You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko musawa farouq ba ya dauki
mug din daya zuba masa normal black tea ya fara kurba.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 135


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA
KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA
IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE
SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA
A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*




135

So take ta zama kaman kowacce mace.....wadda ke dauke da responsibility na
mijinta,kula da duk wani welfare nashi da al'amuran da suka shafeshi,bawai ta
barshi shi yayita hidima haka da ita ba,don haka koda suka qarasa bedroom din towel
ta ajiye masa sannan ta zarce toilet din.

Water heater ta kunna wanda in minutes ta kashe kanta da kanta alamun
ruwan ya tafasa,saita kunna tap din duka guda biyu na famfunan,ta cika masa bathtub
da ruwan me dumi sosai sannan ta saisaitashi ta health faucet saboda kama ruwa da
sauransu.

Ta kammala tana waiwayowa da nufin fita tace ta gama sai ji tayi an
sake sama da ita an tsumbulata cikin ruwan sannan ya biyo bayanta.

"Bansan sai yaushe zakiyi nauyi ba....kosai kin fara turtsi bulli irin na masu
ciki?" Ya fada yana qanqameta cikin ruwan.

"Me yasa da bakya hadamin ruwa me dadi haka?" Ya sake fada yana sake matso da ita
yana shanshana sumarta data fara jiqewa. Bare baki tayi ta soma masa kukan
shagwaba,akan meye zai jiqata bayan ba yanzu zatayi wanka ba. Dariya ya dinga mata
kafin daga bisani ya fuskanci kukan ya koma na gaske ya lalace wajen lallashinta.

Mintuna arbain kafin su fito,tayi daurin qirji da towel tanata goge
kanta daya jiqe. Curling iron din data dauko ya karbe,ya soma tsaga gashin yana
nade mata shi da style din da takeso.

"Hamma.....ana jiranka fa"

"Tare zamu sauka sabrrrr,bazan sauka na barki ba" Karbe curling iron din tayi ta
ajiye

"Mu shirya na rakaka kaci abinci ka fita.....kace kana da hidiman bikin BB
naka.....yaushe ka gama ganawa da mutane ka maida hankalinka akai?". Hancinta ya
lakace mata.

"Yes maaa.....da alama ina da personal assistant me hazaqa,anya bazan sallami
saddiq ba?" Murmushi ta saki tana cewa.

"Ba ruwana,kada yace nasa an koreshi".

Sai data tabbatar ya qoshi sannan ta taka masa har inda yake ganin
baqin da suka zama dole,baqinsa na jikinsa sosai wanda ita kanta batasan da wajen
ba sai a sannan. Zata juya kenan daya daga cikin guard dinsa suka qaraso.
"Malam ne yazo"

"Har sai an nema masa izini?,kace masa ya shigo qasan rumfar can" Ya fadi yana
juyawa yana fasa shiga sitting room din. Hannunta ya kama.

"Muje ku gaisa da malam.....mutumin kirki wanda ta silarsa ne na samu ilimin
addini". Bata musa masa ba suka taka zuwa farfajiyar da aka qawata da kujerun zama.

Tun daga nesa ta gane malam dinta,mutumin kirki na gasken gaske wanda
kusan zata iya cewa tafi fu'ad sanin hakan.

Mamaki sosai malam yayi sanda yake zama saman dayan kujerun dake wajen.
Ta zame tana gaidashi kaman yadda fu'ad yayi.

"Ashe da gaske rumaisa take?,sanda take gayamin ke kike auren muhammadu ba dauka
shirmenta ne kawai.....muhammadu kayi sa'ar mata da gasken gaske" Malam ya fada
yana maida dubansa ga fu'ad. Sabreen fu'ad din ya kalla sannan ya maida dubansa ga
malam.

"Tana da tausayi da taimako......tana da yawan sadaka da kuma kyauta,bata wata
batayi sadaka ga mabuqata ba......marainiya ce muhammadu......nasan halinka kai
dinma.....muna da kyakkyawan zaton nagarta daga gareka......ka riqeta hannu
bibbiyu,lada biyu gareka,ladan riqon maraya,ga kuma ladan kula da iyali".

"In sha Allah malam" Ya fada yana sadda kansa qasa. Inama ace malam yazo a sanda
yake tsaka da fara cusgunawa rayuwarta?,inama ace malam yazo a sannan ya ceceshi
daga feeling guilty da yakeyi a duk sanda ya tuna yadda ya mu'amalanceta a baya?.

Duk da cewa ba laifinsa bane.......yayi dukkanin binciken da zai yi a
matsayinsa na dan adam.....kuma abinda ya samu kenan. Da gaske ga a inda kudaden da
duk take diba sukafi tafiya kenan fiye da jikin 'yan uwanta,sai yakejin wannan din
dama ce ta sake samun wasu labaran a kanta ta wajen malam din.

Hira kadan tayi da malam tana tambayarsa inna ta bada saqon gaisuwa ga
rumaisa da shaida mata sun dawo sannan ta koma ciki.

Da kanta ta shirya abun motsa baki ta kawowa malam din,duk da ma'u
tace ta barshi amma tace sam malam yafi gaban haka.

Qarfe tara tayi shirin bacci,don tunda ya fita ba sake jin motsinsa
ba,ta tabbatar zai wahala idan ba baqin bane suka sha masa kai. Ta dawo parlor din
farko da nufin daukan madarar shanu ma'u na fitowa a kitchen da alama ta gama komai
na yau sai gobe kenan.

Tana mata sallama amma idanunta akan kwalin hannun mau,tsirfa da
tsarabe tsarabe irin na musu ciki haka kawai taji yawunta ya tsinke.

"Amma fa ma'u meye wannan?" Kallon farin box din tayi tayi murmushi.

"Wallahi amna ce ta aikomin dashi,wani doughnuts ne da ta taba ban guda daya ta
yafi dani,sai tace zata sake sakawa a kawomin".

"Mu gani" Sabreen ta fada tana matsowa,bude mata ma'u tayi take yawun bakinta ya
qarasa tsinkewa gaba daya.

"Don Allah ma'u ko guda daya ne" Ta fada tana narke fuska idonta akan doughnuts din
da aka yiwa wankan madara.
Dariya ta qwacewa ma'un,tasan halin ciki yafi gaban haka,bataga abinda
zata samu ta hana sabreen din ba,bare wannan da nan da nan idan sunason wani za'a
sake kawowa.

"Jeki da kwalin gaba daya" Ta fadi tana tura mata kwalin. Har wani dan tsallen
murna tayi,ta amshe tana godiya ta haura saman dashi.

Gudu gudu ta gama shiryawa,ta ware gashinta saman bayanta ta haye sofa
tana bude kwalin. Lashe baki tayi tana jin kaman ya mata nisa ta tsaya bude ledar a
daidai kawai saita farke.

"Uhmmmnnnnn" Ta fadi saboda yadda wata lafiyayyar madara ta hade da doughnuts din a
bakinta

"Ya salammmm" Ta sake fada sanda tayi gutsira ta uku,kawai saita kasa daurewa ta
juya bayan kwalin ta kuwa dace da sunan mamallakiyar abun.

*_Maman ummies delight_*+234 803 049 9555

A fili ta karanta komai tana lumshe ido,saita rasa wanne zata fara kira a
tsakaninsu?.

Landline kawai ta nufa ta soma kiran amna.

"Addarmu"

"Ba wani addarmu......yanzu amna harki samo abun arziqi irin haka amma ki kasa
tunawa dani?". Tsam amna tayi tanaso ta tuna meye,ita ta dauka ma complain zatayi
akan sun sauka bata nemeta ba

" Adda mene?"

"Doughnuts mana.....doughnuts din maman ummi". Dariya sosai ta zowa amna,duk yadda
taso tareta kuwa sai data fito,karon farko data fara yarda masu cikin ajinsu da
zasuga sun fiya fi'ili da neman fitina da gaske sukeyi bawai iya shege bane,yadda
ta fadi doughnuts din maman ummin tar a bakinta saika rantse ta santa farin
sani,kaman ba yaune cin farko ba.

"To adda mu fara da bismillah mana.....dama anni ta gayamin triplets ne,suna sauka
albishir din data fara yimin kenan da alama da abun take kwana tana tashi.....Allah
ya bawa hamma juriya,ni dama guduwa zanyi na barku". Baki sabreen ta kama

"Iyeeee,au gayamin kike aure zakiyi kenan" Kunya ta kama amna kaman sabreen tana
gurin.

"Ni na isa adda...."

"Yanzu mu ajiye wannan maganar.....ina za'a samu doughnuts dinnan?,na kusa cinye
wannan" Ido amna ta zaro.

"Tana kaduna fa?,amma saga kaduna zuwa kano kawo doughnuts dinta kaman kina garinsu
ne,sharp sharp ne.....idan ta kama sai asa hamma ya tashi jet a karbo miki" Dariya
sosai maganan ta bawa sabreen,saidai da gaske dadin doughnuts din har cikin
tsokokinta take jinsa.

"Seriously amna.....am addicted to it......zan samu nayi breakfast dashi?"

"Lemme call her......zaki samu koda wajen 10 ne haka in sha Allah.....ko duba
flight din safe sai ayi idan akwai a sako miki.....amma indai shi zaki koma ci
hamma yana kwale kwale" Amna ta fada tana qyaqyata dariya tayi kuma saurin katse
kiran.

"Kada fa haka ta kasance" Ta fada tana raba ido bayan ta lamushe taji bata gamsu
ba. Ledar tabi ta tande madarar tasss ta saka kwalin a gaba har tana fatan inama
tana sauran wani a ciki?.

Bata ankara ba bacci yazo yayi awon gaba da ita sassaucin da aka samu
kenan.

Qarfe sha daya saura ya qaraso cikin parlor din,idanunsa a kanta,wani
soyayyarta yakeji tana sake ratsa dukka qasusuwansa. Bayanan da ya sake ji daga
bakin malam sai yakejin kamar ta cancanci sama da soyayyar da yake nuna
mata.....kamar ta cancanci sama sa wannan rayuwar da takeyi a yanzu.

Sai daya kammala komai a hankali don kada ya tasheta,ya dawo ya zauna
da wayoyinsa. Su anni farouq da musaddiq duka yakeson kira,yanason komai ya kammala
da wuri,don kwanaki hudu ne kadai suka rage daurin auren.

Sai sannan idonsa ya sauka kan kwalin,ya jawo ya dudduba yana mamakin
yadda aka yiwa ledar tasss,yadan girgiza kai ya kwashe ya zuba dustbin sannan ya
dawo ya zauna yana sake duban fuskarta. Wani kyau take qarayi masa kullum,hakanan
ba qaramin kyau bacci yakeyi mata ba,murmushi ya subucewa labbansa ya fara kiran
farouq.

Kira daya ya daga kaman yana kusa da wayar,muryarsa can qasa yayiwa
fu'ad sallama.

"Are you okay?" Fu'ad ya tambaya tana tsayawa cak.

"Am okay dude"

"Ma sha Allah.....ka karba envelope"

"Na karba"

"Ka bude?"

"Na bude dude.....but I'm.....I'm speechless dude.......rubutun jikin invitation
card dina da ruwan gold na ainihi?" Murmushi ya subucewa fu'ad.

"Kafi qarfin wannan dude......kada ka sake magana akai.....akwai sadakin fannah a
daga envelope din....have you seen it?"

"What?,dowry fa kake magana dude?......wannan gold din ya ninka abinda suke karba a
matsayin sadaki......babanta malami ne,kada yaga mun zura da yawa fa".

"Fannah tafi qarfin haka a gurinmu....tunda takeson wannan tsohon tuzurun namu,ta
kuma amince zata zauna mana dashi da zuciya daya.....sadakin mace baya yawa a
musulunce,ko nawa aka bata yayi,saidai ma yayi kadan,yadda kace babanta malami ne
nasan yasan da hakan,sayyadina umar yaso qayyadewa a zamaninsa,wata mata ta tunasar
dashi annabi baiyi hakan ba, sai ya qyale shima.... Ka fahimta?"

"Ya ilahi dude.....am speechless seriously"

"Zamuyi fada dakai......ina fata ka riqe data din....kwana hudu......saura kwana
hudu dude dina ya angwance" Sautin murmushinsa ya riski fu'ad,hakan kuma ya masa
dadi a haka sukayi sallama. A duniya bayajin yana da wani abu da zai iya sakawa
farouq dashi koda meye yayi masa.
Musaddiq ya kira wannan karon,shima dai kaman yana kusa da wayar ya
daga. Muryarsa da mugun sanyi ya amsa sallamar,still shima tambayarsa yayi lafiya
yake?.

"I'm fine hamma"

"Maamah ko?" Shuru musaddiq yayi yana mamakin yadda ya gano haka ta farat daya.
Shurunsa ya bawa fu'ad tabbaci,ya sauke numfashi.

"Idan ka dorama kanka daukan damuwoyinta ba inda zakaje a rayuwa,zakayita zamane
kamar a inda ta tafi ta barka ba tare da damuwan yadda rayuwa zata kasance maka
ba.....na kiraka na gaya maka,kayi magana da musaddiq kai dashi ku duba gidajen nan
dana bashi details dinsu ku zaba,za'a hade bikinka sana farouq in sha Allah,so ka
ajiye damuwan da bata cancanci damuwarka ba.....ka fuskanci rayuwa da reality
dinka.....but kada ka sake ka manta da wannan......ka riqe mana amna sai mutuwa ce
zata raba". Mutuwar daya fada ta saukar masa da wani irin matsanancin faduwar
gaba......ta kuma tuna masa da maganarsu ta dazu da maamah.

"Mutuwa hamma?".

"Yes.....mutuwa,saboda ita kadaice ta isa ta raba Soyayyar masoya" Shuru ne ya
wanzu tsakaninsa da shi,har sai da fu'ad din yace.

"Kana layi?"

"Inaji hamma"

"Good......komai da amna zata buqata ka rubuta ka turamin.....bance ko sisinka ka
saka a bikinka ba" Baima jira ya masa godiya ba ya katse,saboda baya
buqatarta,yanajin wani wajibinsa ne ya saukeshi.

Anni ce ta qarshe daya kira,amna na kusa da ita ta miqa mata wayar.

Ban gajiya suka yiwa junansu,sannan itama ya buqaci ta bada duk wani
abu da take buqata.

"Muhammadu kabar 'yan uwanka suyi wani abun mana?" Murmushi yayi

"Anni sai idan bana raye.....ki fadawa amna ta rubuta komai da take buqata na
lefe.....idanma ba zata iya ba tazo nan gidan su hadu ita da duniyat....." Saurin
katsewa yayi bai qarasa ba,kunya ta kamashi ya aza hannunsa aka yana sosa sumarsa.
Murmushi me sauti ya qwacewa anni

"Ita da duniyarka ameenatu" Murmushi shima ya saki.

"Su rubuta komai,bance ta dauke masa komai ba". Kaman sauran bai jira ta masa wata
godiya ba ya katse wayar,ya zubawa sabreen ido wani abu yana yawo cikin ranshi.

Da alama baccin ya mata dadi sosai,amma dole ya tasheta don akwai
magana me muhimmanci da zasuyi da bata buqatar takai safiya,yana ganin kaman tayi
nisa.

Wayar anni ta ajjiye gefanta,tana jin wani abu yana sauka a ranta.
Tabbas fu'ad din wani kyautar Allah ne a garesu,bawai don dukiyar da yake da ita
ba.....aah....ta jima da sanin haka tun yana fu'ad dinsa dan makaranta secondary
school,fu'ad dan bautar qasa. Wata irin zuciya ce shimfide a qirjinsa,wani irin
dattako daya girmi shekarunsa......wani irin halin girma me dumbin yawa.
"Tabbas mariya inda kinsan irin kyauta da alkhairin da Allah yayi miki a rayuwa da
baki gudu kin bar muhammad ba.....da baki gudu kinbar musaddiq ba". A tattare dasu
gaba daya tana ganin wata irin nagarta ta musamman.

"Hammanki yace ki rubuta ko kije gurin addarki ki.masa list na kayan lefe duka"
Anni ta fada tana nazarin amna data fahimci ta yawaita shuru shuru tun daga
yammacin yau din.

"Lefe ann?" Amna ta tambaya da wata sassanyar murya

"Wani abun daban kikaji na fada?" Anni ta fada tana nazarinta. Kai amna ta
girgiza,haka kawai taji hawaye sun cika idanunta,sai anni ta kasa jurewa.

"Meya kuma?"

"Tsoro nakeji anni......gabana yanata faduwa" Sai hawayen da take maqalewa ya
gangaro mata.

"Tsoro?" Anni ta maimaita,kai amna ta gyada mata. Yankewa gaban anni yayi ya
fadi,ta sauke numfashi tana ambaton sunan Allah.

"Tashi kije kiyi alawala,ki karanta hasbunallahu wa ni'imal wakil qafa dubu kafin
ki kwanta". Kai amna ta gyada sannan ta miqe a sabule tana fita a dakin zuwa nata.

"Addanmu" Fu'ad dake tsugune gaban sabreen da bacci yaketa danneta ya fada yana
leqa fuskarta. Da qyar ta sake bude idon nata a karo na uku.

"Adda sabreen.....tashi don Allah" A cikin baccin taketa mamakin kiranta da adda
din da yaketa yi,saita miqe tana daquna fuska.

"Hamma.....bacci"

"Zakiyi,na miki alqawari,amma kafin sannan jeki wanki fuskarki ki dawo". A daddafe
ta miqe saboda nauyin bacci,ta lalubi toilet din ta shige.

Ba jimawa ta fito,fuskarta tayi fresh da digo digon ruwa,idanunta sun
dan tashi kadan alamun bacci,ta zauna saman sofa tana dubansa.

Ajiye abinda yakeyi yayi ya taso,ya iso gabanta ya tsugunna a
hankali. Hannuwansa yakai ya kamo tafukan hannayenta a tausashe.

"Adda sabreen" Ya maimaita fadi yana murmushi. Idanu tadan ware tana dubansa wani
malalacin murmushi yana qwace mata. Kai ya jinjina mata.

"Kin bamu daman neman auren sister huda?.....kin bamu izini mu nemawa musaddiq
auren sister huda?".




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 136


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA
KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA
IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE
SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA
A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*




136


Wani saukar ba zata zancen yayi mata,wani irin zuwa ya yiwa kunnuwanta.

"Saddiq kuma?,saddiq dai hamma?" Ta fadi da sautin muryar bacci da har yanzu bata
gama warwarewa ba,banda ta zuba ruwa saman fuskarta da sai tace cikin jerin gwanon
mafarki kawai wannan maganar take dibanta. Murmushi ya saki me sanyi yana jinjina
mata kai.

"Eh......saddiq dinmu addanmu......inaso ya zama mijin huda nan da kwana hudu,kaman
yadda farouq zai zama mijin fannah in sha Allah" A hankali ta daga ido tana sake
duban fu'ad din,sai takeji kaman wasa yake mata da hankali kawai ko tsokana,saidai
kuma ko daya bataga wannan a cikin idanunsa ba.

"Hamma.....huda fa?.....ka manta mudin ba kowa bane hamma.... Mu din ba wasu
madaukaka bane,ni din kawai a cikin family dinku ya isa,basai huda ta shigo ba...."

"Shshshsh" Ya fada yana dora yatsantsa akan lips dinsa. Bayason wannan karayar da
take nunawa,bayason wannan raunin da yadda har yanzu ta kasa jinta kaman
kowa.....bayason yadda ta kasa daina tuna wacece ita a baya

"Damu daku dukkaninmu abu daya ne yayimu.....jirgi daya ne ya kwaso mu.....ki manta
akwai wani lokaci da abinci da sutura suke gagarar muhammad fu'ad?....ki manta
akwai wani lokaci daya shude da yunwa take saka musaddiq kwana yana kukan
yunwa?,kin manta wani lokaci daya shude fu'ad dan jari bola ne?......kin manta
sanda saddiq ke kwana da yunwa saboda ba gatan uwa a gefansa?,duka damu daku ki
gayamin meye banbanci a ciki?" Shuru tayi tana tuna komai kaman yadda yake tunasar
da ita yanzu.

"Hamma.....amma huda batayi qanqanta ba?.....yanzu zata gama secondary school
fa......a haka an sanyata a makaranta da wuri kaman yadda abbanmu yake mana....."
Murmushi ya saki yana dan jan kumatunta.

"Qanqanta?.....ke din kanki duka duka shekara nawa kika bata?,banajin yakai
biyar,ba gashi muna zaune ba?".

"Hamma karatunta fa?" Hannu ya sanya yana dungure mata kai da sauri

"Lallai dai sai an ja mana aji kafin a bamu auren sister huda.....lallai ko yaya
wai sai an wajiga mu?.....me huda zatayi da karatu duniyata?,ba huda ba.....ko
wanda ke rayuwa qarqashin inuwar jadda banajin zai buqaci karatu saboda ainihin
buqata ta lalura.....saidai duk me sha'awa yayi karatun don dai sunansa
ilimi.....ba abinda huda zatayi da takardu.....saidai.idan har tanason karatu
saddiq bazai hanata ba.....za'a dauko mata duk kalar malamin da takeso ya koyar da
ita matakin ilimi daga na college har zuwa university har PhD ma.......idan kuma
makaranta takeso......ta zabi duk makarantar da takeso a fadin duniya cikin jerin
qasashe da muke dasu a duniya 195 zuwa 200....kowacce take so zataje in sha
Allah......sai me kuma......a shirye muke mu karba duka qorafinki" Ya qarasa fada
yana tsareta da ido tare da jiran abinda zata sake fadi.

A hankali ta jinjina kai

"Na amince hamma.....na bada izini bisa sharadi da alqawarin zai bata dukkan wata
kulawa data dace koda bayan raina". Wani zazzaro idanu wajen fu'ad yayi yana
dubanta.

"Kul.....karki sake zancan bayan ranki my world......waye ya gaya miki fu'ad yana
da sauran rayuwa bayan babu taki?". Idonta ta maida ta lumshe a hankali tana
murmushi.

" Zamu rayu tar in sha Allah......zamu kula da yaranmu mu kuma basu tarbiyya tare"
Ya fada yana sumbatar hannunta a tausashe.

"Na gode sosai duniyata.....na gode sosai da sadaukarmana da daya daga cikin
abubuwan da kike matuqar so a duniya.....kika yarda ta zama abokiyar rayuwar
saddiq"

"Kafi qarfin komai a wajena duniyata.....kafi gaban haka muffin". Ta fada itama
harshenta da sautinta cike da qauna da soyayya.

" Bayan gidan malam......sai ina da ina kike kai taimako?" Ya sake soko Mata
tambayar da bata taba kawota ba. Fararen idanunta ta daga ta kalleshi,sai kuma ta
sauke idanun nata qasa tana jin nauyinsa. Batason abinda zai sanya ya dauko mata
wannan zancan na abinda ya wuce a tsakaninsu.

"Ki bani dama.....inaso ki dore da aikin ladan da kikayi niyya in a halal
ways.......inaso na miqar dake kici gaba da abinda kika fara a baya". Sake kallonsa
tayi a karo na biyu......tana jin yana sake shiga rayuwarta yadda ya kamata.
Soyayyarsa tana sake hudata,wani mafarki ne wannan nata,dasu take kwana dasu take
tashi.....hayewar su huda kawai bai sanya zuciyarta ta kwanta d'ari bisa dari
ba.....bai sanya zuciyarta ta samu nutsuwar da take yunwar samu ba. A yanzun a kuma
wannan lokacin sai gashi ya gama qarasa karanta tunaninta kafffff yana son xike
mata ragowar gibin da ya rage.

"Me yasa a kowacce rana kake sake karantar zuciyata?,me yasa a kowacce rana kake
abubuwan da suke sake haukatani a kanka muffin?". Idonsa ya lumshe yana budesu duka
a lokaci guda. Yanason irin wannan yanayin.....yana son irin wannan lokacin da
zaiyi zaune kawai a gabanta yana tana tona masa asirin zuciyarta.

"Sabrrrrr" Ya sake kiranta a tausashe.

"Haqqina ne.....kuma cikar kamalar kowanne d'a namiji kenan,ya karanci wace
matarsa.....me tafi so?,me tafi buqata?,me zaiyi ya mallaketa?". Mallakar daya fada
ta sakata fashewa da dariya tana zaro ido.

" Hamma.....mallakata kakeso kayi?"

"Nama mallakeki duniyata.....na mallakeki....kedin tawa ce ni kadai har abada" Ya
fada yana daga yatsunsa guda biyu.

"Gidan marayu.....gidan gajiyayyu.....yaran da iyayensu suka mutu suka barsu kuma
babu me tallafa musu irinmu" Takai qarshen maganar muryarta tana karyewa.

"Ki zauna ki tsara dukkanin burinki akan wadannan gidajen". Ya fadi yana miqewa
tsaye. Wani irin sanyi taji yana sauka saman zuciyarta

"Ina fata ubangiji ya lullubeka da dukka rahamarsa......ya yaye maka
damuwarka.....ya kyautata qarshenka.....na gode da karamcinka karimin mijina.....na
gode da wannan halin dattako naka uban 'ya'yana". Murmushi me sanyi ya kubce
masa,yanajin alfahari da wannan addu'ar tata.

"Allahumma ameen matata 'yar aljanna.....amma saura abu daya da baki roqamin ba".
Idanunta ta juya,abinda ya sake tafiya sosai dashi

" Me kenan muffin?"

"Baki roqi Allah ya qarawa wannan ameenatun so na ba.....so nake ameenatu ta soni
fiye da yadda takeson kanta,don kuwa ta samu wanda zai kula mata da kan nata" .
Kunya ta sakata sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta kafin tace.

"Inda ana iya bude zuciya ko qirji a nunawa wani.....tabbas da na bude maka tawa
zuciyar kaga abinda yake ciki a kanka,wataqila zakafi gasgatani.....don maganar
fatar baki tayi kadan" Rasa me zaya ce mata yayi,sai kawai ya tsugunna yana kissinh
forehead dinta a tausashi.
Yana dauke labbansa tana daga idanunta da sauri,sai ta soma rarraba
idanun nata tana a narke.

"Kai.......ina doughnuts dina?" . Dubanta yayi

"Wanne doughnut?". Ya tambaya yana tunanin ko mafarki tayi a dazun kafin ya
tashera. Tambayar tata da yayi sai taji kaman zata saki kuka

"Doughnuts dina mana da ma'u ta bani......a nan fa na ajjiye naci kadan na ajiye
sauran". Qaramin murmushi yayi.

"Kin cinye madam....ni na tattara kwalin na zuba a dustbin". Idanu ta waro waje
tana dubansa sosai da salon rigima a muryarta.

"Ka sakamin a shara?,wallahi ban cinye abuna ba,akwai saura" Ta fadi tana miqewa
zumbur gami da nufar dutsbin din. Da mamaki yake binta da kallo ganin yadda ta bude
dustbin din tana ciro kwalayen.

"Kai?,ka cinyemin?" Ta fada cikin sanyin jiki hawaye yana taruwa cikin oily eyes
dinta. Dariya ma abun ya bashi,ya daga hannunsa alamun surrender yana dubanta.

"Innalillahi,Allah ba ruwana,sanda nazo ba komai a ciki sai boxes din da leda".
Dariyar tasa ta qular da ita,sai kawai ta fashe da kuka tana sakin boxes din.

"Wallahi kaine.....kaine ka cinyemin kuma bazan yarda ba" Mamaki sosai ya kamashi
ganin yadda ta zube tana kuka bilhaqqi,hawaye shabe shabe ta dage wai shine ya
cinye mata. Da sauri ya isa inda take yana miqa mata hannu.

"Yi haquri ki tashi.....eh na yarda nine na ci". Ya fadi hakan don ya lura qaryata
ba shine yaci din bama qular da ita yakeyi.

"Dama kai dinne ko?" Ta fada tana watsa masa harara da jiqaqqun idanunta,sai ta
sake fashewa da kuka sosai kaman wadda aka yiwa dukan tsiya harda shashsheqa.



Please Login or Register in order to submit comment