You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwanta ne tana
monitoring dukkan motsin hudan.

Har ta gama juye juyenta,ta fita falo sha biyu saura na dare,shigarta
kitchen da zaman cin abincinta ta gama ta maida kwanon tana jinta.

Har zuciyarta tana son jin muryar bassam dinta.....amma wata zuciyar
tana kwabarta,yau din bai kamata tayi waya dashi ba,don gaba daya jikinta da
zuciyarta babu qwari.

Sha biyu na dare yana zaune cikin kebantaccen dakin nasa,gaban
system da tarin cups na shayi da yake canzawa daga wannan zuwa wancan. Aiki yakeyi
sosai,aikin kuma yana tafi masa yadda yakeso,don yana sake samun wasu bayanai da
yakeso.

Wayarsa tayi qara alamun shigowar kira. Waya ce daya ware musamman
saboda waya tsakaninsa da gurd dinsa musamman idan basa kusa ko basa tare. Jordan
ya gani,sai ya dakata daga dukkan abinda yakeyi din ya daga wayar yana relaxing
bayansa jikin kujerar da yake zaune akai din,don dama yana expecting kiransa daga
wannan lokaci har zuwa asuba zuwa safiya.

"Barka da warhaka sir" Jordan ya fadi da hausarsa da bata gama tsaiwa tar ba

"Barka dai jordan......how far?"

"Fine sir.....duk wani information ya kammalu"

"Very good......" Ya fadi da nutsuwar nan tasa data sake qaruwa sakamakon bacci
dakeson fara kamashi.

"Tell me jordan......"
"Immediately sir" Ya fada yana sake tattara hankalinsa akan boss din nashi.

Idanunshi a lumshe sanda jordan ke sakar mishi bayanai dalla dalla
akan sabreen din. Bayanai ne na bincike da yayi a kanta ta hannun mutane daban
daban da suke da jibi da Rayuwarta.

Ba abinda yake sauraro illa muryar jordan yana masa bayani dalla
dalla har yakai qarshe.

"Good job jordan......na baka hutun gobe.....ka kwanta ka huta sosai.....but idan
ina buqatar wani abu daban zan kiraka"

"As you wish sir" Ya fada cikin girmamawa.

Da wani irin cakudadden yanayi na ajiye wayar gefansa yana furzar da
iska me dumi daga bakinsa. Ba abinda yafi riqewa saman kansa irin kalaman jordan na
biyun qarshe

"A taqaice dai sir ana kyautata zaton KARUWA Ce ko kuma mayaudariyar
maza......wadda maza da dama ke sonta suke kuma kashe mata kudade masu kauri,kuma
daga qarshe abinda yake faruwa ba'a jimawa take rabuwa dasu......tana rayuwa ne ba
uwa ba uba.....amma tsarin Rayuwarta da yadda takema kanta komai da 'yan
uwanta.....koda d'a me uba da kuma tsananin gata sai haka......bata nemi komai ta
rasa ba......sir......akwai wanda ya gaya min tana da hatsari.....tana da
hatsari.....tana kuma da mabanbantan sunayen da ita kanta batasan adadinsu ba".

Ajiyar zuciya me nauyi ya sauke yana jin wani abu yana tokare masa a
qirji. Ya miqe qafafunsa sosai tamkar zaiyi miqa yana jin wani irin ciwo a
zuciyarsa. Qoqari yake ya sake tuno fuskarta ko zai iya banbance shekarunta da yayi
imanin ba zasu wuce ashirin ba tsanani da daya.

Abinda yaqi jinij yaji ko ya gani kenan koda cikin labarai diya mace ta
lalace har haka. A dukka qananun shekaru irin nata ta iya zama mace me hadari har
haka?,har ta iua bada jikinta zuwa ga wasu mazan don ta mallaki abun duniya?,har ta
iya yaudara da damfarar wawayen maza irin Mikhail?. Wannan kadai ya isa ya bashi
tabbacin tabbas ita ta shirya ko ta tsara ko ta jagoranta ko kuma ta bada
gudunmawar faruwar badaqalar cikin kamfaninsu.

"Ya Allah.....how?......diya mace da wannan aikin?,aikin fashi da makami fa kenan a
miqaqqiyar hausa,fashi da makami na yanar gizo.

Shi a yanzun ma idan yace zai kamata yace ya kama wa?,ya gayawa duniya
kamfaninsa na tuhumar mace da kitsa shiga na'urarsu kuma suka kwashe kudaden
asusunsu?. Tabbas ya bari hakan ta faru ba komai bane ga kamfaninsu face zallar
faduwa da kuma sake nunawa duniya rauninsu muraran. To amma idan ya qyaletan kenan
taci bulus?.....jadda company ya zama marainar wayonta?.....jadda company ya zame
mata abun wasa?. Ya kamata ya dauki mummunan hukunci a kanta,irin hukuncin da ko
sunan jadda kadai taji zai gigitata ya dimautata ya kuma sanyata a
fargaba....ambatar sunan kadai ya zamowa kwanyarta da kunnuwanta baraza.

Sai yaji gaba daya tunaninsa ya karkata kan fitar kudin kamfanin karo
na biyu. Idan wannan ita ta aikata ya tabbatar ba zata sake dawowa ba a karo na
biyu gudun kada a kama na'urarsu har a samu isa ga inda suke,tabbas wannan karon
mikail shi ya aikata haka da kansa,don haka ya bude idanunsa yana sake jawo system
dinsa. Yanaso ya sani,yanason yayi bincike ta yadda komai zai tafi masa a daidai.

Cikin qasa da awa daya komai ya fito masa yadda yakeso. Ainihin wanda
kudin suka koma account nashi daga account din wanda aka bawa ajiyar sunanshi ya
fito baro baro da taimakon shigabannin bankunan da dukka suke amfani dashi,wanda
yakan nemesu idan buqata irin haka ta taso

"Rufa'i ahmad mu'azzam" Ya mamaita sunan yana zuba masa idanu.

"Wayeshi?" Amsar da bashi da ita,babu kuma me bayar da ita sai mikail,kasantuwar
hakan kuwa ya zama tilas a gobe mikail ya miqo kansa ko kuma shi yasa a kawo masa
shi.

Kadan yadan daki table din,sannan ya sake jawo wayar gefansa ba tare da
duba da yadda dare yayi ba. Duk da daren hakan bai hana a daga wayar ba da bugu
daya tak.

"Barka da dare sir" Aka furta da muryar dake nuna kiranne ya tasheshi daga bacci

"Barka abdus_samad....i have a work for you"

"Okay sir...." Ya fada yana watsakewa daga baccin nasa.

"Zan tura maka through email then sai muyi magana.....but ina buqatar bayanan as
soon as possible"

"Yes sir" Ya furta cikin matuqar bada girma.

Kiran ya katse don duk wani abu me muhimmanci ba kasafai ya fiya
magananshi ta waya ba,duk da layinsa yana da tsaro sosai......to amma ya sani a
kowanne motsi akwai maqiya abokan gaba da abokan burmi.

Komai ya tura masa,sai a sannan yaji idanunsa sun fara yaji yaji
alamun suna da buqatar bacci,dole ya tattare komai ya tafi ya kwanta don yana da
buqatar ya qarasa hada abinda dukka ya rage masa a gobe tunda jumaa bai fiya fita
office ba,koda ya fitan baya dadewa sosai,ga kuma alqawarin tafiya abuja da ya yiwa
farouq. Bayason ya sake karya alqawarin,duk da yasan farouq zai fahimceshi zai kuma
bashi uzuri fiye da yadda yake buqata ma.

A wannan yanayin kawai yaji ya kamata ya fara amfani da private jet
dinsa,sai ya lalubi me haqqin kula da zirga zirgarsa ya tura masa bayanai sannan ya
ajiye wayar yana nufar qofa bayan ya kashe komai ya kuma kwashe komai da yake da
buqatar fita dashi.


*******Duk wani motsi nata saman idanun sabreen din take yinsa. Tana sake karantar
duk wani yanayi na huda din. Zuciyarta na sake tsinkewa yana kuma saukar mata da
fargaba hakan. A duk sanda zatonta da zarginta ya bata akwai wani ne a rayuwar huda
din?. Abu daya dake sake gigita tunaninta da sanyata jin ya zama tilas ta nuna nata
salon maganar nan da ake cewa duk wanda ya rigaka kwana dole zai rigaka tashi.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 85


Ba wata kalma data sake hadasu da ita,har suka kammala shirin
makaranta,ta dauki jakarta kaman kullum,ta kuma fidda kudin transport dana break.
Wannan karon nadra ta miqawa a maimakon huda

"Ki kula sosai nadra......ana tashi kada ku tsaya ko ina"
"to adda" Ta amsa mata tana kama hannun haneefa suka fara takawa zasu fice.

"Nifa?" Huda da ta kasa fahimtar abinda sabreen din tayi ta tambayeta. Kai ta daga
a nutse ta watsa mata kallo. Sai ta janye idonta daga kallon da takewa sabreen din
saboda yadda idanun sabreen sukafi nata kaifi.

"Na dakatar da zuwanki makaranta" Amsar data bata kenan ta miqe,amsar kuma data
girgiza huda din.

Ta dakatar da zuwanta makaranta kamar yaaya?. Dakatar da ita daga zuwa
makaranta fa kenan yana nufin yankewar ganinta da bassam?. Idan haka ta kasance
kenan sunyi bankwana da bassam?,saidai ta zauna ta zuba idanu tana ci gaba da
rayuwa cikin wannan quntataccen gidan nasu da babu farinciki ko guda daya a
cikinsa?.

Bata sake bi ta kanta ba,dole kuma data gaji da tunanin taja qafarta
tana komawa cikin dakin,yayin da sabreen taci gaba da kai kawo tsakanin falon da
dakin,tana shirya zata kasance da huda a dakin tsahon wuni da kwanakin da zasu biyo
baya. Ta tabbatar idan ta lazimci hakan dole koma meye huda take boyewa ya fito
fili.

Tayi juyi tayi tayi juyi har batasan iyaka ba. A duka hukuncin abinda
yafi damunta shine yanke mata qofar fita. Fitar da itace hanya guda daya da zata
bata damar samun bassam ta kuma shaida masa sabon dokan da adda sabreen din ta kafa
mata. Ta yita zuba ido taga ko zata fita?,saidai yau qiyau miyau,banda toilet data
fita tayi wanka ta dawo ba inda taje,haka suka wuni tana sabgoginta don ko tayin
abinci batayi mata ba,sai data gaji don kanta tana rara gefe ta fada kitchen din ta
diba taci ta koma taci gaba da kwanciyarta.

Ko da akayi sallar isha'i tana jiyosu a parlor suna assignment da
sauran bitocin karatunsu kaman yadda suka saba. Ba wanda yabi ta kanta a tsakanin
su ukun. Gaba daya dakin dama gidan ya sake gundurarta ya kuma fice mata a kai. To
wai shin ita adda sabreen dakeyi mata haka?,ita waye ya takurata haka?,waye ya
dameta haka?,kullum Allah shike da kullum sai ta sanya qafa ta fita waye ya taba
dakatar da ita ballanta ya sanya mata dokar fita.

Miqewa tayi ta zauna bakin gadon nasu tana jan qaramin tsakin
baqinciki. Tana masifar son gadonta da jin dadin kwanciya akai,amma yau gaba daya
sai taji ta tsaneshi ya kuma fice mata a kai.

Wayarta dake haske ta jawo ta buda tana dubawa. Wayar na cikin
personal wayoyinta da ba kasafai take bari saqo ko kira a ciki ya wuceta ba.

"Kina da tafiya on Saturday da mushkur......ina fata baki manta ba?" Saqon da jib
ya tura mata kenan.

Yatsunta ta cusa cikin sumarta tana yamutsawa kadan kadan. Har cikin
jininta taji batason tafiyar,komai kuma ya fice mata a kai,to amma batasan dalilin
da ya sanya wani sashe na zuciyarta ke zugata yana gaya mata BAI KAMATA TA BARI
MASHKUR YACI BULUS BA,KODA DAGA KAN MASHKUR TA RUFE QOFA YA KAMATA YA DANDANI DACIN
QWACE ABU DAGA HANNUN ME SHI.

Idanunta ta juya ta kalli sashen dasu nadra ke zaune. A irin wannan
yanayin ma da take qoqarin fuskantar inda rayuwar huda ke neman dosa,sam sam bata
qaunar tayi nesa da kowannensu don sanya ido akan motsinsu

"Ko ta buqaci friday?,gajeriyar rana ce......sannan kuma tana da tabbacin zai
wahala ta rasa ticket din juyowa a ranar" Tayi zancan cikin ranta,don haka ta soma
rubuta tex tana turawa kowa tsakanin mashkur da jib da zai kula da komai.

Kamar jira akeyi ta kammala muryar ta mamaye ilahirin tsakar gidan
nasu. Da wannan madaukakin sautin nasa da babu komai ciki face takura wulaqanci da
kuma saukar azal akan duk wanda ta ratso dashi.

"Yau kuma akan waye da waye ta fada?" Ta fada qasan ranta,don tasan wajibi sunanta
a sahun farko. Bai taba shigowa gidan ya fita salin alin ba tare daya takalo wani
abu da ita ba,wannan ya sanya ko yaushe take shiryawa zuwansa da ko wanne irin
yanayi ma zayazo dashi.

"Kowa da kowa ya fito,maza da mata,yara da manya,yau dai Allah yayi arziqin me
arziqi ya dawo......rabon bawa da arziqi mutuwa......Allah ya lamuncemin
nima......ku futo yau arziqin rufa'i ya dawo,wanda yayi biyayya aci dashi,wanda
kuma ya bijire saidai yaga ana ci" Ya qarasa maganar yana bin dakunan da qofofinsu
suke a rufe yana bubbugawa.

A nutse ta maida idanunta kan su nadra da suma ita suke kallo. Tana
iya hangen wani boyayyen murmushi akan fuskar nadra din,da alama idan so samu ne
tanason fita ta ganewa idanunta kamar yadda ya gayyaci kowa ta kuma fara jin alamun
suna fita din,don muryar bibo har nan inda suke muryarta zaqwai tana karadi.
Batasan me yasa duk gidan nadra tafi kowa maidashi kaman kakanta ba. Ada muguj
balain tsoronsa sukeyi,amma yanzu kwata kwata bata tsoronsa. Duk sanda ta kwasheshi
idan yana tambotsansa ya dinga zaginta kenan amma ita ko a jikinta,hasalima dariya
take binsa da ita,yayi dukan yayi dukan sabreen tayi fadan amma ko a hancin
takalminta

"Kada wanda ya motsa,ku gama aikin da yake gabanku" Ta dan hade rai tana fada.
Idanunsu suka maida kan litattafansu suna ci gaba da aikinsu,saidai daga ita harsu
kunnuwansu yana tsakar gidan suna tsintar wasu daga kalaman kawun.

A qalla ya kusa mintuna arbain da shigowar gidan kafin suji an banko
qofar dakinsu.

"Barin hali sai mutuwa,miskili kafi mahaukaci ban haushi....halin ne ya motsa ko
baqinciki ake da komawata mawadaci?" Ya qarasa maganar sanda yake sako jikinsa
cikin falon yasha shadda dinkin babbar riga da 'yar ciki yanata bazata.

"Ko daya kawu......ina maka murna.....amma Allah dai yasa ba daga aikin da abban ya
hana bane...." Tayi masa shaguben data tabbatar kaf jama'ar gidan ba wanda ya isa
ya gaya masa hakan,wasu saboda tsoronsa wasu kuma saboda kwadayin abun duniya.

"Sannu ja'ira maras kunya.....ke harni zaki gayawa haka?,yo dani dake waye zaiwa
wani gori?,Allah na tuba ba har gwara nawa kudin ba gwagwarmaya da fargaba nasha na
kuma zuba nawa jarin kadan suka jawomin masu yawa?,ke nawa kika zuba kike samun
naki kudin?" Ya fada cikin bambamin daya sanua huda dake daki kwance yin bakam tana
jinsu,maganar kawun kuma ta sake tsaye mata a rai tare da sake jin wani baqon
yanayi akan sabreen din da yafi kama da haushi haushi da son shinfida tata
rayuwar......ita da aure ma zatayi?.

A hankali ta sauke idanunta zuwa wayar hannunta,maganganun kawun suna
mata wani irin daci cikin zuciya har zuwa saman harshenta. Ba wannan bane karon
farko daya jefeta da magana irin wannan ba muddin zata sako masa zancan
caca.....amma wannan din yayi mata zafi ne saboda ya ambata tsakanin su nadra da
huda da taketa qoqarin gano bakin zaren matsalarta.

"Kome meye dai sama'ila ya shallake......ba kuma zai sake zuwa tambayar komai a
hannun kowa ba.....kuma daga yau har na mutu sunana mawadaci.....munyi hannun riga
da talauci" Ya qarasa maganar yana wara hannayensa kaman me jiran wani yazo ya
rungumeshi.

Sai daya gaji ya sauke sannan ya gyara zamansa yana sake kallonta

"Yauwa......batun kudadenki.....zuwa nayi muyi lissafin abinda kk taba bani na
rage.....don bazan iya biya duka ba domin kuwa tattalin dukiya akeyi
yanzu......yauwa". Badon yanayin daya jefa zuciyarta ba tabbas murmushi ne zai
qwace mata,amma a yanzun sai kawai ta dubeshi ta dauke kai

"Bana buqatar komai a ciki.....hasalima dama kyauta na baka ba bashi ba" . Washe
baki ya fara yi yana shafa habarsa

"Aah......kaga farar diya irin albarka.....diyar da babu kamarta kaf haife haifen
da ahmadu yakeyi baiyi kamar taki ba har yabar duniya.....Allah dai yashi miki
albarka" Ya fada yana sake sakin dariya.

"To ni zan wuce......sai kunzo ganin hamshaqiyar fada ta tarewa nan kusa da kuma
qarin auren mata ta biyu". Kadan ta dubeshi,saita kasa cewa dashi komai,har ya juya
ya fice yanata sakin qarin bayani.

Hannu ta sanya ta dafe goshinta kadan,abubuwa da dama suna mata kai
kawo saman zuciyarta. Kwata kwata DUNIYARTA bata jinta daidai bata kuma kallonta
daidai da duniya kowa. Akwai abubuwa da yawa da takejin suna ba daidai ba cikin
rayuwarta......WAI SAI YAUSHE KOMAI ZAI DAIDAITA?.

_Tambayar data yiwa kanta kenan da bata da amsarta,wadda batasan wannan din shine
MAFARI na komai ba_

*******K'arfe goma na safe ne sanda yake takawa cikin farfajiyar gidan nasu. Sanye
cikin farin lallausan yadi daga lallausar auduga mafi tsada da daraja.

Fari ne qal yadin maras nauyi dake iya bayyana shatin fara qal din
vest din jikinsa sama sama. Kusan komai da yayi amfani dashi a yau din fari ne,tun
daga sutura takalmi da agogon fata me tsada dake daure a tsintsiyar hannunsa. A
irin wannan rana ma ta juma'a motor din hawansa yakan canza zuwa fara duka don
sabunta sunnar ta'ammali da farin abu.

Hularsa tana hannun me sunan malam dake tsaye daga gefe bayan ya karbi
news paper din daya kammala dubawa. Ameh ya sallama daya biyoshi da tray din teen
da zaitun da kuma jan inibi da bai zauna yaci ba,ya juya yana duban me sunan malam

"Ka shiryamin zama da shugaban gidan jaridu a gobe.....don yau din zamuje
abuja.....but zuwa yammaci zamu juyo"

"Okay sir" Me sunan malam ya furta,sai fu'ad din ya sanya hannu ya karbi hular ya
juya yana nufar qofa,abinda ya sanya duka guards dinsa tsaiwa don sunsan inda
zashi,mutum biyun daya saba tafiya dasu sukabi bayansa.

Dab da zai fice a gate din farko yaji tana qwala kiran sunansa da
shagwabar na tata

"Hamma......hamma na". Tun kafin ya waiwayo murmushi ya subuce masa duk da bai
shiryawa hakan ba. Yasan zaisha qorafi saboda haduwa da tayi wahala a tsakaninsu a
kwanan nan.

Barin hali inji hausawa sai mutuwa,tana isowa taja tunga kuwa tana tura
baki gaba

"Hamma.....kace kada na yarda da abinda BB farouq ya fada......kuma ni Allah alamun
nake gani". Wani lafiyayyen murmushi da ba kasafai ake katarin ganinsa saman
fuskarsa ba ya saki yana juya fuskarsa dama da hagu kafin ya tsaida dubansa saman
fuskarta.

"Amneeen hamma amneen anni......zaki yarda magauta su rabamu?" Kai ta girgiza da
sauri tana sake fuskarta qasan ranta kuma tana fata inama saddiq yana kusa yaji
yadda hamma yake ji da ita.

"Kwana biyun nan school ya saki gaba.....nima duka aikace aikace sun
tasomin......ko bakison mu bude company n jewelry sample din farko da zamu fara
fiddawa ya zama naki......kinsan sunan da zamu bawa brand din?" Kai ta sake
girgizawa cikin tsananin jin dadi

"To sai kin kawo cin hanci zan gaya miki" Yayi maganar yana juyawa tare da ci gaba
da tafiya.

Da hanzari ta tattaka ta cimmasa sukaci gaba da tafiya tare

"Please hammana.....ka gayamin cin hancin me kakeso?,kome kakeso hamma zan bayar"

"No....ki canka da kanki kawai ki bada din sai na gaya miki" Shuru tayi tana
zurfafa nazarinta na abinda ya dace ta bashin,dab da zasu fice a gidan tace masa

"Yauwa.....hamma........zanyi maka mata ka huta da gorin yaa farouq akan kaqi nemo
mata......na baka friend dita nasreen...." Dan rage speed na tafiyanshi yayi ya
waiwayo yana jefa mata harara da fararen idanunsa.

Ya yarda autanci da kuma quruciya suna damun amna din da gasken gaske,da
alama fa da gaske take,don daga yadda tayi masa maganar tana zumudi tare da jij ta
masa bajinta kadai zai gaya maka iya gaskiyarta kenan.

"Wannan ba cin hanci bane......saidai ma ki jawo komawa ta biyu da za'a bawa
product din" Hannu ta sanya tana rufe bakinta gami da zaro ido. Sai yanzu ta gane
tayi wautar,ta tuna sunanshi da farouq ke gaya masa,ta kuma tuna shi lamarin yin
budurwa ko zancan aure abune da bata taba gani ya zauna ya bashi muhimmanci ba.

Kunnenta ta kama daidai sanda suke isa qofar gidan wanda sam bata ma
kula da gidan da suke nufa din ba saboda yadda hankalinta ya dauku

"Am sorry hamma.....please,wallahi idan ka fasa yaa saddiq zaiyimin dariya".

"Ki canza wani abun.......but this" Sai ya girgiza mata kai yana maida dubansa ga
muhallin malam Sa'adu wanda bai ganshi wajen ba da alama ko ya zaga ne.

Tun daga shigowarsu gidan har takowarsu farfajiyar gidan idanunta
yana bisa kansu. A yadda tasan hali da dabi'arsa ya akayi yarinyar ta samu
sakewarsa har irin haka?,anya abinda take tunani kowanne dare kuwa bazai afku ba?.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 86


Ita kuwa ta yaya zata bari wani abu ya hada zuri'arta data hajiya
amina?. Muddin da rai da ruhi da kuma numfashi a gangar jikinta.... Koda zata rasa
komai data mallaka.......koda shine abu na qarshe da zata aiwatar cikin rayuwarta
ba zata taba bari wannan tunanin ya wanzu a kwanyar kowa bama bare akai ga haifar
tunanin a zahiri.

Labulenta ta saki zuciyarta na mata wani irin suya. Kwanaki biyu kenan
suna sanyata yin asarar komai data shirya domin su. Yaune cikar kwanakin da bokan
ya diba mata,muddin a yau ma nasara ta qwace mata to lallai zancan bokan ya tabbata
na cewa aikin aiki ne......muddin a yau bata samu yadda takeso ba batajin gobe
warhaka zata kasance a bigiren da take tsaye akai a yanzu......dole ta tafi plan B
da zafi zafinta kuwa.

"Zuwaira.......maza leqa ki gaya masa ya qaraso ciki amma shi kadai......bana ko
qaunar kallon fuskar yarinyar ballantana gangar jikinta ya shigomin cikin gida".

Sosai zuwaira taji nauyin aiken saboda ba qaramin kwarjini fu'ad din
yakeyi mata ba,amma ba zata iya musa umarnin uwar dakin nata ba.

Da bismillah a bakinsa yake shirin sanya qafarsa a step na farko da
zai sadaka da qofar falon zuwaira ta fito. Kai ya daga ya kalleta a nutse ganin
kamar an jehota,sai tayi qas da kanta cikin tsananin qanqan da kai ba tare data iya
hada ido dashi ba tace

"Maamah tace ka qaraso ciki.....amma so samu tanason ganawa da kaine kai kadai". A
nutse ya waiwaya ya dubi amna,suka hada ido sai ya zare idonsa daga kanta,ya miqa
mata hularsa yana cewa

"Riqemin yanzu zan fito" Bata musa ba ta sanya hannu ta karba,ta koma daga gefe ta
zauna kawai jikinta a sanyaye,don inda ya barta gida zata koma,sai yanzu ta tuna
gidan waye ta biyoshi?. Matar da totally ita tsoro take bata tun ranar data shigo
gidansu ta kuma ga abinda tayi musu.

Bai fasa duka addu'anshi ba kafin ya sanya qafarsa cikin matuqar kula
da takatsantsan. Tana zaune saman sofa qafarta daya saman daya tana kadata a
hankali. Ciki ciki ta amsa masa sallamar ba tare data masa wani dogon kallo ba. Ya
qarasa ya tsugunna cikin girmamawa yana fadin

"Barka da safiya.....kin tashi lpy?"

"Koma ka zauna muhammadu" Ta furta kai tsaye wanda baice komai ba ya miqe din ya
koma ya zauna sosai.

"Wacece mahaifiyarka ne muhammadu?" Tayi masa tambayar da wani sauti dake cike da
izza da kuma bacin rai. Kanshi ya daga ya kalleta suka hada idanu,ta tsareshi da
ido sosai da kuma tarin abubuwa daya gansu kwance cikin idanun nata.

"Kece" Ya amsa mata a gajarce.

"To amma banga alama ba.......banga alamar hakan ba......yanzu ace samuwar
farincikina daga gareku sai ya gagara?,yanzu ace samun kulawa da danuwarku a kaina
sai ya zamemin aiki?" Ta jefa masa tambayar da ba abinda tayi tasiri a kai sai tuna
masa da baya da tayi. Ta tuna masa sanda suke da tsananin buqatarta a daidai wannan
lokacin ta tattara hankalinta zuwa ga wani waje daban. Ya tuna tun shekarunsa basu
kai ya koyi wasu abubuwa masu yawa harda ma wadanda sukafi qarfinsa saboda rashin
samun kulawarta. Ya tuna yadda yake kasa yiwa mahaifinsa dake jiyya abubuwa da yawa
saboda bashi da qarfin da zai iya dagashi zuwa toilet da sauransu,saidai su zauna
shi kuka shima kuka. Sau tari

Please Login or Register in order to submit comment