You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani na musamman me cike da alfarma da wata
nutsuwar samun lafiyayyen bacci.

Numfashi biyu kacal ya sauke wani lallausan ringtone ya katse masa
relaxing din da yayi. Duk kiran da zai shigo wayar yasan na wani makusancinsa
ne,hakanan a baya so din ya miqa hannu ya dauko shafaffiyar wayar me wani irin kyan
daukan hankali.

Sunanta da ya gani ya sanyashi miqewa daga kwanciya zuwa kashingida
zuciyarsa tana bugawa,ya lumshe idonsa yana budewa lokaci daya,can qasan ransa yana
fatan Allah yasa ba wani jagwal dinne ya taso ba ko zai sameshi.

Cikakkiyar sallama yayi mata,ta amsa da wani irin yanayi na karsashi
da kulawa.

"Akwai baqi a qofar gida,sun gaya min securities na gidan sun hanasu shigowa" Har
ya sauke qafafunsa qasan gadon da zummar yaje ya duba ta na'urar tsaronsa,sai ya
tuna ashe ba'a gida yake ba nan wani sabon muhalli ne,baida tabbacin an gama
installing nasu,dole ya koma ya zauna gefan gadon a nutse yace

"Baqi kuma maamah?....at these late hours?"

"Eh......ba wasu baqi bane......me aiki ce nace tazo don ta tayata zama,da kuma
yanayin gidan naku dole saida mataimaki daban". Numfashi sosai ya zuqa yana
fesarwa,kowanne taqi kuma kowanne taku da motsi na maamah magana ce me zaman
kanta.....wanzuwar aiki ne da sai ka saka hasashenka da kyau zaka iya cimmasa.

"Amma maamah ina tunanin tafiya zamuyi.....dani da itan gaba daya jibi idan Allah
ya kaimu....so koda tazo dinma zata zauna a gidan ne ita kadai.....nace if possible
ta bari idan mun dawo....i will call you saiki turota" Har tsakiyar kanta taji
wani abu ya tsarta mata,hakan kuma ya bayyana har cikin sautinta daya canza nan da
nan,abinda ya sake bashi wani haske.

"Har zuwa yaushe zaku dawo?".

"2to 3days ne.....just bude kamfani kawai zanyi na dawo" Ya bata amsa bawai yana
nufin dukkan maganganun daya fada haka suke ba. Duk da bai iya qarya ba......amma a
wannan muhallin ya samu fatawar qarya a kansa a yanzu halastacciya ce.

Adadin kwanakin da taji basu da yawa sai taji damuwarta taqaitacciya
ce........ta cika da fatan tafiyar ta sake basu kusancin da zai damqa mata dukka
amanarsa a hannunta,yadda suna dawowa komai zai fara cikin sauqi aminci da kuma
nasara

"To yayi baida damuwa.....ammmm amma ba....kace su barta ta shigo na bada saqo ta
bawa d'iyata". Kai ya jinjina yana cewa

"Alright" Sai ya gintse kiran. Wadanda suke on duty ya duba sannan kai tsaye ya
kira daya daga cikinsu. Saidai kafin basu damar bata damar shigowa sai daya basu
dan qaramin aikin da tun kafin zuwaira ta qarasa ciki suka gama aiwatarwa suka tura
masa.

Bawai bayan ta shigo cikin gidan ba......tun daga farkon layin daya
amsa sunan MUHAMMAD JADDA STREET ta gama raina kanta dama komai nata,bata sake
tsinkewa ba sai da suka iso qofar gate gate guda biyu da fuskar gidan ke dashi
daban daban......ta gama kuma narkewa gaba daya tun daga harabar gidan har zuwa
falon farko da suka zauna suna dakon sabreen.

Kowanne motsi da yadda laila ta gaza sukuni,ta kasa danne zallar
zalamarta da kuma dimuwa da yadda gidan yake duka kan idanun zuwaira take
yinsu,zuwairan da tayi banza da ranta tamkar ma batasan tanayi ba. Mummunar qullaci
ta samu zuciyarta dayi akan hajja harira.....ko maamah bata fuskanci manufar harira
na hadota da ita ba ta gama karantar komai.....baqinciki qyashi da hassadar ta
zauna ita daya a gidan take mata......to itama ta lashi takobin zata gara nata
wasan akan laila da hajja,zata kuma murza musu kalar nata zaren.
Karo na biyu kiran daya shigo mata yadan darsa mamaki a ranta,saidai
a yanzun da 'yan uwanta ke tare da ita,bata jin zata iya tsallakewa kowanne kira da
zatayi mata.....don tana cike da tsoro da fargabar shudewar kowanne minti a sanda
suke tare da ita.

"Ki sauka zuwa falonki kina da baqi.....saqon farko kawai naci su baki.....kiyi
qoqarin fara amfani dashi daga gobe zuwa jibi". Bata jira cewarta ba ta katse
kiran,saita sauke wayar daga kunnenta tana binta da kallo kamar bata gane yaren da
maamah tayi magana dashi ba.


𝐌ðĒ𝐧𝐭ðŪ𝐧𝐚 𝐭𝐚ðĨ𝐚𝐭ðĒ𝐧 𝐛𝐚ðē𝐚 𝐝𝐚 𝐎ðŪðĪ𝐚 ðŽðĄðŪ𝐝𝐞


Daidai sanda jerin motocinsa ke fita daga gidan don komawa nasu gidan,tana
zaune daga gefe zuciyarta tayi wani irin nauyi dauke da tarin kalamai da al'amura
da tayo tsarabarsu cikin gidan.

Tasan tayi qasa d window din motar sanda amna tayo mata rakiya tana
mata bangajiya,amma batasanma bata maidashi ta rufe ba saboda yadda zuciyarta tayi
nisa a wani bigire na daban.

Daidai lokacin da yake zaune bayan motarsa yana danna wayarsa yana
qoqarin neman location na gidan da yazo din. Nishin motocin yaja hankalinsa ya cire
kansa daga wayar yana maidawa kansu.

Motocin muhammad fuad jadda daban suke,kaman yadda komai daya shafi jadda
diamond chore resources ya fita daban. Cikin qirjinsa yake jin buri da fatan inama
ya kasance tamkar wannan matashin me matuqar sa'a?.....wanda ya fado duniyarsa da
wani irin sa'a da yayi Imani ba kowanne dan adam ke samun koda shigenta ba. A
lokaci na quruciya......da qananun shekaru sanda jini ke zagayawa da kyau a
jikinsa......ace ya mallaki d'anyun kudade irin wadannan?.....ya mallaki kyau da
sura irin wannan?.....yayi wani irin tambari da kuma suna,sunan daya watsu sassan
duniya dama kuma ba'a batun tambarar sunansa a qasarsa ta haihuwa.

Kamar cikin majigin film.....kamar wulqawar walqiya cikin sararin
samaniya ya hangi wani Kyakkyawar fuskar......fuskar daya aza dukkanin burinsa a
kanta......fuskar daya sha kwana ya tashi da cikakkiyar sha'awarta tare da tunanin
yadda zai maidata ta zama tasa har abada......fuskar da daga qarshe ta jefashi
cikin bala'i masifa da barazanar faduwar kowacce daraja arziqi da wadatarsa a yanzu
da yaketa fafutukar maidawa......fuskar da a yanzun ba fuskar da yake yunwar nema
ya d'aid'aita rayuwarta irinta.

Bazai iya cewa ga sanda ya zamo ya kuma diro daga saman motar ba sai
da ya fara takawa da zafin nama da zummar ya kamosu,ingarman motocin suka masa wani
irin fit suka barshi da kama iska ba tare ma da sunsan meye shirinsa ba.

"Damn it!!" Ya fada a kausashe yana kaiwa iska naushi da hannunsa. Da gaske itace
matar da muhammad fu'ad ya aura?,da gaske itace amaryar da akace masa ana yiwa
walima yanzu haka cikin gidan Alhaji hamza kibiya?. Wani irin shu'umin murmushi ya
subuce masa ya mamaye fushin da yake kwance akan fuskarsa,ya koma ya daki bayan
motarsa da hannunsa daya dunqule

"Good......komai yayi daidai" Ya kuma fada a fili yana buga wani tsalle ya koma
saman motar yana ci gaba da sakin murmushi,a hankali a hankali murmushin nasa yake
qaruwa kafin daga bisani kuma ya kece da wata iriyar dariya yana sake bugun bayan
motar gami da furta
"MUHSEENA" ainihin sunan da yake shine STAMP dinshi. Da sauri ya kuma saukowa,ya
bude backseat din motarsa ya finciko wata magazine. Magazine ne da suka fidda
sanarwar daurin auren da komai da komai,a sama an rubuta da manyan baqin

_THE BILLIONAIRE'S WEDDING FATIHA_ Kusan babbban abinda suka yita jaddadawa
shine......bikin babban mutum me arziqi kaman muhammad jadda din,yazo ba tare da
wasu shagulgula da aka dade ana hasashen za'ayi ba,luxury events da kowa ke
mafarkin zaiyi a matakin arziqi irin nasa,shin meye sirrin?. Murmushi ya kuma saki
sanda ya karanta tambayar qarshe,sai yaji kaman shi ya cancanci ya amsa tambayar.

"How i wish ina wajen da aka buga labarin nan?,tabbas dana basu full details na
wacece wadda ya aura,ta yaya zaiyi shagulgula bayan BARAUNIYA ya aura?,TSOHUWAR
KILAKI?" Ya fada a bayyane

"Ameenatu!" Ya kira sunanta na ainihi dake rubuce jikin katin.

"You will pay it......dole zaki biya ninkin farashinki" Ya sake fadi still a
bayyane,boyayyen fushin nan dake kwance qasan ransa yana wani tasowa yana bashi
tururin bacin rai har saman fuskarsa.

A gaggauce ya koma cikin motar tasa ya wurga magazine din,shima ya shige
ya kunnata gami da bata wuta ya finciketa yana barin layin don sam yama mance
maqasudin abinda ya kawoshi layin.


*_S A B R E E N_*

Tun bayan sallar asuba take a zaune saman abun sallarta a qoqarinta na
hana kanta komawa baccin daya zame mata al'ada duk safiyar duniya. Bata da matsalar
shirya su haneefa breakfast da sauransu,duka wannan huda zatayi kafin su wuce,sai
yau abun ya zame mata banbarakwai.

Zuwa qarfe bakwai idanunta duka sun daddaure mata sunyi mata wani
iri,ta miqe a hankali ta ninke abun sallar sannan ta taka tana nufar wata drawer ta
zauna gefan gadon tana jawota.

Ledar jiya ce da zuwaira ta kawo mata,ta fiddota tana qarewa ledar
kallo. Abubuwa biyu suna karakaina cikin ranta,kokwanto da kuma qwarin gwiwa,saidai
kuma qwarin gwiwarta a wannan safiyar tamkar yana son korar kokwanton da takeji,don
haka ta riqe ledar da kyau ta fara takawa tana fita a dakin. Can qasan zuciyarta ta
birkita da tunanin me ya samu wayar momma?,me yasa ta kasa samunta?. Daga daren
jiya zuwa asubar yau ta kirayeta har batasan adadi ba,tanaso taji daga
bakinta.......tanason taji me yasa tabar su huda a hannun waccar matar?.

Tsaiwa tayi cikin kitchen din tana tunanin me dame zata dafa ko ta soya
da komai zai narke a ciki ba tare daya bada wata alama ba?. Aqalla ta kusa minti
biyar kafin ta wuce store din.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2

ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ
𝙋𝘞𝙂𝙀 24


24


Inda aka yiwa dankali Kyakkyawar ajiya ta duba,ta debi yadda take ganin
zai isa,ta bude freezer shima ta debi nema ta rufe tana dawowa kitchen din.

Yau sai gata kace kace cikin hidimar hada breakfast,abinda ya zame
mata sai lokaci lokaci idan huda bata da lafiya sannan ta karbeta.

Awa biyu ta share cikin kitchen din,sanda ta gama ta gama gajiya gaba
daya,amma haka ta zaba warmer ta soma zuba komai a ciki.

Sanda ta bude ledar da zummar fara gudanar da aikinta cikin ruwan tea
da dankalin data soya da kuma farfesun naman sai taji hannunta yana rawa. Hannuwan
nata ta sanya da zummar qulle ledar ta maida ciki amma sai sunan HUDA NADRA HANEEFA
ya fado mata......daga bisani maganganun maamah suka dawo.mata fes,sai takejin
kamar umarni ne akeyi mata na KI AIWATAR.

Kai ta soma girgizawa,'yan uwanta sune haqqin farko da suka zame
mata wajibi ta fara kubutarwa.......ba zata wofantar da rayuwarsu ba saboda
mas'alar mutumin da ko qanqani baisan zafinta ko darajarta ba,don haka ta kunce
komai......takuma aiwatar dashi kamar yadda zuwaira ta zana mata,ta debi kayan
abincin ta jerasu saman dining.

Tsaiwa tayi tana kallonsu,kamar ba zata bar gurin ba,sai kuma taja da
baya ta fara takawa tana sauka daga wajen.


▄A nutse yake saukowa daga saman stairs din,sanye da wata lafiyayyar suit ta
kamfanin BRIONI da suka zama number daya wajen fidda suit na manyan mutane daga
auduga da zararruka masu daraja. Yayi wani irin kyau sassanyan kyau kaman yadda
yanayinsa yake nunawa kamar yau din bai tashi da wannan kuzarin nasa ba dake sake
bada bayanin cikakkiyar lafiyar da yake da ita. Qafafunsa sanye cikin rufaffun
takalman dake faman daukan idanu suna qara bayyanar darajar da yawan nauyin kudaden
da aka sanya aka siyesu. Hannunsa daya cikin aljihun trouser dinsa,daya hannun kuma
yana sarrafa wayarsa. Sassanyan turaren nan nasa da bai cika hayaniya da yawa ba
ina busawa a hankali yana karade ko ina. Wani irin qamshi ne na musamman dake
tashin kan mutane da dama,saidai idan ka debe farouq har yau ba wanda zai iya gaya
maka exactly sunan perfume din da yake using. Musaddiq da saddiq sunsha zuwa su
sata,amma sun kasa samunshi ako ina bare su siya.

A yadda yake saukowa daga shi sai wayarsa zaka rantse ba wata
muhimmiyar tafiya bace a gabansa,kamar zaije qofar gidane ya dawo. Haka tsarin
tafiyarsa yake,baya daukan komai sai documents dinsa da wasu mihimman abubuwa amma
banda sutura. Kusan duk qasa ko garin da yake da huldar kasuwanci dasu yana da
permanent gidan da ba abinda gidan ke buqata sai isowarsa.....idan ya sauka a wani
gurin daban ba gidajensa ba to yayi hakanne saboda salon bad da hankali da wasa da
hankulan abokan adawa na kasuwanci ko kuma dalili na ra'ayin qashin kanshi na haka
kawai yaso.

Duba daya ya yiwa hallway din ya maida idanunsa ga qofar da zata
sadashi da parlor din,sai ya maida wayarsa side pocket na rigarsa sannan ya maida
daya hannun shima cikin trouser dinsa yana takawa a nutse cikin falon.

Sai daya zagaya falon tas ya gama duba komai,ya tabbatar komai yana
a muhallin daya kamata ya zauna,sannan ya zarce falo.na biyu ya tabbatar da komai a
yadda yakeson ya zama,sannan ya zarce kitchen zuwa store ya duba komai.

Sanda yake baro kitchen din hankalinsa yakai kan dining din dake jere
da warmers,ya zubawa gurin idanu na wasu mintuna yana qanqance ido,kafin kuma ya
sauya akalarsa yana nufar wajen zuciyarsa cike fal da mamaki.

Cak ya tsaya kan warmers din yana sake binsu da kallo tamkar wanda ke
neman sunan wanda ya qera warmers din a jikinsu. Ya kusa mintuna biyu kafin ya zare
hannuwansa daga aljihun ya fiddosu,bakinsa da yake motsi kadan kadan zaka kalla
kasan akwai abinda yake fadi wanda duka bazai wuce addu'a ba,sannan ya miqa
hannunsa a nutse zuwa ga warmer din yana furta

"Bismillah" A fili,ya murzata ya bude. Daya bayan daya ya bude komai,hatta da hot
water dispenser din da tayi using ta adana tea din sai daya saka cup ya zuba ya
jerasu a gabansa yana qare musu wani irin kallo na qurilla.

Ya kusa mintuna biyar a haka,sai ya saki wani siririn murmushi yana
girgiza kai,ya saka hannunsa ya maida komai yadda yake kamar ba'a taba ba. Hannunsa
ya miqa daga gefan table din ya ciro sticky notes guda daya,yayi gajeran rubutu ya
manne mata jin warmer din ya juya da dan hanzari ba kaman dazu ba yana sauka a
wajen.

"Tabbas ita din aiken maamah ce......" Abinda ya gayawa kansa kawai kenan ya
gangara yana ficewa gaba daya daga falon bayan ya tsinke waya guda daya data rage
ta telephone din dake parlor din.

Kowanne ma'aikaci yana tsaye a matsayarsa suna jiran dakon fitowarsa.
Dukka guards dinsa suna tsaye a inda ya kamata kowa ya tsaya. A yau shigar fari
kowannensu yayi,da wani irin tsarin shiga da sutura da zata bayyana alfarmar wanda
suke aiki a qarqashinsa. Abdulgafar shugaban tawagar tsaronsa shi ya fara nufoshi a
gaggauce cike da kuzari yana tarbarsa cikin girmamawa kaman yadda suka saba shi da
mataimakinsa jordan

"Good morning sir" Ya fara gaidashi kafin muryoyinsu ya karade wajen suna gaidashi
suma

"Morning.....hope you are fine?"

"Fine sir" Suka hada baki wajen amsawa

"Good" Ya maida musu yana gyada kanshi.

"Jordan" Fuad yayi kiransa

"Sir" Ya amsa yana matsowa.

"Where's abdulbasit?"

"Am here sir" Wanda aka kira da abdulbasit ya furta yana matsowa cikin shigar wani
uniform da yasha banban da nasu jordan

"Have you finished?" Kai ya gyada a girmame

"Yes sir...."

"Okay,kada ka manta.....zan bar muku jordan.....jordan,ba shiga ba fita har sai na
dawo ko na bada umarnin hakan. Ko waye bazai shiga ba,ko waye kuma bazai fita
ba......hope i made it clear?"
"Yes sir" Jordan din ya gyada kai,don shi ya fahimci inda aikin yasa gaba,zasu
maimaita salon aikin da sukayi satittikan da suka wuce kenan.

"Yi mana addu'a" Ya fada a taqaice yana duban abdulra'uf wanda kusan duk sanda
qaramin meeting irin haka ya kamasu shike da alhakin hakan.

Cikin mintuna uku aka kammala kowa ya wuce motarsu,motocin suka jeru
kamar kullum,security din dake kula da qofa ya wangale musu ita suka fice daya
bayan daya.

"Am on the way......banason jira" Abinda ya gayawa saddiq kenan da yayi kiransa
sanda suke a cikin motar,sai ya kashe wayar kawai ya maida aljihu. Titi ya zubawa
ido yana fesar da iska daga bakinsa. Baya tunanin maamah zata saka a kasheshi
saidai wani abu na daban,amma ita kuma fa?,may be ta tsallake gona da iri,wala'alla
ta wice limit da iyakokinta,amma duka ita maamah bata gani ba?,why zata zabi mace
me irin wadannan dabi'u da halayen ta kasance a tare dashi?. Tambayar da yaji ta
sake quntata zuciyarsa,abinda kuma bayaso ya faru kenan don yau din yana buqatar
freshness don gobe rana ce me muhimmanci a wajensa.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2

ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ

𝙋𝘞𝙂𝙀 25


25


"Nayi zaton tare zaku tafi?" Shine abinda anni tace dashi sanda yake
zaune sosai gaban abba suna breakfast dashi. Kai ya girgiza

"Ba daman hakan anni,idan munje ma zata dinga wuni ita daya ne saboda ba zama zanyi
ba......akwai baqi da sauran shirin da zamuyi daga yau zuwa goben in sha Allah" Kai
ya jinjina

"To Allah yayi jagora.....yasa a bude a sa'a"

"Allahumma ameen" Suka kusa hada baki wajen amsawa shi da abban.

"Amma ba za'a kai mata abokin zama ba?" . Anni ta fada cikin salon nuna kulawa.
Basarwa yayi don baison anni ta gane komai game da lamarin

"Ba ita daya bace anni,banajin zata damu,akwai mutane a gidan". Kai ta gyada

"To Allah ya tsare"

"Ameen ya rahman" Ya sake amsa mata.

Duka duka mintuna arba'in suka qara suka fice a gidan shi da musaddiq
zuwa airport inda private jet dinsa ke jiran isowarsu.
A hankali hasken ranar dake ratsowa ta tsakanin labule ya soma qarawa
dakin haske yana kuma tabbatar da bayyanar rana sosai ya wuce kai tsaye ya taddata
har inda take kwance,wanda wannan shine abinda ya sanya idanunta budewa a hankali
suka kuma sauka kai tsaye kan agogon dake manne a dakin.

Sha biyu na rana saura minti biyar kacal shine abinda idanunta suka
gani,abinda ya sanyata ware idanunta gaba daya tana kuma miqewa da dan sauri. Bayan
Hannunta ta saka ta mutstsike idonta tana sake duban lokaci,sam batasan tayi bacci
me nauyi haka ba,don ko wanka bata samu tayi ba ta koma ta kwanta bayan ta tabbatar
ta gama duk abinda ya dace.

Miqewa tayi tana miqa,tana jin yadda gajiya kebin duka sassan
jikinta,can cikin zuciyarta kuma tana raya lallai zuwa yanzu ya debi abincin
yaci,tana sake jin wani tabbaci da qwarin gwiwar komawarta zuwa ga rayuwarsu ita da
'yan uwanta.

Toilet ta wuce tayi wanka,ta fito ta shirya cikin doguwar rigar
atamfarJulius gold data zauna mata daidai jikinta da wani irin dinki da bazai
takuraka ba. Sai a sannan taji cikinta yana wani yamutsawa....a lokacin ta tuna
lokacin data dauka rabonta da wani abu me suna abinci cikakke. Plate tummy dinta ta
shafa,sai ta miqe a nutse tana nufar hanyar fita daga dakin.

Tun daga nesa idanunta nakan stairs din har tazo ta gotata tana fita
falon farkon. Tadan shaqi iskar dake kadawa tsakanin hallway stairs din da parlor
din,wani qamshi ne ke kai kawo na daban wanda bata taba jin sassanyan qamshi irinsa
ba,wani sashe daban na zuciyarta kuma tana jin kamar ta taba ji ko sanin irin
qamshin.

Xarcewa falo na biyu tayi,tunda kuma ta fito idanunta suna kan dining
din. Gudun zuciyarta ya qaru kadan,yayin da ta cika da fatan taras da komai ya tafi
daidai.

Bude komai tayi,daga kallon farko ta fahimci ba'a taba komai
ba.....daga nan din kuma dukka gwiwoyinta na qafa da hannu sukayi wani irin
sanyi,sai taji ta kasa tsaiwa,taja kujera daya ta zauna tana girgiza dispensers din
taji ko yawan adadin tea din ya ragu?. Nan ma ba abinda ya sauya,yadda ta zubashi
haka nauyin yake,sai ta saka hannuwanta guda biyu tana dafe kanta,daidai sanda
idanunta suka sauka kan sticky notes din dake maqale a wajen iska tana dan kadata.

Hannu daya ta saka ta ballota daga inda take liqen,ta sanya idanunta
akan kwantaccen rubutun dake a tsare kamar wanda aka tafa a inji bawai hannune
yayishi ba

_mission accomplished_ iya abinda takardar ta qunsa kenan. Jujjuyata ta shiga yi
tanason fahimtar saqon dake rubuce a jiki amma ta gaza kaiwa ga nan,abu daya ne
kawai ya tsaye mata a rai da baici din ba. A niyyarta ta koma daki ta zauna ta jira
wai koda zai sauko yaci bisa rashin sanin ya dade dayin nisa cikin gajimare. Amma
qaguwa dason taga yaci din ya hanata komawar,sai tayi zaune a parlor parlor din
tana saka kunne akan kowanne motsi na gidan,amma sam motsin da take iya ji din ba
wani motsi bane na azo a gani,don hatta da securities na gidan bawai suna kusa da
ita bane bare ta jiyo motsin nasu da kyau.

Sha biyu daya daya da rabi biyu biyu da rabi ba wani batun motsin kowa
da komai cikin gidan,zuwa lokacin ta fara sarewa da lallai bazaya sauko ba,don koda
wasa bata kawo cewa wai baya cikin gidan ba. Koda zai sauko a yadda suka lissafa
mata halinsa tayi imanin bazaici komai na daga breakfast din ba,wannan ya sanyata
cikin mutuwar jiki ta tattare kwanukan tayi kitchen dasu ta ajjiye tana tunanin
yadda zatayi da kayan abincin.
A makare ranar tayi sallar azahar......har ta idar da sallar tunaninta ya
karkata ga me ya kamata tayi?,ta shaidawa maamah din ko ta barta?,kada sanar mata
ya sanyata ta dauka cewa gazawa ce har ta nemi yin wani motsi akan qannenta.

Wannan tunanin ya sanyata ta share,duk kuwa da cewa wani sashe na
zuciyarta a matse yake data gaya matan,amma ta danne da wani irin qarfin hali tana
saka ran zai fito yaci na dare.

Tana idar da sallar la'asar ta fada kitchen,ko a sannan ma tsaiwa
tayi tana tunanin wanne irin kalar abinci zatayi da zaija ra'ayinsa har haqarta ya
cimma ruwa?. Sai data kusa qure tunaninta kaf sannan ta zabi abu daya,ya wuce zuwa
store tana duba dukkanin abinda take da buqata.

Dab da magariba ta baro gaban dining din data cika da warmers masu
dauke da abinci. Tana takawa zuwa hallway din tana satar kallon stairs din.
Zuciyarta cike da mamakin wanne irin mutum ne shi haka?,wanne irin mugun baqin hali
ne dashi da har zai debi wadannan wannin a qunshe a sama ba tare daya sauko ko anji
motsinsa ba?

"Ko yana zuwa masallacin ma oho" Ta furta a ranta a sarari tana jan tsaki gami da
tabe baki,ta tura qofar dakinta ta shiga tana addu'a yadda a daren nan data saka
hope me yawa,ta zuba komai da yawan adadi.....Allah yasa a wannan daren komai ya
ratsahi har fiye da yadda maamah din keso don ta samu tickets din matsawa daga
rayuwarsu ita da 'yan uwanta.

Cikin toilet dinta tayi wanka,takuma

Please Login or Register in order to submit comment