You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan
hajja

"Laila tana lafiya......kuma zata ci gaba da kasancewa lafiya sumul a
hannuna......kinsan na iya riqon 'ya'yan jama'a" Ta fada hankalinta kwance.

Murmushin qarfin hali hajja ta saki,sannan ta jinjina kai

"Ai na sani mariya......mun tashi lafiya?"

"Lafiyarmu sumul qalau hajja....." Daga nan ta fada nazarin da wacce kalma zata
tunkareta. Idanunta ta daga tana duban maamah.

"Muna magana jiya sai kuma Kira ya yanke....."

"Eh wannan case din na gama solving nasa,saura fitar result"

"Zancanmu fa kan laila da fu'ad?" Hajja ta jefa mata tambayar kai tsaye,duk kuwa da
cewa ita kanta me bawa wani amsa ce.....saidai tanaso takai mariya inda take
buqatar aje.

Buda baki maamah tayi da nufin cewa wani abu......amma sallamar jarma
daya daga cikin masu gadin gidan yayi sallama daga can bakin qofar falon.

"Malam jarma ya akayi?" Maamah ta buqata sani sanda yake duqewa a wajen

"Baqi gareki hajiya......ban sani ba zasu iya qarasowa ko a maidasu?". Fuskarta da
dan mamaki take dubansa

"Baqi kuma?,daga ina?"

"Diyar ambassador Khaled mustapha ce,haka tace a gaya miki". Wani madaukakin mamaki
ya cika maamah din,ba ita kadai ba,hatta da hajja sunan yaja hankalinta qwarai da
gaske.

Miqewa maamah din tayi tsaye tana dubansa

"Maza ayi mata izini ta shigo......na tabbatar koma meye ya kawota nan,silar
haihuwar ALKHAIRI ne fu'ad" Ta furta tana jin wani irin alfahari da haihuwarsa fiye
da kowanne lokaci. Uwa uba tana yine da biyu,don ta tabbatar gaba daya hankalin
hajja yana kan abinda yake faruwa.

Sanye take da wani matsiyacin yadi da aka narkar da kudade masu nauyi
kafin siyansa da yagalgalashi,aka kuma yi masa dinkin fitted gown data zauna a
jikin laila......kai kace a jikinta aka dinkashi.

Yadda dinkin ya zauna mata a jikinta.....hatta da dagawar numfashi daga
cikinta da qirjinta kana ganin gudanarsa. Ba mayafi a jikinta,sai dankwalin
material din da aka mata wani dauri dashi saika rantse hula ce ta kafata. Wasu
nau'ikan dan kunne manya ne a kunnenta,wanda suke tafe da.manyan banguls da suka
dace sak kalar material din jikinta kamar a company daya aka qerasu. Highhill ta
sanya masu tsananin tsini sarqafe da igiyoyi,kaman yadda qwayar idanunta ke saye da
tafkeken glass daya kusa cinye rabin fuskarta. Labbanta kwance reras da lip
gloss,iya wannan kadai zai gaya maka tafiya akayi irin ta masu abun,ba wahalar
hanya tunda sararin samaniya ne yayi aikin.

Yadda take taku daya bayan daya tana takowa ciki,idanunta kan kowanne
sashe na parlor din tana yaba alatun da aka zuba.....haka bakinta ke bada satin qas
qas na chewing gum din da take taunawa cikin bakinta.

Tana daga tsakiya,gefe da gefanta kuma fitattu kuma manyan qawayenta
ne,lubna da jalilah,daga bayanta kuma masu aikinta ne data taho dasu suma guda
biyun.

Fuskar fareeda ba boyayyar fuska bace musamman idan kaidin ma'abocin
kallon news ko dabdala a social media ne. Kusan duk wani motsi na mahaifinta ko na
siyasarsa zaka ganta a ciki zaka kuma tsinceta a ciki dumu dumu.

Lafiyayyen murmushi ya kubcewa maamah,ta taka a hankali tana
marabtarsu. Doso sun da maamah tayi shi ya sanya laila cire glass din fuskarta
dukka a qoqarin ta na nunawa girmamawa ga maamah din.

Cikin qasa da minti biyar suka yiwa kansu mazauni a parlor din,sannan
kuma gabansu ya cika da nau'in kayan ciye ciye daban daban na alfarma.

"Nasan zakiyi mamakin zuwana wajenki maamah?" Ta fada tana qoqarin karyar da
muryarta.

Kai maamah ta jinjina,tako ta ina tanajin wani girma yana hawa kanta53


_Daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace:mazan Allah S A W ya ambaci ranar
juma'a,yana cewa "A CIKINTA KAWAI WANI LOKACI,BA WANI BAWA MUSULMI DA ZAI RUSKETA
YANA ME TSAIWA YANA SALLAH YANA ROQON ALLAH WANI ABU FACE SAI ALLAH YA BASHI ABINDA
YA ROQA DIN". sai manzon Allah yayi nuni da hannunsa na qanqantar lokacin (ma'ana
baida tsaho,Allah yasa muna cikin wadanda zamu yita ruskarshi)_
"Eh to.....zai iya kasancewa abun mamakin ta wani fuskar,ta wata fuskar
kuma ba abun mamaki bane,musamman idan kikayi duba da irin kalar zuri'ar da Allah
ya bani" Tayi maganar da nufin jifa ga ma'anoni guda biyu tana gyara zamanta.

Kai laila ta jinjina tana tsare maamah da ido,tun kafin tazo ta hadu da
ita tasan wacece ita,don haka ko sau daya bataji d'ar ba na samun nasara ta
hannunta ba.

"Ko zamu iya kebewa muyi magana?" Laila ta fada tana duban maamah.

"Me zai hana?,bismillah" Maamah ta fada tana miqewa,sannan ta fara takawa,sai kuma
ta tsaya tana duban hajja,wadda keta kokawa da zuciyarta akan tayi abinda ya kamata

"Yi haquri hajja.....zamu gana,yanzu zamu fito" Ta fadi mata tana sakin wani
murmushi dake dauke da ma'anoni da dama. Sabon mariya ne......jifan maqiyi da
murmushi ko kuma abokin adawa,wannan shine kusan makami na farko da take fara yaqar
zuciyar abokin burminta,yayi tsammanin ita din wawiya ce.....itadin ba wani abu da
zata iya,saidai kuma daga qarshe reshe ne yake juyewa da mujiya,sai taje maka da
wani irin kalar farmakin da zaya kaika qasa koda baka shirya hakan ba. Bata da
cikin mutanen da mariyan zata iya farmaka ta haka har kuma ta samu galaba,saboda
sanayya ce ta kar da kar,ba wani abu ko hali nata da zata layance mata dashi.

Dan madaidaicin parlor din shima sai daya ja hankalin laila,duk da ba
wani baqon abu a ciki wanda bata sani ba.....amma yanayin tsarin da yadda aka zuba
komai luxury ya bala'in shiga ranta. Wannan karon maamah ta fahimci haka,saita
jefeta da murmushi sanda take zama tace

"Hala kema ya burgeki?,aikin muhammaduna kenan.....komai nasa me tsari ne". Lumshe
idanu laila tayi tana sake ji yana kuma shiga ranta,jini da jijiya harma da
b'argonta qaunarsa tana sake ratsata

"Inama zaki lamuncemin na zama matarsa.......bisa farashin dala dubu d'ari" Ta
furta qasa qasa tana kallon maamah.

Zubawa laila idanu tayi sosai tana jin sautin muryarta yana zagaya
dakin,duk kuwa da cewa ta kammala taqaitaccen bayanin nata dake qunshe da saqo me
tsananin nauyi.....ci gaba tayi da kallon laila tana son tantance Gaskiyar abinda
ta fada ko kuma akasin hakan.....magana ake ta kusan million dari da hamsin ko da
sittin fa......kawai don tanason fu'ad?,kawai don tanason ta aureshi?.

Wane sashe na zuciyarta da kwanyarta da yake da kaso mafi girma wajen
tsara mata komai ya harba,wannan ya sanya duk wani abu data shirya ambatawa ya
wargaje,take ta sauya yanayin fuskarta daga me yalwar fara'a zuwa tsukakkiya

"Wane irin magana ne wannan?,ance miki neman kai nakeyi da yaro na?" Tayi maganar a
dake cikin qoqarin nuna bacin rai,da kuma tankwabar da tayin gwaggwabar garabasa da
ribar da zata iya samu.

Ga mamakinta murmushi laila ta saki,hankalinta kuma a kwance ta koma
tayi relaxing jikin kujerar tana duban maamah,sannan a nutse ta daga qafarta ta
dora daya saman daya tana ci gaba da dubanta.

"Karki wahalar da kanki.....kada kuma ki wahalar da shari'a,kada kiyi kaman bakison
kudi hajjiya......idan sun miki kadan kawai kice na qara miki,sai na qara mikin a
wuce gurin.....fu'ad kawai nakeso,kudi ba matsalata bace sam sam". Sake tsare laila
tayi da ido a karo na biyu tana karantar gaskiyar abinda take fada har zuciyarta.
Qwaqwalwarta ta lula zuwa duniyar tunani duk da bata barta tayi nisan zango ba.

Akan me zata bari tayi asarar kudin da take gani a gabanta yanxu
haka?,bayan tana da damar mallakarsu?. Tabbas akawai manufar turo laila da ubangiji
yayi cikisu a daidai wannan lokacin da take neman dukka hanyar da zata cisge
sabreen daga gidan fu'ad.....babu ko shakka laila itace macen daya dace ta maye
mata gurbinta.

Duka ma a ture ta batun kudaden da zata mallaka......babban abun
alfahari ne a yadda ubangiji ya yiwa yaronta kudi yabi sahun manyan masu kudin
africa ma gaba daya......ace kuma yau shine yake auren diyar mutum kaman ambassador
khaleed mustapha,wanda a muqamai dai na duniya tana jin ba wanda bai riqe ba,saidai
kuma a lahira idan ana riqewa.

Lallai ne ita mariya sunanta yana dab da sake fantsama cikin bakunan
al'umma.....qawaye dangi da 'yan uwa,tana dab da sake taka wani matsayi na zama
cikin manyan matan da fu'ad har yanzu yaqi sakar mata jelar macijin tayi wasa da
ita da kyau,....wannan shine mafarin da tauraruwarta ta gaza yin haske kaman yadda
takeso. Sunanta takeso ya zama cikin jerin sahun sunayen mata masu aji da sukafi
kowanne mata a africa da duniya ma wasa da kudi.....cikin jerin sunayen iyayen
attajiran 'ya'ya da kowanne taro ake kwadayi da rububin gayyatarsu,saboda sun zama
bangon sugar ko na zuma,masu yayyafin kudi in dollars not in naira......don tana
jin zuwa yanzu a arxiqinsa ita kanta tafi qarfin yin kyauta da naira.

"Ki rubuta dukka adadin da kikeso" Ta tsinci muryar laila tana fadi,saita sauke
idanunta akan abun rubutun da laila ta aje a tsakaninsu tana rutsata da idanu.
Maida dubanta tayi kan fuskar laila,duk da alamu sun nuna tasan wani abu a
kanta......amma ba zatayi saurin bada kai bori yahau ba haka da wuri gudun raini.

"Ba ta wannan nake ba.....kawai ina duba cewa mahaifinki babban mutum ne da yakai
kowacce uwa taso hada jini dashi.....ko don saboda shi zan shige miki gaba har ki
samu fu'ad.......amma samun muhammad ba abu bane me sauqi......da gareshi akwai
wasu tsauraran matakai,kamar yadda nima daga wajena akwai wani mixani da nakeso duk
matar da zai aura lallai saita cikemin su cif da cif......yanzu haka rashin cike
wancan mizanin daga matarsa ta yanzu ya sanya take fuskantar barazanar gutsirewar
aurenta daga yanxu zuwa kowanne lokaci"

"Daga yanzu zuwa kowanne lokaci?,ashe ma baki da guarantee......ashe baki da
tabbas?" Laila ta fada da narkakkun idanunta dake nuna yadda suke da kyakkyawar
alaqa da kayan maye


"Ai kawai kiban wannan kwangilar.......nan da jibi ko gata.....kwanaki uku idan
sunyi yawa zata zama tarihi a rayuwarsa......shiga cikin mutane xai
gagareta......bama ita kadsi ba,haka dukka wani dake da nasaba ko alaqa da ita"
Tayi maganar da cikakken qwarin gwiwar daya sanya maamah tsayawa ta xubawa laila
ido.

Daga jin alwashin dake fita daga bakin laila kadai ya isa ya gaya maka
ita dinma wata akwai wani magana ta daban a kanta......itadin ma a shirye take

"Dole kema nayi takatsantsan dake.....aminta dake haka lokaci guda babban kuskure
ne......amma dole na fara miki da karin maganar nan da hausawa ke fadin DUK WANDA
YA RIGAKA KWANA DOLE YA RIGAKA TASHI.

Murmushi ta sake mata tana dubanta,ta sake yalwata fara'ar dake saman
fuskarta tana kallonta.

"Wannan ba wani abu bane da zai zama matsala......na baki wuqa da nama.....idan
akwai wani information da kike buqata dukka a shirye nake na baki shi". Kai laila
ta jinjina tana sakin murmushi

" Zan iya gaya miki har fiye da abinda kika sani......ina da labarin abinda na
tabbatar ke baki sanshi ba". Ta qarashe maganar tana bude handbag dinta qirar
kamfanin Hermes ta zaro cheque.

Rubutu tayi samansa hankali kwance tayi kuma sign dinta,sannan ta
miqawa maamah. Kudi ne a rubuce kamar yadda ta furta zata bayar da farko,maamah din
bata gama wannan tunanin ba muryarta ta sake fargar da ita

"Wannan din somin tabi ne.....muddin kikayi nasarar zama surukata,zaki mallaki wata
power ta fada a ji a manyan gurare da dama ta hannun mahaifina".

Komai ganinsa maaamah ta dinga yi kaman cikin mafarki,duk da ta
tattara dukka mamakinta ta hadiye don ba buqatar laila ta karanci komai.

"Zamu iya ganawa dashi a yau?" Laila ta tambaya maamah tana jin kwadayin ganinsa a
daren yau.

"Baki da matsala da wannan"

"Zamu wuce masauki yanzu haka don mu huta sosai,bayan magrib sai na dawo,hakan
yayi?"

"Yayi" Maamah ta fada tana daga zaune har yanzu,don mamakin da taketa boyewa yaqi
barin zuciyarta. A gabanta Laila ta miqe tana fita daga parlor din,maamah kuma ta
rakata da idanu.

Tana fita daman jira takeyi,ta miqa hannu ta jawo cheque din tana dubawa

"Da gaske adadin ta rubuta,akwai genuine din signature nata da komai?" Sake
jujjuyashi tayi a hannunta,sai kuma wani murmushi ya qwace mata.

"Lallai ni mariye me sa'a ce,ko rashin samun fu'ad a hannu akan lokaci na yarda
lokaci kawai ne baiyi ba" Ta gayawa kanta da kanta tana gyara zamanta sosai tana
jin kamar kanta zai fashe saboda wata izza da take saukar mata har tsakiyar
ruhinta. Ta zubawa guri daya idanu murmushi na fita daga fuskarta lokaci bayan
lokaci. Yau da wacce irin sa'a ta tashi?,wacce addu'a tayi yau?,babu....shine amsar
data bawa kanta da kanta,don ko basmala cikakkiya bata jin tayi tun daga safe kawo
yanzu.

A dan fusace ta juyo jin an murda qofar ana shigowa,saboda ita din bata
sakarwa kowa da kowa shigo mata guri kai tsaye ba....ko waye kai saika nema izini
ta kuma baka.

Idanu suka zubawa juna ita da hajja,saita janye cheque dinta tana
lanqwasheshi ta daga pillow din kujerar gefanta ta saka a qasansa. Idanun hajja
yana kai,abun kuma ya sake haifar mata da wani matsanancin bacin rai. Iya wannan
abun da mariya takeyi kawai ya isa gaya mata komai daya faru ya faru ne bisa son
ranta da kuma zabinta. Tunda suke da mariyan ba rufa rufa irin wannan
tsakaninsu......tayi baqi ta kasa ganawa dasu a gabanta?,taga takarda duk da
batasan ta mece ba amma mariyan ta jata ta boye?.

"Kinga surukarki ko?,diyar ambassador khaleed mustapha" . Maamah ta sake maimaita
abinda tasan already hajjan ta jishi.

"Musaddiq ne kenan shima????". Kai da maamah kr girgizawa ya hana hajja qarasawa.
" Fu'ad dai,d'ana fu'ad ". Da wani mahaukacin mamaki hajja ke bin maamah dake doka
murmushi da kallo

"Kinga Kalar surukan da ake fatan samu......wadanda za'a ciccibi juna....ba wadanda
suke hangen turmusheka kai da mafarkinka ba.....maciya amana masu fatan kayi
gyangadi su kafta maka sara.......zan shiga ciki in huta,ina da baqi
anjima......idan kin gama ki rufe gurin.....karki damu kanki da lamarin
laila......dama haka rayuwa take.....ka riqe dan wasu kaima a riqe naka,duniyar
juyawa take haka da sauri........su madeena sun isheki zama.....ni kuma laila kadai
ta isheni" Tana qarasa maganarta ta fara takawa zata fice54


_Daga nana aisha RA tace,manzan Allah S A W yace: "anayin wanka akan abubuwa guda
biyar,janaba....da wankan juma'a...da idan anyi qaho,da wankan mamaci(mutum ya yiwa
gawa wanka)_




"Mariya!" Hajja da zuwa lokacin ta kasa riqe kanta ta kirata a hautsine

"Koda wasa......koda tsautsayi kada kiyi tunanin cutar da laila......karki manta
dukka sirrikanki a nan suke" Tayi maganar tana nuna mata tafin hannunta.

Murmushi ta kuma sakar mata sannan ta juyo sosai tana amsata.

"Wadannan sirrikan da kike da ganin sun isa abun tunqaho.....nabar miki su halak
malak kiyi yadda kikeso dasu.....laila kuwa a yanzu mallakina ce,baki da hurumi a
kanta,idan kuma kina ganin zaki iya to bismilla,ga fili ga me doki,kinsan dakin
dana sanya aka sauketa ai" Ta furta tana nuna mata hanya,sannan ta juya hankalinta
kwance tana fita daga dakin.


★k'arfe biyar da rabi yammacin ranar jerin luxury cars dinsa sukayi
matsugunni a babban sashen ajiyar motoci na mansion House din nasa. Wani baqon abu
daya kwana biyu baiyi ba,wato dawowa gida a lokaci irin wannan. Dawowarsa da wuri
shine qarfe takwas zuwa tara na dare,wanda ita kanta matar gidan batasan lokutan
dawowarsa ba.

Kaman ko yaushe daga farfajiyar gidan ya tsaida kowa ya kuma sallami
kowa,wanda kusan quarters ne guda daga can wani sashe daban na gidan da yawancinsu
suke da nasu apartment din,ba lallai ma ka fahimci da wasu dake rayuwa cikin gidan
bayan ainihin masu gidan saboda nisan tazarar dake a tsakaninsu.

A hankali yake takawa zuwa ciki suna magana da farouq qasa qasa.

"Na fita daga company,kuma ina tunanin sai gobe zan sak shiga......wani irin
headache ne yake matsamin tun jiya......but daga dazun zuwa yanzu kaman ya qaru"

"Dude.....kana over work fa?,Allow your self downtime......kana da aure amma a suna
kawai......kasan benefit na aure kuwa da ba zasu qirgu ba?....Emotional support and
mental health duka zaka samesu if ka bawa matarka damar shiga rayuwarka"....


" Hey.....zaka fara ko?,waye ya gaya maka kowacce mace ake bawa dama ta shiga
rayuwarka?,wasu matan poison ne fiye da yadda kake kimantawa,they are wicked" Ya
fadi yana hadiye wani yawu lokacin da madaurin tunaninsa ya warware yana koma masa
can shekarun baya.....sanda maamah ta zama silar rasa lafiyar mahaifinsu duk da
kasancewarsa mutum ke kazar kazar,ta kuma zama silar barinsa sararin da suke kai
yanxu suke rayuwa akai wato DUNIYA. Daidai sanda ta sauka daga saman high chair din
data zauna a akai cikin kitchen din suna taba hira da ma'u,wadda take hada qullin
wainar shinkafa zata soya musu

"Bari na dauko na dawo" Tace da ma'u din tana gyara yafen qaramin Chantilly veil
din data lullube sassalkan gashinta. Furucin nasa ya sanyata tsaiwa cak sanda
muryarsa ta kaiwa kunnuwanta saqon da yake isarwa farouq,sai taja da baya tayi
tsaye jikin qofar yana jiran wucewarsa don ta wuce itama zuwa dakin.

"Let's try not to judge people and instead understand their perspectives".

"Am not judging fa......dude ba zaka gane bane,na iso gida.....i need to
rest.....call you later"

"Okay byee" Farouq ya fada yana sauke wayar iska ya furzar daga bakinsa yana duban
file din dake gabansa cikin katafaren kamfanin sarrafa kayan abincinsu dake sharada
industrial area. Yanaji a ransa zai sake rage kwanakin tafiyar nan tasu ko wataqila
hakan zai kawo kasuncin da yake fata tsakaninsa da ita. Yasha attempting saka amna
cikin abun,yasan zatayi aiki sosai.....saidai kuma amna din quruciya tayi mata
yawa,baisan ya zata dauki abun ba,uwa uba yana buqatar yayi komai cikin sirri.

Shurun da taji cikin parlor din ya sanyata tunanin ya wuce,ta sauke
siririyar ajiyar zuciya,kunnuwanta na maimaita mata da meye da meye ya fada akan
mata?. Siririn tsaki ta saki zuciyarta na siffantashi da jerantashi cikin sahun
mazan da sam bausan mutuncin diya mace ba....suke mata kallon kuma wata halitta da
bata da wata daraja kwata kwata.

Siririn tsakin daya sanyashi daga kansa a hankali daga rufe bottle na
ruwan da ya tsaya ya bude yasha saboda yadda maqoshinsa ya bushe,yana ji kamar
bazai iya qarasawa saman ba.

Guri daya idanunsu suka hadu,ya kafeta da qwayar idanunsa da sukayi
wani laushi tubus saboda yadda ciwon kan ke sara masa lungu da saqo na cikin kansa.
A hankali ta zare nata idanun daga kanshi,sannan ta koma da baya zuwa kitchen din
ba tare data qara koda second uku a wajen ba.

Kansa shima ya dauke yana ajiye robar,sannan ya soma takawa a nutse
yana wucewa ciki kafin ya haura zuwa saman. Tun daga wancan ranar bai qara ganin
gilmawarta ba cikin gidan,wasu lokutan ma sai yaje gaida anni ta tambayeshi iyali
take fado masa a rai. Wani irin mummuna fito na fito yayi da kansa akan damuwa da
abinda tayi masa a ranar din,yana ganin bai cancanci ya sanya damuwarta a ransa har
haka ba.....sai ya sake qarawa kansa wani busy din akan wanda yake ciki,yana saka
ran wannan ya zama silar mancewarsa da komai,wanda yawan ayyukan da suka zarta
qa'ida din daya azawa kansa yake kyautata zaton shine silar wannan ciwon kan da ya
fara fama dashi.

A gajiye da wani irin bacin rai da baisan meye dalilin faruwarsa ba daga
shigowarsa gidan ya dinga zare suit din jikinsa yana zubarwa,duk da cewa ba
al'adarsa bace hakan.

Bathroom ya wuce kai tsaye,ya hada ruwa me dumi da zai dace da
yanayin sassanyar iskar dake kadawa,wanda asalinta hadarine daya hado,bai saukar da
ruwan ba,amma ya canza kala zuwa ruwan toka,ya kuma bada iska me sanyin dadi dake
busawa da qamshin qasa,yanayin da yake bada tabbacin anyi ruwa a wani gurin kusa da
kano.

Mintuna kusan arbain ya fito daure da towel,gargasar jikinsa dama
sumar kansa duka sun jiqe da ruwa. Faffadan qirjinsa dake lullube da gargasa ya
fara gogewa da towel din yana isa gaban madubi,daidai sanda yaga wayarsa na haske.
Kaman ya share saboda bayason doguwar magana,amma koda ya duba yaga maamah ce sai
ya zamana bashi da wani zabi daya wuce ya daga kiran.

Sai daya zauna saman bean bag chair din dake ajiye a gefe sannna ya daga
hade da sallama.

"Barka da yamma" Ya dora da fada yana lumshe idanunsa saboda yadda kansa yake
sarawa.

"Barka kadai......kana office ne?,inason ganinka idan kun tashi,akwai muhimmiyar
magana da zamuyi da kai,sannan akwai baqi da sukeson ganinka" Ta fada kanta tsaye.
Yatsun hannunsa da baya riqe da wayar ya cusa cikin sumarsa,yanajin yadda ta jero
buqatunta kai tsaye ba tare da neman jin uzuri ba.....ya ya wuni?,akwai
damuwa?,yana da lafiya ko babu?. Baisan sai yaushe wannan dabi'ar tata na damuwarta
itace kadai damuwa zata sauya ba.....baisan sai yaushe zata damu da damuwar wani ba
ta aje tata damuwar da son kan a gefe ba.

"Bana company na dawo gida....."

"Okay,to ya za'a yi kenan?,don duk yadda za'ayi inason ganinka lallai lallai a yau
din,ko meye kakeyi ka katseshi kazo ka sameni" Ta sake fadi da dukka sautin da zai
gaya masa da gaske take.

Jaririyar ajiyar zuciya ya sauke yana cire yatsunsa daga sumar tasa

"Ciwon kai nake maamah.......amma zansha magani na kwanta zuwa anjima zan shigo" Ya
fada da raunanniyar murya,yana jin har qasan ransa ya rasa wani part me girma a
rayuwarsa,yanajin ya rasa wani abu me matuqar muhimmanci a rayuwarsa. Duk da yana
da anni,yana da farouq,yana da saddiq da musaddiq,amma lokuta da dama yana jin
kamar shi kadai ne.....yanajin kamar shi kadai yake rayuwa a duniyar,wani irin
maraici da kadaici yana mamayarsa.

"Allah ya kaimu,kada kayi dare da yawa Allah ya sawwaqe" Ta hade maganar duka
lokaci guda.

Ya jima idanunsa saman wayar yana kallonta,zuciyarsa na tuna masa
abubuwa da dama ciki harda abbansu. Tun asali shike damuwa kuma shike kasa bacci
idan dayansu baida lafiya,koda ciwon baikai ya kawo ba. Tun da can ita din bame
damuwa da lamuransu bace,tafi damuwa da duk hanyar da zata maida taro ta koma sisi.

Sai daya bushe tas bai sani ba kafin ya miqe yana isa ga walk-in closet
dinsa,boxer kawai ya zura bayan ya mulke jikinsa da cream dinsa,ya kuma shafe
jikinsa da turarukansa,sai ya koma gefen gado ya zauna bayan ya balli wasu tabs na
saukar da ciwon kai ya sha,ya dauki remote guda uku,daya ya zuge duka labulayen
dakin dashi,daya ya kashe hasken duka fitilun dakin banda ta gefen gadon,dayan kuma
ya saisaita sanyin ac din yadda zai daidai da yanayin da yake ciki.

Cikin duvet ya shiga ya duqunqune yana lumshe idanunsa gami da sauke
nannauyan numfashi,ya lumshe idanunsa yana son fatattakar kowanne tunani da lissafe
lissafe ko zai samu brain dinsa tadan huce.

Ana kiraye kirayen sallar magariba ya farka daga gajeran baccin daya
daukeshi,yaji dadi sosai a jikinsa,sai ya wuce toilet yayi tsarki ya daura alwala.
Masallaci ya wuce kai tsaye,akayi magariba da ishai duka dashi,sannan ya dawo ya
shirya cikin tattausar exclusive Morocco ta maza me zuwa hade da wandonta. Kalar
royal blue ce,sai akayi mata ado da gold zare daga wuyanta hannu aljihu qasan
wandon da tsagar gefe da gefe na rigar. Wata zagayyar hula ya dora saman kansa
ruwan gold din,wanda yawanci yankin larabawa su sukafi ta'ammali da ita,take farin
bafullatanin nan muhammadu jikan jadda ya fito da wani irin kyau da zai wahala ka
kalleshi

Please Login or Register in order to submit comment