You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hadu ba suka
tsareshi a wajen.

Daya daga cikin drivers dinsa ne ya iso da daya daga cikin motocinsa
dake ajjiye a katafaren mansion dinsa na nan abujan qirar Lamborghini. Kai tsaye
jordan ya karbi driving din daga hannunsa suka qarasa zuwa cikin maitama. Plate
number dake jikin motarsa kadai ya sanya me gadin bude musu qofa,Kai tsaye jordan
ya qarasa parking space na gidan ya ajiye motar.

Bai fita a motan ba,har sai da daya daga cikin ma'aikatan gidan ya
sanar da safuura matar uncle din sabreen zuwan fu'ad din.

Tana kitchen tana hada abincin daren me gidan,tuni ta saki girkin tana
cewa.

"Ku bude masa seating room maza akai masa drinks da abinci,me gidan baya kusa,bari
nazo mu gaisa". Fu'ad sunanshi kirkinsa dama kamanninsa duka ba baqinsu bane,wannan
ya sanya suke matuqar girmamashi da yadda kuma ya riqe sabreen dama 'yan uwanta da
kyau,duk da ba gazawa sukayi wajen riqesu ba.

Daidai lokacin fitowar sabreen kenan daga wanka bayan ta murje hadin
dilka dana gyaran jiki da akayi mata,tun daga ranar da tazo mummy safuura ta soma
gyarata ta ciki da waje.

Idanunta kan babbar TV plasma dake maqale a bangon dakin tana kallon
waqar dani kake kama. Sosai waqar ke shiga ranta da wani irin yanayi daya sanya
zuciyarta tayi wani irin laushi,zuciyar kuma ta fada wani matsanancin kewa da begen
mamallakinta wato muhammad fu'ad jadda.

Ajiye towel din hannunta tayi ta taka zuwa gaban mirror tana duban
wayarta dake ajiye a kai. Yawancin lokuta tunda tazo a kashe take barin
wayar,saboda tana tsoron ya kirata yaji inda take yace ta dawo gida. Tanason tadan
sake samun lokaci kadan,duk da tayi kewar komai daya shafesa kewa bana wasa ba,amma
a yau din sai take jin haqurinta ya gaza,koda muryarsa tana da buqatar taji.

Kunna wayar tayi sannan ta zuba numbers dinsa da tuni ta jima da
haddacesu,kiran ya fara gangarawa yana shiga wayarsa dake hannunsa a daidai wannan
lokacin da suke gaisawa da mummy safuura.

Fuskar wayar kawai ya kalla,yadan zubawa kiran idanu yana mamakin ya
akayi ta kirashi a daidai irin wannan lokacin?. Yasan tabbas batasan yazo ba,don ga
mummy din a zaune a gabansu ballantana yayi tunanin itace data shiga ciki ta gaya
mata.

Kife fuskar wayar yayi,har ta gama rurinta ta katse ba tare ma daya sani
ba.

Da dan mamaki ta sake daukan wayar tana sake kira,ta saka a handsfree
ta ajiye tana jin yadda bugun zuciyarta ke daduwa. Still bai daga ba,abinda bai
taba faruwa ba kenan a tsakaninsu. Komai yawan aiki ko uzurin dake gabansa kiranta
na dabanne,to amma batasan wanne irin aiki ya samu da yawa haka a lagos din ba,don
haka sai ta ajiye wayar ta miqe da nufin shiryawa,idanunta kan su fauzan dake bacci
dukkaninsu su ukun abinsu.165


Tana bude luggage dinta hamra diyar mummy safuura ta tura qofar
dakin da sallama ta shigo.

"A tashi HAMFAAL(hamza/farouq/almustapha)". A marairaice Sabrina ta dakata da
daukan kayan da take shirin yi ta dubi hamra,don tunda taji tace hamfaal to
dukkaninsu take nufi.

"Amma dai antynsu fawad ayimin rai don Allah......ina shirin karance littafin girke
girken nan yau duka gaba dayanshi zaki jiqamin aiki?" Dariya sosai hamra tayi,don
ita sam bata ma qaunar yaran suyi bacci. Bata gajiya da rainonsu,zuwansu ne yasa ta
fara jin gidan nasu a mazaunin gida sosai.

"Ayyah.....yau ba laifina bane......daddynsu ne yazo ganinsu". Dum!,taji qirjinta
ya buga,gabanta yayi wani wawar faduwa,tsoro kuma taji ya saukar mata. Ta fidda
idanu waje tana tambayar hamra.

" Please hamra......banason wasa"

"Serious adda......yana seating room,yanzun suka gama gaisawa da mummy" Ta fadi
tana takowa ciki saboda shigowar me aikinsu da zata tayata daukan yaran.

"Gasunan.......ga abun daukansu can" Sabreen ta fadi tana nuna mata tattausan abun
daukan guda uku farare qal dake ajiye a gefe.

Tsaf suka nadesu suka fice dasu,saita bisu da kallo har suka bacewa
ganinta sannan ta maido dubanta cikin dakin tana sauke nannauyan ajiyan zuciya.

Tsoron yadda zata tunkareshi takeji sosai,amma dole haka ta qarfafa
gwiwarta ta som shiryawa cikin mutuwar jiki da rashin kasala.

Dukkanin yaran ya aza saman qirjinsa ya rungumesu yana shaqar
daddadan qamshinsu daya cakude dana mamarsu da yake iya jiyowa cikin jikkunansu
(Shi yasa wannan yake zama babban abun kaico ga macen da take jego amma wai don
wani kayan takaici da baqinciki ka rasa qamshi a jikinta,to wannan qarnin da qarin
da kikeyi haka jikin yaronki zai zama,kada kiji haushi kada kuma kiyi mamaki idan
kikaga yaronki sam baida farinjini duk da kuwa kyakkyawa ne,hakanan kada kiyi
mamakin ganin ana rububin daukan yaron wata kuma bayan baikai yaronki kyau ko saka
sutura me tsada ba,don Allah mu kula da wannan,qamshi rahama ne,koda kuwa iya keda
hancinki ne ma 'yar uwa😂😂).

Bugawar zuciyarsa ya canza sosai daga dumin yaran kawai,sai a lokacin
ya sake fahimtar yayi kewarsu bata wasa ba.

Ajiyar zuciya a jejjere ya dinga saki kafin daga bisani ya saukosu.
Saddiq ya karbi abbanshi hamza. Da fuskarsa da tasu ya manne guri guda,ya basu
tattausan kiss a goshinsu.

Cikin wani tattausan milk material ta shirya,tayi wani irin sassanyan
kyau,jikinta na fitar da tattausan qamshin nan nata na incense by kabo daughter da
yafi qauna. Glowing kawai skin dinta yakeyi na masu danyan jego,ga cikakken hutu ga
kuma gyara da takesha,wanda hatta da abun shanta mummy safuura na daban take bata
na gyaran mata. Kanta ba dankwali sai qaramin mayafin material din data yafa saman
kan nata,wannan ya bawa sumar kanta me sulbi daman fitowa ta gaban goshinta.

A parlor ta samu mummy safuura,saita nuna mata wani kyakkyawan glass
bowl me murfi

"Dauki wannan ki tafi masa dashi......."

"To" Kawai tace da mummy a sanyaye.

Tun daga qofar setting room din ta lura ba alamun takalmin mutum ko
daya,saidai duk da haka bata kawo komai a ranta ba ta taka a hankali ta shiga
parlor din.

Wayam ba kowa cikin setting room din,sai tattausan mayataccen qamshin
nan nasa. Bugawa zuciyarta ta dinga yi d'ai da d'ai d'ai,indai batayi kuskure ba a
nan din hamra ta fadi mata an saukesu,to amma ina suka shiga?.

Mugun sanyi jikinta yayi,tayi taku biyu tana isa saman daya daga cikin
kujerun ta zauna sannan ta ajiye bowl din hannunta. Wayarta data fito da ita ta
zaro ta soma kiran mummy safuura. Bugu biyu ta dauka

"Ya akayi sabreen?".

" Mummy.....banga kowa a seating room din ba.....ba kowa" Ta qarasa fada a sanyaye.

"Kaman yaaya?,yanzun hamra ta baro parlor din fa" Mummy safuura ta fadi da dan
mamaki a muryarta.

"Alla ba kowa mummy" Ta sake fada tana dora tafin hannunta saman goshinta,tsoro
yana kai kawo a zuciyarta bayan wani hasashe da zuciyarta tayi mata.

"Bari ina zuwa" Mummy ta fadi tana cike da kokwanton abinda sabreen ta fada. Wayar
ta ajiye,tana shirin miqewa daya daga cikin yaran gidan ya shigo. Fuskarsa washe da
madaukakiyar fara'a,hannunsa riqe da rafas na dubu daya sabbi kar a miqe.

"Mummy.....baqonku ya tafi.......yace a baki haquri sauri yake,lokacin tashin
jirginsu yana dab da qwacewa,yana gaidaki da kyau,ya mana kyakkyawar sallama,yau
duka mu masu aikinki muna cikin alheri dumu dumu,yace a baki wannan" Ya fada yana
miqa mata envelope din dake daya hannun nashi.

"Waya bawa yaran ya dawo dasu?" Ta tambayeshi tana miqa hannunta.

"Gaskiya dasu naga sun fita......ba da mamarsu suka tafi ba?" Batasan amsar da zata
bashi ba,sai kawai tace dashi

"Madalla.....ka dubamin idan uba ya gama wanke motarnan" Ta fada tana karbar
envelope din.
Budeta tayi a hankali,saiga sabbin dollars a ciki miqaqqu. Ido tadan
fitar cikin mamaki,me yasa sam mutumin nan bai iya qaramar kyauta ba?.

Komawa tayi ta zauna tana ajiye envelope din a gefanta,mamaki yana
cikata. Ya zaiyi da yaran daya tafi dasu?,bai tsaya koda ganin mamansu ba?,bai kuma
gaya mata zaije dasu ba?,kada dai ya zamana sabreen yaji tayi ita ta amsheta bata
sani ba,ko kuma wasa takeyi da aurenta?. Kai tsaye ta dauki waya ta kira sabreen.

"Dawo ciki ina parlor" Bata ko iya amsawa mummy ba,ta kashe kiran kawai ta miqa
bata ko bi takan furar data ajjiye ba ta fice.

'"Zauna a nan" Mummy safuura tace da sabreen tana nuna mata gefanta. Sam fuskarta
ba alamun wasa a ciki.

"Sabreen" Ta kirata a tsanake.

"Na'am mummy" Ta amsa mata kowacce hanta dake cikinta tana kadawa.

"Ki gayamin gaskiya,da iznin mijinki kikazo nan koba da izininsa ba?" Shuru tayi
tana juya maganar mummy,nadama da tsoro suna cikata.

"Ki fadamin gaskiya,don kinfi kowa sanin halina bani da sauqi,ba ruwana da wai
kedin 'yar 'yar uwar mijina ce.....bata yadda za'ayi baban yarannan yayi tattaki
yazo har nan,ya kuma dauke yara ba tare da sanin mahaifiyarsu ba" .

Wannan abun wani baqon abune wajen sabreen din,ballantana ita din da
sam sam bata son tashin hankali ko kadan.

"Da saninsa,saidai baisan nan zamuzo ba,kuma har mu kwana" Take ran mummy safuura
ya baci sosai,ta zubawa sabreen idanu tana jin kaman ta rufeta da duka.

"Me yasa?" Ta tambayeta a taqaice,irin taqaicewar data nuna mata batason wani dogon
sharhi ko dogewa.

"Mummy tsoro nakeji".

" Wani irin tsoro kuma?" Ta fada tana zare mata idanu waje.

"Ciki mummy,inaso na huta......shi kuma haihuwa yakeso akai akai".

"Haihuwarce ke bakiso saboda mamarki kuda yawa ta haifa?". Kai ta girgiza saboda
tasan magana mummy ta gaya mata a fakaice.

"Hutawa kawai nakeso na danyi mummy sab....."

"Gafara can dalla ki rufemin baki malama,"Amma ban taba raina wayonki ba irin yau
sabreen......ni'imar da Allah yayi miki kika sanya qafa kike shureta?.......ashe
baki da hankali ban sani ba?,idan muhammad jadda beso haihuwa a dukiya da lafiyar
da Allah ya bashi ba......ki gayamin me zaiso?,sometimes mata ku kuke kirawa kanku
kishiya wallahi" Idanu a waje ta daga kai tana duban mummy jin ta ambaci kishiya.

"Yes....kishiya,ga abinda mijinki yakeso amma ke kullum kina opposition party
nasa.....me zai hana ya nemo wadda ra'ayinsu da komai nasu yake daidai?......to
wallahi bari na rantse miki,nima yau dinnan basai gobe abbanku ya dawo ba,ba zaki
sake kwanar mana a gida ba.......sauqinki daya na sakaki a jirgi na maidaki gida a
ranar yau,muddin kika sake ya dawo yaji abinda ya faru saikin gwammace bakizo abuja
ba....zan rufa miki asiri bazan gaya masa ba,shine kawai abinda zan iyayi miki"
Kuka sosai ya qwacewa sabreen,komai ya dagule mata cikin lokaci qanqani. Kafin
mummy ta nema musu ticket a gama komai nononta duka ya ciko yanata damunta,alamun
dake nuna mata tabbas su fawwad sun tashi.

"Me zai basu idan sun farka suna jin yunwa?,ta yaya zai iya kulawa dasu?" Tambayar
data dinga yiwa kanta kenan,harta kasa jurewa ta tambayi.mummy safuura.

Duk da yadda tayi laushi lokaci guda ta bata tausayi amma saita jefa
mata harara sanda take hada mata sauran kayanta.

"Ke kika sani,ban sani ba" Ta fada cikin jin haushi.

Haushin kuma bai hanata ta hadawa sabreen din komai ba

"Idan kinje kin nutsu kinwa kanki fada na miki bayani". Abinda kawai tace da ita
kenan. Da kanta ta dauketa a motarta har airport,bata kuma dawo ba sai data
tabbatar da jirginsu ya tashi qarfe takwas na daren ranar.

K'arfe tara da minti ashirin da uku daidai na dare cave din airport ya
saukesu a qofar gidan muhammad fuad jadda. Karon farko da taji tana fargabar shiga
gidan,abinda bata taba ji ba tun bayan data amsa cikakkiyar sunan matar muhammad
fu'ad jadda.

Bata sake fahimtar waye take aure ba......bata sake fahimtar girman
matsayin da Allah ya bata ba sai da suka tasamma shiga unguwar.

Tun a main get na shigowa unguwar suka fara fama da tambayoyi na
securities dake tsaron kowanne gate na unguwar. Yawancin gurare saita laqo tayi
magana sannan suyi salute nata su dage musu su wuce,abinda bai taba faruwa ba
kenan,don duk inda zasu plate number din motocinsu ne kadai amsarsu,amma yau din
sai da tasha bayani kafin su samu su iso qofar gidan.

Gaba daya masu gadin gidan mamaki ya kamasu ganin madam guda a cab.
Cikin rawar jiki da kuma girmamawa suka bude motan suka shiga fidda luggage dinsu
zuwa cikin gidan.

Tun a veranda ta sallami nannies dinsu fawwaz,cikin fargaba ta dinga
takawa zuwa cikin gidan,tana jin kamar ta kirasu su tayata bawa fu'ad din haquri.

"Barka da dawowa......tun daxu nake zuba idanun ganin fitowarki ai" Muryar ma'u ta
sauka a kunnenta.

Dukka dauriyarta ta tattaro ta sakar mata murmushi

"Yauwa ma'u......ashe kina ciki"

"Eh na shigo ne na zare socket na freezer dincan,kayan ciki duka sun qanqare,kada
mu tashi girki gobe qanqara ta hana ciro komai......ya hanya?,dazun na dan jiyo
qushin qushin din mutanen nawa". Dan murmushin yaqe ta saki,ta san tana nufin su
fauzan ne.

"Kinsan basa rabo da rigima idan sukaso,duka su ukun saisun hade maka kai" Dariya
ma'u tayi.

'"Ai inajin sai wajen gobe zamu hadu dasu,Allah ya huta gajiya uwar dakina"

"To ma'u na gode".

"Ba'a buqatar komai ko?" Ma'u ta tambaya.

"Babu ma'u,bari na qarasa ciki" Da haka sukayi sallama ta wuce parlor na biyu kai
tsaye ya doshi hallway dinta.166


Wata matsananciyar kewar yaran takeji tana damunta,tanajin kaman ba
awanni kadai ta dauka bata gansu ba,ji take kaman shekara bata gansu ba,wani
qaunarsu tana sake taso mata kaman ba zata iya qara minti daya cikakke bata gansu
ba.

Kai tsaye dakinsu dake hallway din ta bude,bata gansu ba a ciki,hakan
ya bata tabbacin suna samanshi kenan.

Kaman ta wuce dakinta amma sai taji ba zata iya ba,ta soma takawa zuwa
saman nasa tana qoqarin dake zuciyarta..

Ta kusa minti uku bakin smart door din sannna ta matsa inda tayi
scanning nata,kai tsaye kuma ta bude kanta da kanta tana bata daman shiga.

Scenes din watannin baya da suka shude ne suka shiga dawo kata kanta
sanda ta hangeshi zaune saman minotti sofa dinsa.......watannin da take a matsayin
sabreen dinta ta ainihin,wannan sabreen din wadda babu qaunar Muhammad fu'ad ko
qanqani cikin rai da zuciyarta.

Yana zaune gabansa ya bude apple system dinshi har guda biyu,da
alama kuma aiki yakeyi sosai,koma ya jima a zaune a wajen,don ya saye idanunshi da
farin glass din nan nasa dake bada kalan light blue sama sama wani lokaci wanda ke
taimaka masa wajen zuqe hasken screen din.

Kansa ya daga a nutse yana gyara zaman glass din a fuskarsa,lokaci guda
kuma ya dauke idonsa daga inda take a tsaye ya maida idanun kan screen din yana
taba Bluetooth din kunnensa

"Am hearing you" Daya fada shi ya alamta mata cewa waya yake amsawa.

Duk da haka bata fasa sallama ba don tasan ita din me laifi ce,ta taka a
nutse tana shiga ciki idanunta nakan wani irin gado dake wani shiyya daban na
parlor din. Kaman gado kama lilo haka aka tsarashi,amma idan kakalli cikinsa sosai
zaka fahimci gado ne na 'ya'yan gata wanda aka yi masa lafiyayyar shimfida me
tsananin taushi.

Gaban gadon ta tsaya tana qare musu kallo,sai wani tausayinsu taji
yana ratsata. Kayan jikinsu na dazun yanzun ba sune a jikinsu ba,an canza musu su
zuwa kayan bacci masu taushi na jarirai farare qal dukka iri daya,hatta da socks na
qafansu dana hannunsu,sai suka sakeyi mata kyau,taga kaman sun qara girma akan
girman su na dazu.

Kewarsu takeji sosai,don haka ta miqa hannu don fara daukan almustapha.

A qirjinta ta sakashi,ta rungumeshi sosai tana shafa kan fawwaz. Ta
jima a haka kafin ta sanya fawad a kafada daya,fawwaz a daya kafadar,ta fara takawa
a hankali tana sauka dasu. Sai data kwantar dasu sannan ta dawo ta dauki fauzan.

"Kinci darajar ma'aiki daya hana raba uwa da d'anta......banda hakan da daga yau ba
zaki sake dora hannunki kan yara na ba" Maganar daya fada kenan wadda ta sanyata
tsayawa cak. Batayi tunanin ya gama wayar da yakeyi ba,a sanyaye ta juyo zuciyarta
na bugawa,saidai kafin ta gama ajiye kallonta a kansa tuni har ya wuce dakinsa
abinsa.

Jikinta a mace ta gama shirin kwanciya tana juya maganarsa a ranta.
Tayi fakare tana jira taji ko zataji shigowarsa?,don ko dakin bata kulle ba,hakanan
su fauzan duka akan gadajensu ta kwantar dasu,saidai harta gama zaman jiransa bacci
yayi awon gaba da ita.

Koda ta tashi har an gama sallar asuba. A gajiye ta miqe tana duba ko
ina na dakin,ba alamun ya kwana a dakin,a haka taja jiki zuwa toilet tayi wanka
sannan ta hada da alwala ta dawo ta bada farali.

Shiryawa tayi cikin sassauqar doguwar riga data mata kyau ta fidda
quruciyarta. Qarfe bakwai da ashirin ta wuce zuwa kitchen da nufin shirya masa
breakfast,don bata da scheduled dinsa na satin gaba daya,amna ta tabbatar dole zai
buqaci breakfast din.

Kafin ta kammala har ma'u ta gyara su fauzan gaba dayansu,sai ta
shiga wuce daki kawai ta gyara jikinta.

Kwalliya tayi sosai data dace da safiyar,ta wadata jikinta da
sassanyan qamshin nan da tasan yana masifar so. Bata ma dauki su fauzan ba kai
tsaye ta wuce zuwa samanshi.

Koda ta samu daman shiga parlor din bata wani ji motsinsa ba,don haka
ta wuce zuwa master bedroom dinsa. Tun a nan ta fahimci tuni ya fita,don ga alamu
nan sun nuna,comb dinsa da towel dinsa,da qaramin cup da yasha ruwan dumi duka
saman mirror. Zama tayi gefan gadon tana maida numfashi,hakan yana nufin yayi fushi
sosai da ita kenan?.

Wayarta ta bude ta soma kiran numbers dinsa,saidai kowacce gaya mata
akeyi a kashe take,dole ta haqura da neman nasa ta sauko qasa saboda kukansu fawwaz
da yayi mata maraaba.

Tana shayar da yaran amma duka hankalinta yana kan tunaninsa da
tunanin abinda ya faru. Duk hankalinta a jagule yake gaba daya,ta dinga gwada kiran
number dinsa amma bata shiga,tun tana sanya rai harta haqura ta daina neman
nasa,sai gajeran saqo data tura masa,wanda shima har magariba tayi bata samu amsa
ba.

Magariba ta wuce,isha'i ta shigo itama ta wuce,shuru ba shi ba wayarsa
ba dalilinsa. A haka ta samu su fauzan dukkaninsu sukayi bacci,don dama idan sun
jima sukai bayan ishai'i,idan kuma suka kwanta matuqar sun tashi to yunwa ko
qishirwa ya tashesu,basa farkawa yawanci da safen ma,sai sukai bakwai da rabi har
takwas suna bacci abinsu.

Baccinsu ya sake sakata ta dan qar samun nutsuwa. Wannan karon koda ta
kirashi wayar yana shiga,amma haka ta qaraci b'urarinta ta katse bai amsa ba.

Dole ta ajiye komai gefe,ta qarfafa jikinta ta shiga wanka. Saidai duk
wata laka ta jikinta an zare mata ita. Batajin sam sam zata iya ci gaba da karbar
wannan hukuncin nasa,batasan haka ya iya hukuncin 'yar shariya me ciwo ba sai
yanzu. Zaifi mata sauqi ya kulata,yayi mata fada ma,idan ta kama ma ya zaneta ko ya
zageta zaifi sauqi.

To yau kam ma duk wani shirinta bata samu ganin shigowars gidan bama
kwata kwata. Har sha daya na dare idanunta biyu,batasan kuka ta fara yi ba saida
taji damshi saman fuskar fawwaz dake shan mama wanda ya tashi a sannan,daga qarshe
ma tana tsaka da bawa fauzan mama bacci yayi gaba da ita,wanda a sannan sha biyu
saura na dare.

Washegari taga alamun gidan ya kaana,saidai duk saurint na ta sameshi
bata iskeshi ba. Wunin ranar gaba daya dauriyarta a ya qare,wuni tayi a daki ma'au
nata cigiyarsu,don batason ta fito ma'u taga canji a fuskarta ta zargi wani abu.
Ranar ta rantse ba zatayi bacci ba sai taga shigowarsa,koda zata kwana
ne a zaune,don haka koda goma na dare yayi ta tabbatar yaran sunyi bacci,goma da
rabi ta sauya kayan bacci.

Lafiyayyun kayan barci ne masu wani irin sulbi da yauqi,wadanda ta siya
a HUGUMA CLOSET da sukazo kai tsaye daga Dubai. Suna da wani irin bin jiki da
daukan hankali,lingerie ne sosai na isassun mata.

Curling iron ta saka ta zauna ta yiwa gashinta wani irin nannadewa
kaman macaroni,sannna ta tattarashi zuwa left side na kafadarta gaba dayanshi. Daga
daya side din tadan tareshi da mabanbanta shapes na hair clips. Tattausan lips nata
ta wadata da lips gloss daya qara masa kyau da sheqi,ta wadata kowanne part na
jikinta da kalar turaren da musamman aka yishi saboda gurin,wannan turarrukan ta
sansu da amfaninsu ne a wajen mummy sultana mummyn twins BATOUL DA BENAZEER(Gudun
k'addara).

K'awace ta mummy safuura,ranar da suka isa abuja tazo mata a gaggauce da
nata twins din din batoul da benazeer,wadanda aketa shirye shiryen bikinsu dukka su
biyun,duk da bikin saura watanni shida,amma tsananin gata idan kaga yadda aketa
shiri saika dauja gobe ne ko jibi.

Ita kanta ko yaya ta motsa qamshin jikinta burgeta yakeyi,ta tsaya
gaban madubi taga yadda ta ajiye wani sassanyan kyau,ta gamsu da kanta da kanta,don
haka saita tofe su fauzan da addu'a ta kuma wuce zuwa parlor na biyu.

Ba sabonta bane kallo,amma yau da kanta ta kunna Tv din,ta kuma kamo
tashar tumbin giwa ind suke wani hausa series.

Rabi da rabin hankalinta yana kan wayarta,batasan adadin saqonnin data
aike masa a kwanaki ukunnan ba,amma ko qwaya daya tal bata samu amsarsa ba. A baya
ta shiga tsanani na rayuwa da barazana kala kala,amma bata taba jin tsananin da
yakai mata wannan wahala ba. Bata taba jin nutsuwa da lafiyar zuciyarta tana mata
barazana ba irin na wanann lokacin. A wannan lokacinne take tabbatar da ma'anar
TASHIN HANKALI da kuma rashin sukuni da gasken gaske.



Please Login or Register in order to submit comment