You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta
fada din bane da gaske har zuciyarta.

Da dariya ta qyalqyale sosai,farinciki yana cikata,lallai laila dinta ta
dawo,ta dawo hayyacinta.

" Na godewa Allah daya dawomin dake hayyacinki laila" Murmushin qarfin hali ta
sakarwa hajjan,tanason ta sake bata tabbaci da yaqinin ta warke don ta ware mata
takunkumin hana fita da sanya masu gadi su hanata fita ko nan da can. Ba abinda
takeso irin taje wajen maamah,ta duqufa tayi ta mata bauta iyakar qarfinta.

"Na warke hajja in sha Allahu,kawai zaman cikin gidan nan ne hajja na gaji.....ko
cikin layinnan kya barni na tattaka da qafafuna ko?" Ta fada a shagwabe kaman yadda
take mata a baya.

Fuska hajja tadan bata tana dubanta.

"Aah......ba yanzu ba laila,matar nan makira ce,duk da ance tana can tana jinya
amma ba Allah a ranta,kina kallon yadda take kidnapping 'ya'yan jama'a fa?" Hajja
ta fadi tana nunawa laila girman ta'addancin maamah.

Wani irin tashin hankali da kuma bacin rai ne suka bijirowa lailan,ta
tabbatar yau ko gobe Hajja ba zata barta ta fita ba bare ta koma wajen maamah,kenan
ba amfanin rayuwarta ba tare da maamah ba?". Ta yiwa kanta wannan tambayar.

A take taji indai za'a yanke alaqarta da maamah bata da wani amfanin
rayuwa,don haka ta miqe tsam.

"Bari naje kitchen nasha ruwa"

"Ki tahomin dashi" Ta fada hankalinta kwance don tasan a kitchen din dai ba wata
hanyar fita daga sassan ma bare akai ga gidan.

Idanu kawai take warawa sanda ta shiga kitchen din,gaba daya kwanyarta a
birkice take,neman abinda zatayi amfani dashi kawai take yi idanunta suka sauka kan
gas.

Da sauri ta qarasa wajen,ta saka hannu ta kunna dukka makunnansa guda
hudun da yake dasu. Fita ya fara yi sosai,kafin kace meye wannan warinsa ya mamaye
kowanne sashe na part din hajjan.

Hancinta sosai hajja ta dinga budewa tanason tabbatarwa warin gas dinne?.
Da wani irin sauri ta duro daga saman gadon tayi kitchen da mugun sauri. Duka masu
aikinta ba kowa yau ballantana tayi tunanin wani ne a cikinsu,laila kawai tasan ta
shiga kitchen din.

Cak ta tsaya daga bakin qofar falon,qafafuwanta suna rawa zuciyarta na
wani irin gudu mara fasali. Laila ce tsaye a kitchen din riqe da lighter,idanuwanta
fes kan hajja dake tsaye daga can bakin qofar kitchen din.

"Laila.....laila baki da hankali ne!!!" Hajja ta fadi a birkice ganin lailan tana
qoqarin motsa yar robar data tare bakin lighter din wadda ita zata bata damar
tashi. Wani kalar murmushi ta saki tana duban hajjan

"Kina tunanin zan iya rayuwa ba tare da umarnin maamah ba?,ko kina tunanin zan iya
rayuwa a inda babu ita?.....sai watarana hajja" Laila ta fada cikin qwarin gwiwa.

A gigice hajja ta bude baki tana son gaya mata cewa.

"Kada ki kunna laila.....indai mariya c na bar mata ke har abada,ki hada kayanki ki
koma gareta" Saidai dukka wadannan kalaman basu samu damar fita daga bakinta ba sai
hucin tsananin atsabar zafin wuta da qarar bindigar fashewar tukunyar gas din da
suka cakude waje daya aka wullota waje,wanda daga nan bata sake sanin abinda yake
faruwa ba.

Qarar fashewar taja hankalin sassan matan 'ya'yanta da masu gadi dake
waje,kafin balbalin wutar ya tashi hankalin kowa suka nufo sashen hajja din.

Duk saurinsu turus kowa yayi,saboda wata irin muraddiyar wuta ce me
azabar duhu da Zafar tana harshe ke cin kowanne sashe na hajja din. Babban sashe da
yafi na kowa cikin gidan girma kyau da tsaruwa,sashen da idan ka kalleshi ka kalli
na matan 'ya'yanta saika dauka su din duka sashen ma'aikatan gidanne wato boys
quarters,duk kuwa da cewa mudin na mazajensu ne,dasu akayi wahalar nema da kuma
samu.

Tashin hankalinsu waye da waye a ciki?,suna tsaka da son tantancewa
sukaci karo da hajja yashe a qasa,wadda babban jikanta ne kawai ya iya gane
itace,saboda shi dinma ya shiga dazu kai mata wankinta ya gane atamfar
jikinta,fuskarta kaf da kafadunta zuwa qirjinta sun koma jazur kaman an shafeta da
jar hoda saboda yadda wutar ta kwaye asalin fatarta.

"Na shiga uku......wayyo Allah na..... Wayyo laila......laila kada ki mutu ki
barni......laila bansan kanki abunnan zai koma ba,wallahi laila bake nace a bawa
kici ba......laila don Allah ki fito laila......naci buri a kanki,na shiga uku"
Sune maganganun data dinga fada tana ihu tana kururuwa gami da zabura,azabar zuciya
dana gangar jiki duka sun isheta aka wuce da ita asibiti cikin ambulance bayan anyi
kiran fire service suzo su tsaida watar kada ta soma lasar sassan gidan.

Abun kamar film kamar almara,ana fita da hajjan sanda wutar ta cinye
sassan sarai,surukanta dukka dake tsaye a wajen sai kowacce ta dafe kanta.

"Wayyo Allahna.....wash Allah na.... Wayyo kaina" Shine abinda suka fara fadi a
jejjere,kafin kace meye wannan sai gasu duka su ukun a zube warwas a qasa sun sume.

Akwai wani malamin makarantar almajirai dake a wajen,kallo daya yayi
musu yace basai an kaisu asibiti ba,babban falon gidan yasa aka ajiyesu,ya karbi
ruwa yayi musu tofi sosai ya bawa mazajensu yace a yayyafa musu idan sun farka a
bawa kowacce tasha.

Cikin qasa da minti biyar sai gasu a zaune,kowaccensu kuka takeyi
wiwiwi

"Wallahi saika sakeni......wallahi bazan sake zaman bauta ba..... Idan ta dawo kuma
me ya rage mata?,inajin sujjada zata saka mu koma yi mata" Shine abinda matan
kowacce ke gayawa mijinta cikin kuka. Duka falon sai ya rikice,ga gobara a waje ga
tashin hankali a cikin gidan,su kansu mazan a rude suke,don sam duka abinda matan
ke iqirari akai ba wanda yasan anyi a ciki.

Gyaran murya malamin yayi ya kuma nemi su bashi hankulansu. Bayani ya
musu me ratsa jiki game da lamarin,kusan abune da kaf unguwar ake magana akai yadda
take bautar da uban kowa cikin gidan,kusan duk me hankali yasan aikin sihiri ne.

"Indai har zaku yarda da shawarata ku yafewa mazanku,ku sake sabon zama dasu don ba
cikin hayyacinku dukka kuke ba,wataqila wannan gobarar ta qone duk wani binne binne
ne shi yasa komai ya warware kansa.....sai ku bita da addu'a Allah ya bata lafiya
ya sake fahimtar da ita ainihin rayuwa.....". Da wannan bayanin nasa ya kashe
wannan qurar,hankula kuma suka koma kan wutar dake ci wadda an fara samun daman
kasheta.157


★Tana kwance saman kyakkyawan gadon,sanye da fara qal din abaya har
veil din da tayi rolling dashi,kaman yadda siraran abun hannun azurfa da zobensa da
set din dan kunnensa suka sake qawata mata shigar tata.

Duk da tsufa da nauyi da cikinta yayi hakan bai hanata ado ba......duk
da yadda take komai da qyar amma bata yarda ta bari tayi mummunan kama ba.

Ko a yanzunma akan gadon scanning take,daga daidai kanta kuma muhammad
fuad jadda ne. Sanye yake da farar jallabiyya ta maza saqar morocco wadda ya yiwa
ado da farin hirami daya zauna sosai a kansa,saika rantse da Allah dan asalin qasar
saudiyyan ne. Wani irin ajiyayyen kyau na musamman shigar tayi masa,jikinsa da
fatarsa dukka suna nuna zallar hutu da jin dadi gami da cikakken sukunin rayuwa da
Allah ya bashi. Saman kujera hake,hannunsa cikin tsakiyar tafin hannunta,ya sarqafe
yatsunta cikin nasa.

Daga shi har sabreen din idanuwansu suna kan allon computer
din,wanda balarabiyar ke yawo da kan na'urar saman cikin sabreen din da yayi wani
irin girma.

Sai data kammala scan din tsaf,sannan ta dora hannunta saman board din
computer ta danna tana maidashi 3D scan gami da cewa cikin harshen larabci.

"Sa'ureekum shai'an" Ta fada tana murmushi.

"Na'am" Ya fada yana matse hannun sabreen cikin nasa. Maida mouse din tayi saman
cikin sabreen din,ta matse hoton cikin take yara guda uku suka fito sosai.

"Allahu akhbar.......subhanallah" Fuad ya fada muryarsa tana rawa. Damqe hannunsa
sosai sabreen tayi itama cikin nata,ta kasa magana kaman yadda fuad shima ya kasa
cewa komai face tasbihi ga Allah buwayi gagara misali. Yaran na kwance irin
kwanciyar jarirai uku cikin mahaifiyarsu,kamanninsu sosai ya fito,har ya dinga jin
kaman ya saka hannu ya daukosu.

Cikin qwarewa take juya na'urar tana zoom in musu yaran daya bayan
daya. Qosassu kuma lafiyayyu ko a ido,wanda ko daga yanayin girman cikin sabreen
din shi kansa yasan qosassunne,duk da akance abun ba daga girman cikin bane.

Murmushi ya subuce masa wanda ya taho da taruwar hawaye cikin idanunsa
ganin daya daga cikin yaran da tayi zoom in din babban yatsansa na cikin bakinsa
kaman me shan hannu.

"Astgafirullah......alhamdulillah......subhanallah walhamdulillah wallahu akhbar"
Abinda ya dinga fadi kenan,yana jin kaman kada ta daina nuna masa fuskokinsu,saidai
kuma dole saboda ayyukan da suke gabanta.

Sauke na'urar tayi itama murmushi yana qwace mata,ita kanta yaran sun
burgeta,ta kuma jima bataji jariran da taji tanason ta gansu fuska da fuska ba irin
yaran. Bata sani ba,ko hakan yana da alaqa da yadda ma'auratan suke burgeta?.

Zata iya cewa tsahon shekarun aikinta,taga spouse kala kala,amma ba
wadanda sukafi burgeta tare da qara mata son yin aure a kurkusa irin sabreen din da
fu'ad. Da fari ma ita sam bata yarda daga nigeria suke ba,na farko dukkaninsu
sunayensu batayi tunanin akwai masu irin sunan a bahaushiyar qasa ba,na biyu kuma
yadda fatarsu keda wani irin haske da kadan tasu ta dara nasun,uwa uba yadda
sukejin labarin Nigeria da yadda 'yan qasar suka zubda kansu a qasar saudiyya yadda
ake binsu ana kamesu kaman kaji ko awaki,bata dauka akwai mutane masu qayatarwa da
burgewa kaman wadannan mutanen ba,sam bata zaci zaa samu mutum irinsu a Nigeria ba.

Hannun sabreen kawai ya juya ya dinga kissing,har sai da dariyar
likitar ta dakatar dashi.

Da kansa ya taimakawa sabreen din ta zauna sannan ta miqe tsaye,ya
gyara mata rigarta da mayafin saman kanta,sannan ya taimaka mata ta zauna saman
kujera tayi relaxing sosai,daidai sanda likitar ta dawo dauke da takardu zuwa
gabansu.

"Cikinta yanzu haka yana sati na talatin da uku,kuma yawanci 'yan uku bama bari su
haura sati na talatin da hudu saboda nauyinsu......don haka ina tunanin mafi kyau
sati me zuwa ayi mata CS a ciresu". Murmushi ya sake kubce masa,wannan nesar tazo
kusa kenan,wannan lokacin na haduwa da yaranshi yayi kenan. Already sun yanke ayi
mata CS din,saboda haka kawai yake tsoron tayi naquda,gani yake kaman zai
rasata,tun randa sukazo anti natal suka samu wata mace ta rasu gurin haihuwar twins
dinta. Koda ya shawarci sabreen din bata qi ba,don ita don ta ita bata da wani
zabi,kome ya yankewa rayuwarta tasan bazai cutar da ita ba. Likitar kuwa dama kai
tsaye ta gaya masa cewa.

"Ba kasafai muma muka fiya so ko barin me haihuwar fari triplet ta haihu da kanta
ba,akwai risk,CS is the best idan har ma'aurata sun amince.

"Ba matsala,Allah yasa ayi a sa'a.......a turamin komai da asibiti keda buqata na
komai da komai din,zamu shirya zuwa sati dayan in sha Allah".

"To yayi.....zaku zo a day kafin ranar aikin,don bayan asuba koda sassafe zamu
shiga da ita".

Shi da kansa yayi driving nasu dama zuwa asibitin,yanzunma shi
dinne,don wannan karon kwata kwata daga Jordan dan amanarsa sai abdulgafar,da iya
mutanen daya taho kenan.

Wani rayuwar 'yanci yake abinsa cikin garin madeena,kusan kullum saisun
fita shida ita,strolling ko a mota,suci abinci su dawo gida bayan sun zazzagaya
garin. Ya lura yadda yake qaunar madeena haka ita dinma,yanayin garin da calmness
dinsa yana sakata nutsuwa sosai ya lura da wannan,don haka a yawan lokuta ma ba
hira suke ba,suna tafiya ne kawai a low speed tare da madaidaiciyar qira'ar daya
daga cikin malamanmu na addini,sai kaga duk jikinta yayi weak wani kwanciyar
hankali tana ratsata.

Yanzunma hakan yayi mata,saidai suna fara tafiya tace

"Hamma"

"Na'am adda sabreen" . Yadda ya fada din ya sakata sakin murmushi,muddin zata ce
masa hamma,to shima fa zaice mata adda sabreen.

"Umra nakeso nayi......". Kallonta kadan yayi sannna ya maida hankalinsa kan titi.

"Yaushe kenan?".

"Kafin ayimin Cs.....ban sani ba ko itace ta qarsh"

"Ameenatu!" Ya kirata da wani irin sauti kaman kan motar zai subuce masa kafin ya
daidaitata.
"Don Allah ki rufan asiri karki qara fada,kinsan tsarki da darajar garin nan
kuwa?,kinsan ko ina kayi addu'a indai a cikinsa ne ta musamman ce?,kin sani ko muna
tare da mala'iku?" Ya qarasa fada kaman zaiyi kuka. Sanyi itama jikinta yayi,sai
tayi qasa da kanta tana fadin.

"Kayi haquri,bazan sake ba in sha Allah" Shuru yayi kaman bazai amsa ba kafin ya
saki wata nannauyar ajiyar zuciya.

"Allah yayi miki albarka,ya rayamu a tare"

"Ameen" Ta amsa tana satar kallonsa tausayinsa yana ratsata.

Hanyar komawa gida taga ya canza sai kuma yace mata.

"Jibi in sha Allah zamuje kiya umra......amma muje in nuna miki wani abu" Kai ta
gyada,sai ya qaro sautin qur'anin kadan yaci gaba da tuqin a nutse.

Sosai karatun yake ratsata,qasan zuciyarta kuma tana jaddada godiyarta
ga Allah. Haqiqa tasan bata da haufi.....bata kuma da tsoron kalar uban data zabawa
'ya'yanta. Nagartar fu'ad kawai wata baiwa ce me zaman kansa,ballanta zallar
tausayinsa da jin qansa akan 'ya'ya mata......especially matarsa. Ita kadai tasan
wanne irin kalar miji take aure.....a father...a mentor.....uwa uba Selfless
partner ne. Batasan yawan addu'o'i da take sha ba daga wajensa.....ita take dauke
da cikin kawai,amma ya fita damuwa da kan kanta. Bai taba barinta ta kw ata ba
addu'a ba alwala ba,bai taba barinta tana kallace kallace ko jin kade kade ba,duk
da dama ita din ba gwanarsu bace,saidai akance dan adam ajizi. Da yawan lokuta
yakance.

"Tun a ciki kana iya koyawa yaranka dabi'a me kyau da maras kyau.....tun a ciki
kana iya debewa yaranka albarka kana kuma iya sama musu albarkar.....me ciki kullum
so ake ta zama cikin d'a'a da bin Allah.....ta zama very attached to her rabb,yawan
sadaka.....yawan kyauta,karatun qur'ani ko sauraronsa,ambaton Allah da istigfari,ta
guji gulma zagi mugunta tuggu makirci da qarya......wannan zai sanya ta samu
nagartattun yara in sha Allahu". Kai ta jinjina,kuma tun daga wannan lokacin bata
sake bari ya mata gyara akan duk yadda yakeso ta kasance ba.

Bata tashi bude idanunta ba sai a gaban wani gida,wani irin qawataccen
gida daya fusgi hankalinta tun a waje. Ya bude mata motar ta fito,suka zagayo a
tare,sai yayi tsaye gaban gidan yana zura hannunsa a aljihun rigarsa ya fiddo key.

"Wannan gidan na siyeshi ne da sunan yarana......mallakinsu ne halak malak cikin
wannan garin na madeena,ya Allah ka shaida" Yayi maganar yana damqa maqullin a
hannun sabreen.

"Bude mana" Ya furta yana sakin murmushi. Sanda take budewa dukka hannunta rawa
yake,idan tace bata taba ji ko ganin matar data samu tsananin soyayyar miji ba
irinta batayi qarya ba.

"Kawo nan raguwa ce ke wani lokacin" Ya fada yana tsokanarta sanda ya bude gidan.

Da bismillah da kuma sallama suka sanya qafafunsu. Tun a parlor na
farko tasan sun shigo aljannar duniya ne kawai,wani irin gida me cike da tsari da
nutsuwa ta daban.

Tiryan tiryan yake nuna mata kowanne sashe na gidan har zuwa sanda
sukazo kan daya cikin bedrooms biyar da gidan yake dasu.

Murmushi ya sakar mata yana mata nuni data bude dakin,ta maida masa
sannan a hankali ta saka hannu ta murda handle din ta tura.

"Wow......ya subhanallah" Ta fadi tana ware idanunta da kyau. Wani irin lafiyayyen
dakin yara ne dake dauke da wasu irin designers gadaje masu dan karen kyau. Komai
na dakin an shiryashi da wani irin hikima da tsari me tafiyar da hankali. Komai na
dakin guda ukune tabbacin ana welcoming yara uku kenan. Curtain rug da duk wani
furniture na dakin abun kallo ne.

Bango zuwa bango na dakin dauke yake da frames masu rubutattun ayoyin
qur'ani na tsari kala kala,sunayen annabi da sunayen Allah.

Daga cikin dakin akwai wata qofa,banda tasan cikin gida suke ba abinda zai
hana ta kira da dakin baby shop. Komai akwai a ciki,babu ce kawai. Tarkacen
kayayyaki Cots,baby bassinet,portable cribs kala kala. Kayan sawa kuwa cikin wasu
irin kwalaye na alfarma suke me dauke da wani tambari na musamman da zai tabbatar
maka musamman aka yosu. Tun idanunta na iya fahimta har ta daina gane wasu kayan
ma,don wasu abubuwan ko sanin mene ne batayi ba ballantana amfaninsu. Idan tace
babu ce kawai babu cikin abinda ya shafi tarkacen jarirai sabuwar haihuwa batayi
qarya ba,tun daga nan ta sallama,ta yadda lallai 'YA'YAN GATA zasu shigo duniya.

Fuskarta kawai ta rufe da tafukan hannunta kuka yanaso ya qwace
mata,komai tana kallonsa ne kamar a mafarki ba a zahirin rayuwa ba,sai ya jawota ya
sanyata cikin jikinsa yana bubbuga bayanta.

"Wanne irin so kake musu haka hamma?"

"Beyond imagination sabreen.......ina dreaming gina big family duniyata.......inaso
nayita tara yara nayita tara yara,wadanda zasu zamemin sanyin idaniya" Ya furta
yana hadiye wani abu. Shuru kawai tayi tana sauraren bugun zuciyarsa,ta wani
bangaren kuma zuciyarta ta cika da tarin addu'o'i da fatan samun rayyayun 'ya'ya
masu albarka.


★ *_LOKACI TAMKAR TAKOBI YAKE_*



Kamar yadda yayi mata alqawari ya cikashi,kwanaki biyu rak suka sauka a makka
ta sauke umrarta a ranar. Tayi matuqar qoqari shi kansa ya yaba,duk da nauyin da
cikinta yayi amma tayi addu'o'i sosai tayi ibada a kwana biyu kacal da sukayi.
Ranar da suke sanyan rai zasu dawo sai ga uban 'ya'yan BB farouq da amarya fannah.

Dukkaninsu sunyi wani irin kyau shi da fannah din,sunyi bundum abinsu
gwanin sha'awa. Yayi mamakin saurin qarasowarsa,don dai kawai ya gaya masa saura
kwana biyar ayi CS din sabreen baiyi zaton zai taho da wuri haka ba.

"Dole muzo mu yiwa adda addu'a,sannan so nake a matsayina na uban 'ya'ya na riga
kowa daukarsu" Murmushi fu'ad yayi,yana jin wannan qaunar har cikin jininsa,farouq
na dabanne a rayuwarsa.

Su suka tsaidasu suma saida suka sauke tasu umarar,sannan suka tattara
suka wuce madeena.

A kwanakin sosai sabreen taji dadin zuwan fannah,ta qarfafa mata gwiwa
sosai ta kuma bata shawarwari a matsayinta na wadda bangaren ta karanta. Akwai
fargaba kadan da takeji,amma tana dannewa saboda fu'ad din. Dukka tunaninsa da
hankalinsa yana kanta,burinsa na duniya gaba daya ya tattara a kanta da abinda yake
cikinta. Ta san ko yaya ne sai damuwar ta tabashi,shi yasa taketa qoqarin nuna
komai normal ne.
Ranar da zasu wuce asibiti da azahar,ko kara fu'ad qin yiwa fannah
yayi,ya hanata hada kayan tafiyar,sai list data musu ya zage da kanshi ya hada
komai.

"Zo mu tafi daki abunmu.....muje na baki labari me dadi" Farouq ya fada yana janye
fannarshi.

"A dawo lafiya......Allah ya bada lada" Fu'ad yabi farouq dashi ba tare daya
kalleshi ba,don idan kaga yadda yayi maganar zaka dauka badashi yake ba.

Qaramar dariya sabreen tayi,kominsu yana burgeta,tsakanin farouq da fu'ad
ba wanda ya isa ya shiga,idan ka shiga ma zaka fice da qafafunka don kunya zasu
baka.

Ba'a wuce awa daya ba ya dawo ya janye dude dinshi,can ta hangosu suna
qus qus kafin ya juya ya fice. Idanunta ta lumshe,tana jin wani sanyi qasan
ranta,koda ta mutu wajen aikin,fu'ad yabi bayanta,tayi imani da Allah muddin farouq
yana raye yaransu ba zasu tashi a maraici ba,yaransu ba zasu wulaqanta ba,yaransu
ba zasu fuskanci kalar rayuwar da ita da abbensu sukayi a duniya ba.

Sallamarsu anni kawai sukaji,anni huda da saddiq. Mamaki ya kama sabreen
har ta gaza daurewa,ta taka a hankali ta isa ga anni,sai annin ta rungumeta tana
mata sannu,lamarin da ya sanya sabreen din sakin kukan da batasan meye dalili
ba.158




Hannu anni ta dora saman bayannata tana shafawa a hankali gami da fadin

"Ya isa haka mana.....kukan na mene ummmm sabreen?,habba addarsu.......bakya gani
duka qannen naki suna kallonki?" Annin ta fada cikin murmushi. Kunya kadan ta kama
sabreen,saita boye fuskarta saman kafadar annin tana murmushi.

Qarfe takwas na dare suka shirya suka wuce asibitin bisa jagorancin
tuqin BB farouq,wanda a yau yake jin kansa kamar yafi kowanne mutum farinciki a
duniya. Shi yake driving din fu'ad yana gefansa,a haka suka qarasa asibitin.

An shirya mata lafiyayyen daki kafin isowarsu wanda aka zuba komai da
zai sakasu su jisu comfortable sosai.

Sosai qwalla ta cika idanunta sanda ta bude qofar dakin,wanda aka
tsarashi da gadajen jarirai har guda uku,gadajen da taji zuciyarta na bugawa,yaran
zasu hau?,ko gawarsu ce zata hau?,zata bude ido ta gansu su duka ukun akai?,ko kuma
za'a rasa wani ko ita a rasata?,dukka wannan Allah shi ya barwa kansa sani.

Sukam gaba daya tsarin dakin ya burgesu,sunbar anni a gida saboda
yanayin tafiya da zaman jirgi,don haka har huda da fannah suka samu sakewa abinsu.
Huda kam kaman taso tafi kowa gaza boye farincikinta,idan triplet sukazo zanyi
kaza......ni zanyi kaza.....ni zanyi kaza,har tana dariyar sai ta riga haneefa da
nadra daukansu.

"Idan kika kira kika tsokanesu fa zan iya daukanki mu koma salin alin.....musamman
kika saka mana haneefa auta kuka" Saddiq ya fada qasa qasa yana jifanta da wani
irin kallo da kana gani kasan na shauqin soyayya ne.

Kukan shagwaba ta saki masa,Allah yasa fu'ad a lokacin ya fita magana
da likita. Kunya ta kama sabreen,sai dauke kai tayi tana ajiye kayan kunyarta,sai
yanzu ta fahimci haka sukeyi ashe suma?,kuma ko yanxun ba fasawa akayi ba. Fu'ad
din baya gane kowa baya jin maganan kowa bare ya fahimta a sanda suke tare da ita.

Tana jinsu ta gama,ya lallashi abarsa,koda ta dawo kusa da sabreen
harara ta balla mata.

"Ke bakijin kunya ne?,wannan tabarar da kikeyi ko haneefa sai haka". Dariya sosai
ta ballewa hudan,tadan matsa baya kadan.

"Adda.....bamayin komai fa a kanku keda hamma......adda kinsan kuwa yadda kuke
komawa keda hamma?.....wallahi idanunku ma narkewa suke su juye idan kuns tare,har
wani laushi jikinku yakeyi baki taba lura ba?" Daquwa sabreen ta watsawa huda da
sauri.

"Qaniyarki huda.....kakarki ce ni?"

"Barta ta fadi fa......sister gaskiya ta fada,Allah na tuba waye yayi yaku?,har
yanzu gani nake BB bai kamoku ba,in kuna wani abun sai inga tabbas mu dukka 'yan
koyo ne" Cewar fannah tana dariya bayan ta gama duba bayanan asibitin da yadda zasu
gudanar mata da aikin. Kai kawai sabreen ta girgiza,bata iya ce musu komai ba don
bata da abun cewar. A fakaice take bin huda da kallo,ranta fari tas tana godewa
Allah,tana tuna shekarun baya......tana tuna nasir,wanda tabbas inda yakai ga cimma
gaci qila yanzun huda ba'a wannan matsayin take ba. Yadda ta mori miji haka tayi
imani huda ta mora,ta lura da yadda hudan ke qara mulmulewa abinta,jikinta kuma ya
bata juna biyu ne,fadi ne kawai basuyi ba saboda kunya,uwa uba kuma sai Allah yayi
mata baiwar juna biyu maras laulayi sam sam sam,kawai dai ya sakata mugun cin da ya
sanya taketa qiba. Amna ce tayi fama da laulayi,yanxunma dai daya girma sai a
hankali,abinka

Please Login or Register in order to submit comment