You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsoro na ainihi irin wannan ba.

Qofar data hanga ya sanya taji relief,ta goge fuskarta ta mmiqe a
hankali cikin sanda tana nufar qofar ko zata samu wata hanya da zata fice daga
cikin gidan zuwa bakin gate.

Tana miqa hannunta tana riqe handle din da zummar bude qofar daidai
lokacin shima ya bude qofar da dan zafin nama,abinda ya sanyata ta biyo qofar
takuma yi kyakkyawan masauki a jikinsa.

Dif shi da ita wuta ta dauke musu,ita gaba daya tayi mutuwar tsaye je
zuciyarta na wani mahaukacin bugu cikin saddaqarwa kan ta shiga hannun koma
waye......yayin da shi kuma ba zatar fadowarta jikinsa ya sanya komai ya tsaye masa
can na wucin gadi.

Hannunsa ya sanya ya janyeta gefe yana hade rai da wani mugun
miskilanci,ya hade girar sama data qasa yana dubanta sanda ta samu ta dafe kitchen
cabinet din don ya taimaka wajen tsaiwa

"What's this?" Ya furta a dake yana hade rai. Can qasan ransa yana jin haushi
haushi yana saukar masa. Da biyu ta fada jikinsa ko meye?,ko tsabar sabawa da hada
jiki da wasu ne?,a yanzun an turketa kusan wata guda ba tare da d'a namiji ba ta
kasa daurewa?.

"Ya kamata ki saita kanki,nan din ba irin sauran guraren da kika saba rayuwa
bane....ki koyi controlling feelings dinki" Abinda yace da ita kenan yana takawa
zuwa gaba hadi da miqa hannunshi yana bude drawers din sama.

Sosai ta tattara dukka dauriyarta da nutsuwarta ta dawo da ita gangar
jikinta tana ta kokawar hadiye tsoronta. Wani irin takaici ya kamata bayan data
fuskanci shine. Ya akayi tayi gangancin gaza gane shine ya dawo?,bacin rai ya
hanata komai,sai kawai ta juya tana takawa zuwa qofar data kulleta da hannunta ta
fara bude key din da wani irin zafin nama.

Duk da a rude take amma tasan sau biyu ta murza key din,yanzun ma sau
biyun ta bude amma kuma data tura sai qofar taqi budewa. Sake murzawa tayi daya
biyu har sau uku amma ba alamar qofar zata budu. Wasa wasa haka ta sake gwadawa
amma jiya i yau,sai taji gudun zuciyarta na qara daduwa,don burinta kawai shine ta
fita a kitchen din.

Tayi iya duka qoqarinta amma ko gezau qofan baiyi ba,wannan ya sanya
duk wani karsashi nata ya sulale,ta zame hannunta daga jikin qofar zuciyarta fal da
tunanin ta yaya zata juya tabi ta daya qofar bayan yana kai kawo a kitchen din yana
harkokinsa?.

Duk wani motsi nata yana ankare dashi,har yadda ta dinga qoqarin bude
qofar amma taqi koda motsi. Idanunshi jifa jifa a kanta sanda yake kai kawo
tsakanin store din yana duba abinda zai iya sarrafawa da kuma dawowarsa kitchen din
ya fara marinating kifi da zummar ya gasa shi,abinda ya manta rabonsa da yayi. Ya
kammala cikin sauqi,saboda akwai komai kawai zubawa zaiyi ya saka a oven ya saita
masa lokaci,sai ya saka din ya saita time ya koma ya jingina da kitchen cabinet din
yana harde hannunsa a qirji yana jiran time ya cika yayin da yake sauraren voice
note din da ya tarar daga William.

Da fari baiko kalli sashenta ba koda sau daya kuwa,amma a hankali
sanda hankalinsa yayi nisa da sauraren voice din sai kunnuwansa suka sauko masa
raguwar sautin yunqurin bude qofar da taketa yi.

A nutse ya daga idanun nan nashi dake da wani irin shape da yanayi me
daukan hankali ya saukesu a bayanta daya fidda cikakken shape dinta saboda yadda
kayan suka zauna mata cif da cif,daga kafafunta zuwa qugunta yayin da qugun zuwa
cinyoyinta suka bude sosai suka bada wani faffadan qugu da yalwatattun cinyoyi.

Vintage scarf din dake kanta ya zame ba tare data sani ba,saidai yana
maqale a wuyanta,wannan ya sanya har clip din kanta pink color daya matse gashinta
ya rage tsahonsa da yawansa ya bayyana.

Baisan me ya maida idanunsa saman mazaunanta ba da suka bayyana
sosai saboda silk material din dake jikinta,uwa uba kuma rigar bata qarasa rufe
mata su ba. Abinda ya fara fado masa shine hirar amna da wasu qawayenta daya taba
tsinta dake maganar maganin hips da sauran wasu hanyoyin qarawa mace hips.

"Ita dinma ba zata kubuta daga amfani dasu ba......" Ya furta a ransa bayan da
zuciyarsa ta tuna masa wacece ita?.

"Allah ne yasan maza nawa ne suka taba kai hannunsu wajen,maza nawa ne suka taba
taba wajen sukasan ya fadi da tudunsa yake" Wani mahaukacin tsaki daya cika kitchen
din yaja,wani mummunan bacin rai yana saukar masa. Hannayensa ya saki kawai yana
komawa zuwa bakin oven din yana jin zaman kitchen din yana gundurarsa. A duk sanda
ya tuna iya shekarun haihuwarta a duniya da tayi kwata kwata na shekara ashirin da
hudu cikin ta ashirin da biyar......da kuma adadin yawan mazan da akace masa takai
qasa ko kuma ta taba mu'amala dasu,duk sai yaga ta masa baqiqirin,sai yaji wani abu
ya tsaye masa a rai idan ya kalli koda gilmawarta ne

"Idan tasan me yawan sha'awace me ya hanata ta fadi gaskiyarta a gida ayi mata
aure?" Ya sake rayawa a ransa.

Kwata kwata baya cikin jerin mutanen dake da ra'ayin riqau akan
yaransu mata na sai sun gama karatu kafin a aurar dasu. Ya dauki izinina daga yadda
yanayin halittarshi yake......wanda hakan yana daya daga cikin abinda ya sanya ya
maida kwanyar da zata tsarta masa tunani na sha'awa a ransa cikin muguwar hidima da
sabgar da idan ba mugun qaddara ba baida time da zata dauki wannan feeling din ta
harba zuciyarsa har zuwa sassan jikinsa. Saboda kwata kwata bai shirya aure
ba,totally mata basu taba burgeshi ba.....uwa uba bai tsara tsomasu a rayuwarsa nan
kusa ba,saboda abinda yake kalla kusan dukkaninsu dukiyarka ko nasararka suke aure.

(Kira gareku iyaye mata,a matsayinki na uwa ya kamata ki lura da yanayin kowanne
yaro da kika haifa,don dukkaninsu ke kika haifesu,don kamanninsu daya hakan bawai
yana nufin asalin halittarsu daya ba. Wani lokaci yaro namiji zaiyita nuna sha'awar
aure,amma sai a masa caaa ace ya fiya tsaurin ido......wani lokaci yarinya na nuna
wannan sai ace ta fiya rashin kunya da tsaurin idanu,ba tare sam da duba da cewa
halitta bace daga ubangiji,sai kuyi mata mummunar fahimta,aci alwashin sai an
turata jami'a,koshi yaran aci burin zuzzurfan karatu a kansa ko kuma sai yayi kudi.
Kuskure ne wannan babban,daga namiji har mace idan aka fuskanci haka tattare
dasu,idan tana da manemi nagartacce a aurar da ita yafi alkhairi,idan namiji ne
yana da halin riqe kansa,ko kuna da wadatar riqe masa matar kafin ya qarasa zama
mutum to a rufa masa asiri ayi auren a huta. Idan ba hali ko koya musu azumin
litinin da alhamis,su lazimci karatun qur'ani,yawan tunasarwa da wa'azi,duk juyi
kuma kada a dinga barinsu suna yawan kadaicewa a daki,a kusantasu da abokai na
gari,da zarar dama ta samu kuma ayi a aurar dasu,Allah ya iya mana ya tarbiyyantar
mana ameen summa ameen).

Cikin sa'a ya samu ya gasu,sai kawai ya sakashi duka har aluminum foil
din cikin plate,ya soma takawa yana hanyar ficewa ta daya qofar.

Har ya kusa qofa sai ya fasa fitan,ja yayi ya tsaya sannan a hankali ya
waiwayo,sai ya ware idanunshi a kanta yanata qoqarin kaucewa kallon guraren da yake
ganin bai kamata ya kalla din ba. Cikin jikinta taji kamar da idanunshi a
kanta,tuntuni taji ya tsaya da tafiyar da yakeyi abinda yake bata tabbacin bai fita
din ba. Bata qaunar koda wanzuwarsu a waje daya sam shi da ita. Haushinsa takeji
sosai,irin haushin da ko gilmawarsa batason gani ballantana qamshin turarensa.
Cikin dakiya da jarumta ta soma takowa da zummar gewayeshi ta fice ba tare data
yarda ta kalli ko gefen da yake tsaye ba ballantana tasan me ya tsaidashi din,tunda
dai taga ya shigo ta nan din ta tabbatar hanya ce duk da bata taba bi ta nan din
ba.

Sai da tazo daf dashi zata gotashi din,cikin ba zata ya sanya qafarshi
yana blocking duk wata hanya da zata wuce. Ta qasa ta kalli yadda yayi blocking din
nata,wani abu ya sake zuwa yayi mata tsaye a wuya,sai take jin ta dauki iya abinda
zata iya dauka daga gareshi,abun nashi kaman yanason ya qure iyakar haqurinta.
Bashi da masaniyar kakkaifar katangar qarfe da garkuwar maamah a gareta shi yasa
yake samunta a yadda ya so?,shi yasa yake samun daman juyata yadda yaga dama?,ko
yana tsammanin izzarsa da dukiyarsa da sunansa duka su suka siya masa wannan.

"Ka ban hanya zan wuce!" Ta fada adan zafafe tana jin zuciyarta kamar zata fashe.
Duka abubuwan da yayi mata basu isheshi ba?,yanzun kuma sai ya qara da tarwatsa
mata zuciya ta hanyar tsoratata?. Me yasa dole sai ya shiga harkan rayuwarta ne?.

Hannunsa ya goye a qirjinsa bayan ya ajiye glass dish din da hake
hannunsa yana dubanta. Kana kallon yadda Adams Apple dinsa ke sama da qasa kasan
Shima nashi ran ya fara baci. Ya sake gasgata komai a kanta,yadda kunya ke nuna
qaranci a tattare da ita. Yayi zaton zaizo ya sameta tayi laushi amma baiga alamun
hakan ba.

"Excuse me?" Ta kuma fada tana kafeshi da oily eyes dinta wanda ba kasafai ka fiya
gane da qwalla a ciki ko babu ba,saboda koda yaushe yanayinsu tamkar an diga mai ko
ruwa a cikin su haka suke.

Kanta ta maida gaba ta hade jikinta sosai da zummar rabe masa,saidai ya
hanata wannan damar,abinda ya sanyata sake tsaiwa kenan tana furzar da zazzafar
iska daga bakinta.

"Me kakeso ne?!......me kake buqata?,kome da kayi bai isheka ba?,ka kulleni for
good one month.....kayi disconnecting komai da kowa daga gareni......yanzun kuma ka
dawo kanason kasheni da tsoro?,me kake so?" Tayi maganar zallar bacin rai yana nuna
kansa a fuskarta,tana kuma jin radadin abinda yayi matan da gaske.

"Enough.....ya isheni!" Ta sake fada tana ware hannuwanta tare da fidda girman oily
eyes dinta a kansa.

"Am not your......."

"Just stop!" Yayi maganar da muryar data ratsa har cikin kwanyarta,ta kuma sanyata
runtse idanun dole

"Am not your mate......dole kisan da wanne harshe zaki dinga min magana!" Ya sake
maimaita mata a tsawace. Ji tayi kaman kanta bazai iya dauka ba,muryarsa tayi amsa
kuwwa akunnuwanta sosai da kalar tsawar data manta rabonta da irinta,sai kawai ta
juya da zummar koma yayane ya rabeshi ta wuce. Saidai kuma ina,yana ganin shirinta
ya sanya hannu ya riqe hannunta da zummar dawo da ita da baya.....don dole ya fara
saita mata harshenta kafin komai.

Cikin rashin sa'a dukka maballan gaban rigar suka fara balle kansu da
kansu saboda riqon da yayi mata. Abinda ya qara yawan adadin tashin hankalinta
kenan jin iska ta fara ratsa ainihin fatarta,abinda yake tabbatar mata da cewa
tabbas qirjinta tun daga sama zuwa qasa yana bayyana a waje.

"Leave me.....ka sakeni!" Ta tattara qarfinta tana fada cikin tsawar da batasan ta
yita bama saboda gigita da tsoron fitar tsiraicinta a gabansa,babban abun tashin
hankalin da hannu daya taketa qoqarin kamo rigar saboda daya hannun yana riqe cikin
nasa.

Tsawar tata ya sake rura wutar fushin dake zuciyarsa wadda keta
qissima masa abubuwa kala kala a kanta na irin hukuncin da zai mata. Ba'a saba masa
rashin kunya haka ba,don haka baima san me ya dace yayi mata cikin zafin nan ba,sai
kawai ya sake fincikota da qarfin da sai da taji hannunta ya amsa,batayi wata wata
ba ta fada qirjinsa gaba daya.

Bakinta yaqi mutuwa,ta tattara dukka qarfinta tana son tureshi tana
bayyana tsantsar fushinta cikin maganganunta,ransa ke qara baci,zuciya kuma tana
sake tunzurashi......yana da fushi yana da zuciya,amma ba kasafai ya fiya son
tashin hankali ba

"Shut your mouth" Ya fadi yana dubanta da kyau,saidai kaman bata ji ba,tana magana
ne ransa yana baci,ya sakeyi mata riqon tsauri ba tare daya damu da son qwacewa
takeson yi ba

"Zip it....Hold your tongue" Still fushin da take ciki ya hanata gane me yake
fada....zuwa lokacin hawayen da taketa tattalinsu sun fara yiwa kansu gurbi saman
fuskarta.

"Silence yourself......Don't annoy me!" Ya fada da husky voice dinsa......fushin da
yakeji bayason ya bari yayi hukunci a irin wannan lokacin,don haka kawai sainya
zabi riqe fuskarta cikin tafukan hannayensa da kyau yana furzar da iska me zafi
daga bakinsa a saman fuskarta,idanunshi kan lips dinta dake magana suna rawa,sai
kawai ya hade bakunansu guri daya.

Wata irin tsotsa yakewa lips din nata cikin salon fushi da bacin rai.
Tun a karon farko hankalinta ya fara dawowa kan abinda yakeyi saboda tsananin zafin
daya ratsa lips din nata. A lokacin ne kuma ta fara yunqurin tureshi ta raba kanta
da mummunan zugin da takeji saman lips din nata amma a banza,don ko motsawa baiyi
ba,bai kuma rabu da ita ba sai daya tabbatar taji a jikinta,lips din ya ninka
girmansa na asali......sannan yaja da baya yana dan tureta har sai data dafe
kitchen cabinet.

Qirjinsa sama da qasa yakeyi cikin mode na fushi da kuma mix na wani
feeling da yaji yana ratsa tsakiyar fushin nasa. Gefe tayi da fuskarta saboda kuka
daya taho mata sosai tana dauke dubanta daga cikin idanunsa da suka sauya launi.

"Im not getting into it na zauna ina miki explaining ko doraki a hanya......i have
many ways to punish you" Ya fada sautinsa yana rarrabewa kamar wanda yayi tseren
gudu ya gaji,sai ya fusgi dish dinsa yana ficewa daga kitchen din.

Duk da tasan ya fice din amma ta gaza dago kanta,don jikinta ta
tabbatar rawa yakeyi ko ta ina. Sai data kusa minti daya sannan ta motsa da nufin
fita itama tacan,amma sai taji QIT kamar an cire maqullin jikin wannan qofar aka
murda handle din aka bude sannna aka juya ana barin wajen.

Ko daga qamshin turarensa kawai ta gane shine ya bude,batayi wata wata
ba ta qarasa wangale qofar ta kuma taka tana fita ba tare da ta tsaya tantancewa da
mutum a falon ba ko kuma babu.

*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 31


_Daga abdullahi dan abbas R.A,wata kuyanga(baiwa)budurwa tazo wajen manzon Allah S
A W,ta gaya mishi cewa,babanta yayi mata auren dole,sai manzon Allah S A W ya bata
zabi(haquri da auren ko a raba)_
_____________________________


31



Idanunta a rurrufe ta tura qofar dakin nata ta shiga,ta kuma maida key
din ta rufe tana jin kamar zai sake biyota ne. Wani azababben kuka ta saki tana jin
yadda labbanta ke wani irin zugi kamar zasu cire daga saman bakin nata. Tako ta ina
tun daga saman labban nata har zuwa fuskarta dama qirjinta ba abinda suke fitarwa
sai wannan mayataccen qamshin nasa.

Ta jima tana kuka gami da murza lips din,tana fatan zugin da takeji ya
ragu.....har batasan iya adadin lokutan data shafe a haka ba. Qarar agogon dakin
ya sanyata maida idanunta da sukayi mata nauyi saman agogon,lokaci yaja.....saita
miqe da dan hanzari ta zauna.

Kaman yadda jikinta bai daina rawa ba haka zuciyarta da labbanta basu daina mata
zafi ba. Duka hannuwanta ta saka ta rufe fuskarta dashi tana ci gaba da sauraren
bugun zuciyarta.

"Ba lokacin wannan bane sabreen.....ba lokacin bata lokaci bane wannan,kina sake
bawa maamah damar kasancewa da 'yan uwanki ne kawai a kowacce daqiqa....lokacin
aiki ne tuquru yanzu don qwatar kai.....ki daina bari normal halittan namiji kamar
saura yana firgitaki......wanne iri ne baki gani ba?" Taji ana gaya mata daga can
wani sashe na zuciyarta. Abinda ya zaburar da ita kenan ta fara zame kayan baccin
jikinta ta daura towel ta wuce bandaki.

Wanka tayi ta dawo ta shirya cikin atamfa doguwar riga,ta gyara ta
matseshi cikin hair tie masu wani irin adon stones masu garai garai a jikinsu dan
madaidaita.

Bata saka komai a fuskarta ba,amma tayi wani irin kyau duk da ramar
da tayi,saidai kuma fatarta tayi fresh saboda zama waje daya da rashin bawa rana
damar qona fatarta,uwa uba har yanzu mayataccen gyaran jikin nan yana nan baibar
jikinta ba,batasan wanne irin rantsatsen hadi bane annin ta biya kudi akayi mata.

Duk da yunwar dake qwaqular cikinta amma sai taji sam ba zata iya zama
ba,hasalima duka tasirin yunwar ya gushe,kitchen take da muradin shiga ta shirya
abincin dare,wanda take fatan koda batayi na rana ba aqalla a samu na dare.

Da dan hanzarinta take fitowa daga hallway din,hankalinta yayi gaba
zuwa kitchen sautin muryarta ya dakatar da ita

"Adda sabreen" Amna da shigowarta kenan ta fadi fuskarta cike da murmushi. Suna
hada idanu ta sakar mata fuska da salon nata murmushin. Haka kawai tana tuna mata
da huda duk da hudan miskila ce ba kaman amna ba,amma sai take mata yanayi da
hudan.

"Yaushe kika shigo?,afwan ban sani ba ina ciki ina wanka" Ta fada tana neman gefan
wata kujerar daban ta zauna. Da murmushinta tace

"Adda sai an miki uzuri,matafiyi ba'a rasashi da gajiya a jikinsa,ni har zan kunna
wayata ma na duba wani assignment kafin ku samu fitowa" Kyawawan fararen idanunta
sabreen ta fiddo waje.

"Haba dai,ya zaki zauna kiyita jira,da kin qarasa kinmin magana ai". Bakinta ta
rufe da tafin hannunta

"Kinaso hamma ya ballan qafa?,ba'a shiga shiyyar dakinsa direct ai,BB farouq ne
kawai ya isa". Tabe baki tayi a fakaice,can qasan ranta tana fahimtar tsananin izza
gareshi da shegen mulki.

Fara sako mata zancansa da tayi yasa sabreen miqewa cikin qarfin hali
da son nuna komai lafiya

"Bari na baki ruwa kisha"

"Am full adda.....saidai na rakaki kitchen naga kaman kitchen zaki shiga" Kafada ta
daga da murmushi

"Alright.....muje"

"Yau hamma za'ayi full da abincin addana.....yadda yakeson abinci me dadi na
tabbatar adda na ba daga baya ba.....in fact ma tunda har kikayi nasarar samun
hamma na na tabbatar komai kin hada" Tayi maganar da dariya dariyar tsokana. Bata
ce mata komai ba,tadai qoqarta sauke mata murmushi kawai.

Sanda suka shiga kitchen din duk sai taji ta takura,ta rasa ta inda
zata fara,saboda idan maganar qwarewa ake ta fannin girki tasan bata cikin jerin
wadannan matan,infact ma ita ba gwanar shiga kitchen bace sam.....to ina ma taga
time?,tana ta abinda qannenta zasuci susha su lulluba sutura,suyi magani idan
lalura ta taso?. Tasan huda ta tsere mata sosai ta fagen iya girki,don tun tana
fita tana barinsu hudan tana musu tsumburin burin har tazo ta qware.

"Kaman ya kamata kiyi surprising hamma na ko?" Amna ta fadi da murmushi tana duban
sabreen. Kallonta kawai tayi kallon dake nuna alaman tambaya,sai amnan ta daga
kafada

"Gift dina na yau zan gaya miki best food nashi da daddare.....but nima zaki bani
tukuici ki gayamin sirrin skin dinki adda don Allah?" Ta qarasa fada a shagwabe.
Abun dariya yaso bawa sabreen saidai batayi ba illa murmushi data saki,ta kalli
fatar tata ta kalli amna,ita bataga wani kyau da fatarta tafi ta amna ba

"Seriously adda kina burgeni at the first time dana fara ganinki.....kawai naji
jinina ya hadu da naki" Ta fadi da gasken ta yadda a furucinta zaka fahimci da
gasken take.

Kusan tana zaune amna ta hada duka ingredients din na kalar abincin.
Ta miqe tana daura apron data gani tana bawa amna daya,sai qararrawar dake kitchen
din ta dauki tsuwwa.

Amna ce ta duba,saita waiwayo ta kalleta

"Kira ne daga bakin gate" Tayi maganar tana miqa mata wayar

"Ki daga" Tace da ita,ba musu ta saka a kunne,bayan wasu sakanni ta dawo da dubanta
kan sabreen

"Wai baqi ne dake.....zuwaira daga wajen hajiya mariya maamah". Maganar taji ta
bugu qirjinta don tazo mata kamar a bazata,sam ta mance da issue dinsu,sai ta fara
zare apron din tana cewa

"Kice a barsu su shigo" Yadda ta fada mata haka ta gaya musu,ta zare apron din ta
ajiyeta ta soma dosar kitchen din tana cewa

"Ina zuwa amna"

"Ba damuwa adda" Ta amsata tana matsawa kitchen din don ci gaba da aikin.

Kasa tsaiwa tayi daga cikin parlor din,ta taka har qofar qarshe wadda
daga ita sai balcony din da zaka sauka zuwa farfajiyar gidan. Tsaye tayi kawai riqe
da qofar,ba abinda ya hanata hango wajen sai lafiyayyen curtain din daya raba
tsakaninsu.

"Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta fara rasa falon kafin ta bayyana Laila na biye
da ita a baya da luggage dinta dake da girma,tana takawa d'ai d'ai,tana sake ganin
alatun da aka xubawa gidan,sai take ganin wancan zuwa bataga komai bama.
"Wa'alaikumussalam" Ta amsa mata idanunsu yana haduwa waje daya dana laila.

Wata faduwar gaba ta saukarwa lailan lokacin da idanunta ya shiga
cikin na sabreen dake tsaye tana jiran shigowarsu

"Kambu.....who's she?" Ta samu kanta da furtawa a qasan zuciyarta saidai kuma
labbanta a sarari ma rawa sukeyi.

Yanayin kallon da lailan ke mata sam baiyi mata ba,a nutse da wani
irin jan aji ta debe kallonta daga kan lailan tana maidawa kan zuwaira dake qoqarin
gaidata

"Basai kin tsuguna ba......ta nan ga qofa nan a nan din akwai dakuna a ciki,ku zabi
duk wanda yayi muku" Ta amsata a taqaice don ko tsaiwarsu a wajen sai taji bata
qauna. Tasan da qofar ne cikin ranakun zaman kadaicin data dinga yi cikin gidan


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 32


_Daga abdullahi dan umar R.A yace."manzan Allah S A W ya hana auren shigaari,shi
kuwa auren shigaari shine,mutum ya aurar da d'iyarsa ga wani,bisa sharadin Shima
wancan zai aura masa tasa 'yar,kuma babu biyan sadaki a tsakaninsu(musanye kenan)_

_bukhari da muslim ne suka rawaito_

___________________________

32


Tasan qofar ne cikin ranakun zaman kadaicin data dingayi cikin gidan da
kuma Yanayin wajen kuma tasan guri ne baqi na kusa bayan boys quaters da gidan ya
mallaka na musamman da yake daga can bayan gidan. Bata da matsala dasu,koda dakunan
hallway suka zaba kuwa,don kowacce rana a lissafe kwanakinta cikin gidan suke.

"To.....to madallah......bari mu qarasa" Xuwaira ta fada tana wucewa gaba laila
tana biye da ita. Duk wani taku daya biyu na lailan saisun hada idanu da sabreen
din wadda ke tsaye yana karantar yanayin kowanne a cikinsu.

Dauke dubanta tayi,sai ta koma saman kujerar falon ta zauna kawai
yanayin jikinta yana neman sauyawa.

"Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta sake ratso falon. Idanunta ta daga a hankali
tana duban zuwaira sanda take takowa falon riqe da waya a hannunta fuskarta a sake

"Ranki ya dade.....hajiya nason ganawa dake" Tayi maganar tana miqa mata wani
qaramin akwati da sabreen din ta kasa amsa sai binsa da kallo da tayi. Daya hannun
waya daya akwati,kuma dukkaninsu idanun zuwaira suna gaya mata ana da buqatar
karbar kowanne.

Cikin kwanyarta taji ana umartarta data karba,ba wani laka a jikinta
ta karba dukkaninsu

"Sirri yana da matuqar muhimmanci......hajiya nason sirri matuqa" Ta tsinci muryar
zuwaira tana gaya mata. Idanu ta waiwayowa ta zubawa zuwairan,sai kawai ta dauke
kanta tana nufar hanyar hallway don komawa dakinta.

Kaman ana jira ta shiga dakin

Please Login or Register in order to submit comment