You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fushi kwance a fuskarta
game da sabreen bayan a nashi tunanin zatafi kowa murna da farincikin kasancewar
hakan?. Idan bar ba mantuwa yayi ba.....duka duka ba'a yi watanni biyu ba data masa
kyakkyawan warning akan bawa yarinyar kulawa.....meye ya canza wannan?,wannan kadai
yana sake bashi signal na AKWAI WANI ABU.

Dukka juriyarta da dakiyarta ta tattara sanda suka iso parlor din,kanta
tsaye ba tare da tabi ya banbamin maamah ba ta wuce zuwa dakin anni. Ko wani bai
gaya mata ba tasan maamah din ta bita da kallo ne,kallon da ita daya tasan
ma'anarsa. Tana qasan shower tana jin yadda ruwan kebin sassan jikinta amma
mayataccen qamshin nan nasa bai matsa ko nan da can ba,duk inda ya aza hannunsa a
jikinta sai ta tuna idan takai hannunta,ta kammala wankanta tsaf ba tare da tasan
yadda suka qare a parlor ba don ba damuwarta bane. Ta jona dryer nan cikin toilet
din da busar da kanta,sai abun ya fado mata a rai.

Hala kishi maamah take da ita?,hala maamah tana tsoron kada ta karbe
mata yaro?,qila maamah tana zaton mallakarta ce ita sabreen ke niyyar qwacewa?.
Siririn tsaki ta saki a ranta tana fadin

"Inda tabi a hankali ma wannan rayuwar tasu batamin ba......dab nake da bar mata
d'anta" Tayi zancan cikin ranta saidai idanunta na kallon fuskarta ta madubin dake
gabanta. Dif sai kuma tunaninta ya tsaya cak tana sake maimaita furucinta na
qarshe.

"Idan shi zaki iya barinsa.....zaki iya barin anni da amna?" Tambayar data tsaida
duk wani tunaninta kenan,sai ta samu kanta da neman tabbacin zata iya ko ba zata
iya ba?.

"Su nadra huda haneefa sunfi muhimmanci cikin rayuwata" Ta gayawa kanta a gaggauce
tana kunna dryer din da hanzari tana son binne wannan tunanin daga ranta.

Idan banda rudin zuciya ma duka duka yaushe ta sansu?,yaushe ta fara
rayuwa dasu da har zata shiga shakkar iya barinsu?.

A nutse ya shirya cikin riga da skirt na sakakkun English wears.
Basu kamata ba amma sun mata wani irin dan banzan kyau,musamman sata daure gashinta
data gyarashi da kyau tsakiyar kanta. Wani qaramin hijabin ta samu ta sake dorawa
saman kanta,saidai wannan din da kadan ya rufe saman qirjinta.

Tana jin amna na mata tsiya

"Wannan kwalliyar adda bazan iya cankan nawa hamma zai siyeta ba......kullum sai na
dinga jin inama nice ke adda....inama nike da kyanki?" Harararta tayi

"Zageni da kyau amna.....har kina iya cewa wai na fiki kyau?".

" Da gaske nake adda....ke kam ba zaki gani ba tunda a jikinki yake"

"Bazan gani ba dai saboda kin fadi abinda bashi bane.....matsamin kada lokacin
walaha ya kubcemin" Ta fadi tana sanya dogon hijabinta,da wannan suka rabu amna ta
shiga wanka ita kuma ta tayar da sallar.

Tana shafa addu'o'inta anni ta shigo tana dubanta.

"An gama breakfast.....lokacin cin yayi....ki fara yin gaba kafin amna ta gama nata
laqai laqai din" . Kanta ta daga ta dubi anni,tanason gaya mata ba zata fita
ba..batason sake fita kwata kwata bare taga matar,maganganunta na dazun sun mata
zafi data dangantasu da kafirai,amma kome zatayi tana duba musaddiq ne. Bataso taci
gaba da kusantar inda take har hakan ya jawo musu matsala,amma sai taga kaman bai
dace ta gayawa anni ba zata fita ba.

Abun sallar ta nade,ta rage hijabin saman sannan ta sanya tattausan
bedroom slipper din tana fita a dakin.

Kowa yana saman dining din a zaune kan tashi kujerar,wanda ya rage
kawai ita anni sai amna. Cook din na tsaye tana serving kowa da kalar abincin da
yafi sha'awa. Hankalinsa yana ga farouq wanda ke gwada masa wani sabon app da suka
qirqira don manoma. Musaddiq da saddiq na nasu hiran saidai qasa qasa,sai ya zamana
maamah din ce kadai zaune tana qarewa abincin alatun kallo tare da jin bacin ran
kudin da aka narka tun daga hiring me girkin zuwa kudin kayan abincin.

Maamah dince mutum ta farko data fara ganinta,kallo daya tak da
sabreen tayi mata ta fahimci abinda ke kawo a ranta. Batason irin wannan kallon
haka......saidai ta bawa kanta tabbacin indai wannan dabi'ar na tare da matar zai
wahala su rabu lafiya. Ba komai zata iya dauka daga gareta ba,abinda ta dauka a
baya ma ya wadatar.....yanzun tana jinta 'ya me cikakken 'yanci ne da bata
qarqashin juyawar kowa.

Cikin jikinsa yaji alamun wanzuwarta a wajen,ya daga kansa a natse yana
duban sassan da take tahowa. Fuskarta tayi masa kyau kaman ba dazu ya ganta
ba,tafiyarta me cakude da nutsuwar nan tana tsananin burgeshi,tun a wani lokaci can
baya ba tare da yasan da hakan ba.

Kasa dauke idanunsa yayi daga kanta,yana fatan ta dubeshi da fararen
qwayar idanun nan nasa. Ta gefe yaji an taboshi,sarai yasan farouq ne don babu me
masa haka saishi

"Ina fata ba idanunka ne a kanta ba?" Ya soma tambayar farouq din ba tare daya
dauke idonsa a kanta ba ko g waiwayo ya dubeshi ba. Can qasan zuciyarsa dariya ta
taso masa ya danne,shi bama ta dalilin tabashin yake ba,abinda ya dameshi kawai
kada ya kalle masa mata?. Ya manta saman table din akwai mamansa?,sam kaman baisan
da wanzuwarta ba?,ita yake qoqarin ankarar dashi,don tun fitowar sabreen din maamah
din ta fahimci mayataccen kallon da fuad din yake binta dashi,abinda ya sake
tunzurata,ta dinga kokawa da zuciyarta da kuma fuskarta akan ta shanye amma ta
gagara yin hakan.

"Ni bazan kalli haram ba.....don soon halal dina na tafe......amma dai ka gyara
idanunka akwai iyaye a wajen" Shaf har kuma ga Allah ya mance da maamah din a
wajen,furucin farouq din ya ankarar dashi,sai kawai ya zare idonsa akan sabreen din
yana dojewa kallon maamah,don shine hanya daya da zai kaucewa tuhumarta ko bacin
nasa ran.

"Ta yaya zamu rayu a wajen nan?" Ya tambayi kansa da kansa yana jin idanun maamah a
kansa saidai yaqi yarda ya kalleta ko sau daya,sai ya jawo tab din gabansa yana ci
gaba da duba taswirar da suke magana akai kafin fitowarta shi da farouq.

"Matsa kusa da mijinki kiyi serving nashi". Furucin anni kenan daya sauka a
kunnensa bayan fitowarta daga daki tayi joining nasu a dining table din.

Sosai maganar ta anni tayi masa dadi,ya murmusa can qasan ransa yana
addu'ar a daren yau ta bashi matarsa. Yana jin yakai taki maqura tako ina,muddin
kuma akaci gaba da tafiya a haka baisan me zai faru ba.

Satar kallonsa tayi kaman yadda maamah ta saci nasu kallon. Har ta buda
baki zatayi magana sai wata zuciyar ta tunasar da ita,wawa shike saurin fasa abinda
ke cikinsa,sai taci gaba da juya abincin tana noticing kowa.

Ganin baiko kalli sassan da take ba bayan annin tayi magana sai ya
bata qwarin gwiwar miqewa,ta matsar da kujerar dake kusa dashi a hankali ta yiwa
kanta wajen tsaiwa.

Cikin takatsantsan take zuba masa komai,don ya tattara komai ya ajiye
ne ya zuba mata idanu yana bata order zuba kaza,rage kaza,kaza kadan zaki zuba.
Wannan yaso daburtata,don sau biyu yana kai hannu yana riqe serving spoon din da
take zuba abincin dashi da zummar kada ta zuba masa mayonnaise da man farfesun
naman kan ragon daya dan taso a sama. Ita daya sai kuma maamah suka fahimci yana
sane yake hakan,don duk riqewar sai ya hada da hannunta cikin nasa.

Da qyar ta samu ta kammala zuba masa din,sannan ta aje komai a
gabansa. Dubawa take tana neman plate din da zata zuba nata abincin,duk da tasan
zai wahala ta iya cin abin arziqi,don ya sanyata a gaba da idanunsa da suke sake
zama marasa kunya marasa jin nauyin jama'a. Tun asali ta tsani yawan kallo,to amma
shi din ta fahimci ya qware sosai wajen wannan dabi'ar,abinda yafi bata mamaki
shine......kana iya wuceshi baisan waye kai ba.....kana iya gama sabgoginka a kusa
dashi baima tantance me kakeyi ba......amma ita me yasa yake sha'awar sanya mata
idanunsa?.

"Zauna muyi squatting.......wannan abincin ina zan kaishi?" Ta tsinci muryarsa
katsam yana fadi gami da gyara mata kujerar dake kusa dashi.

Yadda wuta ta dauke mata haka wuta ta daukewa maamah,kaman kuma hadin
baki wajen duka sai ya dauki shuru,sake tura kujerar yayi kusa da ita,bata da wani
option sai janyota da tayi ta koma a sanyaye ta zauna a kai. Tayi zaton
shikenan,zai tsaya iya haka ne,a'ah......sai daya sake janyo tashi kujerar ta zama
kusa da ita sosai har gwiwoyinsu suna gogar na juna.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 95

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



*_Kina da buqatar fara kasuwanci amma baki da jari?_*

*_ko kina da jama'a amma baki da jarin fara kasuwanci?_*

*_kin cika wayarki da contact na qawaye da abokai amma bakya qaruwa dasu?_*

*_MAZA ZO KIYI JOINING HUGUMA CLOSET_*
*_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun suturu na alfarma,siyayya
cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_*

*lace*

*kowanne nau'in shaddodi*

*yadika na maza da mata*

*mayafai*

*lafaya*

*takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da qanana*

*sarqoqi da agoguna*

*under wears*

*abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza*

*_SIYAN DAYA NE NA AMFANIN GIDA KO KUMA REPOSTING ZAKI DINGA YI KINA DORA RIBARKI?
_*

*_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?_*

*Sassauqan farashi me ban mamaki*

*_Qawata adonku da samar muku da latest kaya shine muradinmu_*
_______________________________


95



Ya jima yana tsara yadda bata abinci zai zamo qarqashin kulawarsa.
Yana ankare da yadda take walagigi da cin abinci,wani abu sam da bai dameta ba,a
iya zamanta a gidansa ya lura da haka,kusan duk sati sai ya leqa store din gidan
don ya duba koda akwai wani abu daya qare ba kuma zata iya magana ba a qaro
mata,duk sanda ta shiga yana samun kitchen din danqare da kayan masarufi alamun dai
ba wani amfani akeyi dasu ba.

Tsahon wahala da rayuwar da yayi zamanin quruciya me cike da rashin
gata da wahala yasa yasan illar da yunwa ke dashi,wannan ya sanya sam baya wasa da
lamarin ciyarwa,koda kuwa ga mutanen da ba'a qarqashinsa suke ba.

Sau da dama idan ya kalleta yakan ji a ransa zatafi haka murjewa da
cika muddin ta maida kai ga abinci,bayason ta zama raguwa ko ta kasa jurewa
lalurarsa,shi yasa yake ganin shi yafi cancanta da kanshi ya tsaya a kanta ta
wannan bangaren.

A hankali taji saukar sassanyan tafin qafarsa saman qafarta. Wani
abu taji ya tsarga mata har cikin kwanyarta. Ta daga idanunta a hankali ta zubesu
cikin nasa,kusancin dake tsakaninsu yayi tsananin kusa da har ya sanya ta hangi
wani abu cikin qwayar idanunsa.
"Be serious mana....kisa hannu kici abinci ko na baki da kaina" Ya fada da sound
din da babu meji sai ita. Idanun ta kawar don ya gama kashe mata jiki,ta dubi zara
zaran yatunsa daya sanya cikin abincin masu farare qal din nails da lunula a qasan
farcen daya qarama faratansa kyau.

Batayi ko lomar farko ba amna ta fito cikin skirt itama da riga
English wears,sakakku kaman na Sabreen din,hannunta dauke da wayar sabreen da sam
ta manta ma da babinta.

"Adda.....na saka miki ita tayi full charge.....nikam ko iya yau ne a bani aronta"
Ta fada tana murmushi gami da miqa hannu ta aje mata ita saman table din a gabanta.

Bata gama aje numfashin data shaqa ba idanunta suka sauka akan wayar,

"super nova....diamond edition" Sunan wayar kai tsaye yazo kanta daga kallon farko
da tayi mata tana sake kallonta da kyau don tabbatarwa da kanta batayi dimuwa ko
kuskure ba.

"Tashin hankali......kambun bala'i" Ta samu kanta tana fadi can qasan ranta a
tsananin gigice. Wayar million sabain da kusan bakwai a hannun karuwar 'yar
barikin?,ita kuwa tana me?,yarinyar data dauko ta zame mata tsani na samun ire iren
wadannan damarmaki sai a wayi gari tana budewa kanta da kanta nata
damarmarkin?,wanne irin bacci tayi haka ita mariya?,wanne irin asararren bacci
tayi?,yarinyar da a iya duniyanci da qwarewa duka baifi ta lomaceta ba?,me yasa
take neman zame mata qadangaren bakin tulu?.

Ba zato ba tsammani naman data zuba a bakinta romonsa ya subuce mata ya
wuce mata mashaqar iska,take tari ya sarqeta me matuqar qarfi ta shiga yinsa ba
qaqqautawa.

Musaddiq da yafi kusa da ita shi ya bata ruwan data samu tasha tarin ya
lafa,sannu kawai suke mata,sai taji gaba daya iskar wajen ta mata kadan ba zata iya
zaman wajen ba,don haka tsam ta miqe tana sauka a wajen hannunta saman qirjinta
anni na mata sannu cikin kulawa.

"Ku debi abincin ku bita dashi" Anni ta fada. A gareta sai taji kaman chance anni
ta bata na matsawa daga wajen,don haka ta motsa da nufin miqewa amma ya maidata ya
zaunar da hanyar danne mata qafa. Idanunta ta daga ta kalleshi,sai ya dage mata
dukka girarsa biyun yana tsare gida.

Dole taja bakinta tayi shuru gudun tashin tashina gaban anni

"Amna diba kikai mata" Fuad din ya bawa amna umarni kai tsaye,tana kallo amna ta
shirya abincin musaddiq ya dauka mata wasu suka gangara zuwa dakin annin.

Koda ta shiga dakinma still numfashinta tana jin kaman baya isarta,sai
ta kunna a.c ta dauki remote din ac din tana qure number qarshe,kafin ta qarasa
gaban gado tana wurgi da dan kwalinta. Me yasa duk wani kafi da ta sanya aka mata
baya aiki a kanta?. Ta tambayi kanta da kanta. Duk mutumin da zata daukeshi aiki
cikin tafiyarta.....duk mutumin da zai ratso da kansa tsakiyar harqallarta sai ta
tabbatar ta mallaki bakinsa da tunaninsa.....to amma ita me yasa ta kasa samuwa
cikin tafin hannunta?.

"KINYI KUSKUREN ZABOTA......AKWAI NADAMA ME YAWA......TAURARINTA BASA TABUWA" Duka
maganganun bokan suka dawo mata kamar sannan yake furta mata su.

Juyawa tayi tana neman zama daidai nan musaddiq dake gaba ya shigo
amna na biye dashi.
"Anni ce tace a kawo miki daki,idan kin huta sai kici" Cewar musaddiq.

"Saboda ga mayunwaciya?.....shi zaki a jejinsa har sai an masa tayin
abinci?,aisaidai abinda ya farauto yaci ya bawa sauran namun daji su qarasa abinda
ya rage din" Ta fada tana makawa amna harara. Amna din bata ko daga kai ta kalleta
ba,tadai qarasa ta ajiye tray din kusa da inda musaddiq ya ajiye nasa ta juya tana
ficewa,sai shima ya soma bin bayanta ba tare da kowa yace komai ba.

"Kai musaddiqu zo nan" Ta kirashi a fusace ganin yabi sahun amna. Qofar ya saka zai
dawo ciki ta watsa masa harara

"Rufen qofata shashasha mara kishin uwarsa,kaima ka soma hawa turbar dan uwanka
ko?,an zagi uwarku shine zungui zungui zakabi bayanta?" Ta fada a matuqar hasale,a
yau tana jin shi kansa musaddiq din ya zama silar faruwar wasu abubuwan. Yau inda
ace ya bata goyon baya da nasarorin da zata samu zuwa yanzu sun haura haka.

Baice komai ba ya rufe qofar ya dawo ya zauna yana dubanta.

"Uban waye ya siyawa waccar karyar 'yan barikin waya me tsada har haka?" Ta fara
jifansa da tambayar da tafi damunta. Fuska yadan yamutsa kadan yana maimaita
sunan,hankalinsa ma gaza cafko ainihin wa take nufi.

"Kai maida hankalinka.....sabreena nake nufi" Cak tunaninsa ya dakata na wucin gadi
cike da mamaki. Dama addan take kira da wannan mummunan sunan?.

"Hamma ne....amma ai ta cancanci abinda yafi waya ma maamah,tunda ita din matarsa
ce,kuma yana da halin siya mata,uwa uba ma kuma tana da hankali da nutsuwa,ta
cancanci fin haka ma"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.....kasan me kake cewa musaddiq?" Maamah ta
fada cikin tsananin tashin hankali,idan har abinda kunnuwanta suke jiye mata lallai
shima ya shiga tarkonta......sai taji gaba daya hankalinta yana qoqarin kubce mata.
Amma da yake bariki iyawa ce,sai tayi qoqarin maida hankalinta gangar jikinta
sannan ta zauna a gefansa.

"Amma meye amfaninka a gurinsa musaddiq?,dan uwanka yana irin wannan almubazzaranci
da dukiya amma kana ganinsa?,ba zaka saitashi ba?,ba zaka hanashi ba?,ba zaka
sanarmin ba don in daidaita al'amuransa ba?,wayar million saba'in wa matarsa uwarsa
bata da ta ko million talatin?". Shuru kawai yayi maganganun maamah suna masa
banbarakwai. Kai tsaye zai iya cewa ta jahilci rayuwarsu da gasken gaske,kuma kome
zai gaya mata ba fahimtarsu zatayi ba,don haka ya zuba mata idanu kawai yana
dubanta har takai qarshen maganarta. Da kanta ta sallameshi ta koma tana zama cikin
matuqar firgici da bacin rai,zuwa yanzu tana kyautata zaton BOKAnta tabbas ya
gaza.....yaqin nan da bakinta zata yishi,da dukka wata power irin ta uwa da Allah
ya bata.

Wuni guda gaba daya bata bawa kwanyarta wani sukuni ba ko kadan,gaba
daya tunaninta ta tattarashi akan yadda zata yanke wanzuwar sabreen cikin rayuwar
d'anta. Zuwa sannan jikinta yana bata ci gaba da wanzuwar sabreen din bazai haifar
mata da d'a me ido ba. A dukka shawarwarinta zuciyarta tafi rinjayarta ta bangare
guda......ta raba auren ko da tsiya koda tsiya tsiya......da qarfi da yaji koda
kowa hakan bai masa ba.....zata gwada qarfin qwanjinta da kuma adadin girma izza da
nata ikon na uwa.

Wannan saqar data gama yi ita ta sanya ta fita cin abincin daren ranar
da wani irin izza da cikakkiyar qwarin gwiwar samun mafita.

Ta samesu duka saman dining din,ta bisu da kallo daya bayan daya
tana jin ciwon yadda annin ta samu daman hade kansu duka,yaran da suke nata da
wadanda suke ba nata ba. Ta saki qaramin shu'umin murmushi qasan ranta tana bawa
kanta tabbacin komai dab yake da qarewa.....muddin ta samu nasarar yage KASKA wato
sabreen daga jikinta,sauran zata qarasashi ne da dukka qarfinta.

Kujera taja ta zauna tana shaqar iska d'ai d'ai,ta sake ware idanunta
tana nan sashen da fu'ad yake saidai bata ganshi ba,ta buda baki zatayi tambaya ya
shigo parlor din da nutsatsen takunsa.

Sanye yake da suspender da Fedora hat datayi matuqar masa kyau,tamkar
wani baturen England,kunnensa maqale da earpiece amma dukka hankalinsa yana kan
sabreen dake zaune gefe idanunta akan amna da wunin yau duka take more wayar
sabreen din. Wani abu ya sosa masa zuciya,baisan wanne irin taurin kai gareta
ba......koda wasa bai taba tunanin zata sanya qafa ta shure maganarsa ba,saidai nan
kusa yayi imanin zai ladabatar da ita don duka cikin halinta shine hali guda daya
da bazai iya jurarsa ba.

Kaman dai dazun anni ta sanyata tayi serving nashi,ta miqe a hankali
daga gefansa tana qoqarin zuba mishi soyayyar shinkafar. Hannu ya sanya ya jawo
cucumber a gefansa ya tura gabanta yana fadin

"Slice it" Ya fada da wani irin shanqamshi daya dan bata mamaki. Hannu ta saka ta
jawota,ta dora saman plate ta soma yankawa. Sosai zuciyarta tayi zurfi a
tunani,abinda ya janye hankalinta kenan har wuqar da take yanka cocumber din ta
taba hannunta.

"Wayyo Allah na" Ta fada tana yarfar da hannu tana jin zafi da radadin wuqar yana
shigarta.

"Yankewa kikayi adda?" Amna ta fada da sauri tana matsowa,abinda yaja hankalinsa
kenan zuwa gareta daga kan wayar da yake latsawa.

"Ya salam" Ya fadi yana jin tsigar jikinsa na tashi da jinin dake biyo hannunta,har
baisan sanda wayar hannunsa ta sulale ba maamah tabi wayar da kallo.

Tuni ya miqe ya kama yatsan da jinin ke fita yana kallo,har cikin
jikinsa yakejin kamar shi ya yanke din.

"Me yasa bakiyi a hankali ba?" Ya fada yana zube mata fararen idanunsa. Kanta ta
kawar gefe tana jin kallon nasa ya aza mata nauyi da yawa,uwa uba ga maamah a wajen
da batason komai ya sake hadasu.

"Musaddiq......duba dakin anni ka samo mana abun wanke ciwo" Ya fadi yana janyeta
daga tsakanin dining din zuwa kujerun falon ya samu waje ya zaunar da ita yanayin
tsaye a kanta.

Da qyar maamah ta iya lalubar numfashinta,ya zama dole a yau ta datse
wannan igiyar......ya zama dole ta bata ta kuma tarwatsa koma meye yarinyar ta
qulla.....kowanne irin shu'umin malami ta samu ita mariya saita nuna musu qarya
suke duka ita dashi din.

"Idan ya gama qaramar haukar......ka gaya masa ni uwarsa mariya ina kiransa zuwa
dakina" Ta bawa musaddiq saqon don tana jin kota gefansu ba zata iya rabawa ba bare
ta tsaya tayi magana da dayansu shi ko sabreen din. Kai tsaye hanyar dakinta ta
nufa tana harhada hanya.....a yau koda sakin sabreen shine abu na qarshe da zata
aiwatar a rayuwarta saita tabbatar ya afku kafin ranta ya fice daga gangar jikinta.


*_dan dan dan dan dan dan.........masu karatu.....uhmmmmm......bakina da
goro.....zamu gani kuma......shin xai tabbata ko kuwa?,sai nace ku tara dani ranar
litinin in sha Allah,na gode_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 96


https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



*_Kina da buqatar fara kasuwanci amma baki da jari?_*

*_ko kina da jama'a amma baki da jarin fara kasuwanci?_*

*_kin cika wayarki da contact na qawaye da abokai amma bakya qaruwa dasu?_*

*_MAZA ZO KIYI JOINING HUGUMA CLOSET_*



*_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun suturu na alfarma,siyayya
cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_*

*lace*

*kowanne nau'in shaddodi*

*yadika na maza da mata*

*mayafai*

*lafaya*

*takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da qanana*

*sarqoqi da agoguna*

*under wears*

*abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza*

*_SIYAN DAYA NE NA AMFANIN GIDA KO KUMA REPOSTING ZAKI DINGA YI KINA DORA RIBARKI?
_*

*_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?_*
*Sassauqan farashi me ban mamaki*

*_Qawata adonku da samar muku da latest kaya shine muradinmu_*

____________________________



96


_An tambayi nana Aisha R.A,menene dabi'un manzan Allah S A W,sai tace: dabi'unsa
alqur'ani ne(ma'ana yadda qur'ani ke koyarwa da fadin kalolin kyawawan dabi'u dukka
haka halayen fiyayyen halitta S A W yake)_




A nutse ya zaunar da ita saman kujerun yana riqe da yatsar tata tamkar wadda taji
wani gagarumin ciwo. Sosai idanusa suka bayyana tsananin damuwa,ya tsugunna a
gabanta a hankali idanunsa na saman fuskarta. Bata yarda ta kalleshi ba,tana ji
kusancin dake tsakaninsu kaman yana sake yin yawa,tana ankare da yadda maamah tabar
wajen cikin wani irin yanayi da yafi kama da zallar fushi da kuma fusata,a haka
musaddiq din ya dawo ya aje masa qaramin akwatin yana komawa da baya don barin
wajen kaman yadda sauran suka bari da d'aya da d'aya. Dukkaninsu wata kalar soyayya
suke gani a shimfide saman fuskarsa,kaman yadda idanunsa basu boye komai ba.

Murmushi ya subucewa farouq din yana jin fu'ad yana sake tafiya
dashi,duk da komai yasan yana yinsa ne ba cikin hayyacinsa ba saboda bugar dashi da
giyar soyayya tayi.......ya sanya P_cap dinsa yana daukar key din motarsu ya saka a
aljihunsa don fita dama ke garesu da daren ya soma sauka ta bayan kujerun yana
barin parlor din,don shi kansa bazai iya zama yaga ya wannan love game din zai
wakana ba. Wani sashe na zuciyarsa kuma cike taf da mamakin mode din
maamah......fushin dake tattare da ita da saqon data barwa musaddiq. Ya jima yana
wani tunani akan matar......ya dade yana wani hasashe a kanta,saidai a sanin da ya
yiwa fu'ad ba zasu kasa hasaso abu guda ba.

Zama yayi sosai gaban nata yana fida spirit ya tsiyaya cikin wani dan
abu na silver,ya tsoma a auduga sannan ya dago yana kallonta. Still taqi bashi
daman kallonta. Wani irin yanayi takeji yana bibiyar zuciyarta kaman zai narkar da
ita. Yau ita sabreen yankewarta a hannu ya zama damuwar wani?,wani baqon lamari ne
a wajenta da batasan ya zata fassarashi

Please Login or Register in order to submit comment