You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya rude sosai don ta maida abun serious matter. Ya sulale ya tsugunna
a gabanta yana cewa.

"Am really sorry my world......taso muje ki gayamin a inda aka siyo a sake nemo
wani". Sai data galla masa harara sannan tace.

"Kaduna.....kaduna ne wajen maman ummi".

"Kaduna?" Ya maimaita.

"Eh" Ta fada cikin son jiran mutum yayi wani abun ta sake barke masa. Kansa ya daga
ya kalli agogo yana duba lokaci. Qarfe goma na dare,wa zaya tasa zuwa kaduna yanzu.
Idonsa ya mayar kanta,saiya taras ta zuba masa ido tana kallonsa,dukkan alamu kuma
sun nuna rigima ce a kwance idan ya musa.

"Is alright.....bani details na masu abun".


"0803 049 9555,wallahi tunda ummee ta haifeni ban taba cin doughnuts me dadin nata
ba" Ta fada bilhaqqi da gaske har zuciyarta tana jin tun kafin ya kawl ma yawunta
ya tsinke. Idanu warwaje yake kallonta. Tashin hankali!,ya fadi saboda yadda yaga
tsaf ta haddace number,yaushe hakan ta faru oho shima bai sani ba.

"Ina zuwa" Yace mata yana takawa a hankali yana sauka qasan. Shi kam yasam yanzu ba
lallai a bawa jadda wings daman tashi ba,kafin ma su nemo umarni,pilot din ya isa
su tashi ai asuba yayi,saidai duk da haka bai fasa kiran number din ba.

Ainihin sunan daya fito ameena sai yaji kimar me number ya qaru a
idonsa tun ba'a daga kiran ba. Bugu na uku aka dauka da cikakkiyar sallama ya amsa
shima.

"Am sorry,na kira late at night......i don't know ko matar aurece.....am sorry idan
hakanne"

"Ba komai" Matar me kirki ta fada. Bayanin dalilin kiran yayi sannan ya dora.

"If possible goben zan aiko a taho dake,kizo kiyi mata sai a maidaki.....kiyi
naming price dinki,kada ki damu ko nawa ne ki zaba i will pay it". Murmushi tayi.

"Ba matsala.....ko goben da safen ma ana iya samun ko pieces nawa takeso.....akai
akai sai a dinga zuwa ana karba mata,Allah ya raba lafiya,kowanne ciki da yadda
yake zuwa ma mace,sai haquri". Yaji dadin magananta sosai,don daga yanayinta ya
fahimci ba yarinya qarama bace,yayi godiya sannan ya kashe ya kira farouq.

Bugu daya ya samu farouq,da alama bacci ya fara daukansa ma.

"Farouq akwai matsala fa" Maganan da ta saka farouq miqewa ya zauna

"Me ya faru?" Ya tambaya. Ajiyar zuciya ya saki ya masa bayani a nutse.

"I don't know ina zan samu doughnuts?.....kune masu zuwa irin guraren nan".

"Ba damuwa......bari na duba wani guri kusa damu......sun iya sosai zataji
dadinsa".

"Thank you dude.....you save me" Ya fada yana dan dafe goshinsa sannan suka yanke
kiran.

Lallabata ya dinga yi har aka gaya masa ga saqo daga bakin gate. Sanda
yaje har farouq din ya aje saqon ya juya,ya yaba masa sosai irin saurin da yayi don
duka duka mintuna talatin ya iso,ya tabbatar wannan gudun nasa ya zuba.

"Ga doughnuts din" Ya fada da murmushi yana aje box din a gabanta. Da zumudi ta
jawo ledar ta bude. Tun a yanayin packaging din ta tabbatar akwai matsala,banbamce
babance take gani iri iri da wancan,ta danne tana bude doughnuts din.

Kanta ta daga ta kalleshi,ya dage mata gira yana qoqarin lallabata,can
qasan ransa yana fatan kada ta ballo rigima kuma.

Kanta ta mayar kai,ta gutsira tana kaiwa bakinta. Taunawa daya biyu ta
furzar,muryarta tana rawa ta kalleshi

"Wannan bashi bane.....Allah bashi bane".

" I know sabrrrr.........kiyi haquri kici wannan din,i promise you da safe wancan
din zakici as breakfast"

"Really?" Ta tambaya tana tsareshi da idanu.

"In sha Allah" Ya fada yana bata assurance. Hankalinta taji ya kwanta,amma duk da
haka ta ture wancan din

"Banasonshi....nata yafi dadi yafi madara" Dariyarsa ya boye,yana mamaki ashe da
gaske masu juna biyu suna haka?,idan madara takeso suna da ita kala kala har sai ta
ture,amma ya tabbatar yace tasha din ba sha zatayi ba.

β˜…Tun sanda amna tabar dakin sai taji ta gaza nutsuwa sam sam,hankalinta
ya kasa kwanciya,itama sai ta samu kanta da rashin nutsuwa da kokwanto.

Toilet ta wuce,ta daura alwala,ta dawo ta shimfida abun sallah. Raka hudu
tayi ta zauna ta fara karanta hasbunallahu wani'imal wakil qafa dubu. Ko kadan
batajin bacci a idanunta,haka kuma batasan meye ya dauke baccin a idanunta ba.

Bayan ta gama ta sake gyara tasbaharta. Bismillah hirrahamanir rahim 450
ta karanta,sannan tayi salati 450 shima. Bayan ta gama ta karanta (Allazina qala
lahumunnasu innan nasa qad jama'u lakum fakshauhum fa zadahum imanan wa qalu
hasbunallahu wani'imal wakil zuwa fanqalabu bini'imatimminallahi qafa 45(ko 450
idan zaka iya),ta sake karanta salati 450,sannan ya azizu ya khafi ya qawiyyu ya
ladifu 450,duk inda takai guda 100 saita tsaya ta jaddada roqonta ga Allah,neman
tsari daga dukkanin wani mummunan abu ko abun qi da zai iya samunta ko ya samu wani
cikin ahalinta,ta sake zurfafa addu'ar samun albarka da sanya albarka a dukkanin
wadannan aurarraki da akayi dama wadanda suka wuce.(addu'a ce me kyau da tsananin
tasiri wajen samun biyan buqata wajen Allah,in kin zama me riqe addu'a da barwa
Allah lamuranki kin huta da gasken gaske,shi zai miki komai daidai da yadda ya dace
dake,sadaka ce na baku sai a sanyani a addu'a,ubangiji ya bamu dacewa).

Shafa addu'ar tayi tana jin wata nutsuwa tana saukar mata,ta miqe a
nutse ta shirya don wucewa gurin abba. Sai data gama shirin sannan ta zauna saman
stool,ta debo ruwa a wani babban mug ta soma karanta ayatulkursiyyu qafa ashirin da
daya ta fita da mug din a hannunta.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 137


https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



138


Zuwa takwas da rabi na dare ya shigo gida. Tun kafin ya shiga din ya
sallami kowa,don ragowar lokacinsa yana jin cewa na duniyarsa ne.

Yau din sai take jinta a cikakkiyar matar aure kaman kowacce d'iya
mace. Ta shirya sosai tayi kwalliya da wani farin tattausan lace,fari ne qal babu
sirkin komai a jikinsa. Ya kwanta mata sosai a fatarta,ba makeup a fuskarta,daga
powder data dace da skin dinta,sai wheat lips da ya sanya pink lips dinta suke wani
glowing me daukar hankali.

Sau daya tak ya kalleta yaji tana son raba masa hankali,sai yake ganin
kamar canzata akayi daga fitarsa zuwa dawowarsa,kaman yadda yaji qamshin gidan gaba
daya ya sauya.

Qugunta ya kamo,ya kasa cewa komai sai daya sada lips dinsa da nata,ya
tsotse lips gloss din da kyau kaman bata taba shafa komai akai ba da wani zazzafan
French kiss.

Bakinsa ya zare yana sauke numfashi,idanunshi akan fuskarta,yana jin
yadda fatarta dama kayam jikinta suke fidda wani daddadan qamshin turaren kabbasa.
Idan baiyi kuskure ba har gashinta data harshi baje saman kafadarta qamshin yake
fiddawa.

"Those sweet lips sabrrrr....." Ya fada yana zagaye yatsansa akan shape na lips din
nata,yana jin wani shauqi yana fusgarsa. Murmushi ta saki tana dan kauda kanta
tanason ta karbi wayoyin hannunsa da wata 'yar kyakkyawar briefcase dinsa. Hannunsa
ya sanya ya juyo da fuskarta da sauri.

"Nooo......my lips missed yours sabrrrr......" Ya fadi yana sake hade bakinsu guri
daya.

Wani yanayi ya fara saukar musu shi da ita,har qafafunta suka fara rawa
ta fara jin ba zasu iya ci gaba da daukarta. Shi dinma hakanne,don gaba daya
jikinsa ya dauki shock har sai da suka zube saman sofa sannan ya zare bakin nasa.

"Your lips are the ones.....i want to kiss forever" Ya qarasa fada yana tura
hancinsa wuyanta qamshinta yana bugar dashi.

"Sabrrrr.....so kike ki haukatani da alama ko?" Ya furta yana Dubanta da juyayyun
qwayar idanunsa kaman wanda yasha wani abu. Fiddo idanu waje tayi tana
dubansa,hakan sai ya qara mata bala'in kyau saboda yadda sukayi wani haske,eye
lashes din kuma suka zame musu tamkar wani ado.

"Muffin.....me kuma nayi?.....idan na kasheka kuma na zauna da wa?" Tayi maganar ne
cikin wata irin shagwaba. Hancinta yaja kafin ya lakuce mata kumatu.

"Fisabillahi zan fadi gaskiyata.....wannan qamshin lallai idan kina tare dashi
zanfi tape da taya maqale miki......komai kuma zai iya faruwa ako ina
sabrrrrr.......daga ina wannan qamshin?" Ya fada yana kashe mata ido. Murmushi ne
ya subuce mata sosai,harga Allah da farko ta dauki turaren ne kawai saboda amna
tace ta dauka,cikin irin turarukan da akayi musu ita da huda wanda.ta bakinsa tasan
huda sun iso,saidai tana sakawa a burners dake lungu da saqo na gidan ta gama
giving up.

Lumshe idonta tayi wani farinciki yana saukar mata,ta bude idanun nata
ta saukesu akan kwalbar LAB_LAB da tayi amfani dashi,wanda daga saman kwalbar
manyan rubutu ne b'aro b'aro dake dauke da sunan INCENSE BY KABO DAUGHTER.
(Kunsan ni ma'abociyar son qamshi ceπŸ˜„,na muku tallan turarukan matar nan TASTED
AND TRUSTED ne,duk irin turaren da kike siya ina baki shawara ki gwada nata,yayi
yayi yayi,zaki kuma bawa wani labari,muddin kina da dama amma baki siya ba ina me
tabbatar miki kin loserπŸ˜‚πŸ˜‚,confirmedπŸ™ŒπŸ½πŸ™ŒπŸ½,ba kuma bala'in tsada gareta ba.....sai
sirrin sanin kan turaren,nima dai 'yar gidan malam shehu ce bare ace na manya muke
using ahtoπŸ˜‚πŸ˜‚,ki gwada hajjaju zaki godemin,don tabbas idan me tsoron Allah ce ke
kikayi kabbasarta kika saka humra ko lab lab dinta ba zaki iya fita unguwa ba
saboda fitinannen qamshi suke bayarwa,ki gwada ki godemin +234 803 211 9803).

"Saboda kai ne muffin......saboda kai ne". Idonsa ya lumshe yana sake zuqar
qamshin,har cikin zuciyarsa yake sauka,wani nutsuwa qamshin yake bashi,kamar wadda
aka tsoma a bahon turare.

"Kiyimin rai please sabrrr" Ya fadi yana sake cusa kanta tsakanin dukiyar
fulaninta.

"Name?" Ta tambaya tana murmushi.

"Don Allah kada ki bari wani yaji wannan qamshin idan bani ba". Ya qarasa maganar
yana dago kansa gami da sanya idanunsa cikin nata don ta gane har ranshi,da gaske
kuma yake maganar.

Tafukan hannayenta dasu kansu qamshin suke ta saka tana dago kansa
sosai. Zuwa yanzun tuni ta fara fahimtar yanayinsa....da yayi magana ko baiyi
ba....idan yayin daga ina ta fito?.

"Muffin.....kana tunanin zanbar wani hanci ko wani d'a namijin daban bakai ba ya
samu wannan nutsatsen qamshin?.....har abada idan kace bakaso ko farfajiyar gidan
nan qamshin nan ya fita bazai fita ba......a yanzun hatta da rai ka bani
DUNIYATA......Ka bani rai tunda ka kusanto da makusantana kusa dani......dame ne
zan saka maka ni ameenatu?" Ta qarashe maganar zuciyarta tana karyewa da wani irin
rauni.

Idanunshi cikin nata ya dora hannunsa saman mararta.

"Kin gama sakamin ameenatu.....kin gama sakamin sabreena.....kin gamamin sakayya
duniyata da kika bani iri.....yara uku fa?,lokaci guda?,a qaramin lokaci har
haka?,kika cikamin muradin zuciyata?......abu daya ne ya rage kiyimin,karki guje ni
tsanani ko dadi.....karki bari tarbiyyar yarana ta zama abun Allah wadai......ki
soni irin son da ba wanda zaki bawa katankwacinsa.....that's all" Ya fada yana dage
hannuwansa sama.

Hannunta ta saka daga qeyarsa sannan ta hade goshinsu guri daya suna
musayar numfashi.

"Ka samu muffin.....ka gama samunsu.....amma zan qara da addu'a ga
Abba......mutumin da yayi sanadin haifamin irin wannan mijin.....ubangiji ya jiqa
kabarinsa ya kuma lullube kabarin nasa da dukkanin wani nau'i na rahamarsa"

"Allahumma ameen" Ya fadi muryarsa qasan maqoshi yana sake jin ta masa kima sosai.

"Abinci ko wanka?" Ta tambayeshi ba tare data dauke goshinta a nasa ba still kuma
tana zaune saman cinyarsa.

"Cin abinci sannan kazo kayi wanka yana raunana jiki my world" Idanu ta fitar tana
dubansa bayan ta janye fuskarta.

"Muffin.......da gaske komai naka dabanne,tsarukanka dabanne kaman yadda naji ana
gulmarka......kasan duk wani abu da zai kiyaye lafiyarka"

"Wait" Yace yana hade ransa da wasa.

"Wake gulmata?,farouq ko?" Dariya sosai ta kubce mata har tana sake riqeshi don
kada ta fadi.

"Komai farouq?,komai farouq?.....BB ya kusa hutawa dai,nasan fannarshi zata siya
masa 'yanci". Murmushi shima yayi yana kama hannunta suka miqe,shi kansa baisan ya
wannan ranar zata kasance ba.....kowa ma ya shiga uku.
Tsaf ya janyeta suka shiga wanka kaman yadda rules dinshi yake,har ya fara
zame mata jiki,ya gaya mata sunna ce kuma bazai gaji da rayata ba,don duk wanda
yayi koyi da wani abu cikin abinda manzan Allah yakeyi da zummar koyin yake
dashi,to tabbas yana da ladan koyi dashi.

Cikin wasu sauqaqan couples pyjamas suka shirya dukkanin farare da adon
black wuya da hannu da qafan wandon da bai qarasa idon sahu ba. Kamar wasu
ma'auratan daga wata qasar,suka sauka qasa tare.

Bayan kammala cin abincin basu kwanta ba,dukka maganganu ne da shirye
shiryen biki yaketa fama. Itadai tana gefe tana kallon zallar aikin zumunci irin ma
fu'ad din,ta sake tabbatarwa bawai a banza Allah yaa sanya wannan dukiyar a
hannunsa ba(Tabbas idan har Allah ya baka wadata fiye da sauran abokai ko 'yan
uwanka,to ya baka ne don ka taimakesu,wala'alla duka harda arziqinsu ya saka a
hannunsu don ka zama.silar ciresu daga matsi ko matsala,Allah yana sonka da yayi
maka wannan baiwar,don zaka samu lada sanda kake basu ita ta hanyar data dace,don
ka zama kamar wakilin Allah a bayan qasa,idan kuwa ka riqe ka hanasu yana
kallonka.....tabbas! Kuma sai yayi hukunci akai, 'yan uwa dukiyarka kenan
fa.....inaga wanda zai danne haqqin wani?,ina ga wanda zai cinye dukiya ko gumin
wani?,Allah yasa mu dace,ya rabamu da taba abinda ba namu ba ya hayyu ya qayyumu).

Ganin ta langabe masa zata yi bacci ya katse maganan da yakeyi da kowa ya
dubeta.

"Gate up ameenatu.....naga list na amna.....ke banga naki ba" Ido ta zaro,cikin
muryar soma jin bacci tace

"Muffin.......nawa name?"

"Naki lefan.....naki lefen sabrrrr" Ya fada yana kama hannunta.

"Banda wanda akayimin hamma?" Ta tambaya tana dan dariya saboda ta dauka zolaya ne.
Kai ya girgiza.

"A yanzun ke din cikakkiyar zabin MUHAMMAD FU'AD JADDA ce,sabon lefe sabon sadaki
daga hannun jadda" Ya fada yana zame hannunsa a nata. Qasa ya saka hannunsa ya
fiddo wata kyakkyawar leda ya zube kayan ciki.

Kyawawan akwatuna ne har guda shida masu daukan hankali,iya akwatun
kawai abun kallo ne,ba zaka gane kuma kallo ya koma sama ba sai daya bude abun
ciki.

Wasu irin sabbin designs ne na gold masu matuqar daukan hankali. Uku
gold ne uku kuma diamond,wanda ta gane haka ne ta qaramar takardar dake maqale a
ciki. Uku ya ware a ciki ya tura gabanta,ya bude wani jaka qarama dake gefan system
dinsa ya ciro sabbin rafas na dubu d'aya d'aya na dollars a miqe kar dasu ya dora a
sama.

"Wannan shine sabon sadakin ameenatu muhammad jadda.....idan tana buqatar sama da
haka tayi magana......wannan kuma" Sai ya tura sauran boxes din

"Wannan kuma ladan rainon cikin da za'a yimin....duk da nasan ban isa na biyasu
ba.....duk boxes daya a madadin yaro daya yake.....shima idan baiyi ba kiyi naming
price dinki". Kaf jinin jikinta taji ya daskare na wucin gadi,uwar dukiyar daya
zube mata kawai take.kallo tana jin zuciyarta tana raurawa,sarqoqi shida masu
qololuwar darajar da batasan ya zata kimanta kudinsu ba?,ga tsabar kudi daya kusa
naira million dari da sittin?. Tsoro ne kawai taji yana shirin kamata,tsoron ta
yaya diyar ahmadu kamarta zata mallaki dukiya dare daya irin wannan?.
Tana shirin zamewa tayi kneeling a gabansa ya dagota.

"Kul karkimin godiya....karki qorafi,kinfi qarfin komai da zan baki,don kema kin
bani abinda ban isa ni kadai na bawa kaina ba......kin soni da zuciya daya,kin
tsallake duk wani gwaji da nayi miki da zummar gano dukiyar kikeso ko bata
gabanki,a yanzu ba abinda bazan iya sadaukar miki ba...bare wannan da ba komai bane
cikin abinda Allah ya mallakamin ba.....so komai na dauka na baki kin cancanceshi
ne,addu'arki da soyayyarki kadai su nafi buqata a halin yanzu a rayuwata,Allah ya
yimin komai". Qasa tayi da kanta tana jin hawaye yana sauka a idanunta,sai ya buge
da tsokanarta har sai daya rakata daki,ya tabbatar ta kwanta ya lullubeta da duvet
ya tofeta da addu'a. Sai daya tabbatar bacci ya soma cin qarfinta sannan ya dawo
falon ya zauna yaci gaba da aikinsa.


β˜…Sake juya rubutaccen katin da yake hannunta tayi wanda akayi da zallar ruwan
gold tana bin kowanne ado na jiki da kallo. Ko ba'a gaya mata ba ta sani gold ne
zube a jikin katin daurin aure takarda maras daraja,ballantana zance yanata yawo
anata yamadidin bikin a lungu da saqo na qasar nigeria,tsakanin maiduguri da kano
kuwa dumin bikin ake ba'a cewa komai. Umar Farouq hamza kibiya zai auri fannah
maisharif babaghana .

Sake buda katin tayi tana duba schedules din,duka a maiduguri ne za'a
yi komai,shima abu qwaya biyu ne rakkin sai daurin aure rana ta uku,kamu da za'a
hada da zaman ajo,sai bridal shower sai daurin aure,amma ita kanta tasan ace ma ba
za'ayi ta'adin dukiya ba qarya ne.

"Ranar juma'a kenan fannah zata shigo ahalin hamza da ameenatu?" Ta furta ta daga
kai tana duban wanda ke tsaye a kanta. Kai ya jinjina mata

"Tabbas" Ya bata tabbaci ta cikin baqaqen gilashinsa. Wani shu'umin murmushi ta aje
tana ajiye katin.

"Na samu labarin kai tsaye zasu wuce da ita gidanta.....sai washegari da ameenatu
zata gudanar musu da walima haka ne?". Kai ya sake gyada mata don bata tabbaci.

Wannan karon qaramar dariya ta saki.

"Hakan nima yayimin.....amma kuma dan jahannama.......bazan iya jiran washegarin
ba......inaso ranar juma'ar ta zama rana mafi muni da qunci a wajensu.....inaso
ranar ta juye musu daga farinciki zuwa baqinciki......inaso ta zame musu ranar
tonon sililin baqincikinsu". Kai ya jinjina yanajin hannunsa yana masa qaiqayi.

"Baki da damuwa......zamu ajiye musu tarihin da zai zame musu abun lissafi da irga
har qarshen kafuwar zuri'ar"

"Da kyau" Ta fadi tana cire sarqar gold din dake wuyanta. Sarqa me tsananin kyau
tsada da daraja.

"A auna maka ka saida.....ko nawa ta kama kudin naka ne......bayan kudaden da zaku
cajesu". Wata irin dariyar jin dadi ta qwace masa bayan ya karbi sarqar,ko a
hannunsa kawai nauyinta ya isa ya bashi amsar kudade ne masu nauyi akan
sarqar,baiyi wani mamaki ba ya juya ya fice yana jin dadin yadda zai rabauta da
riba biyu.

_uhmmmmm,zamu gani,waye zai rabauta?,waye zai fadi?,waye zaiyi farinciki waye kuma
zai shiga sasarin baqinciki?_

_Abinda ake gudu fa yana dab da faruwa.....abin boye fa yana dab da fitowa fili_πŸ₯Ή
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 139


https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX


139


*_WEDDING VIBES_*

*_KANO & MAIDUGURI_*

Idan aka ambaci umar farouq kibiya,wani mutum ne me wasu irin halaye
nagartattu,iya mu'amala da mutane da kuma Tarin abokai,duk da kusan kowanne aboki
da zai shigo rayuwarsa yana qoqarin tantance cancantar wanzuwarka a rayuwarsa.

Bikin ya karade kafofin sadarwa masu yawa,ya kuma shiga jerin sahun
bukunkunan da kowa yayi amanna zai bada wani irin salo me qayatarwa,duk da ba wani
abu me yawa aka tsara za'ayi ba.

Tun lahadi ya yiwa maiduguri tsinke ta jirgin jadda wings,yayin da ya
saukewa fuad saboda yanayin hannunsa. Su ahsan da sauran abokansu sune suka zame
masa groomsmen.

Duka komai dasa hannun fuad aka kammalashi da wani irin dattako da nuna
tsantsar 'yan uwantaka,sunyi fuad din zai taho ranar zaman ajo sai kuma da farouq
ya sanya ya masa alqawarin zaije har gurin,saboda yasan halinsa,tun asali dama shi
bameson ire iren wadannan abubuwan bane.

β˜…A nutse suke takowa zuwa farfajiyan da motocin da zasu masa rakiya zuwa airport
daga can su zarce Maiduguri. Hannunsa sarqafe cikin nata,kwana biyu din da zaiyi
sai yake jin kamar wanda zaiyi shekara biyu ne. Ita kanta duk sai takejin kamar ta
sake masa kuka,kewarsa takeji tun bai tafi ya barta ba,duk da takan ji dama dama
idan ta tuna in ya tafin itama zata wuce gidan anni don shirye shiryen biki,wanda
idan an dauko fannah an kawota nan din,walima za'ayi gagaruma guda daya da anni ta
shirya,zasuyi yini randa za'a sauka da fannah,walimar kuma washegari ce,to amma ita
din a yanzun ta zama kamar auntyn amaren gaba daya da angwayen. Tuna su huda na
tare da itan yana rage mata wani kadaicin,duk kuwa da cewa ba wanda ya isa ya cike
wannan gurbin nasa.

Baiko kulaa ko damu da mutane a wajen ba,ya ajiye mata tattausan kiss a
goshinta bayan duka sallamar da akayi a ciki.

"Saina dawo?,ki kulamin da kanki sosai,if possible ki dawo gida ki kwana,banaso na
tuna cewa baki dakinki kinji please" Kai kawai ta iya gyada masa,don idan tace
zatayi magana kuka ne zai qwace mata.
Har ya fara takawa zuwa motar da Jordan ya bude masa ta jawo
yatunsa,ya dawo da baya yana kallonta da narkakkun idanunsa.

"Yadai?.....ko na fasa ne?" Kai ta maqale sannan ta girgizashi.

"BB ne fa......idan banda BB dinne ba wanda zan bawa aronka....."

"Nima banda ina kishin a kallemin ke.....banda ina tattalin 'ya'yana ba abinda zai
sanya na tafi na barki"

"To amma...." Ta fada tana turo baki ba tare data qarasa magana ba. Idonsa ya
lumshe ya kuma budesu yana kallonta,ya mata alama daka akan ta fada.

"Banason ka kalli kowacce mace please...." Tayi maganan tana juya masa baya alamun
kunyarsa takeji. Qaramar dariya ya qwace masa,yasa hannu.ya juyo da ita yana fadin.

"Say it mana.....Louder please!,with all your might" Ya furta yana mata sassauqar
runguma ta baya,yadda ta nuna kishin na faranta masa kaman farincikin na neman masa
yawa.

Kai tsaye ta juyo ganin abun na masa dadi,ta saka idonta cikin nasan
tana dubansa.

"Your eyes belong to me,don't look at any other women please,na maka alqawari a
karan kaina.....my gaze is fixed on you alone,bana ganin kowai sai jadda na" Ta
fada tana rungume Hannayensa". Sulalewa yayi sai gashi saman gwiwarsa a
gabanta,abinda ya sanyata zaro ido ta fara kallon mutanen dake wajen.

Dukka guards nashi sun juya bayansu,ba wani guda daya da yake
kallonsu,saima kaman katanga da sukayi musu ta yadda ba wani a farfajiyan gidan da
zai ganin ainihin abinda ke faruwa.

"Karki damu,My men are extremely competent" Yana kaiwa nan ya kamo yatsuntsa masu
kyau da taushi. Kafin yace komai wayarsa ta dauki tsuwwa,yadan yamutsa fuska yana
cirota a aljihunsa. CP ahmad nuhu ne,don haka ya daga kai tsaye ya sanya a
kunnensa.

Cikin ban girma suka gaisa,kafin ya soma gabatar masa da bayanai.

"Sir dukkaninsu a yanzu sunyi taushin da kowanne bayanai muke buqatar tatsa daga
wajensu zamu sameshi in sha Allah,don yanzu haka bibo da zuwaira ma mun samu
dukkanin bayanan da muke da buqata,ban sani ba ko zamu iya aike maka ta email?"

"Good job sir.....thank you,basai ka turo ba,don yanzu haka mun fara hidimar bikin
dan uwana.....but zuwa Monday dukka zamu zauna dasu,akwai yiwuwar wanda za'a
sallama a cikinsu.....thank you sir"

"Okay sir.....in sha Allah" Cp din ya fada suna sallama cikin farinciki da
mutuntawar yadda dukiyar FU'AD din bata sanya yana musu kallon na qasa dashi ba.
Ya basu dukkan wani girmamawa da dama na gudanar da ayyukansu.

Kashe wayar yayi duka ya sanya a aljihu don kada wani ya katse masa
shauqinsa,sannna ya sake riqo tausasan tafin hannunta da har yanzu yake jiyo wannan
sassanyan qamshin na jiya (incense by kabo daughter+234 803 211 9803 Da gaske
turarenta kwana yake a jiki,kama gida kuma da wuri yake,khumrorinta dukka na
dabanne bare akai ga turarenta).
"Ni muhammad FU'AD jadda,an halicci ruhi Zuciyata dama gangar jikina gaba daya
saboda ameenatu sabreen........har abada gangar jikina da zuciyata sun haramta ga
wata diya mace ba ita ba......mata gaba dayansu wallahi wallahi kallon maza nake
musu 'yan uwana,daga kanki an gama haifar wata diya mace har abada,amana daya
ce......kuma kin sameta,bana canza magana,bana sauya alqawari" . Tasha jin ana cewa
maza basu da magana daya.....ta gani da idanunta yadda maza suke zama wasu ababen
tsoro game da mata,amma a yanzun saita samu kanta da amanna da maganganunsa.

Tana tsaye har dukka motocinsu suka bar harabar gidan,sai ta juya ta
koma a hankali tana jin kaman ita kadai ce ta rage a duniya. Bata dauki lokaci ba
itama sai kawai ta shirya,ta yiwa securities din daya bar mata magana

Please Login or Register in order to submit comment