You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ta fada idanunta suna rau rau da cika da hawayen farinciki

"Ko deboki akeyi a shanya a rana sai yamma tayi a maidaki daki.....ballantana ma
ina miki kyakkyawan fatan tsufa me kyau.....baka mummunar tsufa....baka tsufan
banza muddin ka riqe Allah kayi rayuwa irin wadda Allah da manzonsa suka tsara".

"Haqiqa ba wata kyauta da zaka bani a rayuwa bayan wannan......ba wata kyauta da
tafi wannan.....ka amintar dani daga tsoro na.....na gode.....na gode".

"Ni banason godiyarki" Ya fada yana zare jikinsa daga rungumar data masa,ya kuma
zura qafafunsa ya fita waje,saidai ya babbake bakin qofar motar ya zube hannayensa
a aljihun rigarsa ya zube mata fararen idanunsa.

"Me kakeso hamma?" Ta tambaya a sanyaye. Yadda tayi sanyin ya bashi dariya,ya kalli
qasa ya dara kadan sannan ya dubeta.

"Kici gaba da haifamin yara turmus....bibbiyu uku uku hurhudu harma biyar biyar".
Idanu tadan waro waje kafin murmushi ya subuce mata,kyau tayi masa sosai,sai ya
miqa mata hannunsa yana duban idanunta.

"Me kika ce?" Dora hannun nata tayi saman nasa ya taimaka mata ta fito sannna ta
amsa masa.

"Ka tayani da addu'a Allah ya bani masu sauqi,kuma Allah ya bani ikon tarbiyyantar
dasu"

"Zakk iya in sha Allah......am by your side.......na tsaya miki akan komai
sabreen,na tsaya miki,duk wani kalar jin dadi kulawa da riritawa kikeso....duk wani
kalar rayuwa ko kalan abu da kikeso a rayuwa umarni kawai zakiyi yazo
gareki......kaman yaddana taba yowa kaina alqawari saina cikashi in sha
Allah.....zan maida matata ta zama sarauniya cikin mata....zan sakata da kanta ta
dinga jin ita din ta dabance a cikin mata....zata zama wata gimbiya tauraruwa me
haskawa.....shalelen mata wadda mata zasu dinga jin duk ita suka rako
duniya....komai mulkin mace dukiya ko nasabarta idan tazo inda kike zataji ta koma
tamkar baiwa a gabanki......abu uku zuwa hudu ne kawai nake buqata. Ki soni har
abada har Qarshen numfashi so na fisabilillahi.....wuya ko dadi kar ya zama silar
rabuwarmu.

"Na biyu kiyita haifamin yara kina basu tarbiyya,sahihiyar tarbiyya data dace da
addini."

"Na uku ki bani kulawa.....idan zai yuwu ki fifitani sama da kowa harda yaran da
zamu haifa ma". Wannan gabar sai data sakata sakin dariya.

"Daddyn yara yada haka?" Sassanyan Murmushi daya qara masa kwarjini da kyau ya
saki,kafin ya bata amsa wannan karon sai daya jawota jikinsa suna iya jin hucin
numfashin juna.

"Saboda shi daddyn yafi yaran son mamar tasu.....sannan shi daddyn yafi yaran sanin
tsadarta da kuma darajarta......abu na qarshe shine ki tsaremin kanki.....ki
tabbata a matsayin DUNIYAR MUHAMMAD FU'AD JADDA har Qarshen rayuwarmu". Tun b'a je
ko ina ba da wannan kalaman nashi na qarshe ya qarasa tashin kanta. Tun ba'aje kuma
ko ina ba ta dinga jin kaman zata narke da wata irin soyayya da qauna me tarin
yawa. Tun a nan wajen tasan tabbas tayi sa'ar miji.....an haifota cikin
sa'a.....kalar sa'ar da sai mace me tsananin sa'a take samunta.

Baya yaja kadan,yasa hannuwansa yana gyaggyara mata lafayar jikinta.

"Banaso ko ina ya fito.....komai nawa ne.....you're mine and only mine,all rights
reserved".

"Kowa ma ya sani.....basai ka yita maimaitawa ba yallabai" Muryar farouq ta sauka
daga bayansa.

Baiko waiwaya ba,kaman ma bai fahimci farouq dinne ba yaci gaba da gyara
mata lullubin,a nutse yace.

"Har yanzu ba zaka daina yimin kutse ba kenan farouqu.....wannan....." Bai qarasa
ba saboda idanun da sabreen ke juya masa tana masa nuni da bayansa. Da ido shima ya
tambayeta,tayi qasa da muryarta kamar me rada.

"Like kaman shi da fannah ne hamma" Shuru ya danyi sannan ya dage girarsa yana
sauketa,yaja da baya daga gabanta sannan ya waiwaya.

Fannah dince,tana a gefensa kanta a qasa,kunya kaman zai kasheta.
Tasha labarun soyayyar sabreen da dude enshi,amma bata dauka haka sukejin DUNIYOYIN
nasu daga su saisu ba sai a yau din. Tun daga nesa data hangi yadda guard dinsa
sukayi musu qawanya take mamaki,ta dauka zallar tsaro ne suke bashi,ashe su suna
qarfafa tsinkar fule da fulawar da akeyi ne daga tsakiya. Abun ya bala'in
burgeta,sun kasheta sun kuma tashi kanta,har ta dinga murmushi duk da kunya da
nauyin FU'AD da take danji,don yana mata kwarjini sosai.

"Qaton banza......ka taho da diyar mutane amma ba zakamin magana ba?" FU'AD ya fada
yana hade girar sama data qasa shi a dole babba. Fannah ta qwaci farouq da dariya
ta hanashi bashi amsa.

"Barka da yamma hamma". Qasan ranta tana mamaki dama yana taba barkwanci haka?,idan
kaga face nashi a news ko a news paper ko a wani taro na kasuwanci ba zaka dauka
yana murmushi bama bare akai ga barkwanci,kaman bashi ba.

"Barka kade amarya.....ya baqunta da sabon guri?" Ya fada cikin kulawa da
girmamawa.

"Alhamdulilah hamma....yame jiki?,Allah ya qara lafiya yasa kaffara ne" Fannah ta
hada duka ta fada don kwarjininsa ya mata yawa.

"Ameen" Ya furta yana jin kalmar kaffara din data fada tayi daidai da a roqawa
maamah ita din.

Gaba yayi suna jerawa da farouq bayan fannah ta qarasa wajen sabreen
suka jera suma suna gaisawa. Karon farko kenan da suka fara ganin juna face to
face,saidai kowaccensu yanayin nutsuwar dayar tayi mata.

"Ayi mana afuwa,bamu samu haduwa ba,yanayin yazo da ciwon boss,ba daman nayi nisan
zango na barshi,sai yau Allah yayi muka hadu" Sabreen ta fadi tana dan murmushi.

"Aiba komai.....ana tare ai,shekaru masu yawa a gaba muna fatan hakan,yana da kyau
a kula da boss sosai ai.....kema kuma dole ki rage zirga zirga ai saboda naki
yanayin" Fannah ta fada tana murmushi. Mamaki yadan kama sabreen,wai cikinta ya
soma fitowa ne?duk da fannah din midwifery ta karanta dama,saita dora hannunta
saman cikinta.

"Cikin 'yan uku daban yake ai adda.....sauri girmansa da kuma yawan satittikan da
yake dauka a haifeshi,baya kaiwa dadewar cikin twins ko single baby" Ta fada da
muryarta maras hayaniya. Kai sabreen ta girgiza,bayanin na fannah ya gamsar da
ita,ta kuma fahimta,da alama kuma zata amfana da ita sosai.

A hankali suke takowa shida farouq din suna tattaunawa.

"Mun jima a asibitin,gida zamu wuce.......amma kunyi cikakken magana da likitan da
yake ganinta?" Farouq ya tambaya da dan alamun damuwa kan fuskarsa.

"Banganshi ba.....bansan wanne likita ke ganinta ba.....sai yau na samu shigowa
asibitin".

" Why?" Farouq ya tambayeshi yana nuna rashin jin dadinsa,duk kuwa da cewa yasan
komai,saidai muddin dai maamah tana raye....muddin dai maamah din sunanta
mahaifiyarsu ko sau daya bayajin akwai Randa zaice yayi mata wani rashin kirki ko
me tayi.

"Farouq.....Allah ne ya kiyayeni......da taimakon Allah da taimakon sabreen,banda
hakan nima da tuni yanzu ina nan inata checking BP na......saura kadan jinina ya
hau,ciwo zuciyata ta dinga yi,banda dauki da Allah ya kawomin na bani mace ta
gari......hutawa nayi na kwana uku farouq,bansan da wanne fuska zan kalleku ba kuda
anni.....mahaifiyata ta zama silar da saura kadan anni ta rasa diyarta......wannan
sakayyar ya kamata ta samu ta bangarenmu?" Ya qarashe maganan da alamun abun yana
masa mugun d'aci.

"Dude.....na taba zaginka?.....inajin zan fara wannan karon" Farouq ya fada ba tare
daya dubi FU'AD ba.

"Ashe har akwai banbanci tsakaninmu da ku?,ashe har akwai abinda zamu yiwa anni ta
tsanemu kenan indai zata tsaneku ko.taji haushinku akan abinda baku kuka aikata
ba.....ka saka a ranka ma tun wuri ka sake gayawa kanka cewa....ni dakai mahaifa
daya muka kwanta aka haifomu tare,kaman yadda musaddiq da saddiq suka kwanta
mahaifa daya aka haifosu tare......har abada ba wani banbanci". Shuru kawai FU'AD
yayi,har abada baisan da meye zaiwa wadannan bayin Allah sakayya ba.

"Ya kamata ka duba yanayin jikin nan nata da kyau,anni nata yimin fada tun
jiya......ina ganin ma kamar qasar ya kamata a fidda ita....saidai kaje zaka
gani,hawan jini yayi mata mummunar kayarwa" Ya qarasa fada da sautin jimami a
muryarsa. Kai ya kada yana nazarin abun,hawan jinin da baida labarin sadda ta
sameshi,ya sake kada kai yana tuna wata kalma data taba fadawa abbansu randa ya
dawo result din kamuwa da hawan jini.

"Kadanma ka gani......shi talauci in gaya maka idan ya samu ciwo yaga gurin zama
kenan....duk talaka da hawan jini yake qarewa,kaga somi somin daukan hanyar mutuwa
kenan,ciwon qoda,hanta,zuciya,lalacewar hanji duka daga hawan jini yake
farawa......bari na fara tanadi don kaina" Tayi maganar tana miqewa abinta ta barsu
a dakin da takardarsa da magungunansa a leda.

Bai amsawa farouq ba,illa wani nannauyan numfashi daya sauke bayan ya
gama tuna wannan,sai shima farouq din bai sake cewa komai ba. Ya sanshi,a dabi'arsa
ba komai yake baka amsa ba,idan kuma kaga bai baka amsar ba to lallai baka da
buqatar bada amsar ne.

Dab da zasu shiga reception na asibitin da zai sadasu da sassan
asibitin,sanda guard dinsa ke clearing masa hanya ya tambayi farouq.

"Inasu saddiq?" Harara ya balla masa.

"Zama zasuyi jiranka?,kwanan amna daya a asibiti abba yace kowa ya dauki matarsa su
wuce gida". Ido yadan fitar.

"Me yasa abba bai bari amna jikinta yayi qwari ba?" Ido farouq ya zuba masa sannan
ya bushe da dariyar mamaki.

"Kana tsoron kada ayiwa qanwarka abinda ka yiwa diyar mutane ko?,to abba yace ta
qarasa warkewa a dakinta..
..kaga malam ka barshi shima ya shana......wannan lamari baya buqatar shamaki ko
shishshigi fa" Farouq ya fada yana dan shafa gemunsa cikin nishadi. Dunqule hannu
FU'AD yayi yakai masa duka

"Sai yanzu kasan haka kenan?"

"Fes kuwa" Ya amsashi yana dariya. Mur FU'AD yasha ganin su sabreen sun kusa da
inda suke,farouq kuma yaja tunga.

"Wucewa zamuyi gida.....zamuzo muku ziyara once kafin mu wuce honeymoon" Ya fada
cikin salon tsokana yana bawa FU'AD hannu.

"Sai kunzo....Allah yasa muma ku samemu" Ya amsa masa yana bagararwa.

"Iyeeee.....lallai mutumin nan.....baku gaji ba?"

"Kai ka sani" FU'AD ya fada yana danne murmushin daya taso masa.

Tsayata yayi a bakin qofar amenity din,suka gama sallama da
fannah,sukayi exchanging phone numbers sannan ta tako ta sameshi. Hannunsa ya sanya
cikin nata ya riqe gam kamar wadda za'a qwacewa ita,har sai data daga idanunta ta
kalleshi suka hada idanu,idonsa ya dauke,sai mamaki kadan ya kamata,kaman ya manta
gaban surukarta maras lafiya zasu shiga?,bazaiyi alkunya tafin hannunsa cikin nata
ba,ta bishi kawai yana tura qofar gami da sanya qafarsa a ciki.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 153


*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽

*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*

*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*πŸ˜‚πŸ˜‚

Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*

*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*

*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin
aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ
wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN

08103155915



153


Har yanzu da take zaune saman wheel chair din bata daina qoqarin motsa
kowacce gaba ta jikinta ba,duk da hakan baida wani amfani ko qanqani a tattare da
ita,kaman yadda bai kawo wani ci gaba a yanayin da takejin jikinta ba. Ta sake
tattara duk qarfinta a karo na babu adadi don ta samu koda bakinta ne ta motsa tayi
magana,amma kamar dai mintunan da suka shude ko motsi bakin baiyi ba bare akai ga
fitar wani sauti.

"Innalillahi......na shiga uku!" Shine abinda ta furta cikin zuciyarta,don babu
damar yin magana a bayyane bare wani yaju furucin nata.

"Wai da gaske ne?,da gaske ne ni mariya?,bazan iya yiwa kaina komai ba?,da gaske ne
ni mariya bazan iya tafiya ba?,da gaske ne ni mariya bazan iya yin magana da kowa
ba bare a jini ko a fahimceni?" Tambayoyin kenan da suka cika mata kwanya da qirji
tsahon kwanaki ukun kenan,kuma bata da wani me iya jin tambayoyin bare ya amsa
mata.

Tun daga kwanaki ukun zuwa yau ko sau daya bataji ta gamsu ko ta nutsu
da maganganun likitocin ba da suketa maimaita maganar hawan jini ne wai ya kamata
ba. Tafi amincewa da cewa tabbas wannan abun daya sameta jifa ne......asiri ne
kawai akayi mata saboda kada taci arziqin d'anta. Mutum biyu take zargi,hajja
harira ko ameena hamza kibiya.

Duk duniya wadannan mutanen biyu bata da wani abokan adawa sama
dasu,bata da wani abokin takun saqa sama dasu. Duk da kuma tana zargin ameena
din,amma zargin nata yafi qarfi akan hajja.

"Na rantse da Allah na warke hajja bazaki sha ba.....ba zaki tsira ba....ko ke ko
ameena duk wanda yake da hannu cikin maida rayuwata abun tausayi cikin
qididdigaggun daqiqu" Taci alwashin cikin ranta tana jin wani abu yana tokare mata
a wuya me tsananin zafi.

Checking nata likitan yakeyi yana rubuta bayanan cikin folder dinta yana
hada mata da bayanai duk da yasan bawai zata iya bashi amsa bane,amma yasan tana ji
tana kuma fahimta,maidawar ne ba zata iya ba. Duk abinda yake fadi sam bata bashi
hankalinta bama bare ta tantance ma'anarsa,a nata ganin maganin warware sihiri tafi
buqata fiye da wadannan tarkacen na'urorin da aka zube mata aka. Tayi imani ba wani
hawan jini daya sameta,kawai komai da akeyi din wani bata lokaci ne na daban,tunda
ko hanyar bakin zaren bata ganin alamun daukoshi.

Kaman kowanne kebantaccen dakin asibiti me cike da tsari shima haka yake.
Gadaje guda biyu qananun sofas guda uku da plastic chairs guda biyu suma.

Yadda idanunsu suka sauka a kanta haka itama idanunta suka sauka a
kansu. Wani zazzafan abu ya taso ya lullube mata zuciya.

Sosai ta kafe sabreen da idanu tana dubanta ba tare data dauke dubanta
daga kanta ba ko na second guda. Ita kadai tasan me takeji akan yarinyar......tana
kallonta a matsayin silar komai.....tana dubanta a matsayin wadda ta assasa mata
dukkan wata musiba da take ciki. Gaba daya maganganu akanta da boka ya gaya mata
suka fara dawo mata d'aya bayan d'aya.

"KINYI KUSKURE!" Kalmar farko da ya fadi mata kenan a kanta,ashe tabbas da
gaskiyarsa......da gaske yake kuskuren tayi.....to amma koma meye wannan kuskuren
zata tabbatar ta maidashi kansu muddin lokaci da dama suka sake waiwayarta.

Abubuwa ne da yawa suke yawo a zucoyarsa da idanuwansa sanda suka iso
gabanta. Kallon da take binsu dashi tana raba idanunta tsakanin fuskarsa da tata
kadai ya gaya masa komai. Akwai maganganu masu yawa saman harshenta,akwai saqonni
masu nauyi cikin zuciyarta wanda dama bata bata daman furtasu ba......saidai duk
wani yanayi nata.....duk wani motsi nata karantaccen abune a wajensa da koda da
idanu tayi magana zai wahala ya gaza fahimta.

"Sannu" Ya furta mata yana dubanta. Ido ta lumshe sannan ta budesu,qwaqwalwarta na
dawo mata da haduwarsu ta qarshe. Maganganunsa da sam basuyi mata ciwo ba kaman
yadda babbar damar daya bata ta kubce mata tayi mata ciwo......wata irin gagarumar
dama da bata tunanin zuwanta da subucewarta haka lokaci guda ba.

"Barka da zuwa sir" Likitan ya fada cikin girmamawa.

Waiwayawa fu'ad yayi ya kalleshi.

"Yauwa sannu da qoqari" Ya fadi yana jawo kujera gaban gadon maamahn.

Sabreen ya waiwaya ya kalla sannan ya kalli kujerar.

"Zoki zauna" Ya fada cikin nuna kulawa. Nauyi abun yayi mata,sai takejin kamar
idanuwa ne da yawa a kansu. A darare ta matso tana tsarkake sunan Allah ta
zauna,tasbihin da tunda ta shigo dakin takeyinsa da kallo daya data yiwa maamah.
Tsaf kamannin maamah din suyi wani irin juyewa,qasa da awa saba'in da hudu
kacal?,iya wannan ya ishi bawa girmamawa ga ubangijinsa da kuma sallamawa
lamarinsa. Tsoron Allah taji yana sake shigarta,wani bangare na tausayin maamah din
ya karyo mata.

"Sannu.....ya jikin?,Allah ya mayar kaffara" Ta furta a hankali tana son karantar
yanayin kallon maamah din a kanta.

Kafe sabreen din tayi da idanuwa,tana jin wannan dubiyar da addu'ar
gaba daya akwai isgili a cikinta. Akwai maganganu masu yawa data jima tana tanadin
gaya mata,akwai maganganun data tanada saboda rana irin wannan.....ranar sa sabreen
din zata tona mata asiri,ta kuma yaye lullubin sirrin dake tsakaninsu wa
fu'ad......a ranar ta tanadi abubuwan fada masu yawan gaske a kanta. Saidai kuma
ranar tazo mata da wani babban akasi......akasin da babu daman cewa komai
gareta,sai kallo da da idanu,dukkan wasu kalmomi nata suna mata kai kawo tsakanin
qirjinta da wuyanta amma fitarsu ya zame mata wani jan aiki.

Kallon fuskar sabreen din kadai wani gagarumin baqinciki yake ajiye
mata,saidai sanda ta dauke idanun nata da zummar kauda kanta sai suka fada kan dan
matashin cikin dake kwance a jikinta wanda batasan sanda har ya fara bayyana kansa
ba.

Kulle idanun nata tayi tana jin yadda bacin rai yake hautsinewa a
qirjinta yana kuma bin kowanne sashe da jini ke gudanar mata yana aike mata da saqo
kowanne sashe na jikinta. Batajin zata iya ci gaba da kallonta zaune haka a
gabanta,inda tana da baki da zata gaya mata cewa ta tashi ta matsa daga gabanta
ne,amma bata da wannan damar yanzu haka banda ta kulle idanun.

Sallamar da aka sakeyi ita ta tilasta mata sake bude idanun nata.
Musaddiq ne a gaba,amna na biye dashi a baya sanye da baqar abaya data fito da
hasken amarcinta da kyau,duk kuwa da 'yar rama kadan dake tattare da ita. Kallo
daya tak zakayi mata ka karanci a tsorace take,tana daga bayan musaddiq din,duk
inda ya tsoma qafarsa ya dauke nan yake ajiye tata. Hannunta riqe da nashi hannun
daya bar mata shi ta baya a haka suka shigo.

Kan hannun nasu idanunta suka fara sauka,wannan karon yunqurin miqewa
tsaye tayi ta gwada tata jarumtar na UWA kuma wai MAHAIFIYA,saidai kuma
kash......ba wani abu nata daya motsa balle akai ga batun tashin. Gumi sosai ya
dinga karyo mata saboda abinda takeji a zucoyarta,bala'i da masifa ne fal idanu da
zuciyarta,donme musaddiq din zai debo mata diyar alhaji hamzan yazo mata da
ita?,auren da sukayi kadai bai ishesu ba?,har sai sun qara qunsa mata baqincikin
ganin kasantuwarsu a tare?.

"Akwai buqatar ki saka nutsuwa da kauda duk wani bacin rai daga zuciyarki don a
samu a ceto lafiyarki yadda ya kamata" Likitan ya furta yana dubanta,gumin dake
fita a fuskarta kadai ya gaya mishi akwai wani abu daya motsa zuciyarta,duk da
baisan ainihin meye ba.

Tana labe a bayansa suka qarasa gabanta,ya gaidata gami da yi mata
sannu. Leqowa amna tayi daga bayansa tana mata sannu itama,suna hada idanu ta koma
bayan mijinta ta lafe. Ko kusa ko alama bata qaunar ganin matar,anni ce ta kirata
ba tare da sanin musaddiq din ba tayi yaqi da ita akan ta bishi idan zaije ta
dubata.

"Komai lalacewar tuwo ba'a sauya masa suna.....musaddiq baida wata uwa bayan
mariya,koda ya nuna miki baya sonta wannan wani yanayi ne ya kawo haka.....batun
abinda tayi miki kuma darajar addu'a bata samu galabar komai a kanki ba,sannan kuma
hakan ya zame mata wani sanadi ne na tonuwar kowanne sirri....kina tunanin ke kika
yiwa kanki haka?,ko kadan,darajar addu'a ce da duban zukata da Allah S W T yayi".
Wannan maganar ita ta sanya amna yin qundumbala ta biyoshi.

"Any progress?" Fu'ad ya tambaya yana duban likitan. Ajiyar zuciya kawai ya sauke
sannan yace.

"Idan zai yuwu muje muyi magana daga office ko?" Juyawa fu'ad yayi ya yiwa musaddiq
inkiya,shi kuma ya waiwaya yana duban amna. Muryarsa can qasa cikin sigar lallashi
ya fara magana.

"Calm down dear......ga adda sabreen ku zauna tare da maamah......ba abinda zai
sake faruwa,yanzun zamuje mu dawo.....okay?" Ya fadi yana dage mata dukka girarsa
gami da riqe fuskarta tsakanin hannuwansa. Kai ta gyada masa,sai ya sake mata
murmushi yaja da baya yana juyawa gami da bin bayan fu'ad. Saura kadan numfashinta
ya qwace mata,wani tashin hankali ya sake sauko mata.

"Shima musaddiq din haka yake?" Maamah ta tambayi kanta. Wani irin yanayi ne da
batasan musaddiq dashi ba,soyayya muraran da mace a gabanta?.....wacce irin baqar
rana ce wannan take gani?. Dukka yaranta guda biyu da iyasu ta mallaka a
duniya,kowannensu ya dulmiya cikin soyayyar wata diya macen daban ba ita ba?,wani
irin so me zurfin da bataga kwatankwacinsa a kanta ba a cikin idanunsu?.

Shuru dakin ya dauka,sabreen tayi qarfin halin sakin murmushi ta kalli
amna.

"Ga guri ki zauna amarya.....kada angonki yazo ya tuhumeni na bar masa me a tsaye"
Ta fadi tana ganin yadda amna din taqi sakewa. Ita kanta ta zama tamkar baquwa a
gurinta. Murmushi ta maida mata,ta tako a nutse ta samu gefan sabreen din ta zauna
tana qoqarin sakin fuskarta.
Ashar maamah keda muradin narka musu ganin suna hira qasa qasa a
gabanta amma bakin yaqi buduwa,game kula kuwa zaiga yadda idanunta suka kada sukayi
jajur,daga amna har sabreen ba wanda ya kula a cikinsu,don sabreen din nata qoqarin
jan amna da hirar da zata sakata sakin jiki.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


154


"Shekararta nawa tana fama da hawan jinin nan sir?" Likitan daya gaji da
ganin abun mamaki tsakanin kwanaki ukun ya tambayi fu'ad. Kafadunshi duka biyun ya
dage yana son gano dalilin tambayar.

"Ba wasu shekaru bane,idan ya dade wata daya....."

"Hamma duka baifi sati uku bafa" Musaddiq ya fadi yana duban fu'ad. Dauke dubansa
fu'ad yayi ya maida ga likitan alamun
"Kaji amsar tambayarka?".

Kai ya jinjina cikin matsanancin mamaki. Tunda yake kaf a tarihin
aikinsa bai taba ganin mutumin da jininsa yahau har haka kuma yake iya ci gaba da
rayuwa ba. Matakin hawan jininta yakai mataki na qarshe,wanda daga wannan stage din
saidai mutuwa bama stroke ba.....uwa uba kuma tun a kwanakin da aka kawota yake ta
qoqarin ganin jinin ya sauka amma yana nan a inda yake,ba wani ci gaba. Ya gwada
duk wata basira tashi da dabarun aiki amma abun ya cimma tura.

"Sir......munyi mata dukkan abinda ya dace amma ba wani ci gaba ko nasara koda
alamunta kuwa,abinda yafi bani mamaki shine......yadda hawan jinin yayi mata wata
mummunar rafkiya karo daya,nayi zaton tsohon ciwo ne ma,sa'annan duk wani hanya na
sauke jinin wallahi yaqi sauka,abinda yake dada bani tsoro shine,ci gaba da qin
saukar nasa zai iya zame mata sanadin matsaloli kala daban daban,don a yanzun haka
tsoro nake kaman qodarta tana son harbuwa,bansan me yake faruwa ba,nidai ban taba
cin karo da case me kama da nata ba tsahon shekarun dana dauka a bakin
aiki.......amma abinda nake tunani.......anya ba wani abu babba data sanya a
ranta?,ko wani goal da takeso ta cimma a rayuwarta?,wani matsala dake bata mata
rai?". Wani murmushin takaici ne ya qwacewa fu'ad,wanda tunda suka shigo office din
yana tsaye kawai hannayensa zube a aljihun wandonsa.

Likitan yayi tambaya a muhallinta,duk duniya shike da amsar wannan
tambayar tasa,saidai abune da bai shafeshi ba,koda ya shafeshi ma labarin zai zame
masa wani baqon labari da ko a duniyar hikayoyi bai taba jin irinsa ba. Uwa nason
mallakar d'a kota mallaki abinda ya mallaka kota halin qaqa?,uwa nason tarwatsa
rayuwar 'ya'yanta ta hanyar rabasu da abokan zamansu?......rabo na jikokinta dake
manne a mahaifar surukarta kuma fatanta yabi rariya?,BURIN UWA TARWATSA RAYUWAR
'YA'YANTA ta rabasu da uwa da uban goyonsu da suka zamewa rayuwarsu suttura?,wacce
irin uwa kenan wannan?,baya ga wasu boyayyun al'amura da fadinsu ma baida dadi koda
a baki ballantana ga kunnuwa?.

"Me take buqata?,me ya kamata ayi?" Ya yankewa likitan dogon tunani da zallar
mamakin daya fada

"Tana buqatar kulawa ta wurwuri......kulawa ta gaggawa saboda gudun rasa wasu
bangarori na jikinta,kamar idanunta kunnuwanta ko qoda ko kuma hanta".

"Yanzu me kake gani za'ayi?" Ya sake tambayar likitan,yana jin wani tsoron girman
Allah yana kamashi. Amsa kuwwar muryarta yakeji a shekarun baya yanzu haka.

"Shi hawan jini ai baka rabuwa dashi sai ya lalata maka ji gani qoda ko
hanta.......kai kam gaskiya kaman bakayi sa'ar rayuwar duniya ba?,daga wannan sai
wancan?" Tayi maganar tana tsaye a kan abban nasa sanda duniya tana tsaka dayi mata
zaqi da gard'i. A lokacin shi kuma yana tsugunne a gabansa yana qoqarin ballo masa
magungunansa saboda hakin daya sarqeshi ba qaqqautawa.

"Ina ganin me zai hana ku fita da ita waje?,suna da kayan aikin damu bamu dasu,zasu
sake bincikarta sosai ko akwai wani abun daban da yake jawo wannan matsalar
bayan......."

"Kayi magana da dukka asibitin daya dace ace an kaita din,ka tura adadin abinda
za'a buqata daga dawainiyar asibitin da komai ka sanarmin ta waya" Ya fada kawai a
gajarce.

Yana ji a

Please Login or Register in order to submit comment