You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne da harshen uwa kuma
mahaifiya........ba me cin alfarma ko darajar kowa ba cikin duniya......ina magana
ne da baki na uwa wadda haihuwa ta karramata da wannan darajar..." Tayi maganar a
jere cikin sauti da yanayin da ya sanya yaji kowanne noti na jikinsa ya qarasa
kwancewa

"Wacce irin nannauyar buqata ce haka?" Ya samu bakinsa da subucewa yana tambayarta
ba tare daya shirya hakan ba don dai kawai kunnuwansa sun kasa jumurin jiran jin me
zai fito daga bakinta.


Gajeran murmushi ta saki tana gyara zamanta

"Na godewa Allah da tun yanzu ka gane girman buqatar uwa akan
d'anta.......muhammad" Ta sake kiransa da sunan nan dake masa girma da nauyi.

"Ka jima kana bijirewa umarni na.....kana sabawa Maganata......ka dade ina fadin
magana kana taketa,kana mata riqon sakainar kashi......ina dauke maka kai,ina maka
kara ina maka alkunya......ina maka sassauci irin na uwa......ina da tarin
buqatu......ina da tarin burika.....ina da mafarkai da yawa da nakeso na cikasu
amma dukka ban samu wannan damar daga gareka ba.....a yanzu ina da wani babban
mafarki akanka na samu macen auren dake sonka ba don dukiya ko abinda ka mallaka
ba,macen auren data dace dakai ta gari wadda zata zauna da kai da zuciya
daya......wannan damar da ita nayi amfani na laluba na kuma zaba maka nagartacciya
guda daya......wadda nakeso kai tsaye ka karbeta saboda umarni ne nakai tsayen daga
uwa zuwa d'anta!" Ta qarashe maganar da kakkaifan harshen daya sanyashi wata
matsananciyar faduwar gaba da bai taba jin irinta ba
"Ya ilahal aalameen" Ya furta a zuci da bakinsa murya can qasa. Wanne irin lamari
ne haka katsam lokaci guda?. Matar aure fa take magana maamah din......maamahn da
bata gama zama nagartacciyar uwa cikakkiyar garkuwa ga 'ya'yanta ba ta kowacce
fuska?,yaushe zata samu nagarta fahimtar nagartacciya cikin mata?.

"Maamah......aure ba abun wasa bane,aure ba tafiya ce ta yau kuma a kammalata
gobe.....aure abune da akeso mutum biyu su gani su kuma aminta......"

"Dakata Muhammadu!!!" Ta furta a tsawace tana daga masa hannu.

"Ka manta a farkon zance na?,na gaya maka ba neman shawara nake ba?,hukunci na
yanke ina gaya maka hukincin ne saboda kasan da wanzuwar abun.......zan nema dangin
mahaifinka koda mutum qwara daya ne,da nawa ahalin mutum uku a ciki,su kadai sun
isa suje neman auren.......bana buqatar komai naka a ciki......bana buqatar
sisinka,zanyi komai.....abu guda daya tal nake buqata" Tayi maganar tana daga
yatsanta dan manuni.

"Ka kula da ita yadda zaka kula dani mahaifiyarka......ka bata kulawa ka tattalata
kamar yadda kowanne d'a namiji yake tattala mahaifiyarsa da 'yarsa da
matarsa......idan kanaso ka hadu da mummunan fushi na kuma kalar wanda baka taba
gani ba......ka gwada tsallake wannan dokar" Wani irin mawuyacin hali yaji yana
neman fadawa,lokaci daya taji tamkar an daga duniyarsa ne an kifata daga sama zuwa
qasa,yayi qoqarin tattaro muryarsa a raunane yanason sake fahimtar da ita,don shi
ba abinda ya fahimta a wannan abun face wani kitsatse kuma shiryayyen al'amari da
muddin ya rufta ciki rayuwarsa kaf yana hango rugujewarta

"Amma maamah......"

"Muhammadu.......muddin kace zaka gwada bijiremin.... To ka jira tsinuwa daga
gareni da zata biyo baya......zan daga maka nono......zan maka Allah ya isan nonona
daka sha?!!". Qas yayi da kansa yana jin wata zufa tana keto masa,duk kuwa da
wadatar ac dama pan dake kadawa a hankali.

Jin jikinsa da kansa yakeyi gaba daya kaman ba nashi ba......yanajin
kaman gini me hawa goma ne ya lafto saman kansa. Bakinsa yayi nauyi qwarai,yaji
bashi da wata sauran kalma data rage masa.

"Kiyi haquri" Ya fada a mugun raunane.....raunin da a sannan idan abokan adawar
kasuwancinsa suna wajen zasu rantse da Allah ba muhammad jadda bane.

"Naji......tashi kaje ka fara shiri" Abinda tace dashi kenan wani dadi yana ratsa
qasan zuciyarta ganin alamun nasara baro baro a tare da ita. Zuciyarta fari tas
sanda yake fita,tana jin wannan karon sa'arta ce,lokacin sa'arta yazo,sabreen kawai
ta rage mata,sai kuma ta koma wajen boka ya hada mata dukkan kayan sa'a,ya bata
kuma manya manyan bomabomai din da zata bawa sabreen ta shiga gidan dasu masu
qarfin da sa'arta zata qarasa cimmata nan da nan.

Da qyar yake jefa qasarka gaba yana nufar gidan ba tare da cikakkiyar
fahimtar inda yake sanya qafar tasa ba.

"Wannan wanne irin tashin hankali ne?,wanne irin shiri ne kuma daban wannan bayan
shirinta nason ciyar da su da shayar dasu da kayan tsubbu da suka kaucewa hanya
sunna da kuma koyarwar musulunci?" Ya yiwa kansa da kansa tambayar sanda yake
zubewa saman kujerar falon kowanne sashe na jikinsa yana mutuwa.

"Wanne shiri ne daya wuce ta ajiye maka wadda zata baka komai kaci ka kuma sha kai
tsaye ba haufi?,wadda zaku rayu tare qarqashin rufi daya?,ta yadda komai zaifi
sauqin kama ka?"
"Yes!" Ya samu kansa da fada bayan dogon nazarin da kwanyarsa ta tafi me dogon
zango.

Ba shakka kusan duk wanda ya sani tare da maamah babu wani halin dattako
ko na alkhairi sam sam tare dasu,ta yaya maamah din har zata iya cimma
MAR'ATUSSALIHA da irin wannan halaye da dabi'u nata?. Tsaftatacce sai tsaftatacce
fa haka qur'ani ya fadi Allah da kansa kenan yake bamu labari.

"Wacce yarinya ce ke shirin jefa rayuwarta tsakanin runtsin da yafi qarfinta?,wacce
yarinya ce wannan?" Yayi tambayar a fili yana qanqance idanunsa.

Anaso ayi amfani da maamah ne ko kuma maamah din keson amfani da
wasu?. Ya sake tambayar kansa da kansa yana sake zurfafa nazarinsa wanda yaji kaman
kansa zai tarwatse,sai yaji me yasa bai tsaya ya nema cikakken sani akan wacece
ba?,sunanta?,d'iyar wace?,a ina take?. Yanaso ya sani da gaske.......yana buqatar
sani,amma kuma bayaso yayi kowanne motsi ko taku da zai sanya maamah ta sake
tsaurara aqidarta a kansa.

Tana a wajen tana juya girman nasara takun farko data fara samu ita
da matar da takewa kallon aminiya wato hajja,ta kuma neman alfarmar ta shirya don
rakata wajen boka nan da kwanaki biyu ko uku kafin masu neman auren sabreen sukai
ga magabatanta saiga zuwaira ta shigo.

"Alhaji hamza ne yake son magana dake". Sosai zancan ya bata mamaki,ta dauke wayar
daga kunnenta tana kasheta gaba daya cike da madaukakin mamaki. Alhaj hamza yau a
gidanta?. Bai taba tako koda qofar gidan ba koda kuwa da wasa tunda ta dawo gidan
da zama karo na biyu......ko a baya ma ba zata iya tuna sanda irin haka ta faru ba
sanda marigayi yana da rai ballantana yanzu.

"Alhaji hamza kuma?" Ta sake jaddada tambayar ga zuwaira.

"Eh shi".

"Ce masa ya qaraso ciki,faduwa tazo daidai da zama......nima nemansa nake" Tayi
maganar tana hade ranta da kyau tun Alhaji hamza din bai kai ga shigowa cikin falon
ba,zuciyarta tana raya mata indai har daga fitar fuad ne yaje yakai masa qararta
lallai sai ta saka sunyi nadama daga shi har fuad din. A wannan karon zata nuna
masa shi da munafukar matarsa.....dama sauran dukkan munafukan dake gefe suna kallo
cewa,itace fa ta haifi fuad harma da musaddiq......babu wani da yayi mata
wahalarsu.......babu wanda kuma yasan ciwo da zafinsu sama da ita.



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

̶H ̶U ̶G ̶U ̶M ̶A

◦•●◉✿PAGE 98✿◉●•◦




Cikin sallama da kuma cikakkiyar kamala ya shigo falon. Kujerar da tafi
kusa da bakin qofa ya zauna tare da bismillah a bakinsa.

Ciki ciki ta amsa tana gyara nata zaman gami da harde qafarta ta dorata
daya bayan daya don nuna izza da tata isar.
Bata jin zata iya gaidashi ko gabatar masa da wani ruwa ko lemo wanda
mutumin dake da kima da martaba kawai akewa haka,sai ta jefa masa tambayar

"Ina fata lafiya ce ta kawoka.....sannan ina fatan alkhairi ne ya sanyaka takowa
cikin gida na?". Wani murmushi ya sake dake cike da kamala da dattako. Shi ba mace
bane,saboda haka bayajin yana da wani lokacin bata lokacin gutsi gutsin maganganu

"Batun d'anki kuma d'anmu shine ya taso dani....."

"D'ana dai....."

"Hakanma yayi.......jiya ya sameni da zancan samun matar aure da yake buqatar aje
nema masa ita,kuma cikin qasa da sati uku yakeso a kammala komai".

Wani murmushi ta saki tana kada qafarta,shuru na kusan minti daya sannan
ta soma magana cike da izza.

Malam hamza......ita kuma wacece?,a ina take?,shi yace yanaso ku kuma aura masa
akeso ayi?.....koda yake duka wadannan tambayoyin basu da wani amfani......na yiwa
d'ana mata.....kuma nan da sati uku in sha Allah ya zama magidanci,saboda haka ba
wani batun wata yarinya da zan karba" Tayi zancan tana sauke qafafunta data harde.

Cikin son hadiye dafin maganganunta ya dubeta da duba na tsanaki

"Kin manta cewa a addinij islama muke ba wasu addinan na daban ba?.....laifi ne
idan kin aura masa wadda yakeso shima ya auri wadda yakeso duka a lokaci guda
mariya?". Yayi maganar hankali kwance yana tsareta da ido.

Kallonsa takeyi itama,saidai kaifin nasa idanun ya shafe nata,don haka
ta nanye dubanta a kansa tana jin sam sam bata aminta da wannan zancan nasu ba.
Zuciyarta kawai tana bata wata qulalliyar ce.....sun nemo masa mata ne kawai bisa
hadin baki suna son cusa masa don a samu damar cin dukiyarsa da lasisi (ni kuwa
nace uhmmmm.....idan mutum yana aikata abu sai ya dauka kowa ma haka yake?🤔
🤔....kaico da uwa irin maamah).

"Koma wacece ni uwa ga Muhammed fuad ban karba ba ban aminta ba". Ta fada tana tura
dankwalin kanta gaba.

Shuru ya ratsa na wasu mintuna,tamkar bazaice komai ba sai kuma ya miqe
tsam

" Zai auri zabinki.....kamar yadda ba wanda ya isa ya hanashi auren
zabinsa......abu daya ya rage miki ki bada komai akan yarinyar zamu binciki waye
mahaifinta......idan har ta cancanta.....zai auri mata biyu a rana guda.....zabinsa
da zabinki.....komai bazai wuce kwanaki hudu ba,don haka ki sanar da iyayensa
bangaren danginki don a fita haqqin kowa dake kansa". Daga haka ya juya yana takawa
a nutse yana fita a falon.

Miqewa tayi tsaye tana bin bayan nasa da kallo,Zuciyarta na wata irin
tafasa,ta yaya kansa tsaye da wannan confidence din yakeson nuna mata qarfi da
iyakarta akan abinda duk duniya tafi kowa iko dashi?.

"Ba zata sabu ba" Ta dauki wayarta da sauri tana kiran hajja.

"Daga hankalin na meye?,koma wace muna da boka,fiddata bazai zama wani abu me
wahala ba.....ki bashi kwatance gidan da sunan mahaifinta na ainihi.. ..kibi a
hankali ki zuba masa idanu......wannan karon harshi sai munyi maganinsa"

"Na gode aminiyata......duk duniya bani da masoyi kamarki"
"Yiwa kaine ai" Ta fada da binnanniyar ma'anar da ita daya ta barwa kanta saninta.

*****A mamakance yake riqe da takardu biyun a hannunsa yana dubansu. Gyara zamansa
ya sakeyi sosai sannan ya daga kansa ya kalli anni dake zaune a gabansa

"Abunne yaketa bani mamaki aminatu.....yarinya daya ce shi da mahaifiyarsa duka ke
fatutuka fa". Dan muskutawa kadan anni tayi tana daidaita zamanta.

"Ina cikin damuwa abba tun randa kace maamah ta zabawa fuad matar aure......bamusan
ya zata kasance ba yarinyar.....to amma yanzu kuma na shiga rudani ne,ya akayi
dukansu suke neman yarinya daya cikin rayuwarsa?". Shuru abban ya danyi,sannan ya
ninke takardar ya ajiye a gefansa yana sake dubanta

"Ina aminatu?" Dan murmusawa kadan tayi saboda shi kansa yasan wannan sarar tasa
tana bata dariya

"Gani abba"

"Yauwa.....abu na farko da nakeso ba gaya miki shine......ki dinga tunawa mariya
itace mahaifiyar Muhammadu na ainihi,ita ta dauki cikinsa tahaifeshi ta kuma
reneshi na wasu shekaru kafin ya dawo hannunki.....dole haqqin dake wuyansa nata
yafi naki.....sannan so na uwa daban yake,duk yadda kikeso ki kawar masa da abu me
cutarwa akwai guraren da ba huruminki bane shiga cikinsa"

"Abba nafi mariya qaunar me babban suna....." Wani murmushi ya saki yana girgiza
kai

"Kin fita sanin ya kamata ne,kin fita kuma tausayin dan adam da qaunar yara koda ba
naki 'ya'yan bane.......mu ajiye wannan.....abinda nakeso dake......a baya kafin
bincike ya zamaya ya fito daga gida daya nima ina da wannan shakkar da
kokwanton,saidai kuma ba hurumina bane na hana.....bugu da qari na samu relief da
naji shima itace yarinyar da yake nema din,koda mariya da tata manufar na hadashi
da yarinyar.....to shi ba yadda za'a yi ya cutar ai da kansa da kuma tasa
rayuwar......abun tambayar qwaya daya ne kawai dana gaza banbancewa........ya akayi
dukkaninsu sukasan yarinyar?,kuma dukkansu suka afu a kanta?,wanda samun amsar
shima na huruminmu bane.....don muhammad yakai munzalin baligi kuma aqili da bazai
dauko abinda zai cutatar dashi ba".

Kai kawai anni ke kadawa,maganganun abba suna gamsar da ita,daga bisani da
saki nannauyar ajiyar zuciya

"Haka dukka maganganunka suke abba....daga yau in sha Allah bazan gushe ba ina
adduar idan akwai sharri cikin lamarin.....ubangiji al'arshi ubangijin sammai ya
juyar dashi ya koma alkhairi,ya kuma tsare dukkan wani sharri"

"Yau aminatu na......yanzu kikayi magana me kyau" Sai ta saki murmushi tana jin
kunya tana dan kamata,don har yanzu girma tsufa ko shekaru basu sanya wannan kunyar
dake a tsakaninsu ta gushe ba.

****Shudewar awanni uku kenan da wata murya tayi kiranta,ta kuma shaida mata cewa
kirane nakai tsaye daga gurin hajiya mariya akan batun neman aurenta,ta aminta ko
aje zuwa mataki na gaba?.

Duk da batasan meye ainihin abinda suke nufi da mataki na gaba ba,amma
hakan bai hanata sauke saqo da kakkausar murya ba.

"Idan tana saurare shikenan.....idan kuma saqo zaki isar mata ki tsaya ki saurari
komai dakyau don kada kiyi batan koda harafi daya wajen isar mata da saqona......ni
aminatu sabreen ba haja bace a kasuwa da kowa zai iya tayata da farashin da yaga
dama ya kuma siya,'yantacciyar diya nake ba baiwa ba wadda keda daman zabawa kanta
komai da kuma kowanne yanayi na rayuwa......da ita da d'anta dama dukkan dukiyar da
suka mallaka basa gabana koda kuwa zasu mallakamin dukkan abinda suka mallaka
din.......ki gaya mata kada ta sanya ran wataran akwai abinda zai canza ni......ba
wani abu da zai sauya tunani na akan maza......ba d'anta bama kawai.......har yau
ba'a samu nasarar Haifa min wanda zai janye ra'ayina naji ina da niyya ko sha'awar
ya zama mijina".

Sosai kalaman suka daki maamah wadda ke zaune a gefe tana sauraron
komai. Ba zata iya jurar jin wadannan nauyayan kalaman ba,don haka ta miqa hannu ta
gintse kiran cikin wani matsanancin fushi,sannan ta dauki wayarta tana laluben wata
number tana cewa

"Zaki fahimci cewa komai yana da nasa iyakar".

Numfashi ta zuqa tana duban agogo,sai tayi zumbur ta tashi ta zauna.
Batasan yaushe lokaci yaja har haka ba,batayi sallar azahar ba don haka ta miqe
tana sanya slipper ta nufi tsakar gidan nasu.

Yadda taga kusan kowa da kowa cikin yara da jikokin gidan sun dawo
sai ya dauki hankalinta. Su huda kusan sune sahun farko da sukafi kowa dawowa gida
akan lokaci,ya akayi yau suka zama na qarshe?. Tun tana daura alwala take sanya ran
shigowarsu amma shuru,ta kammala ta wuce daki,ta tayar da sallah ta kammala,sai
tayi zaune a wajen tana zuba kunnuwa.

Shuru maqatau,abinda ya sanyata miqewa kenan gabanta yana faduwa. Basu
taba kai warhaka a makaranta ba,har gashi masu zuwa islamiyya cikin gidan sun fara
wucewa,sai kawai ta dauki wayarta da key din dakin ta fito.

Layukan nasu ta duba amma babu su,abinda ya tsananta faduwar gabanta
kenan. Ta dauki wayarta zummat nemo busari yazo ya dauketa suje makarantar sai
gabanta yayi wani mummunar faduwa sanda idanunta suka sauka kan number wayar da aka
kirata dazu. Tunanin ya sake bnagazar Zuciyarta abinda ya sanya qafafunta yin sanyi
qalau,ta sulale tana zama saman dakalin dake daura da ita hannunta yana yin sanyi
qalau.

Wayarta taci gaba da kalla tana kuma taya agogon dake fuskar wayar
irga wucewar kowanne second,har zuwa sanda ya nuna mata qarfe biyar daidai harda
rabi na yammaci sai kawai ta danna kan number ta kira.

Kira ta dinga yi ba qaqqautawa amma ba'a daga ba,yayin da duhun dare
yake sake kusantowa,yan islamiyya da wadanda na sukaje kasuwa sunata dawowa suna
giftata kowa idanunshi a kanta don bash saba ganinta haka zaune a waje ba,wanda ita
sam bata damu da hakan ba,har zuwa sanda kallon da yawan kiran suka soma quntata
rayuwarta,saita miqe tana komawa cikin gida afujajan cikin matsanancin tashin
hankali.

"Indai tayi kuskuren sanya min 'yan uwa cikin harqallar da daga ni sai
ita......tabbas sai na shayar da ita mamaki koda hakan shine abu na qarshe da zanyi
a rayuwata" Ta furta a sarari ganin yadda duhu ke sake kutsowa ba'a daga wayar ba
ba'a kuma biyo kiran ba.

Sanda ake haramar kiran sallar ishai,sanda take zaune kan abun sallah
ta bada faralin magariba cikin rashin nutsuwa da tashin hankali tare da zurfafa
tunanin inda zata kamo bakin zaren kiran ya shigo wayarta.

Duk da kirana ne da take ta dakon shigowarsa amma bata daga ba sai dab
da zai tsinke.
"Ki sakesu.....don su din basusan komai akan rayuwata ba".

"Good......naji dadi nayi kuma farinciki,haka kwanyarki take ja da wuri?" Hajja
harira ta fada cike da mamakin gaske kan yadda ta dauki haske da wuri. Lalle da
gaske ne da akace musu tana da basira tana kuma da hadari.



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

̶H ̶U ̶̶G ̶U ̶M ̶A

◦•●◉✿PAGE 99✿◉●•◦



Idanunta ta lumshe tana jan wani numfashi har cikin hunhunta,tana jin
wani zafi baqinciki da radadi suna ratsa zuciyarta.

"Ina sake maimaitawa.....kada kuyi involving innocent lives a cikin wannan deal
din......ku sakesu safely".

"Karki damu yarinya.....qannanki zasu dawo hannunki cikin aminci..... Munyi hakanne
kawai don mu gwada miki banbancin tazarar dake tsakanin sama da qasa......don kuma
mu nuna miki girman wutar da kikeson wasa da ita kike kuma tunkara ta hanyar
bijirewa umarninmu"

Sake lumshe ido tayi,maganganun hajja suna ratsata ranta yana sake baci

"Ku sakesu" Ta sake maimaitawa muryarta cike fal da bacin rai. Ta nason fadin
abubuwa masu yawan gaske,saidai kuma tana qoqarin tausar zuciyarta. Ta sani ta riga
data shiga hannunsu,sun mata shigar sauri,sunyi mata kuma shigar ba zata,dole tabi
komai a sannu,dole itama ta shammacesu kamar yadda sukayi mata suma.

"Zamu sakesu amma bisa sharadin kin amince da buqatarmu?......"

Wani yawu me tauri ta tattaro a bakinta ta hadiyeshi da qyar. Baya
cikin tsarinta QARYA amma yanzu ya zama dole ta fara gwadata akan mutanen

"Na yarda" Ta fada kanta tsaye. Murmushi hajja ta saki sannan ta sake cewa

"Kada fa kiyi tunanin kin amince don ki yaudaremu mu sakar miki yan uwa haka
siddan.....lalala.......kina iya karya alqawarin,amma ki sani daga wannan lolacin
daga kuma rana irin ta yay rayuwarku tamu ce,ba wani motsi ko taku da zakiyi ba
tare da munsan ina zaki ko ina kika nufa ba.....ko yaya muka sameki da laifin
yunqurin karya wannan amincewa da kikayi daga yau har zuwa ranar da zaki kammala
aikinki.....hukuncinki abune da bazai fadu ba,na barki lafiya" Daga haka kiran ya
yanke.

A hankali wayar ta sulale daga hannunta,wanne irin abune kuma ke shirin
tunkaro rayuwarsu bayan tarkuna data tsallake masu tsananin girman hatsari?,su waye
ne wadannan mutanen?,me suke nema da rayuwarta?,me yasa basu hango kowa ba sai
ita?. Take idanunta suka sake dawo mata da fuskokinsu.

Fuskar hajja a farko,ta tabbatar a yanzu haka ita uwar wasu
ce......me yasa duniya ta cika da masu son zuciya da masu son rai?,a yadda take uwa
tayi imanin ba zata taba bari wani aibu ko abu me cutarwa ya samu yaranta ba.....
to amma me yasa su take qoqarin ingiza rayuwarsu zuwa ga wani bigire?,don ba itace
ta haifesu ba?,kenan kowa dansa ya sani?,wai shin a duniya WAYE ZAI RUNGUMI MARAYA
IRIN RUNGUMAR DA UWA KEWA DANTA NE?.

A hankali kuma sai tunaninta ya hasko mata fuskar maamah. Har yanzu bata
yarda ita din uwa bace ga yaron da take nemawa aurenta.......idan kuwa har hakan ya
kasance da gaske ita uwarsa ce?tabbas tata lalacewar ta dara ta hajja. Me yasa take
mata famfo akan danta ba zata tayata ta inganta masa rayuwa ba?,me yasa idanunta
suke rufe akan cikar qazamin burin da batasan inda zai kaita ba. Wadannan tarin
tunane tunanen su suka zaunar da ita adadin lokacin da bata sanshi ba.

******Dukkaninsu ta sanyasu cikin jikinta ta rungumesu tana sauke ajiyar zuciya a
tare da hadiyar wani abu wani yanayi yana tsargawa a dukka sassan jikinta
washegarin ranar da tayi zaune tana dakon ta inda zasu shigo. Dukkaninsu cikin
abaya masu tsananin sulbi da tsada. Nadra da haneefa sun kasa daina bata labari
tamkar wadanda sukayi balaguron alkhairi. Da alama zuciyarsu da hankulansu basu
riski wani abu mara kyau ba a zahiri da zai ankarar dasu hadari suka fada ba.

"Suna da kirki adda.....wannan kayanma su suka siya mana fa bayan kowa ya zabi irin
wanda yakeso" Nadra da kanta ke jikin Sabreen ta fada

"Munci kayan dadi sosai adda.......dakin da muka kwana me kyau sosai shima,harda Ac
da komai da komai" Haneefa ta fada cikin zumudin gaske tana riqe box na chocolate
dinta da kyau farinciki muraran cikin muryarta.

Idanunta ta mayar kan huda,ita daya ce kawai a zaune ta zubawa Sabreen
idanu,tunda kuma suka shigo itace bata ce komai ba a cikinsu. Duban tsakiyar idanun
hudan tayi ta karanci lallai nata feeling din akan mutanen yasha banban dana 'yan
uwanta,zataso taji meye a zuciyarta?,meye nata hasashen. Zataso tayi magana da huda
koda ba zata fahimceta gaba daya ba,aqalla ta rage wani nauyi daga zuciyarta dama
qirjinta.

"Ku shiga ciki ku canza wasu kayan.....kema haneefa ki ajiye wannan chocolate din"
. Tare suka miqe nadra tayi gaba haneefa tabi bayan ta suna maganganunsu.

Da hannu Sabreen ta yafito huda,sai hudan ta taso tsam ta dawo
gabanta ta zauna. Dukka hannuwan huda Sabreen ta kama ta sanya cikin nata
hannun,suka fara kallon kallo a tsakaninsu,kafin wani lokaci idanun Sabreen din
suka cika taf da qwalla. Tana jin kamar ta gaza.......tana jin kamar ta kasa basu
kariyar data dace dasu,tana jin tausayinsu matuqa da gaske,tanaso suyi amintacciyar
rayuwa yantacciya kamar kowanne yaro. Tana qyamatar dukka abinda zaya tabasu,to
amma da alama a dan tsakanin nan wata qaqqarfar guguwa ke shirin tasowa,wanda bata
sani ba zasu kubuta daga azabarta da kuma qurarta ko kuma dukkaninsu zasu fuskanci
wani sakamakon da ubangiji ne kawai yasan yanayin qarshensa.

"Inaji kamar na gaza huda.....kamar banyi aikin daya dace ba......" Tayi maganar
qwalla cike a idanunta,muryarta kuma tana rawa sosai kamar zata saki kuka.

Damqe hannunta hudan tayi tana girgiza kai

"Kinyi dukkan qoqari adda.....kin bamu kowacce irin mafaka da kariya a
rayuwarmu.....tundaga sanda suke daukemu jikina ya bani akwai matsala,duk kuwa da
bamu fuskanci komai ba sai haba haba da maraba,sun bamu kowacce irin
kulawa.....amma bamu sansu ba,bamusan su wayesu ba.....adda,abu daya suka gayan
shine,dansu sukeso ki aura......me yasa ba zaki aureshi ba adda?,kaman alkhairi
sukeson hadawa......me yasa bakison aure?". Kai Sabreen ke kadawa da sauri da
sauri.

"Ban shirya aure ba huda.....ban shirya auren kowa ba,koda zanyi aure sai na aurar
daku gaba dayanku a hannun nagartattun mazaje.....saina aurar daku a muhallin da
nasan koda mutuwa nayi bani da haufi......bani kuma da kaico....amma ba yanzu ba,ba
a irin wannan yanayin ba huda....idanma auren zanyi.....bazanyi auren cutatarwa
ba,dansu baimin komai ba,ta yaya zan aureshi kawai don na zama silar da
mallakarsa?" Maganganunta na qarshe ne hudan bata gane ba,sai ta zuba mata idanu
tana kallonta.

Duk da tarin fargaba da yake ciki yake kuma kan fuskanta akan yadda zai
tunkari Sabreen da maganar bada aurenta.....to qarshen tika tika tik inji
bahaushe.........a yau shi rufai ahmad ya karbi komai na auren Sabreen din hatta da
sadakinta bisa yanayin da bai taba zata ba.

Abinda yasha kwana yana mafarki shine......daga shi har Sabreen din sun
cinye dukiyar aurenta da hannunsu,tun daga kudin aure kayan lefe sadakinta dama
komai da komai na kudin baki. Sai gashi a yau ya wayi gari da baquncin wasu
attajiran mutane dauke dakkan wata dukiyar aure. Kama daga sadakin aure daya
tasamma naira miliyan biyar.......maqullin mota qirar Ferrari da baisan inda ma
zasu ajeta ba........da tarin goro daya

Please Login or Register in order to submit comment