You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata. A tausashe yayi kissing goshinta yana dubanta.
Raunin da yake ganin cikin idanunta shi kansa baisan na meye ba,ya saka hannu da
kansa ya bude mata qofar motar dasu huda ke jiranta,ta shiga,ya tsugunna ya tattare
mata abayarta data fito waje ya maida ciki.

"Kada ka dade" Ta samu kanta da fadi masa a karye sanda yake shirin rufe mata qofar

"In sha Allah" Ya bata amsa yana jin dadin kulawa da damuwa dashi din data nuna,ya
rufe qofar a tausashe sannan yaja baya ya kira abdulgafar sukayi magana,ya kira
abdulbasit shima sannan ya sallamesu suka tashi motocin da zasu kaisu gida,ya rage
sauran wadanda zaiyi amfani dasu ne kawai.

Ta cikin side mirror din motar tasu ta zuba masa idanu,suna sakeyin
gaba yana nisa da madubin har ya bacewa ganinta,saita lumshe idonta tana sauke
nannauyar ajiyar zuciya.

Tana jin karadin su huda sanda suke fita daga airport din amma ta
gaza saka baki a hirarsu,kawai tana sauraren yadda zuciyarta take bugawa
ne.......har zuwa sanda qarar harbin bindiga har sau biyu ya sauka a kunnenta.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,hasbiyallahu la'ilaha illa huwa alaihi
tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ta fada da wata irin zabura tana ware
idanunta gami da miqewa ta zauna sosai faduwar gabanta yana ninkuwa.

Salatin da taja shi ya sanya kowa a motar ya dauke wuta,momma dake
seat din gaba ta waiwayo da hanzari tana kallon fuskar sabreen din. Huda ce tayi
qarfin halin fara tambaya

"Lafiya adda?".

" Qarar harbin bindiga huda......bakuji ba?" Ta tambayesu a rude tana raba idanunta
akan fuskarsu.
"Nidai banji ba" Huda ta fada tana girgixa kai

"Naji....harbi ne,amma kamar nesa da nan" Momma ta fadi tana dubansu daga inda take

"Nima naji momma" Nadra itama ta fada tana dubansu. Kan hanya hankalinta yakai,sai
taga kaman driver din nasu ya qara gudun motar fiye da yadda suka fara
tafiyar,hankalinta taji yana neman dagawa sosai,sai ta kalli su momma din tanajin
kaman haki yanason kamata saboda tsananin bugawar da zuciyarta takeyi.


*_Tabdijan.......meke shirin faruwa ne?,me kuke hasashe?,me karatu mu hadu gobe
idan me duka ya kaimu_*

*_akwai yaqi kenan_*



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862




𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³ 118


118



"Momma ba'a nesa harbin nan yake ba......koda a nesa dinne bawai ness
can damu ba......mun baro su hamma a ciki momma.....bamusan me yake faruwa
ba.....driver!" Ta ambata da qarfi kaman numfashinta yana son qwace mata.

"Yes madam" Ya fada da dan qarfi shima yadda zata iya jiyoshi.

"Mu koma mu duba boss......qarar harbi nakeji".

" Am sorry maaa.......nima naji,kuma umarni ne na boss din shi ya horemu,duk sanda
mukaji abu irin wannan kada mu sake mu koma da baya......kuma ko a tsarin tsaro ma
hakan ganganci ne.....kiyi haquri mu qarasa gida.....we are safe in sha Allah".
Yana kaiwa qarshen maganarsa qarar wani harbin a jejjere har guda biyu ya sauka a
kunnensu. Qarasa gigicewa tayi gaba daya,jikinta da muryarta gaba daya suka dauki
rawa.

"Ta cikin airport dinnan ne momma.....idan safe nake hamma fu'ad fa?" Ta jefawa
momma tambayar cikin rauni hawaye na gangaro mata.

Girgixa kai momma tayi wadda ke qoqarin boye nata tashin hankalin.

"Bazaiyiwu a koma ba kaman yadda kika ce.....hasalima baki da tabbacin a inda suke
abun yake faruwa ko wani shiyyar ne na daban.....koda a inda suke ne ma shima
bazaiso ace koma meye ya hada dake ba....." Momma take fadi cikin son lallashinta.
Sam hankalinta ba'a jikinta yake ba,bata ma kama maganar momma ba saita jawo
jakarta jikinta dukka yana rawa ta fiddo wayarta tana cewa.

"Gabana yanata faduwa ne momma,tabbacin akwai wani abu da ba daidai ba" Tayi
maganar tana zaro wayarta da zummar kiran number fu'ad din.

Abun takacin abinda kuma ya sanya a karan farko tayi Allah wadai da
halinta shine. Ba number wata number da tayi kama da tasa cikin contact dinta,sai a
sannan ta tuna,waccan tafiyar da yayi ya kirata sau daya,batayi saving number nasa
bama,kuma koda ta duba call log babu number a wajen.

Kuka ne ya qwace mata ganin yadda suke qara nisa da airport din ba
tare da tasan halin da yake ciki ba.....don gaba daya jikinta yana gaya mata akwai
gagarumar matsala.

"Ni ku saukeni......xan koma na dubashi,zan tabbatar da lafiyarsa saimu taho tare
dashi" Ta fada muryarta na rawa.

"Kiyi haquri madam......aikina bazai cika ba saina kaiki gida lafiya.....aikata
hakan zai zama zunubi mafi girma a wajen boss,har gwara na kaiku gida na miki
alqawarin dawowa na duba miki lafiyanshi". Abdul rauf ya bata amsa shima yana jin
damuwa sosai da fargabar kada wani abu me muni ya faru da ogansu.

Sam bata gane abinda momma ke fadi mata ma,ta rarumo wayar ta soma
lalubar number anni ko amna. Number amna ta fara gani saita kira kawai tana fatan
ta samu su daga don su suna motar gabansu. Bugu daya aka daga,anni ce ba amna
ba,kai tsaye ta fara magana.

"Anni harbi akeyi cikin airport anni.....kice musu mu juya mu koma,munbar hamma a
can,dukkanmu mun taho saura shi kadai". Asalin damuwa anni tana ciki,amma ta danne
don kada ta kashe mata qwarin gwiwa.

"Kiyi haquri sabreena......in sha Allah yana lafiya,don bamusan me yake faruwa
ba,da mutane da yawa a ciki bamusan akan meye harbin ya kasance ba....."

"Anni jikina yana bani wani abu.....anni don Allah ku barni na koma"

"Ameenatu" Anni ta kirata da asalin sunanta.

"Na'am anni".

" Kita karanta lahaula walaquwwata illa billah.......bari mu qarasa gida saimu
laluba abinda ya faru kinji?". Ba yadda zata iya ci gaba da musu da annin,don haka
tace mata to kawai tana sauke wayar daga kunnenta ba tare data kashe ba.

Hannu momma ta miqa ta dauki wayar suka fara magana da anni.

"Ta shiga damuwa,don Allah bahijja ki bata baki,kinga ba ita daya bace,a irin
wannan yanayin bata buqatar tashin hankali".

" In sha Allah anni" Daga haka ta ajiye wayar ta kamo hannun sabreen din.

Duk wani kalar bada baki da bada haquri momma ta yiwa sabreen
din,saidai kawai tana jin momma dinne bawai don ta gamsu da dukka abinda suke fada
ba,tana ji a jikinta akwai wani abu maras kyau daya taba hammanta,a cikin zuciyarta
da ruhinta takejin hakan.

Yadda anni taji muryarta ya sanya tayi ma abdur ra'uf magana dukansu
suka wuce zuwa mansion House din alhaji hamza kibiya.
A babban parking lot na gidan motocin dukka suka tsaya. Abdulgafar ya
qaraso ya bude mata side dinta,su huda da momma suka fita ta daya side din.

Da qyar ta miqe bayan ta zuro qafafunta waje,jikinta idanunta dama
zuciyarta gaba daya takejin sun mata wani irin nauyi. Duba daya zakayi mata ka
fahimci hankalinta baya jikinta,daga airport din zuwa gidan kuwa idanunta sun fara
tasawa saboda kukan data matsawa kanta dashi. A hankali da wani irin sanyi ta zube
idanunta akansu anni wadda ke tsaye ita da musaddiq da saddiq,dukkansu su biyun
waya sukeyi,amna kuma da alama tanata qoqarin samun wata number ne amma kiran yaqi
shiga.

"Anni na kasa samun wayarsa,a kashe take" Muryar amna kenan data sakata jin wani
jiri yana niyyar kayar da ita. Baya ta koma kawai ta jingina da motar data fito a
cikinta,tana jin momma sama sama tana riqe hannunta.

"Na samu Jordan" Muryar saddiq kenan daya fada da wani irin kuzari,abinda ya sanya
anni da su amna duka dawowa gabansa suka tsaya.

Dif sukayi suna jiran joradan ya daga,amma harta qaraci ringing dinta ta
katse bai daga ba. Idanu sabreen ta mayar ta lumshe,tana jin yadda bayan wucewar
kowanne daqiqa zuciyarta ke ninka gudu kaman zata tsaga qirjinta ta fito,tana jin
wata sallamawa tana ratsata,tana jin cewa da gaske wani abu ya taba mata
hammanta......da gaske wani abu ya faru dashi cikin airport din,sai qafafunta suka
fara rauni tana jin suna fara gazawa wajen dauke nauyinta.

A kunnenta kira na uku ya yanke ba tare da jordan ya daga ba.

"Wallahi shine.....Allah wani abun ya faru dashi.....naji a jikina fa" Ta fadi da
qarfin muryar da har na nesa saida suka jiyota,wanda kafin su huda sukai ga riqeta
ta sulale a wajen tana sakin wani tsumammen kuka tana jin mararta na riqewa gam.

Da wani irin sukunannen gudu anni ta qaraso,suka dagata ita da momma
Hankalin annin yana tsananin tashi.

"Karkiyi mana haka sabreen......ba abinda ya faru dashi mana.....ga jordan nan an
samu wayarsa dagawa ne baiyi ba". Idanunta fal da kuka wadanda zuwa yanzu sun canza
launi zuwa red ta kalli anni.

" Indai da gaske lafiya qalau ne ya daga wayar yayi bayani mana?,ya daga wayar yace
ba abinda ya faru mana anni?,me ya hana wayar hamma shiga bayan sanda muka fito a
jirgi ma ya amsa kira?". Rudata kawai tambayayoyin sabreen sukayi gami da sage mata
gwiwa,saita rasa amsar bata. Duk da haka ta rungumota jikinta tana cewa.

"Amma kamar fatan alkhairi ya kamata kiyi ko sabreen da hasashen alkhairi?"

"Na kasa anni.....zuciyata ce taketa gayamin akwai abinda ya faru dashi,ba laifi na
bane......DANGANTAKAR ZUCIYA ce tsakanina dashi.....ko meye ya sameshi zuciyata
zata gayamin saboda alaqar dake tsakaninmu" . Sosai anni ta lura kaman hankalinta
yana neman gushewa ne,don haka ta sake riqeta da kyau tana cewa.

"Shikenan,mu shiga ciki,zan tabbatar miki lafiya qalau yake.....zan kiramiki shi
kuyi magana". Tamkar raguwar ciwo ko zugi daga kasu daya cikin dari shine kawai
d'an abinda furucin anni ya yiwa sabreen cikin zuciyarta. Anni da momma suka riqeta
da kyau kowa cike da fargaba duba da abinda yake jikinta tattali yake buqata kaman
yadda tun a madina likita ya gaya musu suka wuce da ita zuwa ainihin babban falon
gidan.

Baya kadan anni ta dawo tayi magana da saddiq kan yayi duk yadda zaiyi
ya samo ainihin abinda ya faru sannan ta kira musaddiq suka wuce akan yazo ya zauna
yayita kiran fu'ad har sai an sameshi ya daga suyi magana ko hankalinta zai kwanta.

Kaman yadda hawaye yaqi tsaiwa a idanunta haka ma kuka yaqi dakatawa.
Ruwa me sanyi sanyi anni ta saka aka kawo Mata,ta tsiyaya mata ta miqa mata tana
fadin.

"Karbi kisha tukunna ko zuciyarki zatayi sanyi" Kai ta girgiza kawai fuskarta shabe
shabe da hawaye,abinda yake taba zukatan su huda kenan har sai da anni ta sanya
ma'u ta janyesu zuwa wani falon na daban.

"Ko nasha anni bazai iya wucewa ta wuyana ba.....inaso nasan halin da yake ciki ne
kawai". A sanyaye musaddiq daya gaji da kira ana ce masa a kashe take ya dubeta,sai
kawai ya ajiye wayar ya miqe tsam.yana duban anni

"Ina zuwa" Ya fada yana fita da sassarfa daga dakin. Kiransa anni takeyi saboda
jikinta ya bata abinda zai aikata daga yanayin tashin nasa,amma baiko waiwayo ba
bare ya dakata.

"Innalillahi wa inna ilahi raji'un" Anni ta fada tana sadda kanta qasa. Awa guda
kenan amma ko daga security dinsa da guards dinsa ba wanda ya samu labarin abinda
ya faru. Sun koma airport din amma tun daga tafiya me nisa ma an hana shiga gurin
bare su binciki abinda ya faru.....ina yake?,wanne hali yake ciki?. Duk da sun
bayyana kansu a mazaunin masu tsaron lafiyarsa amma an dakatar dasu an kuma basu
haquri ance su jira,ko meye ake ciki daga baya zasuji.

Zamewa tayi sosai a nan inda tayi sallah tana kukan zuci,tana jin kamar
zata hadiye zuciyarta. Batasan ta inda zata fara rayuwa ba idan wani abun ya samu
Muhammad........batasan ta yadda zata iya karbar wannnan qaddarar ba.

Me yasa rayuwa zatayi mata haka ne?,me yasa rayuwa zata zo mata da
irin wannan yanayin ne?,me yasa rayuwa take wasan kura da ita?,take nesantata da
wadanda ta sanya rai da fata me tsanani a kansu?,take nesantata da duk mutumin da
zai jibanci lamarinta?,duk mutumin data dora rayuwarta da burinta a kansa?.

A nan tayi la'asar ba tare data ko motsa ba,anni tasa aka shigo mata
da abinci amma ko sha'awa baya bata ballantana tayi tunanin ci.

Xuwa qarfe biyar ta koma tamkar ruwa saman abun sallar,zuciyarta na
sake yayyankewa da tsananin tsoro da tashin hankali.

Biyar da mintuna anni ta sake shigowa. Duba daya zaka mata itama kasan
hankalinta ba'a kwance yake ba. Musaddiq da saddiq da baisan fitarsa ba har yanzu
bai dawo ba,hakanan tasa wayar still tana kashe shima tunda ya fita yabar gidan.

A sanyaye ta qaraso gabanta tana qoqarin tattaro dukka dauriyarta waje
daya,ta zauna a qasa daidai saitin qafarta tana kallonta.

"Tashi ameenatu" Anni ta fadi cikin jarumta. Kaman ba zata iya tashi ba ta daddafa
ta tashi. Amanta uku ba wanda ya sani,abinda ta dauka tayi adabo dashi tunda ta
samu kulawa a madeena sai gashi tashin hankali ya sanya ya dawo. A cikin aman nan
guda uku ba kalar azabar da 'yan hanjinta basu gani ba,don babu komai a cikin nata.

"Kinyi imani da Allah da ranar lahira?" Kai sabreen ta gyada mata hawaye na fara
taruwan mata.

"Kinyi imani da Allah shine me rayawa shine me kashewa?,shike bada kariyarsa akan
kowanne abun halitta?". Kai ta sake gyada mata hawayen data riqe suna sauko mata.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 119


119


" To inaso ki yarda da Allah ki kama ambatonsa....kibar masa kuma
lamarinsa.....karki dauki haqqin abinda ke kwance a mararki ta hanyar hana kanki
abinci.....don cin abincinki ko rashin cin ba abinda zai canza saima cutar da
yaronki,ki samu wani abu ko ba yawa ki sakawa cikin naki". Hawaye sosai take tana
kada kai.

"Ba hanya anni.....bana jin abinci xai samu hanyar wuce kwata kwata".

"To ai akwai abu me ruwa ruwa a ciki,ki duba ko yaya kisha" Ta fada tana buda
kwanukan gabanta.

Lafiyayyen kunun gyada ne da yasha madara yayi fari sol,da kanta anni
ta zuba mata a mug ta saka sugar dan daidai sannan ta miqa mata.

Karba kawai tayi tana wassafa yadda zata sanya a bakinta,kai.anni ta
jinjina mata cikin son bata qwarin gwiwa,wannan ya sakata kai mug din bakinta.

Kurba uku kawai tayi ta dire,annin bata matsanta mata ba ta dauka kawai
ta rufe ta bata ruwa. Kurba daya shikam ta ajjiye,saboda batajin zai zauna a cikin
ta. Bakinta ya saba da zartsin zartsi na taste din zam zam. Annin ta fahimci
haka,don haka ta qwalawa ma'u kira tace ta duba store ta ciro zam zam babban roba.
Ba jimawa ta dawo dashi,annin ta bude ta tsiyaya ta bata.

Wannan karon anci sa'a,tas ta shanyeshi ta ajiye cup din,hakan ya yiwa
anni dadi,saita matsa ta dauki counter tasbaha ta maqala mata a yatsunta

"Hasbunnallahu wa ni'imal wakil,wallahu galibun ala amrih sau ba adadi" Kai ta
gyada a hankali tana jin hankalinta yana karkata ga addu'a maimakon kuka da bala'in
tashin hankalin da takeji.

Sai da anni taga ta kama sannan ta miqe a hankali ta nufi qofar ta fita
tana rufe mata da nufin dawo dasu huda ciki su tayata zama.

Fitar anni da second talatin kadai wato rabin minti taji kamam muryar
musaddiq cikin kunnuwanta. Sakin counter din tayi ta miqe qirjinta na wani irin
mahaukacin bugu,cikin sanda kaman barawon daya shirya gagarumar sata ta nufi
qofar,ta kamata ta bude a hankali,sai muryar musaddiq din ta fito tas.

"Muje ka gayan me ya faru,koma meye banaso sabreen taji" Taji anni tana fada.

Sakin qofar tayi a hankali ta fara takawa tana biye da bayan annin,duk
da cewa akwai ginin hallway daya rabasu basa iya ganinta amma ita tana iya jinsu
sosai,cikinta hautsinawa yakeyi sosai,tana cike da tashin hankali da fargabar
abinda zataji daga bakin musaddiq din.

Hannun musaddiq kawai anni ta kama kai tsaye ta ajeshi saman kujerun
da suke matsakaicin falon,tashin hankali da rudani sunaso suyi galaba a kanta amma
tana cinyewa.

"Gayamim musaddiq......ina fu'ad.....ina me babbban suna?" Shuru ya danyi,yana juya
yadda zai bata incomplete information,saidai shirunsa zaifi zame mata damuwa sama
da amsarsa

"Sun harbeshi" Ya fada a hankali kaman bakinsa bayason fada.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Anni ta shiga maimaitawa. Wani irin bugu
maganar ta yiwa sabreen,abu na farko daya fara zuwa kanta shine SUN KASHESHI.

Nutsuwarta da hankalinta ne gaba daya suka fara gushewa,sannu sannu
saita fara daina jin abinda musaddiq yaci gaba da fada.....duhu ya fara gilmawa
idanuwanta,ta suma sulalewa a wajen ta zube saman rug din.

"Harbin farko ya kauce basu sameshi ba,ya hangi maharbin sai yayi nufin binsa shine
ya sameshi a harbi na biyu dana uku......suna tare da yaa farouq,tare ma suka
yunqura suka bishin,amma yanxun ba'a ga ya farouq ba,ba'asan ina yayi ba.....shi
kansa hamman da jordan dinma ba'asan ina akayi dasu ko yaya akayi dasu ba" Ya
qarasa fadawa anni maganar zuciyarsa tana girgiza.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Taci gaba da maimaitawa tana jin zuciyarta na
wani irin jijjiga kaman zata ballo daga qirjinta ya fado.

"Musaddiq ina abbanku?" Ta tambaya saboda tana jin duk wata jarumta tata da
dabararta ta qare,tana buqatar tallafin abban a kusa.

Kaman yasan shi take nema sai gashi ya sako kai,kai tsaye ta miqe ta
nufeshi,bata kuma tsaya bata lokaci ba ta fada qirjinsa hawaye yana sauka daga
idanunta,wani abu da bata taba yi ba gaban yaran tsahon shekarun.

"Ya isa ameenatu.....kiyi haquri.....duk inda suke da halin da suke ciki za'a
samosu in sha Allah,karki daga hankalinki da yawa,idan hakan ya faru ita kuma
sabreen muyi yaya da ita kenan?". Kiran sunan sabreen din ya ankarar da ita,ta
janye jikinta daga abban gabanta yana faduwa. Sai sannan ta tuna tayita maimaita
innalillahi da qarfi a dazun,wanda zai wahala baikai cikin dakin da sabreen din
take ba.

"Bari na dubota abba" Ta fada tana juyawa da sassarfa tana nufar ciki.

Tuntuben da tayi da ita shi ya sakata taja baya da sauri,kasa jurewa
abinda idanunta suke gani tayi,sai kawai ta saki qara tana kiran sunan abba a
gigice.

Shima ya kadu da jin qararta,wani abu da bai taba ji ameenatu tayi ba
komai girman jarrabawa,don haka da sauri yayo hanyar dakin musaddiq yana biye
dashi.

"Maza jeka kira mommanta.....kada ka bari yaran su biyoku" Abba yace da musaddiq
saboda a yadda anni ta gigice yasan ba zata iya riqe sabreen ba.

Ba shiri momma data tayar da sallar la'asar din da bata samu daman yi
ba sai sannan ta sallame tabi bayan musaddiq. A gigice ta duqa gaban sabreen tana
dagata,saidai ba wani alamun numfashi a tattare da ita.

"Nutsuwa zakuyi ku taimaketa ta hanyar daukota mu wuce asibiti da ita" Abba yayi
qoqarin dawo musu da tunaninsu jikinsu.

Kaman gawa haka suka dagata,suka wuce kuma kai tsaye bakin farfajiyar
shigowa gidan,don tuni musaddiq ya sanya an matso da mota gaban ginin.

Makeken private hospital dinnan da babu kamarsa kaf Nigeria suka nufa
da ita wato Noor hospital. Idan ka shiga zakayi tsammanin kana qasashen qetare ne
bawai a Nigeria ba kuma gida kanon dabo.

Asibiti ne da yake mallakin Muhammed fu'ad jadda.....amma a sirrance
mallakar ta kasance,ba kowa bane yasan da hakan. Duk wani kalar kayan aikin da bamu
dashi sai a qasashen qetare ya kawosu ya zuba don hana masu kudinmu fita neman
magani waje. Donsu din kawai dama yayi asibitin,don babu wani me qaramin qarfi da
zaiyi gigin kai kanshi nan. Saidai kuma kusan duka kudaden da ake samu ta asibitin
ana tafi dashi ne ta hanyar hidimar al'umma,don baya ci ko karban ko sisi a
ciki,saboda baida buqatarsu.

Dr hajar da Dr mubeena ne suka karbeta,don ba wani likita namiji da
yayi kuskuren zuwa inda take,duk da dama kusan haka tsarin asibitin yake,mata
likitoci mata ke karbarsu,maza kuma likitoci maza.

Cikin qwarewa suka shiga bata taimako don maido numfashinta kan saiti
gudun rasa abinda take dauke dashi,sun samu nasara saidai sun mata allurar bacci
saboda ta sake samun nutsuwa sosai,don ta shiga shocked ba kadan ba. Sunyi duk wasu
gwaje gwaje daya kamata,harda su scanning da basu tsaya anyi a madeena ba,saidai
abinda scan din yaketa nuna musu ya sanyasu a mamaki.

Hankalinta kwance take cikin dakinta tana ninke lace din data siya
jiya naira dubu dari tara da tamanin,ta kuma budeshi don ta tabbatar shi dinne.
Zuciya cike da saqe saqe da taraddadin cikar mission dinta da tafiyarsa daidai?,ko
kuma akasin hakan wato FADUWA wanda ko sunanta bata qaunar taji.

Har yanzu zuciyarta tana mata susa idan ta tuna fattatakar da bokan
yayi mata,sam yama qi saurarenta,wanda ita bataga dalilinsa naqin sauraron nata ba
bayan tana cika masa aljihu da kudi. Ta dora kyakkyawan zato akan hajja....duk da
tasan mutum ne shi da ba'a sakashi ba'a kuma hanashi......amma tana da zato me
girma akan hajja din,wannan ya sauya akalar tunaninta na taci gaba da riqon laila.

Zuwa yanzun lailan ya fara zame mata kaya,don ba wani abu da zata iya
aiwatarwa na qashin kanta saita tambayi maamah din. Daidai da cin abinci wannan sai
data fatattaketa,tace kada ta qara tambayarta don zataci abinci,taci ko kada taci
wannan ya rage nata.

Ko yanzun da akayi mata knocking sai data ja tsaki,tasan bazai wuce
laila din ba,don cikin masu aikinta ba wanda ya isa ya qaraso nan wajen sai idan
ita ta nemi ganinka.

"Waye?". Ta tambaya cikin 'yar qaramar fusata.

" Laila ce".lailan ta fada jiki da muryarta dukka suna rawa. Har ta bude baki zata
koreta,sai kuma taji kaman akwai raunana a muryarta don haka tace

"Meye kuma?,kinsan banason damu ko?".

"Kiyi haquri.....wani abu ne ya faru nazo nuna miki,nima yanzu naga an sakashi a
page din jaridar breakers".
"Shigo" Ta bata dama kai tsaye tanason jin me tazo dashi.

Sanda ta shigo jikinta yana rawa ta miqa mata wayar hannunta. Hannu ta
sanya ta karba cikin yamutsa fuska sai kuma ta waro idanunta dukka waje.

"AN KAIWA SHARARREN MATASHIN ATTAJIRIN NAN FARMAKI A FILIN TASHI DA SAUKAR JIRAGEN
SAMA HARI WATO MUHAMMAD FU'AD JADDA.....HARMA ANA KYAUTATA ZATON
BACEWARSA.....YANZU HAKA BA'ASAN INDA YAKE BA". Sake qarewa rubutun kallo tayi da
kyau,ta maimaita rubutun ta sake maimaitawa sai kuma murmushi ya subuce mata duk da
zulumin daya cika wani sashe na zuciyarta.

"Lokacin tarwatsewarki ameenatu yayi.......tabbas wannan itace dama ta ta farko a
kanki kafin na isa ga dama ta biyu na qarasa murqusheki.....na kuma jefa rayuwarki
data ahalinki cikin halin ni 'yasu" Tayi maganar a sararin tana jin dadin samun
wata gwagwgwabar dama da ta sameta ta sassauqar hanya.



Please Login or Register in order to submit comment