You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Idanunta ta zube akan laila dake kallonta kawai.

"Kina da hanyar da zaki hadamin 'yan press?,ina da buqatar gabatar da taron 'yan
jarida.......ya kamata na fara gwadawa ameenatu nawa salon da kuma ainihin kalata"
Kai laila ta girgiza.

"Bansan yadda zamu kirasu ba.....amma ina da qawa da take aiki gidan radio.....zan
shaida mata sai suzo din".

"Hakan yayi.....gobe da sassafe nake buqatar su hallara a harabar gidan nan,bayan
gida radio dinsu ina buqatar ta qara da gayyatar wasu kafafen yad'a labaran dama na
jaridun......zan biyata akan wannan aikin gayyatar" Maamah tayi maganar tana
lalubar number musaddiq,can qasan ranta baqincikin yadda musaddiq ya kasa kiranta a
matsayinta na mahaifiyarsu ya shaida mata abinda ya farun sai a rariya ta gani.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 120



https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



120


Dab da zata tsinke ya daga,kafin yakai ga gaidata ta amshe

"Duk tsiya tuwo dai sunansa tuwo.....kuma.basai kayi hakan ba zaka tabbatar min ni
ba komin komai bace a wajenku.....abu ya samu dan uwanka musaddiq saidai naji
labari a wani wajen?,yanzun kuna ina?". Tafin hannunsa ya sanya ya riqe goshinsa
saboda yadda kansa yake sarawa......ta dage ita kuma still saita qara masa wani
ciwon.

"Muna asibiti" Ya amsa mata a taqaice.

"An ganshi ne?" Ta tambaya yana fargabar bayyanarsa kafin ta qullawa ameenatu jakar
tsabar data shirya qulla mata.

"Adda sabreen ce....."

"Tayi bari?" Ta qarasa masa da abinda zuciyarta ke fatan ya kasance. Sai daya janye
wayar a kunnensa yana dubanta kafin ya maida cike da mamaki.

"Wanne asibiti ne?" Ta tambayeshi tana kauda waccan tambayar ganin bai bata amsa
ba.

"Noor hospital" Iya abinda dama takeson ji kenan,tana kuma da buqatar zuwa idan
barinne sabreen din tayi ta karbi barin da hannunta ta taho dashi nan ta bawa
karnukansu su cinye su shanyen jinin,ta kuma aikawa sabreen din video din ta yadda
zai zame mata wani mummunan ciwon.

Sharp sharp ta shirya,ta kuma kira driver ya fidda mota suka wuce noor
hospital kai tsaye.

Masifa ta dinga yiwa driver din,tana ganin kaman baya sauri.....kamar
ba zai isa akan lokaci ba. Cikin qasa da minti arba'in sai gashi cikin noor
hospital saboda uban gudun data sanyashi ya dinga zubawa.

"Scanning din da mukayi mata ya kasa bamu ainihin abinda mukeson
gani.....saidai mun samu nasarar ganin two embryos,hakan yana alamta akwai d'a biyu
cikin mararta.....iya abinda muka gani kenan,mararta akwai nauyi da aiki fiye da
marar me dauke da yaro guda daya....so that dole ta dinga kiyaye wasu
abubuwan.....bacin ranta.....aiki me wahala da nauyi da duk abinda zai sanya mata
stress.......babies din suna lafiya......amma idan ba'a basu kulawar data dace
ba.....komai zai iya faruwa" Bayanin likitan kenan da dukkaninsa ya sauka a kunnen
maamah data shigo dakin da qarfinta,saidai ta samu annin da dr mubeena tana mata
bayani a parlor din dakin da sabreen din take.

"Za'a kiyaye in sha Allah Dr...." Anni ta fada jikinta yana sanyaya,tana sake
girmama hukuncin ubangiji da girman qudurarsa da zatinsa.

"Allah kaine Allah,baka da abokin tarayya Allah.....yadda ka samar da wadannan
halittu naka a mahaifar mahaifiyarsu cikin wani salo da hikima irin naka.....Allah
ka fidda mahaifinsu ka kiyayeshi daga dukkan hadari" Anni tayi adduar da take har
zuciyarta ba tare da tasan da wanzuwar maamah a wajen ba.

Duk da taso tazo ta samu gudan jinin yaron a leda amma saita samu
akasin haka.....daga tunanin yaro daya ya koma biyu....bugu da qari ma kuma ana
bata tabbacin raunanniyar lafiyar da suke da ita.....to amma har yanzu tana da
sauran abinda ya rage wanda zata girgixa duniyar anni.....a yanzu zata gudanar da
plan A......plan B din kuma ta ajewa kwanakin da suke zuwa a gaba.

"Zaki gama munafuncinki tsaf.....da duk wata munafukar addu'arki ki gayamin inda
kika kaimin d'ana.....ni dama nasan za'azo wajen.....ko ba dade ko bajima dole sai
kinyi yunqurin salwantarmin da yaro saboda ki handame abinda ya mallaka......to
wallahi baki isa ba......ni mariya nice uwar FU'AD,bazan kuma qyaleki ba idan
yarona ya salwanta". Cak anni ta dakata daga buda qofar ainihin dakin da sabreen ke
ciki,waiwayowa tayi a nutse cike da mamaki tana duban maamah din

"Mariya?,kinsan abinda bakinki yake fada kuwa?". Wani kallo maamah ta watsawa
anni,cike da alfahari da samun tabbaci akan qudurinta.

"Na sani mana ameena.....kina tunanin ba'a hayyacina nake ba?.....UWAR RIQON
MUHAMMAD JADDA TAYI KIDNAPPING DINSA SABODA NEMAN KUDIN FANSA......A HALIN YANZU BA
WANDA YASAN INDA TA BOYESHI....ya kikaga taken wannan labarin a gidajen rediyoyin
Nigeria africa dama duniya gaba daya?" Har tsakiyar kanta anni taji wani abu ya
tsarga mata

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

"Dama ki riqe abarki zuwa gobe.....don kuwa goben warhaka bana tunanin kina cikin
masu cikakken 'yanci kamar haka". Ta qarasa fada tana takawa hankali kwance tana
wucewa dakin da sabreen din take.

Duk wata jijiya ta kanta ta gama tashi saman goshinta,ba abinda
qirjinta yakeyi sai bugawa da wani irin matsanancin fushi. Kowacce kalma data fita
daga bakin maamah a kunnen sabreen ta sauka wadda ke zaune ta jingina da fuskar
gadon tana kokawa da kanta ta samu tasha tea din ko babu yawa.

Zubawa maamah ido tayi sanda take shigowa dakin,qasan ranta cike da
damuwar yadda ta samu sabreen din zaune sosai.....ba wani alamu na fitar hayyaci ko
jigata a tattare da ita.

Kallon kallo sukewa junansu,yayin da kallon da sabreen ke ajiye mata ya
kasance wani qazamtacce kuma wulaqantaccen kallo da bata taba ganin irinsa ba a
kanta. Hakan bai sage mata gwiwa ba,taci gaba da takowa har ta qaraso dab da
gadonta sannan ta janye dubanta daga kanta ta maidashi kan ledar ruwan da aka gama
qara mata.

"Inda zan baki shawara ki dauka......da zaifimiki kyau salin alin ki kwanta a zare
miki cikin nan cikin girma da mutunci......"

".......idan ba haka ba zaki sanya a kwantar dani a kasheni sannan ki qwaqule
abinda yake marata?" Lafuzzan suka fita da wani irin fushi da yaja hankalin maamah
din zuwa gareta.

Wani zazzafan kallo take sauke mata tana kuma ajiye mug din hannunta.

"Eh ina nufin abinda na fada din......kina zaton don kin aikata hakan zai bani
mamaki?" Ta jefa mata tambayar tana dage dukka girarta sama,sai kuma ta girgiza
kanta.

"Ko kadan bazanyi mamaki ba......matar data zabi duniyarta akan
lahirarta?,.....matar data zabi salwantar yaranta ta tsira da qazantar duniya wato
kudi!......ke nake zargi......ke nake zargi da harbin FU'AD!......ke nake zargi da
batarmin da MIJINA UBAN 'YA'YANA......" Ta qarasa maganar tana dora hannunta saman
mararta,wasu zafafan hawaye suna taruwar mata.

Sosai maganar ta zowa maamah a bazata,amma bata dauketa da wani
muhimmanci me yawa ba tunda tana ganin sabreen din bata da wani power hujja ko
damar da zata iya aiwatar da komai a kanta.

Girarta ta dage duka tana yiwa sabreen duban mamaki,wani qaramin
murmushin rainin wayo yana fita akan fuskarta

"Ko?......sannu tattabara uwar aure.... Sannu me miji,to idan nidince fa?,sai
yaya?". Idanu sabreen ta zuba mata kafin wani kwantaccen murmushi ya sauka saman
fuskarta,abinda ya soma sanyawa maamah dawowa hayyacinta. Ba jiya ko yau ba,ta sani
murmushin sabreen din bashi da dadi

"Kina daukan abun da sauqi ne har haka ko?.....haihuwar muhammad da kikayi hakan
bazai qareki da komai ba a sanda kike qoqarin rabani dashi......haihuwarsa bazai
qareki da komai ba a sanda kike qoqarin tabamin shi....lafiyarsa hankalinsa ko
dukiyarsa........ko waye yayi gigin tabamin DUNIYATA sai inda qarfina ya
qare........ciki kuwa harda ke......ke mahaifiyarsa wadda tayi rainonsa na shekara
sha hudu kawai......fu'ad DUNIYATA ne.....duniyar da ko mutuwa nayi za'a binne ni a
tsakiyarta".

Wani gigitaccen yanayi maamah ta shiga,idanunta bibbiyu duka a warwaje
take kallon sabreen din. Kalaman yarinyar na yau sun girmi hankalinta,saidai duk da
haka zuciyarta tana tuna mata ita din MARIYA CE FA.....giwa kuma kota fadi tafi
qarfin wawa.

"Kinyi kuskuren fara son abinda nice silar zuwansa duniya......"

"Amma ina me farincikin bake kika halicceshi ba ko?" Ta maida mata idanunta tsaye a
kanta.

"Ba wani doguwar sa'insa bane tsakanina dake kodon albarkacin wannan dake kwance a
marata...." Ta fada tana nuna cikinta da yatsa.

"Sassauqan umarni ne na ki fiddomin mijina ko ina ya shiga.......awa ashirin da
hudu kacal kike dashi.....sannan......taron 'yan jarida karki fasa.......hakan shi
zai sauqaqewa muhammad sanin asalin launin kalar mahaifiyarsa" Ta qarashe maganar
tana daga mata wayar hannunta.

"Maimakon zazzafan labarin uwar riqo me kidnapping dan riqonta.....wataqila sai
labarin ya canza akala zuwa labarin BAQAR UWA" Ta qarasa fada da wani mugun
confidence daya nuna har cikin idanunta.

Wani gigitaccen kallo maamah ke yiwa sabreen din,wannan wacce irin
BAQAR JARABA ta hadu da ita?,sam sam ta mance da batun video da yake cikin
wayar,lallai kuwa da ta nemi hanyar da zata salwantar dashi,saidai a yanzun ba
salwantar da video din kawai take nema ba......tana neman sassauqar hanyar da zata
shafe babin sabreen......ta kuma shafe labarin rayuwarta gaba daya daga duniya.

Ko sau daya itama bata daga qafa daga kallon maamah din ba,a wannan
karon tanajin takai maqura.......itama takai qarshe,kuma ko meye zai faru saidai ya
faru. Ko kadan bata yi mata kallon bil'adama cikakkiya a yanzun. Tanajin ta shirya
tunkarar kowanne yaqi,ta shirya tunkarar kowanne qalubale akan muhammad fu'ad
dinta......tana jin ta shirya ta sadaukar da komai a kansa koda hakan yana nufin
salwantar numfashinta.

Tsaiwar maamah a wajen yayi mata,don tana jin akwai sauran maganganu
daya kamata ta gaya mata,idanunta suna lumshewa da wani irin bacin rai,mararta tana
murda mata da wani irin ciwo ta kalli maamah

"Ina kyautata zaton har yanzu bakisan asalin wace sabreen ba......amma lokaci ya
kusanto da zata shaida miki ainihin kalarta.......har yanzu baki tunzura sabreen ta
nuna miki wace ita ba......to amma yanzu anzo wannan gabar.....duk inda za'a juya
duk inda zakiyi ki tsaya tsakaninki da ita,huda nadra haneefa anni farouq musaddiq
da saddiq.......uban gayya DUNIYATA fu'ad......wadannan din ahalina ne.....jinina
ne,iyaye kawunnai kuma kakannin abinda yake yake cikina ne,uwa uba me gayya
DUNIYATA jadda.......taba daya daga cikinsu?" Saita girgiza kanta tana sake tsareta
da idanu.
"Bazai taba zame miki abu me sauqi ba.....jeki gwada idan zaki iya.....zabi ya rage
naki.....nima wayewar garin goben nake jira.....ki tara 'yan jarida.....idan kinso
kiqi nemomin mijina kiga yadda DUNIYARKI zata tarwatse a karo daya" Takai qarshen
maganar rashin tsoronta qarara yana bayyana.

"Idan kin fita ki rufen qofan" Sabreen da amai ke tasowa ta fadi tana zamowa a
nutse daga saman gadon ta doshi bandaki da 'yar sassarfa gudun kada ta zube aman a
wajen.

Dif tayi tana sauraren sautin yunqurin aman da takeyi daga
bandaki.....wasu irin taurari suna zagaya kwanyarta tun daga gaba zuwa baya

"Wacce irin lalacewa ce ta sameki MARIYA?" Ta tuhumi kanta da kanta tana jin wani
zazzafan gumi yana karyo mata.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 121


https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



121


Daga nan inda take tana iya jin kakarin aman sabreen da take kwarashi da
wani irin wahala da kuma galabaita. Aman tana yinsa ne da dukka zuciyarta da wani
irin karyewa da sarewa,wani irin rauni ne yake cikata a duk sanda ta tuna
"Ba fu'ad a gefanta.....qarfinta.....rayuwarta......kuma duniyarta gaba
daya,hasalima ba wanda yasan yana ina......yana raye ko ya mutu,me gobensu zata
haifar musu su duka?".

A maimakon tausayi dake sauka zuciyar kowacce 'ya mace a sanda taga 'yar
uwarta mace cikin hali na ciwon laulayi saboda sanin ciwonsa da tsananin da yake
dashi......a bangaren maamah fitar aman sabreen sai takejin kamar wani sauti ne na
barazana a gareta......kamar wani sauti ne dake gaya mata dukkan komai naki ya kusa
zuwa qarshe.....asirinki zai tarwatse muddin haduwa da tabbatuwar alaqa yaci gaba
da wanzuwa tsakanin sabreen da fu'ad.

"Ya zanyi na cire cikinnan?,ya zanyi na rabata dashi?" Abinda zuciyarta ta dinga
gaya mata kenan da wani irin qunci da tsananin takura.

Yunqurin aman shi ya sanya anni qarasowa cikin dakin da wani irin
mutuwar jiki da sarewa,zallar mamaki da kuma tsananin tsoron hali da kuma dabi'ar
maamah din.
Da baya da baya ta dinga tafiya har takai bakin qofar dakin,idanun maaman akan
anni,haka idanun anni din itama akan maamah,saita juya tana fuskantar qofa ta
murdata ta fice.

Asalin gigicewa takeji gaba daya har cikin kwanyarta,me yasa duk wani
motsi da zatayi sai yarinyar ta zame mata cikas?.....me yasa take zamewa rayuwarta
da duk wani motsinta matsala ne?,yaya akayi ta gayyato matsala cikin rayuwarta?.
Idan ta duba ta sasanni da dama sai taga takunta na baya yafi kyau......takunta na
baya yafi fita akan wanda take fafatawa bayan shigowar sabreen rayuwarta. Batasan
me ya dauki hankalinta ba tun a wancan lokacin da har tabar yarinyar da video din
bata salwantar dashi ba,ko a sannan tana ganin bata da wani power.....ba kuma
abinda zata iyayi?,ko wannan shine sila?.

Cikin tausasawa da tausayawa anni ke riqe da ita,tun tana iya fitar da
dan abinda ta samu kurba har ya zamana ba komai cikin aman sai yawu kawai,abinda ya
qara adadin galabaitarta kenan,don tanata yunqurin aman kuma babu wani sauran
abinda yayi saura a cikinta. Wani hawaye na taru idanun anni sanda take kwance ana
qara mata ruwa gudun kada galabaitar ya taba lafiyar yaran da suke cikinta,tausayin
sabreen din yana ratsa anni sosai. Ta sani ba abu bane me sauqi wajen mace ta shiga
irin wannan yanayin.....ko ita a baya data taba rasa abba,bawai rashi na mutuwa
ba,aah saidai rashi na rabuwar aure na dan lokaci,ita kadai tasan me taji,ita kadai
tasan ya taji.....ita kadai tasan abinda ta fuskanta,to ballantana wannan,wani
yanayi ne da babu tabbas ko sahihancin zance akanshi.....wani yanayi ne da ba wanda
yake da tsayayyen abun fada akai. Gefe daya lalurar ciki.....ga qananun shekaru,ga
kuma uwa uba me kankat wato MARAICI.

Ta wani bangaren kuma abinda ke daga mata hankali shine.....irin
maganganun da taji ana musaya tsakanin maamah da sabreen,wanne irin makami yarinyar
ke dashi har haka da ya girgiza mariya farat daya?.

Batasan adadin lokutan data share a zaune gaban sabreen ba,tana riqe
da carbinta wanda har yatsunta sun fara zafi saboda riqonsa. Dare yayi nisa
sosai,ita kadai ce kawai,don ta hana kowa zama tare da sabreen din sai ita,gani
takeyi babu wanda zai iya kula da ita irin yadda takeso,gani takeyi dole ita kadai
ce zata iya bata wannan kulawar.

Yadda taga rana haka taga dare,sau daya tak sabreen ta farka tsahon
daren zuwa safiya,ta bada tea dan kadan,bacci ya sake kwasheta ta koma.

Sai anni take ganin baccin yafi zama alkhairi akan ta zauna idanun ta
biyu tana kuka,ko don saboda lafiyar yaran da take dauke dasu.

*_WASHEGARI_*


K'arfe tara na safe a nan ta yiwa alhj hamza kibiya.....musaddiq da saddiq
da sauran guards na fu'ad wadanda suke gida da wadanda suke kan hanya sanda abun ya
faru. Iya su uku suka shigo,don ko amna ya hanata zuwa asibitin gudun kada su hadu
suyita yiwa mutane kuka.

A sannan anni na gaban gadon sabreen din,tana ta neman yadda zata
sanyata taci wani abun komai qanqantarsa.

Karon farko da magana me zurfi ta hada alhaji hamza da sabreen. Shi ya
tsaya kan saita saka wani abu a cikinta. Tana kuka hawaye daya bayan daya haka ta
dinga karbar tea din daga hannun momma bahijja wadda ta shigo daya baya.

Sai data soma yunqurin dawo dashi sannan ta barta,ta wuce da mug din ta
daurayeshi sannan ta dawo dashi ta ajiye.
Shuru ya ratsa dakin na wani lokaci,kowa ka kalli fuskarsa cikin nazari
da kuma alhini yake. Alhj hamza ne ya fara magana.

"Toh.....bamu da abinda zamu cewa ubangijinmu sai godiya.....kafin ya jarabcemu da
wannan ya mana tarin baiwa da ni'imomin da ba zasu irgu ba....cikar iko da
adalcinsa ne ya jarrabi bawa akan dukkan abinda yaga dama a sanda yaso.....to mu ba
zamu butulce masa ba,alhamdulillah da duk yadda yayi damu......mun tattauna da masu
ruwa da tsaki cikin sha'anin tsaro na qasar nan dama maqwaftanta,kuma suna bamu
tabbacin lalubo inda suke ko wani abu daya shafesu cikin qasa da awanni ashirin da
hudu in sha Allah......su kansu guard da suke aiki qarqashinsa dukkaninsu basuyi
bacci ba,ba wanda ya zauna ko ya kwanta,aiki suke akan batun ba qaqqautawa....kuma
ana samun haske sosai,su kansu na yadda da qwarewarsu in sha Allahu komai zaizo
cikin sauqi" Ya qarasa maganar yana basu tabbaci a maganarsa dama fuskarsa.

"Ubangiji ya amince....Allah ya bayyana gaskiya a duk inda take" Momma ta fada
cikin sanyi jiki da tashin hankali. Sunan sabreen ya kira,ta amsa masa ba tare data
iya dubansa ba,don kuwa ita kadai tasan abinda takeji.

Nasiha sosai yayi mata me ratsa jiki da hankali akan imani da qaddara
da daukarta.

"Zan dauka abba in sha Allah.....zan dauka" Ta fadi kawai tana sauke idanunta saman
tafin hannunta daya wani qara dashewa yayi haske kaman ba cikakken jini a jikinta.

Da daya da daya suka fara juyawa suna fita.

"Saddiq" Ta kirashi abinda ya dawo da hankalin anni kanta don wNi abune da bata
taba yi ba. Shima a mamakance ya juyo yana kallonta,sai ta sanya hannu ta
yafitoshi.

Dawowa yayi a nutse,y jawo kujerar da momma ta tashi akai ya ajiye
daura da ita.

"Gani adda" Ya fada yana mata duban mamaki.

"Akwai labari da nakeso na fitar kashi uku......kashi daya gidan tv radio dana
jaridu......kashi biyun da yayi saura tv radio ne kawai zaiyiwu su haskashi" Ta
fada tana dubansa.

Magananta taja hankalin anni,ta kuma tuna mata da duk tattaunawarsu da
maamah ta jiya. Sakin kayansu da take kwashewa tayi wanda za'a koma dasu gida,ta
tako a hankali har inda suke.

Duban saddiq anni tayi fuskarta ba walwala

"Tashi kaje parlor.....idan na gama hada kayan zan kiraka" Fuskarsa da mamaki da
kuma wani zumudi nason jin qarashen maganarsa da sabreen ya miqe,saidai babu yadda
zaiyi anni ta katsi hanzarinsa.

Inda ya tashi ta koma ta zauna tana duban sabreen.

"Wanne labari zaki fitar sabreen?"

"Yadda akayi uwa ta zama me dillancin yaronta don kawai ta mallakeshi......yadda
wata uwa ta zama azzaluma wadda batasan ciwon 'ya'yan cikinta bama bare na
wasu....yadda wata uwa ke burin murqushe 'ya'yanta ta gaji abinda suka
bari......yadda akayi sabreena ta zama matar muhammad jadda ta hannun mahaifiyarsa"
Sabreen ta fadi muryarta nason karyewa amma tana bawa kanta da kanta qwarin
gwiwa,tana jin babu wani abu da zai hanata aiwatar da wannan abun,daga nan zuwa
dare muddin bataji komai dangane da muhammad dinta ba. Koda sabreen bata fayyacewa
anni komai ba.....annin da kanta ta gama fahimta.....wani tsohon zargi da shakkunta
kan maamah lokacin aurensa shine yakeso ya tabbata bayan wani lokaci.

"Akwai kuskure cikin aikata haka sabreen......kinsan wanne kuskure?" Anni ta
tambayi sabreen tana son qwato hankalinta da nutsuwarta,domin kuwa ta hangi abubuwa
masu tarin yawa cikin idanun sabreen din masu kaifin gaske suna kai kawo.

"Mariya bata da asara.....domin kuwa tata rayuwar tazo qarshe idan aka dangantata
da taku......mariya bata da wata asara me yawa,kece kike da jini a jika.....kace
kike tara zuri'a yanzu.....domme zaki yiwa kanki wannan barnar?" Anni ta fada tana
kallon idanun sabreen tanason taga iya dadin yadda maganar ta shigeta. Kai sabreen
ta mirgina gefe....kamar anni ba zata fahimci nata shimfidadden takun ba.....wannan
abun wani taku ne kuma tarko ne me kyau idan anyi amfani dashi ta hanyar daya
dace......tarko ne da zata kama kowacce kurwa ta maamah din.

"Kinsan wace mariya ta gaske?,kinsan yadda me babban suna suka rayu?" Haka kawai
taji tanason ta sakeji daga bakin anni,ta tabbatar koda shi ya gaya mata.....koda
shi ya labarta mata bazai gaya mata yadda anni zata sanar mata ba,don haka ta
kadawa anni kai a hankali tana dubanta.

A nutse anni ta warewa sabreen komai.....rayuwar fu'ad tun kafin tafiyar
mariya da kuma tafiyartata,yadda ta samesu da irin wahala da tasha kafin ta
maidashi kalar mutumin da yake a yau,duk wani qalubale da kuma gwagwarmayar rayuwa
tasa.

Hannu kawai sabreen ta saka ta lullube fuskarta da tafin hannuwan
nata,sai takejin a wancan ranar a Maldives tamkar bai gaya mata komai nasa
bama.....kaman ba wani abu daya gaya mata daya shafi rayuwarsa. Ta yaya zata iya
controlling hawayenta a fuskarta?,ta yaya zara iya.hana kanta zubar hawaye?,wacce
irin asararriyar uwa suka samu?,wacce irin uwace wannan wadda da ita gwara babu?.
Lallai ba shakka zatayi komai.....har fiye da abinda take hasashe a baya ma zatayi.

Amma da irin wannan abun nata har anni ke duban ta qyaleta?,me yasa
anni ba zata fahimci cewa ita sabreen dama mutuncinta bararre ne a idanun mutane da
yawa?......me yasa anni ba zata Fahimci zata iya saudar da komai wa fu'ad ba?,don
don mutuncin nata da iyakarsa idanun fu'ad dasu anni?,duk da yafi qarfin D'A tunda
wata yarda ce da sassanyan aminci ta samu a muhallin da yafi kowanne daraja.

"Ban gaya miki don kiyita kuka ba.....ban gaya miki don kiyita damuwa da sanya
bacin rai ba.....na gaya miki ne saboda ki sani........ba kowanne mutum kake qarar
da energy dinka a kansa ba". Kai sabreen ta jinjina tana sauke hannuwanta.

"Taso nayi tarayya da ita wajen raya zunibinta anni......ta kawoni da qarfi da yaji
da'irar da ban shirya shigota ba.....saidai a yanzun ina kallon juyewar al'amarin
daga sharri zuwa alkhairi...." A nutse itama ta gayawa anni yadda duka komai ya
kasance tsakanin ta da maamah a wancan lokacin. Tayi shuru anni tana jin komai yana
kwaranye mata,lallai duk inda xa'a qaunaci juna saboda Allah dole a dinga ji a jiki
a duk lokacin da wani abu zai kasance da dayan biyun. Ashe ba'a banza ba ta dinga
jin wani baqin abubuwa dangane da auren?,ba'a banza ba ta dinga jin rashin gamsuwa
da komai?.

Al'amarin maamah sai taji yana sake girma a zuciyarta. Mamakinta tana
jin kaman zai fasa ko ya kashe zuciyarta gaba daya.


*_WANI DARE!_*
Ranar ta kasance musu wani dare da dukkaninsu suka kwana suna juyayi da
mutuwar mamaki kan halayyar mariya da komai nata.....daren ya zame musu wani dare
da sabreen ta kwanta tana jin zata dan dagawa maamah qafa saboda anni data buqaci
wurga lamarinta a kwandon shara abita da ruwan addu'a,saidai kuma wannan daren ya
zama daren da yayi silar da sabreen ta soma sakin UPDATE akan maamah......wanda
batayi tunanin akwai wani abu da zai dakatar da ita ba ko waye ko meye shi!.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 122



122


Har qarfe sha daya na dare anni tana zaune gaban sabreen,lokacinne kuma
Dr mubeena ta gama daura mata wani ruwan daya zama shine abincinta yanzu saboda ba
wani abu da yake iya shiga cikinta ya zauna,koda ya shiga dimma sai ya fito. Rubuce
rubuce Dr mubeena ta kammala yi cikin file din sannan ta rufe,ta ajiye a gefe tana
sanya idanunta kan sabreen dake kwance da shirin yin baccin da ta tabbatar qaryarsa
ya shammaceta......saidai tasan zaizo ne kadai ta hanyar sinadaran da suka zubawa
ruwan dake shiga jikinta,wannan ne kadai yake bata daman yin baccin daya kasance ba
natural na qashin kanta ba.



Please Login or Register in order to submit comment