You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k......" Bai
qarasa ba yaji saukar abu a qeyarsa,agogon hannunsa ya kwance ya sake jifansa dashi
don ya rasa dame zai jefeshi wannan karon.

Dafe wajen yayi ya waiwayo yana dubansa fuska a hade

"Amma dai kasan wannan zallar cin zali ne ko?,ni nakar xomon?,kaje ka yiwa anni
bayanin abinda yasa zaka aikota kwana da ita daki daya mana da kanka".

"Ya isheka farouq" Ya fada yana nunashi da yatsa,alamun ya fara qureshi.

"Oho" Ya fada yana sungumar ruwansa yayi dakinsu baiko sake waiwayoshi ba.

Shuru ne ya ratsa falon bayan wucewar farouq din,sai motsinsu kadan kadan
da yake jiyowa daga dakunansu. Maganar gaskiya farouq ya cuceshi,inda kuma yasan da
wannan da tuni ya sanya an canza musu gida da yafi haka yawan dakuna kafin su
qaraso. Miqewa yayi abisa dole yana soma dosar dakin,abu daya ya sani shi bayason
takura,yana son bajewa sosai ya sake a duk inda ya zabi rayuwa,so wanzuwarta cikin
dakin kuwa bazai bari ya zama silar hanashi sakewa ba.


*Maamah*


Sake juya tickets din hannunta tayi guda biyu tana sake qare masa
kallo. Mamaki da wani irin dunqulallen baqinciki yana yayyanka zuciyarta. Ta rasa
wanne hamshaqinne ya juya tafiyar daga farkonta ta koma qarshe?. Maldevis shine
waje na farko da zasu je a qa'ida kaman yadda ta samu tabbacin dukka iyalin gidan
alhj hamza kibiya can suka wuce.....saudiyya kuma shine waje na qarshe da zasu
ziyarta daga nan kuma sai gida Nigeria,amma wanne hamshaqinne ya karkatar da tata
akalar tafiya daga saudiyya kafin ta sauka maldevis sannan su rankaya su wuce
turkey tare?.

"Hajiya ameena.....tabbas wannan aikin ameena ne" Ta fadi tana jin wutar qiyayyar
matar tana sake ninkuwa a ranta. Zazzafar iska ta furzar tana fitar da idanunta
waje irin na zallar takaici da kuma tunani. Ita kuwa ta yaya zata dagawa ameena
qafa?,ta yaya zata bar ameena taci gaba da shaqar iska cikin aminci?,ba ragi
tsakaninta da ameena har abada......yadda bata barta ta samu cikakken iko da mulki
da 'ya'yanta ba.....tabbas haka zata zama silar tarwatsa nata ahalin gaba daya,duk
wanda ya gaya mata cuta ba shakka ita mutuwa zata gwada masa,sai kawai taja wayarta
tana laluben fareeda,tana jin wannan karon a gaban idanun ameenatun zata gwada mata
nata izzar da qarfin mulkin kasancewar uwar data dauki cikin fu'ad tayi naqudarsa
ta kuma haifeshi.......a gaban idanun kowa zata gwadawa sabreen ta isa da
danta......zata nuna mata kuma tana da ikon sanya yaronta ya auri mata d'ai d'ai
har guda uku rigis bayan ita.

Shuru fareeda tayi tana sauraren bayanan maamah,saidai kuma zuciyarta
cike fal da bacin rai da baqin kishin sabreen. Wata zazzafar iska ta furzar tana
ajiye bututun shisha dinta ta gyara zamanta

"Maldives ai gida ne......ina da sauran visa din qasar da ban gama cinyeta
ba,muddin na samu ticket jibi warhaka ina can......ko ba ticket zan sanya daddy
yamin hiring private jet......kya sameni a can" Daga haka ta yanke wayar tana latsa
wayarta ba bata lokaci tana neman number wayar daddy din nata.

Tafasa kawai zuciyarta takeyi,wannan karon da zafi zafinta zata
shiga,zata budewa sabreen aiki sosai kaman yadda zata budewa fu'ad,tana jin komai
mai sauqi ne......amma zata bari ta tabbatar da samun private jet ko ticket to
Maldives.

Bugu daya rak ya daga,ba kasafai ta fiya masa sallama ba,kusan
sallamarta kiran sunansa ne

"Daddyyyy.....maldevis" Ta fada da wata irin shagwaba kamar yarinyar da aka Haifa
jiya jiya

"Mamana......maldevis a daren nan?"

"Daddy gobe......ina da sauran visa na da kamin last two months.......ticket kawai
daddy nakeso......please daddy,it's an urgent need daddy". Murmushi ya saki yana
juya kai kafin yace

"Wani irin emergency issue ne haka ya taso mamana.....nifa mamana yanzun duk
hankalina yana kan aure,kiyi aure haka mamana.....ki zabi duk kalar mijin da kk so
zan tsaya miki" Maganar sai taji kaman tazo akan gaba,ta saki dariya tana cewa

"Nayi maka alqawari daddy.....indai na samu wucewa Maldives gobe ko jibi,ina dawowa
zan gabatar maka da mijin da zan aura"

"Really mama na?!" Ya tambaya da excitement cikin muryarsa

"Yes dad.....na taba maka qarya ne?" Ta sake fada cikin narke murya

"No mamana......bani minti goma.....i will get back to you"

"Thank youuuuuuu" Ta fada da sautin dariya tana sauke wayar.

Lips nata ta cinje tana duban wayar gami da saqa abubuwa iri daban daban
akan fu'ad. Zuwa sannan ta gama karance halayensa na girman kai da izza,yana da
tsananin taurin kan data tabbatar ita din kanta shaida ce,taso koda bata aureshi ba
ya bata hadin kai su mori quruciyarsu tare,amma martanin da yayi mata ya mata ciwon
data jima tana riritashi a zuciyarta.

"Tabbas saina biyo masa ta bayan gida,idan baiyi wasa ba sunansa ne zai fito a next
newspapers da magazine ba na waccan karuwar matar tasa ba......tunda shine
garkuwarta.......shi din ya kamata na taba qarfinsa" Ta fada da murmushin mugunta
tana murza yatsunta bayan ta tabbatar da hukuncin daya fado ranta shine abinda ya
kamata ta zartar.

Qarar wayarta ya dawo da hankalinta,ta daga da sauri ganin me kiran.
Wani ihun murna ta saki sosai tana jin dadi

"I love you daddy......thank you so so much......bansan ma ya zan gode maka ba" Ta
fada duk a rude saboda jin dadin samun ticket na tafiya Maldives jibi. Tana Lagos
don haka ba ita babu bin jirgi zuwa Lagos din,kawai kanta tsaye jibi zata bi qatar
Airways zuwa can

"Ki kawomin miji kawai bayan kin dawo"

"Baka da matsala dad....." Ta fada tana yanke kiran.

Tun a daren ta gama komai,ta gama hada komai ta kuma tanadi komai gudun
samun matsala goben kada ta tashi da uzurin da zata tashi ba'a daidai ba har ya
jawo ta hada kayanta ba daidai ba.

*_hmmmmmm,uhmmmmmmmmm_*


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


70


Sam sam bata fahimci daki daya farouq ya hadesu ba sai da ya murda handle din
ya shigo cikin sallama. Daidai lokacin da taketa qoqarin kauda luggage din zuwa
kyakkyawan gurin ajiyar kaya dake a dakin bayan ta ware scarfs din kanta ta daure
sumarta dashi.

Kallon juna sukayi,sai kowa yayi qoqarin dauke idonsa daga kan dan
uwansa. Haka kawai ta samu gabanta da faduwa,tunaninta kuma ya koma baya na yadda
aka kasafta dakunan

"Tashin hankali!.....shine part na na?" Ta fadawa kanta da kanta. Sam sam bata taba
hango yiwuwar wanzuwarsu a daki daya ba......ita da mutumin da basa ga maciji sam
sam,ta yaya zata iya hada numfashi dashi qarqashin rufin daki guda daya?,lallai
inda tasan da yiwuwar faruwar hakan wannan kadai a wajenta ya isa dalilin da zai
hanata yin tafiyar ma gaba daya.

Sakin abinda takeyi tayi ta kuma ware veil dinta ta lullube kanta dashi
dukka tana satar kallonsa. Baiko nuna yasan da tsaiwarta a wajen ba,hasalima yanata
daddaga labulayen dakin yana laluba sauran gurare irinsu socket na dakin,switch da
sauran gurare saboda tsaro,gudun samun wata boyayyar camera da basusan da ita ba.

Baisan ta fice ba sai da yaji alamun jan qofar,ya bi qofar da kallo
kafin daga bisani ya dauke dubansa daga wajen yana ci gaba da abinda yakeyi.

Wannan dukka ba take taken raini bane ba?,amma ba wanda ya jawo masa
illa farouq,kuma tabbas zaija kunnensa,bazai yiwu cikin qasashe biyu da xasu sake
zuwa a gaba ya qara hada musu guri ba,duk da kusan duka qasashen ba inda baida gida
mallakin kansa uku ko hudu,da kansa zai zabi gidan da yakeso saboda gudun faruwar
hakan.

Sai daya tabbatar da lafiyar dakin sannan ya soma rage kayan
jikinsa,don bazai iya bacci haka ba,ko wankan ma bayajin zaiyishi sai idan ya
tashi,duk da farouq nason rage masa jin dadinsa.....don da gaske hutu
yazoyi,yazo.ya huta inda ba zaa sashi magana bs ko ciwon kai.

Turus tayi sanda ta fito parlor din,wayam ba kowa sai dan motsinsu daga
dakunansu. Bin duka qofofin dakunan dake kulle tayi da kallo,saita rasa meye
abunyi.
Da kunya dai ta jewa dakinsu anni wanda ta tabbatar a yanzun suma
hutawa sukeyi,idan ma taje tace mata me?. Ba zata zauna daki daya da d'anta ba
wanda mijinta ne a qa'ida duk duniya kuma haka suke kallonsu?,wanda sukasan sahihin
zamansu mutanene daidaiku.......hatta da amna bata sanya ran ta gama fahimtar komai
da komai. Rasa madafa tayi,dole a qarshe kwanyarta ta gaya mata bata da sauran wani
abunyi illa ta koma dakin ta rungumi haquri na yau,zuwa gobe saita nemawa kanta
dalili da mafitar da zata sanya a raba dakin.

Daidai sanda ya isa bakin qofa da zummar kashe switch na qwan ita kuma
ta murza qofar ta shigo. Baikai ga kashewa ba,don haka tsaf ta ganshi.

Murdadde kuma qaqqarfan muhammad fu'ad jadda,ma'abocin daga qarfe da
dukka surar jikinsa ta koma ta qarfafan maza,saidai surar batayi muni ba,ta dace da
zatinsa ta kuma shekarunsa.

Babu komai a jikinsa sai gajeran wando iyakar cinyoyinsa,gaba daya
faffadan qirjinsa dake lullube da ni'imtaccen tattausan gashi ya tare kusan rabin
qofar dashi,abinda ya sanyata saura kadan ta fada qirjin nasa,abinda kuma ya saka
tsoro ya kusan sanyata shidewa,ta daburce duka cikin qanqanin lokaci,saita juya da
hanzari da zummar ficewa a dakin don ba zata juri ganinsa haka ba.

Sosai ya raina sanya hannu qwaya daya ya jawota zuwa gabansa,yanzun
hakan ma yayi mata,ya kuma ajeta a gefe,ya saka hannu ya murza key din qofar ya
rufe dakin,ya cilla key din saman gado sannan ya juya yana kashe switch din. Dakin
yayi duhu,saidai duhun bazai hanaka ganin komai dake dakin ba amma bada fitacciyar
suffarsa ba. Takawa yakeyi hankalinsa kwance zuwa gadon kaman ba'a tube yake ba

"Sannu a hankali wataran zan baki mamaki tunda na hanaki wannan rainin hankalin da
kikemin kaman dodo......sai kace a kaina kika taba ganin namiji a t......" Sai kuma
bai qarasa ba yaja tsaki sanda yake dora kansa saman pillow hadi da lumshe idanunsa
ya sauke numfashi.

Komai ta kasa cewa saboda tsoro daya cakude da takaici. Ta zuba ma
fuskarsa idanu duk da bata iya ganinta sosai tana jin bacin rai yana taso mata. Ta
tsani koda kalma daya ta hadasu shi yasa take kauce masa,don kowacce magana zai
gaya mata bame dadi bace a zuciyarta da kunnuwanta.

Don kanta ta samu waje ta nade tana curewa guri daya bayan ta gaji da
tsaiwa,don tuni yaja duvet ya rufe jikinsa dukka gaba daya har saman kansa.

Tsakiyar baccinsa ya dinga ganinta tana nufoshi cikin swimsuit sanda
yake zaune daga gaban swimming pool din yana kallonta. Kanta tsaye ta yiwa kanta
mazauni saman cinyarsa,yayin da albarkatun qirjinta yake tokare masa fuska da wani
irin salo na tsokana,baisan ya akayi ba ya samu kansa da goga fuskarsa a
jikinsu,abinda ya tashi kowacce tsiga ta jikinsa kenan,kowacce kafar jikinsa ta
soma fidda zufa,ya kuma jawota ya qanqameta da kyau yana cusa fuskarsa tsakiyarsu
kaman me neman taimako.

Wani birkitaccen salo takeyi masa,wanda ya taimaka wajen fitarsa a
hayyacinsa,ya kuma juyeta saman sun lounger din da yake kai,take al'amura suka fara
kankama tsakaninsa da ita.

Karar fadawar wani abu ruwan dake gabansu shi ya farkar dashi har a
zahiri. Idanunsa ya runtse da qarfi yana jin wani abu yana yawo a sassan jikinsa.
Yana jin tamkar a yanzun idanu biyu komai yake faruwa,wani irin zazzafan yanayi da
ya jima bai tsinci kanshi a ciki ba saboda yadda yake yawaita yin takatsantsan.

"Why?,why?" Ya tambayi kansa da kansa muryarsa can cikin maqogoronsa. Me yasa zata
biyo shi har baccinsa?,ba zata qyaleshi ya huta ba kenan?. Ko a baya da yake
fuskantar irin mafarke mafarken nan......babu guda daya daya taba ganin ainihin
fuskar ko gangar jiki,wannan shine na farko da komanta ya bayyanar masa a zahiri.

Fitowarta daga toilet shi ya sanya ya ware rinannun idanunsa a kanta.
Duk da bata iya ganinsa sosai amma taga alamun ya farka daga baccin. Dama ya kamata
ace ya farka din,tunda agogo ya nuna mata lokacin magariba yayi,amma kuma batasan
yadda zata tayar dashi ba,to ya samawa kansa lafiya daya farka din. Dakin ya mata
duhu saboda yadda duhu ya soma mamaye garin,saita laluba har ta dace da makunnin ta
kunna qwan dakin,take haske ya gauraye ko ina tarwai. Idanunsa ya lumshe yana cusa
shi cikin pillow

"Oh shit" Ya fada qasa qasa. Qoqarin tashi yake kafin hakan takai ga faruwa sai
gashi ta rigashi kunna hasken dakin. Ta yaya zai iya tashi ya miqe ya wuce zuwa
bandaki a yanayin da yake ciki?,tambayar dashi kansa baisan amsarta ba.

A nata bangaren ta gama gajiya da zaman dakin,burinta kawai ya budeta ta
fita,bataga wani alfanun zamansu suna musayar numfashi ba idan ba tsabar muguntar
nashi bane ya motsa. Ta duba luggage dinta ma sam bata ga hijab ba,sai mayafai ta
hada kusan uku dasu zatayi sallar. Ba ita ta hada kayan ba,zata iya cewa batasan ma
meye a ciki ba,anni ce ta musu siyayyar duk da uban lodin kayan da suke da wanda
ita kanta batasan adadi ba,amna kuma ta shirya mata tace basai ta buda ba ta saka
mata komai,ta kuma biye matan bata duba ba.

Bashi da wani sauran abinda ya rage illa dole ya tashi din,don haka ya
tattara uban duvet din ya nadeshi a jikinsa ya sauka yana wucewa toilet din a
gurguje. Ta danyi mamakin shigarsa toilet fa duvet,amma sai kuma sai ta kauda abun
daga ranta ta shimfida abun sallah tana jiran lokaci ya qarasa cika.

Ya jima a toilet din yana qoqarin ganin yanayinsa ya daidaita,yasha
azaba qwarai har ya dinga tunanin anya yau zai tsallake kuwa?. Kowanne jijiya ta
jikinsa aikawa take da saqo,sai bayan kusan minti talatin ya samu yanayinsa ya dawo
daidai,amma abinda yakeji a jikinsa bai sauya ba tunda jikin bai samu abinda yakeso
ba. Dukka jikinsa ya wani mutu qwarai da wata irin kasala data sakar masa da nauyin
jiki,haka yayi wanka ya daura alwala ya fito. Sauqinta daya data samu tana sallah
sanda ya fito din,don da alama a yanzun ma gaba gadi ya fito abinsa,ya buda kayansa
ya shirya cikin Moroccan jallabiyya black me adon golden din zare,ya saka qaramae
gold din hula ya feshe jikinsa da turare sannan ya dauki key ya bude qofan ya fice
don zuwa su hada jam'i dasu saddiq kaman yadda suka saba duk sanda sukayi tafiya a
qasashen daba masallaci a kusa da masaukinsu.

Fitarsa sai taji kaman ta samu 'yanci ne,ta kammala sallarta ta fada
wanka. Koda ta fito lokacin isha'i yayi,tasan qwarai tana da nauyin wanka,amma na
yau ya haura na kullum saboda ba qaramar wahala tasha wajen gane yadda zatayi
amfani da kayan bandakin ba.

Da karsashinta ta isa ga luggage dinta,saidai kaf ta cajeshi babu wata
suturar arziqi da zata iya sakata ta fita,sai uban lingerie data zuba mata kaman
karuwar dake neman customer.

Takaici ya sanyata komawa ta zauna ta rafka tagumi,kusan mintina ashirin
ta kashe a haka kafin ta jawo akwatin ta sake birkiceshi ko zata dace. Baqinciki ya
sanyata daga lingerie din daya bayan daya tana qare musu kallo. Kaya ne na rashin
kunyar da ita kanta kunyar wasu a ciki takeji idan ta daga

"Amna kin kwafsamin.....kin kasheni......shi yasa kikace kada na duba kayan" Ta
fada a fili daidai sanda ta daga wata lingerie din da aka yiwa wani yanka na
wulaqanci,aka fidda gidan mama daga qasa kuma aka mata wata huda.
Shigowarsa da sallamarsa duka lokacin guda ne,ta saki rigar da sauri
ya bita da kallo,ta miqa hannu da gaggawa ta tattareta ita da sauran tana zubawa a
akwatin sannan ta miqe.

Tanason masa maganan ya turo mata amna amma batason halinsan nan,ya
kammala abinda yakeyi ya doshi hanyar fita

"Idan kin gama abinda kikeyi din ki fito za'ayi dinner"

"Don Allah ka turomin amna" Ta katsi numfashi tana fadi da sauri har sai daya
waiwayo ya kalleta,karon farko da magana ta nutsuwa da respect harma da begging a
ciki ya taba hadasu,sai baice komai ba ya fice abinsa.

Harara ta ballawa qofan tana jin baiken kanta,me yasa ma ta
roqeshi?,gashinan ya yarfata a banza,dama me hali ai baya fasa halinsa,ta tsugunna
tana hade kayan cikin takaici. Saidai ko gamawa batayi ba amna tayi sallama,ta
tsaya daga qofa tana leqowa a darare.

"Ki shigo malama" Ta furta tana jifanta da harara.

"Shigowa makwancin hamma din kai tsaye haka hadari ne" Ta fada tana shigowa kaman
yadda ta buqata. Tana mamakin irin tsoronsa da sukeyi da yadda suke kiyayarsa
qwarai.

"Yau fada zamuyi dake har anni saita shigo sasanci"

"Me nayi adda?" Ta tambaya tana waro idanunta gami da dafe qirjinta

"Kayan da kika zubamin dama kenan amna?" Ta tambayeta tana dan kama kunnenta. Dafe
kunnen tayi dariya tana kamata,duk da riqon babu zafi amma tace

"Wayyo kunnen autar anni......aradu anni ce tace duka na zuba miki su,ni kuma da
naji tace haka saina kwashe wadancan......bansan mix ya kamata ayi ba" . Kunya ta
saukarwa sabreen,sai kawai ta saki kunnen amna din

"Saikije ki daukomin hijab dinki,kayan fice ficen ma duk na fasa sakasu tunda baki
sakamin kayan zaman gida na arziqi ba,da hijab zanta zama"

"Kaina bisa wuya na" Ta furta tana dariya gami da ficewa. Gudun jira sai kawai ta
shirya kanta cikin riga da wandon,rigar ta sauko mata har saman mazaunanta,wandon
kuma cif jikinta,don ya fidda sigar santala santalan cinyoyinta da faffadan
qugunta.

Murda qofan ya sanyata juyowa da sauri tana zaton amna ce ta
dawo,saidai a maimakon amna din sai taga hammanta. Fuad ne tsaye fuskarsa babu
walwala,kai tsaye ya soma kallonta tun daga qasan qafafunta,idanunsa kuma suka cake
akan qirjinta,abinda ya sanya yaji wani yarrr tsigar jikinsa ta zuba. Fes abinda
yaji da dumi da qamshin da wajen kiyi ya dawo masa fes a qwalqwalrsa,sosai jini ya
harba ko ina a jikinsa,yayi gaggawar damqe numfashinsa gami da hana faruwar abinda
yake shirin faruwar dashi.

Kallon qurillar da a yau yayi mata karon farko a tarayyarsu ya ratsa
kowanne jini dake gudu a sassan jikinta. Idan tace zata juya masa baya nan ma tasan
bata tsira ba,komai na jikinta ita kaΓ±ta tayi imanin a bayyane yake.

"Karki fara gangancin fitowa a haka......ki nema kinomo ko hijab ki saka a
jikinki". Sai ya saki qofar yana juyawa yana jin numfashinsa kaman zai tsaya da
aiki.
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 71



71


Tun kafin ya qaraso idanun farouq yana kanshi,fata ne fal zuciyarsa na
daidaituwar al'amura,yasan sarai halin fu'ad......yana da kafiya da taurin kai akan
abubuwan da bai fuskancesu ba,amma da zarar ya fuskanta din yafi kowa bawa abun
muhimmanci.

Ba jiya ko yau suke tare da fu'ad ba,tsohuwar alaqa ce da aka kafata
tun basu mallaki hankalin kawunansu ba,mutuwar jiki a wajen fu'ad na fassara abu
guda ne tattare dashi,rashin lafiya ta jiki irin ta kowa,da kuma motsawar feeling
irin na kowanne lafiyayyen namiji.

"Baka da lafiya ne dude?" Farouq ya fada qasa qasa sanda fu'ad ke zama a dining din
kusa da farouq din. Qoqarin murjewa yayi yana cewa

"Am fine......bacci nayi bai kuma isheni yadda ya kamata ba"

"I see..." Kawai ya furta da salon dashi kansa yasan farouq din bai aminta ba.

Tare suka jero da amna din suna fitowa,sai ya zare idonsa daga kan
wayarsa yana duban sashenta. Baiyi tsammanin zata saka hijab din kamar yadda ya
umarta ba,saboda yasam taurin kanta da kafiyarta,sai yaji wani sanyi na ratsashi
ganin karon farko tayi abinda yace da ita.

Gaida anni ta sakeyi tana rusunawa,sannan suma suka gaidata harda farouq
da yake da sauqin kai.

Amna ce ta soma servings nasu daga girkin cook din da sukayo hiring
anan qasar wato hidaya. Musulma ce data qware wajen sarrafa abinciccikan qasashe da
dama. Yawa yawan wadanda takewa aiki masu hannu da shuni ne don ta qware matuqa
wajen iya sarrafa tukunya. Da kudi sosai ake daukanta tayi maka iya adadin watanni
ko kwanakin da kakeso,amma a wajen mutane irinsu fu'ad din wannan din ba wani aiki
bane babba.

"Sabreen" Anni ta fada tana dubanta

"Na'am anni"

"Tashi ki serving mijinki" Wani nauyi taji ta aza mata,amma hakanan ta miqe ta
dauki plate ta soma xuba mishin. Tana xubawa tana kallonsa wai ko zaice ya isa
haka,amma abun takaici dukka hankalinsa yana kan wayarsa

"Qila ma chart yakeyi da fareeda" Wata zuciyar ta raya mata. Wato fareedan ce
mutum.....ita tana tsaye saboda shi amma.baida lokacinta?.

Duka anni na ankare da komai,abinda ya sake tabbatar mata da tunaninta
"It's family time muhammadu....a aje wayar nan haka ko?". Kansa ya daga ya dubi
anni yana gyada kai yana sakin qaramin murmushi. Karon farko data gayawa kanta da
gaske yana da kyau kaman yadda takeji daga bakin mutane. Bata taba ganin wani abu
me kama da murmushi akan fuskarsa ba sai a yau,zancan amna ya sake tabbata na ba
wanda yake samun fu'ad din a asalin fu'ad dinsa sai anni.

"Is okay" Yace sanda yake maida hankalinsa kan abincin data zuba masan.

Abinci sukeci cikin qauna da fahimtar juna,saidai ita din ta koma tamkar
bare a cikinsu,hasalima ta kasa sakewa sam,sai juya spoon takeyi.

Sai kunnuwa data sanya sanda suke lissafin ina da ina zaa fara fita a
goben. Amna keta lissafin abinda zasu kashe

"Adda nawa zaa saka miki a account" Amna ta tambayi sabreen,murmushi kadan tayi ta
girgiza kai

"Ko sisi amna.....me zan siya?"

"Tsaraba mana adda.... Akwai traditional market nasu fa,zakiga abubuwa da yawa da
zasu burgeki.....kinji anni wai batason komai......adda komai sai tace bataso?".

"Musaddiq ka saka mata wani abu itama... Mijinta ya qara mata,idan kuma bata da
dolla account saina ara mata nawa guda daya". Anni ta fada tana murmushi,kunyarta
tana dada burgeta sosai. Tsam ya miqe abinsa yana dauke wayoyinsa.

"Zan kwanta anni"

"Mu tashi lafiya,muma kusan kwanciya kowa zaiyi ai dare ya fara" A nan ya barsu
ya gangara ya wuce dakinsa,don bayajin sakewa har yanzu a jikinsa.

71


Tun kafin ya qaraso idanun farouq yana kanshi,fata ne fal zuciyarsa na
daidaituwar al'amura,yasan sarai halin fu'ad......yana da kafiya da taurin kai akan
abubuwan da bai fuskancesu ba,amma da zarar ya fuskanta din yafi kowa bawa abun
muhimmanci.

Ba jiya ko yau suke tare da fu'ad ba,tsohuwar alaqa ce da aka kafata
tun basu mallaki hankalin kawunansu ba,mutuwar jiki a wajen fu'ad na fassara abu
guda ne tattare dashi,rashin lafiya ta jiki irin ta kowa,da kuma motsawar feeling
irin na kowanne lafiyayyen namiji.

"Baka da lafiya ne dude?" Farouq ya fada qasa qasa sanda fu'ad ke zama a dining din
kusa da farouq din. Qoqarin murjewa yayi yana cewa

"Am fine......bacci nayi bai kuma isheni yadda ya kamata ba"

"I see..." Kawai ya furta da salon dashi kansa yasan farouq din bai aminta ba.

Tare suka jero da amna din

Please Login or Register in order to submit comment