You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akyi mata,sai a sannan zaa
san abinda ya kamata ayi mata,amma yanzun xan sake saka mata ruwa don kada jikinta
yayi rauni da yawa".
Yana tsaye a gefe ranshi a jagule ta gama mata komai sannan ta
fice,koda ya matso sai ya samu har bacci yayi awon gaba da ita. Ajiyar zuciya ya
sauke,yana jin kamar ya dawo da ciwon jikinsa,agogo ya kalla.....yau din juma'a
ce,yanason samun sahun gaba gaba a masallacin ma'aiki,duk da zuwa yanzun ma yasan
ya makara,baya ga haka akwai wani al'amari me muhimmanci da zai aiwatar a can
din,wanda bayajin akwai abinda zai sanyashi jinkirtawa ko dakatawa a wannan ranar
ta juma'a. Rana ce mafi dacewa daya aiwatar da al'amarin. Idan yace zai koma gida
ya shirya ma ya bata lokaci,don haka ya daga waya kawai ya kira farouq.

"Ka turo saddiq ko musaddiq......ina buqatan Friday attire please".

" Ina kusa da hospital dinma......but bari na koma na duba maka kayan...."

"Thanks dude"

"Don't mention it....ya jikin nata?" Dubansa ya mayar kanta sannan yace

"Alhmdlh....she's sleeping,inaso naje mosque ne na dawo kafin ta farka"

"Zaa kula maka da ita dude....kada ka damu,dukansu na barsu suna shiryawa zasu taho
nan"

"Alright" Ya fada a taqaice yana ajiye wayar.

Ba jimawa farouq ya qaraso,dauke da wata leda me kauri. A nan parlor din
dakin ya zauna,shi kuma ya wuce ciki inda gadon sabreen din yake.

Cikin qanqanin lokaci ya shirya,Moroccan jallabiyya ce fara tas me
asalin tsada me adon gold din zare,sai zagayayyar hular nan irin ta larabawa wadda
set ce tare sukazo da hular da loafers din dake ciki iri daya. Wani irin sassanyan
kyau ya aje,saika dauka balaraben Morocco dinne,ya matsa inda take kwance tana
baccinta kaman ba abinda ke damunta,ya sunkuya yayi kissing dinta sannan ya fara
takowa yana fitowa.

Tun bai qaraso parlor din ba yaji muryar farouq dana likitan,yana
tsaye sanye da farar lab coat dinsa suna hira sama sama da farouq din. Fuskarsa
sake ya miqawa fuad hannu cikin sanin darajar dan adam da iya aiki,shima ya bashi
suka gaisa,sannan ya fara bude takardun hannunsa.

"After conducting the necessary tests,I'm pleased to inform you that your wife is
pregnant...." Likitan ya fada da murmushi a fuskarsa.

Karon farko da yaji ya koma kaman dan koyo a fannin turanci,kaman ma
baya gane komai. Ya zubawa likitan idanu yana buqatar qarin bayani,muryar farouq ta
dawo dashi hayyacinsa.

"Alhamdulillah......ya rabb lakalhamd.....alhamdulillah......muna godiya sosai
likita" Farouq daya kasa zama ya fada yana kama hannun likitan da kyau ya riqe
cikin nasa.

"Allah ya inganta......ya bata lafiya me dorewa.....ina tayaku murna" Abinda
likitan ya fada kenan yana murmushi,sannan ya miqawa farouq takardan gwajin yana
masa bayani.

"Idan ta tashi a bacci za'a qarasa bata duk wani treatment daya kamata"

"Mun gode" Farouq ya sake maimaitawa yana karbar takardan likitan ya juya ya fice.

Ganin gaba daya fuad din ya zama wani statue ya sanya farouq kai masa
duka

"Dude......kayi nasara.....ka jefa qwallonka a raga daidai" Sai a sannan ya tattaro
kalaman bakinsa da qyar

"Am going to be a father?" Ya tambayi farouq cikin neman bayani gamsashe.

"Yes dude.....bakai kadai ba,harda ni,anni zata zama grandma for the first
time......zamuyi yaro ko yarinya dukanmu......" Bai jira farouq ya kammala ba yayi
masa wata wawiyar runguma hawaye suna kubce masa.

"Ya rabba.....antal kareemul lazi ya yaraddu sa'eelan,la'ilaha llla antar rahmanir
raheem......shukran ya Allah,shukran" Sai muryarsa ta karye,ya dora fuskarsa saman
kafadar farouq kuka nason qwace masa.

"Bansan wannan jarumin muhammadun da saurin kuka ba.....duk da na lura sabreen ta
maidashi baby da gaske" Farouq ya fada shima zuciyarsa tana raunana amma yana
qoqarin bawa kansa qwarin gwiwa. Kansa y a daga yana riqe farouq da kyau,yanata
qoqarin masa magana amma ya kasa,sai kawai ya jijjigashi yana kada kai sannan ya
taka da sassarfa yana komawa dakin.

Baccinta take kaman yadda ya fita ya barta,ya sake sumbatarta a goshi
da labbanta,a hankali ya furta

"Kece duniyata.....na gode,na gode" Sai ya rufe mata qofar yana komawa parlor din
da sauri.

"Zanje nayi sallah masallaci......zan kuma aiwatar da wani abu,idan zakaje mu hadu
a hanya" Ya fada yana saka hannu ya kwashe takardun ya zubasu a aljihunsa sannan ya
fita da sassarfa bayan ya sanar musu su aika me kula da ita zaije juma'a ya dawo.

Ba inda yakejin ya kamata yaje ya juye farincikinsa da godiyarsa ga
Allah irin cikin rauda.....ya godewa Allah daya samu wannan labarin a irin wannan
wajen,banda haka ya tabbatar sai yayi qaramin hauka saboda farincikin yayi masa
girman da zuciya ba zata iya daukarsa ba ita kadai.


*_BAYAN AWA DAYA DA RABI_*


*_B A Z A T A_*


Anni,amna,musaddiq,saddiq dukkaninsu suna zaune a parlor din dakin
asibitin bayan sun shiga sun dubata tana bacci sun fito.

Huda haneefa nadra da kuma momma bahijja sune kadai daga cikin
dakin,suna taba tasu hirar kadan kadan wadda ke cike da farincki da qaunar juna.

Maamah dake zaune kallon kowa takeyi kawai daya bayan daya,yanayin
yadda taga sabreen a yanzu ya soma sauke mata duk wani qwarin gwiwa da takejin tana
dashi akan ba ciki bane a marar sabreen din. A shigarsu ta dazu ta gama qare mata
kallo da kyau,ba abinda idanunta suka hango mata kuma banda dashewa irin ta me
yaron ciki.

Iya wannan abun kawai data gani ya sanya gumi ya fara yanko mata,duk
da yadda zuciyarta keta qarfafata tana mata romon bakan cewa ba ciki bane.

A yau din batajin zata matsa daga asibitin nan ba tare da an gwada
yarinyar nan ba anga uban abinda yake damunta ba.

Sake jan qaramin tsaki tayi jan qasa qasa tana gyara zamanta. Gaba
daya zaman wajen takeji ya gundireta,daidai lokacin fu'ad ya turo qofar dakin da
sallama a bakinsa ya shigo.

Sannu da zuwa dukkaninsu suka fara masa banda maamah dake jifansa da
wani irin kallo. Saddiq musaddiq da amna dukka suka gaidashi da tambayar me jiki,ya
amsa musu cikin kulawa kafin ya qarasa gabansu anni yana gaidasu.

Da qyar maamah ta amsa,ta bishi da kallo sanda yake miqewa zai wuce
ciki

"Zo nan muhammadu" Ta kirashi,sai ya dawo ya samu waje yana zama kujerar dake
fuskantarta.

"Wannan ciwon da yaqici yaqi cinyewa ina ganin ya kamata a auna yarinyar nan asan
me yake damunta,kada mutane suna zamansu lafiya taje tana yawo da ciwo tana yada ma
mutane tunda gata ga yadda take a baya". Sosai maganar maamah ta sokeshi,ya kuma
fahimci inda ta sanya gaba,anni kuwa sai da tayi da gaske ta iya controlling kanta.

Idonsa ya lumshe kana ya budesu ya gyara zamansa.

"Ba wani ciwo da ameenatu take dauke dashi a jikinta......tunda nine mutum na farko
dana fara karbar mutuncinta na 'ya mace......ciwonta na yanzun kuma nine
silarsa.....ga bayanin nan a rubuce" Ya fada yana zaro takardar,sai kuma ya dakata
yana dubansu.

"Naji dadin ganinku a tare gaba daya" Ya fadi yana sake zura hannunsa a aljihun
rigarsa.

Dollars dubu biyu ya fiddo sabbi kar a miqe,ya miqawa maamah takardar
ya kuma miqawa anni kudin.

"Abba......alhaji hamza kibiya ta hannuna ya karbawa musaddiq mahmud jadda auren
amna......bisa sadakin dala biyu biyu lakadan ba ajalan ba......ta hannun wakilinsa
abokinsa alhaji muhyidden kibiya da tarin shaidu cikin masallacin annabi muhammad
SAW,bisa yarjewar waliyyansu ni muhammad fu'ad jadda da kuma abba wato alhaji hamza
kibiya"......


TURQASHI!......FU'AD.....NACE ME JADDA?,WANNE IRIN MATCH KA TARO HAKA?,KO TAKARDAR
DA MAAMAH TA WARWARE BAKA BARI TA GAMA DUBAWA BA?.

TO NIDAI JAMAA WANNAN FADAN YAFI QARFINA
NAYI NANπŸ˜‚πŸ˜‚



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³
π™‹π˜Όπ™‚π™€ 115
_____________________________
_kin dade kina cizon yatsa kan yadda ake kacalcala suturun yaranki da dinkuna
marasa ma'ana?_

_HUGUMA na miki albishir da wajen zazzafan dinki na MS KIDDIES WEARS,irin dinkunan
yaran da kike gani a Instagram TikTok suna burgeki kuma bakisan inda zakikai ayi
miki ba ko kina tsoron tsada_

_Zafafan dinki na gayu da ado kiga yaranki sun fita dagwas dagwas_
_ready

_MS KIDDIES na nan kano gwammaja_

*TRUSTED AND TRUSTED mun gwada mun gani*

_Maza tuntubeta a nan_

+234 708 865 2858

Ko Instagram account dinta

https://www.instagram.com/ms_kiddies_wers_by_nafs?igsh=MTljZWQwM2FsaXlxaA==
______________________________


115



Dukkanin wani da yake numfashi a wajen saida jinin jikinsa ya daskare na
wucin gadi,qwaqwale da yawa suka dakata da aiki na wasu mintuna,yayin da idanuwa
sukayi warwaje a kansa. Kowa dubansa yake d wani irin madaukakin mamaki da tarin ba
zata,dukkaninsu kowa kwanyarsa ta kasa fahimta ko sarrafa maganarsa.

"Mem.....me kake cewa fu'ad?" Anni mutum qwaya daya da tayi qarfin halin sake
tambayarsa tana jin yadda jinin jikinta uske tsinkewa. A nutse ya dubi annin
nashi,yana da qwarin gwiwa da zato me yawa a kanta,don haka kansa tsaye yace.

"Na aurar da amna ga musaddiq cikin masjid nabawi bisa shaidu da wakilai da sadaki
dala dubu biyu" Sai a sannan kwanyar wasu daga ciki ta harba ta kuma dawo da
aiki,ciki harda amna.

Wani tsananin tsoro taji yana shigarta,ta shige jikin anni tana buya
a bayanta gami da cukuikuyeta,idanunta kuma suna sauka kan fuskar maamah. Wannan
fuskar da take bata wani tsoro haka kawai,fuskar da batason kallonta saboda duk
wani yanayi da alamu na rashin wanzuwar alkhairi tattare da ita tana ganinsu......a
yau mamallakiyar wannan fuskar itace a mazaunin surukarta?.

Shi kuwa musaddiq kama hannun saddiq yayi ya riqe da kyau yana
qoqarin tuna maganganunsa da hamman masa mintuna ashirin baya da suka wuce kafin ya
shigo cikin asibitin. Abubuwa biyu ke masa kai kawo suna gwarabkiya cikin
zuciyarsa,farinciki da kuma fargaba da wani sofane na tsoro dan kadan. Kalaman
bakin maamah wani irin daci da dafi ne dasu wanda ya kasa sabawa da jinsu,baya
qaunar komai ya hadashi da ita alkhairi ko sharri,dadi ko akasinsa.

Idanu kawai anni ta zuba ma fu'ad tana jin tsigar jikinta na tashi.
Wanne irin tashin hankali ne haka fu'ad din ya rakito mata tana zaman zamanta tana
lallaba tsufanta?. Wacce masifar ce ke shirin wanzuwa?,meye kuma zai afku gaba ga
amnanta?.

"Allah ya sanya alkhairi......yasa anyi a sa'a" Lafuzzan suka fita daga bakin
maamah da tayi qoqarin ware idanunta daga qanqancesu da tayi.

Ba wanda kalamanta basu bawa mamaki ba.......kaman yadda suka janyo
hankalinsu ga fuskarta wadda ta maida idanunta kan takardar hannunta tana qoqarin
hana zuciyarta tsananin bugun da takeyi,tare da fatan gumin dake yanko mata ya
tsane jikin atamfar jikinta ba tare da kowa ya gani ba.

Abu guda daya data sani shine......tabbas fu'ad ya siyawa amna
tikitin salwantar rayuwarta......don bataga ta inda zata bari itakam da ranta da
lafiyarta ta hada jini da alhj hamza kibiya ba..... Idan fu'ad baiyi wasa ba a
wannan karon,zata rufe idanunta tayi hukuncinta kan me uwa da wabi......zata mance
da alaqar dake a tsakaninsu tunda har ya iya mancewa da matsayinta a wajensa.

Saddiq musaddiq harma da amna sai lafazin maamah din ya sanya suka
fara jin abinda ke ransu yana sassauta,wanda sam ba haka bane a qirjin anni da
fu'ad. Wani duba sukaci gaba dayi mata,kowannensu yana son karanto ainihin ma'anar
maganarta.

Sun riga da sun sani.........banza bata kai zomo kasuwa......hakanan
kowa ya tuba don wuya to tabbas babu lada.......ba haka kawai maamah zata bada amsa
ga lamari me girma irin wannan ba......ba haka siddan zata miqa wuya ga al'amarin
daya fado bagtatan irin wanna ba.....TABBAS AKWAI WATA A QASA.

Lokacin da idanunta suka kai kan conclusions na gwajin sabreen din
sai ta fara qanqance idanunta a hankali,ji tayi kaman debi yaji an watsa mata cikin
idanunta kafin a hankali taji kaifin ganinta kaman yana raguwa.

"Ciki?,sati uku?" Tambayar data samu daman motsa labbanta ta yiwa kanta da kanta
kenan.

Iskar dakin taji tana mata wahalar shaqa,kamar babu isashiyar oxygen
dake wulgawa ta wajen,takai hannunta wuyanta tana janye mayafin data yafa waiko
yana cikin abinda ya jawo mata qarancin iska,still sai taji ba abinda ya canza.

Da gaske iska ke neman mata kadan,wannan ya sanya ta soma jan iska da
qarfin gaske tana aikawa hunhunta don ta samu taci gaba da numfashi,yayin da
ilahirin jikinta ya soma rawa kadan kadan.

Musaddiq ne ya fara ankara da hakan,don fu'ad tuni ya soma takawa
xuwa dakin da sabreen take don kaucewa kallon tuhumar da anni ke jifansa dashi.
Baida matsala da duk wani tuhuma na maamah ko kuma kalar kowanne qalubale daga
gareta,damuwarsa daya yadda annin dama zata karbi abun,ko ita dinma ya shirya
mata,don bayajin akwai wani abu guda daya daya dace yayi sama da wannan din.

"Lafiya?.....kaman numfashinta baya kaiwa" Anni data iso gurin ta fada tana duban
hannunta wanda takardar gwajin da fu'ad ya bata ta sulale ta fadi a qasa.

Yanayin sautin anni ya sanyashi dawowa da baya,yadan daga qafa yana
qarasowa wajen,sai yayi saurin matsawa wayar dake ajiye a dakin don neman daukin
likita ko nurses ya soma kira.

Minti guda kacal sai ga mutum biyu tare da likita sun qaraso,saman
wheelchair aka dorata sannan suka turata xuwa dakin da yake daura da wannan.

Dukkaninsu suna farfajiyar dakin daga waje,suna jira suji bayanin da
likitan zai fito dashi. Duk bayan sakanni sai anni ta daga idanu ta dubi fu'ad,gaba
daya ya gama warware mata zaren tunaninta. Wannan wani abune nashi na daban,tsahon
zamanka dashi zaku iya qareshi ba tare da ka iya fadin gundarim halayensa ba gaba
daya,yakan zo da abubuwan da hankali da tunani basu kawosu ba,yana da bada mamaki
irin hakan,saidai bata taba kawowa zai iya aikata qunar baqin wake irin wannan ba.

shima kansa ya sani,duk wani kallo da anni take masa yana cure ne da
mamakinsa,saidai ya sakawa kansa wannan dakiyar da juriyar da wani irin basarwa,don
haka ko sau daya yaqi kallon anni,saidai yasan shi take kallo ta gefan idanunsa.

Basu wani jima ba suka fito,suka qaraso gaban fu'ad din.

"Ba wani abu bane me tsanani,kawai ta shiga shocked sosai daya sanya jininta hawa
lokaci guda......irin wannan case din yana iya jawo mutuwar barin jiki ko bugawar
zuciya idan yazo da akasi.....zuwa yanzu dai ita Allah ya tsallakar da ita,saidai
kuma jininta yahau sosai,an mata allura ya kuma sauka alhmdlh,nan da awa daya ma
zata iya tafiyarta gida.......amma fa sai tana kiyaye saka bacin rai da damuwa a
ranta".

"Na gode Dr" Fu'ad ya fadi yana bawa Dr hannu sukayi musabaha ya wuce.

Musaddiq ya kalla sai ya taka zuwa cikin dakin saddiq ma ya bishi.
Idonsa yaketa qoqarin kawarwa daga annin don kada su hada ido ya soma takawa zai
shiga ya duba maamah din amma sai sautin annin ya katseshi.

"Ka kyauta" Ta fada kai tsaye,abinda ya sakashi dakatawa daga tafiyar da yakeyi
kenan. Shuru ya ratsa na wasu mintuna,sai kuma ya dawo da baya a nutse ya tsaya
gaban annin.

Hannuwanta ya riqe yana zaunar da ita daidai sanda take fadin.

"Kaga irin abinda ka jawo ko?" Zame takalmin qafarsa yayi ya zauna sosai a gabanta
ba tare daya damu cewa marbles bane a wajen.

"Ban jawo komai ba anni.....kuma komai bai faru ba,ko ba wannan maganar irin wannan
ranar irin wannan lokacin yana dab da faruwa da maamah....... Tunda muka tashi bamu
san wani abu farinciki ba sai a sanadinku.......musaddiq ya rasa abubuwa masu yawa
tun yana yaro......yanzun kuma a sanadinta sai a haramta masa abinda yake buri yake
muradi yake kuma so?,bayan a baya ya rasa abinda yake buri da muradin kuma duka ya
haqura?" Tambayar tasa tadan taba annin,saidai duk da haka sai takejin kaman bai
kyauta ba abinda ya yiwa maamah,ko ba komai ita ta haifi musaddiq din ta kawoshi
duniya.

Ta bude baki zata sake magana yayi caraf ya riqe hannunta sosai,abinda
bai taba yi ba. Idanunta ta daga tana duban nasa idanun,wadannan alamun bacin rai
mai tsanani din sun bayyana sosai cikin idanunsa,alamun ranshi ya motsu sosai.

"Kina tunanin ga musaddiq......zan bari amna ta auri wani a waje koda baice yana so
ba?,wanin da bamu da tabbas a kanshi?,wanin da ban isa na hukuntashi ba idan ya
cutatar da ita duk yadda muke sonta kuwa?.........Karki sake cewa komai anni don
Allah na roqeki,bakinki kada ya sake furta komai a kansu idan ba fatan alkhairi
ba......indai har yanzu kin yarda kina kuma ji a ranki ni da musaddiq 'ya'yanki
ne.....amna qanwata ce halak malak kamar yadda musaddiq yake....to karki sake cewa
komai sai fatan alkhairi.....ko meye zai faru.....ko menene zai taso anni na roqeki
ki saka idanu.....nike da alhakin hakan kuma nine zan dauka". Gaba daya ya gama
kashe mata jiki,ya kuma kashe duk wata kalma da yake da yunqurin fadi. Fu'ad din
wani mutum ne na daban,ajiyar Allah ne,yana da kaifi wajen komai nasa,kaman yadda
nutsuwa da dattako ta mamaye dabi'arsa gaba daya.
"Kai da abba kuka hada baki ko fu'ad?" Anni tayi tambayar a sanyaye. Wani dariya ya
tasowa fu'ad,yayi qasa da kansa yana murmusawa kafin ya daga kansa ya sake maidawa
ga annin.

"Ba ruruwan abbanmu.....kada ki sashi a ciki anni,aikin Muhammadu ne,ni kadai na
kitsa abuna.....saboda asara ce babba ace ba wata dangantaka da alaqa ta dindindin
tsakaninmu da ku anni.....kun gama yi mana komai a rayuwa....kun bamu ruhi me
tsafta.....ruhi bana rai ba.....ruhi na dabi'a addini tarbiyya da ilimi da kowanne
dan adam yake da buqatarsa........ba wata sakayya da zamu iya yi muku sama da
wannan" Shuru sukayi dukkaninsu,jinjina kai kawai anni takeyi. Duk duniya ba wanda
zai kaita son hada jini da musaddiq......to amma ita fitina ba abar so bace.

"Amma anni......me kike tsoro ne duk da tarin jarumtar da kike da ita?" Ya fada
cikin salon tsokana don yadan bata wani nutsuwar zuciya.

Harara ta jefa masa tana dan murmushi kadan kafin ta amsa masa

"Kafi kowa sanin ameenatu ba raguwa bace.....ameenatu ba matsoraciya
bace.....fitina ce kawai ameenatu bataso,ita din me son nutsuwa da kwanciyar
hankali ce".

"Na shaida hakan" Ya fada yana murmushi sannan ya sakar mata hannunta.

Miqewa tayi tana cewa

"Muje na dubata.....saika samu kadan zauna da ita,ka kwantar mata da hankali ka
fahimtar da ita har ta samu nutsuwa". Murmushi kawai ya saki yana zube hannayensa a
aljuhun rigarsa. Anni tana wasu abubuwan kamar batasan halin maamah din ba,kamar
ita din baquwa ce a dabi'unta.

A zaune suka sameta saman gadon,har sun zare ruwa da alluran da suka
saka mata. Ga oxygen din da suka cire mata a gefe. Dakin shuru,banda qarar ac
bakajin komai,musaddiq da saddiq na zaune saman kujera suna zaman kurame su da ita.

Kallo daya tayi musu shida annin ta dauke kanta daga sashensu,don ci
gaba da kallon nasu bazai iya Haifa musu da me ido ba,hasali ma jarumtar da take
jin zatayi tsaf zata iya kwaranyewa tayi nata wajen.

Shigowarsu ya sanya musaddiq da saddiq ficewa,don dama shikam musaddiq
zaman ya gundureshi,hanya kawai yake nema.

"Ya jikin?,Allah ya sawwaqe ya qara afuwa" Ido maamah kawai ta runtse,batason jin
sautin muryar anni sam sam. A halin da takeso ta ganta kenan,ta kuma ganta,saidai
tana bawa kanta da kanta tabbacin wannan shine gani na qarshe da zatayi mata a
haka,next time lallai zai zamana annin ce kwance saman gadon asibiti kamar
haka......wannan alwashin saita cikashi koda numfashinta zai qare.

Juyawa anni tayi ya fita tana basu waje,ya matso gabanta kadan yana
mata sannu da jiki. Idanu kawai ta zuba masa na wasu sakanni,sannan a hankali ta
bude bakinta.

"Ci gaba da qirqirar sabbin kurakurai suma kuskure ne.......yayin gyaran kuskuren
kuma komai yana iya faruwa da kowa ma......kasa a maidani gida.....jibi nakeso na
koma nigeria" Iya abinda ta fada kenan tana yunqurin sauka daga saman gadon. Baice
mata komai ba ya bita da kallo,saidai kowacce kalma data fita a bakinta ya rubutata
tsaf ya ajiyeta,ya juya ya taka a hankali yana fita a dakin don cika umarninta.

Tsaye sukayi a farfajiyar asibitin sanda motar da jordan ke tuqawa
da maamah din a ciki tana barin cikin asibitin. Musaddiq ya motsa don komawa ciki
bayan bacewa ganinsu da motar tayi.

Caraf fu'ad ya damqo hannunsa,musaddiq ya waiwayo da sauri yana duban
idanun fu'ad din. Ko sau daya bai kalleshi ba,yaci gaba da riqe hannunsa yana
takawa dashi a hankali har zuwa gaban motarsa,yana isa abdulgafar ya bude masa ya
tura musaddiq ciki sannan shima ya shige abdulgafar ya rufesu.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 116
______________________________
_kin dade kina cizon yatsa kan yadda ake kacalcala suturun yaranki da dinkuna
marasa ma'ana?_

_HUGUMA na miki albishir da wajen zazzafan dinki na MS KIDDIES WEARS,irin dinkunan
yaran da kike gani a Instagram TikTok suna burgeki kuma bakisan inda zakikai ayi
miki ba ko kina tsoron tsada_

_Zafafan dinki na gayu da ado kiga yaranki sun fita dagwas dagwas_
_ready

_MS KIDDIES na nan kano gwammaja_

*TRUSTED AND TRUSTED mun gwada mun gani*

_Maza tuntubeta a nan_

+234 708 865 2858

Ko Instagram account dinta

https://www.instagram.com/ms_kiddies_wers_by_nafs?igsh=MTljZWQwM2FsaXlxaA==
____________________________


116


Wadannan tsumammun idanun nasa da ya saba hukuntashi dasu tun yana
qanqaninsa ya zuba masa. Wani irin kallon qurilla me dauke da tarin ma'anoni da
suka sanya jikin musaddiq yin sanyi tun kafin fu'ad yace komai.

"Wanne irin tsoro nake gani cikin idanunka musaddiq?" Fu'ad ya jefa masa tambayar
yana nuna qwayoyin idnunsa da yatsunsa. Tambayar tadan daburtashi,har ya rasa me
zaice masa.

"Ashe kai maqaryacin masoyi ne?......bakason soyayya batason ragwantaka ba?,bakasan
mata basason ragon namiji ba?,bakasan soyayyarka bata cika soyayya ba sai ka amince
zaka iya fuskantar dukkan wani qalubale da hatsari akan masoyiyarka ba?,bakasan
soyayya bata amsa sunanta ba sai ta samu sadaukarwa tsananin kulawa da jure duk
wani tsanani ba?........you're very stupid musaddiq muddin baka xama tsayayyen
namiji ba akan amna......na aura maka amna don ubanka saboda ka kula mana da
ita.......ban tsaya a matsayin waliyyinka ba saboda amna ta samu wani uban bayan
abba.....ni waliyyin amna ne da bazan lamunci duk wani rashin kulawa daga gareka ba
a kanta......ka riqe musu yarinya da kyau.......ka xama jarumi a kanta koda kai
rago ne.......wallahi wallahi bazan daga maka qafa ba idan har naga ko naji wani
abu mara kyau dangane da ita a kanka ba......yiwa auren amna riqon wasa ko ka bari
tsoronka ya jagoranci igiyar aurenta dake hannunka.....to kasa a ranka baka taba
sanin wani me sunan muhammad jadda ba".

Gaba daya jikin musaddiq yayi laushi tubus......yana tsananin qaunar
amna,irin qaunar da bai taba yiwa kowa irinta ba,to amma

Please Login or Register in order to submit comment