You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a
rayuwa ba qarya bace,dukkan wanda ya rigaka kwana dole zai rigaka tashi.

Har tana niyyar miqewa ta wuce dakinta,don ba abinda take gani a
parlor din face abinda zai daga mata hankali yakuma sake tunzura mata zuciya,sai ga
musaddiq ya shigo. Ta dauka itace mutum na farko da zai fara gani,tayi zaton itace
ta farko da zai fara zarcewa wajenta,saidai gaba daya hankalinsa yana kansu anni.

"Lalala....waye ya saki kitso?" Musaddiq ya fada yana fito da idanunsa waje ba tare
daya lura anni takewa kitson ba. Kwabe fuska kuwa tayi tana nuna anni da bata
ganinta da comb din hannunta.

"Nice nan dan gidanku" Anni ta fada tana hade rai,saidai kuma qasan hade ran nata
murmushi ne boyayye a kwance da zaka iya karantarsa.

"Ai banga ke bace" Ya fada yana shafa kansa yana saukar da ganinsa qasa gami da
qoqarin boye damuwarsa.
"Maza ka qarasa sakaltata.....tunda shi wancan yayi gudun hijira......nidai wallahi
karku sakani cikin masu yiwa mijin da zata aura bayanin sangartacciyar da zai aura
ahto" Farouq ya fada yana miqewa gami da jifan musaddiq da harara.

"Basai kun wahalar da kanku ba BB.......mijin yafi kowa fahimtar wacece ita....
Lafiya qalau ba wanda zaiji bari ya gani" Musaddiq ya fada kansa tsaye yana aje
dubansa kan fuskar amna. Maganan yadan tabata,sai ya hade mata da jin nauyi,bakinta
yayi murus tayi qasa da idanunta tana tsaga kalban anni din. Ganin haka sai shima
ya juya xai fita,sai a sannan subutar bakin da yayi ya dawo masa.


"Kan uban buhun babbakun bala'i" Maamah ta fada tana jin numfashinta kamar zai
tsinke daga hunhunta yayi qaura yabar gangar jikinta. Ba ita kadai ba,kusan duk
wanda yake wajen ya dauki haske,saidai nasu kyawawan zukatan cika sukayi da
farinciki duk da basu nuna hakan kai tsaye ba.

"Kai musaddiqu!" Maamah ta fusgi sunansa da wani irin sauti sanda yake bin bayan
farouq xasu fice a falon. Farouq din bai dakata ba ya fice abinsa,sai musaddiq daya
tsaya sannan ya dawo da baya.

"Ban ganki ba kina falon ashe.....barka da yamma".

"Don uban banka ta yaya dama zaka ganni?,ai ba zaka taba ganina ba daman tunda
idaniyarku ta jima a kulle,amma aidaka shigo kaga qannen uwarka da yayyen uwarka
rututu ko?". Maganan ta masa nauyi qwarai,bayaso kuma taci gaba a haka,don yasan
inda qarshen maganar xata tsaya.

"Ba'a canzawa tuwo dai suna wallahi.....komai tsahon xamani da shudewarsa dole abar
masa sunansa.....dole kuma abar masa siffa da kamarsa........kasan me yasa na
tsaidaka?" Ta tafi Kai tsaye ga abinda yake tsunkulin zuciyarta.

"Inaso na gaya maka ka shaidawa dan uwannaka........ban haifi yaron da xai yiwa
kansa zabin matar aure ba,yadda na kawoku duniya ba tare da shawarinku ba......haka
zan zabawa kowanne days a cikinku kalar macen da tayimin.....ba kuma uban daya isa
ya hanani tunda ba adopting naku nayo ba,haka ba tsintoku nayi ba.......mutum ya
sabamin kuma daidai nake dana tsine masa albarka sai me?,da can ma aina rayu babu
shi......tashi ka bani waje shashasha wand baisan gurin dake masa ciwo ba". Tsam ya
miqe kamar yadda ta buqata,zuciyarsa na masa wani irin bugu kaman zata balle
qirjinsa ta fito,a haka ya lalubi hanya ya fice yana fatan samun wadayacciyar iska
da tafi ta parlor din yawa.

Ko sanda zata gama da farouq tuni anni ta jima da wucewa dakinsu ita
da amna,suna shiga anni ta maida qofar ta rufe,idanunta zube saman fuskar amna da
yanayi na tuhuma take kallonta.

"Amna!,kalleni da kyau!!" Anni ta fada adan tsawace tana budewa amna dukka girman
idanunta,abinda bai taba faruwa ba tsakaninsu.

"Akwai wata alaqa ta daban bayan ta yaya da qanwarsa tsakaninki da musaddiq?" A dan
tsorace amna ta daga kai ta kalli anni,wani irin tsoron annin ya mamayeta abinda
bata taba ji ba a kanta tunda ta haifeta. Koda cikin tsoro take muddin anni na
gefenta tana samun aminci,amma yau annin ce abar tsoron da kanta.

"Tambayarki nakeyi kinyi tsaye kina qaremin kallo" Anni ta fada bayan ta lura da
yadda zuciyar amna kr bugawa. Ba zuciyar amna kawai ba,itama tata zuciyar bugawa
takeyi......tana bugawa bawai don tsoron mariya ko tsoron abinda zata iyayi
bane.....aah,tana bugawa ne saboda tsoron fitina. Bata qaunar wata fitinar sam a
shekarunta da suka fara turawa,ko a yanzunma a haka addu'a take Ubangiji ya ganar
da mariya......yasa ta fahimci rayuwa a zahirin yadda take.
"Bab......babbu anni"

"Kin tabbatar?" Ta sake tsareta da tambayar tana dage girarta duka sama. Kai ta
gyada mata a sanyaye,ba kuma don wai tana da tabbacin ba.

"Idanma baki da tabbacin inaso ki samoshi a duk inda yake,gina alaqa mukeso ayi
bawai a sake rusata da sabuwar matsala ba" Tana kaiwa nan ta wuce cikin dakin tabar
amna da tarin nazarce nazarce cikin kwanyarta,tsoro da fargaba suna cikata,tana jin
kamar wani farinciki yana dab da barin rayuwarta.

β˜…Tsakanin jiya da yau gaba daya zazzabinnasa kusan cikin jikinta yayishi,jinyar
tasa da komai nasa ya nadeta ya hanata aiwatar da komai,sallah kawai ke tashinsu.
Duk wani motsi nasa idan ta kalleshi labarinsa ke mata yawo,duk da tanajin akwai
ragowar side da bai gama cika ba,tana tsananin buqatar jin yadda anni ta iya riqon
kafaffen mutum irin fuad ta maidashi cikakken mutum haka ta ruwan sanyi,tanata jera
labaran nasu......tanason banbance shi da ita waye yafi wani fuskantar qalubale?.

Ta wani fannin gaba daya ya aza mata nauyinsa,ya narke mata ya zama
wani shagwababbe shagwababbe za'ace?. Wannan narkewar tasa kuma ta fahimci yana
sake amfani da ita ne yana budewa kansa wasu rufaffun qofofi dake cikin lungunan
zuciyarta. Yanayin kallonsa me sanyata tana jin kamar zata narke ne......ko yaya ya
riqe mata hannu sai taji kaman ta mallaki farincikin duniya ne dana lahira,kwana
cikin jikinsa ya zame mata wani abu na musamman ga gangar jikinta dama zuciyarta,ta
yadda komai nauyin baccinta.....muddin ya saketa ko ya matsa daga jikinta sai nata
barcin yayi qaura. Ta fahimci wani abu tattare dashi,yana da tsananin ibadar da duk
riqon da zazzabin yayi masa hakan baya hanashi tashi sallar dare,hakanan ko meye
yakeyi idan time na sallah ya shiga xai ajiye yaje yayi,koda itace cikin jikinsa
duk yadd yake mararin jinsa tare da ita to zai ajeta gefe sai ya bada farillan nan
ya hada da nafilar kafin ko bayan kowacce sallah.

A hankali sai taji wani quruciyar data rasa sanadin hawan girma kanta
tana dawo mata. Ita dinma saita sake zama wata sakaltacciya,zuciyarta ta koma baya
can sanda take da gatan ummienta da abbanta.

A safiyar ranar alhamis dinne ya bude dukka wayoyinsu shi da
ita,duk da shi din taga kaman kwana biyu yana buda wani dan qaramin abu shi ba tab
ba shi ba system ba yana fita outside deck yana zama yayi wayoyin da batasan da
waye yakeyi ba.

Ita ta fara shiga tayi wankanta a sannan yana salatud dhuha kafin ya
kammala. Tasan muddin ya kammala zaice saisun shiga sunyi wankan nan tare,abinda ta
kasa sabawa har yanzu,saidai idan Allah ya bashi sa'a yayi mata kutse,takanji kamar
ta koma cikin cikinta saboda kunya.

Tana gaban mirror tana shiryawa yana addu'o'insa,baice mata komai ba
harta gama shirinta cikin Turkish dressing. Budadden wando me kama da Palazzo da
rigarsa data sauko har gwiwa me dogon hannu.

Ta masa wani irin kyau da ya sanya ya dinga jin tsigar jikinsa na
tashi,to amma ba daman yin komai saboda awa biyu kadai ya rage Lokacin tashinsu.
Banda private jet nema da warhaka suna airport din.

Yana fara cire kayansa ta nufi qofa zata gudu setting room,taku
uku ya cimmata ya maida qofan ya rufe ya sanya lock,sannan ya koma a nutse yana
qarasa fidda kayan jikinsa. Gefe daya tayi da kanta zuciyarta na bugawa,har yau har
kwanan gobe ta kasa sabawa da wannan kalar abun nashi. Yana ganinta baice komai
ba,ya kammala ya daure qugunsa da towel,bata ankara ba ba kuma zato kawai taji yayi
sama da ita ya fara takawa yana dosar bandaki.
Wutsil wutsil ta fara da qafafunta tana bashi excuse.

"Na gama shiryawa fa..... Please ka saukeni,zan jiraka Allah bazan fita ba" Bai
kalleta bama sai daya shiga toilet din.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 107


107


"Nasha gaya miki ai......duk sanda kikayi rushing to bathroom kikayi
taking shower baki jirani ba......sunan wannan wankan FAKE.....Bakisan sunna bane
miji da mata suyi wanka a tare suna kamfata a mazubi guda daya?......bakisan hadis
dinnan ba?" Ya fadi bayan ya zumbulata a bathtub ya dafe hannayensa duka gaban
bathtub din yana zube mata narkakkun idanunsa.

Gefe tayi da kanta da idanunta da suka cika da qwallar yadda ya
sanyata ta jiqe gaba daya,a tsaiwar da yayi a gabanta tana tsoron towel dinsa ya
kwance batasan ya zatayi ba.

"Mu gama wankan na nuna miki number na Hadith din da raweeh din" Yana kaiwa nan sai
gashi tsundum cikin bathtub din.

"Zakiga takan tsiya" Ya fada qasan ranshi. Shigewa jikinta yayi sosai shigewa bata
wasa ba. Wasu irin abubuwa ya fara mata bayan ya samu nasarar cire mata komai data
shigo toilet din dashi. Fahimtar inda ya dosa ya sanyata fara doje masa tana barin
ya bari.....lokaci zai qure fa?,saidai cikin qasa da mintuna biyar ya yaudare
bakinta da duk wani kuzari nasa da salon yaudarar nan tashi,tayi luf tana sauke
numfashi gami da amsar saqonninsa da kyau,duk kuwa da yadda zuciyarta ke warning
nata.

Shurun da taji ya kusa sanyata bude idanunta,Allah ya taimaketa
batakai gayin hakan ba zuciyarta ta gaya mata ke ya tsaya yake kallo. Haka dinne,ya
zuba mata idanu yana karantar yadda dafin da ya zuba mata yake bibiyar duk wani
jininta da bugun numfashinta,amma qi fadi irin nata da tsananin jan girma da ajinta
ya hanata zubda makamanta ta fito masa a mutum.....saidai ya shirya maganinta shima
wannan karon,duk da ya samu dukkan wata shaida data tabbatar masa ya bude wata
babbar qofa a zuciyarta da rayuwarta gaba daya,qofar daya tabbatar ba wani mahaluki
daya taba zuwa koda kusa da ita......yayi nasarar bude zuciyarta gaba daya da wata
irin nasara da bai taba kawowa a ransa ba. Saidai ya lura yadda take da wani irin
aji na daban.......haka soyayyarta take ta daban.....

Ya samu aji yadda yakeso da kamun kai har fiye da yadda yake hasashen za'a
samu wajen wata diya mace,komai nata me ajinne.
"Lokaci yana qurewa......quick" Ya fada yana zare jikinsa daga ita gami da barinta
a yanayin data zurma dukka jikinta da zuciyarta.

Kasa motsawa tayi ko kadan,tayi shuru tana jin wani abu yana mata yawo
kowanne sashe na jikinta. Karon farko da taji wani abu me kama da haushi ya tsaya
mata a wuya,da haushi sanda kake expecting wani abu daga gurin wani kuma ya zamana
baka samu komai in return ba.

Kasa motsawa tayi,yana wankansa hankali kwance yana satar
kallonta,yadda tayi relax cikin ruwan ya masa dadi. Nan kusa yasan zai samu dukkan
abinda yake buri da muradi,ya kammala wankansa tsaf ya daura towel ya nufi qofa
yana cewa.

"Hurry up".

Da qyar ta bude idanunta,idanunta suna cika da hawaye,haka kawai taji
zuciyarta tana karyewa,sai ta dinga jin zafin abun a zuciyarta. Dolenta ko tanaso
ko bataso tasan wanka ya kamata,don bata da tabbacin bai kamata din ba.

Can qasan ranta taji wani abu me kama da haushinsa yana kamata,don haka
koda ta fito ta samu ya gama shiryawa. Wani irin sassanyan kyau yayi cikin 3pieces
suit saqar kamfanin Hugo Boss dan qasar Germany,rufaffen takalmin qafarsa na
kamfanin berluti ya sake fitar da kimar shigarsa,ya kuma qara fidda ainihin darajar
dukiya da Allah yayi masa.

Kallo guda dayan data masa kowanne sashe na zuciya da gangar jikinta
ya aminta da tsananin kyan da yayi,ya kuma soma qoqarin hura wutar daya kunna mata
a toilet,sai tayi ta mata don ba'ace ta maza ba,ta danne komai daga ranta ta soma
takowa cikin dakin tana yin kaman bata san da zamanshi ba.

Comb din da take taje kanshi dashi ya ajiye yan lumshe idanunsa,shan
qamshinta yayi masa dari bisa dari,sai ya sake fidda mata wani kima daban a
idanunsa.

Takowa kadan yayi ya tsaya daga bayanta,yana qare mata kallo,shauqinta
yana fusgarsa,saidai duk da hakan yayi qoqarin controlling kansa yana boye
hannayensa cikin trouser dinsa. So yake ya manna mata taji irin yadda yakeji a
kanta ko yaya ne.

"Sabrrrrrr" Ya kirata da wani irin tone daya kusa tarwatsa duk wani dauriya nata.
Yi tayi kaman bata jishi ba,ya leqa fuskarta ta gefe sanda take qoqarin goge ruwan
sumarta. Wani dadi ne ya kusa sumar dashi,duk da qoqarin boye masa ruwan sumar nata
da takeyi amma tuni shi ya gama fahimtar inda karatun ya sanya gaba. Lallai
tarkonsa yayi kamu......tarkonsa ya kama kurciya. Yanason tabbatarwa da gaske fushi
tayi don ya barta saman hanya?,don haka ya qara taku biyu gaba zuwa inda take yana
kuma sake ambatar sunanta.

"Sabrrrr" Idanunta ta sake lumshewa gami da budesu,saidai har yanxun dai bata motsa
ba bare ta amsa masa.

"My world" Ya sake kiranta yana qara rage tazarar dake tsananin su har yanxun yana
leqen fuskarta.

"Duniyata" Ya fada da wani coolness daidai sanda ya isa bayanta ya kama qugunta ya
riqe yana mannata da jikinsa.

Duk wata tsiga ta jikinta sai daya tasheta da iya haka kawai,to amma
duk da taji haka hakan baxai sanyata saurin bada kanta ba,don haka ta hada qarfinta
duka tana qoqarin turashi gami da cewa.

"I need to get dressed"

"No....you don't" Ya amsa mata yana juyo da ita gaba daya suna facing din
juna,sannan ya juyata zuwa yana hadata da bango gami da ajiye mata wani zazzafan
kiss.

Ta fahimci so yake kawai ya birkitata ya sake tafiyanshi kaman
daxu,itakam wani irin sanyi takeji yana ratsa mata qasusuwanta da kyau kaman ana
hura mata ac.

"Am cold" Ta fada tana sasssuta muryarta saboda yadda yake qara kashe mata jiki.

"I'll keep you warm" Ya bata amsa muryarsa can qasan maqoshinsa,a zafafe ya soma
aje mata kisses masu dimauta nutsuwa.

Kamo hankalinta tayi da qyar tana kauda fuskarta,jikinta nema yake ya
fara shaking,matakin da tasan indai takai ba zata iya qwatar kanta ba.

"Am not wearing anything under this towel" Da bugaggun idanunsa ya saki murmushi
yana dafe bangon da dukka hannayensa

"I know" Ya fadi yana daga girarsa sama. Sosai taja numfashin daya aike mata da
sassanyan turaren nan nasa dake kasheta,yadda ya sakata a tsakiyar yana baza mata
qamshinsa da dumin numfashinsa tana jin kaman zata sume ne.

"Please" Ta fada da raunanniyar murya. Batason yaga faduwarta ko lagonta gaba
daya,amma ta karanci kamar ya shiryawa hakanne.

"Don't fight it" Ya fada yana qoqarin maida bakinsa cikin nata.

"Am in towel fa...." Ta fadi tana qarasa narke masa gaba daya.

"I don't care" Ya fada kaman me rada yana jin yadda shima ya fara kunnuwa,ya sanya
hannunsa yana mayar mata da gashin kanta daya rufe fuskarta baya gami da saka
idanunsa sosai cikin nata kaman bazai daina kallonta ba,wani irin sassanyan kallo
yake mata kaman zai hadiyeta,abinda ya sanya taji qafafunta kaman zasu watsar da
ita.

"Yau zamu fita a muraaka......still Muhammad fuad anata tunanin hukuncin da za'a
yanke a kansa?". Kasa bashi amsa tayi,daidai nan wayoyinsu suka dauki tsuwwa lokaci
guda kaman hadin baki.

" Farouq ne,wallahi nasan farouq ne" Ya fada a wani jigace. Sosai dariya ta taso
mata,amma bata da qarfin yinta,saidai wani mamaki ya kamata da taga daya daga cikin
masu kiran farouq dinne.

Kiran farouq din ita ya ceceta,sai yaja baya ya zauna yana daga
wayar,ita kuma ta kwashi kayanta ta koma toilet din.

Sanda ta fito ya gama hada komai,ya bita da kallo kafin ya daga
yatsansa yana karkadawa. Luggage dinta ya sauke,ya birkitata da kyau ya ciro wata
oversize abaya,ya hado da wani Malaysian hijab ya miqa mata.

Bata musa ba ta karba,zata koma ciki ta sauya ya bake ko ina gami da
mata nuni kan ta shirya a nan. Bata tsaya jan dogon magana ba,tunda ta fahimci
makara suke gab dayi,ta shirya tsaf ya kama igiyan rigar dana hijab din duka ya
daure mata sannan yaja baya yana kallonta.
"Ya salam.....How can i disguise you?" Yayi Maga nan da gaske yana jin da zai yiwu
ya hana kowanne ido kallonta kome wahala zai iya bin tsarin.

"Oho nima ban sani ba" Ta fada tana tura baki gaba don da gaske tana jin haushin
abinda ya matan,duk da tana qoqarin nuna bata damu ba.

Dariyarsa ya danne yasa hannu ya jawota baya yana basarwa.

"Karmu fita ki canza......if not.... I'll be open about my feelings for you....i
won't feel ashamed of anyone...." Idanunta ta fidda warwaje,a yadda ta shaida
rufewar idanunsa akan duk abinda zuciyarsa ta karkata akai,tasan zai iya aikata
komai da komai,tana kuma tsoro da nauyin hakan. Hancinta yadan matse yana gane
tsoronta.

"Don hana hakan faruwa......Handle me delicately....fine"

"Ya salam" Ta fada tana jin fargabarsa yana kamata. Hannu ya miqa ya riqe hannunta
yana fadin

"Ki barshi,Jordan zai kula da komai da muk....." Bai qarasa fada ba dumin hannunta
ya ratsa sassan jikinsa,sai ya dakata da maganar yana kai hannunsa goshinta da
sauri.

"Ya salam......fever?,when?" Ya fada a rude. Idonta ta kada kadan,ita ta dauka ma
zafin jikin bai fito ba,iya ita kadai takejinsa a qashinta.

"Bai dade ba......i will be fine" Kai ya girgixa yana yana azawa kansa laifin,yana
ganin kaman maidata ruwa da yayi da sanyata zubawa kanta ruwa shi ya jawo hakan.

"No.....mu tsaya ki samu relief,zansa farouq yayi magana da......" Hannunta ta dora
da sauri saman nasa hannun.

"I'll manage". Dan jim yayi yana kokwanto kafin yace.

"Really?" Kai ta gyada masa duk da yadda taji kanta yana sara mata. Bataso ace duk
jama'ar dake can suna jiransa jiran ya tashi a banza saboda ita kadai,hakan sam
baiyi tsari ba,sannan ita kanta bata qarfafashi yayi abinda ya dace ba.

Yadda yake riqe da ita kaman zaiyi mata tafiyar da qafafunta ya sanya
mata Tsananin jin kunya,saidai gurin ta sake fahimtar na masoya ne,kowa sabgar
gabansa yakeyi,a haka suka iso private boat din da iya ita dashi kawai zai fitar
zuwa Conrad island su ruski motarsu su wuce airport,don ko Jordan wani boat din
daban ya biyo ba nasu ba.


*MAAMAH*

Kaman wadda bata da aikinyi haka ta dinga bin diddigin shudewar kowanne
awa da minti na zamansu a gurin da delay din fu'ad na qarasowa gurin. Ba shakka
banda idanunsu ameenatu a wajen ba abinda zai hanata komawa gefe tayi kuka koda na
minti ashirinne,wataqila ta samu sassaucin abinda takeji cikin zuciyarta.

Yau ita mariya ta wayi gari karyar farautarta ta farauto abinda take
da muradi ta sakashi a gaba tana wasa dashi yadda taga dama?. Yau ita mariya ita ke
zaune tana jiran dakon isowar yaronta?,wata macen bariki ta riqeshi tsahon wasu
kwanaki?,a yau da take jiran qarasowarsa kuma sai time din da taga daman ganinsa
kowa zai ganshi?,ita kuwa idan batayi taba rayuwar mutanen nan biyu ba ai tayi
asarar zuwanta duniya.
Guda gudan baqinciki haka ta dinga hadiyarsa tana korawa da yawun
bakinta,tana sake tsarawa da shirya yadda zata gigita rayuwarsu duka su biyun idan
sun sauka Nigeria. Tana jin kamar idan ta jira su koma ya mata nisa,don haka ta
koma gefe ta zaro wayarta tana duba wata number tana jin gwara ta shirya komai tun
yanzu,ta yadda komai din zai fara da wuruwuri. Sauran ma'aikatanta dake hannun
yanzu haka dukansu bata da wata damuwa a kansu,tasan akwai babban aiki a kansu daba
wanda ya isa ya furta sunanta da sunan toxarci ko tona asiri.

Tana qoqarin kira wani kiran ya shigo. Matsanancin mamaki ya kamata
ganin sunan fareeda yana yawo saman screen din,bata tsaya jinkiri ba ta daga wayar
tana kiran sunanta.

"Na'am....ya kike?" Tayi namijin qoqarin tausar kanta ta karya harshenta ta
tambayeta.

"Ina kika shiga fareeda?,bayan kinsan babban aiki muka tunkara?" Sake hadiye wata
guduma da taxo kan harshenta tayi,tasani cewa banda tana tausar kanta ta samu isa
ga dalilin kiran da tuni ta jima da daddannawa mariya zagi.

"Kowanne aiki ma yazo qarshe......kowacce magana anzo qarshenta......kowanne
al'amari dadinsa da wuyarsa sun qare..... Kedai kawai turamin date din da zaku iso
Nigeria,da airport da zaku sauka,kano ko Lagos ko abuja". Daga kai tayi tana duban
musaddiq dake nesa kadan da ita.

"Musaddiq" Ta kirashi tana sauke wayar,waiwayowa yayi sannan ya fara takawa a
hankali har ya iso gabanta,a tsume ta danna kan number ta miqa masa wayar.

"Kayi confirming na date din komawarmu da airport din da zamu sauka ka rubutamin a
nan ka tura". Wayar ya karba yana kalla,number ba suna,hakan yadan saka shakka
cikin ransa,amma ta wani sashen kuma daya tuna kalmar UWA UWA CE sai ya rubuta
kaman yadda tace din,ya tura bayan ya gama kalle numbers din tsaf sannan ya miqa
mata yana barin wajen.

Details din daya rubuta take kalla

"Me fareeda zatayi dashi?" Taji tambayar ta tsargo mata. Cak ta tsaya tana son
laluba amsar amma kuma saita kasa. Wani sashe na zuciyarta sai taji yadan shiga
fargaba kadan,sai kuma daya sashen ya taso ya danneshi yana gaya mata.

"Fareeda masoyiya ce....wataqila akwai mafitar data samo mana,zatayi abinda ni na
kasa yi wataqila"
(Ni kuwa nace ummm inji me ciwon haqori......ba girin girin ba tayi mai dai,maji ma
gani wai an binne tsohuwa da ranta).

Aje wannan tunanin tayi tana tureshi gefe,ta kashe wayar tana ajeta da
zummar ci gaba da lissafin sai yaushe zata bar fu'ad din ya qaraso?,sai kuma
idanunta sukayi mata kyakkyawan gani.

A nutse suke takowa da wani irin qyallin da idan ka kirashi na amarci
bakayi laifi ko kuskurr ba. Kanta yana aje saman kafadarsa wanda tayi hakanne bisa
dole saboda jiri jiri data fara ji. Da farko taqi ganin zasu shiga jama'a ne,amma
daga baya dole ta kwanta din saboda indai batayi hakan ba tana iya faduwa ko ya
dagata ya dauketa in ya tabbatar hakan zata faru. Tsakiyar qirjinta kuma wani abune
ya dunqule mata,tana jin kaman amai ne yake taruwar mata,saidai bata gasgata hakan
ba ganin lafiya qalau take ai,bataci wani abu daya bata mata ciki ba bare tace.

"Na shiga uku......la haula wala quwwata" Maamah ta fada tana jin yanayinta yana
hautsinewa gaba daya.......
"Anya.....anya.....anya?" Ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta tana tsoron furta
abinda ke cikin zuciyarta.

"KINYI KUSKUREN ZABOTA" Maganar bokan ta sake maimaita kanta cikin kwanyarta.

"Bazai faru ba.....saidai ita tayi danasani" Ta fada tana furxar da iske me qarfi
daga hunhunta zuwa bakinta.


_uhmmmmmmmmm_




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862




𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 108




108


Idanunta ta dan lumshe kana ta budesu,tana iya hangen maamah dake
farko,farouq daga gefanta kadan yanata amsa waya,anni daga can gaba ita amna.
Musaddiq da saddiq ne bata hango ba,ko kuma yadda amai din yaketa faman mata kai
kawo tsakanin cikinta da maqogorone ya hanata ganinsu oho

"Amai nakeji" Ta fada qasa qasa kanta a kafadarsa,don ta tabbatar zai iya kufce
mata tsaf kafin sukai wajensu. Hannunsa yasa ya riqe hannayenta sosai,kafin ya sake
riqe tafin hannunta da kyau yana cewa

"Ga can hanyar washroom,zaki iya qarasawa?" Ya tambaya a tausashe. Kai ta jinjina
masa

"Oya.....be fast" Ya fada yana mata riqon da zataji dadin tafiyan da kyau,duk da ba
haka ranshi yaso ba,yaso ace ta bari ya rage mata wahalar tafiyar kawai.

Murmurshi

Please Login or Register in order to submit comment