You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ruku'u musaddiq yayi yana cakewa a wajen,ya kama gwiwoyinsa da
hannunsa yana sauke nishin wahala gumi yana fita daga sumarsa zuwa goshinsa.

"Oh shit" FU'AD ya fada yana jan birki,sannan yayi reverse yayo kwana da hanzari
yana dawowa daidai inda musaddiq ya cake.

Baice masa komai ba ya kama wuyansa ya cafka yana tadashi tsaye sosai
saman qafafunsa,abinda ya sanyashi sakin wata qaramar qara yana matse kafadunsa

"Sorry hamma......am really tired wallahi......i try hamma......kusan minti talatin
tunda muka fito muke wannan gudun.....ko doki hamma sai haka"

"Shut your mouth.......malalaci kawai......da wanna halin da dabi'ar naku meye
marabarku da mata?,inajin mun kusa baku jilban da dankwali kuna daurawa ko?". Sosai
dariya taso murqushe musaddiq,amma yasan bai isa ya yita a gabansa ba. Duk wani
training nasa suna shanyewa amma yanzun don ya gaza cikashe mintunan gudunsa shine
ya zama malalaci har zasu fara dauka zani?.

Zanin da ya sake tunawa ya sanya dariyar da yake boyewa ta qwace masa
da gaske,don ba wanda ya hango daure da zani sai saddiq.

Sakin qeyar nashi FU'AD yayi yana watsa masa wani irin kallo da
lumsassun idanunsa dake da wani irin kaifaffen kallo me kashe duk wani zarra ta
mutum

"Are you laughing?,da gaske baka gaji ba......zamu qarasa gida a haka,ko sau daya
kuma ka sake tsayawa kasan sauran......salary dinka na wannan watan zan saka abba
yayi sadakarshi" Ya fada yana gyara doguwar socks din qafarshi daya rufe mass har
gwiwarsa. Kayan motsa jiki ne a jikinsa,amma yadda sukyi masa kyau zata tsammaci ya
sanyasu ne don ado. Sun fidda duk wata qirar qarfi da Allah ya bashi,murdaddun
muscles dinsa zuwa shaffen cikinsa da qirjin yafi cikin dagowa.

"Hamma......wallahi Allah ba abinda kake tunani bane" Ya fada cikin karya wuya da
sanyaya murya

"......Allah hamma kawai musaddiq na hango daure da zani da dankwali......" Sai ya
qarasa fadi yana bushewa da dariyar data sanyashi ya murmusa dole. Dariya yake
sosai yana kuma kallon fuskar fu'ad din.

"Iyakarshi kenan" Ya furta a ransa. Murmushi shine maqurar dariya a wajensa ko yaya
kuwa abu yakai. Kai ya girgiza kawai qasan ransa yana tuno wasu abubuwa na sadiq da
musaddiq din. Suna da wani irin wasan da inda ace shima irin farouq ne baya jin
yaran zasu shuka abun arziqi idan ba shiririta ba. Har kullum abba na jin dadin
jajircewarsa a kansu,don shima din sun maidashi kakansu qarfi da yaji,yayita masifa
yayita masifa amma a banza,maganae mutum guda ce take ratsasu.....zancan mutum daya
ne yake zama daram saman kansu shine zancan muhammad fu'ad.

Bai sake ce masa komai ba sai ya miqe yana zaro wayarsa dake
aljihun wandonsa. Iphone 16 sabuwar qira wanda babban hoton wata kyakkyawar
matashiya ya mamaye ilahirin fuskar wayar. Kyakkyawar bafulatana me wani sassanyan
kyau,cikin kamilalliyar shiga data qarawa hoton da Fuskarta kwarjini. Dududu
shekarunta da suka nuna cikin idanunta da kuma fuskarta goma sha takwas ne.....sha
takwas din da aka soma gangarawa cikin sha tara.

Kalmomin sirri ya sanya ya bude wayar,sannan kai tsaye ya tafi zuwa
ajiyayyun lambobin da basu da yawa cikin wayar. Akan wata number dake dauke da
sunan ABBA NA ya tsaya,ya danna kira sannan ya maidata aljihunsa yana gyara zaman
Bluetooth guda daya dake manne a kunnensa yana bada hasken qyallin wuta time to
time. Sai kuma ya fara takawa a hankali ba tare daya cewa musaddiq komai ba,wannan
ya bawa musaddiq din daman biyo bayansa a nutse can qasan ransa yana murnar yadda
aka haqura da jogging dinnan haka.

"Shi ya dauka kowa kamarshi ne me jikin qarfe da baya gajiya da motsa
jiki......idan na hada qarfi ina zan kaishi" Yayi gulmarsa a ransa yana biye dashi
tare da qare ma bayansa kallo.

Shi kansa yadda yake da ginannun muscles yana burgeshi yana kuma
bashi sha'awa,amma bashi da juriya da qarfin halin da zai building muscles ma
jikinsa kamar nashi.

"Abba ka farka?" Ya fada cikin matuqar nuna kulawa bayan yayi masa sallama.

"Okay gamu nan qarasowa" Sai ya katse kiran ta jikin Bluetooth din nasa sannna ya
dan soma sassarfa yana cewa musaddiq

"Oya.... Mu qarasa gida" Kaman zaiyi kuka hakanan ya taka ya soma bin bayansa.
Kafin su qarasa gidan sai da yaji kaman zai zube,cikin ransa yake ganin gaskiyar
sadiq ashe da yakanyi ciwo ko ya qirqiro uzurin qarya duk sanda ya tasheshi ya
rakashi jogging. Har gwara ku shiga gym room dashi,wannan idan suka faki idonshi
sai su zabi machine daya su haye su kasheshi ko su rage gudunsa sosai.

A hankali suka qarasa hongdae geori cikij estate din dake unguwar. Gida
me lamba ashirin,yayi tsaye yana danna bell yayin da qirjinsa ke dagawa sama da
qasa yana fidda Zazzafan huci daga bakinsa. Ya jiqe sharkaf da gumi,musaddiq kuwa
tuni ya zube saman step biyu dake bakin qofar gidan yana numfashi da sauri da
sauri.

A hankali qofar ta bude,dattijon mutumin nan Alhaji hamza kibiya ya
bayyana cikin wata lallausa kuma kyakkyawar abayar qasar morocco ruwan zuma. Ba
abinda ya sauya tattare dashi sai shekaru da suka fara bayyana kansu a
jikinsa.....bayyana ba me muni ba saboda daular rayuwa da kuma jin dadin da yake
ciki daya zarta ya kuma ninka na shekarun baya ta hannun zaratan yaransa guda hudu
dukka maza.

Da murmushi a fuskarsa kamar kullum yake kallonsa

"Ina dayan me babban suna?" Alhaji hamza ya tambaya saboda idanunshi basu hango
musaddiq ba sam sam.

Da baki ya yiwa abba cunensa,abban ya dora hannu saman baki yana
bushewa da dariya

"Kai......taso dalla.....dama babu me maganinku ai sai me babban suna......tashi
nace mace kawai.....koni nan da shekaru suka fara turamin ina gudun nan,kuma ka
gani da idanunka.....ina zakuyi qwarin damu uwayenku mukayi?,baku da aiki sai hawa
mota sai ciye ciye da shaye shayen banza" Abban ya fada yana wurga hannu. Kai ya
daga da qyar yana duban abban
"Abba wallahi.....bazan iya tashi ba da gaske,qafafuna kamar zasu tsinke.....gudun
fanfalaqi yau hamma ya saka mukayi" Yadda yace gudun fanfalaqin ya tilastawa abba
sakin dariya,yayin da FU'AD ya girgiza kai kawai. Suna ganin iskanci a gidan wajen
sadiq da musaddiq,kullum kaman basa girma,kullum kallon kansu sukeyi kaman qananun
yara.

"Tunda ba zaka tashi ba ai idan wancan qadangare ya shige maka riga ai ka nema
hanyar gida" Wani mugun tsalle ya doka sai gashi a tsaye kyam

"Yauwa.....dan nema ja'iri,zo ka wuce kaji me babban suna" Abban ya fadi yana
komawa ciki fuad yabi bayansa yana dariya qasan ranshi. Har yanzun musaddiq yana
tsoron qadangare kenan tun yarinta?,abun ya dinga bashi mamaki don shi baiga wani
abun tsoro a qadangare ba.

Suna shiga yana biyo bayansu yana dube dube yana fadin

"Wallahi abba ka kusa sakani na saki fitsari a wando......yanzu inda a gaban
nasreen......" Tsaf ya kame bakinsa ba tare daya qarasa ba saboda kallon da FU'AD
ya jefeshi dashi,ya sosa kanshi ya sauya akalarsa zuwa kitchen da kake iya hangensa
tarwai ta falon.

Saman kujera ya zauna a nutse yana warware takalman qafarsa,abban ma
ya koma inda ya tashi ya zauna yana daukar mug tare da ci gaba da kurbar zazzafan
tea din dake ciki.

"Sannu da gida abba" Ya sake fada yana dan jingina bayansa da kujera

"Sannu fuad shugaban 'yan motsa jiki" Abban ya amsa masa da murmushi tare da maida
dubansa ga takalmansa daya cire. Duk abinda ya cire ko yayi amfani ddashi yasan ya
killace shi,zaiyi wuya kaga ya watsar da kaya ko wani abu makamancin hakan. Ya
tabbatar hakan baya rasa nasaba da matsananciyar tsaftarsa da kuma yadda rayuwarsa
ta ginu a shekarun baya,cikin gwagwarmaya da daukar nauyi da lalurar kanshi. Yana
da bala'in tsantsami shi yasa abubuwa da yawa ya gwammaci ya tsaya ya yiwa kansa.
Idan ka ganshi a kitchen yana hada breakfast ko yana dafa tea zaka rantse da Allah
ba shine dan marayan zakin nan ba mamallakin kamfanin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES
ba,wanda jaridu zuwa mujallu kullum kwanan duniya ke zumudi da rububin yin rubutu a
kansa ba domin samun daukakarsu da qaruwarsu. Duk wani rubutu ko labari da wani
gidan tv jarida ko radio zasu fitar akan MUHAMMAD FU'AD tamkar daukaka ce a tare
dasu. Matashin mamallakin kamfanin haqar ma'adanai na diamond ne da makamantansu.
Kifi daya a ruwa da manyan masu sarrafa gwalagwalai da diamond na duniya suke saka
fatsarsu domin kamo kaya daga kamfaninsa saboda inganci da kyansu. Diamond guda
daya daya taba tsinta a sanda yake tsakiyar bautar qasa can cikin jahar kogin
nigeria.


*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 30


Dan bautar qasar da bai wuce sati biyu a camp ba.....wanda ya fita
yawon ganin gari shida shaqiqin aboki amini kuma dan uwansa farouq hamza kibiya.
Haka kawai yayi sha'awar bin daya daga cikin matasan da farouq ya saba dasu a
teburin me shayi wanda duk dare sai yaja fu'ad koda kuwa bayaso,suje su zauna su
sha hira suga yanayin gari da mu'amalar mutanensu. Da fari fu'ad baya so,daga
bisani ne ya sake a hankali bayan da yayi tunanin wannan karin maganar ta bahaushe

"Tafiya mabudin ilimi". Ba yadda zaiyi ya samu ilimin muddin yana nade a camp da
kuma dakin. Abinda yafi damunsa yake hanashi fitar yadda 'yammatan camp din nasu
harma da cikin garin suke da son wasa da wargi gami da son shigewa mutum. Shi kuma
abu guda da yafi tsana kenan kaf fadin rayuwarsa. MACE halitta guda daya da ba
kasafai yake mata uzuri ba a rayuwa.....halittar da yayi amanna ya kuma saddaqarwa
kansa su da KUDI tamkar rai ne da bugun numfashi. Halittar da ya gama karatunta
cewa tafi bawa KUDI muhimmanci sama da komai.....kwadayyar halitta me son
kanta.....mara tausayi kuma mara imani koda akan dan cikinta ne kamar dai MAAMANSA.

Farouq yaso hanashi binsu inda suke haqar a sirrance saboda sanin
tsananin risk din dake wajen. Bawai iya barazanar fadowar rami bisa kan me haqa
ba.....a'ah.....hatta na a tsakaninsu suna iya farde wanda ya tsinta din suyi kashe
mu raba da abinda ka samu.

"Farouq......ragon namiji shike tsoro.....faduwar gaba asarar namiji......ba'a
haliccemu don mu kwanta ko mu zauna iyayenmu su dinga bamu suna mana wahala
ba.....an halicci Muhammad fu'ad don yayi gwagwarmaya ya kuma fuskanci challenges a
rayuwarsa.......na fara gwagwarmaya tun daga sanda na fara fahimtar Muhammadu
sunana ne......na fahimci kuma MAAMA itace ta haifeni......" Ya qarasa maganar wani
abu yana tsirgawa daga tsakiyar muryarsa har cikin qwayoyin idanunsa

"Wai anni bata hanaka zancan maama dinnan ta haka ba?" Farouq yace da fu'ad a
sanyaye. Wani malalacin murmushi ya saki ya sunkuya yana ci gaba da daura boot din
qafarsa da kyau. Ta yaya MAAMA zata bar zuciyarsa wai?,ta yaya?har abada sai randa
qasa ta cike idanunsa.

"Na shirya zan wuce sai na dawo" Ya fada yana miqewa tare da zube hannayensa a
aljihun wandonsa yana duban farouq. Harara ya watsa masa sannan ya miqe da hanzari

"Ina zan barka ka tafi kaje ka bace ka jamin jarfa a wajen abba......qafata
qafarka.....idan ma zamu bata mu bata tare" Yayi maganar yana miqewa.

Miskilin murmushinnan nasa ya saki ya juya yana kada kai. Ya sani
shine dai kawai a gaba kafin abba da yake qorafi akai,kawaidai bazai iya barinsa ya
tafi bane ya barshi,wanda wannan daya daga cikin danqon qauna da 'yanuwantaka dake
a Tsakaninsu.

Yana shiryawa yana mita har ya kammala suka sulale suka fice daga
gidan da aka musu masauki ba tare da kowa ya sani ba.

"Ni bansan me zakayi da wata mahaqa ba.....dukkanmu abba jira yake mu kammala
wannan service din ya bude mana namu kasuwancin"

"Ta yaya zaka zama cikakken dan kasuwar da yasan daraja da kimar dukiya baka iya
gwagwarmaya ba?.kana daga zaune ba tare da ka tara komai ba?" Fu'ad ya masa
tambayar yana kallon hanya kawai ha tare daya kalli farouq din ba

"Gwagwarmaya cikin wadannan qedarun?,don kawai Samuel ya gaya maka za'a je da
kai?,suna da hadari fa fu'ad?" Murmushi ya kuma saki hankali kwance,har yanzu kuma
bai kalli farouq din ba ya sake bashi amsa

"Muhammad fu'ad dan arewa.....ya fisu hatsari.....zaka gane hakan idan sukayi
yunqurin yin wani abu". Maganarsa ta tabbata kuwa a wajen farouq.

Tun isarsu gurin komai ya fara bayyana. Da wani irin kallo ayarin suka
fara binsu saboda ganinsu baqin fuska kuma 'YAN AREWA dake yara yaran hausa. A haka
aka soma tafiyar har zuwa kebantaccen wajen da suke haqar ba dare ba rana don samo
ma'adanai. Samuel shi ya dauki dukkan wani risky ya shige gaba aka barsu har suka
isa gurin cikin wadanda aka aminta da shigarsu wajen.

Duk inda fu'ad zai motsa farouq yana biye dashi,sam wajen shi baiyi masa
ba,hakanan a tsorace yake da wajen,shi sai ya zamana kamar me gadin fu'ad ne a
wajen. Duk wani motsi da za'a yi a wajen ko wani da zai tunkarosu hankalinsa yana
wajen.

A hankali ya tura kansa ramin da fu'ad ke ciki wanda yayi zurfi

"Mutanen nan fa hankalinsu a kanmu yake,duk wani motsinmu suna ankare dashi"

"Karka damu" Kawai yace dashi saboda wani abu daya fara hanga wanda ya dauki
hankalinsa matuqa.

"Farouq" Fu'ad ya kirayeshi da wani sauti me jan hankali wanda yaja
hankalin wanda ke ramin daura dasu ya kumayi tsai yana jiran jin dalilin kiran.

Tura kansa farouq din yayi yana cewa

"Menene"

"Na samo.....na samo" Ya fada da wani irin excitement,yayin da zuciyarsa da
kwanyarsa suka cika da mamakin samun abinda bai taba zaton zai samu ba koda kuwa a
mafarki. Har a qasan zuciyarsa ya gwada zuwa wajen ne kawai don samun experience da
karantar yanayin yadda irin rayuwar yake.

"Duba ka gani farouq" Ya fada yana miqo masa. Farouq din da hanzari ya dira ciki
yana toshe bakin fu'ad

"Keep quit fu'ad.....ka tono masifa" Ya fadi a tsorace. Da wani kallon mamaki yabi
farouq din

"Kaman ya?"

"Kamar yadda ka sani.....kowa dake nan wajen abinda yake zuwa nema kenan kwana da
kwanaki.....kana baqo wanda aka yiwa alfarma.....zuwan farko kayi kacibus da abinda
yake dukkansu shine burinsu?. Akwai shugaba a cikinsu wanda duk wanda ya samo sai
yabi qarqashin umarnin shugaba......zai kuma danqashi a hannunsa....." Tsaki fu'ad
yaja saboda dokokin rainin wayo da yaji farouq yana karanto masa wanda shi baisan
dasu bama,don ya fishi zama da hira da Samuel

"Su sukamin wahalar?,ko an gaya maka nazo nan dinne don na yiwa wani qaton zindiqin
arne aiki?.....let's go mu wuce gida" Ya fada yana kama ramin tare da nufar hanyar
fitowa.

Sanda yayi tsalle ya qarasa fitowa baima lura da wadanda suka kewaye
ramin ba,har sai daya gama karkade jikinsa yaji sadiq daya fito daga bayansa ya
zungureshi.

Lafta laftan yare masu mummunar siffa tun daga halitta zuwa zuciya.
Mutumin da alamu suka nuna shine shugaban yana tsaye a gaba. Ya sake matsowa gaba
kadan ya miqawa fu'ad hannu..

Sarai ya fahimci abinda yake nufi,amma yadda yake kallonsu da dukkan
wani motsi nasa cikin izza da nuna isa ya sanyashi jin har cikin ransa bazai taba
iya bashi abun ba. Ballantana abinda yake wahalarsa kuma guminsa ne. Ko daya babu
me haqqi a ciki bare yayi tunanin cinyewar zai zama laifi har a wajen Allah.
"Ban gane ba" Fuad din ya furta cikin dakiya da jarumta

"Ka miqo diamond din daka samu aka ce...!" Daya daga cikin wadanda ke daura da ogan
ya furta murya a kausashe yana sake matsowa dab da fuad din saboda nuna masa
tsananin buqatar abun da suke da,da kuma nauyi da girman abinda yake dauke dashin.

Cikin qasa da second biyar ya gama fahimtar motsi da niyyar kowa.
Tabbas!.....tabbas babu abinda yafi dacewa dasu muddin yana da buqatar tsira da
wanann abun face tserewa

"Ka shirya farouq.......ka shirya gudun tsira da rai.....ko mu ko su,ka qarfafa
zuciyarka da gangar jikinka" Ya furtawa farouq qasa qasa tare da damqe hannunsa da
kyau.

Kaduwa sosai farouq yayi da abinda yaji fu'ad din yana fada.....yasan
halinsa muddin ya fadi sai ya cika.....amma kuma abinda zasu aikata din mugun
ganganci ne da zai iya zama ajalinsu.

Bai gama sauke wannan tunanin ba yaji qarar wani abu timmmm sannan
yaji an finciki hannunsa. Sanda zai duba sai ya samu fuad dinne ya kaiwa ogan nasu
mummunan naushi har sai da yakai ga zubewa qasa war was,da wannan ya janye
hankalinsu suka tsallakesu,saidai ko taku uku basuyi ba aka samu wadanda suka rufa
musu baya bayan fusatacciyar tsawar da ogan nasu ya buga musu wadda har yanzu yana
zaune a qasa

"Catch them!!" Ya fada qarajin hasaso asarar dake tallafe dashi tare da tsoro da
razanin rasa abinda yake tamkar shine cikamakin burin rayuwarsa.

Wani irin gudu tamkar a indian film fu'ad ya dinga yi,abun har yaso
yafi qarfin farouq banda shi dinma yaci sunan me sunan.

"Mu tsaya fu'ad.....harbi sukeso su fara"

"Wa ya gaya maka ana gudu da waiwaye?......just run!!,run kawai.... Kada ka sake
waiwayawa". Ganin kamar farouq din ya fara karaya ya sanyashi yin wani juyi ya
maida farouq din gaba shi yana biye dashi.

Da gaske dai suka fahimci zaratan samarin 'yan arewan guda biyu na
niyyar kufce musu,sai kawai suka fara harbi,harbin da ya gigita farouq qwarai da
gaske ya kuma dinga kiran sunan fu'ad akan su maida musu abinsu.

"Basu isa ba....don ba abinsu bane,arziqi ne na ubangiji daya shimfida a qarqashin
qasa saboda bayinsa,ba don su kadai Allah ya ajjiyeshi ba" Ya fada a zafafe cikin
yanayin gudun yana sake fusgar hannun farouq da kyau. Wani irin samfurin gudu da
fu'ad din keyi riqe da hannun farouq sai daya zama abun kallo a wajen farouq din.
Bai taba tsammatar iyawa ko qwarewa haka a tare dashi ba wajen sanin kurdawa
tsakanin manyan dutsuna da qananunsu ba sai a sannan. Bayan shafe dogon lokaci suna
fafatawa Allah ya basu nasarar kufce musu

"Park zamu wuce mu kwana a can daga can muyi gida......ba park na kusa da nan ba,ta
gaba da nan" Fu'ad ya fadi yana kallon farouq

"Ya zamu bar camp kuma bamu dauki komai namu ba......sannan kuma......"

"Kana tunanin sun qyalemu ne?,kana zaton idan muka koma can din zasu barmu mu kwana
da ranmu?" Fu'ad ya tambayi farouq wanda da alama baisan girman ta'addanci irin
nasu ba.
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*

*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*

*_KAMAR SU_*

Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes

*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*

________________________

*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks:@Huguma*

https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997

PAGE 31
___________________________


Wani murmushi ya saki

"Ai basu ba,ko jamaa da muke tare dasu sukasan abinda muke dauke dashi sunanmu
matattu......maganar diamond da gold akeyi farouq.......kasan nauyi da girman
ma'adanin dake jikinmu?......mutanen nan sun wuce duk sani da tunaninka.....ni
kaina da na yarda mubi Samuel da shirina,na san kuma cikin su waye zan shiga,kaine
nake zaton bakasan irin girman wajen da muka shiga ba.....banda saa tana tare damu
bamu isa mu shiga wannan wajen bama bare akai ga samun abinda muka samu kuma har mu
gudo lafiya lau dashi......daga yanzu har zuwa sanda zamu koma qasarmu rayuwarmu na
cikin hadari......take care dude...." Ya fada yana bugun kafadar farouq da ya gama
mutuwar zaune.
Bin fu'ad kawai yakeyi da kallo yana mamaki. Yasan girman hatsarin
fiye dashi amma yayi kaman bai sani ba?,ko a yanzun wannan uban wahalallen gudun
ceton ran da sukasha shi kaman ma baiyi ba?. A yadda ya sanshi da I don't care
manner da rashin shiga abubuwan rayuwa sosai bai taba zaton ya iya daukar risk da
tarar aradu da ka ba sai a yanzu.

Tun daga tashar da suka samu mafaka sukasan lallai an baza nemarsu,a
daren suka haye motocin kaya dake lodin arewa suka wuto gida.......wanda sai daga
bisani abba yasan komai.

Yayi fada yayi fada kaman zai ari baki......ya kuma yi musu fadan
da bai taba musu shi ba,musamman me babban suna da yake girmama sunansa yake kuma
qaunar yaron har cikin ransa. ANNI ce ta sanya baki aka samu ya lafa sannan aka
fara tunanin yadda zaa yi da abinda ya haqo din,tunda ya riga ya shigo hannu ba
batun ace za'a maida musu.

Bisa dukkan dokoki da tsare tsare kan tsaftatacciyar hanya aka tsara
komai ya zama dukiyar da a yanzun suke juyata shida farouq dinsa. Abban kuma ya
zame musu jagora madubi.....ma'adanin kuma ya zama shine kasuwancinsu.....babbar
masana'antar karbar haqaqqun ma'adanai su tace su gyarashi su fiddashi xuwa manyan
qasashe,irinsu china,south Korea japan UK da manyan qasashen dake hulda da
cinikayyar ma'adanan qasa masu tsada da daraja.

A nahiyar africa JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES ya zama kamfani na daya
da qasashen ke rububin karbar kaya a hannunsu bayan doke Coregeo mining company din
da yayi. Kamfanin daya jima yana murza zarensa da kyau,sai gashi rana tsaka JADDA
DIAMONDCHORE RESOURCES yazo yasha gabansa ta ba zata,al'amarin daya haifar da takun
saqa me girma a zuciyar kamfanin. Duk da fu'ad yasan da wannan......amma ya dauka
normal competition da kishi ne da kan iya faruwa tsakanin kowanne kasuwanci,saidai
ga mamallakin kamfanin JOE abun ba haka bane.

*_D A W O W A_*


Dubansa abba yayi bayan ya aje mug din hannunsa

"Kwanaki nawa ya rage mu tafi ne me babban suna?" Zama yayi sosai yana goge gumin
fuskarsa da dan qaramin towel din da magaji(hadiminsa) ya miqo masa.

"Ba zamu wuce sati daya ko kwana biyar ba abba,hankalina yana kan
anni......jikintan nan ya fiya matsawa da yawa" Yayi maganar alamun abun yana
tabashi ya bayyana

Please Login or Register in order to submit comment