You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskarsa. Ta gama ganin zallar
mayen giyar da yasha yana narkewa a jikinsa

"No need" Ta fada tana girgiza kai sannan ta dauke dubanta daga kanshi.

Baya yaja kadan yana furzar da iska daga bakinsa. Gulmarta yakeyi a
ranshi,jin kanta yayi yawa,tana da wata izza da wani irin jan aji da kamewar da bai
taba gani a wajen matan titi ba sai a kanta,amma ba komai,yaci alwashin a yau
dinnan sai ya banbance mata aya da tsakuwa,dukka wannan jan ajin garawar da wahalar
dashi data dinga yi sai ya fansheshi a yau.

Tana gaba yana bayanta kamar ma ba tare suke ba har suka wuce ciki.
Bata sake gasgata da gaske yayi booking ba......da gaske lamarin namiji abune me
bada mamaki da daure kai ba sai da suka shiga babban dakin daya kama musu,wanda duk
kwana daya a yadda ta gani cikin jadawalinsu naira dubu tari takwas da hamsinne.
Komai an jere na kayan abinci,isowarsu kawai ake jira. Ya fada saman lafiyayyen
gadon da yafi kama da gadon da ake shirin cin amarci a kai yana dubanta qasa qasa.

"Komai da kike buqata akwai an tanadeshi.....amma inajin sai kinyimin alfarma na
matse baccin nan ko na awa daya ne cakal.....kiji dadinki yadda kikeso.....idanma
akwai wani abu da kike da buqata ga waya can ki musu magana zasu kawo miki" Yayi
maganar muryarsa tana maye ita kanta,da alama baccin yayi mugun cin qarfinsa.

Sanda ya miqe yana shirin sabule wandonsa da riga sai ta kau da kanta
tana jin yadda zuciyarta tayi wani irin bugawa. Irin wadannan abubuwan take gudu
shi yasa bata taba yarda ta biyo kowa wani kebantaccen waje ba,sai gashi haka kawai
jib ya takura mata sai tabi mutum biyu don samun cikar aikinsu.

Yif taji ya koma ya fada saman gadon,koda ta maida dubanta sai taga bai
iya cire komai a jikin nasa ba,kawai kokawar banza ya gama yi ya koma ya fadi cikin
bacci.

Minti goma qwarara ta bashi sannan ta taka ta isa gabansa. Yayi
sadidan a baccinsa,taja da baya a hankali tana jin faduwar gaba tace

"JIB yayi bacci"

"Good" Ya fada yana jawo dukka kayan aikinsa.

"Stay tuned.....minti talatin ya wadatar......ki kula da duk abinda zanyi
requesting"

"Okay" Ta fada tana jin sanyin jiki da faduwar gaban da batasan dalilinsu ba.

Ganin mintuna arba'in suna niyyar shudewa ba wani labarin nasara,ga
mikail yana motsawa lokaci bayan lokaci ya sanyata magantuwa

"Jib.....ya ake ciki?"

"Wannan aikin yayi tsauri da yawa adda.....akwai tsauraran matakai da shinguna masu
zafi a kai,yanxun haka abinda na soma fahimta kamar wani abu ya fara alerting nasu
anason musu kutse cikin asusun nasu" Ya fadi shi kansa kamar yanajin qarfin
gwiwarsa yana son sarewa. Duk inda ya zaci zai samu nasarar balla account din nasu
da dukkan hanyoyi da dabaru amma sai yaga abun kamar ya wuce nan.

Daidai lokacin da yake tsaka da meeting da investors din da suka jima
suna da shaawar sanya hannun jarinsu a kamfaninsa na jadda diamondchore resources
da yake a lagos da kano.....da kuma sabon kamfanin da yakeson yabude din a yanzu na
jewelry da sauran dangin kayan ado da qawa na mata.

Daga saman system dinsa wani abu ya fara harbawa. Alamace da take
nuna masa DANGER. Sosai ya zubawa alamar idanu,sannan da hanzari ya jawo system din
gabansa ya soma bibiyar abun

"What?,scammers?" Ya furta qasan ransa,sai ya kalli baqin nasa yana miqewa tsaye
gami da daukan wayarsa

"Excuse me" Yana daga musu hannu tare da takawa a hankali yana matsawa nesa dasu.
Sadiq dake can nesa dashi ya kira

"Call the security team na kamfani......ka gaya musu akwai alamun shirin yin kutse
su kula".
"Done" Ya fada kaman yadda ya saba gaya masa. Juyawa yayi yana komawa wajen
baqinsa,ya koma mazauninsa ya zauna yana jawo system din gabansa.

Hankalinsa ya raba biyu,yana saurarensu yana kuma duba yadda suke samun
progress na sake kutsa musu. Alama ta qarshe daya gani ta sanyashi lumshe idanunsa
hadi da ture system din gefe kadan ya maida dukka hankalinsa dari bisa dari akan
baqinsa.

"Done adda!......done,millions of naira sunyo dropping" JIB ya fadi da wani irin
sautin farinciki,yana jin sukuni yana ratsashi na samun cikar mafarkin mutanen da
suke rayuwa ruhinsu a jikkunansu.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

Page 73


"Zan iya tafiya?" Shine abu na farko data tambayeshi ba tare da tabi
takan adadin kudin da suka samu cira ba

"Yes adda.... Zaki samu me napep a corner farko na street din yana jiranki gudun
samun delay". Katse kiran kawai tayi,ta miqe tana daukar jakarta ta jefa wayar
hannunta da sauri tana dan duban yadda mikail yaketa motsawa,alamar koda kowanne
lokaci yana iya farkawa,saita wuce kai tsaye ta bude qofar ta fice.

Sai data tsaya da lobby din ta daidaita nutsuwarta da kyau gudun zama
suspect a idanun security na hotel din,sannan ta fara takawa a nutse tana qarasa
ficewa.

Hankalinsa a tashe yake dawowa wajen fuad din,yama gaza kiransa a waya
kaman yadda shi ya kirashi a daxun.

Ta bayansa ya qaraso,yadan rusuna don sanar dashi halin da ake ciki

"Na sani.....jeka jirani mu qarasa mu wuce gida" Ya dakatar dashi ba tare da ya
barshi yace komai ba. Da dan mamaki sadiq yake dubansa ganinsa zaune hankali
kwance. Duk da yasan yafi gaban hakan amma wannan din ba qaramin abu bane da ya
kamata ya ganshi haka a zaune calmly ba yana tattaunawa da investors,to amma bashi
da sauran zabi illa juyawa ya tafi din kamar yadda ya buqata.

Tana tafe a hanya tunane tunane cinkus cikin kanta da qwaqwalwarta.
Haka kawai taji ta kasa isa gida,sai kawai ta bawa me napep din umarnin suna da
wajen da take so ya kaita.

Guri ne very quite,ba cikar jamaa,kuma kowa sabgan gabanshi yakeyi.
Hakanan gurin yana da yalwa da fadin da zaka zauna a guri wani ma da yake nemanka
bai ganka ba. Order din lemo da ruwa kawai tayi don batajin zata iya cin komai.
Batasan me yasa ba.....ba yaune karon farko da haka ta fara faruwa ba amma wannan
din yanason tsaye mata gami da sanyayar mata da jiki.

"Eh ba shine na farko ba......amma kuma yafi kowanne nauyi da girma......baki taba
samun kudade masu tsananin kauri da yawan wadannan ba,sannan kamar an shiga lalitar
wadanda baki taba koda magana dasu ba.....kaman akwai nasu haqqin a ciki". Wani
sashe na zuciyarta ya fara tunasar da ita. Wanda qarar ring na wayarta ya katse
mata tunanin.
Sunan titi data gani shi ya dauke hankalinta daga dukkan tunanin
komai,ba jinkiri ta daga wayar suka fara magana

"Da sauqi.....amma sumanta biyu yau"

"Komai ya qare in sha Allah" Ta bawa titi amsa a taqaice saita katse kiran. Dukka
karsashinta taso dawo dashi,ta fara lalubar wata number da jib ya bata.

Ayyuka biyu tayi a wajen da suka qara kashe mata kusan awa daya da
rabi. Ta tura dukkan abinda mutumin ya buqata don yiwa titi aishatu da dan rakiya
daya visa na fita qasar india da ita da komai da komai da zaa buqata na asibiti
lafiyarta da sauransu wanda ya lashe maquden kudin da suka ninka kudin da akayi
hasashen zaa kashe din. Abu na biyu kuma ta zauna ta datse ta share ta kuma sake
toshe kowacce hanya ko kafa da zata sake sadata da mikail.....sai data tabbatar ta
sanya kowanne shinge da zai nesantata dashi nisa na har abada sannan ta tattare
komai nata tana fita daga wajen.

_hmmm,anya kuwa kayan Muhammed fuad jadda zasu tabu 'yammata?,to muje zuwa dai muga
yadda wasan zai kaya FUAD dinne keda nasara?,ko SABREEN?_

Karo na farko a rayuwarta da taji shigowar sabreen cikin gidan dama
dakin gaba daya amma ta shareta kamar ma bataji ba. Tayi lakur saman gadon tana ci
gaba da kwanciyarta.

Hirarsu da hameed yau ta dasa mata abubuwa da yawa cikin zuciyarta
dangane da yayartata. Tayi amanna ta kuma yarda hameed mutumin kirki ne na
qwarai,daga yadda yake yawan mata nasiha da wa'azin ta kare mutuncinta......ta guji
yawace yawace da yawan fita barkatai.....don duk yarinyar data fiya fice
fice,qafafunta basa zaman gidan tabbas akwai ayar tambaya a kanta ko taqi ko
taso,alamar kamewa ga mace shine ta lazimci zaman gida.

A yau din ayoyi qwalli biyu da hadisai guda biyu suma daya karanto mata
sunja hankalinta. Itakam hameed yayi mata,a yanzu dukka burinta shine tayi
aure......tayi aure ta matsa daga rayuwar da take sake Fahimtar yaa sabreen din
tana yi.....ta auri hameed tayi nesa daga cakwakiyar gidansu.....baqaqen maganganu
zallar gori da habaice habaice. Ta tabbatar zata samu irin rayuwar da takeso daga
wajen hameed,zai killaceta kaman yadda yake fadi din.

Tayi mamaki sosai da taga qofar tasu a bude,sanda ta shiga kuma falon
sai ta tabbatar akwai wani a ciki,sai ta aje jakar hannunta ta kutsa uwar dakin.

Gaban gadon hudan ta qarasa tana kiran sunanta. Da farki sai tayi
banza kamar bataji ba,har sai data saka hannu ta yaye bargon da take ciki

"Lafiya huda?" Ta tambayeta tana qoqarin son ganin fuskarta

"Lafiya qalau" Ta samu kanta da bata amsa kai tsaye. Wani irin mamaki yaso kasheta
a tsaye,amma sai ta cinye wannan. Hudan a yanzun ta fara zama budurwa,shekara sha
biyar ta fara hawa bigiren kaiwa yammatanci,tabbas zata iya faskantar canje canjen
halaitada dabi'u a tattare da ita kaman yadda ta tabaji mamanta ta fadi a sanda
take cika tata shekara sha biyar din,wanda a yanzun shekara biyar daidai kenan

"Idan har lafiya lau huda me zai hanaki zuwa makaranta kuma uhmmm?". Kamar ta bude
bakinta ta gaya mata aure takeso,kamar ta bude baki tace ta bawa hameed ita,kamar
tace mata ta gaji da ganinta kullum tana fita babu sahihin inda take zuwa,ba
makaranta ba ba kasuwa ba,amma sai tace

"Gajiya nayi,amma zani gobe"
"Gajiya?" Ta maimaita qasan ranta,amma a sarari sai tace

"Allah ya kaimu" Ta juya zuwa sashen kayan sawarta tana fidda kayan jikinta don
sauyawa da wasu. Can qasan ranta zuciyarta ta kasa samun nutsuwa,sake gaya mata
takeyi

"AKWAI MATSALA.....DOLE KI NINKA SANYA IDANUNKI" da wannan tunanin ta kammala canza
kayan sannan ta juya ta koma falon don duba me dame akayi da bata nan.

Da kallo ta bita har ta fice,sai taja qaramin tsaki qasan ranta zuciya
da shaidan suna ayyana mata ko dame dame ma tayi sanda ta fitan?,caraf kuma wani
sashe na zuciyartata ya kwabeta

*D U N I Y A TA*

*_H U G U M A_*

PAGE 74


Kaman kowanne lokaci ya bawa kowa daman yayi order na abinda yakeso
qarqashin kulawar sadiq da shike handling kusan komai.

Shi daya ya ware kansa a wani table da corner na daban,ya fidda system
dinsa da ya sanya sadiq dauko masa ita. Ranshi a tsananin bace yake,amma kuma yana
da wani irin abu,ya iya boye fushinsa idan yaso,ya iya kuma danne abinda yake
damunsa,dole da rayuwa sun sanyashi iya controlling anger dinsa.

Yana da matuqar sani da zafi gami da kaifi ta bangaren
computer.....ya koma da baya daga baya cikin karatunsa,ya zabi computer science ya
kashe lokaci akai har sai daya zama qwararre kuma cikakke akan fannin,saidai ba
kasafai ayyuka da cushewar abubuwa ke bashi daman practicing karatun nasa ba,amma
komai nasa zaka sameshi a tsare da burbushi da alamu dake nuna yasan kan computer
sarai.

A nutse ya soma bin komai daki dai cikin matuqar qwarewa tare da sanin
makamar komai. Ba jimawa musaddiq ya iso wajen,sai yayi masa alama yayi joining
sadiq kawai. Juyawa yayi yana matsawa daga wajen don tunda ya ganshi a hakan ya
bawa system nutsuwarshi yasan akwai abinda yakeyi me amfani.

Ya samu sadiq din yana waya wanda ya kasa jurewa ya kira security
team din da kansa. Ranshi a bace shima yake wayar,duk da abincinsa dake ajiye
gabansa baiko bi ta kansa ba. Dan zuba masa ido musaddiq yayi kafin ya
zauna,jikinsa kuma yana bashi lallai akwai wani abu. Jawo tray din yayi yana bude
komai tare da warware spoon da fork din dake nade cikin tissue,ya sanya musu cikin
abincin ya saita musu komai saidai still hankalinsa yana kan saddiq din.

Kusan mintuna goma sha biyar da isowarsa kafin ya kammala wayar,ya
kasheta ya ajiye yana jan tsaki.

"What's going on?" Musaddiq ya jefa masa tambayar yana dage giranshi. Cup din daya
zuba musu ruwa ya jawo yana kurba

"Scammers......hackers.....me ma zance ne musaddiq?". Idanu musaddiq ya waro waje
yana kallon sadiq

"A'ina?Meye ya faru?"
"Sun diba maquden kudade daga cikin asusun company dazu........security team dinmu
sun kasa aiwatar da komai......hamma fu'ad kuma baisan wanne matsaya ya dauka
ba.....duk da nasan bazai qyale ba amma sai naga kaman ya dauki abun da
sanya.....ina dai kyautata zaton yanzun yakebin kadin abun kamar ba kudi masu yawa
aka diba ba" Saddiq yayi maganar yana maida hankalinsa ga fu'ad dake dan nesa dasu
wanda baya iya ganinsa sosai da sosai

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Musaddiq ya soma maimaitawa yana rasa abun
fadi kwata kwata.

Sannu a hankali ya soma bude idanunsa har ya gama budesu gaba daya

"Wayyo......." Ya furta yana miqewa sosai saman gadon yana jin yadda kanshi da
idanunsa sukayi fresh. Komai ya sakeshi kenan,babu wani sauran burbushin giyar a
tattare dashi,komai kuma zai tafi daidai yadda ya dace.

Idanunsa ya fara wurgawa cikin dakin bai ganta ba,sai ya barwa ranshi
tana toilet ne tana shiryawa,don haka ya jawo wayarsa yana yana duba time

"Kai!" Ya fada a mamakance ganin irin baccin da yayi na kusan awa uku maimakon awa
daya kacal kaman yadda yace zaiyi. Jikinsa ya danyi sanyi ganin yadda baccin yayi
tsaho,zuciyarsa ta raya masa yarinyar nada wani irin aji da wahalar samu tamkar
tarwada cikin ruwa,anya zata zauna duka wadannan awannin tana jira?.

"Da kuwa na tafka babbar asara" Ya furta a sarari gabanshi yana faduwa,sai ya jiye
wayar ya miqe da hanzari ya nufi toilet din.

Duka bandakin ya duba ba ita ba alamar ta,sai ya fito ya soma duba
dakin har zuwa balcony dake gaban dakin,lobby da sauran gurare,hakanan ya dawo
zuciyarsa na harbawa da tsananin baqincikin kufcewar wannan damar a garesa

"Wai me yasa ma nasha barasa duk da sunan farinciki?,wannan tsinannen baccin......"
Ya katse zancan bayan ya zauna gefan gadon yana dafe kansa da hannayensa bibbiyu.

Yadan jima a haka yana karatun asarar da yayi,da kuma wassafa yaushe
zai sake samun irin wannan damar?.

Tsaki yaja sanda yaji wayarsa tana qara. Ya waiwaya yana duban me
kiran,john ne chief of security team.

"Ubanshi zan masa......ya barni naji da asarar da nayi" Ya fada a sarari yana
rejecting kiran.

Sake kira yayi bayan sakanni biyar kacal,hakan ya sake qufular
dashi,don daga yanzu har wayewar gari har kwana uku bayajin zai huce daga asarar da
ta sameshi.

Sake rejecting yayi,bai haqura ba ya sake kiransa a karo na uku.
Wannan karon da niyyar cuccusa masa ashar ya dauki wayar,tunda a tsakaninsu kar
tasan kar ne,saidai yana dagawa ya jefeshi da tambayar data sanya ya shiga tunani

"Kana tare da wayarka kuwa?,kasan me yake faruwa?,bakasan anyi kutse account din
kamfani ba?". Dif wuta ta dauke masa,sai kuma ya bude bakinsa

" Kai john banason iskanci.....ka sanni na sanka,idan giyarka ka shawo ka daina
gigin kirana ka bari ta sakeka tukunna,wayata tana hannuna......kuma ba wani abu
daya faru,na sani fa ka dade kana harin muqamina,to qaryarka tasha qarya......in
kanaso sai ka jira sai sanda matsayina ya qara daukaka a jadda company sai ka shiga
takarar neman tsohon matsayi na" Daga haka ya katse kiran yana mitar shi baisan
abinda yake damunsa ba zai qara masa damuwa.
Yankewa yayi kawai ya kirata ya lallasheta ya kuma sake shawo
kanta,tunda kudin kwana biyu ma ya biya,ya samu ko wuni dayan gobe tayi masa tunda
ya tabbatar ba zata taba dawowa a yau ba.

Saqon da idanunsa suka gane masa daga banking da kamfanin nasu ke
ta'ammali dashi ya kusa sanya gudawa da fitsari duka yanke masa lokaci guda. Yayi
wani mugun gigicewa sanda ya shiga saqon idanunsa suka haska masa adadin kudaden da
aka zare daga asusun.

Wani irin abu yaji yana tsirga masa daga kowacce kafa ta gashi dake
jikinsa. Gangar jikinsa yakejin kamar ba tashi ba ballantana ayi batun qafafunsa su
samu daman iya daukansa,don haka sai kawai ya sulale ya zube ragwab a wajen yana
jin kamar numfashinsa zai qwace masa.

Meye ma zaiyi ne?,ihu ko kuka?,hauka zaiyi ko mene?,kudade
maqudai?,kudadenma kuma na kamfanin jadda?,kudaden da akansu yau suke lissafi zasu
kuma gama lissafinsu a gobe?. Shin waye ya aikata hakan?,waye yake da alhakin
aiwatar da hakan?. Yaushema abun ya faru?,wa zai soma kira ya tambaya bayan daga
bakinsa ya kamata a fara ji?,wai yaushe ma abun ya faru ne?.

Ko sanda ya duba time na faruwar abun,da sanda John ya fara kiransa sai
kawai ya saki wayar ya dora hannu saman kai yana fadin

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da qarfin gaske,wanda kalmar ma sam batazo
bakinsa ba sai sannan. Yana dire kalmar farko hawaye suka fara bin kuncinsa. Daidai
sanda kuma kira ya shigo wayar tasa abinda ya sanyashi zabura kafin yakai dubansa
ga wayar.

Sir sadiq daya gani a rubuce ya sanya fitsarin dole kubce masa duk kuwa
da yadda yaso ga riqeshi. Ya shiga uku ya lalace,yasan tunda yaga kiran saddiq din
magana ya gama isa kunnen boss. Da wanne baki zai kare kansa?,idan suka buqaci kuma
ya biya a ina zai samu?,ta ina zai samosu?. Yayi imanin koda danginsa zai siyar
bazai hada wadannan kudaden ba.

Zuciyar dake da Allah a cikinta......hakanan zuciyar dake da yawan
ambaton Allah ce kadai ke samun nutsuwa a sadda bala'i ya durfafo ta,don haka dukka
wata dabara da kuma nutsuwa sukayi qaura daga gareshi.

Ya dinga zirya yana kai kawo,ya kasa aiwatar da komai,ya kuma kasa kamo
bakin zaren komai. A haka lokutan sallah duka suka shude masa,hakanan qarar kiraye
kirayen mutane suka yita shiga kunnuwansa suna fita ba tare daya iya rabar inda
wayar take ba.

Duk wani kira da zai shigo wayar tsoro yake bashi,baya qaunar koda rabar
inda wayar ma take gaba daya.

Sai kusan bayan sallar ishai ya iya fusgo tunanin baiyi sallah ba,ya
miqe yana hada hanya ya nufi toilet don cire jiqaqqen wandon jikinsa daya jiqe da
fitsari ya dauraye jikinsa ya kuma daura alwala. Har a sannan sam tunaninsa bai
kawo masa sabreen ba,ya mance sam sam da itama saboda tsananin rudanin daya shiga.

"Don't call him again......ka barshi,inason naga iya gudun ruwanshi......kafin
sannan ni na gama nawa" Fuad yace da sadiq wanda ke shirin sake kiran mikail din
karo na biyu

"Okay" Ya amsawa fuad din yana maida kansa ga titi.

Ring na wayarsa ya katse shurun daya gilma cikin motar. A hankali ya
maida kallonsa kan screen din. Anni ce,sai a sannan ya manta bai kira ba bai kuma
sanya an kirata ba wunin yau. Zuciyarsa tadan saki daga quntatar da take ciki,ya
daga wayar yana sanyata a kunne.

Kusan tare suka yiwa juna sallama ita dashi,sai suka amsawa juna
sannan tace

"Nace dai Allah yasa lafiya......daga ku har abbanku yau duka kunyi dare a waje"

"Lafiya lau anni.....ayyuka ne suka riqemu,wasu al'amura kuma suka taso wadanda su
suka shagaltar dani daga kiranki"

"Babu komai......kada ka damu,tunda dai dukkaninku kuna lafiya to
alhmdlh......farouq yace min kuna tare da musaddiq ko?"

"Eh muna tare anni"

"To Allah ya tsare,ya dawo daku lafiya"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ya amsa mata zuciyarsa na sake cika fal da qaunarta da
qarin ganin kimarta. Tana taka muhimmiyar rawa qwarai da gaske wajen cike musu
wawakeken gibi da ramin dake zukata da kuma rayuwarsu.

Tun da aka kirayi sallar magariba ta gama shirya komai,sannan ta sallami
masu aikinta kamar jiya. Tsaf ta shirya cikin embroidery holland gold atamfa da
keta sheqi da nuna ainihin tsadar sutturar. Tayi kyau abinta,kai ba zakace itace ta
haifi zabgegen saurayi irin muhammad fuad da musaddiq ba. Ita din ba baya bace
wajen iya kula da jiki da tattalin fatarta da dukkan abinda zaya qara mata lafiya
da kuma quruciya.

Parlor ta koma tayi zaune bayan ta kunna tv ta kuma saita tashar da take
ra'ayi. Ta kame saman daya daga cikin sofas din falon tana kallon hagunta da
damanta. Kujerun take kallo,a ranta tana wassafa ranar da zatayi gwanjonsu. Duk da
tsadarsu da kudaden da aka kashe wajen mallakarsu sam ita bata tuna wannan. Abu
daya dake sake tsaye mata a rai shine,labarin katafaren ginin daular data samu cewa
yana yi cikin garin abuja. Batasan ainihin wacce unguwa bace,amma me kawo labaran
ya shaida mata cikin jerin unguwanni mafi daraja da tsada a garin abuje yake
ginin,kamar yadda yakejin qishin qishin din yana nan yana tamfatsa wani a lagos.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 75


K'aramar qwafa taja,muddin da gaske wannan villa din yake
ginawa.....indai da gaske hoton da me dauko rahotonta ya nuna mata fuad dinta ke
ginawa.....to kuwa koda zatayi yawo tsirara ba zata taba bari ameena da hamza su
sanya qafafunsu cikin wannan daular ba.

Wayarta ta dauko ya kira hajja harira,a nan suka bata lokaci me tsaho
suna sake tsara yadda komai zaya kasance.

Batasan ma lokaci yaja haka ba sai da suka gama waya da hajja harira
din. Ta kalli agogo tana mamakin rashin shigowarsu gidan,fargaba na saukar mata na
kada fa yau ma a maimaita abun jiya?.

Bata samu fuad ba,amma ta samu musaddiq,ya amsa mata da zasu shigo,don
shima baisan fuad din ya gama shirya yadda zasu cinye daren a waje ba.
Ci gaba tayi da duba lokaci mintuna bayan mintuna,saidai duk sanda ta
kalli agogon sai ranta ya sake baci,haka ta sake jawo waya da xummar sake trying
number musaddiq amma ta kasa samunsa.

Ranta ya sake baci qwarai,dama ta sani samun number fuad ba abu bane me
sauqi,sau tari xaka iya kiransa ka kasa reaching dinsa,saboda ba da gama garin
wayoyi yake amfani ba don dalili na tsaro da kuma matakin rayuwa da yake kai dole
yana buqatar tsari akan komai nashi.



Please Login or Register in order to submit comment