You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayar.

Alamun daga kiran ya sanyata sake hada nutsuwarta waje daya,gami da
dagawa hajja furaira hannu wadda ke lissafo mata tsare tsare na abubuwan da suka
shirya gudanarwa a wata shimfidaddiyar farar takarda.

Tsit wajen yayi,bakajin motsin komai da kowa,abinda zai sanya wanda
ke nesa irin fu'ad din xaya dauka ita kadai ce wanze a dakin.

"Barka da warhaka" Ya furta da muryar nan tasa dake da tasirin kwarjini me yawa da
haiba a ciki.

"Barka kade.....ina fata kana lafiya?" Ta masa tambayar data zamo abu mafi dadewa
baiji ba daga bakinta. Duk da zuciyarsa ta kasa yarda haka siddan tayi kiransa amma
ya hadiye wannan.....ko yaya yaji dadin tambayar cikin ransa koda kuwa da manufa
aka yita

"Alhamdulillah.....Allah yasa kuma hakan" Dan murmushi ta saki,zuciyarta tana
ayyano nesanta zuwa kusa da ita.

"Lafiyarmu qalau,sai shirye shirye da muke yi gadan gadan". Bai wani fahimci shirye
shiryen da take magana a kansu tashin farko ba......har sai data dora da nata
bayanin.

" Na kiraka ne don na shaida maka.....ina buqatar wasu kudade da zan qarasa duk
hidimomin da suka ragen.....ta bangaranka da kuma bangaren ita kanta
amaryarka......don kasan hidimar biki ba qaramin abu bane,......bare ni da zan
aurar da dan fari......kuma ita kanta yarinyar ya kamata ace ita,danginta da dukkan
wani dage da jibi da ita yasan cewa tabbas da gaske mamallakin diamond company zata
aura.......banason harkar qaranta......ya kamata duniya kanta ta shaida d'ana zaiyi
auren fari".

Kusan koda yaushe fitar kalmomin bakinta suna zame masa tamkar makaranta
ne......ya jima da sanin maamah din macace me son izza da nuna isa.......ya dauka
wani tsohuwar dabi'a ce a tattare da ita.....amma xuwa yanzun ya sake amanna mutuwa
ce kadai zata iya samun nasarar rabata da wannan halin.

"Me ake buqata?" Ya tambayeta kai tsaye.....don shima da nashi plan din. Zuwa yanzu
yana kallon komai ne tamkar a tafin hannunsa ake shiryashi,abinda ya rage masa ya
sani kuma kadanne da bayajin zai zame masa me wahalar riska.

"Kudi nakeso ka sakamin......sannan ka sakawa amaryarka......kamar million......."

"Kiwa saddiq magana......zan gaya masa ya saka miki adadin abinda kike buqata" Ya
yanke bayanin da taso yi masa da adadin kudaden da duk da yasan ya jima da fin
qarfinsu........amma kuma ana nemansu ne a muhalli da gurbin da babu buqatar yawan
wannan adadin.

Murmushi ta saki tana jin wani dadi yana ratsa zuciyarta,tun a yanzu
tana sake samun tabbacin nasarar dake bibiyarta,tana kuma fara jin qamshi da dadin
da uwa keji a yayin da take gwada girman izzarta akan yaranta suke kuma bibiyarta
sau da qafa akan duk wani buri ko quduri nata

"Allah yayi maka albarka" Ta fada tana murmushi. Kalmar ta dinga masa amsa kuwwa
cikin kunnuwansa,sai ya dinga jin kamar ba daga bakin maamah ta fito ba. Idan yace
bazai iya tuna ranar data fadi wannan kalmar a kansa baiyi qarya ba.

A hankali sai yaji kaman zuciyarsa tana rugujewa. Inama ace ta fadi
kalmar ne domin cancanta da kamatar ta fadeta a kansa?,bawai don duniya ko wani abu
dake cikinta ba?,bawai don son rai ko biyan buqatar rai ba.

Da wannan murmushin dake sake yalwata saman fuskarta a kowacce rana ta
ajjiye wayar saman table din gabanta. Qasaitaccen table ne da yazo cikin set na
kayan furniture din da aka qawata sabon gidan nata data riga kowa tarewa a ciki.
Gida ne datake jin zata kece biki na alfarma a ciki......zata daga sunanta da kuma
martabarta a idanun qewaye dama duniya gaba daya.

"Kowanne motsinsa sai ya dangantani da saddiq hamza kibiya" Ta fadi tana duban
idanun hajja,har cikin ranta tana jin wata wuta tana ruruwa tare dason gaggautowar
ranar da zata saka kakkaifar wuqarta ta yanke wannan alaqar da tafi mata kama da
baqar alaqa.

"Hanzarin na mene mariya?,saurin me kikeyi ne?,saura kwanaki nawa duka duka?" Hajja
ta bata qwarin gwiwa tana cike da kwadayi da son jin abinda ya faru tsakaninta da
fuad din.

Kai maamah din ta jinjina tana son dawo da walwalarta kaman daxun.

"Bai tsaya jin koma nawa nake buqata ba......kawai yace nayi magana da saddiq,shima
zai masa magana na karbi abinda zan karba din......kinga zan karbi kaso biyu
kenan......da nawa dana yarinyar can,zan san mata wani abu a ciki ne kawai.....sai
na cire abinda zan cira a ciki.......zan ware na boka donshi kansa yawan kudin dana
qara masa akan wanda ya buqata na fahimci ya qara masa azamar aikin nan.....hajja"
Ta qarash da kiran sunanta da wani irin sauti dake nuna gajiya da zallar zaquwa.

"Inaso yayimin aiki irin aikin da bai taba yin irinsa ba tunda ya fara harkan
nan......inason yayimin kalar aikin da ba fuad ba......ko tsuntsun gidan fu'ad sai
ya zama me biyayya a gareni........inason yayimin aikin da sabreena zata koma
tamkar bawa da ubangidansa a hannuna........bansan me yasa yarinyar ke yimin
kwarjini ba,bansan me yasa nakeji wani abu daban ba idan ta kalleni......inason
dukka wadannan abubuwan su shafe daga idanuna".

Wani murmushi dake dauke da tarin boyayyun ma'anoni da rufaffun
qudurori dake amsa kuwwa da amon nawa burin yana sama da naki hajja tayi,sannan ta
harde qafarta tana cewa.

"Dukka wannan qanqanin aiki ne a wajensa,kuma ko iya haka aka tsaya zaki bawa wani
labarin zafin aikinsa......isassun mata kawai ke iya aiki dashi,matan manya da
iyayen manyan mutane irinki,saboda daga sadakin aikinsa kawai zaki fahimci ba gama
garin boka bane.....don haka ki rubuta ki ajjiye.....dukkanin wadannan burirrika
naki tamkar sun gama cika ne......saidai banji share dita a wannan kasafin naki
ba".

Rausayar da kai maamah tayi tana sakin murmushin jin dadi. A qasan
ranta tana mamakin son kudi tsantsa irin na hajja din,duk kuwa da cewa lullube take
cikin wadata me tarin yawa.......saidai wadatar yaranta idan kaf idan aka hadesu
batakai kaso daya cikin ukun abinda fuad ya mallaka ba shi kadai......amman duk da
hakan bata raina kudi komai qanqantarsu(tabbacin zuciya ta zarme da yawa dason abun
duniya,Allah ka kiyashemu).

"Baki da dukkan wata damuwa hajja,kina da million uku a ciki,kafin alqalami ne
kawai......kuma somin tabi,nan gaba kadan ke zaki dinga bada wannan adadin a
matsayin taki kyautar"

"Qwarai da gaske kuwa mariya" Hajjan ta fada kanta tsaye tana duban idanun maamah
da wani irin confidence daya sanya maida hankalin maama duka a kanta. Wannan ya
sanya ta sassauta kaifafa harshenta da nuna dukkanin qwarin gwiwar dake kan
fuskarta.

"Yaronki ai yarona ne mariya...ni nasan bani da haufi....ba zaki taba butulcemin
ba" Ta sake yiwa kalamanta ado da wasu kalmomin

"In sha Allahu" Maamah ta amsa tana rausayar dakai har yanzu murmushin na saman
fuskarta,ta kuma jawo wayarta tana fadin

"Bari na nemi musaddiq ya nemo yaron can,don da zafi zafi ake dukan qarfe......gobe
nakeso muyi sammakon tafiya hado dukka ayyukan dama sauran bayanai......bikin nan
da gaske tahowa yakeyi,kwana shida kacal ya rage......inason tasan da zaman kowacce
doka qa'ida dama sharadi kafin ta samu lasisin karbar igiyoyin auren d'ana a
kanta". Da wani kallo hajja ta bita kawai ba tare da tace komai ba.....saidai kuma
can cikin wani saqo na zuciyar magana ce me yawa nauyi da kuma dogon xangon da
bazai yiwu baki ya furtata ba.

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 3


Daure da babban towol da kuma da kuma wani babba data lullufe jikinta
kirif tun daga saman kanta take takowa daga cikin toilet din dake manne da falon
tana dawowa cikin ainihin falon daya zama sansaninta a yanzu.

Nan din wani kebantaccen guri ne cikin gidan nasu,da asalinsa ya zama
muhalli ne na mahaifinsu,wanda tun bayan shudewarsa ba wanda yake ta'ammali da
wajen,don gidan nasu ya wadaci kowa,kawai sai saman inda falon nasa yake ya zama
wajen da akan bude ne kawai a share,sai idan wani taro ya tashi kuma cikin gidan
sannan akan zauna a ciki har ayi a gama.

A yanzun saman ya zama kusan nata,tunda aka fara mata aikin gyaran
jikin ko qasan gidan bata saukowa. An killace muhallin da komai da zata
buqata,kaman yadda aka ajiye mata cima kala kala wanda sam basu taba birgeta ba
koda qanqani. Hasalima ita a yanzu cin abinci ya zame mata daya daga cikin horon da
mamma bahijja keyi mata. Koda kuwa ta kauda kai ta kuma kafe akan ba zataci
ba,mamman bahijjan data tsaya a bigiren da akan buqaci uwa saita nemo wani abu
daban ta bata,takance

"Aure zakiyi fa sabreena,gidan miji zakije,anata gyaran fata amma can cikin ko
oho?,kinsan yadda yunwa ke kassara ni'imar mace kuwa?" A duk sanda ta furta hakan
sai sabreen taji kaman wani abu ya shaqe mata wuya. Wai halan basu kula kuma basu
lura da dukkan komai?,sunata magana akan auren da ba komai a cikinsa face zallar
rudani?,rarrabuwar burika da kuma tarin biyan buqatar rayuka masu yawa a cikinsa?.

A yanxun data dawo daga dauraye jikinta da tayi daga gyaran jikin da
kullum kwanan duniya takeji kaman ana mannawa fatarta wuta.....duk inda ta gifta
kota zauna wani irin fitinannen qamshi take barwa gurin. Wani irin mayen qamshi me
matuqar naci da mannewa jiki dama dukkan wani abu da mutum zaiyi mu'amala dashi.

Qawatattun idanun nan nata da a yanzun suka koma rusunannu ta daga a
nutse tana duban me gyaran jikin dake faman gyara wutar da zata sake turareta da
ita. Ta zama wata kurmar qarfi da yaji,magana na mata wahalar gaske,kwanyarta da
nazarinta harma da dukka tunaninkan da takan raba dare tana yinsu.....dukkansu
sunfi ta'allaqa da kuma rinjaye akan YAYA WASAN ZAI KAYA?......wa zata fuskanta
cikin fuskoki muryoyi dama ruhikan dake zagaye da wannan game din?.

Idan ta tuna da mariya maamah.......tana jin wani abu sosai qasan
ranta......jikinta kuma yana bata wani lamari me nauyi da batasan mene shi ba,amma
kuma wani sashe na zuciyarta yana gaya mata ita din ba komai bace......tayi
ganganci ne ma kawai data kutso kanta cikin rayuwarta......batasan wacece sabreen
ba da gaske da bata aikata hakan ba.......bata kuma san meye da meye zata iya
aikatawa ba. Motsawar sunan muhammad fu'ad kawai cikin kwanyarta shine abinda yafi
sanyawa wani tsagi na zuciyarta damuwa.........lalata dukkan wata alaqa da kuma
dangantaka cikin aurensu shine abu mafi sauqi da zata iya aiwatarwa......to amma
kuma saki fa?.....A HANNUNSA YAKE!,amsar da akowacce rana take qara yawan adadin
fargabarta.

Lumshe ido tayi taja iska sosai cikin huhunta sanda muryoyi biyu suka
sauka a tsakiyar kanta

"Turaren ya hadu kona miqo miki ki zauna akai da kanki....." Cewar basudaniyar me
gyaran jikin,yayin da nata maganar ya cakuda dana mamma bahijja data miqa mata wani
bowl na tangaran

"Bata din.....kafin hayaqin ya gama bin jikin ki saiki qoqari ki shanye wannan".
Dara daran fararen idanunta ta daga tana kallon mamma bahijja kafin ta maida
dubanta kan abinda take miqo mata,itama ita take kallo wannan ya hanata katabus na
musanta mata,sai kawai ta miqa hannu ta karba,saidai kuma data fakaici ta
juya,saita maidashi daga gefanta ta ajiye.

Sanda tururin hayaqin ke ratsa sassan jikinta haka kowanne lungu da
saqo na zuciyarta ke qoqarin bata mafita a lamarin dake tunkarota nan da kwanaki
biyar masu zuwa. Zuwan mamman bahijja ya zame mata wani babban katanga daya hanata
aiwatar da kowanne shiri da zai nesantata da auren.....duk da tarin bayanan da kawu
yayi mata na ba inda zata shiga a duniya ta iya tserewa me jadda........saidai ta
dauki.maganar tasa a wasan yara ne.

Koshi waye.....ko kuma da meye yake taqama tayi imanin saidai idan
bata sakashi cikin plan dinta ba.....


"Adda baki sha bafa" Muryar huda da ke zaune gefanta ta fada,wadda kusan kowanne
shirye shirye da ita ake aiwatar dashi.

Maida idanunta tayi ta sake lumshewa muryar huda na dawo mata,ta
fahimci dari bisa dari ba wani me adawa da auren,kusan kai tsaye ma zata iya cewa
dukkaninsu maraba suke da abun,duba da irin walwalar da suke ciki gaba dayansu.

"Ki nutsu sabreen.......ki nutsu.....karkiyi abinda zargi zai dawo
kanki......karkiyi abinda su mamma bahijja xasu kasa karbarki da wankeki daga laifi
duk sanda kika kammala da wancan game din kika dawo musu" Wata murya daga can qasan
zuciyarta ta soma gaya mata.

Idanunta ta bude ta aza kan huda har sai da hudan tadan sha jinin
jikinta. Sunyi mata farin sani,daga kallonta kawai suna iya karantar umarni da kuma
hani,amma ga sabanin tunaninta sai tayi mata nuni data miqo mata abun. A hanzarce
kuwa ta ajiye littafin hannunta ta miqe ta dauko ta miqa mata.

Tsure abun tayi da kallo wanda batasan da meye da meye aka hadasu
ba,to amma koda meye aka hada din,ta tabbatar mamma tana asarar kudinta ne
kawai,don haka ta kafa kai ta soma kurba a hankali gardin abun yana ratsa kunnenta
duk kuwa da bakinta ba taste,haka zuciyarta a quntace take.


*******Doguwar tafiya,hawa da kuma sauka,kutsawa cikin surquqi dukka ba damuwar
maamah bane. Fatanta da burinta ta dangana ga mubata.160 data miqawa al'amarinta
gaba daya,ta kuma sanya hope me yawa a kansa.

A yanayin data ganshi a yau ya sake saka mata tabbacin samun cikakkiyar
nasara. A hargitse yake yau din cikin zafin ayyukan mutanen da suka zabi ya zame
musu abun dogaro kuma hanyar samun duniyarsu ba tare da damuwa da meye makomarsu ta
lahira ba?.

Bayan shafe shafensa da buge bugensa,ta hautsina dukkanin kayan aikinsa
da yayi,ya kalleta da jajayen idanunsa qananun ainun dake cike da rashin tauhidi da
kuma zallar sabo fajirci da fasiqanci. Dubane daya sake tabbatar mata ba rahama ko
tausayi ko misqala zarratin a cikin ransa

"Akwai tarin sarqaqiya......akwai tarin qalubale......akwai al'amura da yawa da
zasu iya wanzuwa ko su biyo baya........ita din taurarinta nada tsananin haske da
wahalar kutsa kai a cikinsu........tana da wahalar sha'ani na gaske......tabata
kuma abune da zai iya zuwa da nasara da akasin haka.......kaman zan iya cewa KINYI
KUSKUREN ZABINTA.......to amma kuma ba wani tauraro da zai iya shiga nasa taurarin
sai natan......tamkar itace mahadi masarrafi kuma barin nasa
taurarin......taurarinta sune abokan tafiyar nasa.........sunyi matuqar dacewa da
juna.......wanda hakan shine zai bada damar tafiyar umarninmu da haninmu a
kansa......kusan komai nasu suna matuqar kamanceceniya dana juna......ITACE TA DACE
DA CIKAR BURINKI MUDDIN AKA SAMI GUSHEWAR AKASIN DA NAKE HANGOWA......saidai na
gaya miki.....kamar akwai alamun KUSKURE DA NADAMA.......akwai babban
waqeee'a......juyewar komai da lullubewar mayanin duhu bisa faifan qaddara".

Tunda ya fara maganar gabanta ke wani irin faduwa. Hajja da suka gama
sauraron bayanan a tare ta dora hannunta a kafadar maamah da zummar yin magana da
ita da neman qarin bayani......saidai da sauri maamah ta zame hannunta daga
kafadarta......tayi nisan da batajin zataji kira......zuwa yanzu nasara take nema
ta kowacce fuska,ta kuma kowanne yanayi......bata buqatar tsaiko fashin baqi ko
qarin bayani a yayin da take dab da cimma nasararta........bayan kuma a baya ya
bata tabbacin ta wannan hanyar ce kawai nasara zatazo mata babu ko kwanto

"Amma dai akwai hasken nasara ko dan kadanne?". Kansa dake cike da wasu irin
gasussuka ya jinjina ba tare daya koda dubi idanunta ba. Cikin samun qwarin gwiwa
tace

"Nasara duk nasara ce komai qanqantarta,baa canza mata suna daga nasarar
dai,hakanan daga qaramar nasara ake cimma babba......ayimin komai da ake da iko a
kansa.......a sakamin yarinyar a tafin hannuna kafin samuwar fu'ad.......itace
tsanin......ita zan fara mallaka don ta zama hannuna tsani na kuma idona zuwa ga
wancan babban burin nawa!". Ta fadi muryarta na raunana tana tsoron jin akasin
abinda zuciyarta ke muradi.
"An gama!" Ya fada da wata kakkaurar murya maras dadin amo. Saita sauke ajiyar
zuciya tana yi relax ganin yadda ya soma maida hankali akan aikinta.

Boyayyar ajiyar zuciya hajja itama ta saki. Ba haka taso lamarin ya
kasance ba,taso tana kuma so taji cikakken fashin baqi da qarin bayani daga
bakinsa.
Wacce irin sarqaqiya ce?
Wanne irin duhu ne?.
Wani irin baqin lullubin mayafi ne haka?.
Wacce nadama ce zata biyo baya?.
Meye kuskure a cikin zabin nata?.

Dukka wadannan amsoshin tana buqatar saninsu ne don tasan daga ina zata
dasa nata harsashin?. Daga ina tata TAFIYAR zata fara?. Ta wacce fuska zata saita
tata DUNIYAR?,ta aza duniyar SHALELENTA?.

Bata data cewa ko wani motsi,ta sani cikin aikinsa ba shishshigi,ke me
rakiya kuma baki data cewa......hakanan baki da damar yin komayya kiyi tambaya akan
aikin daba naki ba.....wannan kadai ya kashe mata jiki,ta zurfafa a cikin saqe saqe
har ya kammala aikin maamah,ya kuma shaida mata su wuce zasu tadda komai cikin
motarsu da qarin bayani.

Bata sake gasgatawa da imani da zancansa ba saida suka samu komai a
mota a ajjiye kaman yadda yace. Ta sake tsinkewa da lamarin aikinsa,inda da wani
suka je wajen.....ko akwai gilmawar dan adam ta wajen sai tace an ajiye musu ne.

"Kings abun mamaki hajja?,kullum mutumin nan sake dauren kai lamarinsa yakeyi" Ta
fada tana juya kayan tsatsubar dake hannunta.

"Kina zaton gurin qaramin mutum na kawoki......amma mariya?,me yasa kikaqi
tambayarsa dukka qalubale da matsalolin daya hango miki?" Hajja tayi tambayar da
tafi tsaya mata a rai.

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
𝘑𝘒𝘧𝘒𝘧𝘒𝘣π˜ͺ𝘺𝘒𝘳


ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 4


A nutse ta daga kai tana kallon hajjan

"Na tsani matsala ko akasi hajja......musamman a wannan matsayin da nake kai a
yanzu......me zanyi da ita ballantana na buqaci sharhi a kanta?,bana buqatar dukkan
wani jawabi da zai alamta min FADUWA ko MATSALA akan cikar burina a
yanzu.......inaji a jikina da raina cewa......zan iya kauda kowacce matsala da zata
tunkaro muddin na samu nasarar tsallake wannan matakin da muke kai a yanzu......da
qwanjina....da kuma fikirata". Jinjina kai kawai hajja keyi.......tanason taji
wanne tanadi da tsari tayi akan hakan?,amma kuma bataso ta zafafa tambaya akai har
maamah ta zargi wani abun,saita tattarewa ranta komai tana jiran lokaci.....domin
kuwa ta san cewa qwace goruba a hannun kuturu ba abu bane me wahala ba.

********Abune sananne a wajen kowa......sharar biki da yawan maganarsa a bakunan
mutanen mu ya ta'allaqa da suna da sharar iyali dangi ko zuri'ar da za'a gudanar da
bikin diyoyinsu. Hakan itace ta kasance akan MUHAMMAD FU'AD JADDA mamallakin JADDA
DIAMONDCHORE RESOURCES.

Daga qishin qishin zuwa samun tabbacin tasowar maganar aurensa,wanda
tabbacin ya samu ne daga yadda farouq musaddiq saddiq da uban family alhaji hamza
kibiya sukewa bikin shiri na gasken gaske.

Daga abokansu saddiq maganan ya fara yaduwa,kafin kace meye wannan
labarin ya fara kewaye kowacce kafar sada zumunta.

Duk da a qurataccen lokaci labarin ya fasu.....to amma labari ne me
dumin gaske daya bawa mutane da dama mamaki.......ya girgiza zukata da zuciyoyin
'yammata da dama......musamman yaran masu kudin da suke kwana su tashi da mutuwar
sonshi......suke kuma da qaqqarfan hope din samun shiga a wajensa kodon matsayi da
mahaifansu ke dashi......walau na dukiya ko na siyasa......ko kuma kasancewarsu
abokan kasuwancin gold da diamond dinsa.

A gefe guda kuma wajen 'yammatan da suka hada duk wata sura kyau da
isa.....wadanda sukasan basu da wani tsanin isa zuwa gareshi......saidai sunyi
mutuwar murus akan mayatacciyar soyayyarsa......abun ya sake bude musu topic of
discussion......qarqashin kowanne posting na labarin bikin dake dauke da qawataccen
IV na bikinsa da aka qawata da zallar ruwan gold,yake kuma wani irin sheqi da
daukan idanun da zai gaya maka bikin ba na yaro bane......tarin cincirindon
comments ne da mabanbantan kalamai masu yawan gaske. Da yawansu suna fatan inama
zasu samu hotunan amaryar?,ina free wedding pics da sauransu,saidai ko daya basu
samu ba face kunji kunji da shaidar zur daga wasu daga cikin commentators na
qarya,sai luguden labba da tsabar kyan IV din bikin da aka kashesu dashi.......sai
videos na lefen da aka samu wadda ta qwarewa gulma da munafurci ta ba bajesu
dashi......abinda ya sake hura wutar tattaunawar.

Sam wadanda ake abin dominsu basusan anayi bama......daga angon har
amaryar ba ma'abota social media bane........idan kaga ta qulla abota da waya to
akwai sabon mission a gabanta........data gama ta ajiye wayar dama layukan da tayi
aikin dasu,wani ta karya ta zubar.......wani kuma sai bayan wani
zamanin.......yayin da oga fu'ad sam sam ayyukansa basa ma bashi damar tunawa da
wani media......koda WhatsApp dinsa idan ka ganshi akai wani abune ya kama da
lallai yake da buqatar hawa yayi a can din.

Koda yana free ma ko yana annual leave dinsa.......yanayin tsaro da
dukka rayuwarsa ke buqata ya sanya ya sake nesa nesa da duk wani harkoki irin
wadannan......don komai nasa a matakin rayuwar daya taka yanzu yana buqatar
privacy.

A daren da ya rage ayyuka sosai......abu daya tak ya rage masa ya
kammala yabar qasar. Yana zaune saman bean bag chair,daga gefansa ruwan wolfberry
ne me dumi yake sipping yana kuma chewing berries din idan sun shigo bakinsa.

Haka kawai yayi shaawar shiga yaga me duniya ke ciki don duka schedule
dinsa na yau ya kammalasu. Da wani personal account yake amfani,wanda bai taba ba
baya kuma wallafa komai a ciki bare ka iya gano waye mamallakinsa. Akwai account na
company dinsa kala daban daban dake qarqashin kulawar ma'aikatansu dake kula da
wannan fannin,so amma ko su baya bi ta kansu tunda yayi imanin zasuyi handling
dinsa ya dace da abubuwan da ya kamata ace an sanya din.

"Ya salam" Ya fada yana miqewa daga relaxing din da yayi cikin bean bag din yana
kallon yadda hotunan katinan daurin auren ke shawagi cikin media. Da farko ma bai
fahimta ba,saidai daga bisani da suka yita jeho masa ire iren posting din.....kamar
sunayi da gayya sunsan shike da alhakin abun har sai da hankalinsa yakai. Shuru
yayi yana sauka gami da furzar da iska daga bakinsa. Yasan aikin mutum uku ne
wannan farouq saddiq da musaddiq,sai amna ta hudunsu.
Kamar jira akeyi ya gani kira ya shigo masa,a nutse ya jawo yana
dubawa......farouq ne,kusan tun randa yace ya zaba kaya bai sake barin wayarsa
yadda za'a sameshi ba sai yau,sai ya katse kiran,ya koma ya laluboshi video call.

Ta signal ya shiga,amintaccen app din da mafi yawan manyan mutane ke
ta'ammali dashi saboda samun cikakken tsaro.

Shigan farko ya daga,fuskarsa ta fito tarwai kaman yana gabansa.

"Hey...." Ya fada qasa qasa yana duban fu'ad

"Don't tell me baka ma taso ba?" Yayi masa tambayar yana tsuke fuska tare da bata
fara'ar fuskarsa

"Zuwa ina kuma dude?.....bakaga abinda kuka jawo ba?,baka ga abinda ke trending
ba?" Ya masa tambayar shima hana dan bata fuska kadan.

Kai farouq ya jujjuya hagu da dama yana yarfar da hannu

"Am asking you seriously fa.....where are you?"

"Ask media users......farouq,you take it very serious fa.....wannan fa auren ba
wani abu bane da za'a damu dashi har haka ba.....ba wani babban abu bane da zai
zama ya yada ko ina ba......it's just a temporary......."

"Kai kasan wannan......mu bamu sanshi ba......in fact ma idan ka matsa da yawa zan
fiddo komai.....just ka dauko hanya gobe kawai......if not,bazan gaya maka abinda
zai faru ba". Datse kiran farouq din yayi,abinda ya sanya fu'ad sakin murmushi ba
tare daya motsa daga inda yake ba. Da alama farouq din a qufule yake dashi
sosai,shi yasa yayi masa abinda yafi tsana kashe masa kira. Ya kasa fahimtarsa
ne,shi sam baiga me yasa zai damu da abinda baida wani muhimmanci ba,baiga abun
daurawa kai hidima har haka ba......already sun gama diban kudin komai da komai
uban da 'yar,daurin aure kuwa ko aike yayi cikin ma'aikatansa za'a daurashi,gidan
da zai ajeta ko ba yanzun ba zai iya bada umarnin tarewarta idan ya gama sabgogin
gabanshi,for god sake zai bata lokacinsa ne da ranshi akai?.



Please Login or Register in order to submit comment