You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bai sake bi takan farouq ba don yasan fushinsu da juna ba wani abu
bane me dorewa ba. Saidai yadda farouq din yace idan bai dawo ba washegari baisan
me zaya faru ba,yana tsaka da ayyukansa da yake sanya ran sune na qarshe kiran anni
ya sameshi.

Abdul_haleem daya daya cikin guard dinsa ya miqawa folder din
hannunsa,ya koma gefan table din da yake ajiyar takardun ya zauna yana daga wayar.

Cikin nutsuwar nan tata da ko yaushe take qara mata kima da kwarjini tayi
masa sallama cikin tsantsar kulawa da qauna irin ta uwa da d'a. Kaman ko yaushe
shima,cikin tausasawa da matuqar bada kima ya amsa mata sallamar.

"Barka da warhaka anni......anni ayyuka sun sani gaba,ayimin afuwa" Yayi riga malam
masallaci wajen fada. Murmushi ta saki cikin nutsuwa tace

"Anyi maka Muhammadu........ya aikin?,fatan komai yana tafiya daidai?"

"Alhamdulillah anni.....komai alhamdulillah,saidai muna buqatar qarin addu'a" Ya
furta maganar jerin saqonnin daya gani shekaran jiya suna fado masa. Ba'a raina
kaidin maqiyi,kuma abokin adawa ko wanda bai sonka ba'a rainashi komai qanqantarsa.

"Kullum a cikinta muke,ba abinda zai faru in sha Allah sai alkhairi......amma nayi
zaton samun baquncinka a yau......tuntuni mun sauka a sabon gida.....duka duka jibi
ne daurin auren nan......ga baqi a gidan kowa kai yake tambaya". Hannu ya sanya ya
shafi sumarsa,har yanzu ya gaza gano abinda yasa suka daukaki sabgar nan
haka.....har wani taron gayyar jama'a anni itama tayi kenan bayan ta maamah?.

"Jibi din zan shigo in sha Allah anni"

"Anni jibi yayi kusa.....gobe ko yau ya kamata....private jet ne,baida buqatar
samun wani issue ko ya kawo excuse" Ya jiyo muryar farouq daga gefe tana shigo
masa.

Murmushi ya saki da sautinsa ya gaza boyuwa,wato zuwa yayi ya hadashi da
anni kenan?.

"Bani shi anni please" Ya fada da sauri,bata ce komai ba ta miqawa farouq wayar
tana murmushi. Drama din fu'ad da farouq babu me shiga,idanma kace zaka shiga din
kunya zakaji.

"Definitely idan ka samu dama saika shiga tsakanina da anni......ka canza hali
wallahi" Ya fada yana dan daure murya.

"Kome zaka fada ka fada.....ina nan ina jiranka"

"Kaci gaba da jira.....at last idan bakayi wasa ba kai zan daurawa auren nan da
yarinyar......tunda naga ka damu da lamarin ta da yawa" Daga haka ya katse kiran
yana dariya ciki ciki. Yasan ya kunno farouq din,don ba wanda zai rabashi da fannah
dinsa sai Allah.

Haka kawai ya samu kansa dason cika alqawarin daya yiwa anni,ya maida
hankalinsa qwarai kan qoqarin kammala abubuwan da suke gabansa don ya samu isa
nigeria kaman yadda ya alqawarta.

Hannu anni ta miqa tana karbar wayarta daga wajen farouq dake mita.
Duk da mitar da yakeyi din saidai ya kiyaye dukkan wani abu da zai saka anni ta
fahimci akwai lauje cikin nadi.....boyayyen manufa da qudurin data hana fu'ad
damuwa da dukkan wani lamari daya shafi auren.

"Anni kina sauqaqa masa da yawa........hatta da friends dinmu gobe zasu
iso.....amma ace shi yana can neman kudi?.....har yau ya kasa sanin kalmar hutu a
rayuwarsa?.....ta yaya zai kula da diyar mutane?" Murmushi anni ta sake,yadda
farouq din keta mita ke bata dariya

"Banda abinka farouq.....na tabbatar ya fika damuwan ya iso fa.....sannan tunda
kaga haka din ba yadda zai taho dinne,da yau gobe da jibin dukka na Allah ne,kuma
kaman yau ne.......ina da saqo ma da nakeson ka miqawa d'iyata...." Anni ta fada
tana yunqurawa ta miqe.

"Ina amna ta shiga ne?" Farouq ya tambayi anni dake qoqarin bude wani side na wata
qawatacciyar cupboard ta daban dake cikin aljannar duniyar bedroom din nata.

"Tana bangaren beauty spa"


ð˜ŋ𝙊ð™Ģ𝙞ð™Ū𝙖 ð™Đ𝙖 ð™Ģ𝙖 𝙠𝙊𝙙𝙞 ð™Ģ𝙚.
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
ð˜Ąð˜Ē𝘧ð˜Ē𝘧ð˜Ēð˜Ģ𝘊𝘚ð˜Ēð˜ģ
ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2
ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ

𝙋𝘞𝙂𝙀 5


"Okay" Ya fadi kawai a taqaice,don ita kanta yadda yaga alamun ta dauki bikin kamar
yafi yadda kowa a gidan ya dauka.

******A duk bugawar daqiqa,wucewar kowacce saa da kuma bugawar agogo sake kusantar
da ita kawai yakeyi zuwa ga duniyar mamakin abinda ke shirin faruwa da ita. Sannu
sannu taga gidan ya fara cika da baqin fuskokin da da yawansu ta manta da
kasancewarsu ahalinta. Wasunsu tun ana taron alhinin rasa mahaifinsu mamallakin
gidan gaba daya,yau sai gasu da daya da daya suna bullowa da sunan halarta taron
bikin da tayi imanin ba wani bane ya gayyacesu.

Dondai mamma bahijja ba wata mu'amala ke tsakaninsu ba,hasalima ba
sanin kaso casa'in da tara a cikinsu tayi ba. Ba sanin jiya ko yau ta yiwa duniya
ba,ta sani....kusan mafi rinjaye a cikinsu sanin waye yake shirin aurenta shi ya
kawosu bikin,bikin da babu wani abu guda daya da take da masaniyar ita ko mamma
bahijja ta tsarayi,koda an tsara din ta tabbatar aikin kawu rufa'i ne,wanda ya kasa
zaune ya kasa tsaye,komai yana gaba gaba a kai,hakanan ya saki kudi anata hidima
cikin gidan.

Yanayin yadda ya saki bakin aljihunsa ya dasawa sabreen qaqqarfan
yaqinin kudade ya samu ko ya karba daga wajen mutanen daya sadaukarwa da ita. Bata
cewa da kowa komai ba,amma tana karance da kowanne motsi na cikin gidan. Yadda bibo
tayi uwa tayi makarbiya,a rana takan hauro saman da zummar dubasu har babu
adadi,saman da a baya sai da akasha dambarwa da ita kafin ta daga qafan
kasancewarta a can,sai da sukayi baram baram da kawun,ya wanke mata zanin
mutuncinta tas tare da buga mata gori nau'i daban daban,yau din sai gata tana zarya
tsakanin hidimar da ba tata ba bata kuma shafeta ba.

Sanye take da wata simple dubai gown me rangeamen nauyi da sassauqan ado
me daukan hankali,cotton ce me yankakken hannu da ya tsaya iya damtsenta,sai
siririn mayafinta data maidashi tamkar dankwali ta yane sassalkan gashinta dake
zube gadon bayanta ba tare data daureshi da komai ba. Cikin jikinta sam babu
qwari,tana jin kamar iska zata iya dibanta ta kayas da ita,hakan kuwa ta sani baya
rasa nasaba da qauracewa abinci da tayi akan yadda ta saba cin abinci,duk da dama
can ita din ba ma'abociyar cin abincin bace.

Ta samu huda ta dafa shinkafa da wake,sai miya da soyayyen kifi daban.
Goshinta ta dafe tana zama,kanta tun jiya yake sara mata bayan data jiyo mamma
bahijja na magana da qannen mahaifiyarta da kuma kawu Abdul Hakeem,tana shaida masa
jibi gobe kenan shine ranar daurin aurenta bayan sallar juma'a.

"A zuba miki adda?" Huda ta tambayeta cike da fatan ta amsa cewa zataci din.
Hannuwan huda da sukasha lalle tabi da kallo. Ko nata hannuwan farare suke sidik da
zara zaran yatsunta dake dauke da dan baqin lalle dan kadan saman farcenta,ragowar
lallen data yiwa adon yatsunta wata biyu baya da suka shude.

"Zuba......amma kada kisa miya.....mai zaki saka da dan maggi kadan" Ta yiwa huda
bayani a taqaice tana zare idanunta daga sashen da suke. Sauka idonta yayi kan
wayarta dake ajiye wadda a qalla ta kusa kwana biyu a wajen. Sam bata da sha'awarta
ma don batajin zuwa yanzu tana da wani uzuri da ita. Jib,ayshatu,qannenta da sauran
mutanen da takejin sun Ta'allaqa a wuyanta kadai zuciyarta ke mata amsa kuwwar ta
nemesu.......tayi sallama da kowannensu.....saidai kuma wani sashen daban yana bata
qwarin gwiwar bata da buqatar hakan!. Tana ji a rai zuciya dama jikinta tamkar wani
gajeran balaguro ne kawai zatayi daga tata duniyar zuwa wata duniyar,balaguron da
bai wuce misalin qifatawar idanu daga rufewar zuwa budewar ba. Bataji kwata kwata
cewa wai auren zai zama wani dogon aiki da zata kasa yakiceshi cikin qanqanin
lokaci. A yanzun zata zubawa komai da kowa idanu.....kwadin me kwadayi......burin
me buri......da tsarin me tsari a kanta ya kwanta.....sannan ne ita kuma zata
aiwatar da nata shirin hankali kwance( nikam nace uhmmm....qaddara dai ta rigayi
😊
fata).

Da plate huda ta dawo,wanda tsara zuba abincin gwanin sha'awa. Sabreen
tasan duka tayi ne don taci,ta jera soyayyen kifin saman shinkafa da waken,sannan
ta mata roban yaji da magi daban. Da kallo kawai tabi plate din,don tasan yafi
qarfinta koda duniya ma tana kwance bare yanzu da wani abu waishi abinci baya
burgeta.

Sallamar kawu rufa'i da sautin muryarsa kadai ya sanya abincin data sanya
a bakinta ya tsaya mata cak a maqogaronta,sauran na bakinta kuma taste dinsa ya
canza mata,har tana jin ba zata iya taunawashi ba,har sai data tattara dukkan
juriyarta sannan ta tauna ta turashi zuwa maqogaronta wanda ta samu ya wuce da
qyar,sai kawai ta yanke hukuncin ajiye abincin. Idanunta ya sauka kan kawun sanda
take ajiye plate din a qasa,wanda yake jaye da wata mini luxury luggage me azabar
kyau da kuma daukan idanu. Koda bakasan me duniya ke ciki ba,koda bakasan darajar
abinda yake janye dashi ba tabbas zata fahimci luggage ne me tsada da madaukakiyar
daraja.

Wajen zama mamma bahijja tayi masa tana sanya nadra ta ajiye masa drink
da ruwa.

"Ya hidima ya kuma shirye shirye?" Kawun ya furta da muryar dake nuni da zallar
farincikin da yake ciki

"Alhamdulillah.......ai kune da hidima,tunda mu nan ba abinda zamuyi" Kai kawu
rufa'i ya girgiza yana satar kallon sabreen da tunda ta gaidashi bata sake koda
kallon sashen da yake ba.

"Allah ya yiwa yarinyar nan taurin kai bahijja......idan kinga abubuwan da sukaso
gabatarwa zakisha mamaki......har yanzu quruciya ke dawainiya da ita,inda tasan
girman matsayi da darajar mutumin da zata aura,na rantse miki saita qare rayuwarta
tana godemin.....attajirin matashin da babu irinsa a wannan qarnin da muke ciki?"
Dan murmushi kasan momma bahijja tayi,adan zamanta ta fahimci kawun yana sa son
abun duniya

"Duk bama wannan ba rufa'i,indai har bincikenku ya tabbatar da nagartarsa ai magana
ta qare.....dukiya wannan wani abune na daban ai"

"Habawa.....idan ana batun nagarta ma da dattako har ayi magana wadannan dattijan?"

"To alhamdulillah.....haka akeson ji...."

"Yanzu haka ma aike ne......saqo ne na musamman daga surukarta......kaya ne tace a
kawo mata da zata sanya a gobe kenan"

"Tofa.....ikon Allah,kuma dai?,basa gajiya?"Momma bahijja ta fada duba da irin
kudaden da aka narkar,tun daga dukiyar aure har izuwa batun lefen dasu kansu har
yanzu basu gama sanin komai da komai dake cikin akwatunan ba. Tana qara ganin
girman qaunar da suke gwadawa sabreen din,a gefe guda har ranta tana jin tamkar
sabreen din tayi sa'ar inda zata rayu cikin qauna da kulawa.

"Wai wai.....ma sha Allah" Momma bahijja ta furta tana daga lafiyayyen applique
lace da kudi suka koka qwarai wajen siyensa. Daga qasanshi kuma wata bazin ce data
amsa sunanta sai super Sheraton da iya ado da gayu da kashema kai kudi irin na
momma bahijja bata taba katarin ganin irinta ba. Daga qarshe set ne na banguls
earrings da sarqa da zobensu duka na danyen gold me matuqar daraja(nikam nace masu
abu da abinsu).

Ko qwaqwqqwaran motsi sabreen batayi ba ballanta ta daga kanta ko zata
nuna alamun tasan bidirin da akeyi,har sanda hadiyya tayi sallama tana shigowa
falon da guntuwar fara'arta.

Sunan kayan kawai ya gaya mata darajar abinda aka sako a ciki saidai
hakan bai dadata da qasa harta daga kai ta basu darajar kallo ba,don batajin zata
iya rabasu a jikinta. Komai daya fito daga hannunsu duhu yake mata,baya mata haske
ko kadan.....musamman da take kyautata zaton kayan sun fito ne daga hannun waccar
matar maras daraja. Still shigowar hadiyya bata sakata daga kai ta dubeta. Can
qarshen zuciyarta danqare da mamaki,yadda kudi ke iya sauya dabi'un mutanen duniya
cikin qanqanin lokaci,duk da wannan karatun ta jima da haddaceshi......kusan shi ya
zama sila na sauyawar DUNIYARTA.

Hadiyyan ta sauya kamar ba ita ba,abinda bata taba tsammanin zaya faru nan
kusa ba. Bata zaqe da yawa ba wanda tasa tasirin karatu ne wala'alla da salon
gogewa......hakanan kowanne taku kadan tana yunqurin kutsa kai jikinsu ne.

Hadiyya ita ta qarasa daga kayan matsanancin mamaki yana sake kasheta.
Hidima sosai suke gwadawa sabreen din kaman rijiyar kudi garesu. Ba wanda yakai me
kudi sanin darajar kudi,saidai ga wadannan bataga alamun hakan sam daga garesu ba.

"Gashi zakiyi magana da surukarki" Momma bahijja ta fada tana sauke wayarta daga
kunne gami da miqawa sabreen. Dan turus tayi tana sauke fararen idanunta akan
fuskar momma bahijja din. Muddin wannan matar ce sam bata da sha'awar wata magana
da ita. Komai nata bisa gadara ne iko izza da kuma nuna qarfin dukiya,don me zata
zauna tana gwada mata tata izzar bayan ba ita ta gayyaceta cikin rayuwarta ba.

Idanu sunyi yawa a kanta,don haka ta sanya hannu ta karba tana kauda
fuskarta daga kallon idanuwan.

Sallamarta kadai ya gaya mata ba wadda take zato bace,cikakkiyar
sallamar data saukar da duk wani zafi da zuciya da kuma halshenta suka dauka,saita
amsa mata a nutse matuqa

"Kina yini lafiya diyata?" Anni ta fada daga nata bangaren jin sabreen din tayi
shuru. Karon farko sai taji nauyin matar ya saukar mata,batasan me yasa a iya waya
kawai takejin girma da kwarjininta ba......shin itace asalin mahaifiyarsa ko
yaya?.....itadin wacece a wajensa?,waccan ma wacece a wajensa?. Iya wannan
tambayoyin da bata da amsa kadai suna sakata a jikinta tana jin tabbas akwai wani
gagarumin abu birne a qasa.....duk da zuciyarta tana gaya mata ba wani babban abu
bane da zai gagari sarrafawarta ba.

"Barka da yamma.....lafiya alhamdulillah" Ta hade gaisuwar da amsar tambayarta.

"Ma sha Allah"

"Naga saqo,na gode" Tayi hanzarin fada,don a cikin ranta takejin bai kyautu ba har
sai ta magantu.

"Ba komai......inaso ne kawai kiyimin alfarmar sanyasu a duk sanda zaki shigo
ahalinmu" Tayi maganar a tausashe cikin kuma nuna kulawa,kulawar data bayyana kanta
sosai cikin sautin muryarta

"In sha Allah" Ta sake amsa mata
"Ina fatan hakan ba takura?"

"Ba komai....in sha Allah"

"To alhamdulillah......ina roqon ubangiji ya tattara dukkan alkhairanku ga
junanku......ya kauda kowacce irin fitina da abunqi a tsakaninku". Batasan me yasa
ma......amma har tsakiyar qirjinta taji saukar addu'ar......batayi kuskure ba idan
tace kunnuwanta itace mutum ta farko data fara jin addu'ar daga bakinta,sai taji
labbanta sunyi nauyi bare su tallafeta ta amsa.....yayin da anni tayi zaton kunya
da kawaici suka hanata amsawar......a haka tace ya baiwa momma din wayar.

Zuciyarta tayi nisa qwarai da zurfi wajen tunani,har batajin ma meke
wakana cikin falon,sai kawai ta yanke nesanta kanta dasu ta hanyar komawa daki
kaman yadda ta maida hakan dabi'arta.

Bata jima cikin duniyar dakin data maida mazauninta ha nadra ta shigo
dauke da wayarta a hannu.

"Ana kiranki" Ta fada tana miqa mata wayar. Kamar tace mata ta koma da ita sai ta
fasa,ta saka hannu ta karba tana daga kwancen tana duba me kiran.

Sunan data gani ya sanyata miqewa ta zauna sosai babu shiri,hannunta na
gaggawa wajen amsa kiran ta sakashi a kunnenta

"Kicemin kun dawo titi don Allah,kicemin ayshatu ta warke"

"Na warke adda......na samu sauqi" Muryar yarinyar ya saukar mata a kunne. Wani
hawaye me sanyi ne ya kubce mata,kullum da lamarin yarinyar take kwana take kuma
tashi,daga yadda taji muryarta tasan cewa tabbas lafiya cikakkiya ta samu a gareta

"Muna cikin sabon gidanmu yanzu aunty.....na gayawa titi bazan yarda na fara ganin
kowa ba sai ke".

"Yanzu kuwa zaki ganni ayshatu" Ta bata amsa kai tsaye kaman ta manta a wanne
yanayi ita din take.....kaman ta manta rabonta da taka qasar waje wasu kwanaki ne
masu yawa.

Da wani irin excitement ta ajiye wayar,ta zura qafafunta qasan gadon da
hanzari zara miqe da nufin shiryawa,sai kuma ta dakata cak saboda dawowa hayyacinta
da tayi.

Tayi imanin wadannan mutum mutumin har yanzu suna tsaye a qofar gidansu
suna gadinta,yawan mutanen dake kai kawo a gidan bai sanyasu sun tafi ba......don
ko dazu ita iya jiyo baqin tsagin abbansu suna tambaya a kansu.

"Saina fita kota halin qaqa wannan karon......ko meye zai faru saidai ya faru" Ta
fadi tana qarasa saukowa,ta kuma fito kai tsaye zuwa ga falon tana nufar doguwar
veranda din dake saman wanda tacan zata samu hanyar gangarawa qasa ta koma ainihin
dakinsu.


_DUNIYA TA na kudi ne_

08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
ð˜Ąð˜Ē𝘧ð˜Ē𝘧ð˜Ēð˜Ģ𝘊𝘚ð˜Ēð˜ģ

ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2
ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ

𝙋𝘞𝙂𝙀 6


Page 06


Batasan gidan ya fara daukan mutane ba sam sai data sauko din. Gomayyar idanuwa
sukayi kanta caaa ana qare mata kallo. Kowa da nashi tunanin cikin ranshi,wasu na
kallon tsantsra kyan data qara saboda gyaran jiki na musamman data samu tsahon
kwanaki daga wajen qaararriyar me gyaran jiki......wasu kuma na mata kallon sha'awa
suna fadin inama su ko 'ya'yansu keda wannan sa'ar ta auren irin mijinta?,yayin da
wasu nasu kallon na bin qwaqwafi ne hassada da tarin tambayoyin ta yaya KARUWAR
GIDA.....WADDA TA GAMA RABA MUTUNCINTA WA MAZAN TITI TA SAMU BABBAN MUTUM.IRIN
MUHAMMAD JADDA DIN?.

Miskilanci da shariya kusan cikin jininta suke,don haka tayi kaman bata
gansu ba ta wuce dakinsu kai tsaye.....ballantana kusan dukansu tana cike dasu. Ba
wanda yabi takan rayuwarsu.....qaqa suka kwanta qaqa zasu tashi?,amma sai gasu
yanzu zube da sunan sunzo auren yarinyar da basusan yaya ta girma ba?,me taci har
takai wadannan shekarun?.

A gaggauce ta shirya cikin wata luxury Egyptian abaya datayi masifar
karbarta,wadda inda cikin nutsuwarta da hayyacinta take itama ya kamata ace taga
yadda rigar ta karbeta.

Tun daga nesa kana iya ganin mugun kyan da fatarta tayi,wani irin haske
da glowing kawai takeyi,saika rantse da Allah diyar wani hamshaqin ce. Qaramar
handbag kawai ta dauka ta jefa wayarta a ciki da dan canjin da zata riqa saboda
mota,ta fito daga dakin a nutse tana isowa falon,daidai sannan momma bahijja ta
shigo rungume da dinkakkun atamfofin da tasa aka dinkawa su haneefa duk da tarin
suturunsu.

"Ina zuwa kuma?" Momma din ta jefa mata tambayar tana kallon yadda take komai a
gaggauce. Batasan da wanne harshe zata yiwa momma bayanin aysha da muhimmancinta a
wajen ta,don haka a taqaice tace

"Dubiya zani momma...."

"Zuwa ina?.....kuma dubiya a irin wannan lokacin?" Kai ta langabe kadan tana
fargabar kada momma din ta hanata fita,don a irin wannan lokacin ita kadai takejin
zata hanata fitar ta hanu

"Ba niss momma.....ba jimawa zanyi ba".

"Nadra ta rakaki,kuma kada ki wuce awa daya" Ta fada tana qarasawa tana zube
dinkunan hannun nata saman kujera.

Mayafi kawai ta figowa nadra,ta sanya wasu plate shoe nata sannan suka
fito. Sam bata damu da yadda idanuwa keci gaba da binta da kallo ba,har wasu na
qoqarin gaisawa da ita,a haka ta doshi qofar gidan nasu tana tsara yadda zata kaya
tsakaninta da qedarun da aka tsaida a qofar gidan.

Tana takawa zuwa qofan tana jin fargabar yau dame zasu zo mata?,don dai
yadda takeji a ranta yau koda sama da qasa zasu hade sai ta fita.......don ba wani
mahaluqi daya taba saka mata dokar zama cikin gida har haka tsahon
rayuwarta......sai yau gashi sama ta ka wani mutum can da baisan ciwonta ko
darajarta ba......yanason yayi amfani da giyar kudi ya yiwa rayuwar karan tsaye.

Tana tura qofar yana riqeta kana aka qarasa budeta. Fuskar kakkauran
mutumin ta bayyana har abun yana bawa sabreen mamaki. Bata taba kawowa a lokacin
irin wannan zata sameshi tsaye bakin qofar ba kamar wanda aka tsaiguntawa zata
fita......waisu basa zama?,ko basa hutawa da jiddin suna tsaye suna gadin duk wani
motsinta.

"Good evening madam" Abdulgaffar ya furta cikin matuqar girmamawar nan da suka saba
mata magana da ita saidai kuma a dabarance yana matse kowacce hanya da zata iya
rabawa ta fice daga gidan.

Ta gama karantar motsinsa kaf.......bata wani damu da gaisuwarsa ba ta
azawa fuskarta wani irin halakakken bacin rai da kuma d'aurewa

"Kiramin boss dinku" Ta bashi umarni nakai tsaye da wani irin sauti da babu wasa ko
kadan a ciki. Tanaso ta gwada musu girman abinda zata iya aikatawa.......tanaso ta
gwada musu basu ba......koda boss dinsu ma bata daukeshi da wani tarin muhimmanci
ba.

"Bani da connection dashi......idan zan kirashi saina jira anyimin iso kafin na
samu magana dashi......amma ga jordan zai kira miki shi" Abdulgaffar yayi mata
bayanin cikin girmamawa yana matsawa da baya.

Can qasan ranta mamaki yake kamata,wanne irin girman mulki da izzar
kudi gareshi da har yaransa ma ba kowa da kowa keda daman magana kai tsaye dashi ba

"Good evening madam.......kiyi haquri ki jira kadan,yanzu in sha Allah zai amsa"
Jordan ya fada yana rusuna mata. A ranta tanaso ta gaya musu ne a fili

"Qattin banza.....kun zauna kuna yiwa mutum qwaya daya bauta saboda yana da dukiya"
Abinda zataso gaya musu kenan ganin yadda jordan ke lalubar muhammad fuad jadda
cikin girmamawa.

A lokacin yana tsaka da hada duk wasu muhimman abubuwa nashi da
kanshi,ba tare da ya bari hidiminsa ya masa ba wato me sunan malam. Akwai wasu
abubuwan da da kanshi yake yinsu,duk da tarin hadiman dake gareshi. Yana sanye da
fara qal din t.shirt me laushi Vshape neck,hannunta iya dantsensa wanda hakan ya
sanya murdaddun damtsensa dake nuna girman daga qarfe da yakeyi suka bayyana,wandon
jikinsa ma farinne duka duka tsahonsa iya qaurinsa,sai lausasan fararen flip-flops
masu tsananin haske da taushi.

Cikin kowanne irin yanayi tsarinsa na dabanne,kai tsaye zaka iya cewa
gayu ya ratsa jikinsa da gasken gaske.....koda kuwa bacci zai shiga zaka sameshi
neat....komai nashi kuma completed kai kace ba bacci zai kwanta ba. Yadda yake a
nutse cikin wani irin tsari haka komai nashi yake kasancewa,waya.yake amsawa wadda
ya sakata a hands free ya ajiye saman wani zagayayyen kujera me siffar qwallo dake
a gefe. Kadan ya kalli wayar,sai ya fahimci kiran jordan keson shigowa amma yana
buqatar izinin haka,don haka ya katse wancan kiran ya bawa kira jordan din dama

"Barka da wannan lokaci sir" Jordan yayi maganar cikin girmamawan data bata ran
sabreen,ta cika fal da mamakin wanne irin ban girma ne haka kaman yana a
gabansa?,ya kasa miqewa da dukka tsahonsa ya amsa wayar.

"Yauwa Jordan......ya akayi?" Ya tambayeshi kai tsaye. Sai daya dan daga idanu ya
kalli sabreen din da idanunta ke cike tab da fushi,sannan qasa qasa yace

"Madam daka tura a yiwa aiki ce keson magana dakai sir"
"Madam?" Ya tambaya yanason tuna abun don ba komai yake baiwa muhimmanci ba

"Eh sir....."

"Bata wayar" Ya umarceshi kai tsaye don ya tuna inda zancan ya dosa.

"Ka matsa a wajen idan ka bata" Ya sake fadiwa jordan don bayason yayi involving
yaransa cikin abinda bai shafesu ba.....hakanan yana ganin ba girmansa bane su
fahimci komai ba.

Kaman ba zata karba wayar ba don tana jin kamar ta zuba a qasa data nema
magana dashi......saidai kuma girma da martabar inda zataje din ya shafe komai a
idanunta,don haka ta sanya nadra ta karbo wayar daga hannunsa sannan ta karba a
hannun nadra din,ta taka a nutse tana dan komawa ciki duk da jordan ya matsa daga
inda zai iya jinta.

A kunnenta ta kara wayar,saidai har kusan shudewar mintuna guda tim ba
wanda ya cewa da dan uwansa komai.

𝐃𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀 𝐓𝐀 𝘓𝘊ð˜ĩð˜ĩð˜Ē𝘧𝘊ð˜Ŋ 𝘎ð˜ķð˜Ĩ𝘊 ð˜Ŋð˜Ķ
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
ð˜Ąð˜Ē𝘧ð˜Ē𝘧ð˜Ēð˜Ģ𝘊𝘚ð˜Ēð˜ģ

ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2

ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ

𝙋𝘞𝙂𝙀 7




Tana tsananin buqatar ta fita,ta kumayi imanin wadannan gumakan ba wanda
zai musu magana suji sai wanda ya turosu.....tana jin kuma faduwar fara yin magana
dashi. Sanda taji ya motsa da bisa alamun ajiye kiran zaiyi,a nutse ta bude baki ta
soma magana dashi da qaramar muryar nan tata me wani irin tone

"Ban kasance daya daya daga cikin hajojin kamfaninka ba ballantana ka sanya min
masu tsaro na......'yantacciyar d'iya ce kamar kowa,hakanan mutum ce dake da nata
tsarin da qa'idojin da ba komai take jurewa ba......ka yiwa wadannan gumakan magana
da suyi gaggawar matsawa subar qofar gidanmu". Tsayawa yayi cak da abinda yakeyi,ya
harde hannayensa a qirji yana sauraronta da muryar dake nuna tamkar gargadinsa
kawai takeyi kai tsaye.

Idanunsa ya lumshe kai tsaye na sakanni sannan ya budesu,yana ci gaba da
jin qaramin sautinta dake magana cikin yanayi na tsiwa har sai data qarasa
maganarta.

"Bakisan waye ni ba.....i can't tolerate it,dole ki koyi manners......bawai na zama
dani kawai ba,manners akan komai

Please Login or Register in order to submit comment