You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai haqura ba.....shine zai fake da wasu abubuwa
wanda shi kansa ba kubuta yayi daga su ba.....yazo ya samu wannan matar da
qiyayyarsu ta jima da yin tsiro da jijiyoyi a cikin jikinta. Takai qarshen maganar
sanda take bude idanunta saman fuskar bibo.

Haduwa idanunsu sukayi waje daya da nata,ta juya qwayar idanunta tana
watsa mata wani kallo

"Ki dain kallona da wadannan tsayyayun idanun naki na rashin kunya masu kama da
idanun mage.......kai ya kamata ka tsaya a kanta saboda tana jawowa bawan Allah
zagi,wanda ya jima da mantawa ya zauna a duniyar.....amma ina kyautata zaton kullum
ta Allah sai mala'iku sun tadashi zaune sun nuna masa qazantar da d'iyar cikinsa ke
aikatawa. Ya rasu yabar yara sama da goma sha takwas amma ba wadda ke hana masa
kwanciya lafiya a kabarinsa sai ke?,ai wallahi Allah wadai da haihuwar d'iyoyi
irinki.....indai haka haihuwar take gwara mutum ya zauna a haka" Tana maganar tana
jujjuya hannunta guda daya gami da yarfeshi,idanunta a kafe saman fuskarta,kaman
yadda itama tunda ta fara maganar ko sau daya bata dauke dubanta daga kan bibo ba.

Maganganun nata sunkai mata iyaka,tana jin ta gama daukar iya
abinda zata dauka a iya wunin yau,saboda haka a nutse ta sauke qafafunta qasa ta
miqa hannunta ta dauki handbag dinta ta miqe tsaye tana gyara rolling din
mayafinta

"Fita zanyi,kuma ina da buqatar na kulle mana dakin kafin na fitan,idan ba damuwa
ko zamu koma tsakar gida mu qarasa maganar a can?"

"Kaji ko?......dama ai na sani,babu wani sauran wanda take gani da kima a
duniya.......yau koda fadima zata dawo duniya bata isa ta juyata ba bare alhaji"
Tayi saurin cafe zancan.

Wani irin juyowa tayi gareta ta zube mata manyan fararen idanunta

"Kaman bakiji me nace ba ko?,nace muje tsakar gida mu qarasa......bankai ga furta
cewa banda lokacin sauraro ba" Ta mata maganar dalla dalla tana kallonta.

Sosai bibo ta kafeta da kallo,har yanzu babu abinda zai
sauyata......wannan rashin shakkar da rashin tsoron suna nan rubuce baro baro cikin
ayyukanta da dukka motsinta,dakiyarta da shariyarta da daukan abu me zafi ta
wulwulashi ta sauya masa mizani idan taso.

"Idan ta fito kawu qofar kawai zakaja jam lock din zai shige,ka sameni a qofar gida
muddin baka wuce minti biyar ba" Tayi furucin sanda take takawa zata fice a falon
tana riqe da vail din abayarta daya zame tana qoqarin mayar da rolling dinta yadda
yake.

"Tashi muje na sameta a waje din inji da wacce hujjar zata kare kanta kuma" Ya
furta dukka jikinsa na nuna zumudi da qaguwar yaga ya bita.

Da kallo bibo ta bishi tana daga zaune a kujerar ba tare data motsa
ba baqinciki yana kasheta. A yau tana jin kaman ta tashi ta rufe rufa'i da duka.
Yau ya tabbata mara amfani kwata kwata a garesu gaba daya.

"Ko nayi gaba kya rufe musu dakin?" A zafafe ta miqe tana gyara daurin dankwalinta

"In zauna inyi me a nan?,Allah ya sawwaqe,ai ni tawa son zuciyar bai fara sauka har
takan kayan haramun ba" Ya jita sarai,ya kuma san da biyu take maganar,saidai a
yanzu baya jin yana da lokacinta,dukka tunaninsa yana ta'allaqe akan sabreen. Yasan
halinta sarai,muddin ya haura mintunan data dibar masa,yayi imanin da gaske zai iya
zuwa ya tarar ta wuce din abinta.

Tana rungume da hannayenta sanda take tsaye a qofar gidan nasu ta bashi
baya. Fuskar nan dake shimfide da wani irin kwarjini yau din cakude take da ninkin
rashin fara'a da walwala na tun asali da aka santa dashi. Har tsakiyar zuciyarta
takejin wani abu yana tsikarinta duk da yadda iskar dake yawo sararin subhana ke
kada doguwar riga da dan mayafin saman kanta tana watsa daddadan qamshin turaren
dake tashi a jikinta. Turaren da ita kanta yake sanya mata nutsuwa da kwanciyar
hankali,dadinsa ya sanya ta zabeshi a matsayin turarenta na dindindin,duk da batayi
tunani matsayinta zaikai a nan kusa ta mallakeshi ba.

Ta kalli agogon hannunta,yaci mintuna hudu cikin minti biyar din data
bashi,don haka ta fara takawa sannu a hankali tana matsawa daga gaban gidan nasu.

Tun batayi nisa ba ta jiyo taku da kuma muryar kawun nata,bata da
buqatar kallon fuskarsa ko doguwar magana ta hadasu,buqata gareshi zata
sallameshi.....kamar yadda tun tale tale.....kaman yadda tun can baya bashi da
amfani a garesu a yanzun ma bata tunani akwai wani sauran amfani da yake dashi a
rayuwarsu,don haka ta sabule jakarta,ta zuge ta zaro wani abu daga cikin kudin da
yayi saura a ciki ta dunqule a hannunta tana jiran isowarsa

"Ke sabreena......sabreen" Ya hada da qwala mata kira tamkar ya bata bashin kudi
tana kuma shirin gudar masa dashi. Ranta ya sake baci,ta tsani kwakwazo,a banza ma
idanun 'yan unguwar da dukka kunnuwansu harma da hankulansu suna kanta,kowanne
motsi ko taku nata a biye suke dashi,sauraro suke.....jira sukeyi na samuwar dukkan
wata dama da zasu samu abun magana a kanta. Wannan ya sanya tadan saurara daga
tafiyar da takeyi tana dakon isowarsa. Ko a sannan tana iya ganin idanun tsirarun
mutanen unguwar da suka samu sararin fitowa da safen kamar ita yana karakaina a
kanta.

Irin wannan kallon nasu gareta ya zama tamkar jarrabi ko masifa cikin
rayuwarsu. Akwai abubuwa da yawa tasan da akeson gaya mata amma babu wannan fuskar.
Bataga dalilin zallar rashin adalci irin nasu da suke gwada mata ba suke kuma
gwadawa rayuwarta ba. Sun sany hannu dukka da qafafunsu sun tankwabeta sun kuma
tankwabe rayuwarta a sanda take da tsananin buqatarsu......a yanzu kuma data
yankema kanta bata da buqarsu.....a sannan su kuma suke qoqarin dawo da ita su
dankwafar da ita.....suka kuma fidda makamansu da harsunansu wajen illata mata
gangar jiki da zuciya.

"Me na samu?" Ya iso gareta yana tambaya sanda motar da take da tabbacin waye a
ciki ke dab da isowa inda take. Kowanne mutun da zatayi mu'amala dashi ko kuma tayi
mu'amala dashi din......sau daya tak take masa wani karatu a taqaitaccen
lokaci.......fahimtar waye kai?......meye qudurinka.......meye motsinka?.....mene
manufarka......da sauran dukkan wani abu daya shafi rayuwarka yana zama RUBUTACCE
cikin shafin qwaqwalwarta. Bata fiya manta abu ba,haka bata missing target saidai
idan bata nufaci abu ba.
Ta baya ta miqa masa kudin sannan ta fara takawa zuwa ga motar da
tuni ta iso inda suke harma ta samu wajen tsaiwa.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 17


daga inda yake a zaune din yakejin kamar gilashin window din motar ya
masa shamaki daga kallonta duk da yadda yake tarwai yake kuma iya baka daman gano
komai dake ta wajen motar......duk da haka yana jin kamar ya rage ma idanunsa
armashin kallonta,don haka ya kasa haqurin isowartata,ya sanya hannu ya sauke dukka
gilashin nasa qasa.

sau daya tak ta taba ganinsa ido da ido,amma ta haddaceshi
tsaf,tun daga abun hawansa har zuwa halayya da kamanninsa.......

Kakkaura kuma faffada da zaka iya kiransa me jiki saidai bai cancan
ba. Maabocin iya ado sosai da murza hula ta zauna a kansa kamar shi yake saqa ma
kansa ita. Yadda turarensa da shigarsa keda kyau da tsari haka ma kalaman
bakinsa,saidai kash!.....daidai da wucewar daqiqa guda bata taba jin wani abu me
kama da SO K'AUNA KO BEGE nashi ya tsartu a ranta ba.

Waishin mcikina meye SOYAYYA ne?. Ita kanta jerin kalmar SOYAYYA da
yadda mutanen duniya suka daukaketa na daya daga cikin abinda ke sanyata dariya
koda bata shiryawa hakan ba. SHIRME shine cikakkiyar ma'anar da take ganin yafi
dacewa da a kirata ko kuma CUTA,idan akwai sunan da yafi haka lalacewa ma a nata
ganin daidai ne a kirata da wannan sunan.

Yadda yake tsareta da kallo ya sanya qirjinta ya dinga suya duk
kuwa da cewa ta saba da irin wannan shegen kallon. Kwarjininta na daya daga cikin
abinda ya sanya take tsira daga guba da dafin MAZA duk kuwa da cewa ita da kanta
take tsalle ta afka tsakiyar tarkon bisa tsananin lissafinta,ta kuma samu sa'a da
nasarar zame kanta cikin SALO da kuma qwarewar iya wasa.

Da hanzarinsa ya fito ya zagaya don bude mata qofar motar,hakan ya
bawa kawu dake lafe yana kallon komai qare masa kallo.

"Iya shaddar jikin yaronnan kawai ta isheni jari wallahi,wannan tsinanniyar
yarina,yanzu meye aibun wannan da ba za'a aureshi ba?" Ya tambayi kansa da kansa
yana naniqe da kudin hannunsa.

Idanunsa ya aza a kanta bayan ya bude mata motar,sai ya sakar mata
murmushi,tadan lumshe ido tana qaqalo nata murmushin cikin dauriya da son maida
masa. Gefe guda zuciyarta na cike fal da qarin wani mamakin akan D'A NAMIJI. ta
tuna kalamansa akan matarsa dazun dazun nan,amma a yanzun gashi a gabanta ita kamar
zai narke. Ta yaya zata yadda tayi aure a duniya?,ta yaya zata bari zuciyarta ta
kamu da soyayyar wani namiji?,yaya za'ayi ta banzatar da lafiyar zuciyarta cikin
soyayyar wani?,soyayyar halittar da babu tausayi ko jin qai a tare dasu?,halitta
mafi son kai cikin halittun duniya gaba daya?,halitta me tsananin mugunta da son
cutar da halittar mace 'yaruwarta?.

Ba zata iya sadaukar masa da murmushinta na dogon lokaci ba,duk kuwa
da cewa fake smile ne,don haka ta zame jiki ta shige cikin motar ya mayar ya kulle
yana sauke ajiyar zuciya. Yana jin duk duniya ba wanda ya kaishi sa'a a yau din.
Yana jin kamar duka ranar tashi ce.
A kujeran driver ya zauna yana qoqarin tayar da motar amma duka ido da
hankalinsa yana kanta

"Ina muka nufa my life?"

"My life?" Ta sake jaddada maganar a ranta

"Ko ina ya baro matarsa ta sunna da har ita ya danqara mata wannan sunan?" Wannan
ba baqon abu bane a wajenta,saidai har yanzun mamaki da lamarin maza bai gama
sakinta ba.


"SAMHG store" Ta amsa masa a nutse tana gyara agogon hannunta daya goce

"An gama ranki ya dade" Ya fadi cikin zumudi yana tayar da motar.

Sun jima akan hanya yana tauna abinda zaice da ita,don a taqaitaccen
saninsa da ita.....mutum ce me matuqar tsari,nutsuwa da aje komai a bisa gurbi da
muhallinsa. Bayaso ya kwafsa kaman waccan karon,bayaso damarsa ta sake kubce
masa,duk da cewa har kawo yanzun baisan me ya aikata daya rasa wancan damar a
wancan karon ba.

Yaji babu dadi ainun saboda ya qwallafa rai sosai a kanta. Ta yiwa
zuciyarsa wani mahaukaci kamu a ganin farko. Yayi tsammanin kudinsa da ajin mataki
na rayuwa zai saya masa ita cikin qanqanin lokaci,sanin da ya yiwa 'yammata kenan a
yanzun,ballantana ita dake da kyau da aji irin wannan.

Sanda yake wannan tunanin nata nazarin da karatunsa duka a kansa
yake. Yadda yaketa rejecting kiran dake fama shigowa wayarsa a jejjere. Duk kiran
da zai shigo sai ya katseshi. Tuni hankali da kuma jikinta ya bata wanda ke kira.

Idanunta tadan lumshe,koda yaushe su dinne dai,cikin
wahala,qasqanci,tozarta da kuma wulaqanta zaune cikin gidajen aure. Ko meye kuma
zai fito yaje yazo su din yake afkawa.

"Zan iya cewa wani abu?" Ya tambaya a ladabce yana murza steering motar cikin
qwarewa

"Kafin sannan ya kamata ka daga wannan kiran ko?" Ta fada idonta akan fuskarsa.

Motsawa kadan yayi yana duban wayar ta qasa idanu,bai zaci ma ta lura da
hakan ba. Haushi ya soma kamashi akan kiran da take masan babu qaqqautawa. Yasan
zancan gizo baya wuce na qoqi,tunda bai jima da fita a gidan ba,yasan kuma abinda
ya fito ya baro a gidan

"Tarin damuwa ce da matsaloli kawai take dauke dashi" Ya furta yana jan siririn
tsaki.

Har tsakiyar ranta taji saukar maganar,ta lumshe ido kadan tana
budesu. Yana nan din a haka,yana nan yadda ta karanta. Tayi qoqarin tureshi daga
shiga layikanta,tayi qoqarin hanashi shiga cikin tarkonta don baya cikin irin mazan
data zana bisa layi da gurbin rayuwarta,taso ta barshi ya samu me hukuntashi a
gaba.....amma tunda har ya sake dawowa cikin rayuwartata cike da karsashi da
zumudi,to tayi imani hukuntashi yana cikin qaddararta ne. Ba kuma zata qyaleshi
ba,a wannan karon saita hukuntashin yadda ta saba hukunta maza irinsa. Maza irinsa
basa tsira daga tarkonta......basa tsira daga kamunta,hakanan basa tsira daga
hukuncinta.
Cikin salo na dabarar da yake gani kaman ba zata gane ba ya latse
wayar,ya kuma jefo mata maganar da tafi damunsa

"Hanan.......wannan karon bazan bari ki kufcemin ba"

"Nima bazan bari ka tafi ba" Ta furta,a bakinta bisa mizanin ma'ana qwaya daya tak
da hankali zai iya fahimta,amma kuma an aje ajjiyayyar ma'anar da ake nufi da
maganar can qasan zukata.

Wani irin dadin daya sabbaba masa lafiyayyen murmushi ya ziyarceshi.
Bai taba kawowa ko kusa a ransa samun wannan gwaggwabar nasarar a kurkusa haka
ba,amma kuma,sai wani sashe na zuciyarsa ke gaya masa

"Duk kyau ko matsayinta zata sauko......a yanzun fa mata ke neman mazan aure idanu
rufe" Hudubar data shiga kunnensa kenan,kuma ya yarda da hakan dari bisa dari.

"Amma hanan banga alama ba......bansa inane mazaunin da kike rayuwa ba,gida unguwa
da sauransu"

"Gaggawar me kakeyi?,kada ka samu damuwa" Ta amsa masa tana jin ya ginsheta gaba
daya,tana jin ta damu qarshen zamansu yazo,ta qagu su isa SAMHG store ya ajeta ya
bata sarari.

A hankali ya kutsa motar babbar harabar kantin saida dukkanin kayan
buqatar rayuwa,wanda zaifi kyau ka kirashi da kasuwa a sauqaqe amma kuma a
zamanance. Ba abinda basu hada ba na kayan buqatu,tun daga tufafi zuwa kayan
masarufi. Wajen nada matuqar girman da idan ka kirashi da duniyar siye da siyarwa.
Girmansa ya sanya yake da mashigu daban daban da kuma guraren fita mabanbanta.

Cikin tafkekiyar harabar wajen ya aje motarsa,ya kasheta cikin
mutuwar jiki da kasala yana waiwayowa inda take zaune tana qoqarin rataya jakarta
gami da daukar wayarta ta riqe wadda ke aje saman cinyarta.

"Idan ban damuwa zan dan tayaki tattaki zuwa ciki......don naga wajen kamar cike
yake da maza da yawa......ni kuma ina kishin na barki ki fita ke daya a kallemin
ke" Ya furta cikin kulawa da wani irin narkakken so dake ragargazar zuciyarsa.

Da wani sassanyan kallo ta jefeshi,qawataccen murmushin nan dake
qawata fuskarta da kuma labbanta ta sakar masa. Ta rausayar da kanta gefe tana juya
idanunta. So take ta sallameshi a iya haka,bata buqatar doguwar damuwa. A lokaci
irin wannan da takai qarshen mission dinta,ko fita unguwa ba kasafai take damunta
ba sai idan buqatar haka ta taso. To amma hakanan taji akwai buqatar ta fita
din,akwai kuma buqatar ta fita tayi musu siyayya.

"Baka da damuwa akan duka wannan......wannan hanan din ba komai idanunta ke kalla
ba ballantana su burgeta" Ta bashi amsa a nutse.

Murmushi ya saki yana qara narkewa a sonta,yana ji cewa zai iya yin
komai don ya mallaketa,yana jin cewa muddin ya sake barinta ta subuce masa a wannan
karon ya tafka babbar asarar da bazai iya maida madadinta ba,baya jin ma zai bari
hakan ya faru dashi sam sam.....kai koda tuna hakan na iya faruwar bayason yayi.

"Na ga zahiri......na kuma tabbatar wannan halittar ta daban ce......gamu cikin
neman sa'ar kasancewa da ita" Ya fada yana lumshe idanu. Kai ta kawar amma tana
murmushin yaqe. Ya numfasa bayan ya gama qare mata kallo cikin shauqi ya dauki
wayarsa dake aje tun sanda ya maidata silent ya bude.

Tarin miscall a qalla guda goma kyawawa daga gareta. Ya jawo
maballin sama ya sharesu yana sakin tsaki can qasan ranshi tare da wucewa mobile
app na banking da yake ajiyar kudadensa.

Sosai ta jingina da makarin motar idanunta a lumshe sosai,sai kayi
tsammanin bacci ko kuma gajiya ne sukayi mata yawa,saidai a cikin biyun duka babu
ko daya a ciki.

"A taimaka a karantomin account number na dan bada wani tukuici" Idanunta ta janye
daga saman wayar nasa,saita tashi ta zauna sosai tana dan sakin murmushi

"No need" Ta amsa masa a yangance kaman yadda ta saba magana

"Please.......ba wani abu bane me yawa.....just tukucin bani damar ganinki da
kikayi a yau ne" Bata sake ce masa komai ba,sai ta zura hannunta cikin
jakarta,wani dan siririn card me ruwan zaibar gold ta ciro ta aje a gefansa. Ta
dauke kai tana qoqarin bude murfin motar wanda ita kanta tasan ba zata budu ta
sauqi ko dadin rai ba......ta kwana da sanin meta aiwatar mata.

Cikin qasa da minti daya taji ya furzar da iska daga bakinsa gami da
cewa

"Done.....ina fata zakiyi appreciating"

"Why not?,godiya me kima......godiya nake qwarai......but motarka tana nema ta
riqeni fa"

"Da zatayi hakan data taimakeni ai" Ya amsata yana sake lafewa jikin kujerar.
Kyawawan sexy eyes dinta ta waro waje kadan,sai kuma ta daga hannunta tana duban
agogo

"Akwai alqawari da nayi,bana so kuma na saba......idan ka sani na saba
kuma......next time kafin na baka daman sake haduwa dani....." Katseta yayi yana
dariya ta hanyar hada hannayensa biyu waje daya sannan ya saukesu ya juya yana buda
side dinsa

"Lemme check meye ya riqemin amaryata haka".

Da lumsassun idanunta ta bishi da kallo har zuwa sanda yake zagayawa
gaban motar zuwa daya side din da take zaune. Yayi dukan dabarunsa amma hakan
baiba,don haka ya zagayo yana fadin

" Bansan me yake faruwa,lafiya lau qofar yake,bari nasa a duban.....am really
sorry" Ya sake apologizing yana hade hannuwansa.

taka Kai kawai ta daga masa tana irgen lokutan cikar target dinta.
Cikin saa kuwa ya juya ya fara takawa yana barin wajen,wanda hakan ya bata damar
janye kallonta sannu a hankali daga kansa,ta kuma maida saman wayarsa dake ajiye a
wajen tana bada haske,tabbacin yunqurin hanata komawa key yayi daidai kenan,saita
katse kiran da takeyi daga tata wayar zuwa tasa don sanya wayar awake.

A nutse ta jawo wayar ta wuce zuwa ga maballin kira.

Tarin miscall dinne kuwa ta samu kamar yadda tayi zato,dukka kuma
daga number dake ajiye cikin wayar da sunan MOM SUHAIL.

"SUHAIL" Ta ambata a fili,idan har bawai ta manta ba suhail din shine sunan first
born dinsa kamar yadda T.j ya tabbatar mata.

Wani irin tausayin matar da batasan ko wacece ba ya fara ratsa ta.
Tana shirin karkata akalar binciken nata zuwa wani sashe na daban saqon SMS ya
shigo wayar.

MOM SUHAIL kamar yadda yake a rubuce ta bangaren kira. Bata tsaya dogon
jinkiri ba ta bude,gajeran saqo ne kamar haka.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 18


_Nayita kiranka baka dauka ba,kome meye mukayi da kai kafin ka baro gida ai ya
kamata ka tsaya kaji dalilin kiran da nake maka babu qaqqautawa,bayan ka fito ciwon
suhail ya tashi,a yanxu haka muna asibiti,amma babu ko sisi a hannuna,baka barmin
komai ba,already kuma account dina yana buqatar naje banki na gyara bare nayi
hidimata da kudina yadda na saba_.

Wani abu me tauri taji ya tsaye mata a wuya,ta zura hannu a jakarta
ta ciro wayarta,tanason taga nawa ita ya kashe mata?,nawa ya saka mata alhali ko
sisi matarsa bata amfana dashi ba?.

Naira dubu dari ta tarar. Wani matsiyacin tsaki ta saki,cikin
dukkan arziqinsa ya rasa da meye zaiyi mata kyauta sai naira dubu dari?. Bata tsaya
batawa kanta lokaci ba ta sauka ta koma mobile app dinsa da bai jima da fita a kai
ba.

Daga password har username dinsa fes cikin kanta,tamkar hadaka ko
gamayya sukayi dashi wajen creating dinsu a sanda zai bude manhajar. Cikin qasa da
second goma komai ya bude,tarin miliyoyin kudaden dake kwance cikin account din
nasa suka bayyanarwa idanunta,sai ta koms ta jingina da kujerar motar tana
kallonsu,kamar ma bata tsoro ko shakkar dawowarsa.

Numfashi take fitarwa d'ai d'ai qirijinta na sake quntata. Tarin
zallar rashin imanin maza yana sake tabbatar da kansa a zuciyarta.

"Yana da wannan kudin ya fita yabar matarsa babu ko sisi?,yana da irin wadannan
kudaden yabar yaronsa cikin halin ciwo?,yana da wannan kudin ya gaza siya masa abun
hawan da idan lalura irin wannan ta taso baya kusa zata kaisu zuwa ga asibiti cikin
gaggawa?.

Tsanar MAZA tsanar SOYAYYA da kuma tsanar AURE suka sake linkuwa
cikin ranta. Irin wannan shaidojin na gani da ido ta din saidai ta bada labarinsu.
Shi din ma ba komai bane a cikin maza......bata kuma san namiji na nawa bane shi
din da a yau xai shiga makarantarta.......a yau zata sanyashi ya koyi darasi kaman
sauran,saidai nasa darasin yazo ne a gaggauce saboda gamawa da babinsa da tayi,da
kuma dadewa da tayi da sanin shi din wayeshi?.

Beneficiaries dinsa ta duba,cikin sa'a tun batayi nisa ba taci karo
da sunan da yayi daidai da sunan matar
*ameena mu'azzam*.

Kai tsaye ta saka amount din da yayi mata ta kuma karkatasu zuwa ga
account din.

Daidai lokacin data hangi tahowarsa,ta daga hannunta ta zare wania
abu daga jikin qofar,sannan ta maida hankalinta kan wayar kamar ba me wayar ne yake
dosota ba.
Hankali kwance ta koma ta goge alert massage din da kamfanin sadarwa
suka aiko,ta kuma koma zuwa ga email a gaggauce ta goge nashi tayi minimize ta
maida wayar mazauninta tana karanta sunan banking da yake amfani dashi,sannan ta
zaro tata wayar tana duba ma'ajiyar lambobi dake cikin wayar.

Sunayen dake ajjiye cikin wayar ta fara bi,cak ta tsaya saman wani suna
da yayi daidai da sunan banking nasa,ta danna malatsi na tura saqonni,ta kuma aika
da saqon a gajarce

"Done" Ta jefa wayar a jaka daidai sanda ya iso bakin window din suna sake yunqurin
buda motar.

Ja daya bakaniken ya yiwa murfin ya bude,sai ya waiwaya yana dubansa
cikin mamaki,wanda shima cikin manakin ya iso

"Oga ina tunanin kaine baka jawo ta da kyau ba"

"Kai amma nayi mamakin faruwar hakan" Ya matsa yana kama hannun motar ya matsashi
har sau uku. Mamaki yadan sake kamashi,amma kuma kiransa da tayi d nuryarta me
laushi ya dauke hankalinsa daga nan.

"Okay na gode to" Ya fadiwa bakaniken yana cirar wani abu a aljihunsa adan gaggauce
saboda kiran nata.



Please Login or Register in order to submit comment