī. 𝗗ð—Ūð—īð—Ū 𝘀ð—ĩð—ķ ð—ĩð—Ūð—ŋ ð—ģð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū 𝘀𝘂ð—ŧ𝘆ð—ķ 𝘄ð—Ūð—ŧð—ķ ð—Ŋð—Ūð—đð—Ū'ð—ķð—ŧ
ð—ū𝘄ð—Ūð—ŋð—ē𝘄ð—Ū 𝘄ð—Ū𝗷ð—ēð—ŧ ð—ķ𝘆ð—Ū ð—ĩð—Ūð—ąð—Ū 𝗰𝗞ð—đ𝗞ð—ŋ ð—ąð—Ū 𝘀ð—Ūð—ŧ𝘆ð—Ū 𝘀𝘂𝘁𝘂ð—ŋð—Ūð—ŋ ð—ąð—Ū 𝘇ð—Ū𝘁ð—Ū 𝘇ð—Ū𝘂ð—ŧð—Ū ð—Ū 𝗷ð—ķð—ļð—ķ. 𝗗𝘂ð—ļ ð—ąð—Ū
ð—Ū 𝘆ð—Ūð—ŧ𝘇𝘂 𝘀ð—ĩð—ķ ð—Ŋð—Ūð—ķð—ąð—Ū 𝘄ð—Ūð—ŧð—ŧð—Ūð—ŧ ð—đ𝗞ð—ļð—Ū𝗰ð—ķð—ŧ,ð—ąð—žð—ŧ 𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū ð—ąð—Ū ð—―ð—ŋ𝗞ð—ģð—ē𝘀𝘀ð—ķ𝗞ð—ŧð—Ūð—đ 𝗰ð—đ𝗞𝘀ð—ē𝘁 𝗞ð—ŋð—īð—Ūð—ŧð—ķ𝘀ð—ēð—ŋ
ð—ąð—Ūð—ļð—ē 𝘁𝘀ð—Ūð—ŋð—Ū 𝗚ð—Ū𝘀ð—Ū ð—ļð—Ū𝘆ð—Ūð—ŧ ð—ąð—Ū 𝘇ð—Ūð—ķ𝘆ð—ķ ð—Ū𝗚ð—ģð—Ūð—ŧð—ķ ð—ąð—Ū𝘀𝘂 ð—ŧð—Ū 𝘁𝘀ð—Ūð—ĩ𝗞ð—ŧ 𝘀ð—Ū𝘁ð—ķ𝘁𝘁ð—ķð—ļð—Ū,𝘄ð—Ūð—ŧð—ąð—Ū 𝘆ð—Ū
ð—Ū𝗷ð—ķ𝘆ð—ē𝘀𝘂 ð—ŧð—ē ð—Ū ð—ąð˜‚ð—ļð—Ū ð—ī𝘂ð—ŋð—Ūð—ŋð—ēð—ŧ ð—ąð—Ū 𝘆ð—Ūð—ļð—Ūð—ŧ ð—ķ𝘆ð—Ū 𝘇𝘂𝘄ð—Ū 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ 𝘀ð—Ū𝘁ð—ķ ð—ļ𝗞 𝘀ð—Ū𝗚ð—Ū ð—ąð—Ū
ð—ĩð—Ūð—ļð—Ū,ð—ļ𝗞𝘄ð—Ūð—ŧð—ŧð—ē ð—ļ𝘂𝗚ð—Ū ð—Ūð—đð—Ŋð—Ū𝘀ð—ĩð—ķð—ŧ𝘀ð—Ū ð—ąð—Ūð—Ŋð—Ūð—ŧ ð—ļð—žð—ąð—Ū 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ 𝘄ð—Ū𝘁ð—Ūð—ŧð—ŧð—ķ ð—Ŋð—Ūð—ķ𝘆ð—ķ ð—Ūð—ķð—ļð—ķð—ŧ𝘀ð—Ū ð—Ŋð—Ū.
ð—Ķð—Ūð—ķð—ąð—Ūð—ķ ð—ąð˜‚ð—ļ ð—ąð—Ū ð—ĩð—Ūð—ļð—Ū ð—ąð˜‚ð—ļ ð—ŋð—Ūð—ŧð—ąð—Ū 𝘆ð—Ū 𝘀ð—Ū𝗚𝘂 ð—ļð—Ūð—ŧ𝘀ð—Ū 𝘆ð—Ū ð—ĩð—Ūð—ąð—Ū𝘄ð—Ū ð—ļð—Ūð—ŧ𝘀ð—Ū ð—ąð—ŋð—ē𝘀𝘀ð—ķð—ŧð—ī 𝘁ð—Ū
ð—ģð—Ūð—ŋð—Ū𝘁 ð—ąð—Ū𝘆ð—Ū ð—ģð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū ð—ļð—ē ð—īð—Ūð—ŧð—ē𝘄ð—Ū. 𝗎ð—Ūð—Ūð—Ūð—ŧ ð—ĩð—Ūð—đð—ķð—ŧ𝘀ð—Ū,𝗚ð—Ū𝘆ð—ē ð—ŧð—ē 𝘄ð—Ū𝗷ð—ēð—ŧ ð—ķ𝘆ð—Ū 𝘁𝘀ð—Ūð—ŋð—Ū𝘄ð—Ū
𝗷ð—ķð—ļð—ķ ð—Ūð—ąð—ž ð—ąð—Ū 𝘆ð—Ū𝘄ð—Ūð—ŧ𝗰ð—ķ 𝘆ð—Ūð—ļð—ē 𝘀ð—Ūð—ļð—ē 𝘁ð—Ūð—ļð—Ū 𝗚𝘂ð—ĩð—ķ𝗚𝗚ð—ķ𝘆ð—Ūð—ŋ ð—ŋð—Ū𝘄ð—Ū 𝘄ð—Ū𝗷ð—ēð—ŧ ð—ģ𝘂𝘀ð—īð—Ūð—ŋ ð—ĩð—Ūð—ŧð—ļ𝘂ð—đð—Ūð—ŧ
'𝘆ð—Ū𝗚𝗚ð—Ū𝘁ð—Ūð—ŧ ð—ąð—Ūð—ļð—ē ð—ū𝘂ð—đð—Ūð—ģ𝘂𝗰ð—ķð—ŧ𝘀ð—Ū.

"𝗠ð—Ū 𝘀ð—ĩð—Ū 𝗔ð—đð—đð—Ūð—ĩ.... .ð—―ð—ēð—ŋð—ģð—ē𝗰𝘁 𝗚ð—Ū𝘁𝗰ð—ĩ" 𝗙𝘂ð—Ūð—ą ð—ąð—ķð—ŧ 𝘆ð—Ū ð—ģð—Ūð—ąð—ķ 𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū 𝘀ð—ĩð—Ūð—ģð—Ū ð—īð—Ūð—Ŋð—Ūð—ŧ ð—Ŋð—Ūð—Ŋð—Ŋð—Ūð—ŧ
ð—ŋð—ķð—īð—Ūð—ŋ ð—ąð—Ū 𝘆ð—Ū𝘀ð—ĩð—Ū ð—Ūð—ķð—ļð—ķ. ð—Ķð—ĩð—ķ ð—ļð—Ūð—ŧ𝘀ð—Ū ð—ģð—Ūð—ŋ𝗞𝘂ð—ū ð—ąð—ķð—ŧ ð—ļð—Ūð—đð—đ𝗞ð—ŧ𝘀ð—Ū 𝘆ð—Ūð—ļð—ē,𝘆ð—Ūð—ąð—ąð—Ū ð—ļð—Ū𝘆ð—Ūð—ŧ 𝘀𝘂ð—ļð—Ū
ð—Ū𝗚𝘀ð—ĩð—ē𝘀ð—ĩð—ķ 𝗚ð—Ū𝘁𝘂ð—ūð—Ū 𝘀𝘂ð—ļð—Ū 𝘀ð—Ūð—ļð—ē 𝘀𝘂ð—ŋð—Ū ð—ąð—Ū ð—ļ𝘄ð—Ūð—ŋ𝗷ð—ķð—ŧð—ķð—ŧ ð—ąð—Ū 𝗔ð—đð—đð—Ūð—ĩ 𝘆ð—Ū ð—Ŋð—Ū𝘀ð—ĩð—ķ.

ð—Ąð—ē𝗚ð—Ūð—ŧ 𝘄ð—Ū𝗷ð—ēð—ŧ 𝘇ð—Ū𝗚ð—Ū 𝘆ð—Ūð—īð—Ū 𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū𝘆ð—ķ,𝘀ð—Ūð—ķ 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ ð—Ŋð—Ūð—ŧ𝘇ð—Ū ð—ąð—Ū𝘀ð—ĩð—ķ,𝘆ð—Ū ð—ģð—ķð—ąð—ąð—Ū 𝘄ð—Ū𝘆ð—Ū
𝘆ð—Ū ð—ļð—ķð—ŋð—Ū ð—Ūð—Ŋð—Ŋð—Ū.....

"𝗔ð—Ŋð—Ŋð—Ū 𝗚𝘂ð—ŧ ð—īð—Ū𝗚ð—Ū,𝗞ð—ļð—Ū𝘆 𝘁𝗞" 𝗠ð—Ūð—ķð—ąð—Ū 𝘄ð—Ū𝘆ð—Ūð—ŋ 𝘆ð—Ū𝘆ð—ķ ð—Ūð—đ𝗷ð—ķð—ĩ𝘂ð—ŧ𝘀ð—Ū 𝘆ð—Ū 𝗚ð—ķð—ūð—ē

"ð—Ķð—Ūð—ķð—ļð—Ū 𝘁ð—Ū𝘀𝗞 𝗚𝘂𝗷ð—ē ð—Ū𝘆ð—ķ 𝗚ð—Ūð—ļð—Ū ð—ģð—Ūð—ąð—Ūð—ŧ ð—īð—ķð—ąð—Ūð—ŧ ð—Ū𝘂ð—ŋð—ē". 𝗎ð—Ū ð—ģ𝘂ð—ŋ𝘁ð—Ū 𝘆ð—Ūð—ŧð—Ū ð—ąð—Ūð—ŧð—ŧð—ē
ð—ąð—Ūð—ŋð—ķ𝘆ð—Ūð—ŋ𝘀ð—Ū.

𝗗ð—Ū ð—ļð—Ūð—đð—đ𝗞 𝘆ð—Ūð—Ŋð—ķ

Please Login or Register in order to submit comment