You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusa huhu talatin,kwalayen alawa da suka
kusa kaiwa kwali hamsin da tarin dabino da baisan ina zai ajiyeshi ba. Ga wasu uban
kudaden da shi kansa baisan miliyan nawa bane na amarya kyauta ta daban,shi kansa
ga wata dukiyar da aka mallaka masa a mazauninsa na uban amarya,abinda ya sanya
jikinsa dukka ya dinga bari......Allah yasa komai ya tafi a tsari bisa taimakon
kamilin amininsa.

Qarfe uku na yammaci motar da yasanya ta jido komai da komai ta tsaya
a gaban gidan daya kasance gida ga d'an uwansa kuma uban riqonsa da yayi masa
alkhairi masu tarin yawa a rayuwarsa.

Yara masu wucewa ne suka fara tsaiwa kallo ganin mota shaqe da kayan
kwali kamar ana shirin bude provision. Wannan ya bashi damar kiran yaran,kafin wani
lokaci sai gasu sun cika wajen harda wadanda ba'a kira ba,suka fara hidimar diban
kayan suna shigewa cikin gidan dasu.

Hadiyya na daga bakin qofar famfo tana wanke uniform dinta na school
of nursing,tazo gida ne weekend anjima kuma takeson komawa,yayin da bibo ke zaune
saman kujera 'yar tsuguno daga qofar kitchen dinsu tana gyaran wake suna taba hira
da shalelenta.

Daada ce ta fito a daki dauke da buta don kama ruwa gami da daura
alwalar sallar la'asar. Daidai sannan yaran suka fara layin shigowa

"Kai.....kai daga ina?,ko.izzatu ce tazo?,izzatun alkhairi,don ita daya ce kaf
gidan nan ke iya shigowa da kabakin arziqi haka" Bibo ta fada tana sakin murmushi

"Kawu ne yace mu shigo dasu,ku gyara waje don suna da yawa,a ina za'a ajjiye?" Wani
yaro cikin yaran wanda shekarunsa suka dan dara na sauran ya fada yana sauke
kwalayen hannunsa.

"Wai kana nufin rufai?" Bibo ta tambaya

"Indai shine aje masa inda yace,kada yazo ya yiwa jama'a tijara,bansan ma masifar
data sakashi kawo mana kaya gidan nan ba,shi abinsa da baya tabuwa,tunda kudin
cacar nan suka samu mu kuma bamu da kwanciyar hankali". Taja qaramin tsaki daada na
gaban famfo tana tarar ruwa wanda suka kusa daukeshi don haka da qyar yake zuwa.

Tun tana irga adadin kwalin har suka fara yawa suka fara kuma shallake
tunaninta. Tun daada na bandaki har ta fito tana daura alwalarta,sai bibo ta ajiya
farantin waken tana cewa

"Wai rufai sai ya cika mana gida hankalinsa zai kwanta?,wanne irin kwalaye ne haka
na alawa da biscuit masu tsada kuma?,ko kantin siyayya zai bude ai sai haka
ko?......hadiyya tsame hannunki ki leqa ki ganemin". Zubda ruwan kurkurar bakinta
daada tayi,a karon farko tayi magana

"Ke kin fiya ci da zuci wallahi.....wai shinma a kanki kayan zasu zauna?,koma meye
ai zaiyi bayani ko?,tunda shima kinsan bakinsa baya shuru".

"Adai dubo din daada abun ya fara wuce lissafi". Ko kafin hadiyya ta fita ta dawo
kwalayen sun sake yawa,sai gata tana zare mayafinta

"Aida saura bibo.....shikam yana can yanata bawa yara umarnin aci gaba da shigo
dasu". Wannan karon har daada tsaiwa sukayi suna kallon ikon Allah,zuwa wani lokaci
da faffadan tsakar gidan nasu yayi hani'an da kaya,muryar nan tasa dake iya tada
mutum a barci ta karade tsakar gidan,ta kuma ratsa har kunnuwan Sabreen da haneefa
dake riqe da hannun juna a daki.

"Me bacci ya tashi......wanda kuma idonsa yake biyu ya bani hankalinsa ta
nan......me aiki ya ajiye aikinsa saina kammala bayani na" Ya qarashe maganar yana
saba babbbar rigarsa gami da jawo botikin fenti ya haye sama yana harde qafarsa
daya kan daya.

"Lallai ba'a daya a dangi.... Kuma gado ba karambani ba......yau ta tabbata cikin
diyoyin dan uwana akwai wadda tayo gadon arziqi irin namu.....ta fita zakka diyar
albarka haihuwar asuba" Yayi zancan yana dukan tafin qafarsa daya dora saman
gwiwarsa.

Harara bibo ta galla masa tana jan qaramin tsaki

"Kai ka fiya sarqa zance,ba yadda za'a yi kayi magana miqaqqiya......akan meye kake
magana?akan kuma wace?" Tayi zancan gabanta yana faduwa,saboda tsoron kada zuwan
matan nan a wancan kwanakin yana da alaqa da wannan uban kayan da kwatankwacinsu
basu taba shigowa cikin gidan ba.

"Akan waye kuwa nake magana idan ba'a kan Sabrina ba?......akwai wata me qashin
arziqinne sama da ita cikin gidan nan?". Sosai takeso ta rufe kawu da balain yadda
yake ware 'ya'yansu,yana abu kamar su ba haifarsu sukayi ba,to amma kuma tana
buqatar taji kan zancen sosai.

"Sabrina kamar yaya?"

"Sabrina?" Huda itama dake daki ta maimaita sunan tana maida idanunta akan fuskar
Sabreen din data tabbatar itama taji sautin futar sunanta daga tsakar gidan nasu da
yake tamkar sansanin yaqi wasu lokutan.

Wuf tayi zata miqe,Sabreen tasan fita zatayi taji ba'asin sunanta da
aka kama,don haka ta jawota ta zaunar da ita tana girgiza mata kai idanunta cikin
nata.

"Sabreen fa......cikin ikon Allah yau na bada aurenta ga hamshaqin attajirin nan da
basai ba gaya miki sunansa ba.....zaki gani cikin IV" Baki duka suka saki suna
dubansa,banda daada data nufi dakinta tana cewa

"Allah ya tabbatar da alkhairi"

"Ameen hauwa'u....ke da yake baki iya doguwar magana ba" Fara takawa yayi yana
nufar dakinsu Sabreen din yana cewa

"Bari naje na fito" Yayi maganarsa gaba gadi yana dosar dakin.
Page 100


Yau din da cikakkiyar sallama ya shiga falon,wanda duba daya Sabreen tayi masa
qirjinta taji yayi wani mummunan faduwa. Ta dauke idonta a kansa tana amsa sallamar
ta dubi huda.

"Ki wuce ciki ku zauna keda su nadra.....kada ki bari haneefa ta fito" A sanyaye
huda din ta miqe,tana jin kamar ta zauna taji da meye kawun yazo dashi. Abune me
wahala ya shigo dakinsu da alkhairi,koda yaushe idan kaga ya shigo akwai wani
tashin hankalin da yake tafe dashi.

"Yar arziqi......yarinyar kirki,haihuwar albarka,kedai Allah yayi miki
albarka,farar haihuwa,ubangiji ya jiqan mahaifinki da mahaifiyarki,ba abinda zamuce
da haihuwar diya irinki sai sambarka,kin zame mana marufar asiri,kin zama kuma
silar kawo mana hamshaqin attajiri cikin salsalarmu" . Dukka yayi maganar ne yana
kallonta,bakinsa cike fal da fara'a.

Wani irin duba take masa,don gaba daya bata fahimci inda maganar sa ta
dosa ba.

"Nasan ba zaki fahimci komai ba,amma yanzu zan miki bayani......ungo wannan" Yayi
maganar yana ajiye damin sabbbin 'yan dubu dubi din a hannun kujerar da take kai

"Duba tsakar gida daga nan idan zaki iya hangowa....goro alewa da biscuit din na
aurenki......wannan kuma" Yayi maganar yana nuna kudin dake kusa da ita.

"Ki cire million biyar kudin aurenki kenan,sauran kuma kyauta suka baki tukuicin
auren dansu da zaki yi,kome kike buqata kuma ki samu takardar kiyi list......karki
cuci kanki idan da hali ki siyo full scape masu yawa ki raba dare kina lissafawa ba
abinda zaifi qarfinsu don akwai.abun fiye da tunaninki".

Cikin kanta da zuciyarta taji tana tantama,anya mafarkin yin arziqi bai
soma haukata kawu rufai ba?. Kaman yaji me take tunanin,cikin murmushi yace mata

"Kina kallona kamar na tabu ko?,to wallahi koke na gaya miki wanda ya biya sadakin
aurenki saikin zabure.......da farko dai kuma a taqaice na bada aurenki ga Muhammad
jadda......mamallakin jadda diamond chores resources LTD....ga sadakinki
nan......sati biyu masu zuwa zasu zo da waliyyansa da naki a tara shaidu kowa ya
shaida".

Wani wawan duba take masa a kaikaice kamar taga wani tuburarren
mahaukaci,yayin da gagarumar jayayya da yaqi ya barke tsakanin bangarori biyu na
zuciyarta.

Sashen farko ya cika da fargaba da kuma zulumin komai fa kawu yana iya
yi indai akan kudi ne.......kada ya zamana zancansa gaskiya ne.......yayin da wani
sashen na zuciyarta kuma kewa abun kallon zancan shifcin gizo ne kawai. Ta yaya zai
bada aurenta haka?,sai kace wata diyar 'yartsanar roba ko abun wasan yara?,a haka
ake bada aure bada masaniyar kowa ba sai tasa masaniyar shi kadai?. Sam sam kanta
ma bazai dauki wannan shirin film din na kawu ba,saidai batasan me yasa takejin
muguwar faduwar gaba da wani irin tashin hankali dake cakude da fushi ba,ta zuba
masa idanu yayin daya ci gaba da zuba mata bayanan da sam ita bama fahimtar me yake
fada takeyi ba. Abu na qarshe data fahimta shine,wayarsa daya ciro yana cewa

"Kawunki na senegal abdulk'adir ya bani damar karba.....yace kuma idan na shigo na
hadaku kuyi magana".
"Uncle abdulk'adir?......tashin hankali!" Maganar tayita qasan zuciyarta
zuciyartata na wani irin bugu mara misali.

Uncle abdulk'adir.....zazzafan mutum me tsananin tsauri da
kafiya......me zafin zuciya da kafewa kai da fata wajen gaskiya.....mutumin da ako
da yaushe take kaucewa haduwarsu......mutumin da ko yaushe take qaranta yin waya
dashi,mutumin da har yanzu bata yarda yasan ainihin number wayarta ba gudun bin
diddigi tsanani takura da kuma sanya idanu......yau shine kawu rufai ke ambata a
gabanta?. Da gaske bakin alqalami ya riga ya bushe tunda har sunan kawu abdulk'adir
ya fito cikin batun!!!!.

"Kinga ban sameshi ba,dama dazun yacemin yau jumaa sai yammaci yake fita a
masallaci.....qila ya kashe wayar da zai shiga,amma ba matsala anjima saina dawo na
hadaku".

Batasan takai hannu ta watso kudin qasa daga hannun kujerar ba saida
taga kawu na binsu yana tarosu.

"Yaushe mukayi dakai zaka aurar dani ga wani da bansan waye ba?,saboda son
dukiyarka da kwadayin abun duniyarka kawu?......" Saita saki wani murmushi daya
sanya hankalin kawu ya tashi

"Bari na baka shawara......tunda wurwuri.....tun komai da duminsa kaje ka warware
abun nan.....wallahi wallahi wallahi ba wanda ya isa ya auraminshi ko wayeshi
kuwa,bansan da wannan zancan ba haihata haihata,ba kuma abinda ya shafeni bane"

"Za kuwa kiyi kaffara aminatu......" Muryar kawu ta isa kunnenta sanda take
yunqurin shigewa daki abinta don batason taci gaba da zama awajen.

Yadda yayi furucin da wani qwarin gwiwa ya sakata waiwayowa. Yana
tsaye kawun riqe da kudaden

"Zakiyi kaffara.... Don baki da kudin da zaki iya biyan me jadda kudaden kamfaninsa
da kika sace......hakanan bani da kudin da zan biyashi kudinsa da na ci a caca
cikin rashin sani......ke din fansar kudadensa ce......cikin dattako da kuma
alfarma irin tasu duk da haka suka sake biyan wasu kudaden saboda aurenki.......kin
shirya yaqi da fito na fito da mamallakin diamond gold da azurfa?".

Qafafunta taji suna yunqurin kayar da ita,maganganun kawun suna mata
girma akai dama sassan jikinta tamkar bata da jarumta da qwarin gwiwar iya dauke
dukkan bayanansa.

𝙈𝙪𝙝𝙖𝙢𝙢𝙖𝙙 𝙛𝙪'𝙖𝙙


Idanunsa zube cikin na farouq sanda yake masa bayanin yadda komai ya
kasance. Yayi relaxing sosai abinsa,yayin da ya miqe dogayen qafafunsa saman table
din glass dake gabansa yana sipping ruwan wolf berries da wasu daga cikin 'ya'yansa
cikin qaramin cup na glass.

A nutse ya ajiye cup din,me sunan malam ya dauka yana ficewa dashi
daidai sanda farouq ya kammala duka bayaninsa. Yatsunsa ya sarqafe waje guda idonsa
akan farouq

"Duka wannan hidimar wa ya aikeka tsarata?.....bakasan already ta debi kudin
aurenta ba?". Qaramar harara farouq din ya watsa masa yana dora qafarsa shima daya
saman daya
" Duka wannan kai ka sani......abu daya nake da matsaya akai......daga gidan
dattako muka fito....so dole neman aurenmu da kuma matayenmu susha banban da na
kowa......that's all" Kai fuad yake jinjinawa da wani qaramin kwantaccen murmushi
can qasan fuskarsa.

"Tunda kuka sake basu dukiyata dole na tsaurara matakan tsaro.......kuma tamkar kun
sake lafta musu bashi ne.....don already na sallamesu,nace su lissafa cikin abinda
suka dauka su zare kudin komai da komai". Girgiza kai farouq yayi,wai me yake damun
fuad ne akan wannan batun?. Duka duka abinda aka basun ma baikai koda kaso daya
cikin goman abinda yake fiddawa kusan kullum ana rabarwa mabuqata ba. Gyara zamansa
yayi ya sako masa zancan da yafi damunsa tunda suka dawo din......ya kuma tsaye
masa a rai.

"Abu mafi muhimmanci da kuma ban mamaki ma.....kai da maamah ashe gida
daya.....kuma yarinya daya kuke nema". A nutse ya daga idanunsan nan da wani lokaci
suke fita gada gada,wani lokaci kuma su kasance lumsassu kamar wanda bacci ya kama
ya zubawa farouq su

"Ba wadannan idanun nace ka watsamin ba......na gaya maka wani abune da yaban
mamaki". Dan murmushi yaja kadan,idan bai manta ba farouq ya taba gaya masa bai
fiyason ya watsa masa idanunsa ba,don wani lokaci suna masa wani iri da dan sakashi
jin kamar ba me babban sunansa ba.

"Maamah tana da nata plan din......kamar yadda nima nake da nawa plan din......so
an samu haduwar target duka akan abu daya". Zuba masa ido farouq yayi yana jin
zuciyarsa na sake cika da shakkar halin matar,duk kuwa da cewa mahaifiya take a
wajen dan uwan nasa kuma rabin jikinsa. Saidai duk inda akaje aka dawo shi din me
qoqarin saita fuad ne,musamman akan mahaifiyar daya fahimci shi da ita duka
zukatansu sunyi nisa akan abinda suka saka a gaba.

"Kada kayi mummunan zato ko zargi akan yarinyar daka zaba don ta cikashe maka rabin
addini da rayuwarka.....hakanan kada ka dora zargi akan mahaifiyar da tayi silar
shigowarka duniya".

Wani murmushi ya saki yana sauke qafafunsa qasa,sannan ya miqe ya zauna
sosai yana duban farouq

"BB farouq.....har yanzu sai nake ganin kamar baka gama sanin waye Muhammad fuad
jadda ba.....any way......komai ina sane dashi,zan kuma ji dashi daidai da yadda ya
dace...."

"But....."

"But what?" Ya katsi numfashin farouq.

"Don't make....."

"Ba abinda zai faru dude" Ya sake fadi kawai yana miqewa daga zaman alamun yakai
qarshen maganarsa dama hukuncinsa.

Yaji wani irin abu tun daga saman kansa har tafin qafarsa a sanda ya
kammala bincikensa kan wacce maamah keson hadasu. Kenan ba wani guri daya kuskure
wajen fahimtar hatsarin yarinyar?,zallar rashin tarbiyyarta?,qwarewa wajen iya taku
tare da buga kowanne irin wasa da qwaqwale zuciya dama dukiyoyin jama'a?. Kenan ya
tabbata itama jan wuya ce tunda ga hadin gwiwa nan ya tabbata tsakaninta da
maamah?. Abu daya ne tak! Da baikai ga ganowa ba.....hakanan duk wasu 'yan
bincikensa suma basu kai ga ganowar ba shine.....KAN WACCE IRIN KWNGILA SUKA GINA
ALAQAR?......MEYE LULLUBE QARQASHIN BATA AURENSHI?. Shidai yasan tasa agenda
din.....TO MECECE TASU?.
"zaki gane baki da wayo.....i will teach you a lesson........ You'll learn through
experience" Yayi zancan yana fitar da wani siririn murmushi.

Cikin ranshi yake tsara wanne hanya zaibi don ya fara gwada mata nashi
salon izzar?,tasa isar?....da kuma qarfin ikonsa tun daga yanzu?". Dakatawa yayi
daga tafiyar da yakeyi,yadan waiwaya kadan sashen da farouq yake

"Kace ba?,kunkai sadaki ko?" Ya yiwa farouq tambayar data dan sashi maida
hankalinsa akanshi

"Yes.....haka na bawa abba shawara kuma hakan akayi".

"Good boy" Ya fada yana dan murmushi

"Ka gaya musu.....cinta shanta dama fitarta dukka yanzu suna qarqashina......kada
ta sake fita muddin ba da sanina ba".

" What kind of madness......"

"Tell them ko ni na kirashi da kaina....you know ina da number wayarsa ko?".

"Oh sheet" Farouq ya fada yana kama goshinsa.

"Wai meye damuwanka?......bakason komai.....but kana bibiyan komai why?" Juyowa
yayi sosai yana duban farouq din,wannan karon murmushinsa yadan bayyana

"Wickedness" Ya amsa masa a taqaice.

"Bai kamata a dinga qyale irinta ba haka suna ci gaba da abinda sukaga
dama......punishing nasu ya kamata ayi ta hanyar da zasu ji har cikin tsoka da
jinin jikinsu"

Balcony dinsa ya isa kai tsaye hannayensa zube a aljihun wandonsa,yana
bin dukka tsirran dake shuke daga gaban wajen da ido. Haka kawai yakejin interest
dinsa yana qaruwa akan ya hora yarinyar. Abinda ya karanta maza sun badasu da har
ta raina ajawalinsu haka da yawa,so dole ta fahimci nata kuskuren.


*_SABREEN_*


Jadda wani dadadden suna ne daya jima yana shiga kunnenta lokaci bayan
lokaci,saidai ta tantance wayeshi yadda ya kamata abune da bazata iya ba. Tun daga
fitar sunan daga bakin kawun har zuwa shudewar daqiqa sittin kallon kawu din kawai
takeyi,kafin daga bisani qarar wayarsa ta katse wa kowa saqar da yakeyi cikin
zuciyarsa.

Sau da dama bayyanar number farouq cikin wayarsa wani abune dake zame
masa kama da ZAK'I DA MADAC'I,daidai ga gaurayar farinciki da kuma dimuwa a lokaci
guda a kuma muhalli guda.

"Ga iyalin gidannan.....bismillahir rahmanir rahim" Ya ambata kafin daga wayar
kaman yadda amininsa ya bashi shawarar yi domin amintar da kunnensa daga jin abinda
zai dinga daga masa hankali har a samu a qare maganar auren.

Sai daya zauna sosai sannan ya daga kiran,ya bada kunnensa yana
sauraren bayanin da farouq ke masa,wanda duka bayanin yana yinsa ne yadda kawun zai
fahimta.....ya kuma gwammace ya dinga isar da saqon fuad ne gudun kada ya bayyana
halinsa.....ko aljanar daya sake haqiqancewa akwaita ta sanyashi yin wani baqon
halin da mutuncinsu zai zube idanun surukai,duk kuwa da cewa shima dama a karan
kanshi dan kai tsaye ne,dan gaba gadi.Page 101


"To.....to in sha Allahu ranka ya dade.....godiya muke qwarai da
gaske....Allah ya qara arziqi" Yayi zancan yan a kashe wayar,sannan ya maida
dubansa ga sabreen da tuntuni baqinciki ya qarasa kasheta a wajen,ta kuma koma ta
zauna tun kan ya gama wayar,badon bata gaji da zamanta a wajen bane.....aah....don
tana da sauran abun gayawa kawun,saidai kafin ta fara nata jawabin shidin ya rigata

"Saqo ne daga mijinki......yana me umartarki daki lazimci zama a gida......yace a
gaya miki baya buqatar daga yau har zuwa randa zaa tara shaidu a shaida daurin
aurenki ki sake leqawa ko ina.....amma dan uwansa yace idan kina da buqatar fita ki
sanarmin a kawo mota da masu tsaron lafiyarki......zasu kaiki duk inda kikeso a
qasar nan ko a wata qasarma idan kina buqatar haka" Yayi bayanin fuskarsa wasai
farinciki yana nuna kansa muraran a fuskar tasa.

Idanunta ta lumshe tana son tilastawa kanta fahimtar ma abinda kawun
yake cewa. Shigar maganar kunnenta daidai take da wasan kwaikwayon yara.

"Miji?,ita sabreen?,mijin kuma yana iqirarin hanata fita saida izininsa?,wai shin
yaushe ma akayi daren har garin zai waye?,yaushe ta yarda da wannan wasan
kwaikwayon nasu da har zai tunanin ta amsa sunan MATARSA?. Shi a matsayin wa da zai
tilasta ta aureshi?".

"Ko baka qarasa bayanin komai ba tsaf na fuskanci dalilin da ya sanya ka bada
amanna qulla auren nan......kawu......har yanzu ba'a haifi me arziqin da zan
aureshi don dukiyarsa ba koda ina da manufar yin aure......ballantana sam sam aure
shine abu na qarshe cikin jerin lissafin wajibai na rayuwata.......kawu......ka
rubuta ka kuma ajiye,wannan abu tamkar sabreen bata taba sanin ya wanzu ba......ba
wani qato daya isa ya hanani fita a sanda naso a kuma duk lokacin dana ga
dama.....ruwanka kawu ka maida musu dukiyarsa ruwanka ka riqe......abu daya na
sani....kudin dani sabreen na taba na tafi dasu ta hanyar da nake ganin tayimin
daidai.....kuma yayi adabo dasu har abada saidai ya sake sabon zubi da lale" Daga
haka ta miqe tana yunqurin shigewa daki tana jin kwanyarta kaman zata birkice.

Me yasa qaddarorin qulluwar aure suke ta yawo a kanta cikin qasa da
sati daya kacal?. Ta gama laluben hanyar gamawa da issue din wadancan matan?,yanzu
kuma sai ga wannan?.

"Idan dai har kina ganin zaki iya ja dame jadda ga fili game doki nan" Abu daya da
kawu yace da ita kenan ya miqe yana ficewa abinsa yana barin sabbin kudaden dake a
mazaunin sadakinta yashe a qasa.

ᎷᏬᎻᎯᎷᎷᎯᎠ ᎰᏬ'ᎯᎠ

"Hamma?......hamma?" Ya jiyo muryar amna dake cike da shagwaba tana
kiransa da alama nemansa takeyi. Wata iska ya zuqa me yawa yana dauke dubansa daga
saman furannin da yake kalla cikin balcony dinsa tun dazun,ya juya a nutse yana
fadin

"Am here lovy dovy". Dan murmushi ta saki tana qanqame paper din hannunta da wani
tsadajjen biro me garai garai,ta taka a hankali ta isa balcony din inda yayi tsaye
goye da hannayensa a qirji yana jiran isowarta.

"Hamma wajenka nazo" Tayi maganar hannunta boye a bayanta. Murmushi ya saki yana
mata nuni da daya cikin lausasan kujerun dake ajiye a wajen. Ta taka a hankali ta
zauna tana kallonsa da murmushi,fuskarta na nuna wani irin excitement
"Hamma.....zuwa nayi ka gayan favourite colour da kakeso a sawa matarka a
lefe......and then ka fadi dame dame zaa zuba?,lissafin anni ya qure,tace nazo na
sameka naji naka ra'ayin". Ido ya lumshe yana sakin murmushi,ya fuskanci sun
daukaki abunnan,da gaske suka dauki komai,kuma da alama gagarumin shiri sukeyi.

Dukkan abinda suka aiwatar shi ko daya ma baizo kansa ba,ya manta dasu
cikin ma hidimar neman aure,ko ita kanta yarinyar yana mantawa da zamanta sai idan
wani abu ya gilma ko sun tada zancan.

"I don't have anything to say......the choice is yours" Ya fada da tsararren accent
din nan nasa dake nuna gwanancewa wajen iya sarrafa harshe.

Murmushi sosai amna ta saki tana gyara zamanta cikin nuna doki

"Thanks hamma......bari na zabawa addana classy kaya" Ta dora hannunta saman paper
din ta soma zana list.

Da sauri yaja baya sanda yake yunqurin fitowa daga dakin,idanunsa akan
bibo wadda ta afko dakin kamar an tunkudota. Fadowarta dakin bai hana sabreen maida
kanta taci gaba da takawa zuwa cikin dakin a nutse ba.

Maganganun bacin rai ne fal zuciyarta da zataso amayarwa da kawu rufai
din,to amma tanata dannar zuciyartata saboda yiwuwar wanzuwar tata manufar.
Sassauta fuskarta tayi tana fuskantar kawun sosai idanunta cikin nashi

"Banda abun rufai......ai ba'a yiwa 'ya'yan yanzu dole......tunda dai yarinyar nan
tace batayi bataso ka qyaleta mana,gida cike fal da 'ya'ya......nan nan hadiyya
idan kace ita zaka bashi.....wallahi tsaf zaa katse karatun nan duk da
muhimmancinsa.....duk kuma yadda take sonsa....ai aure shine gaba da komai a wajen
yarinya". Tayi zancan tana jaddada masa muhimmancin maganar da kuma gaskiyar abinda
take fada. Hannu yasa ya kama habarsa yana dubanta

"Wato har yanzu dai ba zaki daina hali ba bibo?,kin saurari komai kenan?"

"Kaga rufai kada kayimin mummunar fassara.....saboda Allah don kawai yarinya ta
nuna batayi......na bada shawarar kada a shiga haqqinta saika nemi canzamin
magana?". Karon farko kawu rufai din yaji jikinsa ya sanyaya da bibo din,ya kalleta
sosai cike da mamaki

"Bibo"

"Rufai" Ta amsa masa da sunansa kamar yadda shima ya kirata da sunanta

"Bari kiji na gaya miki......sabreen suka nema ba wata 'ya cikin gidan nan ba..."

"Suka nema ko kuma ka nemo Mata?" Tayi zancan tana yada kanta gefe cikin salo na
watsa habaici.

Wata dariyar takaici kawu rufain ya saki

"Gwara ki fito kai tsaye ki fadi abinda yake ranki bibo......ki saurareni da kyau
kiji.......sabreen bani na nema mata miji ba.....farinjininta da qashin arziqinta
daga Allah ne,don haka bani da hurumin musanya musu da wata.....saiki dage da
addu'a kema Allah ya azurta taki 'yar da koda yaron mijin Sabrina ne". Maganar tayi
masifar sosawa bibo rai,harta kasa masa shuru sanda yake qoqarin fita daga dakin.
Ta saki shewa ta daki cinyarta

"Ahayye......lallai sai yau na sake yarda kai din dan kunama ne.....kuma ka cika
cikakken butulu......to bari kaji,ka tsallake yaranmu kaf ka tafi nemowa wancan
tsintacciyar magen miji saboda tsabar qwarewa wajen munafurci da
tsugudidi.....wallahi indai ina da rai na ci maka alwashin sai hadiyya ta auri
mijin daya kerewa na sabrin"

"Allah ya bada sa'a......ko mafarki kikayi hakan ta faru lallai kin cika me sa'a"
Ya bankada labulen ya fadi mata sannan ya juya abinsa zuwa tsakar gidan don ya
sarrafa kayan da aka shigo dasu din. Ta gefe daya ya dauki dukka maganganun sabreen
ya azasu akan mizanin abinda baida muhimmanci sam sam,saboda shi din yasan waye
muhammad jadda.....kuma duk inda takai ga kafiya da jin kanta to la shakka daidai
yake da zamaninta.

Idanunta ta lumshe tana qoqarin daidaita fitar numfashinta,yayin da
idanuwansu dukka su ukun yake zube a fuskar yayar tasu.

"Kiyi haquri adda" Haneefa dake tsaye sosai a gaban sabrin din ta fada fuskarta
kamar zata saki kuka. Duk da ba komai ta fahimta ba,amma kusan ta saba da hayagagar
kawun,wanda duk sanda ya yita cikin falon nasu to wani fada ne ko tashin
hankali......tun bata fahimta har ta gane komai sannu a hankali.

Cikin zuqar numfashi daya ta dawo da dukka jarumtarta tana sake gayawa
kanta. Ita din 'yantacciyar 'ya ce.....ba property din kowa ba ballantana a ajiyeta
a sanda akaga dama a inda kuma akaso.....sannan a janyeta ko a sauyata a duk sanda
buqatar hakan ta taso.

Murmushi ta saukewa fuskarta,ta miqa tattausan hannunta tana shafar
kumatun haneefa din

"Komai bai faru ba auta.....ku koma parlor ku kunna tv,nasa an gyara muku receiver
din". Kai ta gyada a sanyaye,ta

Please Login or Register in order to submit comment