You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin
cire shi daga depression daya samu kansa a ciki.

Tana shigowa ya miqe,bai barta ta qaraso ba ya isketa a hanya ya
karba tray din ya qaraso dashi. Sanda yake shan kunun a nutse yana kuma cin qosan
tana zaune a gabansa tana karantarsa,tana jin zuciyarta na matsewa,ta kuma damu
tayi masa maganar dake qasan ranta,duk da haka tayi jarumtar sanda ya kammala
sannan a tsanake tace dashi.

"Muhammadu...."

"Na'am anni" Ya amsa mata a nutse yana jin wata nutsuwa da qoshi na musamman yana
ratsa cikinsa.

"Nace anya yarinyar nan basai an taimaka mata da qarin masu aiki ba?,gidan nan sai
nakega ko masu aiki nawa aka zuba masa yana buqatarsu ko don sauqaqawa matar
gidan,duk da yake kai baka fiya son mu'amalar masu aiki ba cikin sha'aninka".
Murmushi kadan ya saki,baisan wanda a duniya ya sanshi sosai ya kuma karanceshi tas
sama da anni ba.

"Kiyi duk yadda ya dace anni......" Ya bata amsa cikin girmamawar data sake sanyata
ta jishi a ranta sosai.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 37


_Daga ibn juhaim bin haris RA(wannan sunan sahabin annabi neπŸ˜„),yace:Manzan Allah S
A W yace "da me wucewa ta gaban me sallah yasan abinda yake kansa na sabo,tabbas da
ya tsaya(ya jira me sallahn ya gama)tsahon gwargwadon shekara arba'in shine yafi
masa alkhairi akan ya wuce ta gabansa_

_Bukhari da muslim ne suka rawaito_




37


"Da ina tunanin na tura mata ma'u da maigidanta malam ibrahim.......zataji
dadin zama da ma'u sosai.....ina kyautata zaton haka,malam ibrahim kuwa koda kana
da ma'aikata da sauransu zakaji dadin zama dashi in sha Allah".

"Anni ki zartar da komai da kike ganin ya kamata......ba buqatar sai kin gayamin
anni" Ya sake fada har a zuciyarsa yana jin annin ta isa ta zartar da komai din.

Kai ta jinjina tana dan murmushi,har qasan ranta tana jin dadin yadda
ya bata girma da kuma dama,duk da cewa tasan cewa abune me wahala ya musanta akan
duk abinda tace din. Har bakin parlor na biyu tayi masa tattaki,bakin ta fal cike
da addu'ar data zame mata dole,kowacce rana dukkaninsu su hudun basa kaucewa samun
kyakkyawar addu'arta da bata gajiya da binsu da ita.

Qafarta daya saman daya take zaue cikin qawataccen parlor din nata da
idan ka kirashi kai taaye da aljannar duniya bakayi kuskure ba,duk da ita a nata
ganin sam har yanzu bai kai matsayin da take buri tsari da kuma mafarkin yakai ba.

Dukkan hankalinta ta baiwa zuwaira dake zayyane mata jawaban da
muhimmancinsu a wajenta ya wuce kimar komai data mallaka a duniya. Jawabin dake da
wani irin kima tamkar ta zinare a idanunta. Duk da bayanan ba abinda suke haifar
mata sai wani irin tashin hankali. ba irin bayanan da take buqatar taji kenan
ba.....amma duk da haka suna da muhimmanci a wajenta,don sune zasu zame mata tamkar
tsani kuma fitilar da zata haska mata matakalar da zata taka zuwa matakin gaba.

"Amma fa tana qoqarin ganin ta aiwatar da aikinta......saidai ban hangi wata
shaquwa soyayya ko kusanci da junansu ba ko kadan"

"Wannan kuma aikinta ne......ita kuma ya kamata ace ta fara samar da wannan
dangantakar a tsakaninsu......a nan gazawar tata ta fito.....ta kowacce hanya ya
kamata ta yaudari zuciyarsa har ya aminta da ita ya miqa mata wuya.......aikinki
yana kyau zuwaira,ina buqatar magana da ita yanzun nan kafin na yiwa tufkar hanci
tun daga tushiya"

"Yanzun zan sadaki da ita uwar dakina" Zuwaira ta fada cikin karsashi gami da jin
dadin lambar yabon data samu.

Batasan adadin sau nawa ta duba agogo ba tana zaman jira da dakon
kiran zuwaira. Qaguwar da tayi ya hanata jira zuwairan ta kirata ta maida kiran
zuwa wayarta.

Ya shiga a daidai kuwa,sanda take rusune daga bakin bedroom din
sabreen tana qoqarin fahimtar da ita amfanin kiran.

"Ina jinki kamar d'iyata ko jikata....ki daure ki saurareta,taqi kadan zai rage ku
rabu in sha Allah". Duk bata gamsu da matar ba,duk da batajin nutsuwa da matar ko
kalamanta,amma a ciki akwai abinda takejin gaskiya ne,a ciki akwai abinda takejin
da gaske ya kusa tabbata din TAQI KADAN YA RAGE SU RABU.

Hannu ta saka ta karbi wayar,sai ta tura qofar bedroom din ta rufe ta
koma ciki. Tana takawa cikin idanunta suna kan fuskar wayar,yau din a matuqar
tunzure take,so batason wani magana da zata sake hasala hali da kuma yanayin da
take ciki.

Gaban madubinta taja stool ta zauna,sannan ta kunna wayar ta sakata a
hands free ta dorata saman madubin,sannan kuma a hankali ta maida idanunta saman
fuskarta kamar me kallon maamah din zaune a gabanta.

"Ina jinki" Ta furta a nutse yana goye hannuwanta a qirjinta.

"Ina fata kina cikin lafiya da kuma aminci qarqashin kulawar d'ana?" Tayi maganar a
nutse tana son kamo bakin zaren ainihin maganarsu. Kamar ba zata amsa mata ba,sai
ta daga idanunta daga kallon dogayen yatsunta da gaba daya lallen da akayi mata na
aure ya fice tas,tamkar ma ba'a taba digawa yatsunta lalle ba,ta maida oily eyes
din nata cikin madubin daya bayyanar da fuskarta dinnan me shimfidadden kyau dake
dauke yau din da wani irin kwantaccen fushi. Zubawa fuskar tata idanu tayi kamar
yau ta fara ganin kanta da kanta,iya kallon kawai yana motsa zuciyarta gami da tuna
mata a karan kanta wacece sabreen,wani sashe na zuciyarta ya motsa yayi aikin daya
jima baiyi ba,taji wani abu ya darsu a zuciyarta wanda ta jima tana yunqurin
daddago dashi amma yana komawa
"Ki ajiye wannan a gefe.....yaya jikin huda?" Tayi mata tambayar da take kwana da
ita tana tashi ba tare da tasan waye zata yiwa ita ya kuma basu cikikkiyar amsar da
take buqata ba.

"Jikin huda?.....alhamdulillah......saidai ban da tabbacin yadda ya kamata ya
kasance". A hankali ta lumshe idonta tana son yiwa amsar tambayar tata fashin baqi.
Bugun zuciyarta yana son ninka gudunsa saboda samun mabanbantan amsoshi daga
mabanbantan lunguna da saquna na zuciyartata wadanda basuyi daidai da fatanta dama
abinda takeso taji ba.

"Mu ajiye wannan......zan dan yaba miki game da yadd kike qoqarin ciyar dashi
abinda muka baki,saidai har yanzu kin gaza cimma manufar abinda kikeyi
din......caring kulawa.....ba wata halitta da batasan kulawa.....dole ki fara samun
zuciyarsa kafin ki samu cikinsa da jikinsa....."

".......ba wannan cikin jarjejeniyarmu.......wai shin..kina zaton ina da buqatar
zuciyarsa?,ko ina da buqatar hanyar da zata sadar dani ga shiga zuciyarsa?". Tayi
maganar kanta tsaye da wani irin tsauri,saboda zafi da a yau zuciyarta keyi
mata,tana jin kamar wani abu me kama da gajiya da kuma fara jin takura yana
mintsinin zuciyarta.

Murmushi me sauti maamah din ta saki tana gyara zamanta

"Bana fatan ki samu zama ko shiga zuciyarsa na dindindin,a taqaicema dai....banda
yanayi irin na lalura banjin kinkai quality din da zan baki license na shiga
zuciyar mutum me tsada,namiji irin muhammadu ba.....amma karki manta,dole ne ki
sadaukar masa da komai don isa ga burinmu.....idan nace komai ina nufin komai da
komai fa,na zabeki ne saboda ina da tsammanin zaki iya bada komai don cikar
muradina.....koda kuwa jikinki ne...."

"Ya isa!" Ta furta a tsawace saboda jin maganar tata ta fara shallake guri,uwa uba
tana neman fin qarfin kanta.

"Kibi a hankali......a yanzun duk da ban mallakeshi ba,amma zakisha mamakin abinda
zai biyo baya idan har na shaida masa matarsa tana min shouting tana kuma dagamin
murya....." Zafin radadin maganarta ta farko bata saketa ba,don haka bata maida
hankali sosai akan maganarta ta biyu ba. Burinta shine ta furzar mata da abinda
yake ranta,tana jin kamar takai maqurar da zasu dinga wasan tamaula da ita tsakanin
ita da d'anta.

"Zanci gaba da ci dashi kaman yadda iya abinda yake zayyane kenan a bisa
yarjejeniyarmu......daga hakan banajin zan qara akan komai.....faduwarki ko
nasararki ya ta'allaqa ne da yadda na samu tabbacin lafiyar qannena" Daga haka ta
katse wayar kawai tana ajeta a gefe.

Taso tayi tariyar maganganun da sukayi da maamah din,amma a yau sai
taji gaba daya bata da buqatar tuna komai.....kawai tana jin ba zata iya ci gaba da
zamowa kamar tamaula tsakanin su ba. Wani irin confidence takeji,saita miqe tana
komawa bakin qofar da zummar ajewa zuwaira wayarta,ta dauka duk sanda ta dawo,don
ko haduwa da ita bata sonyi. Ga mamakinta a tsaye ta sameta a bakin qofar kamar
wadda aka bawa gadinta. Wani kallo ta jefeta dashi tana jin sam matar bata mata ba

"Ba wani abu da ake buqata?" Ta fada da sauri bayan ta karbi wayar ganin sabreen
din na zummar shigewa ciki

"Babu" Ta bata amsa a taqaice tana maida qofarta ta kulle.

Yadda yau yarinyar ke amsa mata magana a tsaitsaye sai takejin kamar
akwai abinda ta taka,akwai abinda ya bata confidence a kanta. Ci gaba tayi da juya
wayar a hannunta tunaninta yana yin nisa gami da rarrabuwa kashi kashi. Wani
tunani ya kutso mata cikin kwanyarta

"Me yasa ba zaki murza kambunki ba?,ki gwada qarfin iko da mulkinki ba har akan
fu'ad din?" Wani sashen na zuciyarta ya bata shawara. Shuru tayi tana sauraren daya
bangaren tare da juyar maganar cikin kwanyarta. Kai ta gyada tana bawa kanta
tabbacin tabbas wannan din zaiyi aiki.....koda baiyi diki dari bisa dari ba to
akwai yiwuwar samuwar galaba.

Tana qoqarin kiransa ta shaida masa tana buqatar ganinsa sallamarsa
ta mamayeta. Tana amsa sallamar farinciki na cika zuciyarta yadda Allah ya dubeta
ya jefo mata shi,saidai a saman fuskarta ba haka bane. Ranta yana hade,hakanan ta
boye duk farincikinta don tanason ko meye zata gaya masa ya daukeshi da muhimmanci.

Sai daya iso gabanta ya zame yana gaidata ta hanyar tsugunawa saman
qafafunta. Bayan ya gama gaidata din shuru ya biyo baya,a nutse yace

"Ba komai da ake buqata?,ba wani matsala?" Yayi tambayar data zame masa wajib duk
sanda yazo gaidatan don qoqarin sauke haqqin Allah da yakejin ya zama wajibi ya
sauke din.

Kai ta girgiza fuskarta a daure.

"Ba abind nake buqata.....amma matsala dai akwaita". Daidaita tsugunnonsa yayi
kafin ya zame ya zauna sosai a gabanta. Duk sanda tayi wannan yanayin kota furta
magana makamanciyar wannan zai wahala idan ba wani aikin bane zaya zameshi.
Idanunsa yadan lumshe gami da budesu duka lokaci guda cikin qoqarin hadiye
fargabarsa,yana tunkarar qalubale komai girmansa.....gaagwarmaya komai wahala da
kuma taurinta,amma har yanzu zuciyarsa baya iya jure wadannan halayen da maamah
din,dabi'unta suna kassarashi,ya kasa sabawa,baisan me yasa ba,ko don ita dinn wata
jigo ce da abubuwanta ke tafiya ba yadda ya kamata ace sun tafi ba?.

"Wacce matsala ce?,me yake faruwa?" Ya tambayeta a nutse.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 38


_Daga abi sa'eed RA yace:manzan Allah S A W yace; "idan dayanku yazo masallaci,ya
duba takalminsa,idan akwai qazanta ya shareta ya kawar da ita daga jiki,yayi sallah
da takalminsa_

*_halal ne sallah da takalmi a qafa,na haramci a ciki muddin ba najasa a jiki_*


38
"Muhammadu" Ta kirashi da ainihin sunansa,ba tare kuma data bari ya amsa ba ta dora

"Nikam bansan a rayuwa akwai wani abu da yafi haihuwarku da nayi muhimmanci ba"
Idanu ya zuba mata yana jin tamkar ya tashi ya fita da gudu ya tserewa
maganganunta,don yasan zai wahala ba kamar kullum bane,dora masa nauyi da
mas'uliyyar da zai gaza dauka kota masa tauri. Kai ya girgiza,ya buda baki zai
magana ta sake danneshi da kalamanta

"Bansan wanne irin rashin muhimmanci nake dashi a rayuwarku ba da har zan zartar da
hukunci cikin rayuwarka,nace kum ga alfarma ko abinda nakeso kayimin ka gaza yi
din,ace har yanzu maganganun ameenatu da umarninta yana zama gaba da nawa?" Ta
qarashe maganar tana jin dacin haka sosai har cikin zuciyarta. Batasan wanne
tozarci ma ya kamata ameenatu ta fuskanta ba aduk sanda haqanta ya cimma ruwa,har
yanzu idan tayi hasashen abinda zata saka ta fuskanta sai taga wannan hukuncin yayi
kadan.

Sam baya qaunar ta dinga sanyo maganar anni cikin maganganu da
ayyukansu,don bazai iya tuna sanda anni ita tayi magana a kanta ba indai ba
alkhairi ba.

"Muhammadu.......yanzu ni da hannuna na baka amanar yarinyar mutane......na roqeka
ka mu'amalanceta kamar kowanne miji da mata.......ka kyautata mata ma faranta
mata,ka jata a jiki amma haka ga gagara?,ka kasa cikamin wannan alfarmar da zata
bayya a irin kima da martabata a idon yarinyar?". Qasa yayi da kansa,shi maganar ma
nauyi tayi masa sosai akai. Ta wani gefen kuma ranshi da zuciyarsa suma motsa.
Yanzu har taurin kan yarinyar da tsaurin idonta yakai ace ta kawo ma maamah
qararsa?,har da maganganu irin wadannan marasa dadin ji?. Sai data gama dukkan wani
fada baice komai ba,har sai da tayi shuru sannan yace

"Kiyi haquri,in sha Allah za'a sake yin qoqarin gyarawa da canzawa". Ya furta a
taqaice. Har cikin ranta yadda ya amsa mata haka a sauqaqe ya faranta mata sosai

"To Allah yayi albarka" Ta fadi kalmar da bazaice when last da yaji ta fada ba.
Muryarsa a sanyaye ya amsa mata,sannan ya miqe yana mata sallama yana fita daga
falon.

Tun kafin ya qaraso Jordan ya wangale masa qofa,da wani irin zafi ya
isa ya shige motar Jordan ya maida murfin motar ya rufe. Suit dinsa na sama ya fara
ballewa yana zareta daga jikinsa saboda wani irin zafi da yakeji tun daga zuciyarsa
har cikin fuskarsa. Iske me qarfi ya fesar daga bakinsa bayan ya zuqi wata

"Wanne abune meqarfi da girma a tsakaninsu bayan wannan?" Ya jefawa kansa da kansa
tambayar yana motsa labbansa.

"Ita ta shiga jikin maamah ko maamah ce ta shiga jikinta?" Ya sake maimaita
tambayar da ba wanda zai iya bashi amsarta. Yanzun har matsayinta da girmanta wajen
maamah yakai ya samu sanyawar albarkar maamah din saboda dalilinta?,wanne aiki take
mata haka me faranta rai bayan abinda yake suspecting?. Tunanin daya rakashi kenan
har cikin office dinsa,ya kuma wuni yana tayashi zama,duk kuwa da uban tarin
ayyukan daya samu suna jiransa. Duba documents da sanya hannu cikin wasu
takardun,wasu takardun suna da buqatar hankalinsa da nutsuwarsa kafin yakai ga
sanya hannu,da qyar ya hada hankalinsa bayan sallar la'asar ya soma duba
wasun,bayan ya yiwa kansa matsayar matakin da zai dauka.

Komawa tayi ta sake kwanciya bayan sallar la'asar din,tana lissafin
nan da awa daya koda rabi zata shiga kitchen saboda shi.....saboda mutumin da ba
ganin girma qima ko martaba sam sam tsakaninsu. Idanunta ta runtse,a yau tana jin
wani zafi zafi na yadda maamah ta bautar da ita. Batasan me yake tilastata lallai
saita yi sai kuma ta cika muradin maamah din ba. Tsaki taja tana bude idanun
nata,sai suka fada saman gift din da anni ta bata ranar da suka je.

Dan murmushi ta saki qasan zuciyarta,matar ta kwanta mata a rai,tana
da wani irin calmness me taba zuciya nutsuwa da kuma wani irin kwarjini. Tashi tayi
tsam ta daukosu ta dawo ta zauna saman abun sallarta data tashi ta soma budewa tana
tuna fuskar matar da takejin kamar ta taba ganinta a wani wajen kafin yanzu.

Littafin farko ta dauka daya qunshi addu'o'i akan kowanne
abu,harkokinmu na yau da kullum. Shafin farko ta bude,sai ta dinga tuna zamanin da
ummensu ke raye,Lokacin da take tsaye a kansu kai da fata,ba batun fashin islamiyya
ko wani abu da yayi kama da wannan. A duk dare itace malamarsu,zata zauna a
tsakiyarsu saita tabbatar kowanne karatunsa ya zaunar masa akai,musamman karatun
addini da a nan tafi qarfi,na bokon tafi jiran abbansu idan ya dawo,musamman idan
ya zamana itace da girki,idan ba ita bace dole saita dauki uzuri an bata lokaci.

Hannu tasa ta shafi addu'ar farko da sam ta mantata cikin
rayuwarta,ummensu itace ta fara koya mata ita tana kuma iya tuna lokacin har
yanzu,sai ta tashi ta koma saman sofa ta zame kadan tana bin addu'o'in daya bayan
daya tana dubawa suna kuma sake tuno mata da kansu.

Sosai takejin dadin karatun,don ya debe mata kewa me yawan gaske.
Babu zato daga saman kanta din,daidai wata kyakkyawar qaramin luxury stand taji
qaraurawa tana kadawa. Zubawa wajen ido tayi,wata mulmulalliyar na'ura ce da take
zubi da telephone. Tunawa tayi amna ta taba dagawa tayi kira zuwa parlor sanda
sukazo,sai a sannan ta tuna na'urar sadarwa ce da aka shiryata duka gidan da kuma
tsakanin dakunan gidan har zuwa Kutchen,wannan ya bata qwarin gwiwar saka hannu ta
daga ta sanya a kunnenta.

"Ranki ya dade......malamarki ce tazo,sabuwar malamar da yallabai ya daukar Miki
saboda karatun yamma".

"Malama kuma?" Ta tambayi kanta da kanta cikin tsananin mamaki tana son tuna yaushe
sukayi wannan maganar da shi?.
"Duk cikin salon da zai miki mugunta ya cusguna miki ne kaman yadda ya dauki
alwashi". Ido ta lumshe tana budesu sannan a nutse tace mata

"Ki sallameta zuwaira......ko kuma ta jira wanda ya tattagota din" Daga nan ta kife
wayar tana komawa ta zauna qirjinta a quntace.

Wannan abun da yayi me yake nufi kenan?,ita din jahila ce?,ko batasan
komai ba saishi zai sanya a karanta mata?. Wannan tunanin ya tsaidata,sai data gama
baqin ran da bacin ran sabon salon wulaqanta mutum daya bullo dashi......hakanan ba
don taso ba ta miqe tana wucewa kitchen.

Tana shiga zuwaira na fadowa,sai ta waiwayo tana kallonta. Cikin
jikinta wani abu ya bata,ta yaya duk wani motsinta zuwairan kamar tana biye dashi
ne?

"Ranki ya dade dame za'a taimaka miki dashi?" A nutse ta juya kawai ta fara aikin
gabanta,kamar ba zata amsa mata ba sai kuma ta tura mata lettuce da cabbage carrot
da peas tace ta gyara ta yanka mata.

Zaman kurame kawai sukeyi cikin kitchen din,zuwaira nata satar
kallonta tana son ta dan tabota da magana don ta gina alaqar sabo a tsakaninsu amma
bataga wannan fuskar ba sam

"Tashin hankali" Zuwairan ta fada qasa qasa,daga ita har mijin haka fuskokinsu suke
kamar na shanu? Ta tambayi kanta,ita dai har yanzu bata taba ganin fara'a ko
dariyar dayansu ba.

Sai da suka kammala komai sannan ta fidda magungunan zata cakuda
kaman yadda ta saba. Ta bude murfin ta karkata gorar,sai kuma ta tsaya cak. A
hankali ta daga idanunta ta zubesu akan zuwaira data tsaida komai tana son tabbatar
da zubawar. Karon farko da cikin jikinta taji kamar nauyin idanuwan wani yana
kallonta zatayi abinda bashi ya dace ace tayi ba akan wani,duk kuwa da tasan jirgi
daya shine ya debo zuwaira da ainihin me kwangilar,amma a yau saita ji wani nauyi.

"Zaki iya bani space?" Ta jefa mata tambayar taba dinke girarta sosai fiye da dazu.

"Au to....to ranki ya dade" Ta fada adan daburce sannan ta juya tana fita a kitchen
din. Haushi ya sanyata kwarara da yawa,idan komai ya qare ai a huta,taga ta inda
zata tuhumeta kuma,sai taja tsaki tana jefa roban a shara sannan ta juya ta fice
tana baiwa zuwaira dake falo umarnin taje ta jerasu,sai ta wuce kai tsaye zuwa
dakinta.

Itama din a gaggauce ta shiryasu tana kallon kayan,baki ta tabe,tana
jin haushin yadda lafiyayyen abinci irin haka yake salwanta,ga nasu iyalan can
cikin yunwa da buqatar abincin da baikai wannan bama,amma akan mutum daya anata
asarar lafiyayyen abinci irin wannan. Hankalinta ta maido jikinta da sauri,saita
juya tana barin falon cikin son kiyaye dokarsa da tsoron kada ya dawo ya sameta a
wajen kamar yadda ya shardanta mata.

K'arfe Tara da wasu mintuna motocinsa suka tsaya a farfajiyar gidan bisa
halastaccen parking da kowanne driver na kowacce mota ya qware akai. A nan harabar
gidan ya barsu ya wuce ciki shi dame sunan malam,wanda iyakarsa qofar parlor din
farko ya juya shima yana komawa cikin guard da security na gidan dake qoqarin
tabbatar da tsaro da lafiyar kowacce mota kafin masu tafiya su wuce a sake tabbatar
da tsaron gidan sannan a maidashi a rufe kaman yadda yake,shida da fita kuma sai da
izinin masu gidan.

A hankali yake ratsa falon farko zuwa na biyu kafin ya isa stairs
dinsa. A gajiye yake don duk sanda yayi dare irin haka a company to tabbas cinkoson
aiki ya riqeshi ne.

Tun daga nesa yana taka stairs din ya hangi maqullin maqale jikin
qofar,ya isa a hankali ya sanya hannu ya cire sannan ya tura qofar parlor din. A
nan zarginsa ya tabbata,mug din da yayi amfani dashi a daren jiya yana zaune abinsa
dirshan saman side table din,yayin da dish din da yayi amfani shima dashi yake
zaune saman dining abinsa hankali kwance.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

39

_Daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace:mazan Allah S A W ya ambaci ranar
juma'a,yana cewa "A CIKINTA KAWAI WANI LOKACI,BA WANI BAWA MUSULMI DA ZAI RUSKETA
YANA ME TSAIWA YANA SALLAH YANA ROQON ALLAH WANI ABU FACE SAI ALLAH YA BASHI ABINDA
YA ROQA DIN". sai manzon Allah yayi nuni da hannunsa na qanqantar lokacin (ma'ana
baida tsaho,Allah yasa muna cikin wadanda zamu yita ruskarshi)_



Wani bacin rai ne karon farko ya sauko masa,ba abinda ya dawo masa akai sai abinda
ya faru a dazu. Yadda maamah ta fitittike tana jaddada masa yadda takeso ya
mu'amalanceta ko ya kula da ita,amma ko kusa ko alama shi baiga alamun tasan
darajar kalmar aure ba koda kuwa auren 'yar tsana aka daura,ballantana shi data
deba kudaden da ranta keso,karamci kuma ya sanya suka qara mata da wasu abubuwan da
shi kansa baisan me su anni suka kashe ba.

Duka sai yaji abun bai masa ba bai kuma zauna masa akai ba,ya kamata
ya qara bata lesson. Yana takawa zuwa bedroom din nasa yana watsar da kayan
hannunsa,kama daga socks takalminsa suit briefcase dinsa da sauran tarkacen daya
shigo dasu. Wani budewa hancinsa yakeyi yana tsukewa saboda bacin rai,ya tsani
raini ya kuma fahimci halinta ne,ya tsani rashin kunya ya kuma karanci dabi'arta
ne. Bai dakata ba sai da yayi wanka,ya hadawa kansa fruit salad a gurguje
yasha,sannan ya zauna yana jawo wayar sadarwar yana kiran number dakin nata.

Ta gama komai tuntuni,ta kuma jima da kwanciyar saidai baccin da
baizo ba. Tayi mamakin jin kiran,saita sanya hannu ta dauka tana tunanin zuwaira
ce,ko meye kuma ya faru a daren nan oho?.

Muryarsa taji sabanin muryar zuwaira da tayi tunanin itace. Har
tsakiyar kanta sautin muryar ta sauka mata da wani irin zuzzurfan amo

"Hello" Ya fada yana qoqarin hadiye bacin ran dake taso masa. Matsar da kan wayar
tayi daga kunnenta da zummar sauke wayar,kaman yasan abinda take shirin yi ta
tsinci muryarsa cikin zafi yana magana

"Kika kuskura kika sauken waya....zakisha mamaki na". Tsauri umarnin nasa yayi
mata,saita samu kanta da gaza ajiye wayar. Sau tari tana mamakin yadda yake cin
galaba a kanta haka da sauri,umarninsa yake saurin ratsata,wani abu guda daya da ta
raina akan kowanne d'a namiji. Bata taba zato ko tunanin akwai wani lokaci da zaizo
da wani namiji zai iya juyata ko ya canzata daga abinda yayi mata daidai cikin
rayuwarta ba,sai ga abun yana tafiya cikin rashin zato bare tsammani.....kamar a
cikin duniyar mafarkinta.

Ci gaba tayi da riqon wayar ba tare data ce komai ba,haka daga nasa
bangaren bataji ya sake furta komai ba. Kusan minti daya wayar na a riqe a
hannunta,sakannin kuma suna ci gaba da motsawa. Kaman daga cikin wayar taji an
murda qofa an kuma budeta. Sauyin yanayin qamshin daya soma mata sallama ne ya
shaida mata tabbas an bude mata qofa,ba kuma cikin wayar bane a zahiri ne.

Tana kwance ne rub da ciki,don haka ta

Please Login or Register in order to submit comment