You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne dake bada wata irin iska me dadin shaqa da samar da
nutsuwa ga zukata,hakan ya sanya zaman wajen yayi masa dadi ,wanda tun bayan sallar
azahar ya zauna a nan din. Yau din zama sukayi sosai da mu'allim,wanda shi yake
kula da bangaren masu buqata ta musamman da kuma neman taimako. Ya karba list na
mutane masu yawa,ciki harda list din anni dana maamah wanda ya jima yana kallonshi.

Sunaye na mutane barkatai,wanda yafi kyautata zaton an shirya sunan ne
kawai an kuma shigar. Ya karba takardar da zummar zai duba din,don hatta da numbers
na wayoyinsu dake a jiki kallo daya yayi musu yaji sunfi masa kama da lambobin
bogi.

A yanzun ya gama shigar da komai cikin laptop dinsa da kusan zaiyi wahala
ka ganshi ba ita. Tana dauke da muhimman bayanansa da kuma sirrika sosai a ciki.

A yanzu da yake zaune yana karbar kira ta kai tsaye ta cikin system
dinsa. Video call ne da daya daga cikin kamfanin narka gold da wankeshi daga qasar
china,farouq ya tako yana isowa farfajiyar.

Kujera yaja ya zauna,sannan ya fidda wayarsa yana duba saqonnin
WhatsApp da tun daxun ya sauka da zummar zai koma din. Hira sosai suka shiga yi da
fannah,don kusan duka saboda ita din ya hau. Jifa jifa yana mata gajeran voice note
don kada ya janye hankalin fu'ad da baqonshi.

A nutse ya kammala amsa kiran,yayi disconnecting sannan ya maida dubansa
ga farouq. Idanu yadan zuba masa,yana mamakin yadda yakejin dadin soyayya gaba
daya,wai shin mene a cikinta har haka da take iya maida mutum wawa ne?.

"Ya dai?" Yaji muryar farouq din yana katse masa tunaninsa

"Am just wondering...."

"For what?" Farouq ya katse masa magana yana maida masa tambaya murmushi dan kadan
yana fita a fuskarsa

"Yadda mutum me hankali yake komawa kaman soko.......wannan abar farouq It doesn't
make sense wallahi" Ya fadi iya gaskiyarshi,gaskiyar da har saman fuskarsa zaka
hangeta kwance quru quru.

Dariya ce sosai ta qwacewa farouq har yana duqawa,abinda ya sanya fu'ad
tsaiwa ya zuba masa ido yana kallonsa.
"To abun kuma ya fara cin qarfina,to be sincere ka fara bani tsoro sama dana
baya.......nafi tunanin kuma yanxun bawai aljana bace ta aureka ba,tunda koda
aljana ce saida soyayya ai ko?"

"Kai ka sani qaton banza" Fu'ad din ya fada yana jifansa da wata harara data sake
sanyawa farouq ya fashe da dariya,don irin wannan hararar kawai yake iyayi masa
idan ya quleshi ya kaishi bango.

Qoqarin daidaita nutsuwarsa yayi don kada ya jawowa kansa jagwal ko
yaqi bashi hadin kai akan batun da yazo masa dashi,ya sani sarai kadanne daga
aikinsa ya murje idanunsa,musamman yanzun da har ya shiga gonarsa ya kuma
tsokaneshi.

"Mu ajjiye wannan batun.....ina nan dai inayi maka addu'a.......na saka a duba mana
ticket zuwa abuja Saturday in sha Allah......already ma nayi payment zai mana
printing ne kawai"

"Bazanje ba" Ya bashi amsa kai tsaye yana qoqarin shutting down system dinsa
idanunsa saman screen din.

Fuska farouq din ya narke yana koma masa kalar tausayi

"Sai na tafi ni kadai.....amma kuma idan ta tambayeka,zan bata labarin ka saba
Alqawarin da mukayi da kai ne" Yakai qarshe yana zuba ma side na fuskarshi idanu.

Shuru yayi kawai bai sake cewa komai ba,wanda alamu ke nunawa farouq
zaiyi wahala yace bazaije din ba. Sau tari shuru a wajensa alamu ne na accepting
abubuwa,idan baya so kai tsaye zaice baiso kuma bazaiyi ba kaman yadda yanzu ya
fada mishi da farki,yana sane kuma ya sanyo zancan cika alqawarin......don ya sani
shi din mutum ne da ba abinda ya tsana irin qarya sam sam,idan kanaso kaga
tunzurarsa ko fadansa to kayi masa qarya.

"Ya ake ciki maganar ginin?" Farouq ya sanyo masa maganar da yasan yanzun itace a
gabansa sama da ko wacce. Sai kuwa ya qarasa kashe system din ya rufeta yana dora
fararen idanunsa akan farouq din.

"Ending month dinnan nake sanya ran gini zai kammala,sai preparation kawai na
budewa wanda shima banaso ya wuce watanni biyu.....duka engines da sauran kaya next
week zasu iso in sha Allah" . Kai farouq yake jinjinawa,yana matuqar yabawa da
hazaqa da qoqari irin na fu'ad din.

Tun farko yasan idan don ta shine bazai iya ba......don haka ma ya saki
wannan ragamar kawai ya miqawa fu'ad din,don tunda shi ya faro barota shine zai
iya. Qaramin murmushi farouq din ya saki,fu'ad ya dage masa gira alamun tambaya

"Ba komai.......kawai na tuna temple run dinka ne......rigimammen dan bautar qasar
da yaje garin wasu ya musu barna.....ya kuma gudo da abinda suke ta buri da nacin
samu......Allah inda a zamanin yaqe yaqe ne zakayi barna da yawa fa" Maganar dole
ta sanya murmushi kubcewa daga fuskar fu'ad,ya zauna sosai yana sake duban farouq

"Mazantaka a zuciya take farouq......sannan dukkan namiji muddin zai amsa wannan
sunan dole kalmar TSORO ta fita daga dabi'arsa......bai halatta ba sam sam namiji
ya zama me tsoro ba..... Idan hakan kuwa ta kasance a matsayinsa na shugaba kuma
jagora,dole al'amura su lalace..... Adinga ganinsu kuma ba'a yadda suke ba".

Duk da tsananin gajiyar dake a jikinta bayan dawowarsu daga wajen boka
DURGUJI amma hakan bai sanyata zama ta huta ba bare akai ga batun kwanciya. Kai
kawo kawai takeyi tsakanin kitchen da dakunanta cikin sabgar dafawa da saukewa.
Wani tsari da takeson fara qirqiro dashi a yau din,don shine hanya guda daya da
zata samu ayyukan da aka tsara mata su tafi yadda takeso.

Ta bata lokaci sosai tana son tuna wanne abinci da wanne abinci
sukafiso ta dafa musu lokacin quruciyarsu?. Da qyar ta dinga tuna wasi abubuwan da
suma shafesu saboda yadda ruhi da zuciya suka jima da yin nisa daga rayuwarsu dama
komai daya shafesu.

Tayi lissafin abubuwa guda hudu duk da tasan sunfi hakan,saidai sauran
ta barwa ranta zata nemi ganin ma'aikatansa da yake yawan rayuwa dasu don samun
wasu amsoshin. Anni ce tasan wadda zata samu amsar kai tsaye daga gareta,saidai
zuwa yanzun tana jin cewa tafi qarfin anni ballantana ta sake neman wani abu daga
wajenta akan 'ya'yan da ita tayi cikinsu ta kuma haife abinta. Alwashi
taci......tana nan kuma riqe dashi......hakanan ba zata runtsa ba ba kuma zata huta
ba har sai ta samu cikar wannan alwashin nata.

Tana aikin masu aikinta suna mamakin shigarta kitchen yau da kanta.
Duk kallon da suke binta dashi bata samu nasarar tantancewa ko kuma kula ba,saboda
hankalinta yayi matuqar nisa akan maganganun da suka tattauna da durguji.

_"sau daya nakewa mutum aiki na gama dashi.....muddin kuma nayi aiki baici ba yana
da wahala na sake na biyu indai ba sa'a ka taka ba......aikinki me hatsarin gaske
ne......duk abinda kikaji ko kika gani kada ki wuce wata guda kacal baki dawomin
ba"_

Ita batun sake aiki da rashin sakewar duka ba damuwarta bane,tunda ta
riga data sani kudi suke juya akalar kowa su kuma sauya tunaninsa. Muddin zata zube
masa kudi ta tabbatar duk taurin kansa sai ya sake waiwayarta. Kawai abinda yake
damunta a yanzu shine yadda zata samu dawowar hankulansu a kanta,ta yadda cinsu da
shansu zai dawo qarqashinta,wanda wannan shine abu guda daya tal da zai sanya
aikinta ya tafi yadda ya dace.

Tana kammala white rice sai ta kasa haquri ta fita a kitchen din.
Dakin gadonta ta wuce ta samu saman sofa bed ta zauna tana latsa wayarta. Number
fu'ad din ta fara kira,daidai sanda yake zaune suka ci gaba da tattaunawa da farouq
yana nuna masa tsarin taswirar ginin kamfanin.

Fararen idanunsa ya daga yana azawa saman wayar. Zubawa wayar idanu
yayi yana kallon yadda sunan ke wucewa ta saman screen din. A duk sanda zaiga
shigowar kiranta sai yaji wani abu tun daga qasan ransa har tafin qafafunsa. Inda
yana da iko bazai daga wayar ba sam sam,to amma wata fuskar tafi gaban mari

"Ina zuwa" Yace da farouq yana daukan wayar ya daga ya saka a kunnensa.

Cikakkiyar sallama tayi da kwantacciyar murya da zai iya cewa ya manta
rabon da yajita daga bakinta,wani abu guda daya sake jan hankalinsa,saidai bai
hanashi amsa sallamartata ba hadi da dorawa da fadin

"Barka da yamma" Dan murmushi ta saki kadan

"Yauwa barka kadai Muhammadu" Ta fada cikin nuna kulawa

"Ka wuni lafiya kai da dan uwanka?,tunda har yanzu ban cancanci a kullum naga
lafiyarku ba......hasalima kamar kuna mantawa ne da rayuwata" Yadda tayi maganar ya
taba ransa kadan,yaji sautin da amon da ya jima baiji daga gareta ba

"Kiyi haquri ba haka bane" Ya maida amsa wani abu yana kai kawo a ranshi

"To idan ba haka bane yaya ne Muhammadu?,kamanhar yanzu kun kasa manta abinda ya
faru ne kawai" Idanunsa ya lumshe kawai yana saurarenta. Zuciyarsa nadan qara bugun
da takeyi yana jin wani abu sosai can qasan ransa da kuma wani sashe na zuciyarsa

"Idan zaku iyayimin alfarma,inaso ana gama sallar ishai ku shigo kai da
musaddiq....inason ganinku duka ku biyun"

"In sha Allah" Ya amsa mata kai tsaye. Wayar na a kunnensa har ta yanke Kiran,sai
shima ya zame wayar daga kunnensa yana kallon screen din.

Sanda ya daga idanunsa sai suka hada ido da farouq,murmushi farouq din
ya sakar masa kawai. Har yanzu bai taba saka baki ko shiga lamarinsa da maamah
ba,infact ma shi bai taba masa magana a kanta ba,ko yaushe shida sadiq suna qoqarin
kiyaye iyakokinsu ne.

Wani irin murmushi ta saki bayan ta ajiye wayar idanunta akan qofa
tana jin wani farinciki yana shigarta. Nasara ce a kusa take shanshanarta......kuma
jikinta yana bata komai yana kusa da qofarta.

Plan dinta guda uku ne qwarara,ta fara da wannan na farkon,idan yayi
aiki shikenan,idan baiyi ba zata wuce plan B,idan shima yayi aiki shikenan,idan
kuma shima baiyi ba tana da plan C......wanda shine tsororuwar shiri mafi tsauri da
tauri.....plan din data tabbatar zai yamutsa hazo iya yamutsawa........ita kuma
zata saki dukkan wata iyaka da ikon da Allah ya bata don ganin tabbatuwar plan din
da kuma wanzar dashi.

Ranta fes,Zuciyarta wasai ta ajiye wayar ta koma kitchen tana shirye
shirye shirye gadan gadan.

Haka kawai yakejin yanayinsa wani iri,jikinsa da zuciyarsa dukka ba'a
sake suke ba,a haka ya shirya cikin Moroccan abaya ne sulbi ya wuce zuwa sallar
magariba.

Kafin ya isa masallacin suna hanya shi da farouq musaddiq da saddiq
suka biyo bayansu. Wannan din wata kyakkyawar al'adarsu ce da anni ta renesu a kai.
Muddin suna garin ko suna qasar,hakanan ba wani babban uzuri ko aiki bane ya riqesu
a kamfani,to zaka samesu a gida duk inda magariba tayi. Kwata kwata basusan yawon
dare ba,farouq ne ma medan sha'awar fitan daren,to sukan fita jifa jifa su zaga a
mota su dawo. A nan zasuyi sallar magariba suyi ishai,suyi dinner tare me uzuru ya
wuce nasa uzurin.

Sanda yake sabule tattausan flip flops din qafarsa yace da musaddiq ba
tare daya waiwayo ba

"Bayan ishai ku shirya kaida saddiq zamu shiga wajen maamah" Dan kallon yayan nasa
kadan yayi,kaman zai magana sai kuma ya fasa ya amsa da to.

Tun bayan magariba ta sallami kowa tare da kafawa kowa sharadi da dokar
bataso kowa ya sake tako mata parlor sai gobe idan Allah ya kaimu.

Ta duba doormat din bakin qofar falon yafi sau goma daga zamanta,ta
kuma tabbatar komai yana nan intact kamar yadda ya kamata ace ya kasance din,sai ta
koma ta zauna tana sauya tashar Tv din zuwa mbc Bollywood bawai don tana jin dadin
kallon ko yana burgeta ba,dukkan hankalinta yanzu da nutsuwarta shine takowarsu
cikin falon,su zauna kuma su cika cikin su da abinci da abin shan da ta tsumashi ta
kuma tanadashi musamman saboda su.


*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*

PAGE 64


Saddiq da musaddiq dinne a gaba shi kuma yana biye dasu a hankali a
hankali,hakan ya sanya suka dan masa tazara kadan. Wayar Mika'il yake amsawa,wanda
yakeso ya tabbatar komai ya zama daidai zuwa ranar Monday da zai koma office.
Yanason ya gabatar masa da dukkan wasu mu'amala na kudi da banking ya samu bayan
tafiyar tasa,komai na shige da ficen kudi.

Yana wayar ne amma hankalinsa yana kan saddiq da musaddiq,tamkar 'yan
biyu kamar yadda kowa yake musu kallo hatta da makarantun da sukayi. Suna hira
abinsu ne cikin wani irin shaquwa da jituwar jini. Malam saidu ne ya bude musu
qofan da kanshi,ya rusuna kuma yana miqa masa gaisuwa sai ya gyada masa kai hadi da
daga masa hannu saboda wayar da yakeyi din,ya taka a nutse yana bin bayansu.

Dab da zasu isa steps din da zasu sadasu da ainihin falon yaji gabansa
yayi wani mummunar faduwa

"Zamu qarasa anjima" Yace da Mika'il a gaggauce yana katse wayar ba tare daya jira
amsarsa ba

"Kai saddiq" Ya furta da muryar da taja hankalin maamah dake falon,wadda dama
dukkan tunaninta yana fa farfajiyar gidan tana sauraren kowanne motsi.

"Saddiq kuma?" Ta tambayi kanta da kanta a mamakance,sai ta tuna kuma bata da
sauran lokacin batawa,don muddin ta bari wani bayan yaran nata ya taka wannan
shirin akwai matsala,don haka ta zabura tayi zumbur ta miqe ta kuma nufi bakin
qofar falon da sassarfa.

Wancakali tayi da doormat din,ta sanya hannu ta dauke abun da yake
qasan,sannan ta finciki tsintsiya dake ajiye a can wani gefe daban ta fara tattara
sauran abubuwan da suka rage.

"Kunyi addu'a ne?" Ya fada yana tsaresu da idanu duka su biyun. Juna suka kalla shi
da musaddiq din

"Hamma ai daga masallaci muke" Saddiq din ya fada dukkaninsu suna sauke qafafunsu
daga saman steps din da suka fara dorawa

"Kuyi addu'a kafin ku shiga.......haka musulunci ya koyar damu,kome zakayi akwai
addu'ar da akeyi masa" Ya fadi idanunsa akan musaddiq

"To hamma" Suka fadi sannan suka maida qafafunsu kowa bakinsa yana dan motsawa.

Da kallo ya bisu zuciyarsa cike da wani wasi wasi da baisan daga inda
ya samo asali ba. Sosai hankalinsa yana kan musaddiq da ya tabbatar baisan komai
akan shirin maamah nason raba tsakaninsu da iyalin alhaji hamza ba. Shi kansa abban
baisan komai ba akai,shi daya yake juya maganar tsakanin qirjinsa da zuciyarsa.

Dan ja sukayi suka tsaya sanda suka sameta duqe tana tattare wani abu
da basusan meye shi ba. Ta daga kai tana dubansu,wani irin bacin rai ya cika mata
zuciya fal.

Ta yaya banda sun raina umarninta zata ce tana buqatar ganinsu su biyu
su rakito mata wani?. Fushin yanason yayi galaba a kanta amma tanata qoqarin
danneshi. Yanzun ba lokacin nuna fushi bane ko fada..... Lokaci ne na sauke kai da
maida komai ba komai ba muddin nasara take da buqata,wannan shine abinda hajja ta
gaya mata.

Dole ta qirqiro murmushi tana cewa cikin nuna kulawa a garesu gaba daya

"Maraba da 'yan samari na" Saita zubda abun cikin kwandon shara ta kuma taka zuwa
ciki tana fadin

"Ku qaraso mana". Sai da suka fara shiga sannan yabi bayansu yana kula da hagu da
damansu

"Ina ma'aikatan suka barki kina shara?" Fuad ya furta da nutsatsiyar muryarshin nan
yana zama hannun kujera hannunsa goye a qirjinsa yana kuma qoqarin karantar komai
dama motsin komai dake a falon.

Dan murmushi ta saki tana zama saman daya daga cikin kujerun alfarma
dake falon

"Ina buqatar kebewa da 'ya'yana,nayi sirri dasu irin na uwa da 'ya'yanta,shi yasa
na sallamesu yau da wuri". Maganar tata sai ta kasance kamar ta jefi tsuntsu biyu
ne da dutse guda,don haka saddiq sai ya rusuna kawai yana gaidata.

"Lafiya alhamdlh saddiq......ya mutanen gidan?"

"Suna lafiya maamah"

"Ma sha Allah,don Allah kace ina gaidata da kyau da kyau"

"Zataji in sha Allah......hamma zan qarasa,saikun fito" Idanu fuad din ya zube
masa,yayin da maamah ta bata fuska tana cewa

"Ina kuma zaka daga shigowarku ko zama bakayi ba?". Dan murmushi yayi yana saukar
da kansa qasa cikin girmamawa

"Gida zan qarasa,jibi zamu koma company ban kuma gama shiryawa ba,kinsan kuma
hamma......bazai dagan qafa ba idan aka samu kuskure" Tabe baki tayi kadan ta yadda
ba lallai bane su fuskanta,qasan zuciyarta kuma cike fal da baqinciki da bacin
rai,amma kuma a fili saita saki murmushi

"Gaskiya ne,to Allah ya taimaka,ka gaisheta"

"In sha Allah" Ya fadi yana waiwayawa gefan musaddiq ya bashi hannu yadda suka saba
yana yin gaba.

Shiru falon ya dauka sanda saddiq ke ficewa,cikin ranta take gayawa
kanta da kanta saura kadan komai yazo qarshe.... .watan watarana saidai ya gifta
katangun kamfanin ya ratse ya wuce ta bayansu,komai na wata dama ta shiga cikin
kamfanin baida ita.

Sai daya kammala ficewa tsaf sannan ta maida dubanta garesu,dukansu ta
fahimci kamar hankalinsu baya tare da ita,don haka ta danyi gyaran murya,gyaran
muryar daya sanya dukansu suka dubeta,sai ta saki musu murmushi.

Amsa gaisuwarsu dukka su biyun tayi,a yau sai take jinta kamar a
aljannar duniya,sai takejin kamar burinta ya gama cika duk da an samu matsala a
karon farko,amma akwai tafiya ta gaba,ta tabbatar ba zasu tsallakewa abincinta ba.

Tanaso a yau tasan abubuwa masu yawa game da rayuwarsu,tanason tasan
adadi da zurfin dukiyar da kowannensu ya mallaka,koda batasan duka ba,tanason ta
karanci kaso me tsoka.
"Ina fata dukkaninku kuna lafiya"

"Alhamdulillah" Suka fada kusan a tare kowa ba karsashi a tattare dashi.

Ta fahimci hakan,don haka ta gyara zamanta tana fadada fara'ar fuskarta

"Ina fatan zaku cire komai daga zuciyarku,kuci gaba da kallona a matsayin
mahaifiyarku,komai zai wuce mu fara gina sabuwar rayuwa tsakanina daku.....ina
buqatar 'ya'yana a kusa dani kamar yadda kowacce uwa take da buqatar 'ya'yanta.
Inaso na kasance daku tamkar komai bai faru ba,nayi alqawarin baku farinciki da
kariya kaman yadda kowacce uwa ke bawa 'ya'yanta" Ta qarashe maganar cikin matuqar
raunin zuciya da karyewar murya kamar wadda ke shirin sakin kuka.

Dukkaninsu dubanta suke,kowannensu da mabanbancin feeling a
zuciyarsa,saidai kuma dukkaninsu akwai mamaki danqare qasan ransa.

Ci gaba da dubanta fu'ad yayi mamakinsa yana qaruwa. Tunda ta fara
magana baiji inda tace tayi nadama ba......nadama koda qwaya daya akan abinda ta
yiwa abbansu ba,su din basu da buqatar ta nema yafiya ko afuwarsu,tunda itace ta
haifesu,tayi silar kowasu duniya.....ba wani abu da zasuyi mata wanda zasu saka
mata da iya wannan aikin......amma kuma abban fa?,kota manta cewa itace silar
komai?,ta manta itace silar faruwar komai?. A yanzun ya Fatimid tafi buqatar
hankalunsu a kanta da abinda suka mallaka sama da nadama neman afuwa ta zahiri da
yafiya daga mutumin da aka zalunta wanda yanzu haka yake kwance a qarqashin qasa.

"Banaso ku dinga nesa dani suka nesanta kanku dani,bani da wani abu dana mallaka a
yanzu sama daku.......ina zaune ni kadai,idan mutuwa ma nayi kenan saidai kuji
labari daga wajen bare?" Ta maida tambayar kan fuskar musaddiq. Kanshi ya girgiza
mata yana sauke kan nasa qasa. Har yanzu idanunsa da sauran tunaninsa sun kasa goge
masa komai,ballantana hammansa daya tabbata komai yana rubuce ne a allon zuciyarsa.
A duk sanda ya kalleta sai ya tuna ruwan data watsa saman fuskar majinyacin
mahaifinsu sanda ya buqaci ta bashi ruwa,shine ya zame masa rumfa yaje ya kwanta a
samanshi da zummar kareshi saboda sanyi da yadda ya jiqe din sosai,a sannan ta taka
ta fice a dakin hankalinta kwance tana waqe waqe abinta.

"Don Allah koda abincin dare ne ku kasance tare dani ko na safe... Ku bani koda
awa daya kowacce rana mu zauna ni daku nasan na haifi 'ya'ya nima kamar kowacce
uwa.....don Allah" Ta sake fada da muryar roqo sosai,raunanniyar muryar daka iya
sauko da tausayi a zuciyar wanda baisan manufar me magana ba.

"In sha Alla" Kawai fu'ad din ya furta. Ya sani koma me zaice yanzu ba maslaha zai
kawo ba,ba kuma zata taba fahimta tunda akwai banbancin manufa a tsakaninsu.
Kowanne a cikinsu abinda ya ajjiye a zuciyarsa daban.

"Muje ga abincin dare can na shirya muku.....abinda nasan kunfi so sosai" Ta fada
tana murmushi ranta yana mata dadi da yadda suka karbi request dinta suka amince da
xuwan nasu.

Ba wanda ya musa mata,suna dai binta da ido da kuma hankulansu har xuwa
sanda ta jawa kowannensu kujerar zama tana fadin

"Bismillah" Inda ta kasance daga kujerar dake facing dinsu.

Serving nasu komai da komai tayi,tana yi tana jansu da hira tare da
qoqarin tuna musu wani abu na daga quruciyarsu. Shidai fu'ad idanu ne kawai nashi
ba tare daya iya maida komai ba,har ta kammala tana fadin

"Gashinan kowa ya dauki nasa". Duban abincin yayi da kyau,gaskiya ta fada batayi
kuskure ba,a baya baida abincin da yakeso irinsa,amma tun daga ranar data dafa
abincin cikin gidansu,ta kuma yiwa mahaifinsu haramiyar abincin a sanda yake kwance
yana jinya.....yunwa take sake take rawa wajen galabaitar dashi,ta hana masa
abincin,abinda yayi silar kwanansa da yunwa,tun daga ranar har kawo yau bai sake
saka irin abincin a bakinsa ba,daga ranar ya fita a ransa,fita ta har abada wadda
har yau bai sake dawowa zuciya da rayuwarsa ba.

"Shikam hamma ai maamah yanzun wannan ba cimarsa bane......nima kuma kin manta dama
ba kasafai na fiya ci din ba?" Musaddiq ya fada yana shafa kanshi idanunsa cikin na
maamah din.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 65



Wani abu ne yaso ya tsaye mata a rai,tunzura takeso tayi amma kuma tana
gayawa kanta ba yanzu ba......idan ma basuci na yau ba ai na gobe yana nan,muddin
kuma zasu ci gaba da taka qafarsu cikin gidan yau ko gobe nasara tana nan tare da
ita.

"Yaushe Muhammad ya daina ci?" Ta yiwa musaddiq tambayar sai kuma ta maida dubanta
ga fuskar fu'ad din a mamakance,saidai kuma sanda suka hada idanu dashi sai komai
daya faru a wancan ranar ya dawo mata a take,amsar tambayarta ta fita kamar budewar
shafukan littafi.

Wani abu taji me nauyi wanda sam baiyi kama da kunya ko nadama
ba,tabbas a baya din don ba cikin daidanta take ba.....ba yaran bane a gabanta
ballantana abinda ya shafesu da har zata lura da meye ya damesu da wanda bai damesu
ba.....amma tabbas sai yanzu ta tuna,tun daga ranar yake bar mata kwanonta gaba
daya yadda ta zuba.

"To amma bai kamata ace bakuci komai ba koda lemo ne" Ta sake fadi tana jan jug din
gabanta tare da qoqarin raba kofunan ta zuba musun kada ya zamana komai da komai ma
tayi asararsa a yau din.

Idonsa still a kanta,ya miqa hannu ya jawo gorar ruwan daya tabbatar a
kulle take ya soma budeta,qarar budewar ya sanya ta daga kanta zuwa gareshi tana
dubansa

"Ruwa kuma muhammadu?,ga lemo dai" Ta fada tana tura masa wanda ta zuba

"Maamah dare ya soma yi.....idan kuma dare ya fara bana

Please Login or Register in order to submit comment