You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta'ala wabarakatuhu yake d'iyar aljanna mabudin
arziqin ahalinta gaba daya". Bushewa da dariya huda tayi tana kallon kawun. Gaba
daya ya canza,quruciyarsa kuma sai dawowa takeyi saboda wadatar daya soma tsumbula
ciki.
"Kawu waye ya kawowa madeena?,kamar bakafi wata shida da komawa bafa" Huda da dama
can tasu bata jiquwa ta furta.

Harara ya dalla mata yana neman wajen zama gami da kalmashe carbinsa.

"Ni yanzu har ayimin maganar hawa gajimare da sauka......mutumin da yake da suruki
irin me jadda gidan gold da diamond?,to bari kiji yarinya,a yanzu haka aminaina
guda biyu dukkaninsu hajjin bana dasu Zamuyi gaba daya,albarkacin me
jadda.....albarkacin d'iyar da aka haifa tsiya tana bacci kariris". Neman wajen
zama huda tayi saboda kada dariya ta kayar da ita,kawun ya gama bata amsa daidai da
ita,saiyayi banza da hudan yana maida hankalinsa kan sabreen.

"Sannu d'iyata.....sannu 'yar nan.....ashe ni ahmadu da fateema suka haifawa ke ban
sani ba?" Ya qarasa fada yana matse hawayensa da wasu sabbin qwalla da suka fara
taruwa lokaci guda.

"Dama na dade inaji a jikina zanyi kudi.....na dade inaji a jikina zanyi arziqi
ashe ta sanadinki ne,ubangijin al'arshi yayi miki albarka,dukka gidanku yanzu ya
koma qarqashin kulawarki,masoyanki da maqiyanki,harda 'yan uwanki na dakin
aure,Allah ya qara miki riqonda zumunci da kuma zuciyar yafiya da afuwa"

"Ameen ameen kawu" Sabreen ta fada tana murmushi. Gaba daya kawun nata ya canza
kaman bashi ba,wata kamala duka ta saukar masa,ga alamun jin dadi da hutu duka
tattare dashi.

"Amma 'yar nan ya akayi haka?" Ya fada yana gyara muryarsa. Kai ta daga tana
dubansa

"Me akayi kawu?".

" Kinyi qoqari dai.....amma ci gaba ya kamata a samu ai,'yan hudu ya kamata kiyi
wannan karon,amma sai aka koma baya kikayi biyu,maimakon ki maimaita ukun?,kinsan
innarmu sai da tayi 'yan uku da 'yan biyu kusan kashi biyar,duka rasuwa sukeyi,ni
kadai da dan uwana ahmadu ne muka zauna,don ko babanki ai tagwaye ne,ni kuwa mu uku
ta haifa,amma ni duka na fisu qwarin qashi ni kadai na zauna".

"Kaine dai Allah baiyi niyyar kashewa ba kawu ba wayonka bane" Huda data goya baby
naseem da baby carrier ta fada duka cikin salon tsokana.

Daquwa ya watsa mata yana dubanta.

"Kinci ubanki.....banda kinci darajar mijinki da ya bani kyautar gida harda mota
satin nan daya wuce yau da sai na karbi goyon na aza a bayana naci qaniyarki sannan
na baki danki kici gaba da tafiya" Daga huda din har sabreen sai a sannan sukasan
saddiq ma yayi kyautar,ba zatar data kashe rigimar kawu da huda ya koma magana da
sabreen.


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 171


*_HUGUMA CLOSET ON TIKTOK_*
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1



171


"Allah ya sambada miki albarka,don Allah.........don Allah ki daure wata
shekarar warhaka ki sake tunkudo wasu hudun" Ido ta zaro da mamaki

"Da gaske fa kawu kake?".

" To me zaki tsaya jira?,banda rainon cikin bakisan wahalar komai ba?,shi kuma iri
kawai yakeso,ai faduwa tazo daidai da zama" Ya fada yana leqa fuskokin yaran.

"Tubarkallah wallahi.....haihuwar masu kudi daban data talakawa,su kansu yaran
daban naku suke da namu".

" Wallahi idan banbar dakin nan ba sai kawu ya sanya cikina ciwo.....adda bari naje
nima nayi sallah a masallaci" Huda ta fadi tana fita ta barsu.

Wannan karon halastacciyar walima jadda ya fara hadawa a birnin madeena.
Walimar maza daban mata daban. Jirginsa daya siya bayan wanda yayi kyautarsa na
JADDA WINGS 002 kawai ya bayar akayi jigilar 'yan uwa da suke cikin list na zuwa
umra a wannan watan aka gabatar da walimar tare dasu,ciki harda maamah,wadda akan
idanunta aka gudanar da komai.

Duk wani motsi na yaran nan guda biyar akan idanunta yake,ta saka
damuwa sosai a kansu tana ganin kamar zasu bace ko zaa daukesu,saidai tana komawa
daidai duk sanda ta tuna amincin da garin yake dashi.

Wannan karon Sabreen itama ta samu mahaifinta,wato AHAMD(Amaan),dan
uwanshi kuma yaci sunan muhammad da kanshi wato takwaran babansa (AMEEN).

Tuburewan tsokana Sabreen tayi.

"Hamma wannan son kai ne.....ni me yasa ba'a fara jira an saka me sunana ba?" Ta
fada tana turo baki gaba. Dariya ya saki yana murza yatsunta sanda take zaune tana
shayar da muhammad ameen din.

"Ki haifomin baby girl ki gani DUNIYATA.....ke kika mana addu'an boys,gashinan ta
shafi kowa cikin familyn jadda,duka maza suke haifa mana,muna da kwadayin mace
dukkaninmu amma bansan kusancinki da Allah ba da addu'arki ta riga tawa tafiya
ba.....at first nafison na samu daughters so samu.....don na basu tarbiyya na aurar
dasu,na kuma rabauta da rabon aljannar da manzon Allah ya yiwa duk wanda yayi irin
wannan aikin alqawarin samu". Dauke kai tayi tana sake tsuke bakinta cikin
shagwabar nan da bata jin ta girma da yinta,kamar yadda shima baya ganin ta girma
dayi masa ita.

"Amma dai it's not fair hamma......sai a jirani sai sanda aka samu baby girl din
aka saka ameenatu".

"Ameenatu ta zama wajib akan dukka diya mace ta farko data fito daga tsatson
jadda......take it easy maa.....ki qara himma next year by now ki ajiyemin girls"
Idanu ta zaro ta bishi dasu,sai ya jinjina mata kai cikin bada tabbaci.

"In sha Allah" Ya fada da yaqinin daya sanyata bata sake cewa komai ba.

Sabreen bata yarda ta koma ba saida jini ya dauke mata,ta sauke umra.
Addu'a tayi me tarin yawa akan rayuwarta data zuri'arta,addu'a ce me yawan gaske
akan zaman lafiyarta dana familynta gaba daya,qannenta 'yan uwanta dama duk wanda
yake da jibi dasu. Ta dade gaban dakin Allah tana neman me kyau a duniya me kyau a
lahira(Rabbana Aatina fiddunya hasanatan wafil Aakhirati hasanatan wa qina
azabannar/addu'a ce wannan me matuqar muhimmanci,ku dage kada kuyi wasa da ita). Ta
roqi Allah dawwamammiyar soyayya a zuciyar mijinta,da kariyar Allah daga jinsa
ganinsa da zuciyarsa dama al'aurarsa akan kowacce diya mace idan ba ita ba.

Cikin wani irin aminci sakewa da walwala take kula da yaranta dukka
guda biyar din. Tana da wadatattun masuyi mata hidima,yayin da ita kuma ta tattara
damuwarta dama kulawarta dukka akan mijinta.

Sai data warware sosai sannan yazo mata da komai da komai na
kammaluwar ginin gidan marayu maka maka har guda uku a arewacin Nigeria,da kuma
gina sabuwar foundation ta kula da marayu da zawarawa da yara marasa galihu.

Kukan farinciki sosai ta dinga yi,saboda cikar ragowar burinta kenan a
rayuwa. Wani irin katafaren gida ne da aka tsarasu bisa tsarin ginin unguwa guda
wato estate. Da makarantunsu tun daga primary har zuwa secondry,jami'a kuwa a qasar
waje yayi planning ya dinga turasu qasashen musulunci,don yana sanya ran a can
zasuyi karatu me kyau,ba tsangwamar mutane ba takurawarsu.

Komai an wadata gidajen dasu,abinci sutura wutar lantarki da kayan
more rayuwa cikin kowanne gida da dakuna. Cikakken tsaro da tsari na addinin
musulunci wanda aka ginashi bisa jagorancin malam da a yanzun shine babban me bawa
jadda shawara akan duk wani abu daya shafi zakka da harkokin addini cikin
rayuwarsa.

"Wannan gidan da komai dake cikinsa kuma mallakin su ayshatu ne......na kusa dashi
kuma na JIB ne,sai kuma guda dayan na busari" Ido ta waro tana mamaki,ya akayi
yasan su jib?.

"Maida idon ranki ya dade don ban gaji da kallonsu ba daga nan har qarshen
rayuwata......karki ce komai,tun daga randa na sameki cikakkiyar mace na bibiyesu
na kuma jawosu cikin rayuwata,yanzu haka busari shine shugaban drivers na
kamfanina,Jib kuma yana jagorantar sashen tsaro na daya kamfanina dake lagos" A
ranar idan farinciki yana kisa tabbas ta tabbatar sai buzunta. A yadda abubuwan
sukazo tana buqatar ma'aikata ita kanta,tana buqatar su zauna su qarasa tsara komai
kafin ranar da zaa qaddamar da qungiyar da kuma qaddamar da gidajen marayun dake
kano kaduna da abuja.

Sosai ta tsananta bincike cikin danginta na uba harna uwarma,ta kuma
zabi amintattu da zasu dinga gudanar da komai,nata aikin kawai tana daga cikin gida
xatayishi cikin system sai waya idan ta kama,sai kuma ziyara da duba gidajen lokaci
bayan lokaci da zata dinga zuwa,da kuma wani taron idan ya kama,kamar ganawa da
ma'aikatanta da sauransu.

Abinda ya bata mamaki shine,albashin da fuad ya sanya mata na million
din kudade. Abun ya qarasa kasheta da mamaki,itace shugaba,yayi dukka aikin ya
mallaka mata,ya bata dama ta sakawa kowa albashinsa kuma zata dinga
biyansa......sannan ita kanta kuma ya yanka mata albashin miliyoyin kudaden da
batasan ma me zatayi dasu ba.

Kuka kam wannan karon barinta yayi tayi abinta,ta shimfida fuskarta
saman kyakkyawan qirjinsa tayi kukanta yadda takeso ta kuma zarce da godiya ta baki
da kuma godiya ta aikace. A ranar ta saje yarda da kanta,ta haukatashi da wani irin
salo......ta sake godewa Bgawo's kitchen and aphrodisiac. Mama macace dattijuwar
qwarai data iya gyara a gargajiyance,saboda cikar hankali da shekarunta da takai
matakin dattijantaka,bata taba ganin gyara irin nata ba,gyara na dattawan tsofaffi
da babu side effects akai sai tsimuwa da jikinki zaiyi da kyau,wanda sun shigo
duniyar gyara ne saboda bada gudunmawa ga matasan mata dake tasowa cikin rayuwar
aure a yanzu.08127084190/08104553105.

Yana jinta da kima a rayuwarsa fiye da duk wani abu me kima daya
mallaka......yana jinta a matsayin abu mafi tsada da daraja a rayuwarsa,don haka
komai nata ya zama na daban kuma na musamman.

Wani tsaro yake bata,guards ya samar mata na musamman,wadanda suke tare
da ita a duk sanda zata fita ko zata tafi zuwa wani gurin. Ya samar mata 'yan sanda
mata biyu jajirtattu da zasu kasance da ita a motor din da take ciki,bayan 'yan
aikinta dake kula da lamarin yaranta,sauran motocin kuma duka guards dinta ne.
Cikin lokaci qalilan Sabreen din ta zama wata me tsada,komai nata kuma ya kuma sake
zama na musamman,ya canza mata mota tata ta hawa da duka sabbin motocin da masu
tsaronta zasu dinga using.


*_BAYAN WASU SHEKARU_*

*JADDA'S VILLA*


JADDA'S VILLA shine sunan dake rubuce b'aro b'aro daga tsororuwa babban
ginin gidan. Rubutun an yishi ne da ruwan GOLD jikin wani qawataccen allon qarfe da
aka yiwa wani irin design me azabar kyau da daukan hankali.

Wani irin shimfideden gida ne,wanda a qalla ya qunshi maka makan
mansions a cikinsa guda shida. Kusan komai na gidajen iri daya ne,saidai banbancin
girma da wani gidan yafi wani yawan dakuna da kuma qawatuwa da kayan alatu na
rayuwa,daidai da yadda mamallakan gidan suke da buqata.

Idan ka kira JADDA VILLA da aljannar duniya sam sam bakayi laifi
ba,don inda akwai sunan da yafi haka nuna tsananin tsari da cikar suffa da haibar
gida ya cancanci ka bashi.

Gidane daya mamaye jadda street gaba daya daga hannun dama,sai hannun
hagun dake dauke da qawatattun gidajen hamshaqai masu fada aji cikin unguwar da sai
ka isa wane zaka mallaki gida a cikinta cikin birnin tarayyar abuja.

Ba gidan kawai ba,unguwar kanta sai kabi matakai daya bayan daya
kafin ka samu nasarar shigarta,bayan kuma ka shiga din zai zame maka barazana
hanyar shiga JADDA VILLA. Birnin da ya shiga bakunan manyan masu kudin da suke
ganin wuyansu yayi kauri a duniyar naira.....birnin daya girgiza zukatan al'umma da
dama ciki harda manya manyan masu kudi na qasata dama qasashen duniya gaba daya.

Manyan gate gate guda biyu da matsakaici guda daya dukka saika wucesu
kafin kakai ga shiga BIRNIN JADDA kaman yadda aka rubuta daga cikin gidan gate din
farko.

Daga can cikin daya daga cikin gidajen dake cikin jaddas villa
din,cikin tsakiyar wani qawataccen courtyard da aka shimfida hikima wajen gini da
tsarinsa. Qawatattun shuke shuke ne masu dauke da mabanbantan furanni masu launikan
dake kiran butterflies zuwa garesu,daga qarqashin shukokin wata 'yar qwarya qwaryar
qorama ce ta zamani da aka qirqireta saboda wucewar wani ruwa me tsananin hasken da
kake iya hangen wasu irin mulmulallun stones masu daraja da tsada dake zuwa a oval
shape,amma suna da nau'in kaloli daban daban,kaman yadda madaidaita da qananun
kifayen dake yawo a ciki suke da wadannan launikan.

Wasu irin Kujeru ne sirara masu taushi aka qawata courtyard din
dashi,wadanda suke farare qal,kaman ba'a tsoron kai kawon yaran da gidajen suka
mallaka,yaran da suka tasamma rai ashirin da shida.

Zafin rana ko sanyi duka basa rabar wajen,guri ne na musamman da
kowanne gida daka cikin gidajen jadda villa aka tanadar dashi bisa tsari na
musamman dake iya daidait weather na wajen. Idan zafi ne weather wajen na fidda
iska me kyau da dadi,idan sanyi ne weather din wajen na bada temperature da zata
dace da yanayin da mutum yakeso.

Saman daya daga cikin kujerun dattijuwa anni ce,sanye da wata
sassauqar riga mara nauyi ruwan madara,wadda take hade da hijabinta asalin saqar
qasar Indonesia.

Daga gabanta kuwa yara ne matasa maza da mata kusan guda biyar,masu
kamanceceniya da juna,wasu kamanninsu sun fita sosai......wasu kuma kamanni ne na
baya baya. Daga gefan daman annin wasu yara ne guda biyu da duka duka shekarunsu ba
zasu haura takwas da tara ba,dukkansu share hawaye sukeyi fararen fuskokinsu sunyi
jajur.

"Kowa ya gama bayaninsa?"ta fada tana duban fuskokin su daya bayan daya. Da fari
gurin shiru ya dauka kafin daga bi sani,ta sake bin fuskokinsu da kallo tana sake
maimaita tambayarta. Kai suka gyada daya bayan daya.

"Da kyau" Ta fada cikin cikakkiyar nutsuwarta dinnan tana ajiye littafin hallul
masa'eel dake hannunta a gefe.

"Ameen" Ta kira sunansa kai tsaye. Yaro da yaci sunan muhammadun ta hanyar fadin
gaskiya akan komai da aka tambayeshi,koda hakan zai ja masa duka......yaron da
kusan halayensu suke kamanni iri daya dana MUHAMMAD SAUBAN(Ku ajiye wannan sunan a
next novel nawa idan rai yakai manaπŸ˜„πŸ˜„). Sauban din da shike binsu muhammad ameen
da ahmad amaan.......amma halayensa sak irin na mahaifinsa......halayensa sak irin
na ameen......shekarunsa duka duka basu wuce goma sha biyu ba......amma wani irin
girma da dattako gareshi.

"Me ya faru ameen?" Anni ya qarasa tambayarta. Bayani yayi mata na iya abinda ya
sani,ya qara da cewa.

"Amma a gaban sauban akayi.....ki tambayeshi". A nutse ta waiwaya ga sauban
din,wanda yake zaune shi daya saman kujerar da babu kowa kusa dashi. Ita kanta
kujerar tayi dan nesa kadan dasu,kunnuwansa manne da headphones wanda ko daga nan
kana iya jin sautin qira'ar qur'ani na fitaccen shaik dinnan wato maheer
almu'aiqaly.

Duk wanda yasan sauban ya sanshi da yawan sauraren karatun shaik
maheer duk sanda yake kebe shi kadai,wannan ne anni take kyautata zaton sanyashi ya
zama na daban cikin 'yan uwansa......hasken alqur'ani kuma take tunanin ya qara
sanyashi me tsananin nutsuwa,duk da tarin zuciya da yaron yake dashi.

"Sauban" Ta kirashi tana yafitoshi da hannu. Kallo daya ya yiwa annin ya saka
hannunsa ya cire headphones dinsa sannan ya taso ya qaraso wajen




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
__________________________

*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*

*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*πŸ˜‚πŸ˜‚

Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*

*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*

*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin
aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ
wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
08103155915

_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 172

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
172


"Me ya hada arham da ahsan?". A nutse ya zube kyawawan idanunsa masu
girma kaman na mamanshi akan dukkaninsu,sai ya matsa a hankali ya zauna gefen anni.

Baiji tsoron idanun kowa ba ya zauna ya yiwa anni bayani filla filla
har yakai qarshe.

" Haka akayi?" Ta sake tambaya,dukka wajen ba wanda ya musa banda hilal da yayi
shuru. Maida dubanta tayi ga hilal.

"Allah yana cewa cikin qur'aninsa,yaku wadanda kuka bada imani da Allah.....idan
fasiqi(mutum)yazo muku da labari,to kuyi bincike,gudun kada ku afkawa wasu mutane
bisa jahilci(rashin sani dalilin rashin bincikenku).saiku wayi gari kuna masu
nadama.......a duk sanda wani mutum yazo maka da labarin anyimin kaza,ko wane yayi
maka kaza,ko kaza ya faru,dole ne akan musulmi ya nemi hujja ko dalili na abunnan
ya faru,dole ne......muna da wata dabi'a ta saurin yanke hukunci,da daukan zance
daga bakin mutumin daya fara zuwa mana da labarin wane yayimin kaza,wane ya batamin
ko yayimin ba daidai ba.....nan da nan wannan daya fara zuwa da labarin saimu dauka
shine me gaskiya,bisa jahilci irin namu na neman jin ba'asi daga bakin wani
sashen,wanda muddin zaka kasance mutum irin wannan a rayuwarka,za'a yita sanyaka
batawa da mutane masu daraja da kirki.....zaka yita fada da mutanen da basuyi maka
komai ba.....za'a sanyaka ka yita yanke alaqa da mutanen da alaqarku keda matuqar
amfani a duniyarku da lahirarku.......wannan ba halin musulmi na kirki bane a
matsayinka na babba hilal.....ba kuma dabi'ar qwarai bace.....ba dattako sam a
cikin ta,dukkaninku daga yau na horeku da zama masu bincike".

"In sha Allah anni" Ya fada yana saukar da kansa qasa. Waiwayawa tayi ga yara biyun
dake gefe tana dubansu.

"Faarees da ra'ess ya tabbata kunyi qarya.....ku bawa Aadeel haquri,sakamakon
qaryarku kuma wannan satin gaba daya kada naga uniform dinku a wash room,da kanku
zaku wankesu duka satin nan.....sannan idan ummenku ta dawo......kune na qarshen
zabar tsaraba har sai kowa ya dauka nashi" Ta fada tana nunasu da yatsa.

Haqurin data buqata suka juya suna bawa wanda ake kira da Aadeel din
haquri,ta kallesu daya bayan daya still tana cewa.

"Ku kyautatawa junanku......kyakkyawar mu'amala itace mutum......girmankai na
shashasha ne maras wayo.....hassada ta maras rabo ce,don tana cinye kyawawan ayyuka
kaman yadda wuta takejin yayi.......shi kuwa sharri dan aike ne,daga inda aka
aikashi duk daren dadewa nan zai dawo......alkhairi kuma danqo ne baya faduwa qasa
banza.......komai dadewa ka shuka alkhairi shi zaka girba,kaman yadda komai dadewa
idan ka shuka sharri cuta ko ha'ince sai ka girbeshi.....kyakkyawar dabi'a jari ce
da babu kamarta,wadda duk dukiyar gidanku bata isa ta siya maka ita ba......hakanan
duk talaucin gidanku idan ka sameta kaiba talaka bane har gaba da abada".

Ire iren kalmomin kaka ta gari kenan a duk wani zama da zai hadata da
yaran,bakinta sam sam baya gajiya da furta wadannan kalmomin a kansu,har sun fara
haddacesu tun basusan ma'anarsu ba,zuwa yanzu kuma wadanda suka fara girma a
cikinsu sun haddacesu tas a kansu.

Basu fita a wajen ba saida kowa ya gaisa da kowa,kowa ya koma yanayinsa
na dazun sannan. A sanda suke fita a lokacin sauban ya koma inda ya taso,ya maida
headphone dinsa saman kansa yayi playing karatun yana ci gaba da ji hadi da lumshe
ido.
Kammaninsa da dabi'unsa kamar babansa,duk wani harka ta hayaniya ko
fada babu shi a ciki,kaman ya yiwa kansa rigakafi daga fushi da zuciyar da yasan
yana da ita.

Dauke kanta anni tayi daga inda yake murmushi yana subuce mata. Tana ji
a jikinta anya sauban din ba shine wannan HASKEN da take gani tsakanin iyalinta
ba?,wannan mai riqon addinin ma'abocin cikakken ilimi daya haura na saura?.

"Allah kayi mana zabi da mafita mafi alkhairi" Ta fada a nutse tana jawo hallul
masa'il dinta tana dubawa.

Tsaiwa Amaan yayi yana hango abokin tagwaitakarsa wato muhammad
ameen dake fitowa daga sassansu. Sanye da fararen kayan da aka yiwa ratsin baqi sak
irin kayan dake jikin Amaan din.

Shima gunsa ya nufo kai tsaye yana dubansa.

"Abbee fa ya shigo yanxun......kuma naga ya shirya.....ina kuma kyautata zaton
ummee zaije daukowa daga airport......na tabbatar dukkaninsu sun manta da yaune
wedding anniversary dinsu,15yrs" Ameen ya qarasa fada da faffadan murmushi daya
qara masa kyau,yana kuma d'age dukka girarsa sama.

"Na tuna......akwai wani abu ne?"

"Yes" Ameen ya fada ya fada yana dariya.

"Ya kamata muyi wani abu,yadda naga abbee yana wani shiryawa yanata duba mirror
kaman wani dan saurayi,dolen saiya burge duniyarshi". Dariya suka saki lokaci
daya,amaan yace.

"Babu ruwana idan ummee ta jika.....let's go,mintunan zuwanshi da dawowarsa basu da
yawa" Hannun juna suka riqe suna hirarrakinsu,wanda kana kallo zakasan akwai
shaquwa da qaunar juna me tsananin gaske.

Ita kadai yau take zaune saman wheelchair din nata,kusan awa biyu
kenan. Mutum daya take sanya ran shigowarsa kaman yadda ya saba......yaro guda
dayan da take mamakin yadda yafi kowa qulafucinta a gidan da qoqarin kula da duk
wani motsi nata......yaro guda dayan da ita kanta yafi shiga ranta sosai wato
sauban.

Jifa jifa tana jin motsin yaran,guje gujensu kasancewar weekend
ce.....amma yau ko wasan kaka da jikan data jima tana nuna musu bataso ba wanda ya
leqota yayi mata,duk sai ta jita ba dadi.

Sabreen ce ta fado a ranta,ba yadda za'ayi duk wuya.....duk runtsi idan
tana nan ta barta ta zauna shuru haka,koda kuwa bata buqatar komai zata umarci biyu
ko uku cikin haihuwa yara rai goma da Allah ya bata wani yazo ya zauna kusa da ita.

Wani abu ta hadiye,karon farko da taji tana dokin ta dawo daga tafiyar
kwanaki ukun da tayi zuwa qasar saudiyya.

Daidai nan yayi sallama,sanye da dinkin kaftan da aka yishi da wani
fari qall din yadi me daraja. Dinkin babbar riga ne da 'yar ciki dinkin da aka
zamanantar dashi,ya kuma sake maida fuad din kaman wani qaramin matashi.

Baiyi amfani da hula ba,sai farin rawani daya nada saman farar hular
kanshi,sai ya fito kaman wani basaraken malami.
Duk da ya dubata dazun yanzun bai gaza wajen dawowa wajenta ba,ya
tsugunna ya gaidata,ta amsa masa da sautin da ba kowa yake iya fahimtar abinda take
fadi ba idan ka dauke shi da Sabreen da suke iya fahimtar kusan komai tace.

Nasarar fara fitar sautin nata ma gaba daya ya samo asali ne daga
Sabreen,wani umra da sukaje,ta samu daman tara roba wajen indararon ka'aba ta tari
ruwan saman dake sauka ta saitin wajen,ta kumayi tofin addu'o'i sosai data samu
daga wajen mallam,ta durfafi bata.

Wani abu ne daya tsayewa maamah din a rai,har yau ta kasa mantawa da
abun,duk da sai bayan nasarar ta samu takejin daga ina ruwan ya fito,basu gaya mata
ba gudun kada taqi sha.

"Yau zata dawo?,daukota zakaje kayi?" Ta tambayeshi sanda ya miqe yana soma takawa
da murdadden harshenta.

A mamakance ya juyo yana duban maamah din,wai yau ita ke tambayar
dawowar Sabreen?,wani farinciki yana sauka a zuciyarsa ya gyada mata kai.

"Eh,saura mintunan kadan jirgin ya sauka".

"A dawo lafiya" Ta furta tana jin wani dadi yana mamayeta .

"Allah yasa" Ya amsa wata qwalla tana cika masa idanu. Yau maamah ke masa addu'ar
da

Please Login or Register in order to submit comment