You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yaji ya kuma ga kaman haruffan sunansa akan labbanta,saidai baisan
ainihin abinda bakin nata ya fadi ba. Duk da ya fahimci inda komai ya dosa yana
kuma ta qoqarin controlling kansa amma ya kasa.......ya kasa yiwa kansa
waigi.......ya gaza tsaida kansa ko saisaita kansa koda na minti daya,bayajin kuma
akwai wani abu dake da qarfin daidait nutsuwarsa a daidai irin wannan lokacin. Wani
irin sabon kuzari yakeji a jikinsa da bai taba jin irinsa ba.....wani sabon qarfi
yakeji tattare dashi,yana jin kaman akwai inda yakeso ya isa,akwai inda yakeso
yakai dole dole......kaman idan bai isa wajen ba zai iya mutuwa.......kaman idan
bai qarasa muhallin ba akwai wani abu maras kyau da zai iya faruwa dashi,yana jin
wani abu can kusa da ransa dama zuciyarsa gaba daya,yana jin yadda yake shawagi
cikin wani sarari da baisan iyakar fadinsa ba.

Wulgawar wani second cikin tunani da lokacinsa da wani irin gigitaccen
yanayi shi ya dawo da hankalinsa jikinsa. Wani irin numfashi me dauke da wani irin
sauti kamar numfashinsa yana shirin barin gangar jikinsa ya sauke......saukar
numfashin da tafi kamanceceniya da gurnanin zaki,kowacce gaba a jikinsa ta saki ya
aza mata dukka qarfinsa wani zazzafan gumi naci gaba da keto masa ta kowanne kafan
gashi dake jikinsa. Qin sakinta yayi ko ya raba jikinsa da ita.......yana jin kamar
idan ya matsa koda kuwa Inches biyu daga gareta zata bace masa......yana jin ko
yaya ya motsa kadan zata iya subuce masa,yana jin kamar motsinsa yana iya sanyashi
ya rasata. Wata qaqqarfar runguma yayi mata cikin ni'imtaccen ingarman qirjinsa.
Jiqaqqen gumin dake tsakanin sumarta goshinta da wuyanta gaba daya ya dinga
gangarowa yana cakuduwa da nasa,scents na turaren jikinsu ya sake zama wani irin me
sanyi tsananin jikkunansu. Wani irin ni'imtaccen qamshi yakeji yana tashi daga
jikinta.......qamshin daya zamewa hancinsa na daban,irin qamshin da zai iya
rantsewa bai taba jin abu me dadi a hanci irinsa ba......all over her body ko ina
idan zai iya tunawa wani irin qamshi me laushi yake fitarwa.

"Dama haka matan suke?" Ya tambayi kansa yana qiyasta adadin shekarun daya dauka
yana zaluntar kansa ta hanyar haramtawa kansa wannan nutsuwar da wannan
ni'imtacciyar rayuwar.

Tunaninsa kaf ya dawo da baya da baya har zuwa sanda ya fara maidata
mallakinsa.....har zuwa sanda ya fara keta gonar tasa.

"She's a virgin?" Labbansa suka motsa ya furta a fili saidai can qasan
maqoshinsa,tamkar dai yana tsoron fada,tamkar dai yana tsoro kada kowa yaji.
Yanajin yadda maqogoransa gaba daya ya soye kaman ba wani sauran yawu daya rage a
jikinsa.

Wani qaqqarfan abu yaji yana mamayarsa bayan wani irin nauyi da yaji
tamkar ya sauka tsakanin qirjinsa zuwa mararsa. Yana jinsa yayi wani irin sakayau
tamkar ma idan ya miqe iska zata iya dibansa ta watsar. Wata irin nutsuwa da bai
taba cin karo da irinta ba ke ratsashi,kaman sabuwar iska sabuwar rayuwa da kuma
sabon ruhi aka bashi. Yana jin wani yanayi na daban na musamman na mamaye ilahirin
bargo da jininsa. Idonsa ya runtse da qarfi yana fadin

"How did it turn out like this?,what's the story behind this??" Ya sake maimaitawa
kaman me tsoron kowa da komai,kaman bayaso kowa yaji fitar sautin daga bakinsa.
Kwanyarsa na cakudewa da kalolin tunanuka iri daban daban,negative da positive
dukka lokaci guda.

Dif!. Kowanne lantarki dake kansa ya dauke ya daina aiki na wasu sakanni
kafin kuma a hankali engine din karbo saqo da aikewa ya soma motsawa yana dawowa
saitinsa. Fuskarta da yanayin reaction dinta kukanta dukka hade da magiyarta
lokacin da yake yunqurin kaiwa bangon da yake muradi.......yadda labbanta suka
dinga motsawa.....yadda oily eyes dinnan da bai taba lura da tsananin haskensu da
sheqinsu ba irin yau suke jujjuyawa cike da tsoro firgici da razanin kasancewarsu
abu guda

"Wannan shine tsoron da akan gani idanun kowacce d'iya mace a darenta na
farko......ranarta ta farko da zata fara sanin d'a namiji?" Ya tambayi kansa sannan
ya amsawa kansa da cewa.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 75



75



"Yes...yes" Zamewa yayi daga gareta yana rage mata nauyin daya aza mata. Tafukan
hannayensa gaba daya ya sanya yana qoqarin dago fuskarta da sumar kanta ta zame
labule a tsakaninsu,fiye da rabin hankalinsa yana kan dukiyar fulaninta da suke
wani irin fusgar hankalinsa suke sanyashi jin kaman ya qare rayuwarsa a tsakaninsu
ba tare da ya motsa ko ina ba. Hannu ya sanya ya yaye sumar data rufe fuskartata
jikinsa gaba daya yana rawa ya kasa samun daidaito. Tari Tarin abubuwa keta kutse
cikin tunaninsa suna fara masa tilawa.....tun daga randa furucin farko ya fara
hadasu da ita,yanata qoqarin tuna abinda ya soma gaya mata.......yanata qoqarin
tuna da wanne harshe yare ko lafazi zaiyi amfani ya fahimtar da ita HAQURI bisa
Tarin kalamansa marasa dadi da ma'ana wadanda baisan adadin yawansu ba.

Da wata irin martaba kima da darajarta da sukayi masa fadowar bazata
cikin tsokar zuciyarsa,suka cakuda da kowanne digon jini dake yawo cikin jikinsa
yakai fuskarsa saman tata ya hadesu guri guda,hancinsa ya saitu da kyakkyawan
hancinta me tudu da tsaho.

"Am.....soo.....amsor....." Yayita qoqarin maimaitawa yana jin wani matsanancin
ciwon kai daya saukar masa lokaci daya. Sai ya zame kansa ya saukar dashi a
kafadarta yana cusa fuskarsa cikin wuyanta. Yana ji ne kaman ya zama wani irin
ragon mutum kuma rarrauna......yana jin kaman kuka yakeso yayi ko zai sake rage
nauyin dake cikin zuciyarsa.

"Ya akayi na zama haka?,how?" Ya tambayi kansa,kafin kuma a hankali ya dora
labbansa saman kunnenta cikin salo na rada.

"Can you hear me.....am sorry......i didn't mean to......to" Sai ya kasa qarasawa
saboda bugun numfashinsa daya tsaya cak lokacin daya fahimci babu fitar numfashi
sam a hancinta. Fuskarsa ya sake kaiwa daidai hancinta,da gaske ba fitar numfashi
sam sam a tattare da ita,wani abu da yazo masa a tsananin ba zata ya sanyashi
gigicewar da har baisan sanda ya kira sunanta ba

"Sabreeeennn" Ya furta yana tashi sosai hannayensa dafe da gadon,saidai kuma
danshin da yaji cikin tafin hannunsa ya sanyashi kai idanunsa wajen ba shiri.

"Jini?" Ya furta yana sake fidda idanunsa waje,ya fadi kalmar ne kamar me tambayar
kansa da kansa,kamar kuma me bawa kansa da kansa tabbaci.

Da sauri ya saka hannu yana jawo comforter din da rabin jikinta yake a
rufe rabi kuma take kai,take ya saketa don bazai iya kallon yadda lafiyayyen jan
jini ke kwance a jikin farin comforter din ba,jikinsa ya dauki rawa gaba
daya......kai kace ba shine mamallakin kamfanin diamond da gold dinnan ba.....kai
kace ba shine Muhammad jadda dake razana zukatan maza ba......kai kace ba shine dan
gwagwarmayar nan ba.....hustler na gaske wanda baisan tsoro bs bare maganan ja da
baya....yakan iya sanya qafarsa kan kowanne bigire ko mataki da ake fargaba saka
qafa saboda hatsarinsa....yana fafata da koma waye komai hatsarin dake tattare
dashi......yau sai gashi labbansa na sama dana qasa suna haduwa ya gaza koda
ambatar sunanta.

"Me ka aikata haka fuad?,me ka aikata mata?" Ya fadawa kansa da kansa da qarfi yana
sanya tafukan hannayensa dukka biyun yana kama kansa da kyau.

Sauka yayi daga gadon da gaggawa yana nufan fridge din dake killace
a daya daga cikin corner din parlor din ya bude. Sassanyan ruwa ya fiddo,ya dawo
saman gadon yana tattarota cikin duvet din da shi kansa yayi bala'in staining sosai
ya azata saman cinyarsa. A cikin tafin hannunsa ya zuba ruwan ya soma shafa mata
daga fuska zuwa wuyanta. Sau uku kenan yana yin hakan.....amma ba wani motsi da
tayi.

"Oh my god!...." Ya fada yana wurgar da gorar ruwan ta fadi qasa ta fata tsiyaya.
Fuskarsa ya kafa saman nata fuskan,ya riqe hancinta ya kuma bude bakinta ya soma
bata iska ta ciki.

Mintuna kadan yaji taja wani irin numfashi da ya tsarga mata har
tsakiyar cikinta kafin ta fiddoshi,dagawar qirjinta ya alamta masa dawowar
numfashinta,sai ya miqe yana duban fuskarta da tayi wani irin jawur idanunta da
suke a rufe suka nuna dagawarsu.

"Sabrrrrrr" Ya taqaita sunan nata saboda fitar hawaye daga rufaffun idanunta suka
kuma gangaro ta gefan kunnenta.

"I was wrong to do that......How can i make it right?" Ya fada yana jin hankalinsa
na sake tashi. Bay qaunar kuka sam sam sam,musamman kuka na diya mace. Daya daga
cikin abinda ya dinga daga masa hankali lokacin quruciya kukan musaddiq......kukan
musaddiq a duk dare sanda maamah ta tafi ta barsu.....kukan abbansa sai ya zama abu
mafi tsanani da azaba daya taba gani.....wadannan abubuwan suka sanya ya tsani kuka
ainun.....duk da yana da tsananin dakiyar nuna bai dameshin ba.
Hannunsa ya dora saman goshinta don cire mata gashin daya sake lullube mata
goshin,yana jin kowacce kalma ya debo saita qwace daga bakinsa.......yanajin duk
duniya ba wata kalma harshe yare ko lafazi da zaiyi daidai da kunnuwanta idan ya
fadesu......shi a karan kansa yakejin kamar ba'a qirqiri wata kalma ta ban haquri
da ta dace ko zata dace da girman laifinsa ba. Da sauri ya janye hannunsa yana jin
yadda fatar jikinta ke fidda wani irin huci kaman yadda jikinsa ke fitarwa

"Ya salam.......ya salam......am sorry,i hurt you sabrrr......Am sorry.....i hurt
you,I'll do everything possible to make you feel better" Ya fada yana neman yadda
zai gyara mata zamanta a jikinsa. Jinginarta a jikinsa jinta take kaman wani nau'in
azaba na daban,batasan yadda wata rai zata fahimci yadda takeji ba.....tana jin
kamar zata sake suma ne,don numfashinta sam baya kaiwa hunhunta yadda ya kamata.
Tanaso ta gaya masa ya janye jikinsa daga nata amma ba wannan bakin,sai kawai
kukanta ya qaru akan nada,abinda ya sake hargitsashi kenan.

A zahirin gaskiya baisan yadda zaiyi mata ba don baisan yadda akeyi
ba,hasalima shi bai taba zama yayi tunanin zuwan rana irin wanna ba a nan gaba a
rayuwarsa bare ya nemi ilimin yadda akeyi ba.

Jikinsa ya zame yana jin yadda zazzabi ke dafa qasusuwansa......amma
tashin hankalin jinin da yake gani daga jikinsa ya dame wannan. Wayarsa ya
dauka,sai ya samu kansa da rasa wanda zai kira.....wazai kira?,wa zai gayawa?,yace
masa me?.

"Farouq" Kawai shine sunan daya fado masa. Bai damu ba da yadda farouq din zai
kalli abun.....abinda kawai ya dameshi yadda zai ceci ranta daga ta'addancin daya
tabbatar yayi mata. Idan ya daga kai ya kalli inda jinin ke kwance sai yaji ya
aikata baqin fasadi ne kawai yau a daren nan,qaramin kisan kai kawai yakeji ya
aikata.

"Hello......zamu kwana ne....wajen nan fa yayimin,ina tunanin dawowa nida
fannah....."

"Am at home" Kawai ya fada da wani irin sound da yaja hankalin farouq din. Aje
yanayinsa yayi gefe da wasan dake cikin muryarsa ya bawa fuad hankalinsa

"Is something wrong?" Ya fada da tsananin kulawa a muryarsa. Sai daya runtse
idanunsa sannan ya budesu yana maidasu inda take kwance sannan yace

"Yes farouq......a rude nake.....please help.....i don't know what to do"

"You are not alone......am here to help,take your time and tell me what's
happening?" Farouq ya sake fadi cikin yanayin kwantar da murya.

"We had our first night farouq......i caused her serious injury" Ya fada da
tsananin nauyin abinda yake fita daga bakin nasa,saidai kuma ya zama dole yayi
hakan,don gani yake kaman tana dab da komawa sumanta.

Wutace ta daukewa farouq din. Shima maganan ya masa dan nauyi kadan,duk
da ya jima da sanin duk wadda zatayi irin wannan karon da fuad din abun bazai zama
da sauqi ba. Don ya bashi relief sai yace.

"Relax....ina zuwa". Yana sauke wayar daga kunnensa. Murmushi kadan ga qwace masa
duk da qasan ransa tausayin adda sabreen ne fal. Yasan za'a fuskanci hakan daga
fuad din,duk da tsananin wayewarsa da sanin lunguna da saqo na qasan
duniya.....gogewarsa da mmu'amalarsa da kalar mutane daban daban jinsi daban
daban......amma yau saboda tsananin kamewarsa da zame kansa daga dukkan wani batu
ko sabga data shafi wannan fannin ya rasa yadda zai taimakawa matarsa. A ransa yaji
tabbas ciwon ba qarami bane tunda yaji damuwa sosai a muryarsa.
Ya jima yana kallon number wayar anni ta qasar yana kwatanta yadda zai
kirata ya gaya mata. Wannan din wani training ne nata data musu. Ko.meye nasu idan
ya samesu komai nauyinsa bata yarda wani ya fara jibantar matsalarsu ba kafin ita
bare a nan din baisan waye zai kira ba,dole ya koma ya shiga sms ya tura mata saqo
kaman haka.

_"Muhammad yana dakinsa......he needs your assistance"_ yana tura mata ya aje
wayar,don bayason ta kira neman qarin bayani don wabillahi baisan ya zai mata shi
ba.

Tsaiwa cak yayi kuma wani abu yana dawo.masa da baya.

"Ya akayi first night yazu musu da hakan if ba virgin bace?" Ya raya maganar a
ransa,sai kuma yayi saurin kawar da ita don shi ya jima da qaryata duk wani hasashe
na fuad tun ba yau ba.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 76


76


Sanda saqon ya iski anni dawowarta gidan kenan,tazo ta samu gidan ba kowa
basu dawo ba. Daki ta wuce ta sauya kaya ta dauki wayar tana fitowa parlor da
zummar kiransu taji me ya kaisu yin dare bayan tayi warning dinsu kan hakan kafin
su tafi?. Jiya sam bataga sukuni ko walwala saman fuskar fuad ba,kuma tana ankare
dashi,yadda ya kasa ya tsare a falon,bai koma daki ba sai bayan dawowarsu. Tasan
yana da zurfin ciki sosai,ba kasafai ka fiya sani ko gane abinda yake damunsa
ba,amma ita din uwace,koda wanne yare sukayi magana su dukkaninsu tana iya
fahimtarsu.

Shigowar saqon ya dakatar da ita daga qoqarin kiran nasu da takeyi

"Wani sabon sakarcin ne kuma haka?" Ta fada tana zama saman kujera da gorar ruwan
dake hannunta ganin me saqon farouq ne.

Sau biyu tana maimaita saqon,tasan tunda ya fada da gaske fuad na cikin
gidan,duk da bataji alamun akwai kowa ba a ciki,amma sai kuma saqon yaja
hankalinta. Cikin fargabar kada wani mummunan abu ne ya faru dashi ta ajiye gorar
ruwan tana maida hijab din jikinta,ta miqe idanunta kan qofar dakin,ta taka a
hankali ta isa qofar.

Knocking ta fara yi,knocking din farko ya sauka kunnuwan fuad dake
tsugunne gaban gadon yana monitoring numfashinta,gani yakeyi ko yaya ya matsa zai
iya sauke idanunsa a kanta ya tarar ba numfashi tattare da ita.

"Waye?" Yayi namijin qoqarin tambaya

"Anninku ce" Ta fada a nutse. Idonsa ya lumshe ya kuma bude duka lokaci daya yana
furta

"Rabbi yassir wala'ta'asir.....ya salam sallim" Yana jin kaf rayuwanshi idan ka
debe rayuwar da maamah ta jefasu y taba shiga tashin hankali irin na yau ba. Baisan
ta yaya zai bari anni ta shigo ta gansu a haka ba duk da zuwa yanzun ya saka
Moroccan jallabiyya a jikinsa tun sanda ya kira farouq. Ita dince sam jikinta yaqi
tabuwa masa,da yakai hannu kusa da ita sai maga ruwan hawayen dake idanunta yana
qaruwa,ba bakin magana sam sam a tare da ita,amma duban data masa guda biyu tal ya
karanto wani irin fushi da kyara a tattare da ita.

"Ki taimaka please.....ki bari ko riga na saka miki" Wani fusataccem fushi ne ya
sauko mata,ya saka mata riga bayan ya gama ketata ya kuma keta haddi da duk wani
mutunci nata da take taqama dashi,ta kuma killaceshi tsahon lokaci?.

Yadda ta maida idanunta ta kulle ba tare data ko motsa ba ya tabbatar
masa bata buqatar ganinsa ne gaba daya,ga anni na tsaye a qofa dole bazai yiwu ya
barta tanata jira ba,haka ya doshi qofar can qasan ransa yana fadin

"Me yasa kayi haka farouq?" Yana qiyasta da wanne idanu zai daga ya kalli anni?.

Fuskarsa kawai ta kalla da yadda ya bude qofar cikin rashin karsashi
tasha jinin jikinta.

"Kana lafiya?" Ta jefa masa tambayar tana tsareshi da ido. A yau dai ko karen hauka
ne ya cijeshi baya jin zai iya kallon idanun anni bare ya mata bayani. Ratsewa
yayi gefe da alamun bata hanya. Itama batace komai ba,ta maida dubanta ne daga
cikin dakin tana hango iya abinda zata iya gani din wanda carpet ne da dressing
mirror kawai take iya gani,sai ta maida dubanta kan fuskarsa da a yau yakejin
idanun anni tako ina a kansa da wani irin nauyi. Batace komai ba itama ta ratseshi
ta soma takawa cikin dakin,wanda taku biyu kacal tayi shi kuma ya fice yana laluben
inda zaije ya aje kayan kunyanshi nesa da annin,saidai a taku na hudu idanunta suka
sauka akan Sabreen,jinin dake jajur yayi staining jikin duvet da comforter din ya
marabceta,cikin qasa da second uku ta fahimci me ya faru.

"Subhanallah" Ta fadi tsigar jikinta yana tashi. Tasan ko meye ya faru a wajen
artabu akasha ba kadan ba,ko tayi taurin kai yaje mata da dukka qarfinsa,qarfin da
sam sam tsakanin nata da nashi baizo daya ba.

"Muhammadu......maida qofar nan ka rufe" Annin ta fada da madaukakin sauti sanda
yake dab da bakin qofar parlor din. Cak ya dakata da abinda yakeyi din,ya maida
qofar ya kulle kaman yadda anni ta buqata,ya dawo kuma a hankali cikin parlor din
yana laluben wajen zama. Gangar jiki duka da zuciya sai yakejin kaman ba tasa
ba,zafin zazzabi yana ci gaba da lullubeshi yana raunana jikinsa,saidai yadda
kunyar anni ta rufeshi tafi masa nauyi akan zazzabin.

A mamakance take isa gaban gadon

"Ikon Allah" Tafada qasan ranta,wato ita dake lissafin ganin result ta hanyar dauka
jika,ashe karatunma sai yanzu aka farashi?.

Sautin muryar anni cikin dakin sai tayi fatan inama qasa zata tsage
ta wuce ciki?,yanzun yana da tsaurin idanun kiran ummansa taga barnar da
yayi?,wanne irin terere ne wannna yaja musu?,anni fa.....anni,ya manta surukarta
ce?,ya manta akwai kunya me girma tsakaninsu?.
"Subhanallah......ya salam" Anni ta.maimaita wannan karon a sarari saboda jinin
data gani muraran daya wuce wanda ta hanga daba bakin qofa. Dukka jikinta yayi
sanyi sosai,ta tabbata babban barna muhammad din yayi.

"Sannu......tashi a hankali ki qarasa bandaki" Anni ta fada tana kamata da tsananin
takatsantsan ta yadda zafin ciwukan jikinta ba zasu dameta da yawa ba.

Wata siririyar qara sabreen din ta saki,qafafunta kuma suka lanqwashe
tilas ta koma ta kwanta duk da anni riqe take da ita. Hawaye ne ke fita ta gefen
fuskarta,tsananin tausayinta ya kama anni. Bata taba kawowa muhammad xai gwada
rashin haquri irin haka ba,dole yarinyar tana buqatar motsawa ta gyara jikinta
kafin ma a samu bakin zaren gane iya adadin barnar data afku.

Yana daga falon amma.yana iya hangensu saboda a bude anni tabar
qofar,uwa uba yana zaune saitin wajen,saidai yayi kaman bashi a wajen.

"Muhammadu" Anni ta kirashi kai tsaye,ya amsa yana tasowa. Idanunshi a kanta yana
sauraren bayanin anni.

"Akwai ruwa me dumi a toilet.......ka kaita ta gyara jikinta tukunna.....ina zuwa"
Anni ta fada tana nufar qofa don itama zuwa yanzun kunyar ke neman kayar da ita.

Hakan yayi masa,yabi bayan annin ya maida qofar ya murza key,sannna ya
tako zuwa ciki yana nade hannun rigarsa. Sai yanxu kwanyarsa ta fara dawowa
aiki,bazai kuma saurareta ba zaiyi kaman yadda anni tace,zaiyi yadda ya dace,dom
haka yana qarasawa gabanta ya sanya hannu ya dauketa cak kaman jaririya haihuwar
yau,ya lullubeta cikin qirjinsa yana wuce toilet din da ita.

Yana jin yadda ta damqe hannuwansa da kyau,da alama haushin dake cikin
zuciyarta ne takejin kamar riqon tsaurinta a garesa zai sassauta abinda labbanta da
bakinta ba zasu iya fada a yanzu ba.

Sake yaye mata dukka suturar jikinta yayi,ta sake runtse ido abun
yana mata zafi. Cikin wasu mintuna jikinta ya zama bayyananne a wajensa?,yana qare
mata kallo haka kanshi tsaye da kaifafan idanunsa da takejinsu a kanta?.

"Bazan kalleki ba indai har bakison hakan.....zan kulle idanuna har saikin bani
izinin na budesu" Haushi da takaici suka lullubeta,harara takeson jefa masa zazzafa
amma bataji idanunta suna a daidai din da zai ga harara tata yadda ya kamata. Banda
ya raina mata wayo yana tsare yana qare mata kallo da wani irin yanayi dake qara
kashe masa gangar jiki.....amma kuma yana gaya mata zai kulle idanunsa?, daga baya
kenan wai anyi sadaka da karuwa ta furta a ranta.

Sake dagata yayi cak ba kuma bata lokaci ya sakata cikin bathtub
din da anni ta hada ruwa me dumi qwarai. Wahalalliyar qara ta saki da muryarta dake
nuna duka qarfinta ya qare.

"Ka sakeni....ka cireni a ciki" Ta fada hawaye na layi bibbiyu akan fuskarta. Wani
irin narkewa zuciyarsa tayi da tsananin tausayinta da bai taba jin irinsa akan
kowacce diya mace ba idan ka cire anni da amna. Saidai ko kafin ma yayi mata yadda
tace ta sake masa wani zazzafan cizo a hannunsa dake dafe da tub din.

"Ouch!" Ya fada yana runtse idanunsa saboda tsananin cizon data sakar masa. Ware
manyan idanunsa dinnan yayi a kanta bayan ya budesu,idanun da bataji komai tsahon
xamani zata iya mance memory din daya aje mata a yau. Labbansa ya motsa yana jin
zafin zazzabin har cikin idanunsa,to amma yanayin daya sakata a ciki yafi komai da
yakeji ciwo. Ya sani ya shigeta ne da duk wani qarfinsa,yana tsammanin samunta
budaddiyar hanya ga kowa......sai abun yazo masa a wata irin bazata a sanda bazai
iya controlling din kansa ba kuma

"I'm truly sorry for the pain I've caused" Ya fada da wani irin calmness cikin
muryarsa,sai ya sanya hannu yana cirota daga bathtub din,yana jin bazai juri
barinta tana jin abinda takeji din ba......baisan girman pain din ba bare ya
kwatantashi,saidai koma meye ya tabbatar radadinsa ya wuce wasa.

Bedside drawer ta isa tsigar jikinta na sake tashi gana girgiza kai
da jinjina barnar data tabbatar ba qarama yayi ba,wayarta ta dauka ta duba last
call dinta. Qawarta da suka rabu dazu hajja saudat ta kira.

"Kuna da wata gynecologist ne mace da zata iya home service kuwa?" Anni ta
tambayeta kai tsaye.

"Eh akwai.....'yar qasar syria ce.....tana da kirki sosai fadwa haleem".

"Na gode.....kimin magana da ita please,ki bata address na gidana.....if possible
tunda bamu da nisa kada ta wuce one hour"

"In sha Allah kusa muke ai"

"Na gode" Anni ta fada tana katse kiran. Farouq ta koma kira,saidai kira har biyu
bai daga ba,sai ana ukun sannan ya daga yana sosa kai.

"Ku kwana a can,ku biyasu kudin kwana daya.....but kakaimin amna gidan saudat acan
nakeso ita din ta kwana"

"Okay.....in sha Allah" Farouq ya amsa shima yana jin dadin hakanma da tace,don shi
kansa a yanzu ji yake ya zama surukinta,ina ga fuad din. Yadai tabbatar ba zasu
qarke lafiya ba idan ya dawo hayyacinsa,to amma wa suke dashi sama da anni?,itace
qawarsu abokiyarsu kuma.


_uhmmmm....tofa,sabreen naga kin dauki zafi da yawaπŸ˜„πŸ˜„.....amma dai muje zuwa_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 77


77


Da wani irin yanayi yake wanke mata kowanne sashe na jikinta da ruwan shower
gel din. Wani kuka take saki kawai tana ji har a ranta ya gama da ita,bata da wani
sauran qarfi da zata dakatar dashi ko guda daya,cizo kam ta masa shi har batasan
adadi ba,amma ko a fuska baya nuna mata yaji zafinsa bare akai ga dakatawa da
abinda yakeyi,tamkar ma ba jikinsa take ciza ba,idan ta saka bakinta ma tsaiwa
yakeyi har sai ta cire don kanta. Shi kadai yasan me yake sake ji cikin jikinsa,ji
yakeyi kaman baiyi komai bama,wani sabon feeling ke taso masa saboda santsin shower
gel din dake sassan hannuwansa wanda da tafin hannu kawai yake dauraye mata jikin
ba tare daya nema loofah ba. Kafin ya gama wanketa launin idanunshi sun sake
canzawa sosai,numfashinsa yana masa nauyi tsakanin qirjinsa da hunhunsa,inda zai
samu....inda zai yuwu yana buqatar sake kasancewa tare da ita ko yaya ne.....koda
na mintuna kadanne,amma shi kansa yasan yadda take a yanzu dole tana buqatar
medical care. Bai taba jin ya zama addicted to wani abu ba irin wannan abun,cikin
qasa da wasu awanni qalilan yana jin kamar an halicci abunne

Please Login or Register in order to submit comment